ya sameta kwance tana bacci cikin kwanciyar hankali. Wani wawan duka ya ɗaka mata da sauri ta mike tana mai......_
```Kuyi hakuri da wannam my fan's ina matuƙar Alfahari daku sosai ina jin dadin comment naku Allah yabar mu tare```
```NEXT PAGE IS LOADING.......```
_VOTES_
_COMMENT_
08132761212
*_MUMMYN SEEYAMA CE_*
[4/19, 7:25 PM] Hafsat A Garkuwa🥰: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*_ABINDA AKA GASA...!_*
_Shi yaga wuta...🔥_
*TRUE LIFE STORY*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*_HAFSAT A GARKUWA_*
~_(Mummyn Seeyama)_~
*_Follow me on Instagram_* -Hayfa869
*_Follow me on whattpad please_* _@Hayfaluv_
My Novels
*_★ Kuncin rayuwa_*
*_★ Zaman takewa_*
*_★ Gidan mijina_*
*_★ Doctor hishmah_*
*_★ Sauyin Hali_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________________*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsap
*_________________________________________*
*_Bissmillahir rahamanir rahim._*
*AM BACK AGAIN*
*D̤̈ë̤d̤̈ï̤c̤̈ä̤ẗ̤ë̤d̤̈:*
```Wannam Page Sadaukarwa ne ga duk wani Maraya da suke fadin duniyar nam```😭😭😭😭😭😭
*_Page 37&38_*
*★★★★★★*
_"da sauri ta miƙe tana daka wani ƙara a zaton ta wani kwarton ne ya shigo mata wani tsawa ya daka mata tare da cewa ke ban son shashanci ba wannam wani irin hauka ne zaki sa makwafta suce ko yankaki nake yi. Maganar ta bata dariya sai dai kuma ba halin yin dariyar nam ta marairai ce fuska tace to Yaya Mai na maka? zaka min irin wannam ɗakar. Wani wawan mari yayi mata tare da cewa dan Ubanki ni kike yiwa wannam tambayar lalle ma kin raina ni. To wallahi ki sani baza ki taba zaman daɗi a gidan nam ba kin dinga fuskantar cin mutunci da barazana a gidan nam wawiya kawai. Daga haka yayi fice warsa tare da buga wani uban tsaki._
_"Abun ya bata mamaki bata ɗauka ƙiyayyan da yake mata ya kai haka ba sai yau gaskiya baza ta iya zama da shiba haka take ta magana ita ɗaya kamar zautacciya da taga dai kukan bazai kai taba taje da ɗauro Alwala tazo ta fata kai kukan ta wajen Ubanjigi. Sai da ta kai 3:00am sannam Ta zauna ta fara azkar har Assalatu Sannam ta gabatar da Sallah anan wajen bacci mai nauyi ya ɗauketa. Shiko tun daga fitarsa a ɗakin ya shiga ɗakinsa wanka yayi yazo ya zauna yana chart abunsa yana cin gasassaun kajin da ya siyo ko a jikinsa ya ma manta da wata amaryarsa yana gamawa yabi lafiyayyar gadon sa._
_Washa gari sai wajen 11:00 na rana Nusaiba ta tashi nam ma Wayar da aka kirata ne ya tada ta. da Salati ta mike ta ɗauki wayar Sister Yasmeen ta gani da Sauri ta ɗauka kafin tayi magana Yasmeen tace Auntyn mu kin tashi lafiya gamu nam zamu zo gidan ki dasu Sakinah zasu wuce yau. Cikin murna tace to Allah ya kawo ku lafiya. Ameen Amarya ya dai kike cikin murna ko dai Yaya jiya yayi aiki ne. Hawayen da take tarewa ne suka gangaro mata ta katse wayar Yasmeen bata kawo komai ba. Suka fara shiri. Itama wanka ta faɗa ta fito ta shafe jikinta da mayuka masu ƙamshi. Sannam ta ɗauko wasu Lace ta saka pink colour yayi matuƙar yi mata kyau sosai. Kwalliya ƙadan tayi sannam ta shiga kitchen tama rasa mai zata ɗaura musu. Nam ta tuna Yasmeen nason Sinasir da miyan kaji. Tana bude firji ta ga kaji guda uku ɗaya ancinye rabinsa cikin murna ta kammala komai tana cikin kaisu dinning ne sai ga Norking din su da sauri ta buɗe tana sakar musu murmushi._
_"Suna shigowa suka rungumi juna a murna nam suka zauna a falo suka fara gaisawa sai tsiya suke mata ita ko dariyar yaƙe kawai take musu dan ita tasan wani hali take ciki daga jiya zuwa yau. Dan yau kam ko ida nunsa bata gani ba. Yasmeen ce tace yanzu kam dai kinji abun da muka ji muma na aure shike nam nam da wata Tara zamu zo musha suna hawaye da take ƙuƙarin tarewa ne ya subuce nam dana idanunta suka cika da hawaye. Yasmen cikin ruɗewa tace haba Nusaiba lafiya?.mai yayi zafi haka. Kafin ta bata amsa ne Mubajjal ya sauƙo daga ɗakinsa cikin shigar ƙana nam kaya. Yayi kyau sosai sai dai fuskarsa a murtuke take. Yace ke Nusaiba zo nam daga haka ya shiga ɗakin da ke kusa da su. Da sauri ta miƙe yasmeen dai ido ta buɗe yadda taga Yayan nata yayi kamar bai san taba. Rahinah tace anya ƙalau suke kuwa?. Sakinah tace gaskiya ba ƙalau ba kam. Yasmeen ce tayi ƙarfin halin cewa aiko indai Yaya ne zakuce haka to bari kuji ƙalau suke zaune dama shi haka ɗabi'arsa take miskilin mutun ne. Sakinah ta taɓe baki tace to Allah ya basu zaman Lafiya. Duka suka amsa da Amin._
_"Nusaiba tana shiga da Sallama ta samesa zaune akan gado yana dannam waya. Dur ƙusawa tayi tare da cewa Ina wuni Yaya. Kamar bazai amsa ba yace Ƙalau. Daga nam shiri ya ratsa tsaka ninsu ita dai tana tsugune sai bayan mintina yace._
_"Mai kika sanar dasu dan gane da zaman mu jiya. Cikin Ƙarfin hali tace Babu abunda na faɗa musu Yaya._
_"To in kika sake naji wata magana kin sanar dasu wallahi zaki sha wahala a waje na. Insha Allah bazan faɗa musu komai ba. "Daya fi miki Alheri ki kawo min abinci na. "Ta amsa da To,daga haka ta mike ta fita kamar wanda ƙwai ya fashe mata a ciki. Shike da wata harara ya bita dashi._
_"Tana fita ta samu suna cin abinci dan Yasmeen ta gaji ta jiran fitowarta ne tace musu kawai suje suci abinci. Tace Yauwa Yasmeen dama ganzu zan zuba muku. Yasmeen tace to mu yau ina zamu tsaya jiranki kun maƙale a ɗaki. Nusaiba bata tsaya bata amsa ba taje ta hada masa komai da tasan zai buƙata sannam ta ɗauko ta fito ta shiga ɗakin da Sallama ta ajiye masa a gaban sa ta miƙe zata fita kenam yace ke dan Ubanki haka ake ajiye wa miji abinci ki dawo ki saka min. Jikinta na bari tazo ta saka masa ta juya ta fice tana goge ƙwallar da ta fito masa._
_"Su Yasmeen sun lura da halin da Nusaiba take ciki amma tambayar duniyar nam sun mata amma sam taki basu Amsa. Haka dole sukayi haƙuri. Mubajjal ko da ya fito a cikin fara'a suka gaisa Nusaiba tayi mamakin haka wato ni kaɗai yake yiwa wannam tsimewar. Haka da yazo fita ya ɗauki bandir ɗin yan dari biyar ya miƙawa su Sakinah yace suyi ƙuɗin mota._
_"Suka ƙarɓa tare da godiya bai bi ta kan Nusaiba ba yayi ficewar sa. Anam suka wuni har yamma Sannam Suka mata Sallah harda kukan ta dam sam bata son zaman gidan._
```Niko nace tun daga yanzu ai tunda kika yarda aka ɗaura Aure keda barin gidan nam sai mutuwa😹```
_"Haka taci gaba da rayuwa a gidan Ya Mubajjal kullum da abun ɗa yake mata na azaba kuma ko ɗaya babu wanda ta sanarwa yanzu Auren su Waya biyar kenam amma babu abunda ya taba shiga tsakaninsu shi a ban garen sa gani yake in har ya kusanceta babu abunda zai samu a gurin ta sai sauran Sado mai shago shi sam bai jin xai samu gamsuwa gashi kuma da shegen jaraba shi gani yake ma tunda yayi Auren Jarabarsa ta ƙaru amma sam bazai iya kwanciya da ita ba. Sai dai kawai ya ƙara Aure._
★★★★★★
_"Su Jawaheer sai da sukayi kuka mai isarsu sannam Rahma tayi ta bata haƙuri sannam tayi shiru. Nam Rahmah tace kiyi haƙuri insha Allah sai kin Auri Mujahit da yardar Allah. To Allah yasa Rahma. Ameen cewar Rahama tace miƙe tace sai da Safe Sultanah ki kwantar da hankalinki. Ba komai Rahma nagode ki gaida du Hajiya._
_"Daga haka ta fito tayi gidan su tana tausayawa Sultanah sosai tana kuma tunanin wacce hanya za subi dan ganin Mujahit ya fahimci Jawaheer itace Sultanah._
_"Tana wannam tunanin har ta isa gidan su Hajiyarta ta samu tana zaune tana jan charbi. Sai da ta kammala sannam ta ɗago tace ke ko a ina kika zauna haka?. Nam Rahma ta sanarwa da Hajiya duk abunda ya tsaida ta ta ƙara da cewa Wallahi Hajiya Jawaheer tana cikin damuwa sosai. Hajiya tace Allah Sarki wallahi na tausaya mata sosai Allah yasa Masoyinta ya dawo domin wallahi shi ya dace ta Aura. Dan shi mai rufe mata Asiri ne. Haka suka yi ta tattauna maganar._
_"Haka Mujahit yake zuwa wajen Malika babu randa bazai je shiga. Abun tun yana bawa Malika Mamakk har ya dai na bata dama ita kam tafi son kullum tana ganinsa. Yau kusan wata guda kenam Amma har yau bai sake haduwa da Sultanah ba. Kuma a dai-dai lokacin da take dawo wa daga gurin aiki suke fitowa sai sun jima a tsaye sannam yayiwa Malika Sallama ita dai bata kawo komai ba._
_"Yau ma Kamar Kullum Suna tsaye a bakin ƙofa tana sanar dashi yaushe zasuje hada kayan Aure domin Bikin Saura wata Uku ne. Mujahit yace ni ai kenake jira yanzu duk lokacin da kika shirya nima a shirye nake._
_"To Sai muje Gobe ko?.Allah ya kaimu. Bai gama rufe baki ba sai ga Motar Sultanah ta shawo kwana. Malika tace yauwa ga ƙawata da nake nema zata hada min Kayan Sokoto dan naji tayi zaman Sokoto nam ta tsaida ta da kamar baza ta tsaya ba amma ta tsaya Malika ta ƙarasa tare da cewa kaga ƙawalliya kullum sai naje na samu bakya nam. Sultanah tace eh wallahi aiki kwanan nam yamin yawa kullum a chan nake kwana yau ne na samu na dawo. Nam suka gaisa take cemata dama maganar mu ne na maganin Sokoton nam Auren fa Saura 3month Da ram kirjinta ya buga tace What! Tare da zaro idanu. Malika tace Yeah! Sultanah bata tsaya ba ta figi motar._
_"Abun ya bawa Malika Mamaki sosai nam Mujahit ya sameta ganin tayi mutuwar kasko. Yace lafiya kuwa. Nam ta sanar dashi abun da yake faruwa ta ƙara da cewa na rasa mai yasa tun randa ta gammu tare ta sauyamin fuska ko dai ka santa ne?. Ta faɗa cikin sigar Tambaya. Yace to bana ceba kinsan mu ɗa jama'a ƙila ta sanni ni kuma ban santa ba. Nam ta sauke a jiyar zuciya suka yi Sallama yana shirin shiga mota Suka ji kira kamar daga sama ana cewa Mujahit! Mujahit! ka tsaya._
*_Wacece Malika_*
```Senator Bashir Ahmad Shine Sunan Mahaifinta Babban ɗan siyasa ne kuma dan Kasuwa ta fanni daban-daban. Senotor Bashir babu wanda bai sanshi ba yana da Mata Ɗaya Hajiya Naja'atu. Yaransu Uku Allah ya basu Malika itace babba Sai Kuma Ikram Sai kuma Ɗan ƙaninsu Shureem yaran sun taso cikin so da ƙauna musamman ma Malika dan iyayenta suna matuƙar ƙaunarta musamman mahaifinta ya sakaltata sosai bata da kunya ko kaɗan in dai tace zatayi abu to fa babu wanda ya isa ya hana ta inko tace baza tayi ba babu wanda zai iya saka ta haka kuma ba'a mata faɗa komai yinsa take tamkar bata da mafaɗi amma kuna a kwaita da ƙwalliya sai dai kuma har yau bata iya girki ba dan bata taba shiga kitchen da sunan girki ba sai dai ta ɗi ba Amma kuma akwai kyau komai na duniya ta haɗa sai kishi na masifa da ta ɗaurawa kan ta Ikram ita ko babu ruwanta salihar macece mai hankali da sanin darajar na gaba da ita komai da ake so mace ta iyasa ta fannin gida Ikram ta iya sa dan sam bata barin Binta mai aikin su ta shiga kitchen ita kaɗai in har tana gida tare zasu shiga shiko Senotor ba mazauni bane kullum baya gida yana wajen kasuwancin sa.```
*_WANNAN KENAM_*
```Zamu kuma Asalin Labarin```.
_Kuyi Manage da wannam Ina ƙaunar ku my Fan's Ina mai Baku haƙuri na rashin jina kwana biyu yachin banjin daɗi ne Hafsat A Garkuwa tana Ƙaunarku Over_
*_NEXT PAGE IS LOADING......_*
```Votes```
```Comment```
```please share```
```08132761212```
*_MUMMYN SEEYAMA CE_*🥰
[4/19, 7:26 PM] Hafsat A Garkuwa🥰: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*_ABINDA AKA GASA...!_*
_Shi yaga wuta...🔥_
*TRUE LIFE STORY*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*_HAFSAT A GARKUWA_*
~_(Mummyn Seeyama)_~
*_Follow me on Instagram_* -Hayfa869
*_Follow me on whattpad please_* _@Hayfaluv_
My Novels
*_★ Kuncin rayuwa_*
*_★ Zaman takewa_*
*_★ Gidan mijina_*
*_★ Doctor hishmah_*
*_★ Sauyin Hali_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________________*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsap
*_________________________________________*
*_Bissmillahir rahamanir rahim._*
*AM BACK AGAIN*
*D̤̈ë̤d̤̈ï̤c̤̈ä̤ẗ̤ë̤d̤̈:*
```Abinda Aka gasa...! Fan's grp```
_ina matuƙar jin dadin hot comment naku over_
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ T͢h͢a͢n͢k͢s͢ t͢o͢*
```Hafsat A Garkuwa fan's grp```
```Al'umma writer's fan's grp```
```Fadar Ummu Fareesa```
```Tame gari fan's grp```
```Gidan littattafan Hausa```
_Ina yinku irin sosai dinnam_
*_Page 39&40_*
*★★★★★★*
_"Yau ma Kamar kullum Nusaiba ne zaune taci Ado cikin Atamfar ta riga da siket Sallam taji da sauricta miƙe ta bude wata matace ta gani ta sakar mata murmushi. Nusaiba tace sannu baiwar Allah. Matar tace Yauwa Sunana Maryam Mmn Adnan ga nam gida nam inda yake kallon naki nace dai bari na shigo mu gaisa. Nam Nusaiba tace shigo daga ciki magana. Mmn Adnan ta shiga ta zauna. Nusaibavta kawo mata ruwa. Sannam ta zauna suka gaisa. Nam Mmn Adnan tace Allah yasa zaki na zuwa mun nina wallahi bani da wani gida dana sani a anguwar nam da bana shiga nam ma naga muna kallon juna ne shiyasa na shigo.Nusaiba tace insha Allah in har ya barni zamuyi zumunci dama nima bana son zaman shiru wallahi. Nam suka ta hira kamar Sun daɗe da sanin juna._ ```Dama kunsan Halin Nusaiba akwai surutu``` _Sai da Aka yi La'asar sannam mmn Adnan ta tafi gaba ɗaya badan sun gaji da hira ba sai dan kowa lokacin dawo war mijinta yayi. Ta raka ta har bakin Gate sannam ta juyo. Ta zo ta zauna ta fara aikin nata wato Tunani. Tana Haka taji Sallamar Mubajjal. Da Sauri ta isa garesa tare da risinawa zata amsa Jakar hannunsa wani harara ya galla mata tare da jan tsaki yayi shigowarsa. Da sauri tashi gaban sa tana cewa. Haba Yaya wannam wani rin zama ne gaskiya in dai haka zamu ci gaba da zama gwara ka sauwake min na tafi gidan mu. Ya ɗaga hannu zai mareta kenam suka ji Sallama Mmn Adnan ne ta shigo ganin yanayin da ta gansu abun bai bmaa daɗi ba. Shiko yana ganinta yayi haurawarsa sama._
_"Nusaiba ta ƙaƙalo murmushi tare da cewe Mmn Adnan kaddai mantuwa kika yi?. Aiko kamar kin sani wayata na manta shine fa na dawo ɗauka. Nam ta ɗauki wayarta tare da mata Sallama ta fice tana Mamakin wannam zama da suke lalle akwai wani abu dake tsakaninsu. Da wannam tunanin har ta ƙarasa gidan ta._
_"Ita ko Nusaiba wani kunya ce ta rufe ta amma babu yadda ta iya ta shige ɗakinta. Tun daga ranar Mmn Adnan bata ƙara shigowa ba yau kusan sati guda Kuma bata sanarwa da Mubajjal ba bare taje ita amma yau tace zata faɗa masa ko zai yarda. Aiko haka aka yi bayan ya dawo yaci abinci taje masa da zancen cewa wannam matar da kaga ta shigo gidan ta na kallon namu ta jima rannam tace in ba komai mu kulla zumunci wallahi matar tana da kirki dama kuma kaɗai ci ya dame ni. Cikin tsawa yace wato an gaya miki dan shiga maƙota kikayi Aure to bari kiji wallahi ban yarda ki fita ba inko kika fita na lahira sai ya fiki jin daɗi. Dan Allah kayi haƙuri ni dama ba fita zanyi ba har sai ka amince amma tunda kace.... Da halla ne bani guri ya faɗa tare da bugeta ya wuce abunsa. Nam ta faɗi ta fashe da kuka._
_"Sai da tayi mai isarta sannam tayi shiru. Ta tashi ta shige ɗaki ta kwanta tana tunani. Wannam wani irin zama ne a kullum in gida suka kiraya kuma zama musu ƙaryar ba komai._
_"Haka zaman su yayi ta tafiya da daɗi ba daɗi kullum ne sai ya saka ta kuka. Aurensu wata 11 kenam Amma babu abun da ya sauya Mmn Adnan kuwa tana zuwa mata ta kuma sanar da ita cewa Mubajjal bai yarda taje ko ina ba. Mmn Adnan tayi tambayat duniyar nam akan ta sanar da ita damuwar da take ciki._
_"Amma Sam taƙi. Dan a kullum Mubajjal sai ya gargaɗe ta. Yau ma kamar kullum suna zaune da Mmn Adnan. Mmn Adnan na cewa wai ke Nusaiba so kike ki kashe kanki ne bari kiji wallahi ba a nuna wa na miji kana son sa sosai dan zaki gasu a hannunsa dan naga alama kina matuƙar son wannam Mijin naki amma kuma shi naga kamar sam bai damu dake ba._
_"Nam Nusaiba ta fashe da kuka tare da cewa wallahi kamar kin sani mmn Adnan sam Ya Mubajjal baya sona hasalima ya tsaneni tsana mai girma. Na. Tana kuka ta zai yane mata tarihin rayuwarta. Sosai Mmn Adnan ta tausaya mata nam ta shiga bata Haƙuri tare da cewa ki kwantar da hankalin ki insha Allah zan gaya miki Kissan da zaki nayi domin ki jawo hankalin sa sai yaji duk duniya babu abun da yafi so sama da ke._
_"Nusaiba tace Allah Mmn Adnan" Sosai ma Kuwa ke dai kawai ki saurari abun da zan gaya miki zamu fara tun daga yau."Kai amma fa Nagode Mmn Adnan._
_"Haba ba komai Ai mun zama ɗaya da farko dai tashi mu shiga kitchen babu musu duka shiga nam suka haɗa lafiyayyun Abinci da Juice masu rai da motse._
_"Suka dawo suka gyara falo da ko ina na gidan sannam tace mata ta shiga tayi wanka bari taje gida ta dawo."Haka kuwa aka yi taje ta Watsa ruwa tana fitowa Mmn Adnan ta shigo da gaushi a kasko a hannunta nam ta sa wani turare tace ta tsugunna ta ɗauko wani dan kyalle ta rufeta dashi._
_"Wani sihirtaccen Kamshi ne ya gauraye ɗakin sai da kaushin ya mutu sannam ta buɗeta Nam ta saka ta tayi kwalliya sannam ta tambayeta ina inda take ajiye ƙananam kayanta babu musu ta nuna mata._
_"Nam Mmn Adnan ta fara dubawa nam ta hango wata fitinanniyar riga wanda maraban ta da babu ma kaɗan ne. Ta miƙa mata. Da Sauri Nusaiba ta zare ido tace Mmn Adnan mai kuma zanyi da wannam?. nifa tunda nazo gidan nam ban taba saka ƙananan kaya ba._
_"Aiko dai yau zaki saka. Ta faɗa a takaice babu musu ta ƙarba Mmn Adnan tace inkin saka kimin magana. Daga nam ta fice ta barta tsaye kamar dotse. Nam ta ƙara ƙarewa rigar kallo pink colour ce. Tana da ɗan tsayi shara-shara ce gefe da gefen ta duk a yage take nam dai tayi dukake ta saka Bz sannam ta saka pant sai ta zura rigar da ƙyar ta shiga tayi masifar kamata sai dai ta mata mugun kyau. Kugunta ya fito sosai na Shanonta ma sunyi lintsum lintsum. Nam ta kira Mmn Adnan._
_"Mmn Adnan tana shigowa taga yadda tayi kyau tace masha Allah. Wallahi yau shi ko Gafaka ne sai yaji wani abu tattare dake nam ta kame mata kanta da robo ta zubo da gajin gadan bayanta sannam ta fesheta da turaruwa masu bala'in Kamshi._
_"Sai da ta gyarata tsaf sannam suka fito falo suka zauna Sannam Mmn Adnan tace kin san mai nake so dake yanzu kawo kunnenki. Ban ji mai duka faɗa ba sai ji nayi sun tafa da shewa.ta ci gaba da cewa Wallahi sai mun gama rikirkita shi sannam zamu fara rama abun da ya mana._
_"Sai yazo yana roƙon mu Allah Annabi sannam zamu sassauta masa nam suka ƙara tafawa. Nusaiba tace to ni dai gani nake kamat baza mu shawo kan saba. Hhmm to ki daina gani ma shawo kansa kamar anyi an gama. Uhm bari na tashi na tafi dan nasan yanzu yana hanya tunda har shida Saura._
_"Nagode Sosai Mmn Adnan Allah yabar zumunci. Haba ba komai Nusaiba ai ƴar uwa na ɗauke ki ke dai kawai kiyi abun da nace. Daga haka suka yi Sallama ta tafi. Shida na ciki sai ga Horn din Mubajjal nam Zuciyat Nusaiba tayi daram. Bayanvyayi parking ya fito tun Daga ƙofar Gate yake jin wani Kamshi na tashi a gidan nasa. Yana bude ƙofar ɗakin yaji Ƙamsho ya ninku. Nusaiba dakr zaune da guɗu ta miƙe tana Oyoyooooo...._
*★★★★★★*
_"Mujahit ka tsaya nace. Da Sauri duka juya domin suga wake wannam ƙiran. Amma wa zasu gani?. Sultanah suka gani tana yana tahowa da Sauri. Har ta iso ta same su ta isa gare sa tare da cewa wallahi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 13