shine har da shafamin fuska, wai Ai aure na zai yi, saboda kawai ya mayar Dani shashasha" na faɗa ido na, yana zubar da kwalla.
"To shine ki ka tsaya kina kuka, baki ci abu ta kaza kazan ubansa ba" mama Rakiya ta faɗa tana Lailayo ashar ta ƙunduma masa.
"A a Mama, bance dashi komai ba, kawai dai na yanke shawarar zan rabu dashi, daga yau babu ni babu shi, tinda ɗai ɗan iska ne" na faɗa ina kallon mama Rakiya, yayin da ita kuma tayi murmushi tana faɗin, Tau shi kenan Malika, kiyi yanda ki ke so, Ni ba zan tilasta miki zama dashi ba, amma kar kiyi saurin yanke hukunci saboda yanzu ranki a ɓace yake, saboda haka, ki zauna kiyi tinani, kuma idan kinje sallar tuhajjid sai ki nemi zaɓi wajen Ubangiji " mama Rakiya ta faɗa tana dafa kafaɗata tare da fita daga ɗakin ta barni.
Nikam a ranar haka na kwanta, zuciya ta babu daɗi, ban tashi ba sai wajajen ƙarfe 1:30am na dare, na shirya muka tafi masallaci wajen sallar tuhajjid nida wasu maƙotan su mama Rakiya, a wannan daren na daɗe ina kai kuka na wajen Ubangiji, tare da roƙon zaɓin sa, ina fatar Allah zai kare min mutunci na har zuwa ɗakin miji na.
Washe Gari bayan na kammala aikace-aikace na, nayi wanka na shirya, na zauna ina karanta Alƙur'ani, a ranar na kammala saukar ƙur'ani na, cikin ma nayi sanya a karatun, domin a watan Ramadan ina saukar ƙur'ani kusan sau biyu, sai gashi sai yau da watan Ramadan ya cika kwana 27 sannan na kammala sauka.
A ranar Maryam ta kira ni a waya, wai nazo inji mama.
Naje na sanarwa Mama Rakiya, sannan na tafi na hau adaidaita zuwa gidan mu, bayan ta gargaɗe ni akan karna sake na sanar dasu abinda ya faru tsakani na da Yaya kamal.
Lokacin da na isa gida kuwa da gudu na faɗa jikin Maman mu, domin harga Allah nayi kewar ta, muna cikin haka, Maryam ta fito da leda daga ɗakin mu, tazo ta baje su a wajen, ɗinkin kayan sallar mu ne da Baban mu ya ɗinka mana, kala uku uku, iri ɗaya nida ita da Nana, less atamfa da kuma abaya, na kuwa gwada, kayan komai cip, Ranar a gidan na wuni sai bayan shan ruwa Maryam ta raka ni ina riƙe da ledar kaya na, sai murna nake, har ta, taramin adaidaita sahu, nace mata, ta koma kawai, saboda saina fara biyawa wajen Mansura, da yake nayi waya da ita, nace mata zan zo. Nan kuwa muka yi sallama na tafi gidan su Mansura.
Banfi mintina biyar ina tafiya ba, na isa gidan su mansura, kasancewar daga gidan mu zuwa nasu babu wata tazara.
Ina shiga gidan kuwa nayi sallama, muka saka ihu muna rungume juna, nan na gaida maman ta sannan muka wuce ɗakin ta.
Sai dai muna zama naji Mansura tace min wai meyasa bana ɗaukar wayar yaya Kamal.
Tsaki kawai nayi ina faɗin.
"Dan Allah Mansura ki daina yimin maganar sa, idan har ba so ki ke yi, na tashi na tafi ba".
"Malika me yayi zafi har haka " Mansura ta faɗa tana riƙe haɓa.
"Hmm nifa blocking ɗinsa nayi, gaba ɗaya, saboda haka ban ma ga kiran nasa ba, ballantana naƙi ɗagawa" na faɗa ina taɓe baki na.
"Malika kenan, wai shi yaya Kamal ɗin, shine akayi blocking, lallai abin naƙi ba ƙarami bane".
"Oho miki, nidai na riga da na yanke duk wata alaƙa tsakani na dashi, yaje can ya nemi ƴar iska irin sa".
"Haba Malika, dan Allah ki daina ce mishi ɗan iska, wallahi duk wani abu daya faru ya kira ni kuma ya sanar dani, yayi nadama sosai wallahi baki san, yanda ya damu ba"......
"Ke Mansura, wallahi kiji tsoron Allah, yanzu mutum ya taɓamin hannu harda shafamin fuska, sannan ki ke cewa wai bada niyya yayi ba" na faɗa cikin mamaki ina riƙe haɓa.
"Malika kenan, daman nasan dole zaki ce haka, amma ki daure ki saurare ni, wallahi idan ki ka ji hujjar sa, nasan dole zaki haƙura".
"Hmm Mansura nikam da ace ban san halinki ba, da sai ince ko saye ki yayi, amma tunda kince haka, shi kenan ina sauraren ki" na faɗa ina kallon ta.
"Malika!".
"Na'am Mansura, ina sauraren ki " na faɗa ina taɓe baki.
"Malika kinfi kowa sanin yanda, ƴan matan yanzu suke, kura ce mai lulluɓe da fatar biri, to shiyasa yayi miki hakan, domin ya gwada ki, wallahi Malika yanda ya nuna min, ba ƙaramin daɗi yaji ba, da kika yi masa hakan, cemin yayi, yaji yana son ki fiye da komai a Rayuwar sa, domin yanzu bashi da wata fargaba atare dashi, a shirye yake ya aure ki a kowane lokaci " Mansura ta faɗa tana kallo na.
Yayin da nayi shiru, bance komai ba, sai naji kalaman ta sun shige ni, to amma meyasa yayi min haka? Hakan na nufin bai yarda Dani bane kome.
Jin da nayi Mansura ta dafa kafaɗata ne ya katse min wannan tunanin da nake yi, na ɗago na kalle ta, ina nazarin kalaman da ta faɗa min.
"Malika ki yarda Dani, Ni wallahi gani nake kamar babu yaudara a lamarin sa, jiya fa yakai awa ɗaya a gidan nan yana roƙo na akan naje na baki hakuri, kuma ki tuna da ace bada gaskiya yake ba da bazai haɗa ki da ƙanwar sa ba".
"To amma Mansura, dole ne sai anyi wa mace wannan gwajin kamin a aure ta?" Na faɗa ido na yana ciko da kwalla,. domin harga Allah ina son, Yaya kamal, kawai dai ba zan bari soyayyar sa ta rufe min ido ba, harta kaini ta baro.
"Ba dole bane Malika, amma dan Allah ki masa uzuri, idan ya maimaita hakan, ina goyon bayan ki, ga duk wani hukunci da zaki yanke".
"Tau shi kenan Mansura, nagode sosai, insha Allah zanyi unblocking ɗin shi idan na koma gida".
"Tau shi kenan Malika, Nagode da wannan alfarmar da ki kayi min".
"Kar ki damu Mansura, muje ki raka ni, Dare yana yi".
Haka Mansura ta raka ni, na hau mashin na wuce gida, lokacin har Mama Rakiya ta fara kira na, saboda ƙarfe tara ta gota.
A haka rayuwa ta cigaba da wakana tsakani na da yaya Kamal, sai dai duk da nayi unblocking ɗin shi, hakan baisa na sake masa kamar baya ba, muna nan dai tare sese sese.
Ana yau daren jajibir ya kira ni, wai zai zo ya kawo min kaya na, da ban karɓa ba ranar nan, nace mishi ya barshi kawai, ya haɗa a lefe, saboda Baban mu yamin ɗinkin sallah, ba yanda baimin magiya ba, amma fafur naƙi.
Washe garin sallah kuwa, haka muka tashi da wuri, muka kammala komai, na abinci, Tuwon shinkafa da miyar alayyahu, muka girka, saboda tun jiya muka yi zoɓo da kunun aya.
Lokacin da muka gama shirin zuwa Masallaci har ƙarfe 8:40am na safe, ai kuwa muka yi haramar zuwa Masallaci, kasancewar bamu nesa da masallacin.
A masallacin, kuwa haka na dage sosai wajen roƙon Ubangiji, ina neman makoma mai kyau a wajen sa, harda kwalla na.
Bayan mun dawo masallacin, haka muka ci, muka sha, na ɗauki abinci na kai ɓangaren kawu Usmanu, wanda tunda nazo baifi sau biyu ko uku dana shiga ba.
Haka na rinƙa raba abinci a maƙota, har gidan mu saida naje na kai, domin wannan al'adarmu ce, raba abincin sallah, a tsakanin mu.
Haka na dawo na kwanta ina huce gajiya, saboda har gidan su Mansura naje na gaisar da maman ta,. saboda ita tana gidan Aunty Fatima, wai bata da lafiya, shine taje ta kwana biyu, har zuwa lokacin da zata samu sauƙi.
Bayan salla da kwana biyu , haka yaya Kamal yazo ya zauna a falon Mama Rakiya, na kawo masa abin sha, ta cincin ɗin sallah, nan yake cemin wai zuwa yayi za muje mu gaisar da yayar sa, nace nikam ba zani ba, mama Rakiya tace nayi haƙuri muje, haka kuwa naje na shirya na saka sabuwar abayar da baban mu ya sayamin, na bishi muka je.
Ina kallo muka shiga unguwar Alero quarters, muka shiga wani babban gida mai matuƙar kyau, mai gadi ya buɗe mana ƙofa muka shiga , yayi parking muka shiga cikin, babu kowa a falon, yace na zauna, shi kuma ya shiga ciki, sai gashi ya fito tare da Nafisa, wannan wacce yace min ƙanwar sa ce, muka gaisa da ita, ta kawo min ruwa wai nasha, kamin Auntyn ta dawo, saboda ta shiga maƙota, har tace ma bari taje ta kirawo ta.
Bayan ta fita, dakyar ya takura Ni nasha ruwa, sai dai har muka kwashe kusan mintina talatin, babu Auntyn babu Nafisa, ga wani bacci da naji yana ƙoƙarin rufe min ido, sai kace wacce tasha ƙwaya, sai hamma nake yi, nan yace min na kwanta a kujera, shi bari yaje ya dubo su.
Daga haka ban sake sanin a inda nake ba, sai farkawa nayi, na ganni a akan gado kwance, wanda da alama na jima a wajen, na yunƙura na tashi, sai kawai naji wata azaba ta ratsa ta tsakiyar ƙafafuwa na, na rumtse ido cikin azaba na yaye bargon da naganni Rufe dashi, ai kuwa da sauri na fasa uban ihu saka makon ganin yanda jini ke bin ƙafa ta, wanda nake da tabbacin an raba Ni da daraja da kima ta, ta ƴa mace.
"Na shiga uku ni Malika! Me ke faruwa ne dani haka?" Na faɗa ina fashewa da matsanancin kuka.
Saiga Yaya kamal ya shigo cikin ɗakin, saka makon jin ihu na, alamun na farka....✍️
Hmm tirƙashi, haƙiƙa Babu wani ɗan adam daya isa ya gujewa ƙaddarar sa, domin a yau Malika ta tsinci kanta a cikin, mummunar ƙaddara, wanda Ni kaina Queen Jiddah ban san menene mafi ta ba🥹.
Gashi kuma anan na kai ƙarshen free chapter, saboda haka, zan cigaba da saka book ɗin a paid group ɗin GAMO MUKA YI da kuma Arewabook insha Allah 🤓.
Daga Alƙalamin 👑 QUEEN JIDDAH......✍️
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels