An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
DAULAR
MUSULUNCIN
ABDUL SALINEADAM SHITU
Rayuwar musulunci ta dauko asali ne daga manzanni, an
kafa musulunci da tsantstsan jarumtaka ilimi, hikima da tsants
kaunar Allah da manzanninsa saboda babu abin bauta da gaski
face shi.
Allah swt ya turo manzanni tun daga kan Annabi Adamu
(AS) har zuwa Annabi Muhammad farsi (saw) a cikin Annabawan
Allah babu wanda ya zo duniya bai sha fama da kafirai ba, duniya ta
fara da yake-yake haka zata kare da yake-yake kuma duka saboda
yaki da musulunci wato addinin gaskiya.
Bayan manzanni Allah ya kafa sahabbai bayan sun shude
manyan tabi'ai, malamai, addinin Allah da wasu kafirai suka yi
rantsuwa ba zai kafu ba, sai gashi ya mamaye duniya yaje duk inda
ake rayuwa a duniya
Allah yayi alkawarin daukaka addininsa a duniyar sa ya basu
dama sun ci gaba da daukar nauyin kafurci sun ci gaba da kare
allolinsu har duniya ta dauki shekarau sama da dubu bayan wafatin
Annabi Muhammad farsi (saw) wadda shi ne manzo na karshe kuma
shi ne yayi mamayar da har gobe ake tare da ita.
Ya zama abin koyi ga malamai, jarumai, sarakuna, ya zamana
komai na duniya ana gudanarwa ne bisa koyarwarsa domin ya zamo
mafificin Manzo kuma gatan al'ummar karshe.
Daulolin musulunci an kafa su a duniya kafurai sun ga bayanta ta
hanyar makirci. Sun rarraba kan kawunan musulmi ta inda ba ayi
tsammani ba.
A shekara ta dari hudu da tamanin bayan wafatin Annabi
Muhammad farsi an yi wata daula da ta zo ta yi tsayin daka waj
kawo gyara da zamantakewar musulunci. An samu wasu ahli da
gabashin duniya wadanda yankin su bai kai ga Makka ba sannan
ratsa ta biranen Yahudawa ya shiga cikin biranen turawa sannan
kuma yana da iyaka da Larabawa.
Ana kiran yanki da Bahara, yanki ne mai girma kuma yana
cike da albarkatun kasuwanci saboda iyakoki da yayi da biranen
Larabawa da kuma turawa ga kuma teku wacce take da nisan da babu
bature
2 Page
3|Page
inda bata ratsawa a fadin duniya hatta yankin bakaken fata da
indiyawa.
Ganin yadda wannan birni yake da yalwa da kuma sanyi da
wadataccen abinci da kuma walwala domin babu wani launin zafin
rana da har zai saka mutum yana share gumi kullum Kasar a lullube
take da ciyayi.
Babbar rashin dabara da birni yayi shi ne ganin wannan
dandazo na yankunan duniya suna shigowa yasa Kasar ta fara
gurbacewa daga turbar addinin musulunci saboda cudanya da kafirai
yasa al'adunsu suka fara sauya wa hatta masarautar ta rage tsananta
wasu abubuwa da suka zama haramun.
Abubuwan na faruwa da yawan yan Kasar suna kokawa
musamman yan kauyukan da abin bai shafe su sosai ba, sai dai ta kai suna iya hana matan su da samarin su zuwa birnin Bahara saboda
tsoron juyewar tunani to amma hakan ba kara min tauye su yayi
saboda ya rage musu kasha hamsin cikin dari na tafiyar da
kasuwancinsu saboda samari su ne masu karfi a jika wajen tabbatar
da nasarar su a kasuwanci.
Sun Kai korafi ga Sarki Muhammad farsi salahudden amma
saboda kutse da nasara wa suka yi wa maasarautar ya kasa aiwatar da
komai duk da cewar Sarki ne adali mai kokarin ganin ya tafiyar da
adalci a mulkinsa
Babban sakacinsa amanna da wasu jigajigan fadar sa
wadanda sune suke tafiyar da komai na mulki, sai abin da suka so ya
ji,
Karku manta mun kira wata kabila a baya wacce ita ce kabila
mafi yawan mutane a cikin birnin Bahara amma kuma ita ce kabila
mafi riko da addinin musulunci saboda an samu manyan malamai da
suka taso a cikin kabilar marasa adadi wannan kabila ana kiran ta da
Kabilar Nur, dan haka ana kiran kauyen Annur. Kauye ne mai
dimbin tarihi wadda ya bar baya mai cike da alfahari, basu kai sauran
kauyuka birnin Bahara yawan mutane ba amma sun fi kowane Kauye
karin suna hatta a fadar sarki baka jin kalmar kowane Kauye face
Annur haka zalika munafukai masu yin zagon kasa suna ambaton
bature
4|Page
kauyen Annur a kowane lokaci, takororinsu kauyuka masu yin
hassada da kauyen suma suna ambaton kauyen Annur.
Abdullahi bin Sharjas Ibn Abdullahi kuwaif shi ne Hakimi
kuma jigo a cikin Hakiman Kasar Bahara.
Yana da shekara saba'in da bakwai. Yana da yaya takwas sai
da ya haifi yaya har biyar mata sannan ya haifi maza uku. Kubra ita
ce matarsa ta farko wacce suka yi gwagwarmaya rayuwa da ita, ita ce
take da mata hudu maza biyu, sai uwar gidan da take da mace daya
namiji daya, Ana mata lakabi da Humaira ibn Sa'ad
Yayansa maza biyu gwarazan jarumai ne masu kaunar ci
gaban musulunci, Babban shi ne Ahmad Abdullahi bin Sharjas
Abdullahi Ibn Kuwaif sai Jarumi Umar Abdullahi bin Sharjas
Abdullahi Ibn Kuwaif matasa ne masu karfi a jika, masu iya sarrafa
duk wani nau'in makami, masu hikima da basira.
Ahmad yana tsaka da horor da mata sa salon yaki a daidai
lokacin da yake cewa "Duk lokacin da yaki yayi tsamari ya zamana
kun, zamo yan kalilan a gaban abokan gaba kamar sun ninka ku sau
uku a hankalce ba za ku tsaya ku ci gaba da fafatawa da su ba, domin
za su yi galaba akan ku, abu na farko ku yi wa jagoranku inkiya don
ya hankalta domin yayi muku izinin ja da baya"
Da gudu wani mahayi ya shigo cikin filin a bisa ingarman
Dokinsa, yana zuwa batare da dokin ya tsaya ba ya dira gaban
Ahmad ya sallama gami da gaisuwa irin ta jarumai ya ce "Yarima
sako daga Yarima Jarumi Umar cewa ya bi sahun wasu daukacin
kekunan doki da suka fito daga Garin DURSA sun nufi babban birni,
ya shaida min cewa lallai yana bukatar mayaka su biyo bayansa.
Koda Ahmad ya gama jin haka sai ransa ya baci ya ce cikin bacin ra
"yaushe ne Jarumi Umar zai daina dauko magana, menene abin da
yayi masa zafi da kafiran Dursa da babbar birni".
Kowa yayi shiru yana sauraren Jarumi Umarni Ahmad kadan
ya ce "DAWAN yanzu shi da su waye tare na ga abokan tafiyar sa
suna muhallin su".
DAWAN ya gyara tsaiwa ya ce, daga ni sai shi muka fice tun
safe ayarin ne suna da yawa akalla mahaya doki ashirin na kasa
bature
5 Page
goma, tare da makamai don haka ya ce lallai sai dai ni na zo don shi
ba zai iya bari su bace masa ba don basu tare da`alkairi".
Ahmad ya ce "Maza ka sanar wa da abokan sa, ku yi gaba ni kuma
zan sanar da Sarki".
Kai tsaye Dawan yayi sauri ya tafi wajen abokansa dan sanar
da su hali da Umar yake ciki.
***
Wani kyakkyawan saurayi ne, mai tarin kyawu da zati irin na
mazaje yana da tsananin kwarjini shekarunsa za su tasarwa ashirin da hudu, Dokinsa wani ingarma ne ya zauna cif cif da shi kayan sulki ne
a jikinsa da takobi rataye a kugunsa, sai kibiya a kafadarsa ya rataya
ta. Ta cikin ciyayi yake bin sahun kafiran Darsun sannu a hankali
yadda ba za su gane ana bin sahunsu ba, daga nesa yana hango yadda
lamarin ke tafiya.
**
Duniya dole ne ta zama tamu, idan har muka bar yakar
musulunci muka juya baya tabbas za su ci gaba da yaduwa a doron
kasa su ci gaba da mamaya, saboda haka dole ne mu kashe
sarakunansu, manyan malumansu mu dasa mugun rikicin a cikin
yankunnansu, mu kwashe dukiyoyinsu, mu zamar da su bayinmu
abin bautarwarmu a doron duniya, Wannanshi ne yakin da zamu yi"
Koda Sarkin JARMUR JAKUB ya tsaya a nan a bayaninsa da
yake guduna a karkashin sarakunan Kiristoci sai ya dube su daya
bayan daya yana mai nuna su da hannunsa cikin izza da isa gami da
kasaita.
An halicci duniya domin mu ne, ba domin su ba, domin mu
ke da mafiya yawan Annabawa muke da yawan lardinai mafi kyau,
muke da fikira, mu ke da gine-gine mafi kyau, su bayi ne namu,
domin su ne manoma, su ne masu kiwo su ke kiwata mana mana
dawakai mu hau, su kiwata mana shanu, raguna, mu ci, saboda haka
ku sani yaki yaune muka fara da, ba kuma za mu daina ba, har
duniya ta tashi, domin mun yi imani baza su taba karewa ba, an faro
bature
6 Page
yakoki sama da shekaru miliyoyi haka za a ci gaba da yi a nan da
miliyoyin shekaru amma a wannan nawa ne yaki na ne, sai na kafa
tarihi mafi kuncin a dukkanin zuciyar wani musulmi duniya a duk
inda yake kowane yanki na duniya sai mun karar da su, domin sai na
rushe shirinsu, kamar yadda giwa zata take ginin toka.
Kai zababben Sarki wadda na wakilta JAREMI zuwa
jagorancin Birnin Hairam, maza ka koma birninka tare da
rundunarka rundunar da zan taso ta izuwa masarautarka ta ishe ka
tsari daga Azabar Sarki Muhammad farsi
Kai Philips ka Koma masarautarka cikin izza babu shakka ko
tsoro domin kana tare da kariyar Babban Sarkin duniya, kai ne kake
jagorantar yanki mafi hatsari yin wasarere da wannan yankin ba
karamar asara bace domin tanan muke mika guba zuwa ga babban
birnin Musulunci. Na dawo gare ku Geogi da Gillasi, yakin da kuke
yi da kauyen dake cikin birnin Ka da ku fasa na san sako zai
iske ni daga Sarki Muhammad farsi, a wannan lokacin da Sakon zai
yi iso wajena, a nan ne zan a jiye babban martani wanda yakin zai
tashi daga kawunanku zuwa gare ni, kowannen ku na sallame shi.
Sarakai huɗu waɗanda aka assasasu a jikin kasar Bahara
domin wanzar da rikici da rashin son zaman lafiya suka mike tsaye
domin komawa masarautansu.
JARUMIN UMAR
Lokacin da Jarumi Umar ya ga wannan rundunar dakarun na
kafurai sun nufi babban birni tare da wasu zaratan karata majiya
karfi, adadinsu zai kai kimanin mutum ashirin da bakwai sai wani
Kije wadda da alamu shi ne wani abu ke ciki ake bashi tsaro mutane
da ke kewaye da Kejin ya sa baya iya tantance mene ne a ciki. A
hankali yake bin bayansu domin tuni yayi aike ga abokin tafiyarsa
bature
7| Page
zuwa gida don sanarwa da mahaifinsa halin da ake ciki, sai da tafiya
ta yi nisa.
A dai dai lokacin da ya fara tunanin matukar an shiga birnin
Bahara an kai ga kasuwar Nur inda ba a banbance tsakanin kafuri da
musulmi komai zai iya kwace masa sai hankalinsaya tashi yake ji ma
kamar ya afka musu shi kaɗai domin ya ga shirin da suka zo da shi,
yana cikin wannan damuwar ne sai ya ga rundunar ta tsaya.
Shugaban tawagar ya bada Umarni a tsaya, duk da cewar
tafiyar bai ce ace an yada zango ba domin baza ta wuce ta sa'a ɗaya
ba. Don haka a ransa yake tunanin mene ne dalili tsayawar ta su.
Wani mahayi da sauri ya zaburi dokin su ya baro cikinsu ya
dawo hanyar bayan ganin haka ya sa Jarumi Umar dakatawa ya
kuma boye sosai a maboyarsa domin ka da wannan mahayi da taho
ya gan shi, mahayin ya zo daidai in da Jarumi Umar ke tsaye ya ja
dokinsa ya tsaya yana dube dube hakan ya tabbatarwa Jarumi Umar
cewa lallai akwai dalili, don hakaya kara boye kansa jim kadan
mahayin ya kara zaburar dokinsa ya sukwane shi zuwa inda ya baro
su.
Tafiya ce ta ba ta wuce rabin sa'a a ce an kai ga babban birni
ba, don haka babban cikinsu sai ya nufi wannan babban keken dokin
mai dauke da Keji take majiya karfin da suke tsare a bakin kofar
suka bude kofar Kejin.
Wasu kyawawan mata ne suka bayyana su biyu masu sanye
da fararen kaya da shiga ta mutumci "Ina da bukata".
"Kina da bukatar me?"
"Ina da bukatar yin fitsari".
Sai babban cikinsu ya dubi na kusa da shi ya kece da dariya
ya ce "Akan wannan bukatar kika sa muka tsaya, bakya kallon a
hanya muke ki yi kayanki a cikin Kejin mana kamar yadda doki yake
yi".
bature
8|Page
Dayar da take gefe daya ta ce "Ai mu ba dabbobi bane irin
ku, in za mu yi bukata waje muke samu killatacce a mutunce mu yi
A nan take ya ɗaga bulalar hannunsa ya jinjina zai shauɗa
mata sai Babban na su ya rike hannunsa ya ce "Ba mu da wannan
ikon domin an Umarce mu da mu kai su cikin koshin lafiya ba tare
da cin zarafi ba, yanzu abin da za a yi shi ne rufe kofa mu ci gaba da
tafiya,in ta ga dama ta yi in bata ga dam aba ta zauna da shi saura
kalilan lokaci mu karasa Bahara mu danka su ga tawagar Waziri
Ja'afar domin tura su wata masarauta".
Daga nesa da Jarumi Umar yake bai iya hango abin da ke
faruwa amma jikinsa ya shi fursunoni a cikin kejin kuma daga
dukkanin alamu wani babban al'amari ne shi yasa aka sashi a keji
wadda yake a rufe to ma mai zai kai su birnin Bahara da fursunoni
haka? Ya tambayi kansa amsar da bai da masaniyarta ke nan
Dai dai lokacin Wannan budurwa ta cikin Keji ta saka kafa ta
tare kafin Barden ya ida rufi kofar ta ce “Ni ce matsalar ku, wannan
da take da bukata baku da damuwar kubcewa daga hannunku, domin
ba ita ce kuke nema ba ni ce, don haka ina mai umartarku da ku ba ta
dama ta je ta yi uzurinta ta dawo sannan mu ci gaba da tafiya”.
Da shugaban da mai rufe kofar suka kalli juna a lokaci guda
ko me shugaban ya tuna sai kumaya gyaɗa kai alamar a bar ta,
sannan a saka mutum biyu su yi mata rakiya,
Dukka matan biyu suka dubi juna, uwar gidan tata ta jinjina
mata kai alamar karfin gwiwa ita ma ta mayar da martani amma a
cikin dar-dar.
Har ta fita ta na kallon ta. Ta nufi wajen da zata samu ta tsirar
da rayuwarta gadan-gadan majiya karfi na biye da ita aikuwa cikin
sa'a sai ta fyalla da gudu bana wasa ba, su ma su ka bazama suna bin
ta ta cikin ciyaye take suka zare Kwari da baka domin su harbe ta a
kafada.
bature
9 Page
Dayan daga cikinsu ya sakankance cewar ya gama samunta
sai kawai ji yayi ya yarda kwari dinsa kasa ga mashi nan ya huda
hannunsa ya fito ta baya, ya kwala ihu, dayan bai san ta ina aka yi
wannan harbin ba sai ya zare takobi yana jiran ganin ta inda
maharbin zai fito, kwatsam bai yi aune ba ya gan shi a gaban wani
katon sadauki mai suffer karfi Karo Jarumi Umar yayi masa da kai
kawai ya baje kasa a sheme.
Nan da nan ya bi bayan wannan budurwa inda ta diririce ta
ma rasa hanyar da za ta bi. Kwatsam ta yi ido biyu da Jarumi Umar a
gabanta kamar wani ifiritu Aljani.
Abin duka take nema domin ta kwaci kanta ya ce "Kwantar
da hankalinki, bana daya daga cikinsu, wadanda suka biyo bayan ki
na kwantar dasu jinya suna neman agajin 'yan uwansu, tun dazu
nake biye da ku”.
Kafin ta yi Magana wasu masu, masu hatsarin gaske sun nufo
in da yake da alamar dauke masa numfashi, kai tsaye ya zare takobi
ya kifar da masu guda biyu zuwa gefe yayi a dingore zuwa ga
budurwa ya fille kafafuwanta don ta samu zaman dirshan ka da
kibiya ta same ta. "Kar ki motsa".
Abin da kawai ta ji y ace ke nan sai ta neme shi ta rasa ashe
waani tsalle ya sake yi ya fita da gudu kamar walkiya ji kawai ta yi
mai harbin kibiyar yana ihu sai daga bisani ta ji karar karyewar
kashinsa ɓass! Da sauri ya dawo gare ta "Ta shi mu je na kwabotar
da ke suna da yawa, su iya cimmana".
"Gimbiya" abin da ya ji ta faɗa ke nan".
“Gimbiya” ya nanata gami da duban Keken dokin da kuma
dakarun da suka durfafo shi "Bari na jarrabawa sa'a Da izinin Allah.
Abin da ya furta ke nan ya zare takbobinsa ya tunkare su kai
tsaye ba tare da tsoro ba Jarumi Umar yana ji da karfin jiki don haka
ne a duk lokacin da zai kai wa mutum hari to sai ya saka jikinsa ya
bature
10 Page
bangaje a matakin farko kafin yayi amfani da takobi yan fara ɓasgar
fuskarsa da ɓalla kasusuwansa, ta haka ya fara kafin daga bisani ya
hau sara da suka da haka ya bazar da mutum goma kasa batare da
sara ko suka ba, gadan-gadan yayi kan sauran sadaukan su ma suka®
nufo shi cikin shiri ba tare da ɓata lokaci aka yamutse mutum ɗaya
ya zamar musu kamar shaiɗan, ko wacce zuciya tunanin yadda za a
magance matsalarsa ake yi addu'o'I su ke yi domin ganin yadda za
su kwaci rayuwarsu daga hannun Jarumi Umar Bin Abdallah kafin
ka ce mene ne wannan ya bazar da ragowar dakarun saura
shugabansu da ke bisa doki yana zazzare ido da barazana “Idan ka so
rayuwarka ta ci gaba da tafiya a doron kasa ka sallama idan kuma ka
so ka bi sawun yaranka da suke kwance cikin jinya mu je zuwa"
Duk in da jarumi yake yi baya ganin gazawa kullum gani
yake zai iya domin a ganinsa shi ma za a iya tara masa dakaru sama
da hamsin ya bazar da su, kamar yadda Jarumi Umar ya yi don haka
sai ya kyalkyale da dariya ya ce “Kai Jarumin kauye masunci
manomi kai gani kake wani abin bajinta ne domin ka salwantar da
yarana, to maza bisa kanka".
Ya rugo da gudu ya na ihu cikin salo ya fara kaiwa Jarumi
Umar sara da suka, Jarumi Umar yana kare sara ya na mayar masa da
kwarewa aka samu rabuwa ta martani shima yana karewa cikin
dan lokaci kowa ya fuskanci lagon juna bai san waye Jarumi Umar
ba shi yasa yake tsammanin zai zo masa da wannan salon ammaa
lokacin da ya yiwa Jarumi Umar wata shiga sai Jarumi Umar yayi
walankeluwa ya zille masaya wuce cikin iska fuu amma sai ya
tangaje shi da kafada aikuwa wannan shugaban Barada yayi wata
mummunan faduwa tamkar ya yi karo da dutse, tsoro da fargaba suka
ziyarce shi a karon farko ya so ya saduda amma sai ya tuna shi ma
Jarumi,cikin a zama ya mike tsaye ya fara neman takobinsa ya gyara
mata riko ya kara dawo wani shammace Jarumi Umar yayi ya gabza
baturė
11 Page
masa naushi wanda yayi sanadiyar fitar hakoransa, yaransa da da
suka samu ikon fardaduwa daga dakuwar da suka yi suka rirrike
shugabansu.
"Mai girma Jesus mu gudu wannan ba mutum ba ne".
Ya na dagewa haka suka ja shi suka haye dawakai suka gudu
Jarumi Umar yayi godiya ga ubangiji da ya bashi nasara ko da ya
waiga inda budurwa take ashe tuni ta kwance yar uwarta daga cikin
Keji ta kuma fito da ita.
A hankali ya kara so inda suke su biyu suna kallonsa su kansu
sun tsora ta da lamarinsa Gimbiyar ce ta ce "Waye kai? Ka sayar da
rayuwarka a kan ceton ta mu alhalin baka san mu ba,mene ne
bukatarka?"
Maganar ta cikin izza ta masarauta, haka akwai tunkaho da
isa a ciki, wato dole sai don wata bukata za a taimake su.
"Ni suna na Jarumi Umar, daga kauyenmu zuwa in da na
hange ku babu nisa, na saka ido ne a kan tawagar ku saboda tunanin
akwai wani abu da aka boye na tura abokina domin sanarwa Sarkin
garinmu cewar abiyo bayanmu saboda ga tawagar kafurai tare da
Keji waddaban yadda da shi ba ashekuwa wannan Keji dauke yake
daku. Nan da kauyenmu babu nisa, mu je na isar da ku wajen Sarki
domin a baku kulawa ta musamman'
"
Gimbiya ta ce "Mu na da nisa, sannan idan mun je kauyenku
tamkar mun kai muku jaraba ne domin dole sai an bibiyi sahunmu,
zuwa yanzu da ka tseratan da mu mun gode kabar mu mu shiga jeje
mu tafi can wani waje inda ba za a taba gano mu ba mu boya har mu
koma Kasarmu, ka sani cewa wannan tafiya da ake yi damu ita ce
tafiya ta karshe zuwa birnin nan don kai mu in da ake bukatar kai
mu,shi ne ka yi sa'ar dakatar da mu”.
Koda Jarumi Umar Bin Abdallah ya ji wannan zance daga
bakin gimbiya sai y ace da ita "Rayuwa kala biyu ce in ma a zauna a
bature
12 | Page
yi nazari mai kyau domin a samu a kubuta in ma a yi dirshan da
shawara mara kyau daga baya a yi danasani,zuwa fadar Abdalla tsira
ce daga gare ku, sannan Fadar Sarki Abdallah ba ta gudun Farmakin
abokan gaba, ba kuma ta juya baya daga ceton mai nema, idan haŋ
silar cetonku zai zame mana yaki, to za mu daura damara, idan kuma
sulhu ne za mu zauna a kujerar sulhu ya ke gimbiya kada ki yi jiji
dakai datakama ki biyo ni ba za ki tabe ba"
Da Gimbiya ta ji kalamansa sai ta samu yadda da abin da
yake fada mata amma a wata zuciyar sai ta ji wata kagawa ta zo mata
don me zai yi mata Magana a haka ba ladabi. Don haka sai ta yi niyar
kin daukar shawararsa. Duk da yayi gaba ya fara tafiya abinsa. Yar uwar tafiyarta wato Hadimarta HANZIYA ta dube ta ta ce "Ya ke
gimbiya kamar muna neman mu yi wa kanmu rashin adalci, a hakika
nin gaskiya muna neman dauki, ba don komai ba ko dan mu tsira da
rayuwarmu da kuma fadawa Koma Sarki Nasir kin sani sarai
matukar sun kai mu fadar Sarki Nasir duk wani takama da wani buri
naki ya kare babu wata mafita da ta wuce mu bi wannan sadauki”.
Gimbiya ta dube ta cikin alamun amsar shawarartada akasin
haka, daga bisani ta ce "Haka ne amma bakya ganin yadda yake
mana Gadara".
Hanziya ta yi murmushi “Ki manta da iko da takamamuna
halin neman ceton ne daga ubangiji kuma ya kawo mana wannan
Sadauki, lallai bujirewa wannan kamar rashin godiyar Allah ne".
Ba tare da ta kara cewa komai ba suka haye dawakai suka
nufi hanyar da ya bi suna biye da shi yana gaba a bisa Doki.
**
Birnin Bahara birnin albarka a wannan karni, kowane rai
yana fatan ya kasance a cikin birnin Bahara, saboda kasuwancin dake
gudana, sannan babu Kirista babu Arna, kowa yana iya rayuwa a
cikin birnin ya yi kasuwancinsa, sai dai bisa sharadi karya dokar
1
bature
1
28 Page
su kashe shi shi ne ya sa a wannan lokacin ba ni da wani sukuni tun
fara ciwo yau gobe lafiya gabana ki faduwa".
da Sarki yaHindu ta yi shiru cikin dan gajeren lokaci har sai da ta ji uwar
dakin nata ta share hawayen ta ja shessheka sannan ta ce "Neman
taimakon Hakimin Annur daidai ne a gare ki, domin shi mutum ne
adali kuma mai matukar son gaskiya, idan Allah zai baka kariya ba
da kansa zai zo ya baka kariya ba, amma shi ne zai zama sanadin
haka, kin fi ni sani duk wani ilimi a wajen kin a samo shi, tsantsaini
da tsoron fadawa halaka yake sawa kike wannan tunanin ai saka miki
damuwar da kuma tunanin nemo wadda zai tsayawa danki ki dauka
ubangiji ne yake haska miki, a da can ban da karfin gwiwa a game da
Yarima Abbas amma wannan maganar take ta sa na fara jin karfin
gwiwa, tabbas mu yi hanzari ka da