Sharjas, mutumci da karamci kuma ga
iyalansa".
Koda sarauniya Hauletu ta ji wannan batu daga bakin Hindu
sai ta yi shiru tana nazari a cikin ranta daga bisani ta ce "Akwai
babban matsala a cikin gidan nan yake aminiyar sirrina, ki yi sani
cewa dana na cikin barazana da rayuwarsa akowane lokaci har maina
jin tsoron, tsoro yana kamani yana hanani sukuni a duk lokacin da na
kasance cikin wannan yanayi nakan dage karanta (LAHAULA
WALAKUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYUL AZIM) domin
danganta komai wajen ubangijin talikai, a kwana kusa zuciyata tana
gaya min, dole na nemi taimako daga wasu manyan mutane da Sarki
yake basu daraja, domin su kulamin da yaro na".
Ta yi shiru a daidai wannan lokaci daga bisani ta dora
"Babana yana cewa a duk halin da ka kasance ka da ka nemi
taimakon kowa ka nemi taimakon Allah, amma kullum zuciya tana
gaya min in nemi wani na bashi amanar dana Yarima Abbas da a
yanzu ya kai kimanin shekaru a shirin da haihuwa tabbas zai zamo
abokin gogaggayar Yarima Yazid na ganin yardarsu a wajen manyan
kasa, a wannan lokacin, saboda makirci kina ganin yadda ba a bar
Yarima Abbas ya saba da koda shugaban dakarun gidan nan ba, bare
har ga ya saba ga Shugaban Dakarun kasa, bai taba kai ziyara
Sansanin Dakaru ba, bare har a fara tunanin gwada shi a matsayin
magajin Sarki, kamar yadda kika sani ni ma na sani, babu yadda za a
yi a rashin adalcin da kirki irin na Abokan zamana Yarima Yazid ya
zama sarki su kyale min dana a raye, dole sai sun kirkiri hanyar da za
bature
13 Page
Bahara, akwai dakaru a ko ina, sai dai duk tsaron bai hana birnin ya
zama mahadar Kafurai wajen shirya tuggun yadda za su kawo
karshen brnin da musulmai.
A cikin kasuwa mafi daraja a kasar Bahara wacce ake mata
lakabi SUKUL SA'A wasu gungun Kirista, shugabansu JARFIS na
tafe yana duba kayan da aka kasa a kasuwa, yana duba wa wadanda
suka yi masa yana siya tsawon lokaci yana cikin wannan lamari da
dakaru a bayansa har suka isa wani babban shagon wani tsohon da
ake kira Kirzalu, Kirzalu asalin dan kasar Bahara ne wadda jinin
kasar ne shi wadda kuma ya rudu da dukiya saboda yana zaune ne
domin ya zama idon Kafurai da duk wani abu dake faruwa, kuma a
nan ne suke kitsa shirinsu na zalunci.
Babban shago ne da shi. Dai-dai inda Jarfis ya iso sai ya fara
kamar duba kaya da haka ya shige cikin shagon dakarunsa suka
tsaitsaya a bakin shagon ko da shigarsa sai suka nufi wani guri da ba
zaka taɓa tsammanin kofa bace amma Kirzalu yana dafa ta sai ya
murza wani mabudi take kofar ta bude kawai sai suka shege ciki
tare, koda shigar su ciki sai ga su a cikin wani kayataccen ɗaki mai
dauke da kujerun zama da matasai a ɗaya cikin matasai wani
hamshakin mutum ne zaune a gabansa akwai kayan marmari yana
zaune yana dauka daya bayan daya yana tauna inibi, batare da ya
daga kai ya kalli wadda yake shigowa ba. Har Jarfis ya nemi wajen
zama zai zauna sai wannan hamshakin mutumin ya daka masa tsawa
gami da dagowa ya dube shi "Waye kai da har zaka same ni a zaune
ba tare da na yi maka izini ba ka nemi wajen zama, maza ta shi ko
takobi na ta raba kanka da gangar jikinka"
Jarfis ransa ya baci kamar yaki bin umarninsa amma dole tasa
ya tsaya saboda a kowane lokaci ana koyar da su da su bi musulmi
domin su samo lagon da za su kama su da sasari.'
bature
Data
28 Page
su kashe shi shi ne ya sa a wannan lokacin ba ni da wani sukuni tun
da Sarki ya fara ciwo yau gobe lafiya gabana ki faduwa".
Hindu ta yi shiru cikin dan gajeren lokaci har sai da ta ji uwar
dakin nata ta share hawayen ta ja shessheka sannan ta ce "Neman
taimakon Hakimin Annur daidai ne a gare ki, domin shi mutum ne
adali kuma mai matukar son gaskiya, idan Allah zai baka kariya ba
da kansa zai zo ya baka kariya ba, amma shi ne zai zama sanadin
haka, kin fi ni sani duk wani ilimi a wajen kin a samo shi, tsantsaini
da tsoron fadawa halaka yake sawa kike wannan tunanin ai saka miki
damuwar da kuma tunanin nemo wadda zai tsayawa danki ki dauka
ubangiji ne yake haska miki, a da can ban da karfin gwiwa a game da
Yarima Abbas amma wannan maganar take ta sa na fara jin karfin
gwiwa, tabbas mu yi hanzari ka da mu yi kasa a gwiwa”.
"Maganar ki gaskiya ce, wannan haka yake, to amma yake
Hindu ya kike gani za mu yi wajen ganawa da Hakimi Abdullahi bin
SHarjasllah, ki sani cewar matukar sun san wani shiri to za su gyara
na su shirin, abin da nake tunani wani amintacce za ki nemo min
wadda zai kai masa ziyara wadda shi da kansa Hakimi zai nemi
yarima ni kuma zan gayawa yarima sakon da zai je masa da shi”.
**
Lokacin da Jarumi Umar ya iso babban turakar mahaifinsa, a
daidai lokacin Hakimi na nazari game da bakuwar Suhaila bin
Ababakari da kuma tunanin sakon da Sarauniya Hauletu ta zo masa
da shi na son haduwa da Yarima Abbas.
A wannan lokacin ya yanke kai ziyara babban birnin domin
ganawa ta musamman da Sarki a game da sabuwar masarautar da ake
rigima a kai, sannan kuma zai yi amfani da wannan dama ya gana
Yarima Abbas.
da
29 | Page
Ya dubi 'ya'yansa biyu da suke durkushea gabansa ya fara da
cewa "Ya kai Ahmad ina son kasani za mu yi tafiya a safiyar yau
zuwa birnin Bahara, kai za ka yi min rakiya zuwa can".
Ya dubi Yarima Jarumi Umar da yake a tsorace daga furucin
Hakimi, domin idan akwai abin da yaki jini ya ji ko gani mahaifinaa
y acc zai yi tafiya ba tare da shi ba. "Ya mai martaba ka yi sani cewa
zuciyata tana shiga rudani hankalina baya kwanciya a duk lokacin da
na ji cewa za ka fita daga cikin wannan kauye, Ya mahaifina ka sani
cewar makiyan da suke son ganin bayanka a kasar nan sun fi
makiyan waje yawa, idan har za ka kai...."
Hakimi ya dakatar da shi da cewa "Ka kwantar da hankalinka
Jarumi Umar, ka sani cewa wani muhimmin aiki ne ya taso wadda
kuma yana bukatar na motsa, kai ma kumana tura ka wani aiki na
daban aikin suna bukatar a yi su a tare domin dole ne na je na gana
da Sarki Muhammad farsi dangane da matsalar Salman da Hilal, dole
kai ne zaka tafi izuwa kasar Shamnun domin ka gano mana halin da
ake ciki"
Ran Ahmad ya baci ya dubi Jarumi Umar ya cc "Akowane
lokaci kana jin cewar kai kadai ne kariya ga ahalin gidan nan, idan
har ba zan iya kare mahaifina ba, na tabbata ba zai yanke shawarar
tafiya da ni ba".
Jarumi Umar ya girgiza kai yace "Ba haka nake nufi ba dan
uwana, babu mai kare wa face ubangijin musulunci, abin da nake
tsoro da fargaba shi ne buguwar zuciya yayin da na tuno kuna halin
tunkarar birnin da yake cushe da makiyanmu, masu son ganin bayan
mahaifinmu da ahlinsa".
Hakimi yayi murmushi ya dubi Ahmad y ace "Iya abin da
dan uwanka ya fada shi ne kadai abin da yake gudu, amma ba ya
nufin cewar kai ba zaka iya bani kariya ba."
bature
30 Page
Sannan ya dubi Yarima Jarumi Umar ya ce "Aikin dake
gabanka ya fi wanda ke gaban mu hadari, dole sai kun yi kaffa kaffa
domin na san za a zuba dakarun da zasu hana ku ganawa da Sarki
Hilal, domin ba bukatarsu a yi sasanci ba bukatarsu ayi tashin
hankali a tsakanin kasashen musulmai, amma a zarar kayi tozali da
Sarki Hilal ka yi masa albishir da cewa na tafi zuwa babban Birni
don tabbatar da cewar shin Sarki ya san da abin da yake faruwa a
kasar Shamnun ko kuma bai sani ba, wannan kalamin shi ne kadai
zai sa Sarki Hilalya barku ku dawo gida lafiya, kuma idan yana da
hankali shi zai sa a barwa duniyar musulunci zabar Sarki mafi daraja
a tsakaninsu shi da dan uwansa Salman, amma matukar basu gan ku
kun gana ba, to ku yi kokari tsirar da rayuwarku domin sun shirya ayi
duk abin da za a yi, ka ga ke nan za su fara da kai”.
Jarumi Jarumi Umar ya jinjina kai ya kuma fuskanci lallai
akwai babban aiki a gabansu,don haka ya jinjina kai ya ce “Insha
Allahu komai zai tafi kamar yadda ka tsara Baba".
Hakimiya jinjina kai gami da cewa "Masha Allahu, yanzu ka
je ka yi shiri tun da har yanzu muna cikin duku-dukun safiya, don
haka idan kun tafi yanzu kafin la'asar za ku isa birnin Shamnun,
kuma lokacin mun fara neman hanyar dawowa daga Birni, duk ku
tashi ku je ku yi shiri".
Ahmad da Jarumi Umar suka fito daga babbar turakar
mahaifinsu cikin fushi da Ahmad yake ciki da dan uwansa domin shi
sam gani yake kanin nasa ya raina masa tunani jarumtakarsa gani
yake shi ke sama da shi”.
9
Abin da Jarumi Jarumi Umar ya lura da shi ya dubi dan uwan
nasa ya ce "Amanar mahaifina da kuma kai kanka tana hannunka, ka
da ka yi wasarere da rayuwarku duniya ta yi mana kunci"
Kalamansa suka sanyayyar da gwiwar Ahmad a dai-dai
lokacin da Kubrat da su GImbiya Suhaila bin Ababakari suka
bature
B
31 Page
tunkaro in da suke Jarumi Jarumi Umar ya ci gaba da cewa "Ya kake
tsammanin idan wani abu ya same Baba, da kai kana tunanin
tsohuwar nan tamu mai tsananin kaunarmu zata iya dauka, a
kodayaushe ka tuna da ita ka kuma tuna da al'ummar da suka jingina
da mahaifinmu"
Jarumi Ahmad ya ji dadi sosai har ya jawo Jarumi Umar ya
rungume shi suna masu murmushi so da kauna, Ahmad y ace "Ka ji
abin da Baba ya ce tafiyarka tafi ta mu hadari da taka tsantsan, ya
kamata a ce ka kula kuma ka dawo cikin koshin lafiya domin
rashinka kamar ragewa masarautar annur karsashi ne, rayuwar
mutanen Annur sun dogara da Allah da kuma kai, kai suke yiwa
kallon mahaifinmu, don haka ka kula dau uwana".
Dukkaninsu suna murmushi na jin dadi da kuma wata
karyewar zuciya har ta sa suka zubar da kwalla,dai dai lokacin
Kubrat ta karaso da ita da Suhaila bin Ababakari. Kowa yana saurin
goge kwallar don kar mahaifiyarsu ta fuskanci kuka sukeyi, kallo
daya tayi musu ta fahimci damuwa a tattare da su, da yake ta riga da
ta san halin da ake ciki tun a daren jiya ta yi nata kukan, sai ta share
ta kasance don karfafa musu zuciya.
Jarumi Umar ya dubi Gimbiya Suhaila bin Ababakarit ta
dukar da kai "Barka da safiya”.
Ya yi mata murmushi cikin kallon cikin idonta ya ce
"Dafatan kin tashi lafiya”.
"Ku yi kokari ku shirya domin ku isa a kan lokaci,kamar
yadda mai martaba ya fada, ina muku fatan alkairi yarana Allah na
tare da ku❞
Duk su biyun suka rungume ta "Insha Allahu"
Su ka furta tsoron da take ji shi ne ta fara kuka yasa ta sake su
ta dubi Suhaila bin Ababakari “Zo mu je wajen maimartaba yana jiran ki”.
bature
32 Page
Gimbiya Suhaila bin Ababakari cikin jin nauyi ta ce "Idan
babu damuwa zan gana da Jarumi Jarumi Umar na dakika daya kacal
Jarumi Jarumi Umar ya kalle ta ya kalli mahaifiyarsa Kubrat
ya kuma dubi dan uwansa, sannan ya dawo da kansa gare ta, yayi
shiru gami da cewa "Mu je"
Ya yi gaba ita ma ta dubi Kubrat gami da murmushi sannan ta
bi bayansa a nutse sai da ya bada tazara mai yawa sannan ya tsaya,
ya tsaya dai-dai inda abokansa suke zaune don haka suka tsira masa
ido sanin halinsu yasa ya fara kame kame ya dube ta ya ce "Ko zaki
bani dan lokaci zan Jarumi Umarci abokai na don su je su yi shiri
domin tafiya Shamnun”
Ba tare da ta ce komai ba ta jinjina kai alamar ta fahimci
uzurinsa".
Ta tsaya ta zuba wa bayansa idanu yana nufi wajensu kafin
yana isa suka amsa masa sallamar da yayi musu cikin zolaya yakalle
su daya bayan daya ganin idanuwansu suna kan Gimbiya Suhaila bin
Ababakari sai ya juya ya dube ta itama idanuwanta a kansu yake tana
mai mamakin kallon da suke yi mata. Ya dawo da dubansa gare su y
ace “Wai me ye haka kukeyi, komai wane abu yana da gurbi kar ko
dora giwa a kan dantsako".
Dawan ne mutum mafi maida hankali a cikinsu don haka shi
ko dariya ma bai fiya yi ba, babban burin Dawan ya ga ana batun
tafiya don aikin Allah don haka shi ya fara dakatar da su da cewa
"Me ke tafe da kai?"
Nan ne ya daina harararsu ya dubi Dawan y ace "Mu na da
babban aiki a gabanmu, ku je ku shirya yanzu za mu tashi zuwa
Shamnun don fara ni ma zan gama da gimbiya ne na tafi nawa shirin
watakilatana da sako ne yasa take son mu yi Magana"
Mu'az ya ce "Kowane lokaci a shirye muke ka je ka gama
muna jiranka a wajen dawakai"
bature
bature
B
33 | Page
Kubait kuma ya ce "A gaida gimbya"
Bai saurare shi ba ya juya ya koma ga Gimbiya Suhaila bin
Ababakari ya tsaya tana kallonsa sai da ya dan tsaya ya ga ta ki
Magana sannan y ace "Ina sauraren ki❞
Ta gyara murya ta ce "Dama na so na sanar da kai ne inda
yayana ya sanar da ni yana boye ko zaka taimaka ka ceto shi daga
zalunci dan uwansa?”
Ta fada cikin rudu da sunkui da kai kasa ya dan yi shiru ya
dago ya kalle ta "Ki kwantar da hankalinki Gimbiya, babu wani abu
da zai sami dan uwanki Salma, kuma da yaddar Allah Salman zai
zama Sarki in dai shi ne zababben mahaifinku, wannan alkawarin
Allah ne, domin na tabbata matukar mahaifina ya tattauna da Sarki
Muhammad farsi, ni kuma isa birnin ku, na kuma kai sako na, babu
wani taurin zuciya da zai saka Dan uwanki ya yiwa Sarki gardama
domin ya san ba zai taba yin nasara ba, don haka ki kwantar da
hankalin ki Gimbiya".
Ta yi wani murmushi jin dadi ta ce "Insha Allah, kuma na
gode bisa taimakon da ka yi min a jiya na kara gode maka bisa
wannan taimakon da z aka kara yi min, ina maka fatan dawowa cikin
koshin lafiya".
Shi ma ya dan yi guntun murmushi gami da cewa "Amin, y
ace za mu hau hanya Allah sa mu dawo da mu same ku lafiya”.
Daga gama wannan maganar sai ya juya ya bi hanyar
bangaren Maza na gida ya shiga turakarsa duk wani abin bukatarsa
ya dauko ya fito, bai tsaya ko in aba sai wajen abokansa, da sun yi
shiri tafiya.
A dai-dai lokacin da suka haye dawakai sai suka rufarwa
hanya babu ji babu gani. A daidai wannan Lokacin Shamsu bin
Aujarbn Abdallahi ya na hangensa daga can saman gidansa koda ya
bature
(.
>
34 Page
ga sun fita sai yayi sauri ya sakko ya nufi cikin gidan dan sanin abin
da yake faruwa.
A lokacin da Sarki Abdullahi bin Sharjas ya gama kintsawa
sun fito tare da matarsa da kuma Gimbiya Suhaila bin Ababakari da
Jarumi Ahmad. A hankali ya matsa gare shi jiki a sanyaye. “Dan
uwana naga Da na Jarumi Umar tare da abokan gumurzunsa sun
sukwani dawakai, kai kuma ka fito cikin shiri shin akwai wani abu
ne da ba mu sani ba”.
Hakimi yayi murmushi ya ce "Kwantar da hankalinka yanzu
nake shiri na shigo Bangarenka na zayyana maka abin da ke faruwa,
sai kuma g aka, Amanar mutane na iyalina, da gari na na hannunka,
domin wata tafiya ce wacce ba a kimtsa mata ba ta same mu, dole
daga yanzu za mu wuce Bahara, zan gana da Sarki akan matsalar
gimbiya Suhaila bin Ababakari, sannan Jarumi Umar da ka gani ya
fita shi ma ya tafi Shamnun ne domin magance matsalar da ikon
Allah zuwa yammaci za mu dawo"
Koda Shamsu bin Aujarya ji wannan batu sai yayi shiru da ya
fuskanci shirun nasa zai kawo wani tunani daga dan uwansa sai ya ce
"To Allah ya dawo da ku lafiya, kuma za mu ci gaba da gudanar da
tafiyar komai har Allah ya dawo da kai lafiya".
ya
Daga nan ya bi su da kallo suka dunguma kusan dakaru
ashirin ne ke musu rakiya. Bai gushe ba yana kallonsu har sai da
suka bace masa da gani sannan yayi sauri ya nufi gida, ya sa a kira
wo masa babban yaron sa Alban koda zuwa Alban sai dube shi ya
ce "Maza ka je ka tashi ka je ka isar da dan aikin Waziri cewar lallai
dan uwana ya yi abin da yake zargi wato ya nufi Bahara, shi kuma
Jarumi Umar ya nufi kasar SHamnun, ka yi maza ka da ka bata
lokaci".
Alban ya fita da hanzarinsa don kai sakon maigidansa abin
sirrinsa gatan sa kuma.
bature
B
35 Page
Shamsudden wani mashahurin tsoho ne wadda yake adawa da
mulkin dan uwansa, bai yi amana da Abdullahi bin Sharjas ba domin
gani yake shi ne mafi cancanta da sarautar Annur, don haka kullum
cikin bakin ciki da zagon kasa yake yiwa Mulkin Abdullahi bin
Sharjas tsawon shekaru bai taba samun nasara ba, Abdullahi bin
Sharjas ya sha kama shi da hada baki da wasu maha'inta kasa amma
yana masa afuwa, saboda son a zauna lafiya domin abin da Abdullahi
bin Sharjas yake fadi kullum shi ne dukkaninsu sun zama dattijai
lokacinsu kalilan ne a duniya, baya son dan uwansa ya mutu a
matsayin mai ha’intar kasa, kullum yana gyara masa kurakurensa,
amma ya gaza fahimta, don haka duk lokacin da ake so a cimma
wata manufa a cikin kauyen Annur to da shi ake hada baki, don a
jiya da waziri ya bar kauyen sai ya sa dan aike zuwa gareshi ya sanar
da shi cewar yana bukatar jin duk wani motsi da ya ga dan uwansa
yayi.
Tun da Waziri Ja'afar ya bar Kauyen Annur bai tsaya ko ina
ba sai gidansa a babban birni saboda ya san cewar za a samu wannan
babbar matsalar, don haka washe gari da sassafe ya zo fada don ya yi
tsarin da zai warware kansa daga cikin matsalar birnin Shamnun
kafin a samu wata matsala
Ana zaune a fada kowa ya iso isowa Sarki Muhammad farsi
kawai ake yi. Wasu da dama a fadar sukan tattauna batutuwan da
suka zo wa da Sarki shi na yadda za su sanar da shi, wasu kuma na
kokarin gyara Kujerar Sarki wasu na gyatta tsayuwarsu, malamai
wasu daga cikin Hakimai da aka gayyata, Sarkin Kasuwa, Sarkin
gida, da na fada Shugaban Dakarun waje da na Gida duk sun hallara
suna jiran Sarki.
Kwatsam sai ga Busar Sarewa alamar Sarki ya taho,
‘ya'yansa biyu ne suka fara shigowa cikin takama da nuna izzar
mulki wato Yazid da Abbas. A nan take kowa ya mike a fadar aka
bature
ミ
36 Page
fara dukar da kai kasa ana gaida su. Sai da suka nemi wajen zama
sannan ne kowa ya zauna kuma waje yayi shiru. Jim kadai sai ga
Sarki nan shi ma nan aka kara tashi yana tafe wasu dakaru biyu suna
biye da shi kansa a kasa yake har ya isa inda kujerar mulki take
wadan an dakaru suka koma hagu da dama suka tsaya a bayan kujera
sai ya dago kai ya dubi duk inda mutane suke sannan ya daga hannu
ya fara addu'a domin fara zaman majalisa, a ka yi salati ga manzon
rahma, aka yi kirari ga ubangijin talikai aka nemi taimakonsa da goyan bayansa a game da daukaka Kalmarsa. Sannan aka shafa da
fatiha. A sannan ne ya nemi waje ya zauna.
To fa babu mai zama a wannan wajen har a tashi taro a haka
kowa zai tsaya.
Mai rubutun kundin mulki da kuma gabatar da abin da za a
fara jira yake Sarki ya daga masa hannu ya fara domin dole shi ne
farko adaidai lokacin Sarki ya daga hannunsa sai wannan mutumin
da ake cewa da shi Zarkifilu ya fito gaban Sarki da katon kundinsa a
hannu ya fara da cewa
"Allah ya ja zamani Sarki ya karawa Sarki lafiya kamar
kullum da kodayaushe, batu daga Sarki Jarumun Jakub cewa a karo
na biyu yana bukatar birnin nasa wadda aka kwace masa Birnin
Hilayan, sanan yana bukatar diya ta rayuwakan da aka salwantar a
birnin yayin gwabza yaki, ya kara tabbatarwa ba zai kara turo sako
na hudu ba, kaifin takobi ne zai ci gaba da Magana.
A bagaren Kauyen Dire Hakimi Suleman yayi batu a game da
bullowar Hangalawa tsille tsille suna zuwa babbar kasuwar Kudu
suna tare mutane suna kuma zuwa suna amsar haraji, lallai yana mai
kira da babbar masarauta a dauki lamarin da gaske domin sun fara
dawowa.
A ziyarar da Waziri ya kai kasuwa jiya, ya ci karo da sabbin
mutane wadda ya sa an yi bincike a kansu ya gano cewar lallai wasu
bature
37 Page
mutane ne da suke son haddasa husuma domin sun dauko 'yar
marigayi Sarki Ababakari zuwa wannan birnin amma cikin ikon
Allah Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya kwace ta daga hannunsu.
yau".
Wannan su ne bakin labarin da za mu fito da su a zauren mu
Fada ta kara yin shiru bayan da Zirkifilu ya kammala kawo
batutuwa kamar kullum. Sarki ya gyara zamansa kai tsaye
idanuwansa ya dago ya dubi kafatannin ‘yan zaman fada kafın ya
dora ya ce "Sako zuwa ga Kafiri Jarman Jakub a gaya masa cewar ba
mu da lokacin mai kori, ba kuma da wata Magana da ta rage a
tsakanin mu, idan har ya tabbatar Takobin ce kadai za ta yi Magana,
to na mu kodayaushe cikin washi suke.
Game da Hakimi Suleman lallai a tashi dakaru na gaske a je
Kauyen a yi bincike na gaske.
Kafin Sarki ya kara Magana ta gaba, sai ga Shugaban Fada ya
shigo tun daga nesa ya duka yayi gaisuwa "Akwai sako na
musamman ya Sarki mai daraja”.
Tun da Waziri ya ga shigowar Sarkin Fada sai hankalinsa ya
ta shi, ya shiga zare idanu amma tun da dai yay i aikin hankali tun a
jiya ya shigar da batun kafurai a kasuwa karyar da zai yi za a iya
gasgata ta, maganar Salman ce wajen binciko lamari wannan kuma
ya san shi zai jagoranci zuwa birnin kuma ko ma waye a cikin fadar
to maganarsa yake ji.
Har Sarki Fada ya je kusa da Sarki yayi masa Magana da ba
kowa ne ya ji ba. Ya bawa Sarkin Fada Jarumi Umarni ya fice "Batu
a kan Yar Sarki Ababakari ga Hakimi Abdullahi bin Sharjas nan ya
iso domin yi mana cikakken bayani".
Kowa da ke wajen sai da gabansa ya fadi domin koda wasa
aka furta sunan Abdullahi bin Sharjas sai mutane sun shiga
hankalinsu sun fara tunanin wata badakalar ta su za ta iya ta shi,
bature
:
| Page
saboda tsoronsa da kuma, Sarki na rufe baki Abdullahi bin Sharjas ya
bayyana cikin sallama bangaren ya tsaya cak yana kallon kowa cikin
fara'a.
"Bangaren Masarauta, Malamai, Hakimai 'yan uwana dakatai
Wazirin ina muku sallama ta addini musulunci".
Kowa ya amsa masa sannan ya nemi wajen tsayuwa ya tsaya
a sahon Hakimai.
Bayan yin shiru na dan lokaci sai Sarki yayi gyara murya ya
ce "Abdullahi bin Sharjas, sako ya zo daga Wazirin Bahara cewa ka
kubutar da 'yar Sarki Ababakari daga hannun kafura, z aka iya
fitowa ka yi mana Karin bayani”.
Abdullahi bin Sharjas ya fito daga inda yake tsaye ya tsaya y
ace "Tabbas da na Jarumi Umar shi ne ya tare su ya kuma amso ta ita
da wanda yake yi mata hidima, sannan bayan haka Waziri ya zo har
Kauye nemanta da yunkurin a bashi ita. Gimbiya Suhaila bin
Ababakari ta sanar da mu cewar Dan Sarki Salman ya saye duk wani
Dakare, da duk wani dan majalisar Sarki shi da mahaifiyarsa, na
lalllai shi ne zai gaji Sarautar mahaifinsa, a yanzu haka ma ranar
rantsuwa kadai ake jira domin shi yake gudanar da komai, sannan ta
ce ya bazama nemo dan uwansa Hilal. Shi kuma Yarima Hilal shi ne
yay i sako ga 'yar uwarsa cewar ta gudo daga birnin a kokarinta na
guduwa suka kama ta kuma suka tilastata akan sai ta kai su ga inda
Yarima yake, dakarun da suke tare da ita kafurai ne, kuma sun nufi,
Birnin Bahara da ita, wannan dalilin yasa na ce ya dace na zo kada
da kafa domin jin ba'asi ko sakacin da Sarki ya jima yana yi ya fara
taba martabar Sarautar Bahara"
x
Wata tsawa Shugaban Dakaru da Waziri suka dakawa
Abdullahi bin Sharjas, har da zare takubba. Sarki ya daga musu
hannu alamun su dakata cikin tsawa. Shi kuwa ko gezau bai yi ba
bature
B
38
39 Page
domin bait aba zuwa fada bai furta Kalmar sakacin nan ba, ba kuma
su fasa kawo masa bar aba, sarki bai fasa dakatar da su ba
"Muna bukatar ji daga gare ku, sannan kada ka manta Waziri
Ja'far sa'a daya da kawo Suhaila bin Ababakari wajena ya biyo
sahunta, shin me ya sani dangane da zuwanta, dole sai an sarewa
maciji kai kafin a samu nutsuwa"
Koda Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya zo nan a batunsa sai
yayi shiru ya kuma koma ya tsaya jin ta bakin Sarki Muhammad
farsi.
Lokacin Sarki Muhammad farsi yayi dakika biyu yana nazari
kafin ya ce wani abu, a wannan lokaci shi ma Waziri Ja'afar yana na
shi nazarin da ya kwana yana maimaita amsar da zata fitar da shi
daga zargi, don haka tun da dan aikin Shamsu bin Aujarya zo masa
yayi tashi dan aiki zuwa masarautar Shamnun abu na farko ya
gargadi 'yan majalisar masu zabar Sarki saboda su ne wadanda aka
tilasta su, aka kuma cika musu aljihu da sulalla, sannan aka yi musu
alkawarin ci gaba da zama a majalisa, batare da yi musu wani sharri
da kagen da za a kore su daga kan karagarsu ba.
A dai-dai wannan lokacin Sarki ya katse shi yana mai cewa
"Ko Waziri ja'afar yana da wani sani dangane da Gimbiya Suhaila
bin Ababakari?"
Waziri Ja'afar ya amsa "Ina