Share this page
4 / 9
in group muke abubuwan mu, da isar mu, muka shiga hole ɗin tare da neman wajen zama muka zauna, aka fara gabatar da program ɗin wajen, bayan an gama aka saki music mutane suka fara rawa, mu kuma muna a gefe zaunen mu, Kasan cewar mu huɗu muka je, Mansura dani Sai kuma Nadiya da Shamsiyya. To ita dai Mansura Daman tana da Saurayin ta, wani malamin mu ne na makaranta, to tun kafin muyi graduation yake son ta, har muka gama makaranta, kuma ya riga da ya tura magabatan sa, a gidan su, gashi kuma shi ɗin ɗan wani Alhj Kallamu ne, mahaifin sa, yana da kuɗi sosai, kasancewar mahaifinsa sananne ne, shiyasa ba'a sha wahala ba wajen bincike aka basa izinin zuwa zance gurin ta, to muna a wurin Dinar ma yazo suka koma gefe suna shan soyayyar su, domin yace baza tayi rawa ba, don shi ustazu ne. Nadiya kuwa muna a gurin zaune wani babban mutum ya aiko da yaro akan tazo dan Allah yana so za suyi magana, tace da yaron ya koma yace ba zata zo ba, idan yana so yazo da kansa, har yaron zai juya na riƙe sa, nan na lallaɓata akan tayi haƙuri taje bata san ko waye shi ba, kuma bata san dame yazo ba, badan taso ba haka tabi bayan yaron tana ƙunƙuni, harta isa gurin Mutumen, nan kuwa duk wata rashin kunya da take da ita ta ƙare, domin wani babban soja ne, tare da securityn sa a zagaye dashi, sunan sa Genaral Jamal Abbas, babban sojan ƙasa. Shi kuwa murmushi ya saki, yana kallon ta, domin yana kallon duk fitsarar da take yi, lokacin da ya aika a kira ta, yanzu kuwa duk tabi ta tsorace sai biyar sa da ido take, wurin zama ya nuna mata ta zauna nan dai yayi mata bayanin kansa, ashe shi abokin angon Yaya Fatima ne, kuma yana da mata ɗaya da yara biyu, sannan shi da maganar aure yazo domin ta kwanta masa arai, nan dai suka tattauna domin itama taɗan Saki jiki tayi masa baya Ni dangane da kanta. Mu kuwa nida Shamsiyya sai dariya muke mata, domin muna kule da yanda duk tabi ta firgice daga ganin sa, nan Shamsiyya ke cemin ai idan naga budurwa ta kalli saurayi ta firgita, to alama ce ta tana sonsa, saboda da haka matakin soyayya ke farawa, nidai murmushi kawai nayi , araina kuwa cewa nayi, to nikam taya zansan yanda soyayya ke farawa tunda ba yinta nake yi ba, ai wannan sai su, Suda ake furta wa kalmar so. Shamsiyya ce ta katsemin tinani tana faɗin. "Kinga Malika! Zo muje muyi rawa tunda su wa'yan nan sun barmu mu kaɗai, sai soyayya suke sha gefe"ta ƙarashe maganar tana jan hannu na muka shiga tsakiyar hole ɗin. Muna shiga ciki, muka dinga rawa iya ƙarfin mu, duk da cewar Ni ban sake sosai ba, amma dole nake rawar, saboda yanda shamsiyya ke riƙa kafaɗuna tana jijjiga ni, daga sama kawai muka ji ana mana ruwan kuɗi, nikam na dakata daga rawar da nake yi, domin ganin shin waye ke mana liƙin kuɗi har haka, yayin da Shamsiyya taci gaba da rawar ta, ba tare da ta damu ba. Koda na juyo sai ido na, yayi tozali da wani kyakkyawan saurayi, cikin shigar ƙananan kaya, dogo ne kuma yana da ƙasumba, sai naga yamin kyau sosai domin yayi kala da namijin da nake so, ganin da nayi ya matsa daga inda nake yana mai wucewa kusa da Shamsiyya wacce ke shan rawar ta cikin burge wa da Class, hakan ne ya farkar Dani daga duniyar kallon sa, dana lula, saina ɗan matsa gefe ina kallon su, yayin da ya isa kusa da Shamsiyya cikin takon sa na Class yana taya ta rawar, abokanen sa kuwa suka zagaye su, sai liƙi suke musu suna shewa. Wani abu ya tokaremin ƙirji na, sai naji ya min nauyi, yayin da ƙafafuwa na suka yi sanyi, har naji suna ƙoƙarin kasa ɗauka ta, hakan yasa na sulale a hankali na bar filin, na koma Ni kaɗai a wata kujera na zauna, tare da lumshe ido na, na sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da furzarda zazzafan huci daga baki na, saina samu kaina da jinginar da baya na a jikin kujerar, tare da lumshe ido na, domin yin hakan shine kaɗai mafita a gare Ni. Har akaci aka suɗe wurin ban sani ba, saida naji Muryar Mansura, tana dafa kafaɗa ta, tare da kiran suna na. "Malika! Malika! Wai meke damun ki ne haka? Tun ɗazu kina nan zaune kowa sai rawa yake banda ke, gashi ma har an tashi, su anty Fatima ma sun wuce, tashi muje kar dare yayi".... "To ba dole tazo tayi zaune anan ba, bakin ciki ne da haddasa ke ƙoƙarin kashe ta!" Shamsiyya ta faɗa tana jijjiga jikin ta sai kace ƴar restilin. Da sauri na buɗe lumsasshin idanu na, wa'yanda ke rufe tun ɗazu, sakamakon jin furucin da Shamsiyya tayi. "Haba Shamsiyya! Wannan wane irin rashin mutunci ne haka, yanzu ƙiyayyar da kike wa Malika harta kai ga kiyi mata irin wannan furucin? To saboda me baƙin ciki zai kashe ta?" Mansura ta faɗa ranta a matuƙar ɓace tana kallon Shamsiyya. "To ba dole kiji na furta hakan ba, ai baƙin cikin naga tayi shiyasa nace haka, idan bashi ba, taya zata dinga bin saurayi na da kallo sai kace wata maiya! Rashin mashinshini hauka ne halan? Dahar zata dinga biyar namiji da ido sai kace wata wawiya! Wannan ai zubarwa mata Class ne". "Ke Shamsiyya! Wai da gaske saurayin ki take kallo?" Nadiya ta faɗa riƙe da haɓa tana kallon Shamsiyya. "Wallahi kuwa Nadiya kallon sa ta dinga yi har saida ta tashi faɗuwa ƙasa, anan wurin Dina ya ganni yazo yana min liƙi, harya karɓi number na, shine yake tambaya na, wai wacece Malika, tin ɗazu sai kallon sa take yi, naja mata kunne gaskiya saboda shi bayason kallo"....... "Inna lillahi wa inna lillahir Raji'un, Malika yanzu da gaske kallon maza ki ka koma yi?"...... "Dan Allah Nadiya rufe min baki, wai wannan wane irin abu ne haka, yanzu fisabilillah ke Shamsiyya ko kunya bakya ji, ace saboda saurayi kike ƙoƙarin tozarta Malika?" Mansura ta faɗa idon ta cike da kwalla tana kallon su. Yayin da Ni kuma na mayarda ido na, na lumshe ina sauraren su, tare da yin nadama marar iyaka akan wannan Dina dana halarta. "Haba Mansura! Wai ke meyasa bakya son kiji anfaɗi laifin Malika ne? Kodan ba saurayin ki take shigewa ba" Nadiya ta faɗa tana kallon Mansura. Murmushi Mansura tayi tana faɗin. "Ko kaɗan Nadiya, ki sani niba irin ku ɓace, dahar namiji zai shiga tsakani na da Malika, domin koda ace Malika miji na ta aura, to wallahi bazan tozarta taba, domin ba haramun ta aikata ba"...... "Allahu akbar Mansura!" To wallahi ki sani Ni Shamsiyya bazan iya wannan jahadin ba, yanzu haka yana jira na a mota zai maida Ni gida, saboda haka saida safen ku, ke kuma Malika sai abi a hankali, kar ayi hauka saboda an rasa mashinshini!"..... "Haba ke kuwa Shamsiyya ina zaki je? Jira Ni mana, nima ai General Jamal, yana jira na tare da muƙarraban sa, yace a gida zai sauke Ni saiya wuce, saboda haka muje tare" Nadiya ta faɗa tana rataya jakar ta. "To Mansura! Mukam zamu wuce, sai dai gobe idan mun haɗu a wajen walima" suka faɗa a lokaci ɗaya, tare da wucewa wurin samarin su. Mansura kuwa da hawayen ta, shaɓe shaɓe, ta dafa ni, tana faɗin. "Malika dan Girman Allah kiyi haƙuri, karki riƙe su Nadiya a zuciyar ki, ki yafe musu, son abin duniya ne kawai ke ɗawainiya da zuciyar su ba wani Abu b"...... Ƙasa ƙarasa maganar ta tayi,. sakamakon ganin yanda na buɗe jajayen idanuwa na, waƴanda suke a lumshe tun ɗazu, tare da jifar ta da Miskilin murmushi, na miƙe tsaye tare da gyara zaman jakar dake rataye a jiki na, na furta. "Karki damu Mansura ko kaɗan ban riƙe su a raina ba, Ni zan wuce gida, saida safe". Da sauri ta riƙo hannu na, tana furta. "A a Malika, tare da Yaya nake, don Allah kizo mu tafi tare sai mu sauke ki a gida ". Hannun ta dake ajiki na na kalla, tare da sanya hannu na, na janye nata hannun, data riƙe ni, ka na na ɗan matsa daga gefe ina furta. "Karki damu Mansura! Ki barni kawai naje, bana so nazo kema na ƙwace miki naki saurayin".......✍️ Hmm Rayuwar Malika muke magana akai fans, tabbas akwai ƙalubali a cikin ta saboda haka muje zuwa💃 Yawan like share da Kuma comments shine zai saka nayi update gobe insha Allah 🤓. Daga Alƙalamin👑 Queen Jiddah.....✍️ [12/15, 10:07 PM] Queen Jiddah: The Pen Of 👑Queen Jiddah.....✍️ Channel Link https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H Update group Link https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=hqrt3 YouTube channel Link https://youtube.com/@queenjiddahhausanovelschannel?si=NajxqyDlNBtjeOPh Arewa Book channel https://arewapen.com/u/hauwaumusa06 Facebook page Link https://www.facebook.com/profile.php?id=61580403014165 Facebook group Link https://facebook.com/groups/559415480283144/ 🥹GAMO MUKA YI 🥹 True Life Story By Queen Jiddah 👑 Chapter 11 Tass! Naji Mansura ta wanke Ni da lafiyayyen Mari, na ɗago da fuska ta, idanuwa na sun kaɗa sunyi jajir, zuciya ta sai raɗaɗi take min. Ban Ankara ba naji ta fizgomin hannu, ta jani zuwa motar saurayin ta, tana faɗin. "Wallahi Malika bana son shashancin banza da wofi, Ni an gaya miki cewar, zuciyar shashashun mata ce Dani, dahar zan iya barin ki anan wurin saboda wani saurayi?, to ki buɗe kunnen ki da kyau kiji, Ni da zaki amince ma saina saka Yaya Ammar ɗin ya haɗa mu, mu biyu ya aura! Na gani shin idan ƙawaye suka auri miji ɗaya mutuwa suke yi ko me". Ta ƙarashe maganar dai dai lokacin da muka ƙarasa kusa da motar tasa, bata jira ta baki na ba, kawai sai gani nayi ta buɗe murfin motar gidan baya, ta jayo hannu na, tana wani haɗiye fuska tace min, na shiga ko kuma ta ɗauke ni, ta saka ni, harga Allah ta bani dariya, musamman yanda ta zage damtse sai surfar masifa take yi, kamar wata uwa ta, amma yanayin da nake ciki na ɓacin rai, ya saka bance da ita komai ba, na shiga cikin motar, ita kuma ta rufe ƙofar tare da zagayawa gaban motar ta shiga, shi kuwa Uncle Ammar ya ja motar muka bar wajen. Jiyowa yayi yana kallon ta ganin yanda take ta faman cika tana batsewa sai kace wacce aka daka, ya juyo sit ɗin baya, da nufin ya tambaye ni akan Meya same ta, sai dai ganin da yayi cewar nima bana cikin walwala kamar yanda na saba, sai hakan yaso ɗaure masa kai, gashi ma koda muka shigo motar ko gaida shi banyi ba, sai kawai ya juya gefen ta yana faɗin. "My Dear! Meya same ku ne haka, kamar wa'yanda aka aiko wa saƙon mutuwa, hope dai Lafiya?". Murmushi Mansura tayi, wanda Ni kaina nasan a iya fuska ya tsaya, sai tace mishi. "A a wallahi My Dear! Ba komai fa, kawai Halin Malika ne ya motsa, to kasan idan ba masifa ne akayi da ita ba, hankalin ta baya kwanciya" ta ƙarashe maganar tana sakar masa da murmushi. Murmushi shima yayi, yana juyowa ɓangare na, tare da faɗin. "Ikon Allah, Malika wai da gaske ne My Dear take yi, cewar halin naki ne ya motsa?" Yayi maganar yana murmushi. Ban ce komai ba, na juya gefen Mansura ganin yanda ta liƙamin sharri, muna haɗa ido kuwa ta dalla min Harara, tare da kawar da kanta gefe, wai ita ala dole na bata haushi. Daina kallon ta nayi, na mayar da kallo na wajen Uncle Ammar, nace. "Ba komai wallahi Uncle, kawai fa kaina ke min ciwo ita kuma ta dame Ni da surutun ta, Ni kuwa naƙi tanka ta, to shine fa take wannan hasumin" na ƙarashe maganar ina murmushin yaƙe,wanda yafi kuka ciwo. "To nidai babu ruwa na, sai dai nace kuyi haƙuri, saboda bazan shiga tsakanin Mansura da Malika ba, daga ƙarshe nazo naji kunya" ya ƙarashe maganar yana mayar da hankali wajen tuƙin sa. Nidai shiru nayi ban ce komai ba, sai Mansura ce tace masa. "Da dai ka shiga, gobe kuwa kaji kunya". Shima ya maida mata da zancen, ina dai jinsu suka yi ta firar su irin ta masoya gwanin sha'awa, har muka ƙarasa ƙofar gidan mu, ban sani ba, saboda ido na yana a lumshe, sai da Mansura ta taɓa ni, nayi firgigit na biɗe ido, tace min mun ƙaraso, na buɗe murfin motar ina faɗin. "Nagode sosai, saida safen ku". "Allah ya tashe mu lafiya" Uncle Ammar yace, har zan rufe motar na tsinkayo Muryar Mansura tana faɗin. "Gobe ki shirya da wuri, walimar ƙarfe Huɗu ce, zamu zo nida My Dear sai mu wuce can insha Allah". Kai kawai na jinjina mata, tare da rufe murfin motar na shiga gida, saboda yanda nake jin kaina yana bala'in Saramin, kamar zai rabe gida biyu. Da sallama na shiga gidan mu, sai dai koda na ƙarasa cikin gidan na tarar da tashin hankalin da yafi wanda na baro a wurin Dina, domin Baban mu ne, keta famar surfa masifa maman mu na basa haƙuri, ina isowa kuwa na risina zan gaida shi, ban ko kai ga rufe baki ba naji saukar mari, nan ya rufe Ni da masifa wai saboda me zanje Dina tun ƙarfe bakwai na yamma amma ace har ƙarfe 10:00 ban dawo ba, wannan ai shashanci ne, inda yake shiga ba tanan yake fita ba, harma yayi rantsuwa akan wai gobe bazan je wani event ba, kai gaba ɗaya gobe bai yarda na leƙa ƙofar gida ba, yana gama faɗar hakan yayi shigewar sa ɗakin sa. Na sulale nan kasan Barandar mu tare da lumshe ido na na kwanta, domin ni mutum ce, wacce idan raina ya ɓa ci bana iya kuka sai dai na lumshe ido zuciya ta, tana famar raɗaɗi. Maryam tazo kusa Dani tana dafa kafaɗata, tace min. "Malika dan Allah ki tashi muje ciki, karki ɓata kayan ki, Kinga gashi nan kin kwanta a ƙasa". Idan ƙofa tana magana, to ni Malika na tanka ta, domin kuwa koda idanuwa na da suke a lumshe ban buɗe ba, kuma bana da niyar tashi daga inda nake. Maman mu ce, tazo taja min hannu na, tare da faɗin "Malika! taso muje ciki, kar Malam ya fito ya same ki, kin san halin sa sarai ba kyale ki zai yi ba". Ta ƙarashe maganar tare da jan hannu na muka shiga ɗakin mu, ban zame a ko ina ba, sai kan katifar mu, na kwanta ba tare dana ce komai ba. Maryam tace "gaskiya Malika baki kyau ta ba, kinfi kowa sanin halin Baba to meyasa kika je kika yi zaman ki, Bayan kin san Dinan ma dakyar ya bari ki ka je". Ban tanka ta ba, haka zalika Ban motsa daga kwancen da nake ba, maman mu kuwa duk tafi ta damu, domin tasan rashin maganar nan nawa matsala ne, tafi so ace koda kuka ne nayi, saboda raɗaɗin ya fita cikin zuciya ta, duk da cewar tayi mamakin yanda wannan ƙaramin abun ya ɓatamin rai har haka, bayan nafi kowa sanin halin Baban mu, wannan ba baƙon abu bane a wurin sa. "Malika! Wai Meya same ki ne haka, ki saki ranki dan Allah, nifa na yarda dake kuma na san ba zaki taɓa aikata wani abu wanda bai dace ba, to meye na wannan damuwar, idan ma har dan saboda fitar da yace ba zaki yi gobe bane, to ki kwantar da hankalin ki, nasan ransa ne kawai a ɓace, insha Allah goben zai sauko" maman mu ta faɗa cikin sanyin murya tana kallo na. Sai a lokacin naji wani abu mai kama da hawaye na gangarowa a kumatu na, na buɗe baki na, to a lokacin ne sautin kuka na ya fara fita har numfashi na yana shuɗewa. Maman mu kuwa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, tana kallo na, ban taɓa ganin wanda ake hamdala a lokacin da ya zubar da hawaye ba sai ni Malika! Domin har addu'a maman mu keyi akan hawaye su sauko daga ido na, idan raina ya ɓaci, saboda idan har banyi kukan ba, to nakan ɗau lokaci ba tare da naci abinci ba, zan kwashe mako ɗaya ba tare da nayi magana ba, ka na zan ɗau tsawon lokaci zaune a wuri ɗaya! Mutane har tsegumi suke yi akan wai ina da Al'janu! Amma maman mu sam bata kula su, bawai don bata yarda ba, domin ita kanta tasan cewar ina da Al'janu, saboda yanda nake wasu abubuwa a wasu lokutan, ga kuma yawan GAMO da nake yi. Kuka nake yi sosai kamar raina zai fita, babu wanda yayi ƙoƙarin dakatar Dani a cikin su, suka barni saida nayi mai isa ta na gama, tsawon mintina Talatin, sannan Maryam taje waje ta ɗebo min ruwa masu sanyi cikin tukwanen Laka, ta kawo min, na karɓa nasha saida suka ishe ni, sa'annan na ajiye kofin na tashi na fita waje na ɗau buta na shiga banɗaki na fito, na dawo tsakar gidan mu tare da ɗauro alwala na shiga ɗaki na shimfiɗa darduma na tayar da Sallah. Har a lokacin Maman mu da Maryam suna nan a zaune, har ji nayi tana cewa Maryam ta lallashe ni na kwantar da hankalin na, idan dai akan fitar ne, to zata yiwa baban mu magana, saboda ita fa duk a zaton ta, akan fita gobe ne nake wannan kukan, saboda amintar dake tsakani na da Mansura, ni kuwa Allah ne kaɗai yasan abinda ke damu na, sam zancen baban mu bashi ya ɓata min rai ba, domin ko bai faɗa ba ni ba zanje walimar nan gobe ba, kai ba zan je ko wane event ba ma, wannan ma da naje ya wadatar. A wannan daren gaba ɗaya raya sa nayi da nafilfili da karatun Alqur'ani, tare da gayawa Allah kuka na, hatta da abincin dare banci ba, gashi a wajen Dina ma ban samu naci abinci ba, saboda yanda hankali bai kwanta ba. Kuka nake ina magiya a wurin lillahi wahidul qahhar, Alhayyul ƙayyum ya zaljalali wal Ikram, wanda baya barci ballanta na gyangyaɗi, ka na shike yin yanda yaso a lokacin da yaso, ya hanawa wanda yaso, haka zalika ya baiwa wanda yaso. Ni kaina na gasgata cewar babu abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma shine kaɗai wanda ya cancanci a bauta masa, a wannan halin da nake ciki, ni Malika nayi imani da cewar babu wanda zai share min hawaye na sai Ubangijin sammai da kassai bakwai, wato lillahi wahidul qahhar. Washe Gari Koda na tashi haka naji raina yayi fayau babu abinda ke damu na, na tsinci kaina cikin nishaɗi da annashuwa, wannan yana ɗaya daga cikin falalar ibadah! Domin duk mai yin ta bazai kunyata ba. Cikin kwanciyar hankali muka kammala aikace aikacen mu na gida, ciki kuwa harda girki. Nayi wanka na ɗauro alwala saboda lokacin har an fara kiraye kirayen sallar azahar, ban ɓata lokaci ba na shirya na fesa turare tare da sanya hijabi na tayar da Sallah, bayan na sallame na zauna nayi azkar tare da sake kai kuka na wajen mahalicci domin nasan yana ji, kuma yana gani, na tofe addu'ar na tashi zuwa barandar mu, wajen da Maryam ke jira na muci abinci. Hannu na wanke tare da zaunawa saman tabarmar na sanya hannu na fara cin abincin ina yatsina fuska, saboda yau tuwon shinkafa da miyar kuka muka yi, ni kuwa ba son kalar girkin nake yi ba, muna cin abincin muna taɓa hira nida Maryam, har take cemin wai zata so taga miji na, musamman idan shi masoyin tuwo da miyan kuka ne, sai taga yanda zanyi, nidai ban kulata ba na cigaba da cin abinci na, saiga maman mu tazo ta zauna kusa damu tana cemin wai na shirya muje walimar Baban mu ya haƙura. "Maman mu nifa babu inda zanje, gaskiya ba zanje wata walima ba, wanda naje jiya ma ya wadatar". Na faɗa ina cigaba da cin abinci na ba tare da na ɗago ba. "Wai Malika lafiyar ki ƙalau kuwa? Nifa ban gane miki ba, tun jiya fa na lura akwai abinda ya ɓata miki rai, bawai faɗan da malam yayi miki ba" Maman mu ta faɗa tana kallo na. "Maman mu dan girman Allah ki bar maganar nan, Ni wallahi banason zuwa wajen walimar nan" na sake faɗa ina cigaba da cin abinci na. Maman mu kuwa cewa tayi "to shi kenan Allah ya kyau ta" ta tashi tabar wajen. "Hmm lallai kuwa Malika, to ai saiki san me zaki cewa Mansura idan tazo, domin ɗazu kina salla ta kira, dana ɗaga take cewa wai nace miki ki shirya da wuri, zasu zo saisu wuce da ke"Maryam ta faɗa tana tunzure baki, tare da cigaba da cin abincin ta. Na ɗago da sauri ina faɗin "Maryam dan Allah idan tazo ki gaya mata, baban mu ne yace ba zanje walimar ba, yayi ta faɗa jiya kuma har rantsuwa yayi, kice mata yanzu haka ina nan a kwance bani da lafiya tun jiya, dan Allah Maryam ki gaya mata haka" na faɗa ina haɗe hannaye na duka waje ɗaya alamun roƙo. "Wa! Wai nice za'a yi wannan ƙaryar Dani Malika? To wallahi ba zanyi ba"........✍️ Karku manta har yanzu muna nan a cikin littafin GAMO MUKA YI 🤓. Yawan sharing da liking ɗin ku harma da comments, shine zai saka nayi saurin yi muku update 🤣🤣. Daga Alƙalamin 👑Queen Jiddah.... ✍️ [12/17, 10:55 PM] Queen Jiddah: The Pen Of 👑Queen Jiddah.....✍️ Channel Link https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H Update group Link https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=hqrt3 YouTube channel Link https://youtube.com/@queenjiddahhausanovelschannel?si=NajxqyDlNBtjeOPh Arewa Book channel https://arewapen.com/u/hauwaumusa06 Facebook page Link https://www.facebook.com/profile.php?id=61580403014165 Facebook group Link https://facebook.com/groups/559415480283144/ 🥹 GAMO MUKA YI 🥹 True Life Story By Queen Jiddah 👑 Chapter 12 "Maryam dan girman Allah kar kimin haka, wallahi ke kanki kin san haka kawai ba zance ba zanje b".... Da sauri na gimtse baki na, ganin yanda Maryam ta cire hannun ta daga cikin kwanon abincin da muke ci, ba tare da ta kula ni ba, taje bakin panpo ta wanke hannun ta tare da shigewa ɗaki, ta barni nan zaune sake da baki. Cikin sanyin jiki na karasa cin abincin, ina tinanin yanda zanyi idan Mansura tazo, saboda daga ganin yanda Maryam ta nuna min nasan ba rufamin asiri za tayi wajen Mansura ba, Maman mu ma nasan ba zata goyi bayan hakan ba. Da wannan tinane tinanen na ƙarasa bakin panpo tare da ajiye kwanon abincin na wanke hannu na, na dawo ɗaki na nemi guri na zauna, koda na shigo ma sallama na kawai Maryam ta amsa, ta juya kanta gefe tare da cigaba da dannar babbar wayar ta, Ni kuwa na koma gefe ina saƙa da warwara. Cikin barcin da ya fara ɗiba ta, na juyo sallama kamar Muryar Mansura, ban ankara ba naji an ɗa ka min duka a cinya, nayi firgigit na buɗe ido na, na kuwa ganta tsaye a kaina, tasha wankan ta na tsadaddar abaya tubarkalla Masha Allah, tayi kyau ba laifi, domin Mansura kyakkyawa ce sosai ajin farko, kuma fara ce sosai, irin jar fatar nan, gata mace ce mai jiki ko'inan ta ɓul ɓul da ita, ba kamar ni ba, figaggiya kamar a busa na faɗi, Ni ba fara ɓace, sai dai ina da hasken fata, domin ba zaka saka ni a jerin baƙaƙe ƙirin ba, sannan ni doguwa ce, tsayi na dai dai misali, ba mai muni ba, sai dai duk da cewar bani da jiki, inajin abokanai na na makaranta suna faɗin ina da sharp, ɗan jikin nawa ɗan ɗagwas dai dai da Ni. "Yanzu fisabilillah Malika bacci ki ke yi? Keda na gayawa ki shirya da wuri, saboda tare da Dear zamu zo, haba Malika" Mansura ta faɗa tana marairaice fuska kamar za tayi kuka. "Wallahi Yaya Mansura karki wani ɓata lokacin ki, kawai ki tafiyar ki, Domin Yaya Malika tace ba zata je walimar ba, har cewa ma tayi idan kin zo nace miki, ba tada lafiya kuma baba yace ba zata je ba saboda kawai"...... "Kai Maryam ya isa haka! Haba dan Allah, kince ba zaki yi ba, to ba shi kenan ba, meye kuma na maimaita zancen?" Na faɗa ina watsa mata harara tare da miƙewa tsaye ganin Mansura na ƙoƙarin buɗe labule ta fita ba tare da tace komai ba. "Mansura! Mansura! Dan Allah ki tsaya kiji, karki tafi" na faɗa ina riƙo hannun ta. "Malika dan Allah ki sake ni, kar raina ya ɓaci, dan wallahi ba raga miki zan ba, kin dai san hali na sarai" Mansura ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai tana kallo na. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke tare da ƙara riƙe hannun ta da kyau, ina faɗin. " Mansura dan Allah

Chapter 4 of 9