Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
Shamnun na sani cewa akwai dana Jarumi Umar da ya je domin ya gano min abin da yake faruwa don tabbatar da gaskiya, ku yi aiki na gaskiya a birnin don wanzar da zaman lafiya, sannan ka rike Jarumi Umar matsayin da kake son ka rike ni domin shi ne abin kallo a yanzu a kabilar mu, mu tamu ta kare muna kan gaba da ta kowacce fuska da makiya ta kowane fuska neman rayuwar mu suke yi, shekaru, a sun saka mu a gaba a kowane lokaci mutuwa na iya riskarmu, daga karshe ina mai sanar da kai ka rike gaskiya da amana, ka kai kukanka wajen ubangijin da ya halicce ka, duk rintsi duk tsanani, tabbas za kasamu babban rabo, zan wuce ina maka fatan Nasara a inda zaka je domin sassancin". "Nagode kwarai, na ji dadin maganarka, Allah ya daukaka musulunci da kasarmu baki daya". "Ameen, Allah ya dawo da kai lafiya, kuma ka bi a sannu, domin duk takunka daya bayansa makiyinka ne ke saka kafa". Daga nan kowa ya juya yana mai jin dadin tattaunawar da suka yi, Abbas ya haye dokinsa, shi ma Abdullahi bin Sharjas ya haye nashi dokins suka tasarwa hanya shi kuwa dan munafukin Waziri Ja'afar sai da ya tabbatar kowa ya baci da gani sannan ya zo ya hau nashi dokin ya sukwane shi bashi ya tsaya ba sai gidan Waziri Ja'afar, ai kuwa Waziri yayi matukar jin dadin hirar da ta wanzu a a tsakanin Yarima da Abdullahi bin Sharjas, ya zo kan gabar da zai ruru wutar gaba a tsakanin yarima da Sarki, ya kuma hada wutar gaba da Abdullahi bin Sharjas har ya ja a kashe Abdullahi bin Sharjas domin alaka da yayan Sarki ita hanya mafi sauki da zaka hallaka makiyinka. Don haka ya ci ka da farin ciki yayi kuma tura bature 54 Page wata Baiwarsa zuwa cikin gidan Sarki don ta kai labaringa Siyama domin itama ta kwana tana farin ciki Washe gari da safe gidan Sarautar Shamnun ta cika ta batse domin an yi sanarwa an kama daya daga cikin dan leken asiri za kuma a gurfanar da shi a rataye shi kamar yadda ake yiwa duk wani mai laifin cin amanar kasa. Saboda haka tun sassafe mutane suke zuwa wannan filin. Mu'az, Dawan, Kubait Saklahul dukkaninsu suna cikin wannan babban fili domin saka ido su ga waye maciyi amanar kasa, duk da zuciyarsa na dukan uku uku idan sun tuna cewar Jarumi Jarumi Umar ne da aka kama suka yank masa wannan hukuncin sai hankalunsu ya tashi har su rasa abin da za su yi, sun saka a ransa matukar Jarumi Jarumi Umar ne ba za su bari hakan ta faru ba, sai sun yamutsa wannan waje yadda sai dai su gaba daya a kama su a kashe su gabadaya. Wajen awa guda ke nan suna tsaye suna jiran ganin abin da suke zargi, sai ga mahaifiyar Sarki ta fito a madadin Sarki wato Sarauniya Ruma, Waziri na beye da ita a baya da zabga zabgan karatan dakaru domin basu kariya, an tanadi wajen zamanta mai kawatarwa. A inda take zaune akwai raga raga yadda babu wani mahaluki da zai iya cutar da ita. Bata jima da zama ba aka fito da Jarumi Umar fuskarsa a rufe kuma an daddaure shi da sasari na bakin karfe ana tunkudo shi dakaru ne suka baibaye shi. ** A tsakiyar fili ga wajen rataya nan a bisa wani babban teburi wadda sai mutane sun daga kawunansu sannan za su iya hango mutum an tsara wannan wajen tun shekaru dari uku da suka shude, tun lokacin da kafurai ke mulkin kasar kafin kasar ta dawo hannun musulmai. bature 55 Page Lokacin da aka gabatar da shi wajen ya rude har wasu da aka biya kudade aka dauki nauyinsu suka fara jefansa da takalmansa wasu da basu san hakikanin meke faruwa ba su ma suka dauki duwatsu da wasu abubuwan kasazanta suna jefansu da shi Tun kafin a cire masa abin fuskar da takalminsa da kafadarsa suka shaida abokinsu ne kuma shugabansu, sai suka fara shiga damuwa domin basu san hanyar da za su bi don yaki da wadanan zaratan dakarun ba, nasihar Abdullahi bin Sharjas a kullum kodayaushe, ka da ka yaki dan uwanka musulmi da takobi, ka yake shi da zuciyarka, da kuma harshenka, iyaka iyawarka, idan kaga zai cutar da kai ka guje shi. Babu abin da Hakimi ya tsana irin yakar juna. Tabbas suka zare makami sai an yi mutuwar kasko kafin su kwaci Jarumi Jarumi Umar, to amma tunda har Jarumi Umar ya gaza aiwatar da komai, dole su yi hakuri da shi dominn yin wani abu a wannan wajen zasu tsinci kansu cikin rashin madafa, tabbas suka kasha rayukan musulmi fushi zai tabbata ga Hakimi kuma za su mutu a matsayin makiya musulunci. Babu abin da ya fi musu a nan face addu'ar fadin "LAHAULAWALA KUWWATA ILLA BILLAHILA ALIYUL AZEEM. Wasu majiya karfi suka tura Jarumi Umar izuwa wajen igiyar, batare da sun bayyana fuskarsa ba suka saka masa igiyar sannan suka tamke ta, suka koma da baya suna jiran Jarumi Umarni Sarauniya Ruma. Duk abin da ake yi idonta na kai, tayi shiru tana kallo bata bada damar a sake shi ba har sai da waziri ya ce "Ranki ya dade muna kara bata lokaci". Sannan ta dawo hayyacinta ta mike ta fuskanci jama'a "Wannan da kuke gani, dan leken asiri ne, masu son haddasawa kasarmu rikici, masu kaunar ganin jininmu na salwanta a banza, mun bature ค kama shi ne da laifin kawo maganar karya da gaskiya akan abin da ba zai haifar mana darashin zaman lafiya ba", saboda haka zamy yanke masa hukunci na kisa bisa rataya". Ta yi shiru mutanen gari suna nuna goyan bayansu da amanna da abin da ta fadi, kai tsaye kuma sai ta daga hannunta sama wadda ta ta sauke za a janye turbin da yake kai ya zama igiyar ta shake wuyansa harya sheka barzaho cikin dakika daya". Abokansa suka dora hannu a ka suka ci gaba da addu'a neman dauki ubangiji a daidai lokacin da Sarauniya Ruma ta sauke hannunta kasa, alamar Jarumi Umarni da cewar a aiwatar. Jarumi Umar addu'o'I yake cikin zuciyarsa wadanda koyowar Annabin Allah ce idan mutum na halin gamuwa da azalumai da A'AUZUBIKALIMATILLAHILTAMMAT masharranta, MINSHARRI MAKALAKA Aka ture wannan turmin Sadauki Jarumi Umar ya fara wutsil wutsil bai fasa addu'a du'a'a a ba cikin zuciyarsa, jin an ture turmin sai ya fara kalimatusshahada. A lokacin da karfin wutsul-wutsul din ya fara ragowa, idanuwansa, sun kunburo ya fara sakin wani kakari na mutuwa, gaba daya idanuwansa sun saki, mutuwa na shawagi a ruhinsa, suma ya gabato a gare shi. Kulli nafsin za'ikatulmaut. Mutane da ke tsaitsaye suna dubansa wasu cikin tausayi wasu cikin tsana abokan tafiyarsa a dai-dai lokacin Mu'az ya kasa jure wa yayi kukan kura ya kwalla kabbar, dukkanin su uku suka zare takubbansu suka dauki kan Jarumi Umar. Dakaru suka sha kanšu suka tare su ana kokari fara dauki ba dadi. Wata kibibiya kamar walkiya ta ta wuce ta saman kawunan mutane daidai igiyar da aka daure Jarumi Umar ta shigar burgu ta yanke ta, kai kace takobi aka saka aka yanke igiyar, Jarumi Umar ya fadi kasa ko shurawa baya yi. bature 56 Page 57 Page Sarauniya Ruma da Waziri suka mike da kallo cikin kaduwa da tunanin waye ya zo ya katse wannan al'amari. Idanuwansu akan Yarima Abbas yana tsaye da kwari a hannunsa idanuwansa na kallon gangar jikin Jarumi Umar. Koda ganin Yarima Abbas sai kowa dake wajen ya rissina kai kasa alamar girmamawa, hatta Waziri da Sarauniya Ruma, sai da suka sunkuyar da kai kasa, cikinsu ya duri ruwa. A Wannan lokacin Mu'az da su Dawan suka yi sauri suka ratsa mutane suka isa kan gawar Jarumi Umar suna masu ihu da kururuwa. Dawan ya fada kansa ya dago shi ya cire masa bakar hular rufe fuska da take sanye akanshi, duk ya hada majina idanuwansa sun yi tulu-tulu kamar zai zazzago. Dawan ya saka hannunsa kan jijiyar wuyansa. Saklahu ya saka a hannunsa, duk su biyu suka fara wata irin fara'a kamar wasu ciwon hauka, "Yana raye yana raye yana raye, haka suka dinga maimaita. Muaz ma hannunsa ya saka ya ji, yana tabbatarwa ya saba shi, a kawo agaji yana daye yana raye. Waziri ya karaso ga Yarima. Yarima bai dube shi ba, idanuwansa na kan Jarumi Umar da ake kokarin ceton rayuwarsa. "Yarima...." دو Yarima ya katse shi da cewa “Ka je ka yi kokarin ceton rayuwar Jarumi Umar kafin ka zo mu yi Magana duk wani likitan da ka san kwararre ne ka neme shi domin ku ceci rayuwarsa. ** "Ki ta shi❞ Wata murya ta tashe ta, a cikin baccin da take cikin dare, ko da ta mike zaune sai ta ga dakin babu kowa,tabbas kuma ta ji an tashe wani haske ta hango daga bakin kofa tana tsayar da hankalina wajen ta hango wata kyakkyawarmace sanye da fararin kaya sannan bature • 58 | Page haske har daukar ido yake, ta mike tsaye budurwa ta ce "Ki zo in sada ki da dan uwanki Salman". Ta fada da daddar muryarta, kafin ta yi mata tambayar budurwa ta yi gaba ita kuma sai ta ji tana mai bin bayanta har suka fita daga cikin daki ta fito waje babu kowa a farfajiyar gidan Hakimi Abdullahi bin Sharjas, abin da ya bata mamaki ke nan. Babu masu tsaron dare bare na safe babu kowa sai kukan tsuntsaye ta so ta gaza bin bayan budurwa amma tazarada ta bata ya sa takeson ta ji me ke tafe da ita. Don haka ta kara sauri dan ta cimma ta. Koda ta ci gaba da binta a baya har suka yi nisa can nesa kadan sai wannan budurwa ta kyakyace da dariyar mugunta. Jin wannan dariya ya sa Gimbiya Suhaila bin Ababakari ta dago da kanta cikin mamaki sai ta ga wajen ya cika da mutane sannan ga wani mutum a gaban rundunar dakaru sama da dubu sun sashi a gaba daure yake da sassarin bakin karfe hannu da kafa, fuskarsa a rufe ba a gane ko waye shi. Tana tsaye ta zuba ido gabanta yana faduwa sai wani mahayin doki mai suffar kafurci ya bayyana a bisa dokinsa yana zagaye wannan mutum da yake a daure, har sai da ya zagaya shi sau uku ana hudu ne ya tsaya ya saka kaifin takobin nasa ya cire wannan hular da ta rufe wa mutumin fuska sai ga Jarumi Jarumi Umar ya bayyana suka yi kallo kallo da shi idanuwansa na zubda hawaye. Ta tawo da gudun don ta zo inda yake amma kafin ta zo wannan Katon Sadauki ya saka takobinsa ya cirewa Jarumi Umar kai, jinin yayi tsartuwa har ya bata mata fuska. Ta kwala wała mahaukaciyar kara mai amsa kuwa da amon. Tana ji tana kallo gangar jikinsa ta sulale kasa, haka kansa yayi katantanwa a gabanta, da ta durkushe a kasa. Kafafuwanta sun kasa daukarta. bature 59 Page "Jarumi Umar Jarumi Umar! Jarumi Umar!! Ta kwala kiran sunansa sau uku. Firgigit ta farka daga bacci mai nauyi ne ya dauke Gimbiya Suhaila bin Ababakari bayan da ta idar da sallar asuba, ta yi sa'ar gaske da ta samu wannan bacci tsawon lokaci da ta dauka bata samu kanta a wannan halin ba, don haka babu ma wadda ya tashe ta ko don ta je ta gana da Abdullahi bin Sharjas domin jiya ya dawo a ciki dare. Ta farka a razane a tunaninta abin da ya faru yana nan a zahiri don hakada gudu ta fita, Kuyangarta Rumaisa, ta riko hannunta, ammaina ta kwace tana za su kashe shi. Tana fita sararin tsakar gidan taga ana ta aiki irin wanda aka saba yau da gobe batare da wani tashin hankali ba. Addu'a ta fara yi tana sauke numfashi kasa kasa. Kubrat dake bada Jarumi Umarni ta lura da ita. Gimbiya Suhaila bin Ababakari tana ci gaba da addu'a har ta samu nutsuwa acikin ranta ta tabbatar da ba gaskiya bane abin da ya faru da ita mafarki take yi. Akwai wata budurwa da bata wuce sa'ar Suhaila bin Ababakari ba, ana mata lakabi da Hamdiya, Hamdiya wato kyakkyawar budurwa ce da ta zama ‘yar riko a hannun Kubra, tun tana da kuruciyarta, yar aminin Abdullahi bin Sharjas ce da ya rasu tun tana karamar yariya, a wata tafiya da suka yi, da shi da matarsa aka farmusu aka kashe su akan hanyarsu ta zuwa Birnin Bahara, don kasuwanci. 5 - Tun daga wannan lokacin Hamdiya take rike a hannun Hakimi Abdullahi bin Sharjas ta zama tamkar ya a wajensa, Hamdiya ta kasance mai matukar kyau da biyayya ga Uwar rikonta Kubra, kuma ta kamu da matsanancin son Jarumi Umar tun tana karama, tana yawan nunawa Jarumi Umar kaunarsa da take yi amma yana nuna mata bai fahimci indata dos aba, saboda shi kwatakwata babu ita a cikin zuciyarsa a matsayin ya so ta da aure amma yana bature 60 Page matukar sonta yana tausayinta a matsayin da yake daukarta na kanwarsa marainiya. = Hamdiya ta fahimci Jarumi Umar sosai sai dai soyayyarsa kullum karuwa take a cikin zuciyarta, duk wacce mace da ta gani ta fita kyau da tsari sai ta ji kishin ya kamata domin tana jin tsoro ace Jarumi Umar ya kama da son wata,a ganinta gwanda a ce da ita da Jarumi Umar sun tsufa a haka basu yi aure ba da dai ta gawata mace ta auri Jarumi Umar, saboda haka tun da ta lura da Gimbiya Suhaila bin Ababakari, ta ga ba tsaranta bace a fagen kyau, sai ta dauke ta tamkar wata kishiyarta, duk da cewar bata ga wata alama da ta nuna suna soyayya da Jarumi Umar ba, amma haka nan take jin haushinta take ji kamar ta shake ta ta mutu. Saboda haka Hamdiya a daidai lokacin da Gimbiya Suhaila bin Ababakarita fito daga dakin da aka sauke su, ita ma tana zaune ta hango fitowarta don haka da suka koma daki Uwar Gida Kubra ta bi bayanta sai ita ma ta tashi ta bi su a baya. Rumaisa ta kasance tana tambayar Gimbiya Suhaila bin Ababakari abin daya faru, ta fara koro mata bayani “Mafarki nayi, wai an kashe Jarumi Umar..... Daidai lokacin da ta furta an kashe Jarumi Umar Kubra ta karaso dakin ta kuma wannan Kalmar. Jikin uwar gida Kubra yayi sanyi ta dubi Suhaila bin Ababakari "Me kika ce?" Suhaila bin Ababakari da Rumaisa suka dago da kai, da Sauri Suhaila bin Ababakari ta kara sa inda take. "Ki gaya min gaskiya mai ya faru, jiya mahaifinsa ya dawo ya min bayanin dangane da halin da Jarumi Umar ke ciki haka dan uwansa, ki daure ki sanar da ni gaskiya". Rumaisa ta ce "Mafarki ta yi Mama". batúre 1 61 Page Ta sanar da ita jikinta a sanyaye Suhaila bin Ababakari ta kama hannuwan Uwar gida Kubra ta ce "Wani mummunan mafarki nayi akan Jarumi Umar?" Nan take ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar da ita. Yanayin yadda hankalin Gimbiya Suhaila bin Ababakari yayi matukar tashi ya sa Kubra take kokarin ta kwantar mata da hankali "Yar ta hankalina ya kwanta da ji kin ce mafarki ne? mafarki ba gaskiya bane, sai dai kuma wata alama ce ta nuni ga wani abun amma akodayaushe muna fatan ganin alkairi akan yaranmu, ki kwantar da hankalinki". Gimbiya Suhaila bin Ababakari ta fara zubar da hawaye ta ce "Mama ina tsoro ace ni ce sanadiyar mutuwar danki, daga zuwa na". Dai dai wannan Kalmar Hamdiya taji a lokacin da ta zo ta labe a kofar dakin. "Jarumi Umar ya mutu! Innalillahi wa inna ilahir raj'un wata kara ta kwala mai firgitarwa wacce hankulansu ya dawo kofar dakin 'Jarumi Umar" Ta kwalla kara mai karfi wacce duk maʼaikata da suke wajen gidan sai da hankulansu ya dawo kanta. Kubra da Rumaisa, gimbiya Suhaila bin Ababakari suka fito suka tarar da ita a matukar rikice "Ke ba alkairi bace" Ta fara nuna Suhaila bin Ababakari, ke masifa ce a cikin birnin mu, Jarumi Umarya mutu ta kashe mana Jarumi Umar”. Mama Kubra ta daka matsa tsawa ta ce "Waye ya gaya miki?, ki nutsu ki shiga hankalinki" amma ina ta kara rikcewa ta na kokarin riko Suhaila bin Ababakari, ai kuwa ta yi sa'ar cafar wuyanta ta shake tana ihun ta kashe Jarumi Umar.da kyar matan da ke wajen suka kwace ta, ta ci gaba da ihu da kururuwa har sai da Kubra ranta yayi mummunan baci ta zabga mari, domin ta shiga hankalinta bature Ta rike kunci cikin tsananin takaici, Uwar gida Kubra ta cc da ita “Me yasa baki yin abu cikin hankalinki nc, waye ya sanar da ke Jarumi Umar ya rasu, a ina kika ji wannan maganar?” Haushi da fushi ya fusata tata ta bar harabar wajen, Gimbiya Suhaila bin Ababakari ta rike wuyanta, Uwar gida Kubra ta ce "Shiga da ita ciki Rumaisa, sannan ta dubi ragowar jama'ar ta ce "Rashin nutsuwa ne da rashin fahimtar Magana irin na Hamdiya, tana gaya min ta yi mummunan mafarki ga Jarumi Umar ne kawai ta ji karshen maganar shi ne ta zo cikin rashin nutsuwa, babu abin da ya faru da Jarumi Umar”. A sannan ne nutsuwa ta zo wa kowa a gidan sannan kowa ya koma ya ci gaba da al'amarin gabansa. Hamdiya ta tafi dakinta ji take zuciyarta ta dauki zafi, ta kasa saita nutsuwarta, a yau ta kara tabbatarwa akwai wata makarkashiya da ke zuciyar Kubra so take ta bada auren Suhaila bin Ababakari gad anta Jarumi Umar, lallai son zuciyar da ake sanar da ita na Uwa Kubra ya tabbata sau tari matar SHAMSU BIN AUJARtana sanar da ita, amma bata taba yadda cewar son zuciya da son abin duniya ne da it aba sai yau. Zuciyarta ta kara kumbura ji take kamar ana turo mata wuta cikin tashin hankali ta yi watsi da wani karamin ma'adanin abubuwanta komai dake kan abin ya waste ta kara rusa kuka mai tsanani ta fada kan shimfidarta. Babu wacce ta isa ta auri Jarumi Umar matukar tana raye, sai ta yi sanadiyar kashe ta, it ace zata auri Jarumi Umar duk rintse idan kuwa bata aure shi ba to kuwa sai dai su rayu a haka, babu wadda zai yi aure. A bangaren dakin da Suhaila bin Ababakari suke Uwar gida Kubra na tsaye a kanta don kwantar mata da hankali "Kiyi hakuri ki bature 62 Page kwantar da hankalinki babu wani abu haka take bata da nutsuwa akan komai kuma zan tsawatar mata". Suhaila bin Ababakari ta dubi uwargida Kubra ta kuma fahimci abin da take kokarin yi na son kwantar mata da hankali ta ce "Ba wani abu Mama, ko ubangijinmu baya kama dan adam da laifin cikin rashin sani, wannan ba komai bane, akwai damuwa sosai rasa jarumi kamar Jarumi Umar a cikin al'umma, na fahimci damuwarta sosai kuma na yafe mata". Uwar gida Kubra ta ce "Kina da zuciya mai kyau, nagode da fahimta, in kin kimtsa idan Hakimi ya fito fadar tsakar gida ki je ki gaida shi". Gimbiya Suhaila bin Ababakari ta jinjina kai alamar zata je. Sannan ne uwa Kubra ta fita daga cikin dakin ta kuma nufi dakin Hamdiya tana kwance tana garzar kuka ta zauna kusa da ita. "Ban san me yake damun zuciyarki kike bijirewa koyarwar mu ba, akodayaushe muna koyar da ku muhimmancin bako a wannan masarauta amma bakya ji, duk ranar da za a yi bakuwa komai girmanta ko matsayinta sai kin nuna mata halinki na rashin kauna, ki saita zuciyarki ki iya mu'amalar kirki da mutane musamman 'yan uwanki mata ace a duk fadin garin nan da wajensa baki da wata kawa ko aminiya, ke kullum cikin rigima kike da 'yan mata, dan Allah ki gyara halayenki ki guje abin da zai sa na kara dora hannu akan fuskarki, kin san ina son ki, ina kaunar ki ko da ba ni ce na tsuggunna na haife ki ba, ina jin matsananciyar damuwar da kike ciki". Idan kina jin damuwar da nake ji da tuni kin tilasta aurena da Jarumi Umar tunda kin sani sarai babu wani mahaluki da nake so in ba shi ba Ta fada a cikin zuciyarta har Kubra ta gama yi mata nasihar ta gaji ta fita ba tace mata ta tafasa ba, jira take ta fita ta bata guri bature 631 64 | Page domin ta fara shirin da zata yi domin kawar da Gimbiya Suhaila bin Ababakari. Aka dauki Jarumi Jarumi Umar zuwa cikin dakin magani cikin sauri da gudu gudu, da fari aka fara da zuba masa ruwa domin ya dawo hayyacinsa, cikin ikon Allah numfashinsa ya dawo a hankali, suka dinga godewa Allah, a hankali ya fara budewa idanuwansa ya ganshi tare da abokansa duk fuskarsu hawaye ne ke kwaranya. Batare da sun lura da ya bude idanuwansa ba, daga can suka ji muryarsa na amsa amo da cewar "Na gaya muku zuwan mutuwa a gare ni ba sauki bace". Suka dube shi cikin farin ciki da annushuwa murmushi yake yana shafa wuyansa saboda zafin da wajen yake masa ga shati sosai wajen yayi jawur. "Su ka hada baki saboda duk wasu lokutan da ya kutsa hadari ya samu ya kubuta irin Kalmar da ya kesanar da su kenan cewar Zuwan mutuwa ba sauke ce a gare nib a, maʼana mutuwa ba za ta zo ta dauke shi cikin sauki ba, sai an sha artabu, wannan addu'arsa ce ta neman yaddar Allah akan yay i mutuwa a cikin abokan gaba yana yaki domin daga Kalmar Allah". Suka rungume shi, har sai da mai saka masa magani ya gama hada maganin sannan suka rabu da jikinsa ya saka masa maganin a wuyansa. F "Me ya faru?" Ya yi musu tambayar a lokacin da ake saka masa magani. Adai-dai wannan lokacin Yarima Abbas ya shigo cikin daki da dakaru na biye da shi. Ya kara so duk suka zuba masa idanu, har ya kara so kusa da Jarumi Umar ya zauna ya mika masa hannu domin su bature 65 Page yi musabaha Jarumi Umar ya dube shi da mamaki ya ce "Ranka ya dade" Bai dauki hannun ba ya kara jinjina kai ga Jarumi Umar domin ya aminta su gaisa. Jarumi Umar ya mika masa hannu cikin girmamawa shi ma yarima ya amsa yana mai cewa "Mahaifinka ya sanar da ni cewar nayi kokari na kubutar da kai daga sarkakiyar dake cikin kasar nan. Lallai Allah ya nufa da kwanan ka a gaba”. Jarumi Umar ya dube abokansa alamun tambaya domin bai san cewar yarima ne ya cece shi ba, suka daga masa kai alamar tabbatarwa. Jarumi Jarumi Umar ya jinjina kai “Ina godiya ranka ya dade, ya mahaifina yake dafatan yana cikin koshin lafiya?" "Yanzu haka ya koma gida tun jiya mun rabu da shi, kuma ya san da cewar kana cikin hadari tun da ya fuskanci Waziri Ja'afar ya san cewar ka taho birnin don haka da zan zo nan ya bani amanarka, nagode wa Allah da ya sa na riske ka a kan lokaci. Yanzu abin da nake da bukata da kai ka kwanta ka samu hutawa, duk wani abu da za a zartar da shi ko fahimta a birnnin Shamnun yana gare ni, kuma zan aiwatar da shi bisa yaddar Allah, wannan nauyin mahaifina ya dora min kuma shi ne gwaji na farko daga samun nagartar sarauta ta”. Yarima Abbas ya mike tsaye cikin sauri ya juya ya fita tare da dakarunsa ya barsu a tsaye anan. Kai tsaye ya shiga bangaren sarautar gidan. Bai tsaye ko ina ba sai karagar mulkin gasar Shamnun. Babbar fada da ce da aka kawatata da gini na alfarma waje ne mai girman gaske, da yake mallaki ne na Rum, a shekaru masu yawa kafin yaki sarkin wancan zamani a dawo da ita karkashin ikon musulmi sun yi matuka batar da dukiya da basira wajen gina wannan fadar can nesa kujerar mulki take, sannan daga hagu da dama akwai kujerun alfarma na waziri dakuma Babban Dakaren birnin sannan ga bature 66 Page 'yan majalisar sarki su ma kujerunsu da aka kerata da zallan zinare a shimfide sahu sahu a gaban kujerar Sarki. Kai tsaye Yarima ya je bakin kujerar mulki ya zagaye ta wajen sau uku kafin ya samu wajen zama. Ya zauna sosai yana kallon kofar shigowa wacce take kallon saitin kujera bai dauke idanuwansa daga wajen ba har sai da Yarima Hilal da kuma Waziri suka shigo cikin fadar. Ganinsa a kan karagar mulki duk hankulansu ya ta shi ainun suka tsorata matuka. Ba wani abin tsoro bane domin wani mai babban matsayi ya zo karamar masarauta ya zauna a kujerar mulki hakan dama yana faruwa, idan Sarki Muhammad farsi zai je kowacce kasa da take karkashinsa shi ne zai gudanar da komai har ya bar kasar, amma abin da yasa suka tsora a wannan lokaci suna jin cewar Sarki Muhammad farsi ya aiko dansa Yarima Abbas ne domin ya kwace masarauta a datseta, har sai an kamala bincike wadda hakan idan ya faru, babu shakka sai sun rasa kujerar mulkinsu, domin za a iya dauko wasu daga cikin jinin sarautar a basu tun da sun kasa daidaita kansu. Waziri Adnan ya kara so cikin sunkuyar da kai kasa shima Yarima Hilal. 'Ranka dade ina mai maka maraba da zuwa birnin Shamnun". Yarima ya kalle shi cikin nutsuwa. Ya mayar da kansa kan Yarima Hilal Yarimaya dube shi a dari dari “Barka da zuwa dan uwana Yarima Abbas". Yarima Abba yace "Na zo takasanas daga Babban birnin zuwa birnin Shamnur domin aiki mafi muhimmanci a gare ni, na zo domin na fitar da gaskiya na kori karya, kuma nayi alkawari ba zan bar birnin ban sai na tabbatar da adalci, na kuma danka mulki ga wadda ya cancanta. Yanzu mene ne laifin Jarumi Umar da kuka yi kokari kashe shi? Shin baku san waye shi bane?" bature 67 Page Waziri ya dago da kai a tsorace ya ce "Ranka ya dade ba mu san wane ne shi ba". "Shin bai sanar da ku ba?" Waziri yayi shiru har sai da Yarima Abbas ya kara maimaita tambayar, sannan ne Waziri Adnan ya ce "Ya sanar damu amma saboda halin da muke ciki na bukatar Yarima Salman da tsoron shirin da zai zo mana da shi ya sa muka yi tunanin karya ya shiryo mana don ya samu ya kawo mana sharri cikin masarauta”. Yarima Abbas ya jinjina kai “Wane bincike kukayi domin ku tabbatar da hakikanin gaskiyarsa ko akasin haka?" Waziri Adnan yayi shiru domin bai da tacewa "Mun

Chapter 5 of 9