mu yi kasa a gwiwa”.
"Maganar ki gaskiya ce, wannan haka yake, to amma yake
Hindu ya kike gani za mu yi wajen ganawa da Hakimi Abdullahi bin
SHarjasllah, ki sani cewar matukar sun san wani shiri to za su gyara
na su shirin, abin da nake tunani wani amintacce za ki nemo min
wadda zai kai masa ziyara wadda shi da kansa Hakimi zai nemi
yarima ni kuma zan gayawa yarima sakon da zai je masa da shi".
**
Lokacin da Jarumi Umar ya iso babban turakar mahaifinsa, a
daidai lokacin Hakimi na nazari game da bakuwar Suhaila bin
✓ Ababakari da kuma tunanin sakon da Sarauniya Hauletu ta zo masa
da shi na son haduwa da Yarima Abbas.
A wannan lokacin ya yanke kai ziyara babban birnin domin
ganawa ta musamman da Sarki a game da sabuwar masarautar da ake
rigima a kai, sannan kuma zai yi amfani da wannan dama ya gana da
Yarima Abbas.
bature
14 Page
Ya tsaya yana jiran umarni daga Waziri Jafar. Batare da Jafar
ya ba shi umarni ba ya mike tsaye cikin izza da isa sai da ya yi taku
biyu zuwa uku sannan ya dakata yana kallon Jarfis sannan ya ce “Ina
sokon da kake tafe da shi?"
Jarfis ya gyara tsayuwa ya ce "An taho da Gimbiya zuwa
wannan birnin zuwa dan takin lokaci yarana za su iso da ita kamar
yadda ka umarta za a kaita masaukin da ka umarci a a jiye ta a can”.
Waziri Ja'afar ya ce "Ka tabbata ka zabi kwararrun kuma
masana wajen aiwatar da wannan aikin kamar yadda muka yi da
Sarki Jarmusu Jakub".
Jarfis ya ce "Kamar yadda ya umarce mu haka komai ya
gudana, daga nan zuwa kowane lokaci dan aike zai iya zuwa ya sanar
damu cewar an kai ta masaukin da ka tanada don kai ta can".
Waziri Ja'afar ya jinjina kai ya ce "Za mu ga ni,
sauraro".
kuma muna
Har Jarfis ya bude baki zai yi Magana sai daya daga cikin
yaron Kirzalu yayi sallama tare da cewa "Akwai bako daga Kiristoci
ya kara so".
Koda jin haka sai Waziri Ja'ffar ya dubi Jarfis ba tare da yace
da shi komai ba. Jarfis y ace "Babu shakka 'yan sako sun iso don
haka ya shigo ya gabatar da bayani a gaban Waziri Ja'afar".
Jim kadan bako ya shigo cikin dakin yayi gaisu wa da Jarfis
tun da Jarfis ya ga jikinsa duk rauni hannunsa na dama sai digar då
jini yake sai ya zabura ya ce "Ya kai Sarkal, mene ne yake faruwa na
ganka a haka ka tabbata kun iso da Gimbiya kun kaita inda aka
Umarce ku?"
Sarkal ya sunkuyar da kai kasa cikin nadama game da cewa
"Ya shugabana ka dauki rayuwata domin ba ta da wani amfani a gare
ka, mun yi rashin nasara gabatar da Gimbiya zuwa inda aka Umarce
mu".
bature
15 Page
Har Jarfis ya zare takobi zai sare masa kai sai Waziri Ja'afar
ya daka tsawa gami da cewa "Ni nake yanke hukunci a nan, saboda
haka ni ne zan dauki mataki a kan ka da kuma dan sakon ka".
Koda ya dakatar da Jarfis sai ya tako sannu a hankali zuwa ga
Sarkal "Kisan ka ba shi da wani amfani a gare mu face bata kaifi
takobi da bata waje, amfani daya ya rage maka a gare mu yanzu shi
ne "A ina kuka yi shashancin sakaci da gimbiya?"
Sarkal ya duka har kasa ya ce "Waziri nayi iya bakin kokari
na na ganin na cika aikina kamar yadda na faro shi, amma na gaza a
daidai madakatar Annur, inda wani Jarumi guda daya tal kamar
shaidani ya baiyana a gare mu, duk ya bazar da yara na suna can
cikin halin mutuwa ko rayuwa, dakyar na iya rarrafowa na kawo kai
na nan domin na sanar da ku halin da ake ciki".
Waziri ya jinjina kai game da cewa "Mutum daya kace kuma
dai dai mararrabar Annur. To me ya hada ku da shi a wane dalili?”.
Duk yadda ta faru Sarkal yay i bayani Waziri ya tafi nazari a
ransa yana tunanin waye wannan mutum daya, ko ma waye zai
kasance daga cikin jaruman Hakimi Abdullahi bin SHarjas. Koda
gama wannan tunanin sai ya dubi Kirzalu y ace "Maza ka basu
rawani da alkyabba mu isa Annur kafin faduwar rana, domin
matukar ba mu tafi da Gimbiya ba Hakimi Abdullahi bin Sharjas zai
yi wani abu maza ku shirya.
**
Fadar Hakimi Abdullahi bin SHarjasl cike da jama'ar ana
shirin bada umarni abi sahun Jarumi Jarumi Umar bayan da yayansa
Abdullahi ya bi shi tare da dakaru goma. Ana wannan zaman ne sai
ga Jarumi Abdallahi da mutum goma da ya tafi da su, gaba gare su
ga Jarumi Umar nan da Gimbiya a bisa dawakai sun nufo kofar gidan
Hakimi Abdullahi bin Sharjas. Kowa da ke wajen suka zuba wa
bature
16 Page
Jarumi Jarumi Umar da baki ido har suka iso bakin fada a inda
Hakimi Abdullahi bin Sharjas ke zaune a bisa kujera ga dattawan
gari suna zaune.
Jarumi Umar Bin Abdullahi bin SHarjas ya karaso fuskarsa
cike da annuri ya iso wajen mahaifinsa ya fadi yayi gaisuwa gami da
yin gaisuwa ga dattijan majalisa suka amsa masa.
Bayan Abdallah ya sauko daga dokinsa ya zo kusa da dan
uwansa sai ya dubi Jarumi Umar ya ce "Ya mai girma Mun fita
hanya don zuwa kaiwa Jarumi Umar dauki kamar yadda ka umarce
mu,sai muka gan shi ya taho tare da wadan nan matan guda biyu, bai
yi mana wani bayani ba, mu ka biyo bayansa har zuwa gida".
Guri ya kara shiru mutane suka mayar da hankalinsu ga
Gimbiya da abokiyar tafiyarta. Hakimin wato Abdullahi bin Sharjas
Annur wato mahaifi ga Jarumi Umar ya kalle shi cikin alamun son
Karin bayani Jarumi Umar ya gyara murya y ace “Ba wani abu da na
sani dangane da su Baba, abin da nasani shi ne na kwace su daga
Annabi hannun Kafirai ma'abota kaucewa daga koyarwa
Muhammad farsi, sun so na bar su su ci gaba da tafiya a cewarsu
zamowarsu a nan zai haifar mana da barazana gami da farmakin
abokan gabarsu"
Daga nan bai kara cewa komai ba. Hakimi ya dubi Gimbiya
da suke tsaye suna neman izini. Ya jinjina kai ya ce ‘Yata matso
kusa".
Gimbiya na jin haka sai ta jinjina kai alamar amanna sannan
ta taho ga tsoho Abdullahi bin Sharjas ta duka ta kai gaisuwa "Yata,
wace ce ke, daga ina kike?"
Gimbiya ta ce "Ranka ya dade Suna na SUHAILA BIN
ABABAKARI, ni 'ya ce ga Sarki Abubakari wadda yake mulki a
kasar Shamnun,an kamo ni ne a lokacin da nake kokarin tsarewa
daga masarautar mu domin gujewa ballewar rikicin sarauta, wadda
bature
17 Page
tun daga mutuwar mahaifinmu magauta suke ta kokarin ganin sun
hana kasar zaman lafiya, har yayan mu Yarima SALMAN ya gudu
daga kasar saboda farautar rayuwarsa da ake yi, saboda da yawa a
cikin kasar Yarima HALIL ne ya siye su don zama magajin mahaifin
mu, yayana Yarima Salman ya turo min sako na gudu a cikin dare
saboda matukar ya hau kan karagar mulki duk wasu ‘ya'yan
mahaifiyarmu sai ya kashe su, mummunan kisa, wannan shi ne abin
da ya baro ni daga kasar mu, sai kuma aka kamamu, aka kuma danka
mu a hannun wadan nan kafuran za su danka mu wani hannu da ba
mu san ko su waye ba a cikin Bahara shi ne Allah ya hada mu da
wannan Jarumi ya kubutar damu, amma suna yawan zantawa za su
kai mu wajen waziri Ja'afar don gabatar da ni ga Sarki Nasir
Su ka hada ido da Jarumi Umar ta yi masa kallon tambaya, ya
sunkuyar da kai kasa yana sauraren abin da mahaifinsa zai ce
matsalarsa dama dan uwansa Abdullahi da ya tuna hakan su ka yi ido
biyu da shi a dai-dai lokacin shi ma Abdullahi kallonsa yake irin
kallon tuhuma.
Hakimi ya ce "Duniya bata samu ba, sai da jini ya zuba,
addinin musulunci bai kafu ba sai da jini ya zuba, sulhu baya yiwuwa
sai an zubar da jini, taimakon ‘wata kasar da wata baya tabbata sai an
kwantar da wasu, ki saka a ranki ke ‘ya ce a gare ni kika taho neman
tallafi na, maza Shame'u zo a shiga da su ciki, koda duniya zata
3 tunkare ni, ba zan bari a tafi dake ba, Allah ya kawo ki ne gare mu
domin ya san za mu iya ji da duk wata bakar guguwa da zata
mamaye duniya..
Jarumi Umar ya jinjina lamarin yana wani murmushin jin
dadin tarba da mahaifinsa ya yiwa su Gimbiya. Hakimi ya dubi
Jarumi Umar ya ce “Abin da ka yi yayi dai-dai ɗana”.
bature
18 Page
Ba haka Abdallahi ya so ji ba,domin a zatonsa za a yi wa Jarumi Umar fada kamar yadda wasu lokutan yake debo ta da zafi azo a yi masa fada musamman fada da arnan daji. SHEMA'U ta zo cikin sauri ta talbe su, ta yi cikin fara’a da murmushi daya daga cikin kannen Jarumi Umar kenan. "Hakimi ya kara da cewa "Kowa ya zauna cikin shiri domin komai zai ya faruwa daganan zuwa gobe za mu iya yin baki" daga nan matasa da sauran wadanda babu su a zaman majalisar Hakimi duk suka koma bakin aik, dattawa da Hakimi suka ci gaba da tattauna a game da harkokin mulki na yau da gobe
Jarumi Umar dubi abokansa su hudu da suka saka shi a
tsakiya Daddar ya ce "Eh ba mu labari umi Umar dube shi duban
tuhuma y ace “Labarin me ke nan?"
"KUBAIT ya yi muurmushi tsolaya yace "Ka da ka yi mana
rowa mana, na ga fa yadda kake kallon gimbiya, ita ma na ga yadda
take kallon ka❞
Duk su hudu suka kwashe da dariya shi kuma ya hade rai
"Wai me kuke nufi ne?"
Kubait ya tsaya da dariya ya ce "Mafaraucin dabba ne yau
yayo farautar mutum, shin akwai wadda ya isa ya kwace masa abin
farautarsa”.
Su duka suka kara kwashe da dariya Jarumi Umar ya kara
hade rai "In kun gama nishadinku ku ne me ni, babu ni a cikin*
wannan gayyar".
SAKLAHUL ya ce "Ita fa ba kamar Jaruma bace, ko wani,
dutse mai nauyin gaske da za a nuna mata mazantaka, idan ka tafi ma
za ka dawo kana ba mu labarin, eh ita zuciya ba komai take iya
jurewa ba, domin wani abin gubace sai an fesar ake samun sukuni”.
19 Page
"Idan ku kun kuna da sararin da za ku na barin zuciyarku da
duk wani abu da bai shafi tafarkin Allah da ma'aiki ba,ni ba ni da
shi".
“Tafarki da sunnar ma'aiki duk suna daga cikin abin da muke
maka fatan kasancewa tare"
MU"AZ yay i furucin duk suka kwashe da dariya har yayi
nisa yana jin su. Wani tsaki ya kara yi a ransa ya ce “Shashashe, ko
me suka ga ni har ya sa suke zargin na kamu da so".
**
A nan take Waziri suka hau hanya don zuwa Kauyen ANnur
wadda anan ne za su ji su tabbatar da inda su Gimbiya suke a hanyar
ne Jarfis ya radawa Sarkal rada cikin hikima yadda babu wadda ya ji
abin da ya sanar da shi ya ce “Lallai zabi wani a cikin mutanen mu,
ka je ka labartawa Jagora Philiphis halin da a ke ciki domin ya san
shirin da zai yi."
"An gama ya shugaba na" Sarkal ya sulele a hankali ya je ya
sanar da wani daga cikin dakarunsa sakon da Philiphs ya sanar da
shi, ba tare da bata lokaci ba Mahayin ya sulele a dokinsa ya nufi
wata hanya.
Tun da suka fito daga babbar birni ba su kara yada zango ba
sai a cikin kauyen Annur. A dai-dai lokacin da Hakimi zai shiga
cikin gidansa sai ga tawagar Waziri nan cikin sauri sauri sun iso
bakin fadar Hakimi".
Koda Hakimi da sauran yan fadar da basu tafi ba suna niyar
tafiya suka ga Waziri a halin sauri sai suka dakata domin za su iya
tafiya Hakimi ya sa a kirawo su su dawo saboda ganin Waziri sau
tari babu alkairi a ciki ziyararsa.
Kowa dake wajen ya duka ya gaida Waziri amma banda
Hakimi Abdullahi bin SHarjas, kamar yadda ya saba a kowane lokaci
bature
9
20 Page
matukar ba fadar wani ya je ba ba zai zube yayi maka gaisuwa irinta
sarauta ba sai dai za ku gaisa kamar yadda shari'ar Allah ta ala ta
tanadar. Waziri ba yau kadai ya san da wannan rashin girmamawa da
Hakimi Annur yake yi masa, duk kuma yadda zai yi yayi domin a
kwace hakimanci daga hannun Abdullahi bin Sharjas abawa dan
uwansa SHAMSU BIN AUJAR amma sarki ya nemi dalili, ganin
dalilin rashin girmamawa ba zai sa Sarki ya sa a sauke Hakima
domin ko shi da kansa Hakimi baya masa gaisuwa da ta dace suna
rayuwa ne tare kamar da da mahaifi, kuma Sarki bai taba jin wani
abu a game da haka domin yana girmamawa Hakimi Abdullahi bin
SHarjas.
Bayan kowa ya nutsu Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya ce
“Lafiya muka ganka da yammaci likis haka ya Waziri Birnin Bahara
Allah ta Allah yasa dai lafiya".
Waziri ya waiga gefe da gefansa ko zai ci karo da wani alamu
na gimbiya, ganin bai hango komai ba ya sa ya dawo da hankalinsa
ga Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya ce Ko ka ji labarin batan Yarima
Salman ko 'yar uwarsa Suhaila bin Ababakari, ‘ya'yan marigayi
Sarki Ababakari?"
Kowa da ke wajen sai yayi shiru har sai da Waziri ya
tabbatarwa zuciyarsa akwai Gimbiya Suhaila bin Ababakari a
hannunsu, sannan ya kara da cewa "Ya kai Hakimi ka yi sani cewa
Wannan Gimbiya Suhaila bin Ababakari da wannan yaro Salman
lallai masu laifi ne kuma ababen nema ruwa a jallo, don haka
matukar suna nan ka gaggauta bani su domin na kaisu Masarautar
Shamnun domin gujewa afkawa yaki tsakanin kasashen musulunci"*
Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya yi murmushi ya kara taku
biyu zuwa gaban Waziri Ja'afar ya kare masa kallo sannan ya ce
"Yaushe Bahara ta fara tsoron ‘ya'yanta da fada da darashin adalci,
yaushe karamar kasa kamar Shamnun ta samu karfin gwiwar gwada
bature
21 Page
kwanjinta ga Bahara, har yaushe Bahara ta samu rashin kuzarin da za
a aiwatar da wani abu a wannan yankin da take da mallakinsa batare
da ita ce ta shugabantar da shi ba? Ya kai Waziri ina tare da Gimbiya
Suhaila bin Ababakari a karkashin tsarona, amma bana tare da
Yarima Salman, sannan ka sani babu mace a cikin rikicin rigimar
mulkin domin haka zaka iya tafiya neman yarima Salman ka kuma
gurfanar da shi a gaban Sarki Muhammad farsin, amma Gimbiya
tana tare da iko na".
Waziri ja'afar ya jinjina lamarin a zuciyarsa, domin ya san
taurin kai irin na Annur gabaki dayansu wasu irin jajurtattun mutane
ne marasa tsoro don haka dole ne ya sake sabon shiri don tunkarar
daukar gimbiya Suhaila bin Ababakari daga gare su……..
Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya katse masa numfashi da
cewa “Oh na manta, wai ma Sarki ne ya turo ka ko kuma zuwan kan
ka ne?"
Waziri yayi shiru,domin ya san cewar Sarki ba shi da sani a
cikin wannan lamarin duk yadda zasu yi su boye kada ya sani sun yi,
tabbas ya cika matsawa a cikin lamarin nan ya san cewar Hakimi zai
jewa da Sarki maganar wadda haka kuma barazana ce ga Yarima
Hilal don haka ya ce "A matsayina na mataimakin Sarki aka wakilta
ni domin daidaita lamarin birnin Shamnun, na kuma amince da
yadda Sarki, burina na hada kawunan Yarima Hilal da Salman".
Hakimi Abdullahi bin Sharjas yadube shi yace "Amma me ya
kawo kafurai suka tsare Gimbiya Suhaila bin Ababakari? Ko su ma
suna cikin masu nemarwa musulmai zaman lafiya?"
A rude Waziri Ja'afar "A'a bani da masani ya akan haka?”
Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya ce "Me yasa baka nemi ta
yadda aka samo gimbiya ba? An samo ta ne daga hannun kafurai
suna kokarin shigar da ita birnin Bahara shin wajen ka za sukai ta
dama ko kuma wajen Sarki?"
bature
(1)
Waziri ya kara shiga rudu amma sai ya daure yayi murmushi
gami da shafa gemu “Mene ne alakata da Kafurai da su kama
gimbiya su kawo min ita, babu mamaki sun kwace ta ne a hannun
mutanen da suka taho da ita, lallai mun godewa Allah da ta dawo
hannun na gari ba ta fada hannun yahudu da nasara ba, ya kai
Abdullahi bin Sharjas na barka lafiya ka kula da gimbiya Suhaila bin
Ababakari"
Koda fadin haka sai ya juya cikin sauri masu bi masa baya
suka bi shi da baya. Hakimi murmushi yayi kawai ya dubi jama'arsa
ya ce Za mu yanke shawarar abin da ya dace bayan Sallar Magriba
**
Sarki Muhammad farsi mutum ne mai son addini da ci gaban
al'ummar sa, yana da son addinin musulunci kuma yana bawa
addinin gudunmawa da gasken gaske, ta waje daya ya samu tawaya,
auratayya, ya hadu da mata mara sa kishin musulunci, da ci gaban sa,
wannan dalilin ya haifar da yaduwar masu taimaka masa a bangaren
sarauta suka zamo munafukai masu son duniya da abin da yake
cikinta, duk da tsatson su musulunci amma sulallan Zinare ya mayar
da su bayi, ba masu yiwa kasa hidima ba masu yiwa matan Sarki
Hidima game da bukatunsu, wannan dalilin yasa birnin ya zama ba
shi da wata kariya duk kokari da yake yaken da Kakaninsa suka yi
don gujewa fadawa tarkon Yahudu da Nasara soyayyar matar tasa ya
girbe dukkanin wannan nasara sun shiga tarkon Yahudu da nasara
dumu dumu, ana aiwatar da abubuwa da dama a cikin gidansa bai
sani ba, ana aiwatar da abubuwa a kasa bai sani ba, za a zartar da
hukunci bisa saka hannunsa batare da ya san an yi hakan ba.
Ba kowa ce Ummul aba 'isin wannan barnar ba face matarsa
ta kuma Siyamal Ihud, Siyama kyakkyawa ce ta kwatantawa,
bunkasa gidan Sarauta da haihuwar tanjamemen Saurayi wadda Sarki
yake matukar kauna kasancewarsa babban dansa Yarima YAZID
bature
22 Page
23 Page
bayan shi tana da 'ya'ya uku dukkansu mata, sai matarsa ta biyu mai
suna HAULE ibn Abbas 'yar babban wani shehin Malami ce a
wadda yayi mamaya a dukkanin daulolin na musulunci wadda ya
samar da litattafan addini, kwararre ne kuma wajen ba da magani don
haka Likita ne kuma Malami ne, aboki ne ga tsohon Sarki Wato
Junaid babban Muhammad farsi. ZULEHA ibn Abbas tana da yara
biyu mace da Namiji ta haihuwarta biyar ragowar duk an salwantar
musu da rayuwarsu,idan ta haihu yaro baya cika shekara biyu yake
mutuwa, wadan nan biyun ne Allah ya tseran mata da su wato
Yarima Abbas da kuma gimbiya Jauhariya.
Sai mata ta uku wato HAULE ita ma kamar SIYAMAN ce
har ta fi Siya ma iya makirci da tuggu, matsalar ita bata taba haihuwa
ba, don haka ta koma ta kama kafa da Siyama, saboda SIYAMA duk
ta fi su dukiya, saboda danta ana ganin shi nemagajin Sarki duk wata
dukiya da za a bayar kyauta ga gidan Sarauta idan ta wuce Sarki to
shi ita ake bawa, ko a al'adance itace Shugaban gidan ta fuskar
fifikon Sarki,ta fuskar siye duk wani wadda yake da ruwa da tsaki a
cikin gidan biyayya take yi mata, haka duk wani da ke wajen gidan
da yake da alhakin kawo ma'aikatan gidan Sarauta to shi ma bauta
yake mata, saboda haka sai abin da ta ce a gidan ake yi.
A lokacin tana zaune a kan hamshakiyar kujerar mulki ta
cikin gidan Zuleha na gefanta a zaune barori da 'yan aikin gidan
Sarki na zagaye da ita, wasu mata na can wata da'ira ana busa da
gara garaya suna dan rausayawa, ta na zaune idon ta kyam akansu
tana murmushi, wasu in sun shigo sai sun je sun yi mata kamar sujjada su kuma sumbaci kafafuwanta sannan su nemi wajen zama su
zauna.
A wannan Lokaci Hauletu na bangarenta ‘yar ta yar kimanin goma sha biyar na gefanta a zaune da barori waje da cikin daki suna
masu jiran wata bukata a isar mata da shi, kaf cikin masu mata
bature
241Page
hidima Siyama ce ta kawo su, mace daya ce aminiya kuma 'yar uwa,
wacce ita ce kadai amintacciya a wajenta wato HINDU. Da ita take
duk wani sirrinta a gidan.
Hauletu ta dubi 'yar ta "ZAHRA ta ce "Ki je daki ki kwanta
za mu yi Magana da Hindu".
Zahra ta dubi mahaifiyarta cikin girmamawa ta ce mike tsaye
gami da jinjina wa "Na barki lafiya".
Ita ma Haulet ta jinjina kai ta ce "Sai na shigo duba ki a
turaka ki yi addu'a sosai ki kuma yi karatunki kafin ki kwanta".
Zahra ta fara tafiya ta na zuwa bakin kofa wasu mata biyu
masu yi mata hidima suka bi bayanta doguwar rig ace a jikinta an yi
mata dinki da na kawa rigar jikinta har jan kasa take yi kamar
Dawisu yana tafiya. Sai da ta fice aka mayar da kofa a ka rufe sannan
Haulet ta dubi Hindu ta ce "Yake 'yar amana ta, me kika sani
dangane da Kauyen Annur,shin kin taba zuwa ko kuma kina da
labara, ko akwai wani da kika sani a kauyen".
Da Hindu ta ji wannan batu sai ta yi shiru tana nazari cikin
dan lokaci ta dago da kanta ta dubi uwargidanta cikin nuna kulawa
sosai ta ce "Amincin Allah ya tabbata a gare ki, ‘yar malamai jikar
malamai, jinin malamai matar hamshakin Sarkin duniya Muhammad
farsi, ina da sani a game da kauyen Annur, har ma ina da alaka da
Hakimi Abdullahi bin Sharjas, ya sanni farin sani, domin tawagarsa
ce ta samo ni, ta kuma musuluntar dani, kafin ta kawo ni gidan
Sarauta, saboda haka na koyi abubuwan da yawa a cikin kwanaki
goma da nayi a gidansa kafin daga bisani a kawo mu nan". Haulet ta jinjina kai “Yayi kyau, na kuma godewa Allah da
na samu haka daga gare ki, abin da yasa nay i tunanin tambayarki a
game da birnin Kauyen Annur na taba ji kina maganar Kirkin
matarsa Kubra, a lokacin da kike bawa Hindu labarin jarumtar
bature
25 | Page
kauyen, ban kuma ta shi bukatuwa da son sanin ba sai yanzu da wani
dalili da ya ta so".
Hindu ta yi sunkuyar da kai domin jin daga bakinn Haulet, jin
shiru yasa ta ce "Ranki shi dade me kike nema daga gare ni, in sanar
dake dangane daga Kauyen Annur”.
Sarauniya Haulet ta yi shiru daga bisani ta ce "Wani abu ke
dauremin kai yake kuma sani tunani game da rayuwar kauyen, gashi
karamin kauye ne amma yadda kowane munafuki yake tsoron
kauyen abin yana daure min kai, hatta Sarki akwai shakkar Annur a
ransa akwai girmamawa ta musamman, a bangaren Sarauniya
Zulehat kuwa bata da wani tashin hankalida ya wuce ta ji an am baci
kauyen Annur, mahaifina in har ya zo wannan yankin to zai ce da ni
zai je Kauyen Annur ban taba tambayarsa wani abu da ke faruwa a
kauyen ba, sai yau na tashi da son jin labarin kauyen shi yasa kika ji
na fara da tambayarki, shin me yasa duk mai mutumci yake girmama
kauyen, me yasa duk munafuki yake shakkar Kauyen?"
Hindu ta yi shiru tana dan murmushi tana tuna wasu abubuwa
da suka faru a kauyen kafin ta dawo gidan Sarauta ta ce "Zama ne ya
kama mu a gidan a lokacin muna matsayin bayi. A lokacin da muka
isa Kauyen Annur a matsayinmu bayi mun taho cikin kaskanci da
yunwa kishirwa da wahala, amma kallo daya Hakimi Abdullahi bin
Sharjas yayi mana ya fuskanci damuwarmu a cikin Babbar Kasuwar
Birnin nan.
A lokacin ya kawo abinci da dabbobi daga kauyensa don
siyarwa ya same mu a kasuwa a cikin wannan halin mu biyar ne.
maganar farko da ya yiwa mafarautar mutane "Ku basu abinci da
ruwa su sha, idan kuka kyautata musu za su yi daraja maimakon ku
bar su suna cikin yunwa ga wahala".
bature
Daya daga cikin Dakarun ruwan sai ya ce "Ba z aka koya
mana yadda muke sana'ar mu ba, idan sun yi maka ka siye su ka
basu abincin da ruwa".
Bai ji haushin bakar magar da yayi masa cikin fara'a ya cc
"Har nawa ne?"
Daya bayan daya ya fadi farashin mu, duk da kudin sun yi
ya kalli abokin tafiyarsa ya ce "Ka biya shi kudinsu”
yawa saiWannan mutumin ya dubi Hakimi Abdullahi bin Sharjas a
tsora ce ya ce "Ya kai dan uwana kana hauka ne, idan muka sayi
bayin nan da wadanan nan kudin dukkanin kudin mu sun kare, ga shi
ba za mu kara dawowa kasuwa mu sayar da amfanin mu ba, har sai
bayan sati, wannan ba karamar barazana bace ga rayuwar mu da
iyalin mu".
“Ya dube shi ya ce “Ka biya su na ce da kai, Allah da ya
halicce mu, shi ya hore mu da kyautatawa da abin da muke da shi,
yayi alkawarin ninka mana, na ji tausayin matan nan kuma ina saka
rai Allah zai ninka mana a nan gaba"
Haka kuwa a ka yi ya saye mu ya kawo mu gidansa ya ba mu
Kalmar shahada muka amsa matansa suka koyar da mu addini. In
takaice miki a kwana biyu wani Sarki ya kawo ziyarsa a cikin mu
Sarkin ya sayi bayi guda biyu, dukiyar da Hakimi ya samu duk da ya
rangwantawa Sarkin akan yadda ya biya shi domin ba ciniki aka yi ba kawai y ace In an sayar masa zai bada ninkin biyar na yadda aka
saye su, a su kadai sun dawo da dukiyar da Hakimi ya saye mu, kafin
Sarki Muhammad farsi ya zo da tawagarsa don ziyarar Hakimi a
halinsu na dawo daga tafiya ya biya kudin mu uku shi ma kuma
ninkawar yayi kamar yadda waccan yayi,a duk da Hakimi ya so ya
bada mu kyauta, amma Sarki Muhammad farsi ya ce ya kara ninka
kudin.
bature
26 Page
27 Page
A zaman da nayi a cikin ahlinsa na so ace na ci gaba da zama
da su, domin tun daga ranar da suka fahimci ya amshi addinin
musulunci da gaske sai suka kasance da ni cikin kulawa a dan
kwanaki da nayi mun saba sosai har sai da nayi kukan rabuwa da su.
Yau shekara goma ke nan kin ji ta inda na san adalci da tausayi irin
na Hakimi Abdullahi bin