hatsari, musamman in sun gano cewar ni din
danka ne, zai fi kyau da muhimmanci na fita daga garin nan na nausa wani
wajen yadda za su biyo bayana..."
Abdullahi ya jinjina kai game da duban dan nasa ya ce "Ya kai
dana, shin baka yi sani cewar rayuwa kashi biyu ta kasu ba, rayuwa ko
mutuwa, Mangalawa sun iso cikin yankin Bahara da mayaka runduna
runduna, wannan alama ce ta gagarumin yaki ya tunkaro kasar Bahara,
sulhu da Mangalawa ba zai taba zama alkairi ba, domin idan har
Mangalawa sun nemi a yi sulhu wahala suka sha kuma sun nemi sulhu ne
domin a kyale su su je su kara shiri. Allahi ya ji kan Sadauki Nabaru, a
waccan lokaci tarihi ya nuna cewar kada a bar kowane Bamangale a doron
kasa, matukar bai yi imani da ubangiji musulunci ba domin ba za su taba
saduda ba, a lokacin da yaki ya ci su aka kashe sama da kaso takwas cikin
goma na mayakansu, sai suka yadda da a zauna a yi sulhu, wadda a wannan
lokacin idan da an yake su an gama da babin wata fitina, amma Ahlul kitab
su ne suka yi uwa da makarbiya wajen tabbatar da wannan sulhu, a lokacin
da Nabaru ya fadi gaban Sarki na wancan lokacin ya ce ka da a taba yadda
da wannan sulhu tunda an nemi a farko sun ki suka fito yaki aka yake su.
Amma Sarki da yake yana son zaman lafiya yana ganin abin kamar aikin
gama ya gama an riga an ruguje su, sai ya yadda da sulhu tun kafin a je ko ina ana samun matsaloli kadan kadan daga Mangalawa, da suka tumbatša
sai da suka nemi yadda za ayi a kasa dukiyar kasa a basu kasansu nan ma
aka yi musu lamuni, akan wannan haraji an sha samun sabani da su, amm
son zaman lafiya ake biye su, saboda a zauna lafiya. Yau ita ce ranar da irin
Sadauki Nabaru suke gudu. Na tabbata ba alkairi ne ya kawo su Bahara ba,
masu leken asirinmu sun tabbatar mana cewar sun kewaye kauyekan sashin
nan domin su mamaye su, da tsokanar fada za su fara, don haka koda kayi
yaki da su ko baka yi ba na san za su zodomin tuni labara ya zo sun bazo a
ko ina, sai dai wata dabara ta zo min cikin raina yanzu a game da batunka".
bature
106 Page
107 Page
Hakimi Abdullahi ya jinjina kai ya ce "Ka tafi izuwa Kogon Sulkui
kai da abokan tafiyarka, domin janye su daga cikin kauyen nan, saboda yara da manya za mu biyo sahunka ni da mayaka a yi karan batta a can,
zanyi haka ne domin mu magance shirinsu na afkamana gari".
Koda Jarumi Umar ya ji wannan batu sai dadi ya kamashi ya ce “Na ji dadin da ka fahimce ni ya mahaifina, zanyi duk mai yiwuwa wajen ganin na tsere musu har mu hadu a can Kogon Sulkui.
Koda gama fadin haka sai ya mike cikin sauri ya fita ya samu
abokansa ya tabbatar musu da cewar mahaifinsa ya aminta da shawararsa
batare da sanin kowa ba suka haye dawakai suka nufi hanyar barin gari tare da neman hanyar da 'yan leken asirin Mangalawa suke labe domin gano
waye Umar daga ina yake ina zai je.
A lokacin da umar ya baro inda ya yake su a jiya kamar ya san
cewar su biyo sahunsa sai ya sauka daga kan dokinsa adai-dai mararrabar
hanyar da zata sadaka da hanya uku. Ya yanken reshen katuware bishiya ya saka igiya mai tsaye ya daure reshan sannan ya daure a kogunsa yadda zai
zama yana janye da bishiyar idan yana tafiya a dokinsa har zuwa inda zai je
batare da sun tantance sawayen dokin ba zai kasance yana tafiya reshen
yana share sawayen dokin sannan sai ya ki bin mikakkiyar hanya yake bi ta
tsakankanin koramai da ciyaye a haka ya je har gida, wannan dalili ne yasa da suka zo suka kasa tantance inda za su samu Jarumi Umar.
Don haka ba za su tafi ba saboda suna zargin hanyoyin da yabi
suna cikin hanyoyin da suke wannan waje to amma rashin tabbas yasa suka
tsaya suna jiran abin da hali yayi don basu isa su koma su sanarwa da
Shugabansu cewar basu ga wannan Jarumi ba domin amsawar mutuwa ce a
gare su suna kwance cikin kwantan bauna irin na Mangalawa masana sirrin
jeji sai suka ji sukuwar dawakai da karfi tana kusanto in da suke nan suka
kara sunkuyawa kasa domin a tunaninsu wata runduna guda ceke tafe,
bisamamakinsu sai suka ga wannan Jarumi da aka turo don zuwa bin
diddiginsa a gaba wasu majiya karfi Jarumai na biye da shi suna sarrafa
dawakai kamar tun da suka zo duniya basu da aiki sai tukin dawakai, sun
wuce wajen kamar walkiya, aikuwa batare da bata lokaci ba suka kama
dawakansu suka bi bayansu, basu suka daina binsu ba har sai da suka
tabbatar da cewa sun isa Kogon Sulkui. Daga can nesa da su suna kallon
lokacin da suka shige cikin wannan kogon.
Koda ganin wannan ala'amari suka tsaya a can nesa sai daya daga
cikin dakarun Mangalawa y ace "Mutum daya ya komaga Rundunar Ulgurt
ka sanar da shi cewar ga inda wannan Jarumi yake don haka muna
bature
| Page
saurarenku a nan idan kuma sun matsa daga nan wani daga cikin mu zai babu yadda za mu bari su bibiye su yayin da wasu za su jira harku kara so,
bace mana".
Suleman wani tsohon hakimi ne da a yanzu babu wani daga cikin
masu mulki a daular Bahara da suka kaishe tarin shekaru don a kalla ya kai kusan shekaru dari da biyar mayaki ne na kwatace a zamani Sarki Farsi saboda haka yanzu ya kasance wani mutum mai fadi a ji a dukkanin Daular Fansi saboda girmansa da kuma dattako irin nashi. Hakimi Sulelam Bn Auyub na zaune a kofar gidansa bisa wani dakali da ya saba zama da jikokinsa yana musu tarihi sai dakaru da ke kewaye wajen don yin aikinsu, masu fita gona, masu fita kiwo duk in sun fito su kan zo su yi gaisuwa
sannan su wuce.
Yana nan zaune ya ji ihun mutu ne da guje guje dawakai jin hakan ke da wuya ya mike tsaye ya kuma fara tattara 'yan kanun jikokinsa da tattabekunnensa yana tura su zuwa cikin gidansa.
Domin tun da ya ji wannan amsa kuwa ya san cewar hari ne aka
kawo musu. Batare da bata lokaci ba dakaru suka cika a gabansa domin tsare lafiyarsa ya zare wata takobinsa domin shirin fafatawa da wadan nan mahaya da suka shigo cikin garinsa. Lokacin da yayi ido biyu da Mangalawa sai hankalinsa ya tashi ainun take ya umarci daya daga cikin
dakarunsa cewa ya je ya sanar da Kauyen kusa da su, daga nan ka wuce har babban birnin domin sanarwa da Sarki halin da muke ciki idan har ba a
kawo dauki ba Dakarun Mangalawa za su iya nasara akan mu”.
Yana gama fadin hakan dan aikin yayi sauri ya dauki doki ya sulale
ya bar garin, tuni guri ya yamutse da azababben yaki, babu ji babu gani ake
dauke ba dadi ya tsananta Hakimi tare da iyalansa da dakaru suna kokari
kare martabar garinsa, yayin da Jagoran dakaru na uku Barroji Ujjakallah,
da runduna ta bakwai Salkaf, duk a cikin tawagar da Bagulbasi ya taho da
ita daga yankin Mangalawa domin rushe musulunci a doron birnin Bahara
baki daya su mamaye birnin kamar yadda suka sha alwashi shekaru masu
yawa da suka shude.
Rundunar ta uku da ta bakwai runduna ce aka zabo manyan saboda
kowann Kwamandan yakinta jajurtacce ne kuma mai cikawa ne batare da
matsala ba, don haka Bagulbasi ya turo shi yankin nan domin ya shafe su,
ya zama shine misali na farko da za su fara aikatawa a birnin amma cikin
umarnin a taho masa da Hakimi Suleman Bin Ayyub saboda tsohowar
gabar dake tsakaninsu ta kin yadda da a yi sulhu a wancan shekaru sunan
bature
108
109 | Page
Suleman yana kan allon mangalawa saboda su ne suka so a mamaye su a kashe kowa a lokacin da suka kare a filin yaki dan haka dole sai an tara ire
irensu waje guda an gurfanar da su gaban Dodonsu kafin a shanye jininsu.
Batare dabata lokaci matansa barori da dakaru da duk wani mutum
yaro ko babba aka kashe shi cikin sa'a uku suka babbaki gari ko 'ina ya
zamana yana ci da wuta.ba tare da kakkautawa ba, abin bau tausayi dakarun
Mangalawa take gawarwaki suke yi suna shewa da murna cin nasara a karon farko.
Ba tare da bata lokaci ba suka dauki Hakimi Suleman suka daure
shi a jikin doki suka ja shi domin komawa masaukinsu, don gurfanar da shi wajen shugaban tawaga.
Sarki Muhammad Farsi na zaune a fada kamar kullum domin
‘ya'yansa ne za su gabato da irin kwazon da suka aikata a aiken da yayi musu sai ya zamana fada ta cika makil har a saman bene ta wata 'yar kofa Sarauniya Siyama na zaune tare da hadimanta suna kallon abin da ke faruwa a fadar Kamar kullum aka bude da addu'a sannan aka gabatar da Yarima Yazid yayi bayanin a game da aiken da aka yi masa zuwa Birnin Haiman, zuwa ga Benjamin, dukkanin abin da ya faru ya ci gaba da zayyanowa Sarki da wakilai na birnin da Hakimai tsoffin da manyan dattawan Sarauta suna kallo kuma suna saurarensa. Mahaifiyarsa gumi ne yake tsirfo mata domin ta san cewar lallai akwai damuwa duba da yanayin da take kallon fuskokin mazauna fadar Sarki musamman Dattawan fada. Sai da ya kare da yin bayaninsa tsaf mai rubutu yana rubutawa kamar a al'adance duk wani abu da aka zauna a fada ana tattaunawa z aka samu ana rubuta shi cikin wasu na’un fatoci falli falli.
**
Lokacin da Yazid ya gama jawabansa sai hankalin kowa ya koma kan Yarima Abbas a lokacin da ya fito ya tsaya ya fara karanto al'amarin da ya faru a birnin Shamnum da yadda ya gudanar da komai cikin nasara kuma aka zartar da hukuncin da ya dace, abin da ya rage ya barwa mai martaba Sarki Muhammad farsi don haka a cikin fadar duk wani mai kallon
mulkin birnin a matsayin tsira ne ga al'ummar duniya ba domin wani buri na tara dukiya ko burin son mulki ba sai fuskarsa ta cika da murmushi jin cewar lallai Sarki ya samu magaji, musamman dattawan birnin da Ulama'u wato Malamai magada annabawa.
Duk inda ran Siyama da na Waziri Ja'afar ya kai yayi mummunan faduwa, kuma zuciyarsu cike take da kuna da zafi mara misaltuwa. Sarki
ya bawa Yarima Abbas umarni da ya koma ya tsaya a matsayarsa. Domin *bature
3
110 | Page
ci wasu su zo su ci gaba da karanto al'amuran na yau da gobe abin da ya gaba da wakana kenan har ya zama an zo kan Sarki zai yi jawabinsa,
wadanda duk wani dake cikin wannan fada abin da yake so ya ji ke nan.
Sarki Farsi ya mike tsaye cikin juriya yana mai fuskantar jama'a ya
fara da cewa "Masarautar mu, ta wanzu cikin shekaru shekaru masu yawa
da kafuwa, an zubar da jini makiya Allah, wadanda 'yan uwa ne a gare mu,*
an zubar da jinin kafurai Mangalawa da sauran Bokaye 'yan tsibbu
wadanda suka saka birnin mu a gaba suna son ganin karshensa, cikin ikon
Allah da taimakonsa mun rusa birane mun kama birane mun musuluntar da
al'umma a ban kasa fiye da kima, mun yi aiki kafada da kafada wajen
jaddada Kalmar Allah.
Ina ba da tsohon labari ne da tun kafin zuwana duniya, zuwan
dukkanin wasu da suke nan duniya, mun jera da iyayenmu mun tari
bataliyar mayaka daga Rum, mun tare bataliyar mayaka daga hindi, mun
tare bataliyar mayaka daga sassa na duniya anyi hadin gambiza domin a
kawar da Daularmu, amma cikin ikon Allahu mun zamar musu gagara
badau. Ina daga cikin zababbun jarumi da sunansu ba zai taba gogewa ba a
doron kasa a can nahiyoyin kafurai da yahud domin irin nasarar da na samu
a kansu.
Na zama sarki saboda bunkasar jarumtaka ta, na zama zakara fidda
gwani a jerin dakarun birnin Bahara, zamowa ta Sarki labarin da bunkasa
ya ci gaba, amma lokaci ya wuce an fara samu sauye sauye na daga ci
gaban musulunci, lallai Zakin da ya rayuwa a baya, zai ci gaba da wanzuwa
a nan gaba, domin akwai bayin Allah da suka rayuwa suna kyautatawa suna
aikin kirki amma a karshen rayuwarsu suka juya ba suka koma shaidanu,
wa'iyazubillahi Ya Allah ina rokonka karshe na ya zama ya fi farko na
kyawu, ya ubangiji ka agaji ne ka karfafeni domin na ci gaba da dira birnin Bahara a kan tafarki gaskiya da sauran kasashen duniya mu ci gaba da
yadawa da'awa mu kai musulunci inda bai je ba". Ya zare takobinsa a dai-dai wannan lokaci ya daga sama yayi
kabbara nan take wajen ya kaure da Kabbara "Allahu Akbar! Allahu
Akbar!! Allahu Akbar!!!
Guri ya dauki shiru bayan an kaure da kabbara ana sauraren Sarki
Muhammad Farsi. “Mun yi aike ga Benjamin yayi rashin ladabi ga dan aikinmu, duk da dan aikin ya kasance jinin sarautar birnin Bahara, wannan
kuskure ne a gare su, kuma tsokanar fada ce bisa gayya a ka yi, ya zama
dole mu kwace Hairama domin ta dawo karkashin ikonmu.
bature
111 Page
Babu musayar zance a tsakaninmu, babu yarjejeniya ko zama
ashimfidar sulhu face kaifin takobi ta ratsa jini da tsoka domin mu
kausasa su fahimci har yanzu Bahara na nan a raye bata mutu ba,
tabbas sai an nufi Rum da gungun zunzurutun gawarwakin sama da
dubu.
Daga karshe ina mai sanarwa ga shugaban dakarunmu ya tura
sako zuwa kowanne kauye cewa za a aje a kwace hairam, domin In
danka mulkinta ga dana Yazid.
Birnin da suka zubar masa da kima da mutumci zai zama
jagoran birnin anan da kwana biyar masu gabatowa".
Gaban gimbiya Siyama ya kara faduwa hankalinta ya kara
dugunzuma dogon burinta na ganin danta ya mallaki birnin Bahara
ya na neman ya salwanta saboda tabbas aka danka masa mulkin
Haiman shi kenan sai idan har rabo ya rantse na tabbatuwar sa Sarki.
A hargitse ta fice daga cikin dakin da take iya juyo
maganganun da ake a zaman fada ranta a bace suka koma cikin gida.
Daga wannan Sarki ya sallami kowa domin tun daga yau ba
sai gobe ba a fara shiri duk wani mayaki ya gyara takobinsa duk
wani maharbi ya gyara kwarinsa, mai duba lafiyar dawakan birnin ya
ci gaba da aikinsa, makera masu kera makamai su wanzu batare da
sun hut aba wajen samar da sabbin makamin yaki. Domin yaki babu
fashi, don haka gari ya rikice da zaryar bakin kauyekan nesa, mata
suka wanzu suna yiwa mazajensu shiri, mazaje suka dukufa wajen
ganin sun barwa iyalinsu abin da za su ci su sha har Allah ya dawo
da su, masu rauni suna kuka rabuwa da iyalansu. Yara wadansa
karfinsu bai kai a fita yaki da su ba hankalinsu ya tashi suka koma
gefe suna kunci da takaici domin babu yadda za su iya har sai jarumi
ya kai shekaru ashirin a dokar birnin kafin a fita da shi yaki.
Sarauniya Siyama ta rasa tsuntsu ta rasa tarko dole ne ta yi
wani abin da zai haddasa dakatar da fita wannan yakin saboda yinsa
babbar asara rayuwaka za a yi wanda kuma tana da tabbacin sai an
yashe birnin Haiman an kwace shi ya kuma karkashin kulawar
mijinta, tabbas yin hakan babbar asara ce a gare su, dole tana bukatar
yin sirri da babu wani mahaluki da ya sani a cikin birnin Bahara, dole
bature
112 | Page
za ta fita ta gana da mahaifinta don ta san shi ma yanzu ya san
yakin sannan hankalinsa yana dugunzume kamar yadda nata
dugunzume me, dole ta shirya fita domin ganawa da shi ko da wata
dabara da za ta hana wannan fita yakin.
Ta kai gauro ta kai mari tana zagaye tana son ta samu yanay?
mai kyau don ta tsayar da tunani da za ta yi amfani da da damarta
kafin lokaci ya kure mata.
Yanzu ne maso ma labarin Daular musulunci
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels