Mansura ta ƙarashe maganar tana kallo na cikin kulawa.
Ɗago da fuska ta nayi, tare da sanya hannu na goge hawayen dake zuba a ido na, tare da ce mata.
"Mansura ki kwantar da hankalin ki, Ni sam ba cewa zanyi bana son sa ba, sai dai kawai ina jin abin ne, wani banbarakwai, wallahi Mansura ji nake tamkar a mafarki" na ƙarashe maganar ina ɗan murmusawa.
"Yes! wai Malika dan Allah da gaske kin amince da Yaya kamal?".
Murmushi nayi,tare da girgiza kaina ina faɗin .
"Kai Mansura meye kuma na wannan ihun?".
"Malika kenan, ba zaki gane bane, wallahi na zata sai kin sakamin ciwon kai kamin ki yarda" ta faɗa tana murmushi.
Nima murmushi nayi ban sake cewa komai ba, domin ni kaina nayi mamakin yanda farat ɗaya naji ya kwanta min a rai, kuma zuciya ta, ta natsu dashi, nida ba kasafai nake yarda da mutum ba, amma wannan ɗin daga ganin foton sa, naji zuciya ta tayi kyakkyawar bugawa daga cikin inda take ajiye a ɓargon ƙirji na, irin bugun da bata taɓa yimin ba, sai dai ina fatar hakan ya zama Alkhairy a gare ni.
A hakan muka cigaba da firar mu nida Mansura, wanda daga ƙarshe muka koma falor muka haɗe dasu Shamsiyya da Nadiya muna fira.
Duk da cewar ba yanda Mansura ba tayi ba akan na ƙarbi waya muyi magana dashi, amma sam naƙi, domin ni kaɗai ce nasan irin luguden da zuciya ta keyi, wani sabon al'amari nake ji a tare Dani, wallahi ganin hakan nake tamkar a mafarki, yayin da wani gefe na zuciya ta nake jin tsoro, domin a zahiri ni bana son Alaƙa da ƴaƴan masu kuɗi, wanda idan har ba ƙarya kunne na kemin ba, ji nayi Mansura tace min wai Yaya kamal ɗan gidan Ministan Shari'a ne.
"Yaya Kamal".
Na sake maimaita sunan afili ina murmushi.
Duk da cewar Mansura tana lura da duk wani motsi na a wajen, domin har cemin take yi wai sabon shiga! Nidai bana tanka ta saboda na lura abin nata harda sheɗanci a cikin sa.
Ana cikin haka saiga su Aunty Murja ƙawayen Aunty Fatima sun shigo da manyan kulolin abinci guda biyu, tare da faranti shima biyu.
Wanda da alama Shinkafa da miya ce suka yi tare da coslow, shine suka sanya coslow a faranti ɗaya, soyayyin kaji ma suka sanya su a ɗayan faranti.
Mukam muna zaune har suka shigo dasu tare da wucewa kitchen, ba wanda ya kula mu a cikin su, muma kuwa muka yi banza dasu.
Bayan munyi sallar La'asar, haka muka tashi nida su Mansura tare da share gidan Muka yi mopping ko'ina Sannan muka sanya turare a kowane lungu da saƙo.
Bamu jima da gyara gidan ba, saiga tsayuwar motoci a ƙofar gidan, Wanda hakan ne ya sanar mana da isowar su.
Nidai zaune nake shiru, na rafka uban tagumi, sai biyar su nake yi da idanu, ganin yanda suka fara gyare gyare, ba Mansura ba, ba kuma su Nadiya ba, dasu Aunty Murja ƙawayen Aunty Fatima, kai harma da Aunty Fatiman ita kanta, domin ba ƙaramin ado ta caɓa ba, tsadaddar atamface ta sanya ɗinkin fitet gown tayi kyau sosai, duk da cewar Mansura ta ɗan fita haske, sai dai ba sosai ba, domin ita kanta Aunty Fatiman farar mace ce.
Duk wannan abin da suke yi, ko motsi banyi ba, domin Ni bana yin abu saboda wani yayi, nakan tsaya akan aƙida ta ne kawai.
Har Mansura saida tamin magana akan wai meyasa ni bazan yi kwalliyar ba, sai kawai nayi banza da ita, amma da yake ita ƴar wahala ce shine ta bini har inda nake zaune tare da powder da soso, ta shafa min harda man leɓe, duk kuwa da yanda nake tirjewa.
Da sauri Mansura da Nadiya tare da Shamsiyya sai kuma su Aunty Murja suka nufi ƙofar falon, bayan sun feshe jikin su da tirare kala kala, sakamakon nocking ɗin su da muka fara jiyowa a wajen tare da hayaniya, kasancewar ƙofar falon a rufe take.
Ai kuwa sai yanga da karairaya suke yi, burin kowanen su bai wuce yaga abin son sa ba.
Nidai ban fito falon ba, nayi zama na a uwar ɗaka, nida Aunty Fatima, sakamakon jin da nayi zuciya ta na tsananta bugawa, Allah kaɗai yasan me nake ji a wajen, domin wallahi a matuƙar tsorace nake.
"Na shiga uku Ni Malika!".
Na faɗa ina rumtse idanu na, sakamakon jin da nayi Aunty Murja tayi sallama tana cewa Aunty Fatima ta fito wai ana neman ta a falor, aiko na susuɗa nayi shigewa ta toilet gudun kar tace sai na zo mun tafi falon a tare.
Babban mayafi ne a jikin ta, kanta a sunkuye, a haka ta Tako harta iso falon, wanda ƙamshin tiraren ta, shine ya fara sanar da zuwan ta.
Suka rangwaɗa guɗa wanda har saida amaryar ta rikice, yaya muktar kuwa ya taso cikin azama ya riƙe amaryar sa, abokanen sa sai tsokanar sa suke yi, wai ango kasha ƙamshi, shi kuwa yayi banza dasu ya mayar da hankalin sa wajen amaryar sa.
Uncle Ammar ne yayi wa Mansura raɗa a kunne wai ina nake? Ai kuwa ta tashi da sauri tana faɗin, bari naje na kirawo ta.
Da sallama ɗauke a bakin ta, ta shigo ɗakin .
Na ɗago na kalle ta, tare da amsa mata sallamar.
"Malika me ki ke jira ne haka? Gashi nan kowa ya fito falor amma banda ke" Mansura ta faɗa tana tsure ni da idanu.
Murmushin ƙarfin hali nayi, ina faɗin.
"Ba komai fa, kawai banɗaki na shiga, yanzun nan ne ma fitowa na".
Murmushi Mansura tayi tana kallo na, wanda bana buƙatar ƙarin bayani nasan ta gano lago na, tasan
Cewar fita ne kawai banso nayi, domin Ni mutun ce, wacce bana yawan yin fitsari, koda ace fita muka yi nida ita, to sai dai ita tayi ta yawon yin fitsari, amma nikam ko sau ɗaya ba zanyi ba, komai daren da muka yi kuwa, kuma bawai saboda bana son yin fitsarin bane, a a wallahi kawai dai fitsarin ne bana ji, amma fa abin mamaki daga zarar na dawo gida, tofa tun a ƙofar gida fitsarin zai tare ni, naji kamar zanyi shi a wando, ai kuwa da gudu nake zuwa banɗaki.
Dafa kafaɗa ta naji Mansura tayi, na ɗago na kalle ta, saita sakarmin murmushi tare da faɗin.
"Malika ki kwantar da hankalin ki dan Allah, insha Allah ba abinda zai faru sai Alkhairy, ki tashi muje kinji".
Murmushi nayi ina jinjina mata kai, na miƙe muka nufi falon a tare, ina ji kamar karna fita.
Lokacin da muka shiga falon, gaba ɗaya saina jini a wani takure, sakamakon yanda idanu ke yawo a kaina, duk da cewar ba wanda na kalla a cikin su, amma ina da tabbacin daga cikin masu min wannan kallon harda Yaya kamal!.
Na nemi guri a kusa da Mansura na zauna ina matsar waya ta, duk da cewar a zahiri wayar ce kawai a hannu na, amma a baɗini ban san ma me nake taɓawa a cikin ta ba.
Muna zaune ne gaba ɗayan mu a falon muna fira, har akayi kiran sallar magriba, Mazan suka tashi zuwa Masallaci,yayin da mu kuma matan muka yi haramar zuwa yin Sallah, muna nan har akayi kiran isha'i, muka sake tayar da Sallah, bamu jima da kammalawa ba sai gasu sun dawo, nan fa kowace ta shiga kawowa masoyin ta abincin sa, tare da kayan alatu, Aunty Fatima ce ta haɗowa yaya muktar nasa abinci, a cikin wasu tsadaddin kuloli na alfarma, tare da flate da spoon, ta haɗo su duk a cikin faranti.
Sai kuma Mansura wacce ta haɗo komai da komai na abincin a cikin ƙaton flate, tazo ta girke a gaban uncle Ammar ta zauna suka fara ci, to gaba ɗaya sauran ƴan matan haka suka haɗo nasu, Nadiya da General Jamal Abbas sai kuma Shamsiyya da saurayin ta, tare da kuma su Aunty Murja da nasu samarin.
Yaya Kamal ne kawai tare da wani daga cikin abokanen su, aka haɗewa a flate ɗaya ganin cewar sune ba sada budurwa a wajen.
Suka kuwa yi zaune gaba ɗayan su a falon, suka fara cin abincin su.
Nikam zaune na nake a kujera nayi shiru ina wasa da ƴan yatsun hannu na, saboda da alama Mansura ta hau jirgin soyayya ta manta Dani, sai dai ina jin yanda idanun yaya Kamal ke yawo a kaina, amma koda wasa ban ɗago ba, can dai naji yana faɗin.
"Haba Ƙanwa ta Mansura, yanzu fisabilillah nida ba gauro ba sai a haɗe min abinci da wannan tuzurun" ya faɗa yana marairaice fuska kamar ƙaramin yaro.
"Ayya Yaya kamal Ni wallahi kwata kwata na sha'afa" ta faɗa tana dafe goshi.
"Bari naje na sanyo maku wani, idan yaso shi yaya Umar sai yaci wancan ɗin " Mansura ta sake faɗa tana miƙewa ta nufi kitchen.
Ni kuwa nayi shiru kamar ban gane me suke nufi ba, yayin da mutanen falon suka yi tsit kamar munafukai, domin duk a cikin su babu wanda ya fahimci inda maganar tasu ta nufa, musamman wa'yanda ke ganin ni Malika ban kai wani ɗa Namiji ya so ni ba!.
Bata jima ba sai gata ta fito daga kitchen ɗin, ɗauke da ƙaton flate, mai cike da jerin binci kamar irin nasu, tazo ta ajiye a gaban shi, tare da lemun kwali da kuma ƙaramin cup na tangaran, sannan ta koma ta zauna.
Cikin kuskure na ɗago ido na, ai kuwa Mansura ta dallaramin muguwar harara, wanda saida na tintsire da dariya, domin harga Allah ta bani dariya.
Shikam Yaya kamal da yaga ba zan zo muci abincin ba, sai ya ɗauko kwanon bincin ya dawo kusa Dani, yana min magiya, a haka dai na sauko muka fara cin abincin bayan na ja masa aji.
Sai fira yake ja na, ni kuwa abinka da ba'a saba ba, saina dinga jina wani iri, gashi abincin yayi daɗi sosai, kuma kalar wanda nake so ne, shinkafa da miya da coslow, harda soyayyin kaji, amma inaji ina gani, dole na rinƙa ci a hankali saboda karna cofsa a gaban sa.
Nida Mansura kuwa muna lura da yanda Nadiya da Shamsiyya ke bi na da idanu, amma muka yi kamar bamu gani ba, domin lamarin Allah daban yake, kuma a dare ɗaya Allah kanyi Bature. Babban Abin da ya basu Mamaki shine yanda ɗan gidan Ministan Shari'a da kansa ke lallaɓani akan wai naci abinci, hmm abin nasu dai kamar baƙin ciki, domin babu wanda ya sake a cikin su kamar yanda suka saba, ranar a haka suka zauna babu yabo babu fallasa, sunan wani baiti na waƙar Ado gwanja.
"Babu yabo babu fallasa, mu haka suke gaya mana, kaf a cikin su banda Allah waye yake mana".
Wuraren ƙarfe tara da rabi muka yi haramar wucewa gida, kasancewar dare ya fara yi, Aunty Fatima kamar tayi kuka, saboda daga yau ba lallai ta sake ganin mu nan kusa ba, a haka dai suka mana rakiya gaba ɗayan mu, yaya muktar sai lallashin ta yake yi.
Sanda muka fito ƙofar gidan, bansa komai a raina ba, na nufi motar uncle Ammar, kasancewar ita Mansura ma harta riga da ta shiga, ai kuwa nan Mansura ta fito, tace min wallahi ba zan shiga motar mijin ta ba, tinda dai ga tawa motar mijin a kusa.
Na zaro idanu hannu na dafe da ƙirji ina kallon ta, da yake ƴar banzar taso shuka min tsiya sai tayi kamar bata ga reaction ɗina ba, ta dage sai masifa take zuba min, nidai nayi sororo ina kallon ta.
Shi kuma yaya Kamal abin nasu sai kace haɗin baki, sai gashi ya taso yazo kusa Dani yana faɗin.
"Kinga matata! Zo ki rabu da ita, tinda Allah ya hore mana motar ai sai muje na sauke ki a gida, daga nan ai Kinga zan san gidan mu a sauki, gobe ba saina tambaya ba idan zan zo" ya ƙarashe maganar yana murmushi.
Ina ji ina gani, a haka na juya zan shiga motar sa, bayan na zabgawa Mansura harara son raina, ita kuwa ko a jikin ta, saima harshe data zuro a waje tana min gwalo.
Da kansa ya buɗe min motar, bayan na shiga yaja ƙofar ya rufe, yana yi masu saida safe, ina ji sanda Uncle Ammar ke min saida safe, tare da yimin dariya, amma naƙi tanka sa, saboda daga shi har mansurar tasa haushi suke bani.
Hmm Nadiya da Shamsiyya kam, abin duniya duk ya ishe su, domin su kan su, sun sani ministan shari'a ba ƙaramin mutum bane a jahar Kebbi, domin yana da daraja sosai fiye da kima, wanda su kansu sun sani Yaya kamal yafi samarin su da komai, har dashi General Jamal Abbas ɗin, ballantana kuma shi saurayin na Shamsiyya, wanda ke ƙorafin ina kallon sa.
Koda muka fara tafiya akan titin, bai tambayi sunan unguwar mu ba, domin yasan a unguwar su Mansura nake, surutu kawai yake zubamin a mota, nikam bana ce masa komai, daga Eh sai A a, har muka fito daga titin G.R.A.NEFA muka hau titin da zai sada mu da masallacin central mosques.
Da sauri na ɗago na kalle sa, sakamakon Jinda nayi yayi parking, bayan nasan bamu isa kai gida a lokacin ba, kasancewar tun lokacin da na shigo cikin motar kaina yake a sunkuye.
Bai kula Ni ba, yace min.
"Just two minutes please, I will be right back".
Yana ƙarashe faɗin hakan ya buɗe murfin motar ya fita, ba tare da ya jira jin me zance ba.
Saina ɗago kaina da kyau don ganin ina zaije haka, ai kuwa nayi sororo ina kallon wurin.
Domin idan harba manta wa zanyi ba, to wannan wajen ne da uncle Ammar ya tsaya jiya, ya saya mana Shawarma nida Mansura, wato MARACANA.
ina cikin tunanin naji ya sake buɗe mota ya shigo yana faɗin.
"Am sorry please beb, na barki kina jira ko?".
Ban tanka shi ba, illa murmushi da nayi, ina mai duba agogon waya ta, wanda ke nuni da ƙarfe 9:40pm na dare.
Shi kuma ya ja motar da ɗan gudu, bamu fi mintina uku ba muka isa ƙofar gidan namu, da kwatancen da nayi masa.
Ban fita motar Ba, saida muka yi exchanging numbers ɗinmu, sannan nayi masa saida safe tare da fita daga motar zan shiga Cikin gidan mu.
Ai kuwa ya tsayar Dani yana mai fitowa cikin motar da sauri shima ya zagayo inda nake, riƙe da uwar leda a hannun sa yana miƙomin. Na zaro ido na hannu na dafe da ƙirji ina kallon sa.
Nan ya rinƙa lallashi na akan na karɓa, amma fafir naƙi, domin nasan idan har na karɓa, to wallahi Maman mu sai tayi ƙuli ƙulin kubra Dani, na marairaice fuska ina cewa.
"A a wallahi kabar shi kawai, rage min hanyar da kayi ma nagode"....
Ban rufe baki ba ya tari numfashi na, yana cemin.
"Me ki ke nufi Malika? Kodai baki karɓe ni a matsayin masoyi ba ne?" Ya faɗa a yanayin dake nuna cewar baiji daɗin hakan ba.
"Nace mishi "A a wallahi ni sam ba haka nake nufi ba, kuma ni bana buƙatar komai daga wajen ka, sannan Maman mu ma ba zata ji daɗi ba idan ta ganni da wannan ledar haka" na faɗa ina sunkuyar da kaina, domin Ni harga Allah bana so.
" Malika kenan, wallahi naji daɗi sosai daya kasance Maman mu ta baki wannan tarbiyyar, sai naji sonki ya sake ninkuwa a zuciya ta, kuma idan wannan ne karki damu, gobe insha Allah idan kin min izini zan zo da kaina wajen baba, domin na nemi izinin zance dake a wajen sa! Kuma wannan ba wake na bayar ba, ki kaiwa ƙanne na, su na siyawa, kuma gobe insha Allah zan zo mu gaisa dasu " ya ƙarashe maganar cikin fara'a.
Ni kuwa sai naji gaba ɗaya jiki na yayi sanyi, sakamakon jin kalaman sa, a haka na karɓi ledar tare da yi masa godiya, ba don raina yaso ba.
Muka yi sallama, ya tayar da motar sa, ina a wurin tsaye har ya wuce, sannan na motsa gaɓoɓi na tare da buɗe ƙofar gidan mu na shiga, jiki na a matuƙar sanyaye, domin ban san da wane ido ne zan kalli maman mu ba, da wannan ƙatuwar ledar, to ma, nace mata a ina na samo, ko kuma wa ya bani, nasan halin maman mu ba ragamin zata yi ba.
A haka nasa SAKATA na garƙame gidan, na nufi cikin gidan sumui sumui da ƙatuwar leda ta, kamar wata tsohuwar munafuka, jiki na a matuƙar sanyaye.....✍️.
Hmmm yanzu muka fara littafin GAMO MUKA YI insha Allah 🤓 abin dai sai wanda ya gani, saboda haka karku bari a Baku labari🤌.
Daga Alƙalamin👑 Queen Jiddah.....✍️
The Pen Of 👑 Queen Jiddah....✍️
Channel link
https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H
🥹 GAMO MUKA YI 🥹
True Life Story
By Queen 👑 Jiddah.....✍️
Chapter 15
Tun a waje na tsinkayi hasken fitila cikin ɗakin mu, wanda ke nuni da Maryam bata yi bacci ba.
Na sanya hannu tare da yaye labulen ɗakin , zuciya ta na dukan uku uku, da sallama ɗauke a baki na.
Turus nayi! A bakin ƙofar ɗakin, ina kallon ledar hannu na, ba tare da na ƙarasa ciki ba, sakamakon ganin Maman mu da nayi zaune a ɗakin tare da Maryam, wanda babu tantama tsumayin dawowa ta suke yi, gashi Ni sam ban tsammaci na tarar da ita a ɗakin ba.
"Yaya Malika lafiya dai ki kayi tsaye a ƙofar ɗaki?".
Maryam ta faɗa tana kallo na, ni kuwa nayi shiru ba tare da nace komai ba.
Maman mu ta tashi daga zaunen da take, tana mai takowa ta ƙaraso kusa dani, jikin ta a matuƙar sanyaye.
"Malika! Menene wannan a hannun ki? Ko Wani abin ne ya faru a wajen Yinin Amaryar?".
Maman mu ta faɗa tana kai hannu ta kan ledar dake riƙe a hannu na, ai kuwa inajin ta taɓi ledar nayi maza na saki, ji kake tass! Ledar ta faɗi ƙasa, kayan dake ciki suke zube a ƙasa.
Maman mu tayi maza ta kalle ni, cike da alamun tambaya, Maryam ma tasowa tayi tazo wurin tana ƙarasa fitar da sauran kayan waje.
Nikam nayi narai narai da fuska, ai bansan lokacin da hawaye suka fara fita daga ido na ba, nayi durshim a ƙasa zaman ƴan bori, na ɗaura hannu na akai ina faɗin.
"Wallahi Maman mu ba abinda nayi, Yaya kamal ne ya siyamin, kuma saida nace mishi bazan karɓa ba, amma ya nace saina karɓa, Nace mishi idan Maman mu ta gani duka na zata yi, sai yayi fushi wai bana so na karɓa, Maman mu wallahi idan ma baki yarda ba, to ki kira Mansura kiji, nasan zata gaya miki gaskiya".
Na ƙarashe maganar ina mai fashewa da kuka, sai kace wacce ake yanka naman jikin ta.
Ina ji Maryam na tambaya ta.
"Yaya Malika waye yaya Kamal?".
Amma nayi banza da ita, sai rera kuka na nake yi.
Maman mu ta miƙa hannun ta zata taɓa ni, nayi wuf zan sheƙa ina faɗin.
"Na shiga uku ni Malika! Maman mu dan Allah kiyi haƙuri wallahi dole yamin na karɓa".
"Wallahi Malika bana son shirme, ni wani abun ki kaji na ce kinyi? Ko kuwa cewa nayi roƙarsa ki kayi?".
Maman mu ta faɗa cikin yanayin dake nuna cewar ranta ya soma ɓaci.
Da sauri na girgiza kaina, hawaye na tsiyaya a ido na.
Hmm! Maman mu ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta matso kusa Dani tana mai dafa kafaɗa ta tace.
"Kinga Malika! Kwantar da hankalin ki, ba abinda zan miki kinji? Saboda haka gayamin ina jinki, me ke faruwa? Kuma waye shi wanda naji kina faɗar sunan sa.
Na ɗago da sauri na kalle ta, saita jinjina min kanta, alamun na kwantar da hankali na.
Kaina a sunkuye na shiga bata labarin Yaya kamal, da yanda Mansura ta gayamin yana so na, har zuwa shi da ya bayyana min da kansa, na gaya mata yanzun ma shine ya sauke ni a ƙofar gida, tare da bani wannan ƙatuwar ledar, dana ce bazan karɓa ba yace wai gobe idan Allah ya kaimu zai zo wurin Baban mu domin a bashi izinin zance waje na.
"Kuma Allah Maman mu ni bance ina son sa ba" na faɗa ina kuka, da sauri na gimtse baki na, sakamakon ganin yanda Maman mu tayi murmushi, tare da faɗin.
"Kai Malika! Kedai komai sai kin masa kuka, ni Salame zan so naga ranar da zaki daina kukan nan, saura kuma ku ɗurawa cikin su tarkace da yawa, naji wanin ku yace cikin sa na ciwo gobe, Ni zanje na kwanta saida safen ku".
Ta ƙarashe maganar tana fita daga ɗakin, zuwa ɗakin baban mu.
Nayi sororo ina kallon ta, har saida ta fita daga ɗakin ba tare da na iya cewa komai ba.
Tana fita kuwa Maryam tace me zata yi idan ba dariya ba, ta tasa Ni a gaba tana min dariya harda ruwan hawaye tana riƙe ciki.
Nima dai murmushin nayi ba tare da nace mata komai ba, domin Allah kaɗai yasan yanda na shigo gidan, wallahi a matuƙar tsorace nake, saboda banyi zaton Maman mu ba zata dake ni ba, domin hakan ba wani abu bane a wajen ta.
Ita dai Maryam bata bi ta tawa ba, ta fara fitar da kayan dake cikin ledar waje.
Shawarma ce har guda biyar, wacce kuɗin kowace ɗaya daga cikin su zai kai akalla 3k.
Sai kuma wani cips dake haɗe da gasasshen kifi, ga kuma manya manyan Rufaida yogouth guda uku, tare da ice cream Shima guda uku, sai nutrimilk na ƙaton kwali guda biyu, tare da sauran tarkace da ba'a rasa ba.
Maryam ce ke duk wannan lissafe lissafen, nidai ko jinta bana yi, ina kallo ta tashi taje ta saka wasu daga cikin kayan a ƙaramin fridge ɗin mu dake ajiye a ɗakin, tazo ta baje kolin kayan sai kwasa take yi, duk wannan abun da take yi ina kallon ta amma Ban motsa ba, har saida nayi waya ta tayi ƙara, alamun shigowar saƙo.
Na sanya hannu ta ciro waya ta daga cikin jaka, nayi turus ina biyar wayar da idanu, sakamakon ganin numbern dake yawo a gaban wayar, duk kuwa da cewar a yau ɗin nan ne na fara ganin numbern lokacin da muka yi exchanging numbers dashi, sai dai ko shakka babu wannan numbern sa ce.
Da sauri Maryam ta fizge wayar daga hannu na, ganin yanda nayi shiru ina biyar wayar da ido, ta fara karanta saƙon a fili.
"Assalamu Alaikum abar ƙauna! Wallahi daga ɗazun nan zuwa yanzu har nayi kewar ki! Nasan ba lallai idan na kira ki ɗaga ba, saboda may be kinyi bacci, but I want you to always knows that, ni Kamal Usman Tunga ina matuƙar ƙaunar ki! Ji nake kamar bazan iya jure rashin ganin ki har sai gobe ba, ina matuƙar ɗaukin haɗuwar mu abar ƙauna! Love you beb!".
Maryam na gama karanta text message ɗin nashi, ta wani daka tsalle harda taka rawa, wanda Ni wallahi saida na ɗauka kodai aljanun ta ne suka tashi.
Yayin da nayi shiru, kalaman sa na kaida komowa a zuciya ta, Sai tsokana ta Maryam keyi, Ni Kuma nayi banza da ita.
Ban iya cin komai ba a cikin kayan, nayi sulalewa ta a katifa na kwanta, ko kayan jiki na ma ban cire ba.
Maryam kuma, saida tayi nak, kamin ta tashi a wurin, domin saida ta tabbatar da cewar babu sauran space a cikin ta, dan ba ƙaramar ɓanna tayi a wajen ba.
Koda Maman mu ta shiga, wajen Baban mu, shi kansa saida ya fahimci tana cikin farin ciki, daya tambaye ta ne take ce masa, wai Malika tace a sanar dashi gobe zai yi baƙo, shima kuwa saida ya nuna jin daɗin sa, domin a bayyane yake cewar Malika ba tada Manema!.
Washe Gari
Cikin bacci naji waya ta tana ringing, ba tare da na buɗe ido na ba, na ɗauka ina mai faɗin "Hello" cikin magagin bacci.
"Ayya abar ƙauna, baccin ne har yanzu?".
Ai da sauri na tashi zaune, tare da sanya hannu ina mutsuttsike ido na, sakamakon jin Muryar sa.
Na sake duba numbern da kyau, naga lallai numbern ce.
"Hello! Hello abar ƙauna!".
"Na'am" nace cikin sanyin murya.
"Tashi kiyi Sallah kar lokaci ya wuce, Kinga yanzu kusan 5:43am
Saboda haka ki tashi kinji?".
"Tau" na amsa ƙasa ƙasa.
"Tau shi kenan Allah ya miki Albarka".
"Na'am, me kace?" Na faɗa ina zaro ido.
Ina ji sanda ya datse kiran yana dariya ƙasa ƙasa.
Nima murmushi nayi tare da yin miƙa na sakko daga kan katifa.
Koda na sakko naga Maryam tsaye a kaina ta rafka uban tagumi tana faɗin.
"Hmm su yaya Malika sabon shiga, shine ki ka wahalar dani tin 'dazu nake cewa ki tashi kiyi Sallah ki ka ƙi, ashe abin ƙaunar ki Yaya kamal