yi
babban kuskure ranka ya dade a gafarce mu?"
Yarima Abbas ya mike daga kan kujerar mulki Shamnun ya
nufo inda waziri Adnan yake yana cewa “Kai ne magajin birnin
Shamnun, kai ne abokin Sarki Kawu na Ababakari shekarunka sun yi
tasirin da zaka wanzar da masalaha a tsakanin wasiyar da Sarki ya
bari, kai ne za ka yi bi duk hanyoyin da za yiwa 'yan uwa juna
adalci, amma kai ne mai kuskure aiwatarwa, da ace a lokacin yarima
Hilal ya fara mulki ne za a iya yi masa afuwa bisa ajizanci da kuma
girma irin na sarauta da rashin kwarewa zai iya kuskure, amma babu
wani abu da baka sani ba, saboda haka baka cancanta da zama Waziri
birnin Shamnun ba”.
Ya zube kasa ya fara neman kama kafafuwan Yarima Abbas
"Kayi hakuri ranka ya dade shekaru ashirin ina kan matsayina ka
tausaya min na mutu, ina zan kai darajata kima da ake kallo na da shi
a cikin birnin na".
“Ka koma ka yi bautar Allah kajira lokacin da Allah zai dauki
rayuwarka, ko ka samu ka rabauta zuwa ceton Manzon Allah amma
babu wani dalili da me kuskure irin wannan ya ci gaba da zama
waziri birnin Shamnun."
bature
Dakarun hudu suka shigo cikin fadar suka bambare shi daga
jikin yarima Abbas suka fitar da shi yana ci gaba da magiya amma
Yarima Abbas ko kallon inda yake bai kara yi ba.
Ana fita da shi sai ga dattijan birnin sun shigo wadanda suke
da alhaki akan zaban Sarki, Yarima Hilal yana dubansa gabansa, sai
da suka gama shigowa suka samu waje suka zauna sai Yarima Abbas
ya fara tafiya cikin takama da izza irin ta saraki, har sai da ya ya isa
inda suke kansu a sunkuye alamar girmama Yarima Abbas.
"Ina Adalcin ku, ina iliminku, ina tsoron Allah da shi ne ya
baku cancanta aka dauki kujerun nan aka baku, tabbas kun ci amanar
Allah kuma kunci amanar masarauta dole sai hukunci ya tabbata a
gare ku, domin ba ku zamo adalai kamar yadda ake tsammani ba."
Shugaban Dattijan majalisar Abu Kaisar yayi ajiyar zuciya
gami da "In an bani izini ina da Magana."
Yarima Abba ya dube shi ya ce "Da sauran lokaci kafin wani
ya yi Magana".
Abu Kaisar ya jinjina kai gami amsawa da girmamawa.
Yarima Abbas ya dubi yarima Hilal yace da shi "Na yi kokari gano
inda Yarima Salman yake boye a jiya da yamma shi ne dalilin da
yasa na samu kurewar lokaci ban shigo birnin nan ba a daren jiya,
sannan na samu aiko da sako zuwa ga wasu yan majalisar Sarki don
su shaidamin dalilin da yasa yarima Salman ya gudu, na samu
dukkanin labari, abin da ya faru, sannan dukkanin alʼamarin da ya
faru na samu hujja mai karfi wacce zan iya yanke hukunci kai tsaye,
amma bisa adalci ba zan yanke hukunci kai tsaye akan ku ba, saboda
laifinku na tilastawa ne ba kamar Waziri ba da na samu dumu-dumu
da laifi barkatai, "Ka shigo min yarima Salman".
Ya dubi daya daga cikin dakaren da yake tsaron lafiyarsa. Kai
tsaye dakaren ya tafi zuwa bakin kofar fadar yana zuwa yayi Jarumi
Umarni da hannu aka shigo Yarima Salman cikin fadar. A nutse yake
bature
68 Page
69 Page
tafiya cikin izza ta mulki babu tashin hankali ko firgici a tare da shi,
ya zo gaban Yarima Abbas ya tsaya cikin girmamawa, Yarima
Abbas ya dube shi cikin kulawa sannan yace "Me yasa ka bar birnin
Shamnun
"Na bar birnin Shamnun wane dare da na kwana da zargin
cewar akwai makarkashiyar daga fada, na gano cewar an shirya
hallaka ni ne, saboda yadda na isa sansanin dakaru, na duba yadda su
ka amshi ne a matsayina na wadda mahaifina ya bar suna na a
matsayin magajinsa, har sai idan akwai wani abin cutarwa da na taba
aikatawa bayan ba ransa kafin nadin sarauta, na shirya zama da yan
Majalisar dattawa na gidan Sarauta, ban samu hadin kan kowa daga
cikinsu ba, sai wasika a cikin dare da wani daga cikin majalisar
dattijai ya turo min da ita"
Koda ya zo nan a zancensa sai ya dauko wannan takardar da
aka rubuta wasika ya fara karantawa don kowa ya ji
Ka bar birnin Shamnun a daren yau, ka da ka bari ka kwana,
babu yadda za mu iya ta dole da sa hannun kowane dattijon majalisa
saka hannu a kashe ka bisa zargin da za a dora maka na cin amanar
kasar wadda za a turawa Sarki Muhammad farsi a matsayin laifi.
Bai bayyana ko wane ne shi ba saboda tsoro na so nayi tirjiya
na dake na ki guduwa amma kuma sai na tuna matukar bakuna sun
hadu to bani da wani karfi da zan iya tunkarar su, sai nayi amfani da
wannan shawara ta wannan mai turo min da sakon takarda na bar
birnin, haka kuma ya kara tura min sakon na janye yar uwata daga
birnin Shamnun saboda ana kokari ayi amfani da ita don gano inda
kake, wannan dalili yasa na bar birnin nan nab ace cikin wani
rukunin kauye a cikin birnin Shamnun yadda babu wadda ya isa ya
gano inda nake, sai a lokacin da nag a tawagar Yarima Abbas na
daren jiya na bayyana a gare shi domin zayyane masa dukkan abin da
ke faruwa.
bature
70 Page
Koda Yarima Salman ya gama jawabinsa, sai yarima Abbas
ya juya kan yarima Abu Kausar yace "Kana da damar da za ka fadi
albarkacin bakinka".
Shugaban zauren majalisar dattaje abu Kausar ya mike tsaye
gami da cewa "Mun yi babban kuskure a bisa al'ada na dan adamda
tsoro yake bin jinin jikinsa da son duniya, na yabawa dattijai na
karkashina da a karon farko sun turje, duk da cewar an dauki silalla
masu daraja an basu, an kuma yi musu alkawarun masu nauyi duk da
hakasun turje sai akafarayi musu barazanar kisa, sannan aka hana
tura mu sako ko kuma fita daga birnin ta kowacce hanya, ni ne nayi
amfani da wani bawa na da babu wadda ya san shi nake aikawa
Yarima Salman sako, sako na farko da na biyu, mun gaza a
matsayinmu na masu karfi a masarauta, mun saka tsoro a
rayuwakanmu, na so mun jajurce koda za a jininmu zai zuba a doron
kasa amma dayake mun yadda Allah daya ne kuma zai kawo mafita
sai muka dage da addu'a Allah ya wargaza wannan al'amari, a
kullum mukan hadu mu sauke alkur'ani mai girma, babu taba
gajiyawa ba, cikin sauki Allah ya kawo mana mafita, ya kai Yarima
mai daraja, muna sanar da kai babu wani ko wani da ya ci koda daya
daga cikin sulallan da suka ba mu, sannan muna farin ciki a yi
gaggawar yi mana hukunci mafi dacewa saboda mu masu laifi ne".
Koda ya zo nan a zancensa sai Yarima Abbas ya jinjina kai
gami da duba lamarinsu da kuma kokarinsu na kai kuka ga ubangiji,
sai ya ce "Na bar lamarinku ga mahaifina, domin bazan iya yanke
wannanhukuncin ba, a kai tsaye zan iya yi muku adalci, amma ban
sani ba ko masarauta za ta iya yafe wannan laifin amma a bangarena
na jinjina muku”.
Sai a wannan lokacin Yarima ya koma ga Yarima Hilal ya ce
"Me z ace dangane da al'amarin da ya afku, shin akwai sharri ko
kage a ciki?"
bature
71 Page
Yarima Hilal yayi shiru kansa a kasa daga bisani ya dago kai
ya dubi Yarima Abbas yace "Ba ni da wani kudiri da na kunsa a
raina illa na gaji mahaifina, dalilina kuwa shi ne tsoron makoma ta
da kullum ake tsorata ni da shi shi ne idan Yarima salman ya zama
Sarki zai kashe mahaifiyata, sannan zai kashe ni da yan uwana,
saboda tsoron za mu zama barazana a gare shi, na yadda na amince
cewar zan zama Sarki amma ba hannu na a cikin duk wadannan
al'amarin da aka aikata na bada sulalla, na yunkurin kashe yarima
Salman, da ma tara dattijai domin tilasta su, abin da na yadda da shi
zan zama Sarki wannan kuma shi ne fatana".
"Tun anan ta tabbata ba z aka iya zama Sarkin birni guda ba,
tunda har za ka iya kauda kai a yi duk abin da aka ga dama,saboda
haka baka cancanta da zama Sarki ba kai da duk wadda yake da
hannu a cikin birnin nan za a rufe ku sannan za a rantsar da Yarima
Salman a matsayin sarki a gobe hukunci yana hannunsa"
Koda ya zo nan a batunsa sai ya fice daga cikin fadar
dakarunsa suka bi masa baya. Dakarun da suke bawa Yarima Hilal
tsaro suka dawo bayan Salman.
Bai tsaye ko a’ina sai kofar fada a lokacin da Jarumi Jarumi
Umar ya samu kansa sosai har an bashi abinci da ruwa ya ci ya
koshi, da sauran abokansa, Yarima Abbas ya kasance tare da su, ta
hirar jarumtaka da yadda za a kawo gyara da sauyin tsarin birnin
gaba daya.
Jarumi Umar yayi nisa cike da damuwar abin da yake taba
masa zuciya yace “Ranka ya dade, Kasar mu na cikin mawuyacin
halin kuma tana gab da zubewa matukar aka kasance a haka, ku ne
masu iko da gyara komai na sarauta da kuma juya akalar al'umma
zuwa ga bin tafarkin gaskiya.
A tarihin da muka samu a shekarun baya lokacin da Kakanku
na mulki, babu wani kafiri da ya isa ya shigo cikin birnin Bahara har
bature
72 | Page
sai an yi da shi ya kuma saka hannun cewar ba zai sabaka'idar birnin
ba, ba kuma zai yi shigar banza ba, sannan ba zai yi addininsa a
bainar jama'a ba, a wannan lokaci ba a samun musulmi yana shan
giya, ba a samun musulmi yana canca, ba a samun musulmi yana
aikata zina, musulmai na lokacin Kakanka sun kasance masu
matukar tsoron hukunci, koda a ce babu tsoron Allah a ranka to la
shakka kana tsoron hukunci daga masarauta, masu bin addinin kuma
suna tafiya a tafarki daya babu rabe raben kawuna, idan an ga wata
kowa yana yadda kamar yadda Sarki zai yi bayani, haka zai dauki
azumi kamar kowa, babu malamai masu zuwa da sukar hadisan
manzon Allah sallallahu alaihi wasallam, babu masu zagi da cin
mutumci wasu ahli da manzo ya zauna da su a matsayin 'yan uwa
ana matukar tunkarar birnin Bahara da yaudara domin kowanne
malami ko bayahude da ya yi baddakama ya shigo birnin ya san
karshen kaifin takobi ce karshen numfashinsa, amma yanzu
kauyukan irin namu na tsoron shiga cikin kasuwar birnin domin
tsoron kada yara su dauko munana akidu daga kafirai yahudu, ranka
ya dade yaushe ne wannan makircin da yahudu ya shiryawa birninmu
zai kau daga doron kasa.
Maganganun sun shiga zuciyar Yarima Abbas kuma ya ji su
har cikin ransa, tabbas Jarumi Umar bashi da tsoro ko fargaba kamar
mahaifinsa, domin dukkan mutanen birnin suna tsoron zuwa yiwa
Sarki wannan tambaya amma sun kasa, sai Abdullahi bin Sharjas ne
kadai yake iya gaba da gaba da Sarki ya gaya masa gaskiya, yau
gashi dansa bai ji shakkarsa ba,shi maya tare shi ya sanar da shi.
"Lallai komai yana da lokaci, kuma yana da karshe, insha
Allahu za mu yi maganin komai da yaddar Allah. Yanzu na san a
kagauce kuke da kuka ma hanya don komawa gida. Za ku iya tafiya,
Ya kai Jarumi Umar ina son sanar da kai cewar a duk lokacin da na
bukaceka da kai da abokan tafiyarka lallai na ji dadin kasancewa tare
bature
2
73 | Page
da ku,domin a rayuwata na tsani munafunci, kuma ina son mutum
gaya min gaskiya duk dacinta, saboda hakaina bukatarku a tare da ni,
kuma ina nan zan kawo maku ziyara bayan na kamala da ayyukan da
mahaifina ya sakani".
Suka jinjina kai alamar gamsuwa da maganarsa. Jarumi Umar
ya ce "Na ji dadin yadda ka gyara lamuran birnin SHamnun a
kankanin lokaci, ina fatan ka taimakawa Sarki Muhammad farsi a
dukkan tafiyar da lamuran kasarsa Allah ya taimake ka"
Yana fadin haka suka mike tsaye Yarima ya dube su "Insha
Allahu za mu yaki kafirai kafada da kafada tare da ku, za mu
fatattake su daga birninmu insha Allahu, Allah ubangiji ya tsare
hanya".
Suka amsa da amin su dukansu sannan suka nufi hanyar fita
yana tsaye yana kallonsu, yana ji a ransa akwai nasara a rayuwarsa ta
zama Sarki a haduwa da ahlin Abdullahi bin Sharjas, domin ya
fuskanci ta inda zai gyara tafiyar birninsa ta hanyar shawarwari ga
mahaifinsa sannan kuma ya samu tsakwakuren da zai yi tare da su
har suka fice yana murmushi.
**
Wata irin bakar runduna ce mai tsananin yawa ta taso daga
yammacin birnin Bahara, wasu gungun bataliyar dakaru ne iya
ganinka rukuni rukuni sun kai rukuni goma, duk rukuni daya z aka
tadda su birjik kamar gudaje, sanye suke da bakaken kaya da aka
sana'antashi da batar bakar damisa, idanuwansu jajaye da hula na
akansu wadanda suke da kahon saniya guda daya daya a tsakiyar
goshinsu.
Dawakansu ma bakake ne wuluk babban cikinsu na tafe, yayi
wasu zaneka da baki a kan fuskarsa wadda alamun hakan yaki ne
labbansa bakinkirin, yana muzurai yana zare ido.
bature
74 Page
Babban Dakare na kare dange daga cikin Dakarun Hangalawa ne ke tafe a gaba da kamar taku shida sannan dakarun nasa na biye da shi a baya kato ne na gaske, haka dokinsa jibgege ba karamin namijin gaske bane zai yi idi biyu da wannan katon bai koma da bay aba, yan da suma kamar mahaukaci a kansa sannan akwai wata
jelargashi guda daya ta ka har gadon bayansa. Ana Masa lakabi da BAGULBASI. Su ne arnan daji na cikin daular musulunci wadanda
aka ci su da yaki suka koma rayuwar kauye tun shekaru masu aka
fatattake su da shirkokinsu da Allolinsu aka kusan karar da su,
wadanda suka kubuta ne suka koma jeji, suka dauki gina sabuwar
rayuwa tun a baya da shekaru masu yawan gaske, su kan fita su sato
jarire su maishe da su nasu, su dora su akan yaki, baya da shekara
dari biyu suka fara bayyana a duniya aka fahimci suna nan basu kare
ba, su kan zo kauye su farmake su su kwashe dukkanin yara su kashe
tsoffai su kwashe mata. A wannan lokacin su ka addabi duniya ba
musulmi babu kafirai ko ina yaka suke yi, sai aka samu hadin kai na
kafurai da musulunci a lokacin Sarki Ahmad aka yi mummunan
yakin da ta sa kowa yayi asarar rayuka.
Da aka fahimci yaki da sub a zai ba su ma suka tabbatar da
aka ci gaba da yakin za a kara mai da su baya sai Kiristoci su ka
nema shawarar sarki Ahmad akan cewa sulhu shi ne mafita, to a
wannan lokacin aka zauna sulhu aka yi da su, zasu dinga amsar
haraji daga bakin da suke zuwa daga bangaren bakaken fata wadanda su ne a bangarensu, sannan babban birnin zai basu wajen rayuwa a
zauna a tare. Sai suka ki yadda cewar su ba sa zama a cikin gini basa
su rayu a cikin birni da aka kayata shi baza su koma jeji su ci gaba da
rayuwarsu, sannan kuma sun amince da za a dinga amsar haraji kaso daya cikin kaso hudu, za su yi kasuwanci na noma suna shigowa da
shi, amma sub a za a shigo musu da komai.
1
bature
75 | Page
Aka yadda da sharadinsu, aka zauna lafiya da su amma a
cikin kasan zuciyarsu suna nan suna hayayyafa suna kai farmaki
wajejen sin suna kamo jarirai suna manyan fashe a bangaren teku, da
haka suka kara hada babbar fada suka tumbatsa suka bada horo mafi
tsananin ga dakarunsu domin suna son yin shirin na gaske da sai sun
fitar da musulmi daga cikin birnin tunda birninsu ne tun asali.
Su kan jima basu kawo matsaloli a birnin ba, sai jefa jefa
kuma da an je an zauna da shugabansu zasu nuna bada goyan
bayansu ba, a nemi wasu daga cikin dakaru a yi musu hukunci
acewar su ne suka aikata da haka suka mamaye jejin tsoro da fargaba
kowa a duniya ta fita daga zuciyarsu.
A yau shugabansu Sarki Alifkato ya fara turo runduna guda
domin fara mamaya shi ne wannan fitowa domin fara nunawa birnin
cewar sun shirya domin yin fito na fito da su. Don haka suke tafe
cikin izza da takama, kai tsaye wasu irin makamai ne a hannun
kowacce ruduna da take tafe, wasu za ga duk yawansu Gatari ne mai
sheke da walwali a hannunsa, wasu kuma za ka gansu da mashi,
fikakku masu tsayen gaske,wasu rukuni duk kwari da bakoki ne a
hannayensu cikin shiri,wasu takobba, wasu kuma al'amudi ne,suna
tafe suna yiwa abin bautarsu kirari don neman yaddarsa a fitowarsu. **
Lokacin da Yarima Zaid isa bakin kofar shiga birnin Haiman
karkashin jagorancin Benjamin sai yayi Jarumi Umarni da a tsaya da
dawakai domin neman iso. A ka bude karamar kofar birnin Sarkin
kofar ya fito a bisa dawakai mutum biyu na biye da shi. Fararen
dawakai ne sun ado na kawa da gani kasan akwai kyalli da
kyalekyale a cikin birnin tun daga tufafin dakarun birnin da yadda
aka yi wadaka da dukiya wajen ginin katangar birnin. Lokacin da
dakarun suka iso sai shugaban dakarun kofar ya iso gaban Yarima
Hilal ya ce "Lalle marhaba da zuwan dan Sarki Muhammad farsi,
bature
76 Page
tun saura rabin sa'a muka san da zuwanka domin masu kula da
dajijjikanmu sun kawo mana labari, Shugaba Benjamin na maka
maraba, amma ya sanar da ni cewa ka shigo cikin birnin daga kai sai
mai yi maka hidima wato bawanka domin tsari da birnin mu yake da
shin a son zaman lafiya shiga da dakaru irin wadannan zai sa firgici
da tsoro a zuciyar mutane mazauna birnina"
Koda Yarima Zaid wannan batu daga bakin bakin shugaban
dakaru sai yayyi murmushi ya ce "Dukkanin nahiyar nan mallakin
birnin mu ce, dukkanin iko da Jarumi Umarni yana karkashin
masarautar mu, saboda haka sa'a daya kaci har da zan bi wannan
Jarumi Umarni, dama ban zo da niyar na shiga birninku da dakaru
ba, na zone domin na shiga ni daya, saboda haka mu je zuwa”.
Shugaban dakarun yayi murmushi shi ma sannan ya juya
dokinsa Yarima da Hadiminsa Arif suka bi bayansa.
A haka suka isa har babbar fadar Benjamin, a lokacin
Benjamin na zaune akan karagar mulkinsa Yarima Hilal ya shigo
cikin fadar cikin Gadara da isa irin ta masu mulki. Benjamin bai tashi
daga kan karagar mulkinsa ba har sai da Yarima ya zo daf da shi,
sannan ya saki fuskarsa gami da murmushi na rainin wayo ya ce
"Sarkin Muhammad farsi ya aiko ka ne domin jin ta bakina game da
neman 'yar Sarki Ababakari, idan na canka zan baka gamsasshiyar
amsa".
Yarima ya kufulo da halin Gadara da Benjamin yake yi masa
ya ce "Kai kafiri maʼabocin bautar wanin da ba Allah ba, ka yi sani
cewa alfarmar zaman lafiyar da yake rubuce akan tafarkin takarda
yake zaune da kai a wannan kujerar har kake iya yin wani motsi,
baya ga haka da ire irenku basa numfashi, ka yi biyayya cikin ladabi
ka kuma lura da kanka da ke kan gangar jikinka, koda na bar
makamina a waje zan iya amfani da naka cikin 'yan dakikai na sare
wuyanka a take a yanzu".
bature
77 Page
Wasu dakaru da suke tsaye a fusace suka motsa suna shirin su
afkawa Zayed, sai Shugaban Benjamin yayi dariya ya ce "Karfin
gwiwarku da kurinku yake tsoratar da matsora ta, na fi ka tsanar
rubutaccen alkawarin zaman lafiya domin bana bukatar zaman lafiya
na fito a kodayaushe na ganni inashawagin cikin musulmi ina cire
kansa kamar ina sassabe a gona, ka yi sa'a saboda wannan
yarjejeniyar zaman lafiyar da baka isa ka fita daga cikin fadar nan a
raye....
Kamar an jefa kibiya daga cikin gwafarta Yazid yayi tsalle
kan Benjamin,dukkaninsu cikin shirin farmakarjuna suke sai shima
Benjamin yayi kururuwa ya taho suka gwabzo, kowa ya ji jikin dan
uwansa,dakarun Benjamin da bawan Yazid kowa yayi yunkurin
tasowa. Benjamin ya daga musu hannu "Kada wadda ya motsa,
wannan bai sabaka'ida ko yarjejeniya ba, yaro ne yake so ya gwada
gwanjinsa don haka ku bar shi”.
Ran Yazid ya kara fusata hankalinsa ya dugunzuma ainun ya
kara farmakar Benjamin akaro na biyu suka kaure da yakar juna
kamar wasu zakaru a fagen fafatawa.
Yazid na da jarumta ta ban mamaki ko da yake dama babu
wani matashi a kasar Bahara da ya kasance rago musamman jinin
sarauta babu takobi a hannunsa, cikin kwarewa ya zare daya daga
jikin wani matashin badakare da ya ZO kusa dank are
shugabansa,amma shi kansa bai san lokacin da
takobinsa ba, saboda tsananin zafin nama.
Yazid ya zare
Suka kaure da yake suna kaiwa juna sara da suka kowa yana
karewa iya karfinsa, idan Benjamin ya matsa kai sara da suka har ya
kusa kure Yazid sai Yazid shima ya kufula ya harzuka ya taso da
nashi sara da suka har sai ya kai Benjamin mukura aka dauki kusan
rabin sa'a batare da wani ya samu lagon dan uwansa ba.
bature
78 Page
Kafin kace mene ne sun zamar da fada tamkar wacca aka
kwana ana yaki, kuma duk da haka ba a samu wani ya samu nasarar
sarar dan uwansa ba, duk irin mugun nufin da suke kai wa junansu.
Tsamari yayi tsamari har ya kai har da yawa daga cikin
manyan dakarun Benjamin sun iso fadar Sarki amma Benjamin ya
dakatar dasu da niyar daukarmataki, a na cikin wannan fafatawar ne
Benjamin ya kuntata Yazid da sara da inda ya kai masa wani sara a
lokacin Yazid ya kwanta a kasa, sun hada kaifin takubbansu inda
Yazid yana kasa yana kokarin yayi amfani da damtsensa wajen
wancakalar da Benjami amma Benjamin ya daddage domin so yake
ya fi karfin Yazid ya ya kais hi karshe ana cikin hakada Benjamin
yaga ya gagara kaiwa ga gaci gashi kuma karfinsa na neman karewa
sai yayi dabara ya zare wata wuka daga kubensaya yanke hannun
daman Yazid. Yazid yayi kara gami da sagewa har Benjamin ya kusa
kai takubban kan wuya Yazid, sai Yazid yayi wata kabbara wani
sabon karfi ya zo masa duk da yankan da yake hannunsa ya fara fitar
da jini amma hakaya wuncakalar da Benjamin ya mike tsaye ya dubi
wajen yankan,amma cikin jarumta ya kara gyara takobinsa ya farwa
Benjamin dake kasa, amma kafin ya kai kansa ya mike tsaye ya zame
banda zamewar da yayi da sara ne mummunan zai tsagashi gida biyu.
Benjamin ya rufo bayan Yazid da niyar ya farmake shi ta
baya, sai Yazid ya wani juye Benjamin ya wuce kamar iska, a
wannan yanayin Yazid yayi amfani da kwarewarsa ya saka takobinsa
ta yanke kuben cikin Benjamin,
Benjamin ya rike wajen ya duba hannunsa yaga jini face face,
yayi murmushi shi ma Yazid yayi murmushi ya ce "Ka ci darajar ^
yarjejeniya da wannan yanka farke cikinka zanyi hatta da hanji su
fito su bata fadarka, to amma ba wannan ne ya kawo ni, na zo gare
ka domin na ji dalilin dayasa kuka farmaki Yar Sarki Ababakari”.
bature
79 Page
Shugaba Bejamin ya jinjina kwazo da bajinta irin ta Yazid
sannan ya ce "Ka koma ka sanarwa da Sarki mun kama ta ne saboda
muna son mu kaita ga Sarki Mu'azzam domin soyayyarta da yake yi
tun shekarun baya da suka wuce, don haka mu a kan kin kanmu ba
mu da wata alaka da ita face hada soyayya tsakaninsu da Sarki
Mu'azzam da ke mulki birnin Sarraf, yarana sun dauketa su kaita
Bahara sannan su dankata da hadiman Sarki Mu'azzamda so kai
masa ita ya aureta".
Koda Yarima Yazid ya ji wannan batu sai ya cika da mamaki
domin Sarki Mu'azzam dan uwan ne ga mahaifina, wadda yake dan
ne shi ga Yayanshi, sannan kuma Sarki Mu'azzam bashi da son rai
yana bin mahaifinsu batare da wata boyayyen munafunci a zuciyarsa
ba, Sarki Mu'azzam ya bada rayuwarsa ga Sarki Muhammad farsi
don haka ya ce "Wannan yana daga cikin aikin shaidanci da fajirci
irin naku, saboda haka karya kake, idan Mua'zam zai nemi auren
'yar Sarki Ababakari, kai tsaye bazai fito ta wannan sigar har ya hada
kai da ku".
Benjamin ya ce "Ji ya zama dole ka bukata na sanar da kai,
wannan matsalolinku ne, kamar yadda aka so ka zo ka ji na sanar da
kai, idan Sarki Muhammad farsi yana bukatar shaidawa muna ita,
domin ba ma yin kwanmu sai da zakara”.
Koda jin wannan batu daga bakin Benjamin sai Yarima Yazid
ya jinjina kai daga nan kuma sai ya girgiza kai yace "Kayi babban
kuskure, ko kana da laifi ko baka da shi, wa'adin mutuwa ya zo
gareka, ka jira martani”.
Daga fadin haka ya fice daga cikin birnin koda Yazid ya fita
sai babban mai kula da cocin birnin dakuma manyan dakaru suka zo
gaban Benjamin Babban shugaban coci ya ce "Kayi ganganci ya
shugaba, shin baka tunanin matsalar da zata biyo baya".
bature
80 Page
"Ban so abubuwan nan suka faru ba, domin ba abu ne mai kyau ba, ya ci a ce mun bi shirinmu a hankali, tabbas dole mu kara tsaro da kuma garkame birninmu sannan dole a samu a aikawa da
masarauta rum sako".
Benjamin ya ce "Masarauta ta gaji da zamowarmu bayin musulunci, ita da kanta ta so mu aikata fitinar da za mu warware
yarjejeniya saboda mun tanadi mayaka marasa iyaka za mu iya yaki
da su a yanzu".
Dukkaninsu suka yi shiru suna nazarin maganganun da yake
fada,amma a zuciyarsu suna cike da tsoro domin Sarki Muhammad
farsi ba kanwar lasa bane, ba a taba gane shirinsa sai a ranar da ya
tunkare ka domin yaki
Basu bar wajen ba sai da aka tura sako zuwa rum sannan aka
tura sakonne zuwa birane uku da suke makota da su wadanda za su
basu taimakon gaggawa kafin isar sakon zuwa rum. **
Al'amarin Jarumi Jarumi Umar lokacin da suka nufo hanyar
gida kai tsaye batare da jira ko bata lokaci ba, sai gasu a kauyen
Annur cikin annuri akan fuskokinsu, a na cikin zaman yamma na
Majalisi sai gasu sun shigo cikin kauyen. Kowa dake cikin kauyen
sai ya kasance cikin farin ciki ganin jarumi Jarumi Umar da
abokansa sun dawo cikin koshin lafiya batare da an daukowani akan
gadon marasa lafiya ba.
Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya mike tsaye ya fara furta
Shukran ya rabbi, Alhamdullahi, godiya ta tabbata da mai bawa rana
Jarumi Umarni ta fitowa da kuma koma,