da ƙyar suka auru, ita ɗayar ma sai da tayi cikin shege, bayan ta zubar wanda yayi mata cikin shine aka samu ya aure ta, da biyar malamai da komai, saboda ɗan gidan masu kuɗi ne shi.
Shi kawu Usmanu shine wanda yayi sa'ar mace ta gari, domin Mama Jamila mace ce mai mutunci da tsoron Allah, yanzu haka ta aurar da babbar ƴar ta mace, ƙaramar ce dai ta rage, wacce take sa'ar Maryam.
To da Mama Rakiya taga ba zata shawo kan Kawu Siddiqu bane ya saka tace masa, wai tana so ya bata izini akan ta nemi na dawo nan gidan su da zama, saboda azumi yanzu saura Sati ɗaya, gashi ta aurar da ƴaƴan ta, tana so nazo na taya ta aiki.
Bai tanka ta ba, saima cewa da yayi, taje gurin Malam Umaru, wato baban mu, ta nemi izini da kanta idan ya yarda shi bashi da matsala, duk kuwa da yasan tana da wata manufar a ƙasa.....✍️
Hmmm littafin GAMO MUKA YI zance ko kuma Rayuwar Malika?🤔 To ko ma menene ku cigaba da kasancewa tare dani Queen Jiddah a cikin littafin GAMO MUKA YI, domin ganin yanda zaman Malika zai kasance a gidan kawu Siddiqu, wajen Mama Rakiya 🤌.
Daga Alƙalamin 👑 Queen Jiddah.....✍️
The Pen Of 👑Queen Jiddah...✍️
Channel link
https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H🥹 GAMO MUKA YI 🥹
True Life Story
By 👑 Queen Jiddah....✍️
A chapter 20 free Chapters zata ƙare, saboda haka sai ku biya ₦500 kacal, idan na kammala document zai kama ₦1000.
0686693377 .GT Bank
Hauwa'u Musa Yeldu.
Shedar biya ta wannan lambar.
08145999600.
Chapter 18
"Shigo mana Malika! Noƙe noƙen me ki ke yi haka? Sai kace wata baƙuwa" Mama Rakiya ta faɗa tana ajiye wayar ta akan kujera.
"Uhm, ba komai Mama, daman Wani abu ne nazo na gaya miki " na faɗa ina soshen soshen kai na.
"A a, to Bismillah a Mana zo zauna" ta faɗa tana nuna min kusa da ita, hakan kuwa yasa naji sanyi a raina, koba komai ta nuna min ƙauna, saboda tunda nake da Maman mu, bata taɓa bari mun zauna kan kujera idan tana akai ba. Zama nayi ba tare da nace komai ina wasa da ƴan yatsun hannu na, tsoro fal a raina.
"Oh oh ni Rakiya Matar Siddiqu! Malika wai sai yaushe ne zaki daina ɗari ɗari da mutane ne? Abu sai kace ba wayayya ba, ina ce har University ki ka yi, yaci ace wannan duhun kan naki ya wanke haka" ta ƙarashe maganar cikin kulawa tana kallo na, tare da dafa kafaɗa ta.
Hakan yasa naji duk wata fargaba ta, na neme ta na rasa, naji wani ƙarfin guiwa ya shige ni a lokaci guda. Na kuwa saki jiki, na gaya mata komai tas, sai bayan na gama faɗar na tuno da ɓaran ɓaramar da nayi, ai kuwa nayi zuru zuru da idanu, fata na ɗaya shine kada Baba Siddiqu yaji, domin nasan idan har yaji to tamkar Baban mu ne yaji, idan kuwa baban mu yaji, babu shakka kashi na ya bushe.
Amma ga Mamaki na, sai naga Mama Rakiya ta washe baki, harda tashi tsakiyar falon, tana taka rawa, daga ƙarshe nima ta jawo ni, wai sai munyi rawar a tare, nidai kunya duk ta ishe ni, saboda daman can ni mai kunya ce.
Munkai tsawon mintina biyar kafin nan muka tsagaita, nan ta ɗauko jakar ta, tare da ciro dubu biyu ta miƙo min, wai nayi Maza naje shago a can waje, na siyo musu ruwan gora da lemun kwalba. Na kuwa ɗau mayafi na zuciya ta fess na tafi, domin a yanzu ji nake ashe gidan mu kurkuku ne mara daɗin zama, komai kayi laifi, wani sa'in ma harda duka, yanzu kuwa Mama Rakiya ta nuna min ina da ƴan cin nayi soyayya babu wani shamaki, Zaman Yini ɗaya a gidan, ya sa ni na canja, domin Ni kaina na san wannan Malikar ba irin waccan bace, domin yanzu ina opportunity.
A can ɓangaren Mama Rakiya ko, harga Allah taji daɗin zuwan da su Yaya kamal zasu yi, domin ko ba komai tasan dole zai zo da abin arziki, domin daga labarin da kawu Siddiqu ya bata, ta tabbatar shi mutum ne mai kyauta.
Ban jima ba na dawo riƙe da kayan a leda, na buɗe fridge na saka, sannan muka shiga kitchen da Mama Rakiya, domin haɗa musu abin taɓawa, saboda a cewar ta ba lallai suci binci ba koda kuwa an dafa.
Babu baƙin ciki kuwa haka Mama Rakiya ta fitar da gyararrin kaji guda biyu a fridge ɗin ta, ta bani na wanko na ɗaura tafasa a ƙaramin gas, saboda an ɗauke wutar lantarki bada jimawa ba, albasa na yanka na saka Corry, tare da wani ɗan ɗanon Magi mai suna LARSOR na rufe tukunyar, na ɗauki kayan jajjagen da ta gyara ta wanke, naje can bayan gidan, na goge turmi na zuba na fara dakawa, saboda papa chicken za'ayi musu.
Lokacin da na dawo kitchen ɗin har Mama Rakiya ta juye kazar a kwando ta daura man suya, ƙamshi sai tashi yake yi, ina gefe ina kallon yanda take haɗa papa chicken ɗin, bawai don ban iya ba, sai don ina so na ƙara ilimi sosai a wannan fannin, muna aikin muna fira abin mu, gwanin ban sha'awa, domin cikin ƙanƙanin lokacin na saba da ita, saboda ita mace ce mai sakin fuska da wasa da dariya, ba kaman Maman mu ba.
Nan na barta a kitchen ɗin, naje na ɗauko Aya a store ɗin ta, nazo na wanke, na fita maƙotan su na kai niƙa, saboda Mama Rakiya cewa tayi idan aka haɗa da kunun aya abin zaifi Ma'ana. Ina hanyar dawowarsa naji jiki na yayi sanyi, dana tuna cewar idan Maman mu ce, ko kallon arziki ba zan samu a wajen ta ba, sai kuma wani ɓari na zuciya ta yace min, ai shiyasa Allah ya dube ki ya kawo ki a inda zaki samu farin ciki, na kuwa yi murmushi bayan gama sauraren zuciya ta da nayi.
Koda na shigo kitchen ɗin, har Mama Rakiya ta saka papa chicken ɗin a cikin babban food flak's mai matuƙar kyau, bata a kitchen ɗin, wanda da alama tana bedroom ɗin ta, ai kuwa na ajiye ƙaton hijabi na, na ɗauko Mataci na fara tace kullun ayar dana niƙo, saida na tace shi gaba ɗaya a wata matsakaici yar roba, sannan na saka kayan yaɗi harda su vevi mix , tare da saka muciya na motsa, na ɗanɗana, naji komai yaji, sannan na ɗauko wani kyakkyawan jug da naga Mama Rakiya ta ajiye na zuba na saka a fridge, sauran kuma na ɗauki jarkar galan na zube gaba ɗaya, na saka a fridge, na gyara ko'ina na share, na saka moper nayi mopping, sannan na wanke kwannan da muka ɓata. Duka duka a cikin abinda baifi awa ɗaya ba na kammala na nufi ɗaki na. Ban ɗaki na faɗa nayo wanka tare da alwala, na shirya tsaf a cikin Wata jalabiya baƙa, mai matukar kyau, sannan na saka hijabi na tare tada sallah, bayan na sallame, saida na ɗau lokaci wajen addu'a ina neman zaɓi mafi Alkhairy a wajen Ubangiji, sannan na ɗauko waya ta, saboda lokacin har ƙarfe 4:10pm.
Abin Mamaki, miss calls ɗin sa har biyar na tarar, na Mansura ɗaya.
Banyi yunƙurin kiran su ba, na kunna data ta kai tsaye, duk da cewar ina da kati, domin katin da ya sakamin a waya aƙalla zai kai dubu biyar, Data kuwa ba'a magana.
Chat ɗin shi na fara shiga, na tarar da voice note ɗin shi, wai idan ya dawo masallaci daga sallar La'asar zasu zo, ai kuwa banyi wata wata ba na danna masa voice nima, tare da yi masa kwatancen gidan, duk da cewar baya online nasan daga zarar ya hayo zai gani Kuma ya saurara.
Chat ɗin Mansura na shiga, itama dai tambaya take yi, wai ya na ƙare da Mama Rakiya. Ita kam tana online saboda munafurci, ai kuwa nace mata.
"Kai Mansura, wai nikam yaushe ki ka iya tsegumi har haka? Tsabagen son Gulma shine ko online ɗin baki sauka ba" na tura mata tare da Emoji na dariya
Itama dariyar tayi, tare da faɗin, "mutuwa aka fasawa ko hisabi? Nidai bani in sha".
Ai kuwa nan da nan na gaya mata yanda muka yi da Mama Rakiya, harda girke girken da muka yi masa.
"Kai Malika amma wallahi Mama Rakiyar nan tana da kirki sosai, Ni ban taɓa saka ran zata yi haka ba, gaskiya ke kam dawowar ki gidan Alkhairy ne".
"Hmm Mansura kenan, ina kuwa ki ka sani? Ai nasan da a gidan mu ne, sam ba za'a lamun ta ba, amma nan kam cewa tayi na kwantar da hankali na, ko kawu Siddiqu ba zata gayawa ba" na faɗi hakan cikin sanyin murya, domin haka kawai nake ji na wani daban.
"Oh oh su Malika an fa ɗa kogin soyayya, Allah dai yasa kar a nitse " ta faɗa cikin tsokana tana yanke waya, nikam tsaki nayi ina ajiye wayar nace.
" ta Allah ba taki ba, dan haka ba nitsewar da zanyi".
Bayan mintina kamar biyar saiga kiran sa, wai yana a unguwar sai dai bai gane gidan ba, nace masa ina zuwa, na kashe wayar tare da ɗaukar mayafin abaya ta na yafa.
Mama Rakiya na faɗawa sannan na tafi waje don na tarbo shi, a bakin gate din na tsaya ina yi masa bayani, harya ƙaraso gidan, ya kuwa fito a mota, tare da wacce yake iƙirarin ƙanwar sa ce, wanda saida Naji wani abu mai kama da kishi ya shige Ni, saboda tsananin kyan ta, amma dana tina cewar ƙanwar sace, saina watsar da komai na tarbe su hannu bibbiyu muka shiga cikin gidan, ina riƙe da hannun ta shi kuma yana bayan mu, harda cewa yayi wai zata ƙwace masa mata, muka saka dariya gaba ɗayan mu.....✍️
Shin a ganin ku, tsakanin soyayyar Maman Malika da kuma ta Mama Rakiya, wacece soyayyar gaskiya daya kamata iyaye su baiwa ƴaƴan su?
Anya kuwa wannan sauyi da Malika ke kira oppotunity zai haifa mata ɗa mai ido?.
Ku kasancewar tare dani a chapter ta gaba dan ganin yanda zata kaya.
Free Chapters zata ƙare a chapter 20 saboda haka sai ku biya ₦500 dan cigaba da karanta littafin GAMO MUKA YI, idan kuma kun fi so a kammala document, zan sayar dashi ₦1000.
8145999600. Monie Point
Hauwa'u Musa Yeldu
Shedar biya ta wannan lambar
08145999600
Daga Alƙalamin 👑 Queen Jiddah....✍️
The Pen Of 👑Queen Jiddah...✍️
Channel link
https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H
🥹 GAMO MUKA YI 🥹
True Life Story
By Queen Jiddah...✍️
Free Chapters zata ƙare a chapter 20, saboda haka sai ku biya ₦500 domin cigaba da karanta littafin GAMO MUKA YI, idan na kammala book ɗin zan sayar dashi ₦1000.
8145999600 Monie Point.
Hauwa'u Musa Yeldu.
Shedar biya ta wannan Lambar
08145999600
Chapter 19.
Next to the last.
Suna zaune a falon gaba ɗayan su, bayan na kawo musu ruwan gora da lemun kwalbar dana siyo na saka a fridge ya ɗau raɓa, sannan na ɗauko musu kunun ayar dana haɗa, tare da food flak's ɗin da Mama Rakiya ta saka papa chicken ɗin kajin a ciki.
Duk nazo na ajiye musu a gaban su.
Yaya Kamal yace min, "abar ƙauna wannan wahalar har haka?".
Nace mishi, "Mama ce ta yi muku" ina murmushi.
"Bari na kirawo ta ku gaisa" na sake faɗa tare da tashi daga inda nake na nufi ɗakin mama Rakiya.
Tare muka fito nida ita, tana sanye da babban mayafi, cikin fara'a ta zauna a falon, tana yi musu Barka da zuwa.
Yaya Kamal kuwa, ya sauka daga kujerar da yake kai, ya durƙusa a ƙasa, yana gaishe ta, kansa a sunkuye, mama Rakiya ko taji daɗin hakan, domin sai wasar baki take yi, nan suka gaisa da Nafisa, wacce yace ƙanwar sa ce, itama ba laifi, daga gani akwai tarbiyya a tare da ita.
Ana cikin haka saiga yara, sun shigo da kayan abinci, katon katon na indomie da macaroni harda Taliya, saboda a ɗan zaman da muka yi dashi, ya fahimci nafi son cin, indomie, akan abu mai nauhi.
Nan kuwa suka ajiye kayan a tsakiyar falon mama Rakiya, ya basu ƴan canji suka kama gaban su, nikam tsuru tsuru nayi, ina kallon kayan, domin a ƙalla ko wane zai kai katon biyar biyar, sai na tina hukuncin da na, karɓa a wajen baban mu, wancan karon, yanzu ya zanyi kuma idan aka ga wannan, oh ni Malika na shiga uku, na faɗa a zuciya ta. A zahiri kuma, murmushin ƙarfin hali nayi ina kallon gefen Mama Rakiya, sai dai ita ko nuna alamar taga kayan bata yi ba, saima shigewar ta, da tayi ɗaki ta barmu a falon.
"Zauji meyasa ka kawo kayan nan? At list ai ko shawara ta ce, ya kama ta ka nema" na faɗa ido na, yana ciko da kwalla.
Murmushi ya sakar min, yana mai faɗin.
"Hana abar ƙauna, yanzu dan zan ɗauki nauyin iyali na, har saina nemi shawara? Karfa ki manta, zama zaki yi a gidan, kuma dole zaki ci abinci, to shiyasa na kawo wannan, domin ni wallahi banƙi ma ace, ko mai zaki shafa, Ni zan saya ba" ya faɗa cikin confidence yana murmushi.
Nikam ai komai ban sake cewa ba, gudun karna dizga shi a gaban ƙanwar sa, sai kawai na watsar da zancen, in yaso daga baya na ja masa kunne kawai.
Ɗakyar na samu suka ci abincin, koshi kuwa sai da suka ga ido na ya fara zubar da kwalla, ai kuwa nan da nan yaya Kamal ya rikice, ya fara shan kunun aya, wanda da alama yayi masa daɗi, nikam murmushi nayi a zuciya ta, domin hawaye ba wani abu bane a waje na, ko zaune nake haka kawai idan naso, zasu zubo, yanzu kuwa zan fara amfani dasu akan sa, tunda na fahimci baya son ganin su.
Ba laifi, sun sha lemo da kunun ayan, amma papa chicken ɗin ba wani mai yawa suka ci ba, a raina nace, to daman ta ina zaku ci, ku da ku ka mayar dasu kamar ruwan shan ku.
Wuraren ƙarfe biyar da ƴan mintina suka bar gidan, bayan ya ajiye wa Mama Rakiya bandir ɗin kuɗi, ƴan ɗari biyar sababbi guda biyu, a kan kuje ra, dana fara yi masa ƙorafi, sai yace min ai Na mama ne, tukuicin girkin da tayi ne. Nan kuwa naja baki na, nayi ƙus.
Har waje na raka su, bayan munyi exchanging numbers da ƙanwar sa Nafisa, suka tayar da motar, Ni kuma na koma gida.
Lokacin da na shiga falon, mama Rakiya bata nan, wanda da alama banɗaki ta shiga, sai gata ta fito daga toilet ɗin. Na kuwa yi narai narai da fuska, ido na yana ciko da kwalla, nace.
"Dan Allah Mama Rakiya ki yi haƙuri ki rufamin asiri, wallahi idan Baban mu yaji to kashi na ya bushe, kuma wallahi ban san zai kawo ba" na faɗa a yanayin da ni kaina ban san wane hali nake ciki ba.
Ƙarasowa Mama Rakiya tayi kusa dani, tare da dafa kafaɗa ta tana murmushi, sannan tace.
"Malika!".
"Na'am Mama" na amsa cikin fargaba, kaina a sunkuye, domin ba zan iya haɗa ido da ita a wannan yanayin ba.
"Ƴa ta Malika, ki kwantar da hankalin ki dan Allah, ina so ki sani , Ni ba irin Salame nake ba, da zan rinƙa takurawa yaro haka kawai ba, ki saki jikin ki kici arziki, Allah ne ya nuna miki, saboda haka kiyi amfani da damar ki, kuma insha Allah, ko malam ba zan bari yaga kayan nan ba, a kitchen zamu ɓoye su, mu dinga cin abin mu hankali kwance, saboda haka maza zo kama mu shiga dasu ciki, kar wani idon ya faɗo" mama Rakiya ta faɗa tana nufar wajen kayan.
Ni kuwa na sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da jin sanyi a raina, domin harga Allah ban tsammaci zata rufamin asiri har haka ba, sai kawai na saki jiki, muka dinga shiga da kayan cikin store ɗin ta, har muka kwashe gaba ɗaya.
Sannan muka baje a falon, muna cin papa chicken ɗin da suka rage , na kuwa ci nayi bam, tare da shan kunun ayar da ke wajen, domin har ga Allah Naji daɗin sa, muna ci muna firar mu gwanin ban sha'awa.
A haka rayuwa ta, ta cigaba da tafiya a gidan kawu Siddiqu, cikin ƴanci da farin ciki da walwala, sai nayi kwana biyu ma ban kira Maman mu ba, Maryam kuma muna yin chat da ita a waya, na saki jiki sosai da duk wasu shawarwari na Mama Rakiya cikin abinda bai wuce sati ɗaya ba, ai kuwa zo kaga yanda na canja, nayi kyau nayi haske nayi jiki abina, sai son Barka.
A haka har watan Ramadan ya ka ma, domin a daren jiya Sarkin Musulmi ya saka akayi sanarwar kowa yayi niyar tashi da azumi, saboda anga watan Ramadan a ƙasa mai tsarki.
Da asuba kuwa, tunda muka yi sahur ban kwanta ba, har sai da na kammala aikace-aikacen gida gaba ɗaya, sannan nayi wanka tare da karatun Alqur'ani na kwanta.
Ita ma Mama Rakiyan bacci take yi, a ɗakin ta, kasancewar ita bata yi bacci ba sai wuraren ƙarfe 11:am na safe.
Ai kuwa bamu tashi ba sai bayan sallar La'asar, da yake idan akayi salla muna tashi muyi sannan mu koma bacci.
Haka muka shiga kitchen gaba ɗayan mu, muka fara shirye-shiryen buɗin baki, kamar yanda kowa keyi.
Da yake Ni ke haɗa na buɗe bakin, wato jouloup ɗin shinkafa da kabej tare da ferfesun kifi, sai kuma koko da kosai, wanda za'a fara buɗe baki dashi.
A gefe guda Ita kuma Mama Rakiya, tana gaɗa abincin sahur, saboda da wuri take yi sai ta saka food flak's, yanda ba zai yi sanyi ba, ya zamana da cewar idan aka sha ruwa, zata mayar da hankalin ta ne kawai a wajen ibada.
Koda shida tayi, mun kammala komai, hakan yasa kowace mu ta wuce ɗakin ta, nikam ina shiga na wuce banɗaki na watso ruwa sannan na dawo kan gado na kwanta ina huce gajiya.
Ni kaina na san idan nace banyi kewar gida ba, haƙiƙa na yaudari kaina, domin da a gidan mu ne, da yanzu ina tare da maman mu da Maryam, kai harda Nana, muna aikace-aikace a tare, sai dai yanzun ma ni bani da wata damuwa, domin yanda Mama Rakiya ta riƙa ni, ko ƴaƴan ta ne, nan ta tsaya.
Duba waya ta nayi, sai naga ƙarfe 6:30pm na yamma, ai kuwa na zabura na fita kitchen, na fara yanka fruit cikin sauri, haka na yanke lemo da kankana da gwanda, harda abarba, na sakawa Baba Siddiqu a wani kyakkyawan faranti, kasancewar Mama Rakiya ce da girki, yau a nan zai sha ruwa, bayan na zuba a farantin na ɗauko flet na saka nawa, dai dai yanda zai isheni, sannan na saka su gaba ɗaya fridge cikin gidan ƙanƙara saboda yayi sanyi da wuri.
A falon Mama Rakiya, Na kai duk wani abin buɗe baki na ajiye, ba'a jima ba saiga kawu Siddiqu ya shigo, na gaisar dashi, naje kitchen na ɗauki kayan da na haɗawa kaina na buɗe baki nayi ɗaki na.
Na zauna ina addu'a sosai, har aka kira sallah, muka sha ruwa.
Sai dai duk wannan aikin da nake yi, inajin kewar gida tana lulluɓe ni, domin da'a gida ne, da yanzu muna nan a tsakar gidan mu, an shimfiɗa tabarma, kowa yana zaune yana buɗe baki.
A kwana a tashi har azumi ya kai goma sha ɗaya, sai dai duk bayan kwana biyu, yaya Kamal ya kan zo muyi fira idan aka sha ruwa, kuma baya taɓa zuwa min hannu sake, saiya riƙomin kayan kwamulashe, nazo mu baje nida Mama Rakiya mu cinye abin mu.
Mansura ma, tazo gidan lokacin da azumi ya kai biyar, muka sha fira abin mu, ranar anan tasha ruwa, sai bayan mun dawo sallar tarawihi, da ake yi nan a masallacin unguwar, Sannan na raka ta, ta wuce gida, sai dai ita batasan duk wannan hidin dimun da Yaya kamal keyi Dani ba, domin Mama Rakiya cewa tayi karna sake na gayawa kowa, idan ba so nake, najawa kaina tsiya ba, domin idan har baban mu yaji, to cewa zai yi na koma gida da zama.
Kwanci tashi asarar mai rai, domin yanzu har mun wuce azumi goma na Marmari da kuma na tilas, mun shigo na murnar sallah.
Wato azumi ishirin da ɗaya, nikam na dage sosai da zuwa sallar tuhajjid, ina kaiwa Allah kuka na, tare da neman zaɓin sa, Ni kaina na sani, cewar wasu daga cikin halaye na sun canza, sai dai gefen ibada ta ina nan ina yi, kuma ban fasa ba, domin wannan lokacin shine lokaci na ƙarɓar addu'ar bayi .
Ana sallah saura kwana uku, ranar da dare bayan sallar Isha, yaya Kamal ya kira ni a waya, wai gashi nan a ƙofar gida, lokacin kuwa, murna fall Raina, domin ɗunki na , na sallah ya kawo min, da yake shekaran jiya yazo muka je wurin telan aka auna Ni, abinka da masu kuɗi shine wai har an gama.
Na kuwa ɗanɗasa kwalliya na fita waje, a ƙofar gidan na hangi motar sa, na buɗe na shiga, sallama ɗauke a baki na, sannan na gaida shi, sai zumuɗi nake, domin na ƙagu naga kayan wallahi.
Ai kuwa nace "zauji ina ɗinkin? Yayi kyau k"....
Ban ƙarasa ba na zabura da sauri ina kallon sa, raina a matuƙar ɓace, sakamakon jin da nayi ya riƙe min hannu, yana tsure ni da ido kamar wani maye.....✍️
Hmm! Littafin GAMO MUKA YI kenan, daga Alƙalamin 👑 Queen Jiddah....✍️
Like share and comment fisabilillah 🙏.
Free Chapters zata ƙare a chapter 20, saboda haka sai ku biya ₦500 domin cigaba da karanta littafin GAMO MUKA YI, idan na kammala document zai kama ₦1000 kenan.
8145999600 Monie Point
Hauwa'u Musa Yeldu.
Shedar biya ta wannan Lambar.
08145999600.
Daga Alƙalamin 👑 QUEEN JIDDAH....✍️
The Pen Of 👑Queen Jiddah...✍️
Channel link
https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H
🥹 GAMO MUKA YI 🥹
True Life Story
By 👑 Queen Jiddah....✍️
A chapter 20 free Chapters zata ƙare, saboda haka sai ku biya ₦500 kacal, idan na kammala document zai kama ₦1000.
0686693377 .GT Bank
Hauwa'u Musa Yeldu.
Shedar biya ta wannan lambar.
08145999600.
Sanar wa, zan fara Paid page, 03/1/01/2026 wato gobe kenan Ranar Asabar idan Allah ya kaimu.
Chapter 20.
"Wai meye haka Yaya kamal? Dan Allah sake min hannu" na faɗa ina ɗaure fuska ta.
"Yaya Kamal? Yau ko zaujin ma babu?" Ya faɗa , cikin ko in kula da yanda raina ya ɓaci, yana mai ɗaura hannun sa akan fuska ta yana kallo na, har yanzu kuma bai sake min hannu ba.
"Mtsweeet!" Na ja tsaki, tare da faɗin, " dan Allah cika ni, bana son haka fa, nifa ba ƴar iska bace, idan ma haka kake tunani, to kayi kuskure".
"Malika! Why? Ni ki ke dangantawa da ɗan iska? Meyasa bakya so na taɓa ki, ko kin manta aure za muyi, kodai bakya so na ne?" Ya faɗa yana sake min hannu ransa a ɓace.
Yayin da Ni Kuma nayi shiru ina kallon sa, ba tare da nace komai ba, domin harga Allah yau Yaya Kamal, kama yake min da mayaudara, musamman yanda yake magana, har ni zai rainawa hankali kenan, bayan nasan da haka ne aka yaudarar ƴan mata, da sunan za'a aure su.
Sai Naji, kwata kwata bana son ganin sa, domin idan da akwai abinda na tsana a duniya, shine namiji yayi ƙoƙarin taɓani, nan take zan daina ganin duk wata kima da darajar sa.
Hakan yasa ban samu furta masa komai ba, na buɗe marfin motar na fita, ina ji yana kira na amma nayi banza dashi nayi shigewa ta, gida ko ɗinkin nawa ban amsa ba.
Yayin da shi kuma yayi bala'in rikicewa, domin shi kanshi ya san ya kofsa.
"Or sheet!" Ya faɗa yana dukan starin motar sa.
Nikam koda na shiga gida, a falo na tarar da Mama Rakiya, ban Kula ta ba, nayi shige wa ta, ɗaki ina kuka, ta tashi da sauri ta biyo baya na, tana tambaya ta lafiya? Meya faru ne, ko ɗin kin nawa ne ba'a kammala ba.
Nikam kasa cewa komai nayi, sai kawai na faɗa jikin ta ina kuka, nace.
"Na shiga uku mama, ashe daman Yaya kamal ɗan iska ne" na faɗa ina kuka kamar raina zai fita.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un, Me ya faru har haka Malika? Me Kamal ɗin yayi miki?" Mama Rakiya ta faɗa tana Bubbuga baya na.
Na ɗago daga jikin ta, ina share hawaye na, tare da jan majinar hanci na, nace.
"Wai haka kawai ya riƙa min hannu, dana yi masa magana