Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
ubangiji mutane da Aljanu mai iko akan kowa da komai, masha Allahu ya rabbi. Lokacin da Jarumi Umar ya karaso ya sauka daga kan dokinsa kai tsaye ya nufi mahaifinsa, ya gaida dattijan fada sannan ya matsa ga mahaifinsa, duk abin da ya faru ya sanar da shi, tun daga bature 81 Page kan tafiyasu zuwa Birnin SHamnun har zuwa lokacin da aka yi kokarin rataye shi, har zuwa da Yarima Abbas ya zo ya kubutar da shi har ma da yadda Abbas din ya gudanar da bincike har ya zartar da hukuncin da yake da ikon yin. Dukkanin jama'ar fadar sun jinjinawa Yarima Abbas kuma sun yi murna da ya zamo aikinsa na farko na matsayin Yarima nuna halin girma da kuma nuna cewarshi jagaba ne mai adalci. Gimbiya Suhaila bin Ababakari na nesa tana hango Jarumi Jarumi Umar jira take yi kawai ya baro fada ya zo wuce wa zai shiga gidata tare shi ta yi masa Magana don jin abin da ke faruwa, aikuwa cikin ikon Allah bisa mamakinta sai ta ga ya yi sallamada manyan fadar Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya nufo hanyar da zata sada shi ga cikin gida. Dukkanin abokansa sun tafi na su sashin da sauri ta nufe shi. Kwatsam ya ganta a gabansa tare da zakuwa a cikin ranta Ya sakar mata murmushi mai taushi, hade da jin kwarin gwiwa samar mata da farin ciki na bata daddan labari. "Dan uwanki yayi nasara zama sarki”. Nan take ta durkusa kasa ta yi sujjadar shukra ta dago tana yiwa Allah kirari da sunayensa tsarkaka kallonta kawai ya tsaya yake yii yana wannan murmushi wadda shi kansa bai san yana yinsu. Sai da ta kamala sannan ta dago ta ce "Da me zan saka maka ya kai Jarumi Umar". Ji ya yi kamar yace wani abu amma sai ya dauke idanuwansa da barin kallonta domin ya fara yi mata wani kallo wadda shi da kansa ya fahimci ya wuce gona da iri ba wacce suka yi sabon da zai mata wannan kallon bace domin a tsakaninsu kawai taimako ne”. "Da ni da ke duk mu godewa Allah mu kuma godewa masarautar Bahara, da yarima Abbas, ban da zuwan da yayi a kan lokaci da tuni na rasa rayuwata". bature Ta kara fadada murmushinta "Kai ne kataimake ni daga fadawa tarkon kafure, ka kubutar da ni daga hannunsu, ka tseratar da rikicin da zai hadu tsakanin kasashen musulunci. Kai ne ka sayar da rank aka tafi kasar da ake neman mai goyan bayanmu, domin su hallaka shi, kai ne ka cancanci yabo da godiya a gare ni, ina mai kara gode maka, kuma watarana zan rama maka wannan halacci" Bai san Gimbiya Suhaila bin Ababakari na da matukar kyau irin na yau ba, sai da ta kasance cikin nishadi tana dariya, koda yake murmushi shi ke tona asirin kyawun dan adam, saboda haka ya zama wani saakarai wajen kallon kyawun fuskarta, har sai da ta tsayar da kallonta a kanshi ta fuskanci yadda yake kallonta, ya dimauce ya kasa samun yadda zai sarrafa kansa har sai da ta dan jima itama tana kallonsa a ranta ta ce Jarumi Jarumi Umar shi ne namijin da take buri ta samu a matsayin mijia gareta yana da zati irin na mazajen gaske dirin jikinsa ya amsa, yanayin jarumtarsa abin burgewa, shine mijin da zai iya kare iyalinsa daga dukkan karfinsa, yana da kirki da kunya kamar yadda take da buri, shi kansa ya manta da yanayin da yake ciki, kwakwalwarsa mai saurin kawomasa shawarwari ta fara shawartarsa a game da wani abu dangane da gimbiya Suhaila bin Ababakari, amma bangaren zuciya mara karfin gwiwa na bashi labarin matsayinta da na sa matsayin wannan tunanin ya dawo masa da mafarkin da yake kokarin dorawa ransa. "Dan uwana rabin raina”. Muryar Hamdiya ya karade kunnuwansu kuma ya dawo dasu cikin hayyacinsu, cikin rashin gaskiyar da gimbiya take ciki na tunani dole Hamdiya ta fuskanci abin da ke wakana don haka ta yi sim-sim ta bar wajen. Ya dubi Hamdiya, da take kokari yi masa Magana "Ban san me yasa kake son ka bada rayuwarka ga mutunen da basu da amfani a gare k aba, dan uwa na sha kukan rashinka". bature 82 Page 83 Page Ya dube ta duba na mamaki "Ban fahimta ba,su waye basu da marasa amfani a rayuwata?" Ta juya ta dubi Gimbya da takekokarin shiga cikin gida shi maya kalle ta tare da suka dawo da dubansu ga juna ya riga ta Magana ya san abin da take son sanar da shi “Kin ga Hamdiya rayuwarta ta kowane dan adamce matukar ya bada gaskiya ga ubangijin talikai, babu wani dan adam da za a zalunta ina kallo batare da na taimakeshi ba, ina so ki koyi hana kanki shiga cikin lamurana, ki zauna a matsayinki na 'yar uwata, ki koya wa ranki sanin cewa ban taba fita daga gida da saka san cewa lallai zan dawo na same ku ba, saboda haka ban saka ki lalubamin mutanen da suke da muhimmanci ko wadanda basu da shi a cikin lamurana". Yana fadin haka ya bar wajen ya bata waje tana kallonsa kamar ta fasa ihu don takaici. ** Sarki Muhammad farsi Farsi shugaban kafatanin nahiyar larabawa a zamaninsa, yana zaune cikin kulawar matarsa Siyama tana shayar da shi kayan alatu a kyakkyawan lambon gidansa suna taba hira sama sama, ta lura da akwai tarin damuwa ga Mijinta Muhammad Farsi, don haka sai ta fara tunanin ta yadda za ta shawo kansa ya sanar da ita damuwarsa, saboda ita ya nuna mata kaguwa da son sanin damuwarsa zai iya share ta, ta kawo maganar barin 'ya'yansa birnin don zuwa cika aikinsa, ta fahimci damuwarsa ba ta wannan bangaren bane, saboda haka sai ta tuna da zuwan Abdullahi bin bin Sharjas da ya zo garin yau kwana uku da suka wuce don haka sai ta fahimci lallai akwai wani abu dangane da zuwan nasa a cikin bacin ran Sarki, ta yi nisa ta mika masa wani karamin kofi da yake cike da tataccen ruwan inibi, bayan ya amsa ta ce "Zuwan Abdullahi bature 841 Page bin Sharjas birnin nan ya zo da batutuwa da dama, a game da zargin Waziri Ja'afar, ya sarkin duniya mai kake tunani game da lamarin?" Kamar ta sosa masa inda yake masa kaikayi, ya kurbi lemon ya mika mata kofin ta amsa ta ajiye a gefe sannan ya ce "Rashin walwalar da nake ciki ta rashin jin dadin jikina a shekaru biyu baya zuwa yanzu, na kasa katabus a harkokin mulki na ya fara taba min martaba da kima, da yawan mutane suna tunanin na gaza yin riko da adalci, suna min ganin na gaza samar da ci gaban musulunci, ina damuwa matuka da wanzuwar lamarin da suke zuwa kunnuwana ina takaici da abu guda, makusanta na basa iya fayyace min duk abin da yake yawo a birnin bare koma sauran kasashen da muke mulka, har sakacina ya kai ga mutuwar ga ‘ya'yan Sarki dan uwana suna kokarin kashe junansu a kan mulkin masarautar da muka danka musu batare da sun zo don a yi musu sulhu ba, mene ne amfanin waziri Ja'afar da ya zamo wakilina akan komai, mene ne amfani shugaban dakarun na birni da kauyekan wannan birni har ace kafurai za su kafa wata rashin gaskiya su aiwatar a cikin kasuwar da afarma mukayi musu suke zuwa su yi saye hajojinmu, mun yi cece kuce da Hakiman Kauye akan basa bukatar shigowar kafurai amma mun danne su da karfin mulki saboda muna musu fatan samun tagomashi daga ababen da suke sana'antarwa, kuma ga ni a raye ban mutu ba, mene ne yake damuna ne? ba cuta nake yi kamar ajali ba, mene ne yake sakani na zama kamar sakarai". "Ranka ya dade". Ta tare shi da murya mai cike da shagwaba, yanga jan hankali da kuma kwantar da hankalin ma'abocin saurare, ya tsayar da kansa ^ a kanta a nutse yana son ta ce wani abu. "Ranka ya dade" ta kara maimaita cikin sigar muryar jan hankali “Ka yanke wani hukunci wadda ya yi min dadin ji a zaman fada na ranakun da suka gabata, cewar ‘ya'yanka duka za su fara shiga sabgogin mulkinka kai tsaye bature 85 Page na tabbata jininka ba zai yaudare ka ko gaza wa da abin da ka umarce sub a, batu akan Waziri shi ne karfinsa bai zamo kamar na Sarki ba, amma karfin da ke hannu yaranka tamkar naka karfin don haka ka yanke hukunci mai kyau, sannan kuma na san tun daga yau in sun iso za mu samu kyakkyawan labari”. Ya dan yadda da maganar ta, amma dai ya kalli kansa "Me na rasa ni da ba zan yi da kaina ba mene ne damuwa ta, lallai zan canza mai duba lafiyata". Gabanta ya yanke ya fadi domin hakan na daf da tonowar asirinta ta ce "Kana zargin wani abu ne?" "Bana zargin Mustafha da komai face tsufa da kuma kamar bai da kwarewa a game da abin da ke damuna tunda ba cuta nakeyi ta rashin lafiya ba, cut ace ta rashin sukuni, karfin gwiwaa, karsashi shiga kowane sha'ani batare da gajiyawa ba". Jikinta yayi sanyi tabbas ta gaddame masa yana dab da zargin wani abu, don haka sai ta karkace ta gyara zamanta ta kalle shi “Idan dama taki sai koma hagu maganarka gaskiya ce, fatanmu ka kasance cikin karsashi kamar koda yaushe?" Tana fadin haka yayi shiru idanuwansa na kallon guri guda, gaba daya hankalinta ya bar wajen jira take yi kawai Zulehat ko Hauletu su karaso cikin lambu ta mike dan zuwa ta sa a yi mata kiran Mustafa ta kuma gana da waziri. 'Yarsa ce Gimbiya Zahra, ta nufo lambon cikin ado barori biyu na taki mata baya, tsawon nisan tafiya taku gomasha biyu da inda Sarki yake barorin suka tsaya gami da sunkuyar da kawunansu kar, don kada su kalli inda Sarki yake, daga nan ne Gimbiya Zahra ta ci gaba da tafiya har ta iso wajen da ake tanadarwa mahaifinta dan hutuwa da yammaci sakaliya. Gimbiya Zahra ta sunkuyar da kai kasa ta yi gaisuwa ga mahaifinta, ya amsa mata cikin murmushi da nuna mata waje kusa da shi ya ce "Zo ki zauna”. bature 86 Page Ta tafi cikin ladabi ta samu wajen zama ta zauna daf da ashi ya dafa bayan "Ya Zahra ta, kyakkyawar diya ta, mene ne damuwarki?" Ta yi murmushi ta kalli Sarauniya Siyama dake a takure waje guda duk hankalinta ya dagule ta rasa mene ne abin da zata yi don magance matsalar da za a jefa su ciki. Ta tuna wasu lokutan can baya a lokacin da Likitan Sarki Mustafa ya fito daga sashin sarki yana kokarin duk damuwa ta dame shi adai-dai lokaci Siyama ta biyo bayansa bayan ta fuskanci ya fahimci abin da yake damun Sarki yaki yin Magana ne saboda bai san yadda maganar zata zama a cikin gidan ka iya yiwuwa ya yi laifin da zai ja masa kisa, ko wani dauren saboda babu wani likita amintacce da Sarki ya yadda da shi kamar Mustafa. ta yi sauri ta sha gabansa a lokacin da ta lura da babu mai ganinsu, su ka yi ido biyu gege domin da Mustafa. Mustafa yana muzurai yana kallon gefe da kadaice da matan Sarki matukar ba dakin gani ba haramun ne kuma kisa ne a kanka saboda hakan sai hankalinsa ya tashi. "Kwantar da hankalinka babu wani da zai gan mu”. Ya dube ta da alamun tambaya ta riga shi kara wata maganar "Akwai wani abu dangane da ciwon Sarki me yake faruwa?" Ya fara nuku-nuku ta daka masa tsawa "Ka fada min me ka fuskanta?" Babu yadda zai yi yace "Aikin sihiri ne, da aka yi amfani da shi a bargon da karkashin matashin kansa tsawon lokaci su ne suka haifar masa da ciwonsa, daga kwakwala zuwa karfin jiki, sihiri ne mai karfe da ya kashe masa karfin jiki ya kuma kashe masa karfin ^ nazari da hangen nesa". R Ta dube shi tana nazarinsa domin tana da sakon da zata bashi "Me kake tunanin aikatawa yanzu ina nufin me za a yiwa Sarki da zai samu lafiya”. bature 87 Page "Ina son sanar da likita kuma sirikinsa bin Abbas ne domin shi ne likita mafi rinjaye kuma yana aikin sihiri don haka shi ne kadai zai iya da wannan al'amari da izinin Allah". "Ibn Abbas, to ahir, ka da ka kuskura ka kawo wani cikin gidan nan domin kula da Mai martaba kai ne za ka ci gaba da kulawa da shi". Ya dubeta yana son yi mata cikakken bayani bayan ya hadiye wani yawo ya ce “Bani da kwarewar da zan iya magance matsaalar Sarki ranki ya dade, matukar ana son Sarki ya samu lafiya dole ne sai mun yi amfani da jarraba malamai wadanda suke da ilimi wajen yakar sihiri, wannan yana ci masa jiki zuciya da kwakwalwa za ta iya kai Sarki ya rasa hankalinsa wata rana ko kuma ya karfin lakar jikinsa ta daina amfani, hakan zai iya sawa a rasa Sarki". Ta Harare shi "Matukar ka sanar da wani wannan al'amari abin da kake tsoro shi zai faru gare ka, domin zan maka sharrin kai ne ka hadawa Sarki wannan sihirin idan kuma ka hakura ka ci gaba da bashi taimako zan saka maka da mafificin alkairi ko bayan babu rayuwar Sarki z aka ci gaba da kulawa da na Yarima Yazid. Cikin rudani da tashin dade?" hakali ya ce "Me kike nufi ranki ya "Ba sauri nake yi ba, na baka lokacin yin nazari da tunani, sakamakon bijirewa za a dauki rayuwarka kacokan daga duk ranar da ka yi tunanin sanarwa wani, duk sahun da zaka taka mutanenmu na bibiyar lamarinka dan haka tunaninka da yankewa hukuncinka a hannunmu yake" Tana fadin haka ta nuna masa hanya domin ya ci gaba da tafiya, sannu a hankali da sanyin jiki ya bar wajen.. Ta dawo daga wannan tunanin da ta yi hakan ya sa ta yi karfinhali mikewa domin fita daga lambon Sarki. “Ranka ya dade, bari na barka ‘yarka”. bature 88 | Page Batare da yayi mata Magana kai kawai ya jinjina mata ta mike ta fita barorinta na bakin hanya suka bi bayanta don mata rakiya cikin gida. "Baba tun da ka zama babu lafiya horar dani a matsayin jaruma ya tsaya, babu mai kula ni ko Yaya Yazid ko Abbas". “Uhmm shine damuwar, rabu da su kin ji farin cikin idanuwana, zan samo likita ingantacce domin kulamin da lafiyata, ko don na ci gaba da baki horo, ai na gaya miki za mu tafi yaki tare kina bisa doki da takobi a hannunki kina wulwalata sama kina cire kan munafukan Allah ta Allah' "Da gaske Baba?" "Sosai". Ta yi shiru tana wani tunani “Naji Mama ta ce ciwonka Sihiri ne ba cuta ce daga Allah ba kirkirarta aka yi”. "Me kika ce?" Ta kalle shi "Na ji suna hira da Hindu, ta ce tana yi maka magani a boye batare da sanin kowa ba, tana addu'a tana tofa maka duk ranar da ta kasance kana tare da ita, a turakarka". Maganar ta dake zuciyarsa sai da har ya samu wani lokaci sannan ya dawo hayyacinsa ya dubi Zahra ya ce "Na gaji da zama ki rike hannayena mu koma ciki, ga magriba nan ta karato”. Lokacin da sarauniya Siyama ta koma dakinta sai ta samu kuyanganta abokiyar sirrinta ta kut da kut ta zauna ta rubuta sako zuwa ga Waziri na bukatar son ganinsa cikin gaggawa da bayanin a takaice abin da ya sa ta ke son haduwar ta su saboda kada yayi kasala. Da fitar wannan hadimar tata kuwa sai ga wata yar sako daga shugaban masu aikin gidan zuwa gare ta. Ta shigo falon ta fadi ta yi gaisuwar ban girma gami da cewa "Yarima Yazid ya dawo, yana kwance a dakinsa". bȧture 89 Page Ta zaro ido cikin tsoro da fargaba "Me ya same shi me ya faru da shi? Bata jira jin ba'asi ba ta riga wannan yar sakon fita daga dakin ta fice zuwa sashin 'ya'yan Sarki maza ta wata karamar kofa wacce ita take sadaka da bangarensu, kuma bisa al'ada babu wadda yake shiga ta kofar sai Yarima shi ma sai yayi izini an kuma amshi izinin nasa am bashi dama, iyayensu da 'yan uwansa mata na iya kai musu ziyara duk lokacin da suka so, ta isa falonsa a lokacin yana kishingide a kan gadonsa na alfarmababu riga a jikinsa ga hannunsa an daure masa da wani farin kyalle" da sauri ta kara sa "Dana Yarima, me ya faru da kai?" Ta kama hannun tana kallo "Ba wani abu bane yanka ne kar ki damu?" "Me ya faru kagaya min wasu ne suka tare ku?" "Shugaban dakarun Benjamin.. amma kar ki damu na bishi na dasa masa ciwon da ya fi karfin wadda ya dasa min akwai katon yanka a cikinsa?" Tana kallonsa tana saurarensa cikin rashin fahimta "She Benjamin ya iya yi maka wannan raunin a wane dalili kar ka bata komai dana Sarki yana tura ku ne domin ku je ku gwada fasaharku ta iya siyasa da da yadda za ku iya kwantar da kai ku samu nasara wajen makiyanku, idan ya tura ku yaki, yana so ku je ku nuna tsantsar jarumta ta damatsa, da karfintakobi, ammaa duk sanda ya tura ku sulhu sulhun nan kadai yake bukata, ba yaki, me ka je ka aikata ya kai dana". Ya girgiza kai yana ciccije baki “Mama nasani, ki kwantar da hankalinki, ba yaki nay i ba, Benjamin yayi haka ne domin ya turo sako zuwa ga Sarki, don ganin sun shirya yaki Mama, sun daina shakkar masarautarmu, saboda baba ya gaza tabuka komai, lokaci yayi da Baba zai dauki kujerar mulkinsa ya dankamin domin kada martabar kasarmu da Kalmar Allah ta yi kasa a wannan nahiyar bature 90 Page kasashen da suke tsoron koda inuwarmu yanzu suna iya fito na fito da mu kaico" "Ka tafka kuskure Yazid ka tafka kuskure wannan nakasu ne wannan nakusu ne,me ya faru". Duk abin da ya faru ya sanar da ita ta kama girgiza kai "Kayi kuskure, wannan labarin ba zai je kunnen Sarki ba, dole a rufe baki a kan maganar fadanka da Benjamin za mu basu labarin saranka da yayi ne kadai a kafada". "Ba ni da ko shakka ban yi wani abu a bisa kuskure ba, nay i abu ne domin nuna karfin ran jinin musulmi Benjamin yana daukar cewa shi zarra ne, na kuma ladaftar da shi na nuna masa ruwa ba sa'an Kwando bane, ki kwantar da hankalinki babu wani abu da zai sauya". Ta ci gaba da girgiza kai “Baka san komai a kai ba Yazid, baka san mene ne burin da manufar mahaifinka ba, tura ka gwaji da yayi kai da dan uwanka yana son ya auna tunaninku da kuma hikimarku ne, idan Abbas yayi nasara ba z aka taba zamowa Sarki ba, domin Sarki zai bada sunan Yazid". Yayi shiru yana kallonta "Mene ne idan Abbas ya zama Sarki ni ban zama ba, me kike shakka da shayi, Abbas kani na ne, ina alfahari da shi, idan har fi ni cancanta zamowa Sarki zan goya masa baya kamar yadda shi ma na san idan na fishi cancanta zai goya min baya". "Baka da wayu baka san abin da kake yi ba Yazid, idan har Abbas ya zama Sarki zai tarwatsa komai namu, zai salwantar da ruhin duk wani dana a doron kasa?" "A wacce hujjar, da dalili, waye ya gaya miki wannan Mama ki guje maganganun irin wadannan domin rayuwarki zata zama gajera, 'ya'ya Sarki Muhammad ne jikokin Farsi masu Sarauta daular musulunci, tarbiya da kaunar juna a jinin jikinmu, take, matukar bature 91 | Page bamu zalunci dan uwanmu ko nuna masa rashin goyan baya, ko fitowa mu yake shi ba na tabbata zai ba mu kariya zai kuma daga darajarmu". Ya koma ya kwanta tayi suroro tana dubansa wannan lamari shi ke tayar mata da hankali bata da wata mafita illa ta fice daga dakin zuwa ga jin ba'asi dangane da sakonta data aika. Lokacin da Sarki Muhammad ya isa fadarsa sai ya yi wata irin shiga ta irin attajirai ba sarakai ba, ba tare da kowa ya sani ba ya fice ta kofar da ya saba fita in zai yi irin wannan fitar ta basaja. Kai tsaye gidan Imam Muslim ya isa, tunda ya lura mutane na fitowa daga dakin da yake bata karatu sai ya tunkari cikin dakin karatun. Yana zaune a durksuhe da dalibai a gabansa sun tsirawa guri guda ido inda yake musu bayanin game da addini, kai tsaye ya samu wajen ya zauna a ka zagaye malam da shi batare da kowa ya fahimci wane ne ba" "Ilimi wajebi ne ga musulmi, domin da ilimi kadai ne zaka fahimci wane ne addininka wane ne mahaliccinka, sannan zaka fahimci wanene shugaban halitta, idan hark a bar kanka babu ilimi lokaci zai zo da za a yi ta sabawa koyarwar ma'aiki domin kawo rudu daga cikin addininmu, ga ka musulmi a riga amma kafuri a zuciya, abin da zai kawo maka kariya daga wannan gubar ka san Allah kuma ka san Manzanninsa, Annabi Isa (Alaihil salam) bawan Allah ne, kuma manzon sa ne, wadda Allah ya turo domin isar da sakonsa, ya isar sun kashe shi, daga bisani an sauya labarin me ya faru, shine suke bautawa a matsayin Allah, wannan aikin shirka ne, darasi ne a gare mu, da muka zamo a cikin al'ummar Annabi mafi girman daraja a wajen Allah, akwai mushirikai da suka juya wancan lamarin ya koma Allah, ba za su yi kasa a gwiwa ba za su yi ta kafa siradi har duniya ta nade ba za su fasa ba, za su dinga danganta Allah da Annabinsa, wasu za su yi kokarin canza labarin to amma ilimi bature kadai ne zai zame mana mafi amfani a rayuwarmu da ta al'ummar nan gaba". A nan ne malam ya dago kai yana duban dalibansa ya zurawa mutumin da ya zauna ido bai ganeshi ba har sai da ya dago kai sukayi ido biyu da Sarki Muhammad Sarki Muhammad ya yiwa SHehul Islam alamun yayi shiru ya ci gaba. Wani daga cikin dalibai ya ce "Ya shehul Islam an ce Ka bautawa Allah shi kadai ka roke shi biyan dukkanin bukata ba za iya rokon Annabin Allah ba kenan?” “Shehul islam yayi murmushi ya ce "Allah da bakinsa ya furta cewa (Ihdinalsiradalmustakin) babu wani wadda za ka roka biyan bukata face Allah babu wani da zaka bautawa face Allah, shirka ce ka hada Allah da wani. An je ma'aikin Allah yana fushi da hani akan hakan, ya shaida mana cewa shi manzon Allah ne wato dan aikin Allah ne, Allah mabuwayi yayi bayani a al'kur'ani game da zuwan Annabi Muhammad,ya gaya mana fifikonsa da sauran Annabawa, shi ne Annabi mafi daraja yi masa karya, kafirci ne, bare kuma ka bauta masa ko ka hada shi da Allah". Wannan mutumin yayi shiru ya ce "Malam ni daga Dusara nake tafe yau kwana nan arba'in a Birnin Bahara, kuma ina yawaita zuwa karatunka, duk inda na ji ana wa’azi na kan tsaya na saurara, na ci karo da wani malami a dusara yana mai fadin “Idan har baka hada rokon Allah da sunayen Annabi ba, to addu'arka ba za ta taba karbuwa ba?" Malam ya dube shi ya ce "Kamar yaya?" "Ya ce Sai dole Annabi Muhammad (SAW) ya amsa sannan Allah zai amsa." " ?" Malam ya furta kai tsaye ya ci gaba da cewa "Annabi Muhammad (SAW) shi ne mafificin manzon a cikin Annabawan bature 92 Page 93 Page Allah kuma shi ne mafi daraja. Saba masa sabawa Allah ne, a cikin saba masa kuma akwai masu yi masa kage, duk wadda ya yiwa Annabi kagi ya kafirta, duk wadda ya bautawa wani ba Allah baya kafirta, Ka so annabi mafi kololuwar soyayya ka bi dukkanin umarninsa a cikin umarninsa ba za ka ci karo da shirya ko wani abu da zai sabawa al'kur'ani saboda haka karya suke shi yasa nake sanar da ku ku yi karatu, a cikin ilimi ne kadai za ku karkade wannan datti, domin abubuwa suna da yawa wadanda suka nuna karya ce karara ake yi masa wannan ya ta faruwa bayan wafatinsa, za mu samu lokaci da daliban ilimi masu zuwa garuruwa don wa'azantarwa da da'awa domin su fara yaki da irin wadannan muggun 'yan ta'adda acikin addinin musulunci Insha" ya dan yi shiru yana duban jama'a daga bisani ya ce "Za ku iya tafiya sai bayan magriba za mu dora”. Bayan kowa ya watse a masallacin jikin gidan Shehul Islam, Shehul Islam ya ce "Ranka ya dade kai ne da kanka cikin wannan badda kama?" Sarki Muhammad yayi shiru yana kallon Shehul Islam har Shehul Islam yayi tsammanin akwai abin da Sarki yake nazari akansa har yayi shirin yi masa Magana sai Sarki Muhammad ya ce "Ya kai Shehul Islam, na zo gare ka ne domin ka gaya min gaskiya, ka kuma gaya min laifukana da Hakimi Nur ne kadai ke iya tunkara ta ya sanar da ni, a fadin duniya, na san ina da matsaloli da suke yawo a cikin hakimai na, suna tattaunawa a junansu, talakawana suna tattaunawa a junansu Sarakai suna tattaunawa a junansu, amma matsalar da nake da ita ana tsoron tunkara ta da ita,wacce koma baya nakai birnin Bahara, wane ci gaba na kai Birnin Bahara?" Koda Shehul Islam ya ji wannan batu sai ya dago da kai ya dubi Sarki ya ce "Ranka ya dade, na ganka cikin shiga ta badda kama, ko zan iya mikewa mu tashi mu shiga gari mu zagaya majalisu na talakawa, mu shiga kasuwa mu ji kukensu?" bature 94 Page Sarki Muhammad ya ce "Ba ni da karfin jiki domin yanayin jikina amma zan jure ka shirya mu je?" Ba tare da bata lokaci ba Shehul Islam ya mike gami da zuwa cikin gida yayi shiri yadda ba kowa zai gane shi ba, ya fito ya samu sarki suka kama hanya a dawakai suna tafiya suna tattaunawa a cikin tafiyarsu ne aka zo wani majalisi inda wasu dattawa suke zaune suna hirarrakin yau da gobe da alamun makotan juna ne, Sai Shehul Islam ya ce "Mu ziyarci wancan majalisi ko za mu iski wani labarin sarautar birnin daga gare su ** Lokacin da Umar bin Abdallah ya fito daga cikin gida domin yin shirinsa na fita zagayen jeji kamar yadda suka saba shi da abokansa a kowacce yammaci suna zuwa

Chapter 7 of 9