Jeji su yi karamar farautar
abin da za su zo da dare su gasa a naman da suka samo, suna gasawa
suna ci suna hirarsu cikin aminci da kaunar junansu.
Koda ya fito Shema'u na gefe guda tana kallonsa, har ya isa
bargar dawakai ya kwance dokinsa ya jawoshi izuwa farfajiyar tsakar
gidan. Ya saka masa siddi yana shafa gashin dokin, kamar ance daga
kanka ya daga kai domin duba turakar da aka sauke su gimbiya
Suhaila, dafda lokacin ta fito daga cikin turakar suka yi ido biyu sun
dan jima suna kallon juna. Kunya ta kamata a lokacin da ta dawo
hayyacinta ba, ta yi gyaran murya gami da karasowa inda yake.
Shema'u tana tsaye wani haushi ya kamata ta ji kamar ta je ta shake
ta ta mutu, dole sai ta yi maganin wannan yarinya dole ta fada cikin
ranta.
Gimbiya Suhaila ta kara so dauke da murmushi da kuma
kunya rungume a fuskarta, kyakkyawa ce Suhaila a fagen kyawu,
tana da zati da haiba matuka gaya tana shafa bayan dokin “Jarumi ina
kake shirin tafiya?"
bature
2
95 Page
Ya tsaya da shafa wuyan dokin cikin murmushi ya ce "Yar
Sarki zan tafita farauta ne ni da abokaina?"
Ta daga idanuwanta dara dara kamarmadara farare sol ta kara
da tattausan murmushi "Farauta a wannan lokacin?"
Ya ji wani abu ya soke shi a cikin ransa hankalin kwance ya
ji yana rage shakkarta domin yana ji a ransa akwai wani abu dangane
da ita "Muna zuwa farautar yammaci domin samar da abin zai ta ya
mu zama a daren da zai gabata".
"Uhmm"
Ta daina shafa dokin ta rike hannuwanta guda biyu waje guda
"Yaushe ka huta daga doguwar tafiya da har zaka fita, farauta kar
kamanta tafiya sa'a biyar ka shafe a hanya zuwa nan me zaihana ku
hakura ku huta, hutu yana da dangantaka da samun karfin gobe”.
Ya yi murmushi "Na so haka, to amma shi ma yawaita motsi
yana kara samar da horarwa a kowane irin hali, ban sani ba ko
abokan tafiya ta za su iya biyo don ban sani ba”.
Tana tunanin wani abu a ranta amma babu lokacin nazari ta ji
bakinta yana fadin abin da ke ranta "Dama za su ki zuwa su barka
kai kadai".
hakan".
Murmushi yayi "Idan basu je ba ke zaki yi min rakiya?"
Ya fada cikin karfin gwiwa domin yana tunanin tana bukatar
Ta kara fadada murmushinta "Zan so na fita farauta domin na
kara ganin salonka".
Murmushi ya kara yi ya mika mata linzamin dokin don ta rike
ya nufi bargar dawakai da murmushi a ransa ya jawo wani
kyakkyawan farin doki ya ce "Batare da na ta kura sub a mu je nay o
mana farautar?"
Murmushi kawai ta yi ta kama dokin ta haye, shima ya haye
nasa dokin suka jera Kubrat na daga cikin babbar turaka tana
bature
kallonsu, murmushi ta yi kawai ta jinjina lamarin domin ta gama
karantar yanayin.
Tun daga farfajiyar gida suka fara tafiya sai da suka fita cikin
gari sannan ne ta zaburi dokinta domin ta jangwalo shi su yi tsere
yanayin yadda ta hau kan dokin tun a fari ya fahimci kwarewarta da
iya sukuwa, don haka bai yi mamaki ba domin duk ma'abocin doki
mafi kwarewa ya samu fili to zai sake shi ne, bai gama murmushi ba
shi ma ya rufa mata baya. Gudu suke suna kara dawakai kwari
gwiwa suna tsale da shillo.
Da wasa ya dauki abin har suka isa inda nan ne za su dakata
amma bata tsaya ba yana mata alama da ta tsaya domin an zo gejin
da tsallaka shi zai iya zama matsala amma bata fahimci abin da yake
nufi ba, ya karawa dokin kaimi a karon farko ya tisa ta a gaba,daf da
zai isa inda take ya hango wata rundunar mayaka marasa iyaka sun
yanyame ko'ina tana waigensa bata Ankara ba tana kara tunkarar
wadannan mayakan, batare da ya dakata baya ci gaba da zaburar
dokinsa don ya hanata isa wannan wajen ya zamana bai fi kiris ya
rage ta isagare su ta juya ta cigaba da kallon gabanta sai idon ta yayi
tozali da dakaru sun tsaitsaye suna kallonsa har ma wani dake
gabansu ya amshi kibiya ya saita ta yana shirin harbota. Umar yayi wata kabbara dokinsa ya shakan nata dokin ya ja hannunta don ta yi
gefe aikuwa tana kaucewa kibiyar ta wuce fuu!. Ya sake hannunta ya
ce da ita "Juya"
A tare suka juya dawakansu suka kara zaburarsu a fusace
"Zaki iya ko na dawo da ke nan?”
Cikin nuna jarumta ta amsa "Mu je zuwa".
Shugaban dakarun Mangalawa Sashin ULGUT ya dakawa
wasu dakaru goma tsawa "Ku zo min da su".
Nan take suka su ka bi bayansu a tsiyace gudu na kece raini
aka dauka ana fafatawa ga harbi da suke yi da kibiya da jifa da
mashi, hakan yasa zuciyar Umar ta karaya domin yana ganin
Gimbiya Suhaila zata iya sarewa don haka ya ce da "Ki yi maza ki
bature
96 Page
97 Page
karasa gida abokaina ki sanar da su cewar ina cikin halin fada da
Mangalawa lallai su kawo dauki kafin su cin min?"
Ta dube shi "Ba za ka iya
ka".
fada dasu kai kadai b azan taya
"Idan baki yi maza kin je min dukkaninmu za mu iya rasa
rayuwarmu, ki yi maza wannan ita kadaice mafita".
Suna gudu a dawakai suna maganar ganin za ta yi masa taurin
kai yasa ya dakamata tsawa “umarni nake baki ki tafi”.
Takobinsa ya zare tashin farko ya kade wani mashi da yayi
dokin wuyanta, har sai da ta yi wata 'yar kara saboda firgita. "Ki
tafi".
Ya kara maimaita mata ta karawa dokinta kaimi domin bin
umarnin Umar amma tana tafiya tana juyo tana kallon yadda ya bi
wasu mutum uku da suke son biyo bayantaya tsare musu hanya suka
fara dauki ba dadi da su. Mangalawa suna damasifaffen naci da
dagiya wajen yaki basa iya bijerewa umarnin shugabansu koda
mutuwa ce ta gabace su. Don haka su ka rufe sun hana shi
sukunikamar yadda ya hana ko dayansu ya bi bayan gimbiya Suhaila.
Har sai da ta kuleya daina hangeta sannan ya kara rikon takobinsa
"Ka mutu ka mutu ka mutu" a bin da kawai suke fadi.
Yana da tarihin fada da Mangalawa domin tsananin yawansu,
idan kana yaki da kadan akwai da yawa bisa hanya don haka dole ya
yi aiki tukuru ya kararda wadannan mutum goman a cikin kankanin lokaci.
Wani da ya raina Jarumi Umar ya fito cikin daukar numfashin
Umar da niyar suka masa mashi, Umar ya goce ya daki bayansa, nan take ya fado daga kan dokinsa, kafin ya mike wani ma ya kara
kusanto umar a fusace, da niyar Sarensa da gatari, cikin karfin hali
Umar ya dake hannunsa gatarin yayi sama Umar ya riga shi kama
gatari take ya sara masa shi a goshi ya barmasa shi a tsakiyar kai
wanda ya fado daga kan dokin ya yunkura yana kokarin cillo Umar
daga doki, kafin yunkurinsa Umar ya saka masa takobi a tsakiyar
kirjinsa, duka a cikin dakika ya kamala kasha mutum biyu.
bature
"
Wasu fusatattu hudu suka taso masa domin daukar fansar
mutum biyu ya zabiri dokinsa yayi zarya da su domin su bashi sarari,
yana jinjina takobinsa akan iska fusataccen ciki ne ya ma dogon
mashi a hannu ya karaso yana ihu da karaje ya kawo suka ya goce,
ya wuce fuu Umar bai yi sa'ar sare masa kai domin gocewa sarar da.
yayi, hakan ya bashi damar jin kansa amatsayin wanda zai gama da
Umar falan daya domin sun yi turmi daya kowa bai samu nasara ba.
3
Ya juyo da dokinsa kamar yadda Umar yayi suka fuskanci
juna wani ma daga bayan Umar ya nufo shi domin su saka shi a
tsakiya su lahanta shi, amma Umar sai ya kara gyara tsayuwarsa
wancan dake gabansa saito dogon mashin ya kara sukwano dokinsa
domin ya tsire Umar shi kuma daya ya nufoshi domin su hadashi su
masa farat daya,cikin matsinancin wanda ko bamakami in har an
hadu sai an ji jiki aikuwa Umar yayi amfani da dabara ya saka
takobinsa ya dakemashi ya sauya mashin hanya take na bayansa shi
da ya zo da mugun nufi sai mashin ya tsire shi a idonsa na hagu. Ya
kwala ihu mai tsanani Umar ta dake dokin mai mashin dokinya ci
kasa dakaren ya zube kasa kasa ta turnuke ta rufe masa fuska yana
laluben hanyar bi idanuwan da bai kara bude su ba ke nan, Umar ya
saka takobi ya dauke masa kai.
Mutum hudu sun kwanta dama saura shida Cikin fushi shida
suka zagaye umar nan take wajen ya karade da karar karafa idan wannan ya kaiwaUmar sara sai wannan ya kai masa suka da mashi,
su shidan haka yake ji da su kamar wani shaidan gurin ya yamutse
Umar da ya kara tunawa kowanelokaci za a kara turo wasu sai ya
kara zama cikin kankanin lokaci ya barsu cikin munanan raunika wadda basu isa su biyo shi ba saboda sara da suka da ya dinga yi
musu, yana da tabbacin sai dai rayawa ta Allah amma ba kowane zai iya rayuwa ba, ganin wannan nasara da ya samu yasa ya kara wa dokinsa kai mi ya bar wajen ya nufi Kauyensu domin zuwa ya
kwantar musu da hankali kafin sui so kowa ya san su waye
mangalawa addababbun mutane ne masu son kashemutane bagaira
ba dalili shan jini duk wani wadda baya bautar abin bautarsu shi ne
jahadinsu, zaman lafiya da su babbar asara ce a gare ku.
bature
98 Page
| Page
Bayan Jarumi Umar ya bar wannan wajen da suka fafata yaki
da shi da mangalawa ya bar wasu tuni sun jima da komawa ga Allah
ya bar wasu suna zaune cikin jini da magagin mutuwa. Kwatsam sai
ga tawagar shugaban dakarun watao Ulgut ya kara so. Ya sauka daga
kan dokinsa yana duban matattun mutane da rayayye wadan da suke
cikin mawuyaciyar rayuwa, Ulgut yayi ihu yayi gunji mai tsananin
amsa amo, wasu kalamai marasa kangado ya ci gaba da furtawa
kamar mai kokarin tayar da aljanu yana zazzare idanu yana muzurai,
yana gama wadannan surutai nasa sai ya zare wata karamar wuka a
jikinsa ya fara yankamagoraon raggowar dakarun da basu hallaka ba,
daya bayan daya yana fadin "Rahmata tabbata a gare ku".
Sai da ya gama wadannan surutai nasa sannan ya dubi
dakarunsa “Ku tabbata kun nemomin labarin wannan jarumi da ya kashemin mutum goma daga cikin mutum dari da shugaba ya turo ni da su wannan yanki, lallai ko su waye sai an gurfanarmin da su na hallakashi sannan na kone kauyensu da duk ahlinsa, lallai a bi sahunsa a gano min ina zai je daga ina yake dan wane kauye ne".
Ya na gama fadin haka wani mutum biyar daga cikinsu suka
fadi gabansa "Za mu cika umarninka ya kai shugaba Ulgut,da iznini wuta mafi girman daraja”.
Daga fadin haka kawai sai suka mike suka sauya kamanin suka haye dawakansu suna tafe suna bin sawayen dokin Umar. **
Lokacin da Sarki Muhammad da Shehul Islam suka ajiye dawakansu suka nufi inda majalisar dattawan nan suke in da suke
tattauna al'amuran rayuwa sai Sarki Muhammad da Shehul islam
suka tsaya daga nesa kadan kamar suna jiran waani har ya zamana wadanan mutane basu lura da su ba domin hirar da suke yi ta dauke
musu hankali daya daga cikinsu yana Magana suna saurarensa dattijo
ne mai kimanin shekaru hamsin yake baya ni "Daular Dut ta ruguje
ne dalilin auratayya da Sarki Shamnar yayi, bayan ya bijirewa yan
uwansa ya aure bayahudiya a hankali ta dinga jawo 'yan uwanta
cikin masarauta har ya zmana Yahudawa sun yi tasiri a cikin sarautar
DaularDut suka dinga aiwatar da komai babu wadda ake jin
bature
P
99
maganarsa face ya hudu batare da kowa ya san yahudawan bane,
kuma a karshe majiya ta zo matarsa da ya auro ce take samar da su a
cikin birnin ta karkashin kasa tare da sahalewar wasu mutane a cikin
daular.
To ina mai tabbatar maka cewa sarautar Bahara idan has
Sarki Muhammad bai tashi tsaye ba, abin da ya faru a wancan daular
tabbas za ta iya faruwa a nan, duba da yanayin da kasar mu ke ciki
yanzu,ka duba fa ka ga, yadda dansa ne yayi tattaki zuwa birnin
shamnur ya samar da adalci ga 'yan uwan juna ya kafa mulki ya yaki
adalci ya kori tsinanne Waziri Adnan, shi yana kwance a gida banda
Hakimi ABdallah ya ziyarce shi da bai san da wutar da ake tonawa
ba".
Sarki da Shehul Islam suka dubi juna cikin mamaki da
taʼajjibin yadda maganar ta yadu a kankanin lokaci.
Jin za su ci gaba da katobara Shehul Islam ya ce "Ranka ya
dade mu je gaba❞
Har sun fara tafiya wani daga cikinsu yake cewa "Ba ma
wannan ba, yanzu ka duba fa ka ga, yawancin Kauyukanmu sun
daina shigowa da samarinsu zuwa kasuwancin babban birni tunda
ana shan giya, ana caca, ana yin duk wani nau’in zunubi har gidan mata masu zaman kansu akwai a boye a cikin birnin mai tsarki kamar
Bahara da shekaru da dama bayin Allah suka samar masa da nutsuwa
lokaci guda mutum daya ya ruguza mulki shi yasa Mahaifiyata ta
taba cewa da ni "Isma'il Farsi shi ne ya dace da mulkin Bahara
amma aka batar da shi aka wulakanta shi a wata majiyar ma ana
tunani sun haukatar da shi."
Hankalin Sarki Muhammad farsi yayi mummunan tashi a lokacin da aka tuna masa da dan uwansa Isma'il batare da SHehul
Islam fara tafiya ba shi ya fara tattaki ya bar wajen. karkashin Idan mulki al'amura munana sun rincabe a
mulkinka ka kasa gano mafit, ka yi badda kama ka sulale ka shiga cikin al'umma batare da sanin ko kai waye ba, domin duk lokacin da mulkinka yake kan doron zalunci ba zaka yi nisan kiwo ba za ga
bature
100 Page
101 Page
fuskanci matsaolinka, idan kuma mulkinka na tafiya daidai akan
gadon baccinka ma zaka iya fahimtal
Wannan tunanin ya fado masa a rai a lokaci guda, lallai yayi sakaci mai girma.
Tsakiyar gari suka nufa suka ga cincirindon mutane sun
kewaye wani farin mutum mai cikar kamala da haiba, yana sanye da tufafi farare tas, da rawani a kansa baki, kayansa har zuwa idon
sahunsa na kafa, da kyakkyawan murmushi a kan fuskarsa yana
bayani dalla-dallah. Basu zame ko ina ba sai a wannan wajen.
"Tabbas bayan annabi Muhammadu, babu wani annabi da zai
kara bayyana, kur'ani ya tabbatar mana da wannan shi ne annabin
karshen kamar yadda kur'ani ya tabbatar mana da cewar Annabi
Adam shi ne annabin farko. To amma fa ba ana nufin shi kenan
bayin Allah sun kare ba, shi kenan Allah ba zai kara turo wani ba,
bayan manzo, akwai mutane halittu da suke zuwa duniya da
karamomi su ma duk daga Allah suke, sannan akwai na'u'ikan
mutane masu daraja da suke zuwar da sababbin abubuwa wadda
Allah yayi musu baiwar da Ihlama Allah yana sanar da su, ta fanno
ni da dama yadda za su gyara waal'umma ibada, bayan wafatin
ma'aiki an samu sahabai da suka gyara wasu al'amura na addini,
jama'a da dama suna karyata Shehun malami Albardi Ibn Ru'uyan
wadda yau shekaru dari uku da rasuwarsa wadda ya zo da tabbatuwar
auren wadda ya bi addinin kiristanci ba daidai yake da wadda ya
zauna babu addini ba, ya tabbatar da kirista zai shiga aljanna kamar
yadda musulmi wadanda suka yi zunubi za su shiga aljanna illa dole
sai an saka su a wuta an an yi musu hukuncin da ya dace da su”.
Sarki Da shehul Islamsuka kalli juna gami da cewa
"Auzubillahi minalshaidanir raj'em" har Sarki zai motsa sai Shehul
Islam ya ce "Dakata ranka ya dade, idan har mun dauki mataki anan
dukka damarmakin da ya dace za mu rasa su, muna bukatar sanin su
waye su, daga ina suke? Mene ne ilimin da suke son isarwa....
Wani nutsattsen matashi ya ce "Malaman addinin musulunci
da suka gabata sun tabbatar mana da cewar duk wadda ya hada wani
da Allah kafiri ne, kuma kafiri ba zai taba shiga aljanna ba?"
bature
102 | Page
Nan take Shehul Islam da Sarki suka kara nutsuwa domin jin
amsar da wannan mutumin zai bayar sai ya ce "Ilimi kogi ne dan
samari, ni ma a nawa bangaren ina da ja akan maganar malam
Albardi to amma da nayi zurfin ilimi nayi bincike sai na gano cewar
akwai litattafai na addinin Islama da aka kifar a ruwa aka salwantas
menene dalili kifarda su, mene ne dalilin da yasa aka salwantar da su,
dalilili yana kan litattafan malam albardi wadanda nan gaba kadan za
su ke yawo a tsakaninku, da kanku za ku cimma wannan hujja”. Mutane suka fara maganganu a junansu har Malam yayi
musu sallama haye Rakuminsa gami da tafiya yana mai yi musu
murmushi cikin salama
Sarki ya dubi Shehul Islam yace "Ya kake ganin za a yi da
wannan kafirin?"
Shehul Islam yace "Idan muka daure shi ko kama shi wani
zai zo ya fara wa'azin cewar saboda zai fadi gaskiya an boye shi ko an kashe shi, abin da ya za mu yi yanzu mu baza idanunmu a duk
inda za a yi wa'azi mu kirawo wadannan mutane domin zama dasu, a
bainan nasi mu kunyata su mu karyata su da ilimi ba ta kaifin takobi
ba, muna saka takobi a cikin wannan lamarin komaiya lalace".
Koda Sarki Muhammad Farsi ya ji wannan batu sai ya jinjina
kai ya kuma yi amanna da shehil Islam daga haka sukaci gaba dazagaye gari har zuwa daf da magriba adaidai kofar wani gida suka tsaya suna son su samu ruwan da za su yi alwala su yi sallah domin
kada lokaci ya kufce musu.
Suna nan tsaye suna tunanin abin da za su yi gida ne gua daya tal a wajen daga haka sai filaye Shehul Islam ganin hayaki yana
tasowa daga cikin gidan ya ce "Da alama akwai mutane a cikin gidan nan don haka bari mu nemi su taimaka mana da ruwa domin mu yi
alwala. Kafin ya ji ta cewar Sarki ya kwala sallama aka amsa masa
dakyar daga jin murya tsoho ne ko tsohuwa.
Suna nan tsaye suna jiran a leko sai ga tsohuwa tana takowa
da sanda dakyar ta kara so gare su "Ku ne kuke sallama?"
Suka amsa "Sannunki"
Ta amsa "Yawwa, wa kuke nema?”
bature
103 | Page
"Shehul Islam ya ce "Muna neman ruwa ne domin sallah ta
riskemu a halin tafiya”.
"Sallah za ku yi?"
Shehul islam ya amsa da cewar "Sallah za mu yi, ko akwai
masallaci nan kusa?"
"A'a babu masallaci, yanzu masu arziki sun rabu da gina
masallaci, masarautu ma sun rabu da ginin masallaci sai gidajen
rawa, gidajen bakin haure ma'abota littafi, daga nan tafiyar da za ku
yi ku riski masallaci har sai kun danganta da cikin gari sosai".
Sarki Muhammad Farsi ya ji kamar ta soka masa kibiya a
cikin kokon zuciya, yaushe rabonsa da gina masallaci, a kullum da
kodayaushe gini ake yin a bakikamaryadda ta fada".
Su ka hada ido da SHehul Islam ya tuna lokacin da Shehul
Islam ya ziyarce shi Idan aka ci gaba a haka ya Sarkin duniya za mu
tsinci kanmu a koma baya sosai, mun bar gina Abubuwan ci gaban
musulunci mun zauna muna gina rayuwar baki, ban ce baki kada a
basu masauki ba, amma hakan kada ya dakatar da mu aikata abin da
zai bawa addininmu ci gaban, makarantu don koyar da al'umma,
masallatai don samun wadatar bautar Allah"
Dukkaninsu sai da suka tuna wannan maganar a tare suka
sauke ajiyar zuciya Sarki Muhammad Farsi ya dubi Shehul Islam a
lokacin matar ta koma domin daukar musu ruwan alwala "Matukar
Daular Musulunci ta fadi ni ne alhakin komai, domin ire irenku kun
yi min bayanin da ya dace nayi dogon tunani da nazari amma hakan
ya gagare ni, tabbas na cancanci tuhuma, na kuma amshe laifukana".
Shehul islam bai ce da shi ko ta tafasa ba saboda a lokacin
tsohuwar nan ta zomusu da ruwa suka yi alwala suka gabatar da
sallah sannan suka ci gaba da tafiya **
Tun lokacin da Waziri Ja'afarya ji sakon da Sarauniya ta aiko masa da shi hankalinsa yayi mummunan tashi ko baccin kirki bai iya
yi ba, haka washe gari ya kago rana ta raba domin ya samu isa wajen
Sarauniya domin su tattauna abin da yake akwai aikuwa lokaci na isa
bai tsaya bata wani dogon lokaci ba ya haye dokinsa sai gidan Sarki
bature
104 | Page
Muhammad Farsi. Yana isa kamar yadda yake cewar ya kagauta
lokacin nan yayi ita ma sarauniya Siyamata saka hadimanta mafi
kusanci da ita cewar a duk lokacin da waziri ya iso su sanar mata
domin ta gaggauta fitowa dakin gani, aikuwa yana bargar ajiyar
dawakai sai ga wani cikin masu yiwa Sarauniya hidima daga wajer
gidan Sarki ya zo ga Waziri ya sanar da shi cewar yayi maza ya isa
dakin gani tana saurarensa a can.
J
Batare da bata lokaci ba ya isa wannan guri. Babu wani
dogon bayani ko gaisuwa ta dubi Waziri Ja'afar ta ce "Muna cikin
babbar matsala da musifa abu biyu ya faru a lokaci guda wadanda
dukkaninsa asara ce mu a wajenmu, Yarima Yazid yayi mummunan
kuskure inda ya je ya fafata da Benjamin harma sun yiwa juna rauni,
labara ya zo mana cewar Yarima Abbas ya isa birnin Shamnum ya
kuma gyara dukkanin matsalolin da muka kunna a cikin birnin abin
tashin hankali ace Sarki ya gano muna da hannu wajen zuga Waziri
Ja'afarda mahaifiyar yarima Hilal, idan har Sarki Muhammad ya ji
wannan a lokacin da ya nemo lafiyarsa kashinmu ni da kai ya bushe
sannan burinmu a kan Yarima Yazid bazai taba yiwuwa ba, abu na
biyu kuma yanzu haka Sarki ya fara zargin akwai wani kulli da aka
yi masa amfani da shi dan dauke hankali a kan mulkinsa da yake yi
kasalada gajiyawa da rashin maida hankali da aka yiwa
kwakwalwarsa aiki, ya fara tunanin neman magani don ya ce dani zai
nemi magani har ma a jiyan ya fita da yammaci na sa abin bayansa
bai tsaya ko ina ba sai gidan Shuhul Islam, bayan nan kuma suka
zaga gari suka dawo gida, yanzu ya kai Waziri Ja'afar mene ne abin
da kake ganin za mu yi domin magancematsalolin nan da za su saka
mu asarar duk tanadinmu?"
Waziri Ja'afar yayi a jiyar zuciya gami da cewa “Ranki ya
dade akwai babbar barazana da matsaloli da sai mun yi da gaske za
mu iya kawo karshensu, abu na farko shi ne rashin kwarewa ne muraran
yarima ya aikata wajen fito na fito da Benjamin, abu na biyu kuma ba mu
isa mu hana Sarki neman magani ba, idan har muka ci gaba da hanawa ko
Magana da likitocinsa ba kowane likita bane zai ji shakka ko tsoronmu
kamar yadda na baya suka yi, ba ma musan a ina zai samu likitan ba bare
mu yi tunanin wasu dabarun tsoratarwa ko zuba dukiya don hana aikin na
bature
105 | Page
hakika, a shawarce mu ja da baya, matukar ba so muke mu kwana kiyama
ba, mu taya Sarki neman magani idan ya so daga baya sai mu sake sabon
shiri".
Tun da ya fara Magana zufa take keto mata domin ta san dama zai
iya biyowa ta wannan bangaren domin shi kansa ta siye shi ne ta dalilin zai
ci gaba da zamaa matsayinsa na waziri matukar in Sarki ya mutu danta ya
zama Sarki, tana amfani da shi ne saboda soyayyarsa da mulki da kuma
kudi, da mugun kishin da yake da shi ga duk wadda yaga ya fishi kusanci
da Sarki, sannan ta sa Sarki ya yafe masa kurakure masu yawa.
"Kana ganin idan Sarki ya dawo hayyacinsa, zai ci gaba da zama
da kai amatsayin wazirinsa bayan akwai korafe korafe akanka da dama,, ka
da ka manta badakalar kasuwa, masarautar Shamnumda hadakar da kake yi
da kafurai".
Ya dube ta cike da mamaki, ya san ta san yana da alaka da
shamnum da wasu korafe korafe amma bai san ta san badakalar da yake yi
a kasuwa ba, da kuma hadaka da yake da su da kafurai. Nan take
hankalinsa ya tashi ya bude baki zai musa mata "Waziri Ja'afar babu wani
taku da kake yi a cikin masarautar Bahara da ban san da it aba, na zabeka
ne saboda na san za cika min burina na ganin mun gaji sarautar bahara
daula ta dawo hannun dana, idan har ka ce zaka juyamin baya kwana biyu
uku kacal yayi yawa kanka zai rabu da gangarjikinka domin kalma daya tak
na sanar da sarki na kafa shaidun na gaskiya kashinka zai bushe, ka ci gaba
da amsarumarni daga wajena mu gudu tare mu tsira tare”.
Ya saka babbar rigarsa ya share gumin da yake tsattsafowa daga
jikinsa hankalinsa ya kara ta shi y ace "Ranki ya dade wane ni na juya miki
baya, baki fahimce ni ba ne...."
"Na fahimceka, tunda za ka ci gaba da zama da Sarki a matsayin
waziri baka da damuwa, za ka koma kalallaba Yarima Abbas ka dinga yi
masa biyayya domin ganin cewar ya taka matsayin zama Sarki daga nan
shikenan ka tafi kabarmu duk ukubar da ta zo kan mu za ta afka, idan har
ka yi ganganci to la shakka kwana uku kacal mutuwa za ta yi maka
sallama".
Ta na fadin hakan ta mike daga inda take bata kara saurarensa ba ta
wuce cikin gida, jikinsa a sanyaye haka ya mike lallai mata shaidanu ne na
gasken-gaske zikirin shaidancin matan nan da su ya isa fada kwata-kwata
jikinsa babu kwari.
bature
Tun a daren jiya da Jarumi Umar ya dawo daga fafatawa da
Mangalawa ya zamana cewar cikin kauyen Nur suke cikin shirin domin
suna da tabbacin matukar sun fahimci daya ne daga cikin kauyan ya yake.
su,to babu shakka za su biyo sahu, don haka tun daga farkon shigowa garin
aka kara masu tsaro da masu kai rahoton farmaki, saboda kasancewar cikin
shiri.
Lokacin da Umar suka kadaita da mahaifinsa sai ya ce "Ya
Abbana, ka yi sani cewar zan iya ja da bataliyar Mangalawa guda ni da
abokaina, akwai yara kanana da mata a cikin birnin nan, saboda haka zama
na a tare da ku akwai babban