ki ke jira" ta ƙarashe maganar tana dariyar shaƙiyanci, ni Kuma nayi banza da ita, tare da fita waje, addu'a ɗauke a baki na.
bayan munyi sallar asuba, bamu koma bacci ba muka shiga aikace aikacen gida, kamar yanda muka saba, ka na muka haɗa karin kumallo, koko da kosai, ga kosan yayi matukar yin laushi, gaba ɗaya gidan ya ɗau ƙamshi.
Da misalin ƙarfe 8:30am na safe, muka kammala komai, nice na fara shiga banɗaki nayi wanka, dana fito sannan Maryam ta shiga, sai dai duk wani abu da nake yi, ina yinsa ne kawai, domin kalaman yaya Kamal ne kawai ke yi min yawo a zuciya, daga jiya zuwa yau, na saurari kalamai daga wajen sa, masu matuƙar tasiri, wanda Ni kaina saida na tabbatar ya iya tsara zance, sai kace wani marubuci.
Vaciline nake shafawa a jiki na, na kamfanin Cocoa votta, mai matuƙar ƙamshi, ina shafawa ina murmushi, domin Ni kaina a yau na tabbatar da cewar, soyayya wata garkuwa ce a jikin ɗan adam, wanda duk kyau da kwarjini gami da ƙasaitar mace, ba zata san irin matsayin da take dashi ba, har sai tana da wanda yake son ta , domin komai yana da bagiren shi na daban a rayuwa.
A yau ni Malika na tabbatar da cewar yaya Kamal ya cike mini wani gurbi a rayuwa ta, wanda na jima babu shi a tare dani, sai dai nasan ba kowace mace bace zata fahimci hakan, sai wacce ta taso a irin rayuwa ta, a matsayin ki na mace, ina so ki ƙiyasta yin shekara goma sha takwas ba tare da mashinshini ba, ya zaki ji? Musamman idan ki ka kasance a cikin ƙawaye waƴanda keda samari, ya yanayin yanda zasu tsangwame ki yake? Da kuma yanda zasu rinƙa goranta miki, wasun su ma zasu iya dena ƙawance dake, domin gani suke zaki kwace musu samari!.
To kamar haka ne ni Malika rayuwa ta ta kasance, bani da aiki sai kuka, ako yaushe jina nake mace ba kamar sauran mata ba, sai dai Ni na kasance mai kaiwa Allah kuka na domin nasan bazan taɓe ba, ayau na ga yanda rayuwa ta, ta kasance, gobe kuwa Allah shine mafi sani.
Ina cikin haka itama Maryam ta fito daga wanka, ta fara shirya wa, bayan mun kimtsa gaba ɗayan mu, muna zaune muna Karyawa saiga Maman mu ta shigo, muka yi mata ina kwana.
Ta amsa cikin fara'a tana tambaya na ina muka ajiye abin karyawar Baban mu.
Da hannu na nuna mata saitin da na ajiye masa break fast ɗin, kular ƙosai da kuma jug ɗin koko akan faranti.
Bayan Maman mu ta ɗau farantin take tambaya na, wai Baban mu yace a tambaye ni, da yaushe Yaya kamal zai zo?.
Murmushi nayi ina sissinne fuska ta ba tare dana tanka ba.
"Oh ni Salame, Malika wai yaushe ne wannan kunyar taki zata ragu?".
Maman mu ta faɗa tana riƙe haɓa.
Nayi murmushi ina faɗin.
"Wallahi Maman mu nima bai gayamin ba".
"Tau shi kenan, Daman saboda a gayawa yaya Usmanu ne Siddiqu" Maman mu ta ƙarashe maganar tana fita daga ɗakin.
Ni kuwa na sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da cigaba da cin abinci na.
"Hmm Yaya Malika yanzu fa ko Engagement ba'a yi ba, amma ki ke wannan kunyar, to idan aka ɗaura aure aka kai ki sai muga ƙarshen kunyar!"......
"Bafa nason iskanci Maryam, kamar ya kuga ƙarshen kunyar, ko Ni sa'ar ki ce?" Na faɗa ina zaro ido, saboda Ni harga Allah bana son raini.
"Yaya Malika me yayi zafi har haka? To Allah ya huci zuciyar ki, Maryam ta faɗa tana gimtse dariyar ta, tare da cigaba da cin abincin ta. Yayin da Ni Kuma nayi ƙwafa ina cigaba da cin abinci na.
Bamu fi mintina biyar da gamawa ba, saiga Muryar Mansura tana doka mana sallama, lokacin ma har ƙarfe 10:7am na safe.
Maryam ce ta karɓa mata sallama, saboda Ni Ko gefen ta ban kalla ba, don da alama munafurci ne ya kawo ta. Maryam kuwa daman abin duniya ya ishe ta, ai saita shiga labartawa Mansura text message ɗin da ya turomin jiya da dare, harma da tashi na sallar asuba da yayi da safen nan.
Mansura kuwa daman abokin yi take nema, ia kuwa suka dasa Ni a gaba da tsokana, tin ina fuskewa har dai na haƙura, muka sake, sai fira muke.
Ana cikin haka sai waya ta, ta fara ruri, a jiki na naji cewar shine ke kira na, kasancewar bani da wani Mai kira na a waya bayan Mansura, yanzu kuwa gani tare da Mansura, saboda haka sai dai idan shine.
Ina dubawa kuwa naga shine, na yunƙura da sauri da nufin na fita waje, saboda harga Allah ba zan iya waya a gaban su Mansura ba, musamman yanzu da naga reni naso ya shiga tsakani na da Maryam.
Mansura kuwa tayi wuff ta danne ni, nace .
"Mansura meye haka?".
"Lafiya ce ta kawo hakan, idan kuwa ba zaki ɗaga anan ba sai dai ya tsinke" ta faɗa tana dariyar shaƙiyanci.
Tinda ta faɗa kuwa nasan ba zata barni naje waje ba, Hakan yasa na dallara mata harara, tare da picking call ɗin, lokacin ma wayar na batun tsinke wa.
"Amincin Allah ya tabbata a gare ki, abar ƙauna ta!" Yaya Kamal ya faɗa cikin Muryar sa mai kamala da kwarjini.
Murmushi nayi, ina mai gaisar dashi, nan yake cemin insha Allah zasu zo bayan sallar La'asar .
Na dafe ƙirji ina zaro ido, nace" Daman ba kai kaɗai zaka zo ba ne kenan?".
Murmushi yayi yana faɗin "Beb kenan, ai bazan iya zuwa gaisar da sarakai na, Ni kaɗai ba, abin ai da kunya, saboda haka tare dasu muktar zan zo".
Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ina faɗin.
" yaya muktar! Mijin Aunty Fatima kake nufi ko wa?".
"Eh shi nake nufi, tare dashi zamu zo, da kuma General Jamal Abbas insha Allah".
Murmushi nayi ina faɗin "to Allah ya kawo ku 'lafiya".
"Amin" ya amsa, ka na muka yi sallama.
su Mansura kuwa kasa kunne suka yi suna jin duk yanda muke yi dashi.
Nan Mansura ke faɗin,
"Wai wane General Jamal Abbas! Ba dai saurayin Nadiya ba?".
"Hmm Mansura kenan, shi ɗin dai yake nufi, Ni wallahi haka kawai wannan General Jamal Abbas ɗin bai kwanta min a rai ba" na faɗa jiki na a sanyaye .
Mansura tace," oho dai, su suka sani ai, nidai bari naje na gayawa Mama lokacin da zasu zo".
Nayi charaf na riƙe ta, ina faɗin " Mansura ina zaki je ne wai?".
"Kai Malika! Tsakar gida mana zanje, Wajen Mama na gaya mata ".
"Ki gaya mata fa ki kace Mansura, ko kunya bakya ji?" Na faɗa ina langwaɓarda kaina.
Tsaki Mansura taja tana faɗin.
"Ai kuwa dole naji kunya tinda nice ke" ta faɗa tana gallara min harara, tare da wucewa tsakar gidan wajen Maman Mu.
Murmushi Maman mu tayi, bayan da ta gama jin bayanin Mansura, nan fa ta lissafawa Maryam cefane, taje kasuwa tayo siyayyar kayan da za'a yi amfani dasu.
Nidai ina ɗaki ban fito ba, domin harga Allah kunyar Maman mu nake ji.
Haka Mansura da Maryam suka aiwatar da duk wani abu daya dace, akayi shirin tarbar su, dai dai ƙarfin mu.
Domin kunun Aya ne suka yi, yaji kayan haɗi sannan suka saka a fridge tare da zoɓo, sai kuma Alala wacce taji kayan haɗi harda ƙwai, tare da jolouf ɗin shinkafa da kifi, da zogale, dai dai kalar abincin gidan talaka.
Basu jima da kammalawa ba akayi kiran sallar Azahar, suka tashi domin haramar sallah.
Muna zaune gaba ɗayan mu a ɗaki bayan mun gama sallar La'asar, muka jiyo Muryar Baba Usmanu da kuma Siddiqu sun shigo, su ɗin sun kasance ƙanne ne a wajen Baban mu, shine ya gayyato su, domin a nemi izini a wajen su, kasance War sa mutum mai karanci da Dattaku.
Nan Maman mu ta gaisar dasu, tare da shimfiɗa musu tabarma, suka zauna, sannan ta kawo musu ruwa da abinci.
Bayan mintina biyar da shigowar su, saiga text message ɗin Yaya kamal, wai na fito yana ƙofar gida.
Nan fa Mansura ta tasani a gaba, saida na sanya sababbin kaya, wani leshi broun color ɗinkin doguwar riga A sharp, na saka, ai kuwa ba ƙaramin kyau nayi ba, powder kawai na shafa sai kwalli tare da man leɓe, amma kar kaso kaga haɗuwar da nayi, nan na fesa tirare mai sanyin ƙamshi, na wani tsohon kamfani da aka jima ana yayi, wato Tony Montana, na yafa mayafi bayan na saka takalma plat shoes, kasancewar inada tsayi shiyasa bana saka takalma masu tsini.
Hannu na sanya, ina mai yaye labulen ɗakin mu, cikin fargabar ganin su Baba Usmanu dake tsakar gidan, sai dai koda na fito basa nan, wanda da alama sun shiga ɗakin baba.
Na sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ƙarasa fitowa madaidaicin tsakar gidan mu, wanda Mansura ta share shi tass, sai ɗaukar ido yake yi.
Ina gab da fita ƙofar gida, naci karo da yara guda biyu maza, kowannen su ɗauke da ƙaton buhun shinkafa, sai naji jiki na yayi sanyi, domin ko ba'a faɗamin ba nasan aikin yaya Kamal ne, domin daga jiya zuwa yau ɗin nan na fahimci shi mutum ne mai son kyauta, sai dai Ni bana buƙatar wannan hidin dimun daga wajen sa,yin hakan kamar raina arzikin Mahaifi na ne, kuma nasan shi kanshi Baban mu ba zai lamunci hakan ba.....✍️
Like share and comment fisabilillah 🙏
Daga Alƙalamin 👑 QUEEN JIDDAH.....✍️
The Pen Of 👑Queen Jiddah...✍️
Channel link
https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H
🥹 GAMO MUKA YI 🥹
True Life Story
By 👑 Queen Jiddah....✍️
Chapter 16
Jiki na bai sake mutuwa ba, har saida na fito waje, na tarar da wasu kayayyakin abinci, tare da katon katon na Taliya da macaroni, harda Taliyar yara, galan na Man gyaɗa harda Manja. A raina nace to ko bawan Allah nan ya zata yunwa ce damu, tinda harya ganni a rame kamar figaggiyar kaza.
Ina tsaka da wannan tinanin, sai kawai naji Muryar mutum a kusa Dani, na juyo ƙirji na sai dukan uku uku yake yi, domin nasan yau kashi na ya bushe a wajen Baban mu.
"Abar ƙauna lafiya ki ka tsaya a nan?".
Na tsinkayi Muryar yaya Kamal yana faɗin haka.
Murmushin yaƙe nayi, wanda yafi kuka ciwo nace mishi.
"Uhm Babu komai, sannu da zuwa".
Shima murmushin ya mayar mini, ba tare da yace komai ba.
Sai nace mishi.
"Bismillah ku ƙaraso ciki" dai dai lokacin da su yaya muktar mijin Aunty Fatima da kuma General Jamal Abbas wato saurayin Nadiya suka ƙaraso wajen, muka gaisa a taƙaice, ina fara wucewa gaba, su kuma suka biyo ni a baya.
Koda muka shiga cikin gidan namu, haka suka dinga biyar ko'ina da kallo, domin duk da yanda yake ƙaramin gida, amma a tsare yake, babu wasu tarkace cikin sa, sa'annan ko'ina tsaf tsaf dashi gwanin ban sha'awa.
A ƙofar ɗakin baba na tsaya, tare da yi musu iso cikin ɗakin, sai dai Ni ban shiga ba, domin ina ganin sun shiga ciki na juya Ni Kuma na shiga ɗakin mu, inda na tarar da Maryam da Mansura, sai farin ciki da murna suke yi, ganin yanda na shigo ya saka su tasowa jiki a sanyaye suka zo kusa Dani.
"Malika Lafiya dai?, me ke faruwa ne? Ko Yaya kamal ɗin Ya fasa zuwa?".
Mansura ta jefomin tambayoyin a jere tana kallo na, yayin da Ni Kuma na girgiza mata kaina hawaye na gangarowa a ido na, sai dai na kasa furta komai.
"Kai Yaya Malika, dan Allah ki gaya mana meya faru ki ke wannan kukan haka, ko wani abu ne baban mu ya faɗa akan sa?".
Maryam ta faɗa tana riƙomin hannu itama hawaye na cikowa a idon ta.
" Ba abinda ya faru, ku kwantar da hankalin ku dan Allah" na faɗa ina share hawaye na.
"To kenan me ki ke wa kuka idan har babu abinda ya faru?" Mansura ta faɗa tana tsure ni da ido.
"To ba dole nayi kuka ba Mansura, ni wallahi lamarin yaya Kamal ɗin nan bayamin daɗi ko kaɗan, fisabilillah ki duba waje ki gani abinda ya kawo" na faɗa ina nuna musu tsakar gidan mu da hannu na.
Ai kuwa kowannen su ya miƙa don ganin me ke faruwa a tsakar gidan, basu fita ba, labulen ƙofar ɗakin kawai suka yaye, ai kuwa idanun su suka sauka akan wa'yannan yara maza guda biyu, wa'yanda ke ƙoƙarin shigo da kayan abinci suna ajiye wa a tsakar gidan mu.
Jiki a sanyaye suka dawo suka zauna, kowacce ta rafka uban tagumi tana kallo na, muka yi shiru kuwa gaba ɗayan mu, muna jiran hukuncin da baban mu zai yanke.
A ɗakin Baban mu kuwa, koda suka shiga da sallama ɗauke a bakin su, bayan anyi musu iso, ka na gaishe gaishe ya biyo daga baya kamar dai yanda Al'adu suka tanadar.
A kan tabarmar dake shimfiɗe a tsakiyar ɗakin baban mu suka Zauna, suna gaisar da su baba cikin mutun tawa, Su Baba Usmanu da Siddiqu kuwa hakan ba ƙaramin daɗi yayi musu ba.
Ita dai Maman mu bata ma cikin gidan baki ɗaya, saboda maƙota tayi tafiyar ta, wai ala dole ni ƴar fari ce.
A haka dai su Yaya muktar suka bayyanar da abinda ya kawo su a tsanake, shida General Jamal Abbas, domin shi Yaya kamal komai baice ba, bayan gaisuwar da yayi, sai kawai ya sunkuyar da kansa yana murmushi, domin mu a al'adar mu ta hausawa kuma mutanen birnin Kebbi, a duk lokacin da akaje neman aure ko gaisuwar sarakai, to shi mijin baya cewa komai sai dai yayi shiru, domin yin maganar sa a wajen zai iya zama rashin kunya a wajen iyayen.
Su Baba Siddiqu ne suka s amsa wa su yaya muktar cewar sun bada izinin zuwa zance waje na. Amma da suka buƙaci lokacin yin tambayar aure, sai Baba Usmanu yace, su dakata za'ayi bincike tukunna, Sai General Jamal Abbas yayi murmushi tare da yin godiya akan hakan.
Nan muka ji Muryar Baban mu, yana ƙwalawa Maryam kira, wai akawo wa su Yaya kamal abinci.
Nan fa suka ce, ba zasu ci ba, Baban mu yace akai musu a mota su tafi dashi.
A haka Mansura da Maryam suka kwashi kayan suka kai mota, suna zullumin hukuncin da baban mu zai yanke idan ya fito tsakar gida yaga kayan da su Yaya kamal suka kawo.
Suna ƙoƙarin shigowa gidan bayan sun ajiye kayan a mota, suka yi
Kiciɓis dasu a tsakar gidan, nan suka samu damar gaisawa, Yaya kamal yayi wa Mansura godiya akan ƙoƙarin da tayi masa, shi kuwa Yaya muktar ya balbale Maryam da Masifa, wai bata je bikin su ba, to ita kanta tasan bata kyauta ba, shiyasa tayi ta sissinne fuska tana bashi haƙuri, nan suka fito da bandir ɗin kuɗi guda biyu ƴan ɗari biyar biyar sababbi gadagal, suka miƙo masu, Amma fafur suka ce ba zamu amsa ba, har saida yaya muktar ya nuna ɓacin ransa, sannan suka amsa suna godiya suka wuce cikin gida.
Lokacin da suka shigo ɗakin nikam ina nan a zaune duk tsoro ya kama Ni, domin Allah kaɗai yasan yanda bugun zuciya ta ya tsanan ta.
Nan fa suka ajiye min kuɗin a gaba na, suna bani labarin yanda suka yi da su Yaya muktar a waje, nidai bance komai ba face zubawa kuɗin ido da nayi, tare da rafka uban tagumi.
***
"Baban Malika! Baban Malika!".
Naji Muryar Maman mu a tsakiyar gida tana ƙwalawa Baban mu kira, wanda da alama yanzu ta dawo daga maƙota, kuma tayi tozali da kayan dake tsakar gidan.
Jin yanda Maman mu ke ƙwalawa Baban mu kira yasa shi fitowa da sauri, dan ganin me ke faruwa, ai kuwa yana fitowa yayi turus a ƙofar ɗakin, ba tare daya ce komai ba, ganin shiru ne ya sanya Baba Usmanu da Siddiqu suma suka fito dan ganin me ke faruwa, ai kuwa suma suka yi turus suna faɗin.
"Salame waye ya kawo kayan nan har haka?".
"To yaya Usmanu ni ya za'ayi na sani, yanzun nan ne fa shigowa ta, shiyasa ma na kira Baban Malika don na tambaye sa" Maman mu ta faɗa cikin girmamawa tana kallon su.
"Ikon Allah, to Salame idan har ke baki san waye ya kawo kayan ba, mu taya za'ayi mu sani?".
Baba Siddiqu ya faɗa yana ta'ajjubin al'amarin, yayin da mu kuma duk wani abu da suke faɗa yake zuwa mana a kunnen mu.
"Malika! Malika!".
Na tsinkayi Muryar Baban mu yana ƙwalamin kira, jiki na yana ɓari na fito waje tare da rissinawa a gaban sa ina faɗin Baban mu gani.
"Waye ya kawo wannan kayan?" Naji Baban mu ya faɗa ransa a ɓace yana nuna saitin kayan abincin da hannun sa, ba tare da ya dubi wajen da nake ba. Sai naji jiki na yayi sanyi, hawaye sun fara cikowa a ido na, domin nasan za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya.
"Dake nake Malika, waya kawo kayan nan?" Baban mu ya sake faɗa a fusace yana kallo na.
Da ƙyar na iya motsa baki na nace.
"Wallahi Baban mu, ban san zai kawo ba, kuma bai gayamin b".....
Tass! Naji Baban mu ya ɗauke Ni da wani lafiyayyen Mari, wanda har saida na daina gani na ƴan wasu sakanni, yayin da naji zuciya ta tayi min ɗaci, domin bazan iya tina ranar da baban mu ya ɗaura hannun sa a jiki na ba, da sunan duka, sai gashi a yau da ta kasance rana mafi muhimmanci a gare ni, na samu kyautar Mari daga Mahaifi na.
"Malika ni zaki mayar mutumen banza? Ko ce masa ki kayi ina da yunwa a gida na? Da har zai ɗauko wannan abincin ya kawo, salon Maƙota suce sayar dake zanyi, ko yana tinanin zai saye ni ne da waƴan nan kayan abinci? To wallahi wannan bazai saka na ɗauki auren ki na basa ba, har sai nayi bincike a kansa, domin bincike ne kawai zai bayyanar min da kowaye shi, kuma ki Buɗe kunnen ki da kyau ki ji, muddin na sake ganin makamancin hakan a gida na, to wallahi ranki zai yi mummunan ɓaci, domin ni ba mutumin banza bane!" Baban mu yana ƙarasa faɗin hakan ya yi shigewar sa ɗakin sa, ransa a matukar ɓace.
Su kawu Usmanu da Siddiqu suka bi bayan sa, ba tare da ko kaɗan sunga laifin sa akan hukuncin daya ɗauka ba, domin a ganin su hakan shine dai dai. Ba kamar iyayen mu na yanzu ba, da a wannan zamanin suka ɗauki son abin duniya suka ɗaurawa kansu, suka baiwa ƴaƴan su lasisin lalacewa da kansu, suka zama sanadiyyar gurɓacewar ƴaƴan su da hannun su, wanda wasun su ke ɗaukar hakan a matsayin waye wa, wasun su kuwa gani suke sun haifi ƴaƴa masu kyau, saboda haka dole suji ɗaɗi su wataya, hakan yasa suka mayar dasu kayan jarin su, sun manta cewar Allah ba zai ƙyale su ba, kuma dole su fuskanci hukunci ga duk wani zunubi da suka aikata, dole su girbi abinda suka shuka!.
Durƙushe nake a wajen, ina tsiyayar da kwalla, ba tare dana ce komai ba, har baban mu ya gama faɗan sa, ya yi shigewar sa ɗaki.
Ita kanta Maman mu jikin ta yayi sanyi, sai dai tasan hakan da baban mu yayi, ko kaɗan babu kuskure a ciki, domin ice tun yana ɗanye ake tanƙwara shi.
Bata cemin komai ba, face kafaɗu na data riƙa tana mai miƙar dani tsaye, tare da jan hannu na muka yi cikin ɗaki.
Anan ƙasan ledar dake shimfiɗe a tsakiyar ɗakin na silale na kwanta, sai a lokacin na samu damar yin kuka, ka na nauyin dake ƙirji na ya ragu, na ringa rera kuka sai kace mai rera waƙa, da yake daman kuka ɗabi'a tace.
Mansura ce ta taso tana lallashi na, itama kukan take yi, domin suna laɓe a ƙofar ɗaki sanda baban mu ya zabga min mari.
"Malika meyasa ya kawo kayan nan, bayan kin san halin Baban ku ba lamuntar hakan zai yi ba".
Ina ji sanda Maman mu ta jefomin tambayar, sai dai ban iya cewa komai ba, domin ba lallai kona faɗa a yarda ba, shiyasa na cigaba da kuka na kawai, ko na ji sanyi a raina.
"Wallahi Maman mu ba laifin Yaya Malika bane, ita kanta bata san da kayan ba, Maman mu acikin su ma, bamu da tabbacin waye ya siyo kayan" Maryam ta faɗa cikin sanyin murya, idon ta na ciko da ƙwalla.
"Eh Mama, gaskiya Malika bata da masaniyya akan hakan, zaima iya yiyuwa shi Yaya kamal ɗin bashi ya shiya ba, abokanen sa ne suka yi masa ka ra" Mansura ta faɗa tana share ƙwallar da ta zuba agefen idon ta.
Maman mu kuwa, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, tana faɗin.
"Mansura kenan, to idan har ni na yarda ba lallai iyayen ku Maza su yarda ba, domin yanda naga yanayin Baban ku, na tabbatar ba ƙaramin ɓaci ransa yayi ba" Maman mu ta faɗa tana kallo na.Yayin da ni kuma duk wannan zancen da suke yi, ba jin su nake yi ba, domin Allah kaɗai yasan abinda nake saƙawa a raina, ni kaɗai nasan abinda zanyi wa Yaya kamal, tinda har yayi sanadiyar jefa ni a wannan halin.
Mansura kuwa ganin da tayi nayi shiru, tasan ba Alkhairy nake kitsawa a raina ba, shiyasa tace min.
"Malika dan Allah kar ki hukun ta Yaya kamal a bisa hakan daya faru, saboda ba ma da tabbacin shine ya siyo kayan nan, kuma Kinga shi bai san yanda tsarin gidan nan yake ba, yanzu ne ya kamata ki sanar dashi".
"Haka ne Malika, Mansura gaskiya ta faɗa, saboda haka ki sanar dashi dokokin mahaifin ku, idan har ya sake to lokacin ne za'a hukunta shi" Maman mu ta faɗa cikin bayar da umurni tana kallo na.
Sai a lokacin ne, na samu damar buɗar baki na, na ce.
"Amma Maman mu shi kenan sai nasha mari a banza saboda shi?".
"Haba yaya Malika! Wai meyasa bakya ɗaukar shawara ne ke kam? To idan ma baki haƙura ba me zaki masa, ko rama marin za kiyi a kansa?" Maryam ta faɗa tana kallo na.
Maman mu ma, bata ce komai ba, domin harga Allah taurin kan nan nawa Mamaki yake bata, ta rasa a ina na samo shi, koda yake haka Baban mu yake, idan har ya kafe aka abu, to babu wanda ya isa ya canza shi.
Nikam da naga babu wanda ya goyi baya na a cikin su, sai kawai na juya musu baya, na cigaba da kuka na, saboda idan da sabo na saba.
Muna kallo Baban mu ya saka aka fitar da kayan abincin gaba ɗaya, buhun shinkafa kusan goma da katon ɗin Taliya da macaroni harda Taliyar yara ko wane biyar biyar, a haka aka rabarwa maƙota shi, gaba ɗaya.
Domin cewa yayi baya da buƙatar wannan abincin ko kwara ɗaya a gidan sa. Sauran galan ɗin Man gyaɗa da man jan da suka rage cewa yayi a kai gidan Kawu Usmanu da Siddiqu, amma nan wurin suka ce basa da buƙata, domin dukan su a aƙida ɗaya suke tsaye, suna da matuƙar haɗin kai sosai.Nan kuwa aka fitar dasu aka ƙarasa rabarwa maƙota. Ita kanta Maman mu bata ji daɗin hakan ba, domin bata so aka rabar da kayan duka ba, inama laifin a kyautar da rabi a bar rabi, amma ba yanda ta iya dole tayi gum da bakin ta, domin a yanda ransa yake ɓace idan har tace zata yi Magana, to zai ce ita ta baiwa Malika goyon baya aka kawo kayan.
A ranar dai haka muka wuni cikin alhini, Mansura ma bata wuce gida ba sai bayan isha'i, Maryam tayi mata rakiya a ƙofar gida.
Koda su Baba Usmanu suka koma gidajen su, A unguwar Bayan Kara, kasancewar a gida ɗaya kawu Usmanu da Siddiqu suke zaune tare da iyalansu, kasancewar gidan na gado ne, tun na iyayen su, to baban mu ma anan ya fara zama, sai bayan da aka haife Ni ne ya tashi daga gidan ya koma gidan da ya gina, saboda shi baya da ra'ayin zama a gidan gado, sai ya barwa su kawu Siddiqu shi, mu kuma muka dawo nan da zama.
To yanzu haka a gida ɗaya suke zaune sai dai kowanen su ƙofar sa daban.
Bayan kawu Siddiqu ya je gidan ne yake baiwa Matar sa Rakiya labarin abinda ya faru, nan take nuna masa ai bai kamata a mayar da kayan ba gaskiya, kasancewar ta mace mai son abin duniya, domin a irin tirbar da ta ɗaura ƴaƴan ta mata kenan, wanda gaba ɗaya unguwar su ake zance, wanda sai