_"Mubajjal yana fita ya nufi wajen aikin sa inda ya fara a wani Private Hospital yana aiki ne ta fannin mata. Yana zuwa ya fara aikinsa ba kama kafar yaro amma kuma wani gefe na zuciyarsa tana tuna masa Alakakan da aka hada shi da ita wai yanzu aurensa saura wata biyu da wannam ficiciyar yarinyar gaskiya zata ci Ubata wallahi. Wani murmushi yayi na mugunta tare da wani kwafa. Sai karfe biyar ya dawo gida. Yana shigo yayi fanninsa yana shiga ya fada toilet yayi wanka ya saka jallabiya dan yau yace babu inda zai fita. Ya kira Wayan Mommyn sa yace aka wo masa abinci dakinsa yau baya sha'awan ci da kowa. Tasan halin yaron nata ta amsa masa da cewa ana kawo wa. Tana kashe ta kira Nusaiba tace kizo ki kaiwa Yayanku Abinci yana dakinsa badan ta so ba ta amsa da to Mommy daga haka ta shiga kitchen ta hada masa komai sannam ta dauka ta nufi dakinsa kirjinta na bugawa sosai. Da Sallama ta shiga yana kwance a falo yana kallo ya amsa mata a ciki- ciki ta ajiye masa zata juya yayi saurin fin cikota ta fadi a ka ji kake tum. Ta saki wani kukan azaba shiko ko tausayinta bai jiba ya kama kunnenta tare da cewa mai nace miki?. Ba cemiki nayi karki sake zuwa inda nake ba. Ko ke kunnam kashi ne gareki?. Ita dai kukan azaba take dan goshinta ya bugu sosai. Dan Ubanki baza kiyi magana ba. ya fada cikin tsawa. Cikin Kuka tace dan Allah kayi hakuri bazan sake ba. Mommy ne tace na kawo maka. Yaja tsaki tare da cewa tashi ki bace min da gani Allah yasa ki kara zuwa inda na ke zaki ga abunda zan miki. Ta mike cikin sauri ta fita dan yanzu kam ya fara bata tsoro. Tana shiga falonsu ta shige dakinta da gudu ta saki wani kukan sai da tayi mai isarta wani bacci wahala ya kwasheta tun daga ranar bata kara bari sun hadu ba duk hanyar da tasan wani abu zai hada su sai ta rufeta har Allah yasa ta kammala makaranta ya kama bikinsi saura sati guda kenam amma har yau basu hadu ba kusan wata biyu kowa yana rayuwarsa.shirye- shirye ake sosai har yau jumma'a ranar daurin Aure kenam._
*★★★★★★*
_" *Mujahit* ya turo gidan su *Malika* Kuma an bashi Auren ta dan yanzu kowa yasan *Mujahit* a gidan su *Malika* . Ta harkar kasuwancin sa kuka sai dai muce Alhamdulillah. *Nura* ma ya turo iyayensa kuma an bashi shima. Yauma Kamar Kullum *Mujahit* ne da *Nura* suka Nufi *ZONE B* wato anguwarsu *Malika* kenam sun ci kwalliya sosai. Suna shiga gidan suka samu Malika ta fito da wani tire ta nufi inda suke hira dan yau kam ma *Mujahit* bashi da niyar zuwa hira amma ta sakashi dole sai yazo tana kallonsa ta saki kayataccen Murmushi suka karasa gaba daya falon nam suka samu *Ikram* tana gyara wajen. Suka hau gaisawa nam kowa yaja tasa suka fara soyewa. *Malika* ne ta shagwabe fuska na cewa sai anje ansha Icream aiko nam *Nura* ma yace sai anje *Mujahit* babu yadda ya iya yace to shikenam kafin su gama su *Nura* sunyi waje har sun hau Mota sun fita waje suna jiransu. Su *Mujahit* ne suka taso cikin so da kauna sukectafiya sai dariya suke suna fito wan. A dai-dai lokacin Motar *Jawaheer* ta shawo kwana tana daga idanu taga *Mujahit* tare da *Malika* sai dariya suke daga ganinsu soyayya suke wani jan birki tayi........_
_Kuyi Hakuri da wannam bana da charge in har sun kawo wuta zuwa anjima zan sake muku postin in naga Comment amma_
*_NEXT PAGE IS LOADING........_*
_VOTES_
_COMMENT_
_08132761212_
*_HAFSAT A GARKUWA CE_*🥰
[4/19, 7:24 PM] Hafsat A Garkuwa🥰: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*_ABINDA AKA GASA...!_*
_Shi yaga wuta...🔥_
*TRUE LIFE STORY*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*_HAFSAT A GARKUWA_*
~_(Mummyn Seeyama)_~
*_Follow me on Instagram_* -Hayfa869
*_Follow me on whattpad please_* _@Hayfaluv_
My Novels
*_★ Kuncin rayuwa_*
*_★ Zaman takewa_*
*_★ Gidan mijina_*
*_★ Doctor hishmah_*
*_★ Sauyin Hali_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________________*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsa
*_________________________________________*
*_Bissmillahir rahamanir rahim._*
*AM BACK AGAIN*
*D̤̈ë̤d̤̈ï̤c̤̈ä̤ẗ̤ë̤d̤̈:*
_My Husband_
_Ina matukar alfahari da kai Mijina ka bani gudum mawarka sosai Allah ya barmu tare_
*_Page 33&34_*
*★★★★★★*
_" *Jawaheer* Wani Wawan Birki taja jika ke kir! Kir! Cikin firgici suka juyo suka kalli motar. *Malika* ta isa wajen tana cewa Jawaheer lafiyan ki kalao kuwa?. Cikin Karfin hali *Jawaheer* tace lafiya klao kai na ne kawai yake saramin. *Malika* yau ke na gani da saurayi. Keda bakya kula su. Yau kuma na ganki da wani. *Malika* tace wallahi da din ma ban samu wanda nake so bane sai yanzu shiyasa dan har an saka mana rana. Wani zare ido *Jawaheer* tayi tare da cewa an samuku rana fa kika ce?. Eh Nam da wata. Biyar za 'ayi Auren mu. Da Sauri *Jawaheer* ta figi motarta. Ta bat wajen gudu take sosai har ta isa gidan ta wanting. Hon ta buga wanda mai gadin yasan yaufa ba lafiya yayi hanzarin bude mata ta shiga saura kadan ta bige sa yayi saurin kaucewa. Tana Parking ta fito da gudu tayi cikin gida tana wani irin kuka ta zube a tsakar falo, kuka take sosai tana cewa Haba *Sultanah* mai yasa zaki cuci kanki?. Mai yasa zaki tsaya wata ta kwace miki Farin cikin ki?. Gaskiya gwara ki tashi tsaye domin ki kwato Abun Alfaharinki a hannunwa. Karki yi sake. Ta sake wani sakin kuka tana ta Sambatu. Da sauri ta dauki wayanta ta danna Number Uncle Doctor. Yana dagawa ta sake fashe masa da kuka cikin rikitar zuciya ce mai ya faru kike wabnam kuka?. Cikin kuka tace *Mujahit* ! Shikenam zan kara rabuwa da shi Har an saka masa rana da wata. Cikin kidimewa yace baza ki rasa saba *Sultanah* insha Allah *Mujahit* baki ne ke kai. Ina nam zuwa kiyi hakuri ki bar kuka. Daga haka sukayi Sallama taci gaba da wan kuka._
*★★★★★★*
_"A yau Jumma'a ne duban jama'a suka halacci daurin Auren *Mubajjal Hamza* da Amaryarsa *Nusaiba Kabir*. An daura aure akan Sadaki Dubu Dari da Hamsi. An daura Lafiya *Mubajjal* kowa Dariyar yake kawai yake yi *Mudan'sir* sai masa dariya yake shi kowa ya cika ya batse kamar bai tama dariya ba kafin wasu mutanen su gaisa dashi ya sa ki jiki ya bar wajen yayi bakin gidan su ya faka Motar yayi kwanciyarsa a ciki yana jin wani bakin ciki wai yau shi aka daurawa Aure da wannam yarinyar. Wai yau ni zan aure sauran Mai shago gaskiya anyi matukar cutata sosai. Yana cikin wannam tunanin yaji ana masa Norking. Dam kamar bazai bude ba ganin *Mudan'sir* ne yasa shi budewa. Yana shiga yace Haba Abokina ya ana gaisawa da kai kawai aka ne meka aka rasa?.Kai Malam dan Allah karka dame ni ka barni naji da abun da yake damuna. To Allah ya baka hakuri Ango cewar Mudan'sir yana yar dariyar Mugunta. Yace Yanzu zuwa anjima zamu shirya wajen Dinner ko?. Wani kallon Raini Mubajjal ya masa tare da cewa wai so nawa zan fada naka ni babu wani abu da zanyi a bikin nam to bari kaji na sake fada maka Wallahi Babu abunda zanyi na biki. Ya daka tsaki tare da mikewa ya tada Motar suka shiga cikin gidan. Yana fitowa aka fara rantaba guda aba masa tsiya shiko fuskar nam kamar bai taba dariya ba haka ya shige fuuu....! Kamar iska *Mudan'sir* ne yake amsa musu tare da ta yasu yi maaa tsiyar.Suna shiga ya zube akan Gadon sa Mudan ganin ba wanka zai shiga ba ne yasa cikin sanyin murya yace pls ka tashi ka shiga wanka kacshirya domin muje wajen Waliman nam kasan duk sun wuce mu ake jira. Babu yadda ya iya haka ya mike ya shirya cikincwani dakakkiyar Shadda Sky Blue shima Mudan shiryawa yayi sau daukan Kamshi suke suka fito suka tafi. A bangaren Amarya kuwa tunda aka Daura Auren jikinta ya mutu sosa dukctaji wani kasala ya shigeta duk sonta da Auren sai taji sam bata so. Amma fa Amarya tasha kyau sosai sai kyalli take zubawa. Su Yasmeen ne a gefenta sunata mata tsiya wai yau dai sai gidan Ya Mubajjal zata kwana bata so haka ba amma Daddy yace zuwa yamma za'a kaita gidan ta dake._
_"Arkillah Lowcos. Haka dai tayi zugum taba jin tsiyar da suke mata da wasu kawayenta biyu Rahina da kuka Sakinah. Ko Abinci ta kasa ci a ranar tana tunanin zaman da zasu fara da jan gwarzon ta. Da misalin Karfe 6:00pm na yamma na wannam ranar Wasu Motoci ne na fada a jiya suka shigo gidan su Mubajjal domin daukar Amarya aiko nam aka fara shiga aka fito da Amarya tana kuka sosai da kyar aka cireta daga jikin Hajiya babba da kuma Hajiya Karama suma sai da sukayi kuka. Hajiya Kaka ko dariyar ta take sha tare da cewa dole kije gidan mijinki! Nasan zaki sha walaha a wajen sa. Duk da saura zai dauka. Mutanen wajen sun jita ras amma babu wanda ya tamka mata dan sun san halinta ras. Ana ta shiga mota naga wata katowar mota aiko na kusa dan naga suwaye a cikin ta cikin Mamaki naga yan' grp din *Abinda aka gasa...! Paid Group* ne nace wadannam kuma ina suka san da wannam auren Basu samu damar gaisawa da kowa ba suka bi yan kai amarya dan kar a musu nisa basu san kuma gidan ba Gidan mutane kadan ne basu jeba dan suma iyaye ne shiyasa basu je ba Amma Hajiya Karama taje kai diyarta haka suka dauki hanba basu wani jima bacsaboda basu da wani nisa sosai tsakanin su. Nam naga sun faka a wani katafaren gida. Aka shiga da Amarya ta wagar *Abinda Aka gasa..! Paid grp* ma suka shiga su *Umm-Muhammad* sai ware ido ake yi anga gida kamar gidan Aljannah nam suka shiga falon gidan Babban falo ne da ya dau kayan more rayuwa Nam suka haura samma inda dakin Nusaiba yake kusa dana Gogan ta suna ajiye ta manyan ciki suka kara mata nasiha a tsatstsaye domin yanzu za'a mai dasu suka watse Su *Yasmeen* aka bari da kuma *Sakinah* da *Rahinah*. Domin su jira zuwan angwaye sai akai su dan kar a barta ita daya. Suna cikin hira suka ji Sallamar su Sis Nafisa yan' grp din Abinda Aka gasa...! Da Sauri Nusaiba ta mike domin ta gane su tace *Mom Haidar&Khairat* ! *Sis Nafisa* , *Ummu-Muhammad,* *Suleja,* *Maryam a tafida,* *Nana Khadii,* *mmn ibtisan,* *Ummu Eeman,* *Brr Husnah,* *Ummu suhaima,* *Mummy Jiddah,* *Halima,* *Zainab,* *Aisha Abubakar.* Lalle kun min karamci sosai wallahi nagode Allah ya bar zumunci *Mummy Jiddah* tace ba komai Kawa ai mun zama daya(Niko nace O ko yaushe ta santa har ta zama kawarta Ohoo Lol.). *Yasmeen* tace *Nusaiba* ina kika samu wadannam kuma?. Ta bada cikin sigar tambaya._
_" *Ummu-Muhammad* ne ta galla mata wani harara har da murguda baki(Kai Ummu Tambaya fa kawai tayi nima ai dole in tambaye ku yaushe kuka santa har kuka je bikinta). Nusaiba tace ke dai ki bari kawai wadan nam yan Amana ne a Grp Din *Abinda aka gasa...! Na Sister Hafsat A Garkuwa* muka hadu wallahi suna da mutunci sosai. Yasmeen tace aiko dai kam gaskiya muna godiya da wannam zumunci Nam kowa ya dauko abunsa ya kawo mata ya mika mata daga mai kudi sai mai kayan mata da dai sauran su. Su *Nana Khadii* iyayen Mako ne bata bada komai ba. Haka suka mike saboda driver yana jiran su a yau zasu koma. *Nusaiba* ha da dab kwallanta ta raka su har bakin kofa suna musu godiya suka rabu. Nam suka dauki hanya su sis Nafisa basu so subar gidan ba saboda gidan ya hadu sosai. Nam suka dauki hanyar kumawa. Su Nusaiba ko suka kuma suka zauna suna dan taba hira ganin fa Angwaye basu da niyar zuwa ne yasa Yasmeen tace bari dai na kira Ya Mubajjal dare sai yi take yi. Sakina tace gaskiya kam ta dauki wayarta ta kira sa sai da ta kusa katsewa ya daga tayi sallama ya amsa mata tare da cewa Yaya Muna ta jiran zuwan ku amma har yanzu shiro... kafin ta kara yace dama ai ban ce kowa ta jirani ba dan haka ku kama hanya ku tafi ba yanzu zan shigo ba daga haka ya kashe wayar. Yasmeen ce tace to kunki dai abun da yace dama Hand-free ta saka nam suka mike suka mata Sallam tana kuka suna kuka suka rabu Yasmeen ta jasu a motar ta suka yi gida._
*★★★★★★*
_" *Malika* ta sake baki tare da karasawa wajen *Mujahit* yace wanchar kuma waye take so ta bige minke dariyar yake tayi tare da sanar masa yadda sukayi. Sai da gaban sa ya fadi a yanzu ya sake tabbatarwa wannam *Sultanah* nan sa ce. To mai yasa *Sultanah* zata masa haka kenam?. Mai yasa bata Mutu ba za'ace ta Mutu?. Mai kuma tazo yi nam garin?. *Malika* ne ta katse mata tunaninsa ta hanyar cewa muje mana dan anaci yana ta masifa nam suka shiga motar *Nura* yaja su yana mita suka nufi Halwa I Cream. Wajene babba nam suka ta jidar Icream sannam suka zauna *Malika* da *Ikram* da kuma *Nura* ne kawai suke sha amma *Mujahit* ko kallon abun bai yi ba tunani kawai yake yi. *Nura* nevya lura da haka yace Abokina wai meke faruwa ne haka?. *Mujahit* yace ba komai kuyi kusaha mu tafi akwai abunda zanyi yanzu jin haka *Nura* yace kawai mu dauka mu tafi dashi *Malika* bata so haka ba amma suka tattara suka shiga motar suka tafi suka ajiye su a kofar gidan suka yi sallama suka juya.su kuma suka shiga gida. Suna juyawa *Mujahit* ya sanar masa duk abunda *Malika* ta sanar masa ya kara da cewa *Nura* babu makawa *Jawaheer* itace *Sultanah* ta. *Nura* yace Lalle nima yanzu na yarda da haka amma kana ga wacce hanya zamu samu dan mu gane itan ce. Da akwai hanya *Nura* kaga yau da ta gammu ta shiga damuwa sosai in har ta ci gaba da ganinmu da kanta zata zo ta fallasa kanta. Dole naci gaba da zuwa hira wajen *Malika* kuma dai-dai lokacin da *Sultanah* zata dawo daga aiki mu futo waje dancta gan mu dan *Sultanah* tana da matukar kishi. Gaskiya haka za'ayi to in kuka ka gane itan ce ya zaka yi da *Malika* . *Nura* ya zanyi da ita kowa dole sai na aureta dan bazan yau dareta ba amma inhar *Sultanah* ce Wallahi Zata kwacewa *Malika* fadar ta a waje na dab dama ba wani sonta nake ba wallahi kawai dai na rasa wacce nake so ne._
_Kuyi Manage da wannam Ina matukar Alfahari daku fan's dina wanda na sani da wanda ban sani ba Ina kaunarku a ko da yaushe_
*_NEXT PAGE IS LOADING......_*
_VOTES_
_COMMENT_
_08132761212_
*_MUMMYN SEEYAMA CE_*
[4/19, 7:24 PM] Hafsat A Garkuwa🥰: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*_ABINDA AKA GASA...!_*
_Shi yaga wuta...🔥_
*TRUE LIFE STORY*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*_HAFSAT A GARKUWA_*
~_(Mummyn Seeyama)_~
*_Follow me on Instagram_* -Hayfa869
*_Follow me on whattpad please_* _@Hayfaluv_
My Novels
*_★ Kuncin rayuwa_*
*_★ Zaman takewa_*
*_★ Gidan mijina_*
*_★ Doctor hishmah_*
*_★ Sauyin Hali_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________________*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsap
*_________________________________________*
*_Bissmillahir rahamanir rahim._*
*AM BACK AGAIN*
*D̤̈ë̤d̤̈ï̤c̤̈ä̤ẗ̤ë̤d̤̈:*
*_Ummu Suhaimah_*
```Ina jin dadin hot comment naki ina yinki irin sosai dinnam```
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ g͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
```My bestynah Hafsat Hafnan ƙaunarki daban take a jikinah bani da tamkarki kin nuna mun ƙauna sosai Allah Ubangiji ya barmu tare Allah ya ƙara mana ƙaunar juna.```
*_Page 35&36_*
*★★★★★★*
_"Haka *Jawaheer* taci kukan ta sosai Tana haka *Doctor* yazo yasameta da sauri ya ƙarasa wajen ta tare da cewa haba *Sultanah* mai yasa kike haka kefa kika roƙeni akan nayi nesa dake daga garinku amma gashi yanzu kuma kina kawo wani abun daban kuma. Haba mai yayi zafi haka Dan kawai kinga *Mujahit* shikenam kuma ki ruɗe. Kiyi hakuri karki tona sirrin nam Allah zai baki wani da danginsa zasu soki. Cikin kuka tace Uncle bazan iya hakuri da *Mujahit* ba ƙawata fa yanzu yake soyayya da ita gaskiya zan faɗa masa gaskiya. Dan ina son *Mujahit* sosai wallahi bazan iya rayuwa batare da shiba ada na haƙuradashi saboda bana ganinsa.amma yanxu ina kallonsa bazan iya haƙura ba. Jkin sa yayi matuƙar sanyi yace to shikenam Sultanah Allah ga baki sa'a Allah yasa ya dawo gareki. Ta Amsa da Ameen Nagode *Uncle* . Daga haka yayi mata sallama tare da fatan nasara yazo fita kenam ya haɗu da Rahmah kallonta yayi tare da cewa Rahma kin shigo kenam cikin dauriya tace Eh UnCle Ina wuni. Lafiya ƙlao ya mutanan gidan ku. Duna lafiya daga haka yayi waje ita kuma ta ƙarasa ta zauna kusa da Jawaheer ta na cewa ashe duk labarin da kika bani na ƙarya ne shine kika bani labarin Sultanah ashe shine labarinkin mai yasa kika ɓoye min?. Miye ribarki nayin hakan?. Mai yasa kika bar Mahaifiyarki kika dawo nam?. Mao yasa aka sanar da cewa kin mutu Alhali da ranki da kuma lafiyarki?. Haba Jawaheer. Cikin Kuka Jawaheer tace zan sanar miki da komai Rahma Amma kiyi hakuri zuwa anjima in munyi Sallar i'sha. Allah ya kaimu lokacin cewar Rahma tana buga Uban tagumi. Babu wanda ta kara magana a cikinsu har aka kira sallahr I'sha suka mike kowa ta ɗauro al'wala suka zo suma gabatar da Sallah kowa tayi ta zabga Addu'a barin ma Jawaheer .sanam Jawaheer ta fuskanci Rahma tana hawaye tace yau zan sanar miki *Abinda aka gasa..!* yau zaki san ya aka yi ban mutu ba yanzu kuma zaki san dalilinah na barin Ahalinah na dawo nam.ta fara da cewa._
```SHEKARU SHIDA BAYA```
_"Nam ta sanar da ita labarinta kaf fa ƙara da cewa a lokacin da Doctor ya shiga dani domin ya dubani yayi nasarar ceto rayuwata dama Numfashi nane ya ɗauke ya tsaya chak. Ina farkawa yace sannu baiwar Allah. Nace masa yauwa Doctor na gode da taimako. Yace ba komai yanzu ina ne ke miki ciwo?. Nace ba ko ina. Yace Alhamdulillah. Doctor dan Allah inaso ka min wani taimako._
_"Nam ya dawo ya zauna yace ina jinki.Allah yasa zan iya taimakonki. Insha Allah ma zaka iya na ƙara da cewa dan Allah Doctor in ka fita ka sanar dasu bana raye na mutu saka makon jinin dana bayar. Cikin firgici yace ke kuma miye ɗalilinki da zaki fadi haka. Cikin kuka nace saboda babu mai ƙaunata a duniyar nam, duk wanda ya sanni kuma yasan Labarinah sai ya tsane ni Alhali ba laifinah bane.Nam ta sanar dashi labarin rayuwarta ta kata ɗa cewa kaga in aka ce na mutu shikenam tsangwama da kyara ya ƙare.kaga zan bar garin zan kuma damu Mijin Aure dan Allah ka taimake ni. Share hawayensa yayi yace to in nace kin mutu ina zaki je?.kuma in za a sallace ki fa?.Duniya zan shiga har Allah ya hadani da mutane na gari, zancen gawa kuma nasan baza a rasa gawar da aka rasa danginta ba kaga shikenam an wuce gurin. Doctor yace zancen ki shiga Duniya bai taso ba, inhar kin amince akwai gida na da nake zaune da Matata aka min sauyin gurin aiki muka dawo nam mai aikin mu ce kawai a gidan a garin Abuja. In kin yarda zan kaiki chan ki zauna har Allah ya kawo miki miji, inhar kuma baki yarda ba nima bazan taimakeki da komai b a. Cikin kuka tace na Amince nagode Allah Allah ya saka maka da gidan Aljannah. Nam ya fita ya sanar musu. Tana jin yadda Mujahit yake kuka nima kuka nake sosai. Haka kuwa akayi aka dauko wata gawa aka mata wanka aka basu ita a maimakon nii. Aka kaita gidan ta na gaskiya. Sai dare tukun muka tafi da Doctor gidan sa Matarsa da taji labarina tayi kuka sosai a gidan na kwana, washe gari da safe muka ɗauki hanyar Abuja da Doctor da matarsa. Domin Aunty Aisha taki zama ita dole saita rakoni muna isowa banji mamakin ganin katafaren giɗan ba dan gidan da Doctor yake ciki nah Sokoto yafi wannam komai. Sallama mukayi muka shiga Baba Asabe wato mai aikin gidan ta amsa mana tana mana lalle marha bun._
_"Nam muka gaisa Doctor yayi mata baya ni ya kara da cewa zata zauna a gidan nam har Allah ya kawo mata Miji na gari. Baba Asabe tayi murna sosai dan dama bata son zama ita kaɗai ta nuna min ɗakin da zan zauna. Du Doctor basu tafi ba sai da ya siyomin duk abunda yasan zan buƙata tare da sayan kaya ya kaiwa tailer ya zo ya ganni tare da masa Alƙawarin nam da sati zai kawo min ɗinkin sannam suka tafi. A ranar na fara sabuwar rayuwa kullum ina cikin kukana rashin sanin halinda Umma nah take ciki, Baba Asabe tana bani kulawa tamkar ita ta haifeni kullum Doctor da Aunty Aisha sai sun kirani domin suji lafiyata kasan cewar ya sayamin waya kafin su tafi. Wata na. Biyu a gidan, Doctor ya juna min school jami'a da taimakon Allah tunda na fara ban samu matsala ba Samari ki nayi su kamar miye. A haka dai har na kammala na samu aiki a Hospital na kuɗi albashi na dubu talatin duk wata. A nam ne kuma na haɗu dake Rahma kika zama Aminiyata. Yanzu haka Baba Asabe watan ta ɗaya a garinsu taje ganin gida. Rahma wannam shine Labarina na ɓoye hakan ne saboda a Aureni da mutunci. Ba tare da wanda zan Aura yaji labari nah na gaskiya ba. Wallahi ina matuƙar ƙaunar mujahit kawai dai babu yadda zanyi ne nasan danginsa basa sonah. Ta fashe da kuka Rahma ma kuka take nam suka rungumi junah suka ci gaba da kuka mai sosa zuciyar mai karatu._
_"Tunda su Yasmeen suka tafi Nusaiba ta ke cin kuka sosai tayi kuka kamar ranta zai fitaSai karfe 12:00pm ya shigo tana jinsa tana kwance ta lullubu dan wani zazzaɓi ne ya kamata. Sai 1:00 sanna ya shigo ɗakinta. Yana shigowa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 13