da shi ya Sarkin duniya”.
Sarki ya nuna inda ake tsayuwa a yi bayani don Wazirin ya
fito yayi bayanin kare kai. Batare da bata lokaci ba ya fito ya tsaya a
gaban Sarki nesa da juna inda kowa zai saurare shi ya ce "Daga
birnin Shamnun sako ya zo gare ni cewar Gimbiya Suhaila bin
Ababakari ta gudu daga masarautar Shamnun, saboda haka Sarki mai
jiran gado Hilal maijiran gado ya bada Jarumi Umarni a kamo ta duk
inda take, wannan labari ya iso min daga masarautar Shamnun cewar
an nemi Gimbiya an rasa, dalili ke nan da na ji labarin cewar an
bature
40 Page
ganta a wajen Hakimi Abdullahi bin Sharjas, shi ne bai yi kasa a
gwiwa ba na isa wajensa domin na gasgata”.
Yadda Waziri ke maganar cikin ladabi da nuna tsantsar
gaskiyarsa.
Sarki Muhammad farsi ya jinjina sannan ya dubi Abdullahi
bin Sharjas ya ce “Kaji bayaninsa, kuma shine na wakilta game da
masarautar Shamnun, ka ga yana da ikon sanin komai”.
Da Sarki ya gama wannan jawabin sai ya kara duba ga Waziri
Ja'far ya ce "Me yasa Salman ya gudu ya bar Shamnun, me yasa
Gimbiya Suhaila bin Ababakari tashiga hannun Arnan, me yasa baka
zo min da labarin yanayin da birnin Shamnun ke ciki ba domin a
yiwa 'ya'yan Sarki Sulhu?"
Waziri Ja'afar ya hadiye wani yawo yace "Amsar farko
Yarima Salman bashi da rinjiya a majalisar zabin Sarki, shi ne dalilin
da yasa ya gudu saboda an same shi da bada dukiya ga wasu masu
zabar Sarki, har sun fito sun bayyana, wadda hakan yana nuni da
cewar kai tsaye kisa kai ne domi ya saba dokar masarauta, amsa ta
biyu Gimbiya Suhaila bin Ababakari, eh Yarima Salman ya tura
mata da sako ta barauniyar hanya domin ta gudo ta je gare shi,
domin yana tsoron kada a hallaka ‘yar uwarsa, Yarima Salman yana
tare da Kafiri Jaremi bincike ya nuna mana cewar kafiran da suka
dauko ta za su kaita birnin Hairam, domin su haddasa yaki a tsakanin
yayan Sarki biyu ta wannan damar kuma za su yi amfani da hakan
wajen fuskantar matsaloli a yankin musulmai, dalili na uku kuma
jiya na dawo daga birnin Shamnun ina son a zaman da za a yi yau na
kawo maka bayanin duk da ya faru ya Sarki mai daraja.
Bayan waziri ya gama gabato da labarinsa sai ya juya ya dubi
Abdullahi bin Sharjas daga nan ya bawa Waziri dama ya koma ya
tsaya.
bature
41 Page
Sarki yayi kusan dakika uku batare da ya ce wani abu ba, sai
daga bisani ya dago kai ya dubi dansa Abbas da Zaid ya ce "Zaid ka
tafi da dakarun sulhu zuwa birnin Haiman don fuskantar Benjamin a
game da dalilin dauko gimbiya Suhaila bin Ababakari kai kuma
Abbas na baka aikin bincike da tabbatar da gaskiya a birnin
Shamnun, Waziri zai kasance da mu a nan saboda fuskantar wasu
matsaloli, ina maka fatan nasara a farkon ayyukanka a masauta a
yau.
Da yarima Abbas ya ji wannan batu sai ya duka kansa kasa
cikin girmamawa ya ce "Amin Baba, kuma da yardar Allah zai yi
duk wani abu da zai gamsar da kai da kuma fitar da masarautarka
kunya bisa tafarkin shugaban mu Annabi Muhammad farsiu
Sallallahu alayye wassalam"
Zaid shi maya dukar da kai cikin girmamawa ya ce “Insha
Allahu komai zai tafi kamar yadda ka Jarumi Umarta".
Sarki ya amsa a cikinsa gami da ci gaba da batu "Hakimi
Abdullahi bin Sharjas, ka yi namijin kokari kuma a jinjinawa Jarumi
Umar a gaya masa muna alfahari da shi bisa kokarinsa na ceto yar
musulmi kuma Gimbiya daga gobar kafurai, sannan muna maka
maraba da zuwa babban birni don shigo da abin da ya shige maka
duhu, za mu yi aiki kai da fata wajen magance dukkanin abubuwan
da za su kawo mana ci gaban kasarmu da musulunci".
Daga nan Sarki ya nemi wani mai Karin bayani kowa yayi
shiru bai ce ta tafasa ba haka ya tabbatar da cewa ba wani korafi don
haka Zaman majalisa ya tashi".
**
A tsakanin dagawa rana zuwa kwallewarta suka isa cikin
birnin Shamnun, sun yi gudu da dawakai ba tare da yada zango ba,
sun isa birnin dai-dai da lokacin da ake kiraye kirayen sallar la'asar
don haka sai suka yada zangon farko a bakin garin kusa da wata
bature
42 Page
rijiya daga gefe ga wani gini nan na saukar baki akwai masallaci a
wajen.
Lokacin sallar ya riga ya kure shi yasa basu bata lokacin hutu
ba suka yi sallar laʼasar sannan ne kuma suka fara tunanin abin da ya
dace ayi. A dai-dai wannan lokacin ne suna zaune a bakin ganuwar
birnin Shamnum suna hutawa tare da cin abubuwan don cika cikinsu.
Jarumi Umar ya nisa ya dubi abokan tafiyarsa ya ce "Da
akwai alamun tsaro a birnin nan mai tsauri, kuma ina kyautata zaton
maganar mahaifina ta tabbata sakon zuwan mu ya riga mu kara sowa,
yanzu dole mu sake shiri domin muka ce za mu tafi gaba gadi tabbas
za su yi galaba akan mu a ka ma mu a rufe ko a hallaka a saka mu a
lissafin masu goyan bayan rikicin masarauta don haka dole mu yi
aikin da hikima".
Suka shiru suka zurfafa cikin tunani domin gano abin da dan
uwansa ya hango a nan gaba. Ko da suka samu dan takin lokaci suna
wannan nazari sai Mu'az ya ce "Hikimar ka muke jira ya kai
gwarzon Karni domin ka san dai duk abin da za mu ce naka shi ne
mafita, domin ban hango wata dabara da za mu yi wajen shiga birnin
Shamnum batare da mu samu matsala ba".
Jarumi Jarumi Umar ya dubi kowa daya bayan daya domin
tunanin ko akwai mai Magana duk kowa ya girgiza alamar ba shi da
cewa sai da ya je kai Dawan sai Dawan yace "Mu'az shi ne mafi
hikima baya kai tun da har ya baka damar naka nazari ba mu da wani
abin cewa don haka muna saurarenka".
Jarumi Jarumi Umar ya dauki wani kara dake gefan kafarsa
yace “Ni ma bani da wata dabara, ta shiga gidan Sarauta har mu gaña
da Sarki sai hanya daya, hanyar daya ce dole a cikin mu za mu
rarrabu kashi biyar kowa yayi na shi kokarin duk wadda ya sha a
kokarin shiga gidan Sarauta to shi ne zai fanshe wanda aka kama in
kuma mun shiga dukkanin mu, to hakan shi ne fatan mu, Mu'az ka
bature
43 Page
tafi izuwa gidan Sarauta a matsayin dan aike daga bakin Mahaifina,
kai ma Dawan, Kai ma Saklahu, kai ma Kubait, kowa zai tafi da
ma'ana daban, idan Mu'az ya je bakin kofa in fadawa sun tutsiye shi
zai ce da su matafiyi ne shi daga Kasuwar ASSUK, ya zo ne domin
tallata hajjarsa ga sabon Sarki, saboda kaji labarin za a yi rantsuwar
don haka ka zo da bayanin siya da siyarwa ga Sarki.
Dawan kai kuma in ka is aka sanar da su cewar Manomi ne
kai da ka zo daga Zurkul domin kawo tallafin kayan noma ga Sarki
za ka je fada domin neman yaddar Sarki don gabato da kyautarka a
ranar bikin nadin Sarauta.
Kubait ka je a matsayin Malamin da zaka nemi yaddar Sarki
na yin wa'azi a ranar bikin sarauta, Saklahul kai kuma za ka je a
matsayin dan aike daga Birnin Bahara zuwa ga Sarki ka tubure sako
ne da kai da za ka kaiwa Sarki, ku tabbatar kun rike wannan dabarar
duk wadda ya samu nasarar koda an kama mu to tabbas shi zai
fanshe mu domin dolen Sarki ya gaza aiwatar da komai matukar in
ya ji da kunnensa cewar Sarki Muhammad farsi ya san da zuwanmu"
Da wanan shawara suka tasamma cikin birnin kai tsaye ba
tare da bata lokaci ba kowa ya waste ya nufi gidan gadan-gadan
gari guda, masarautar Shamnun
tsohuwar masarauta ce da wani hamshakin takadirin Sarki yayi mulki
a shekaru dari da suka shude, shi ya samar da masarautar tana da
girman gaske don a wancan lokaci a cikin masarautar dukka jama'a
birnin suke, saboda girmanta, a nan gidaje da kasuwannin birnin
suke, sai da duniya ta kara fadi aka samu jama'a da baki da dama,
sannan ne aka samar da wasu sasssa a cikin birnin. Saboda haka
yanzu idan ka ga wani a gidan to attajiri ne ko mai mulki a kasar,
amma duk talakawan gari da baki an tanadar musu waje a waje.
Babban gida ne ko na ce
bature
44 Page
Lokacin da Mu'az ya isa kamar yadda Jarumi Umar ya
Jarumi Umarce shi hakaya sanar da masu gadin wajen amma sai suka
nuna sam ba zai shiga ba, haka Dawan da sauran abokansa.
Duk Jarumi Umar na gefe yana kallon su, sai da ya tabbataṛ
duk basu samu nasarar shiga ba sai ya matso kusa da masu tsaron
kofar birnin da nufin shiga sai suka dakatar da shi “Kai ina za je?”
Jarumi Umar yayi shiru daga farko, sai da mai tambayar ya
kara maimaita tambayarsa sannan ya ce "Dan aike ne ni daga Salman
zuwa ga Sarki Hilal?”
Koda ji haka sai dakarun da suke tsaitsaye a bakin kofar suka
tsare shi da dogayen masu suna masu huci da kokarin sukar sa".
"Ka ce mene ne?"
“Ina so ku kai ne gaban Sarki domin ina da sako daga dan
uwansa?"
Dawan Kubait da sauran abokan tafiyarsa da suka ga an tsare
shugabansu da masu sai hankalinsu ya tashi suka yi niyar cire
makamin jikinsu, sai ya daga hannu daga nesan suka fuskanci abin
da yake nufi suka fasa aniyarsu.
Shugaban Dakarun ya ce "Mazak u rufe shi a kurkuku, ku ci
gaba da tsaro ni kuma zan je na sanar da Waziri halin da ake ciki".
"Ba wajen Waziri aka aiko ni ba wajen Sarki Hilal aka aiko
kuma ina da sako ne daga Sarki Muhammad farsi, zuwa gare shi, yin
ganganci da rayuwata tamkar yin ganganci ne ga rayuwar masarautar
Shamnun, don haka kai tsaye ku kai ne ga Sarki".
Shugaban Dakaru ya daka masa tsawa ya ce "Babu wani
wadda zai zo da sako makamancin wannan a bar shi ya shiga ya gana
da Sarki kai tsaye lallai sai dai waziri don haka za mu tsare ka aka
jira har Waziri ya bada Jarumi Umarni, saboda haka ku tafi da shin i
kuma ina nan zuwa”.
bature
45 Page
A haka aka tsare Jarumi Jarumi Umar Shugaban dakarun da
wasu masu dakaru biyu suka bi bayansa zuwa ga Fadar Waziri.
Hankalin abokan tafiyarsa ya tashi ainun suka rasa inda ke
musu dadi illa Mu'az ne kadai babu wani damuwaa tare da shi, daga
bisani ya ce "Ku kwantar da hankali, tabbas Jarumi Umar yana sane
da abin da yake yayi hake ne don a hana mu shiga, shi yasan yadda
zai shiga ciki, domin idan da bai yi haka ba duk ba za mu shiga ba,
kuma za a ka ma mu hakan da yayi akwai hikimarsa, yanzu ba mu da
abin da zamu iya sai mu jira zuwa anjima mu ga ni".
Lokacin da Dakaren ya shiga wajen Waziri Adnan a lokacin
yana tare da wasu dattijan kasa ana shirin yadda za a cimma nasara
wajen dora Yarima Hilal a kan karagar mulki a gobe, sai ga sakon
zuwan dakaren kofa,, ko da jin haka sai ya dakatar da bayanin da
yake domin ya san akwai babban al'amari.
Koda ya fito sai shugaban dakaru ya zayyane masa duk abin
da ya faru har ya shaidamasa yanzu haka yana hannu mun tsare shi".
Koda waziri ya ji wannan batu cikin gaggawa yayi gaba don
zuwa kurkuku domin ya je ido ya gane ya kuma tabbatar da zargin da
ake yi.
Koda suka isa kurkuku sai masu tsare wajen suka fito da
Jarumi Umar suka gurfanar da shi gaban waziri suna mai dukar masa
da kai kasa. Waziri yayi dariyar keta yace "Ku kyale shi, ai bako ne
kuma ba mu da tabbacin abin da ke tafe da shi."
Suka sake shi Jarumi Umar ya dago kai ya dubi Waziri
Adnan ya ce "Ka sada ni ga Sarki Hilal domin ina da sakon gaggawa
a gare shi, kafin wata matsala ta biyo baya".
Koda Waziri ya ji wannan batu sai ya gigiza kai yana dariya
ya ce "Me ke tafe da kai ga Sarki?"
bature
?
46 Page
Jarumi Umar ya girgiza kai ya ce "Da ace sakon naka ne da
zan sanar da kai amma tun da har wannan sako ba naka bane, babu
dalilin da zai san a sanar da kai".
Waziri ya ce "Ashe ba zaka rayu ba, matukar baka sanar da ni
, to ka yi sani cewar rayuwarka tana kan gargara”.
sakon Sarkiba Jarumi Umar yayi murmushi ya ce "Kamar yadda taka
rayuwar take kan gargara, bari in baka wani labara kadan mu biyar
ne ke dauke da sako zuwa ga Sarki, ragowar hudun suna kokarin
ganawa da Sarki akowane lokaci idan sun hadu da Sarki za su bashi
labarin cewar kana tsare da ni, idan kuma suka koma ga Sarki
Muhammad farsi za su sanar da shi labarin cewar kai ne
ummul'aba'isin hana ruwa gudu kamar yadda Yarima Salman ya
sanar da shi cewar kun siye duk wani mai zaben Sarki a majalisa kun
basu dukiya don su zabi Sarki Hilal maimakon zababben Salman".
Koda jin wannan batu sai hankalin Waziri Adnan y abaci ya
tunzura wani gumi ya fara taso masa. Don haka sai ya fadi a fusace a
mayar da Jarumi Umar cikin kurkuku da ya fito kai tsaye yayi sirri
da dakarun don su yi binciken gidan kaf domin neman wasu baki da
ba a san kosu waye ba.
Sai da aka kusan yini har yammaci ana wannan kewayen ba a
samu su Dawan ba, aka zo aka sanar da Waziri hankalinsa ya kara
tashi, don haka sai ya tashi dan aike kai tsaye zuwa ga waziri Ja'far
domin ya tabbatar masa da halin da ake ciki.
Lokacin da Waziri Adnan ya koma majalisinsa ya kasa
sanarwa da Tsuffin fada abin da ke faruwa saboda dama yana kan
kara basu Karfin giwa akan zabar Sarki Hilal, don haka sai ya
sallame su ya ci gaba da nazari da safa da marwa yana cikin wannan
lamarin sai uwar Yarima Hilal ta fado masa a rai ita kadai ce zata
samarwa da lamarin mafita saboda tafi danta son ya zama Sarki
saboda tana tsoron Salman akan irin yadda ta ci zarafin mahaifiyarsa
bature
47 Page
da yadda ta yi sanadiyar barinta duniya, wadda ta san cewar matukar
Salman yah au kan karagar mulki sai ya daukarwa mahaifiyarsa
fansa.
A dakin gani suka hadu wani daki ne dake mararrabar fadar
Sarki da cikin bangaren mata wacce idan ana zaman fada aka so
matan Sarki su ji abin da ke faruwa suna iya hawa sama suna hango
mutane amma mutane basa hango su, saboda wasu raga raga a can
sama sannan suna jin duk abin da ke faruwa, haka dakin Gani yake a
kasa idan wani mai mulki ko wani dan aike ko mahaifin Sarauniya ya
zo wajen diyarsa idan za su gana suna amfani da wannan dakin gani
ne, babu kowaye kai idan ka zo daki ne guda biyu wanda aka tsaga
raga raga a haka za ku gana da ‘ya'yan Sarki ko wasu masu aiki a
gidan Sarki ba a yadda a hadu fuska da fuska ba, sannan za ka yi
kasa da kanka ko ta cikin ragar baka isa ka hada ido da matar Sarki
ba.
da
=
har zuwan Sarauniya Ruma, koda ta
iso bai bata lokaci ba ya zayyane mata duk halin da ake ciki, hatta
dan sakon da ya tasa zuwa wajen waziri Ja'far ya sanar mata. Koda
ya zo karshe sai ta ce "Lallai muna cikin tashin hankali, amma duk
da haka ka yi abu mai kyau, abin da nake so mu yi yanzu, lallai shi
ne ka samu Yarima Hilal ka sanar da shi, cewar shi wannan dan aikin
dan leken asiri ne ba wai aikoshi a ka yi ba, saboda ya bada damar
kashe shi, idan mun kashe shi, batare da Sarki mai jiran gado ya san
cewar dan aike ne daga fadar Sarki Muhammad farsi, ina maitabbatar
maka har yanzu akwai shakka da tsoro a zuciyar Hilal, saboda haka
kada mu bari ya ji wani labara Sarki Muhammad farsi don zai iya
tsorata ya hakura da wannan mulki saboda tsoron mutuwa, idan
kuwa muka kashe bakon nan babu wani abu da zai biyo baya koda ya
biyo za mu sanar da Sarki Muhammad farsi cewar cewa yayi damu
shi dan aike ne daga Yarima Salman.
A nan Waziri ya kasance
bature
48 Page
Koda jin wannan shawara da sarauniya Ruma ta bada sai
Waziri ya samu kansa yana mai cikin farin ciki domin lokaci guda ta
fitar da shawara mai kyau, dan haka bai jira wata wata ba ya koma ya
sanarwa da masu gadin Jarumi Umar cewar lallai su tsaurara tsaro
akan wannan bakon domin akwai hatsarin gaske a tattare da shi, ya
kuma tsallaka ya kara gargadi kan cewar lallai a kara baza bincike a
game da bakin ido, ko wadanda aka gansu sun nuna alamun tambaya
a cikin birnin koda sun kasance yan asalin birni.
Kai tsaye ya tura sakon ganawa da Sarki mai jiran gado wato
Hilal domin sanar da shi karya da gaskiya.
BABBAN BIRNIN BAHARA
Lokacin da Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya fuskanci lallai
akwai babban kalubale a game da ja da waziri, domin ya gama cutar
masarauta, ya gama shiryawa duk wani makircin da ya tsara sai tsoro
da fargaba suka tasarwa ransa ya fara tunanin makomar dansa, nan
da nan hankalinsa ya karkata zuwa gida, don ya san cewar tunda har
Waziri ya san zan taku zuwa ga Sarki to babu shakka ya san labarin
zuwan dansa Shamnun, hankalin Hakimi Abdullahi bin SHarjasllah
yayu matukar dugunzuma, nan take a dakin da aka sauke shi ya mike
tsaye da niyar fita domin su koma gida sai kuma ya ji tafiya a na
kokarin shigowa cikin dakin. Abin da ya dakatar da shi daga mikewa
ke nan, ya na zaune wani bawa ya shigo ya durkusa ya gaida shi,
gami da mika masa wata farar takadda, cikin mamaki ya amsa ya ce
"Daga ina?"
Bawan ya jinjina kai ya kalli takaddar "Idan ka karanta zaka
fahimta, an bani ne kawai an ce na kawo maka”.
Daga nan ya fahimci abin dan haka sai ya salami Bawan
bayan fitarsa da kadan ya bude takaddar ya fara karantawa kamar
haka
bature
49 Page
"Zuwa ga adalin Hakimi, mai yi domin Allah, da na zai
kasance a bisa hanyar RUD, mararrabar da zata yanke zuwa tafiyar
da Sarki ya Jarumi Umarce shi zuwa birnin SHamnun da kuma
tafiyar kauyenka, idan hark a riga shi isa ka jira shi a can, idan kuma
ya rig aka zai jira ka" daga Sarauniya Haulet ibn Abbas.
koda jin wannan batu sai Waziri Abdullahi bin SHarjas ya
fice daga dakin tarar baki kai tsaye ya nufi inda Abdallahi da
tawagarsu ke tsaitsaye batare da bata lokaci ba kawai ya kama
dokinsa ya haye suma suka haye nasu dawakan, cikin sauri ya zaburi
dokinsa, suna fita daga masarauta dama akwai wani munafuki da
waziri ya masa Jarumi Umarni da duk inda suka bi yabi sahunsu
haka kuwa aka yi yana barin masarauta wannan munafukin ya ci
gaba da binsu nesa nesa, har izuwa mararrabar rud, adaidai nan ne
Hakimi Abdullahi bin Sharjas ya ce mu dakata anan mu yi sallar
la'asar kafin mu ci gaba da tafiya.
Tun da munafikin yake biye da su basu taba tunanin su yi
binciken hakan ba dan haka har zuwa wannan masaukin nasu basu
iya gane wani na biye da su ba. Da suka samu wajen shi ma sai ya
nemi wani waje nesa da su yayi kwantan bauna yadda babu wanda
zai hango shi, Shi kuma yana hango su.
Waziri Ja'afar kai tsaye ya sa a ka kira sarauniya Siyama
domin hakansu na neman cimma ruwa.
Lokacin da ta iso dakin gani yana tsaye yana jiranta don haka
gaisuwa kawai ya gabatar mata ya dora da maganar da ta kawo shi,
duk abin da ya faru ya sanar da ita.
"Akwai babbar matsalar da zata iya jefa mu cikin rikici
matukar Hilal bai zama Sarkin Shamnun ba saboda shi ne kadai
Sarki daya da ya rage da zai bamu goyon bayan wajen dabbaka
Yarima Hilal idan lokaci yayi, muna bukatar masautu shida,
wadanda suke karkashin mulkin Bahara, wadanda mun kafa biyu
bature
50 Page
Shamnun zata zama ta uku, kin ga in mun samu Shamnu mun ci rabi
kenan, ragowar za su zamo mana a saukake, to amma yanzu Sarki ya
tura Yarima Abbas akan sasancin matsalar da take faruwa a birnin
Shamnun".
Siyama ta yi shiru tana jujjuya maganganun waziri Ja'afar
bata ce komai ba har sai da ta yi nazari sosai sannan ta ce “Ja'afar ka
yi dukkan me yiwu wajen kare mana mutumci a tun baya a yanzu ma
kayi iya bakin kokarinka a gaban Sarki domin kahanashi ya fahimci
mu ne muke da hannu dumu-dumu akan rikicin birnin Shamnun,abu
daya za a yi yanzu ina a shi ne mu tabbatar da cewar mun samo
Yarima Salman, domin mu hallakashi, na fuskanci matukar Salman
yana raye sai yayi duk yadda zai yi wajen kwatar masarautarsa,
kuma matukar ya gana da Mijina Sarki Muhammad farsi ka yi sani
cewa Sarki na cikin halin kasala da rauni na dangane da maganin da
yake kwana akai wanda muka samu dakyar, kuma ka san wa'adin
wannan maganin yana daf da karewa matukar Muhammad farsi ya
dawo cikin hayyacinsa, ba mu kafa kanmu ba akwai babbar
barazana, lallai ka tashe manzo zuwa Shamnun da dinare masu
yawan gaske don a kara rabawa tsoffin nan aka kuma karawa Hilal
karfin gwiwa akan ya cire tsoro babu wani abu da zai faru, inda sun
tsaya akan yadda muka dora su, to la shakka yarima Abbas ba zai
fahimci komai ba”.
Da wannan waziri Ja'afar ya baro dakin Gani da ya faru
tsakaninsa da Matar Sarki Muhammad farsi Siyama, don haka kai
tsaye ya koma gidansa don kara shiri na gaske. A lokacin da rundunar Yarima Abbas ta iso mararrabar Rūd
sai ya sa aka dakata da tafiyar da ake yi, nesa kadan da inda su
Hakimi Abdullahi ya yada zango.
bature
51 Page
6
Bayan ya sauka daga kan dokinsa wani Bawansa da ake kira
Banu, ya ja doki izuwa wata inuwa ya daure shi a jikin bishiya ya
dawo domin bin Jarumi Umarnin Yarima Abbas.
"Ka je ka nema min iso wajen Hakimi Abdullahi bin
Sharjas".
Jim kadan ya dawo ya sanar da Yarima cewar Hakimi yana
jiran zuwansa. Shi kadai batare da wasu dakaru sun rufa masa baya
domin sun nufo shi ya dakatar da su. Shi ma Abdullahi bin Sharjas
sai ya baro sansaninsa sai da suka zo tsakiya sannan suka hadu a
karkashin wata bishiya a kuma daidai inda wannan munafukin yake
labe wanda zai iya jin duk wani abu da za su zanta.
Yarima Abba ya yiwa Abdullahi bin Sharjas murmushi gami
da durkusawa da niyar ya gaida shi... Abdullahi bin Sharjas ya rike
hannayensa ya tashe shi tsaye gami da cewar "Idan Allah ya so a
yiwa wani gaisuwa makamancin haka to Manzon Allah ne, idan
ma'aikin Allah ya so mu yi haka wajen gaisuwa mai koyi da bautar
Allah,ba zai hane mu ba, ba kuma zai bawa dukkanin makusantanshi
hannun dan yi musabaha ba. Ku ne mafi daraja domin ku ne sarauta,
amma gaisuwa da addini ya tanadarwa bayin Allah shi ne su yi
musabaha shi ne ladan hakan yake a rubuce".
Wani kayataccen murmushi Abbas yayi gami da cewa
"Wannan koyarwa ce da Kakana, yake yawan sanar da ni, Abban bin
Zubair nagode kwarai".
Abdullahi bin Sharjas yayi murmushi gami da tunawa da
Abbas. Ya ce "Allah ya kai rahama kabarinsa... Mahaifiyarka ta
sanar da ni zamu yi ganawa ta musamman da kai, ina fatan dai lafiya
kuma babu wani abu da na kuskure da muka aikata”.
Yarima Abbas yace "Astagfirilla, babu wani zargi mara kyau,
daga gare mu zuwa gareka sai tsantsar fahimtar da kuma soyayya,
Mahaifiyata ta turo ni wajenka ne domin muna da bukatar samun
bature
goyon bayanka, a game da duk abin da yake faruwa a masarauta, ta turo ni ne a madadinta saboda idan har ta yi gani da kai to munafukai
zasu fahimci wani abu, za kuma su iya kulla sharri da zai jefa mu
cikin tsananin Sarki da azabarsa".
Abdullahi bin SHarjas yayi murmushi gami cewa “Me ke tafe
da kai, me kuma kuke bukata daga gare ni?"
"Goyan baya kamar yadda na fada a farko, kasancewar ba mu
da wasu masu goya mana baya a gidan sarauta ta saurari labarinka
daga wajen wata Baiwarta da ka taba kyautar da ita ga Sarki wacce
ka musuluntar ka saka mata suna"
Hakimi yayi shiru yana tunani daga bisani Yarimaya rage
masa dogon nazari ya ce "Hindu"
Hakimi Abdullahi yayi murmushi yace Baiwar Allah, na tuno
ta kwarai da gaske. To abin da zan sanar da kai Yarima shi ne
birninku yana cike da kalubale, munafukai mahandama, ba zan
fahimci wane daure bane ya mamaye masarauta amma daga
bangarena ina da tabbacin Waziri Ja'afar yana daga cikin matsalolin
masarauta wanda a yanzu na fahimci zahirin abin ba badini ba, na
baro babban birni da haushin Sarki Muhammad farsi saboda gabaki
daya Sarki Muhammad farsi ya sauya daga babban rikon da ake yiwa
Daula, ya zama kamar amsar Jarumi Umarni yakeyi daga jama'ar da
yake mulka, abin da nake nufi sam Sarki ya sauya. "Tabbas akwai abubuwa da dama wadanda suke da daure kai
ammayin fito na fito da a zauren Majalisa babban kalubale ne malamai da dama sun rasa rayukansu, duk bautar da suka yi wa kasa sun mutu a matsayin maciya amanar kasa, duk kuma ba don dalilin
sun gaza ba sai kulla sharri"
"Ina son gaskiya, ina son aiki da amana kuma ina son ayi komai domin Allah ba domin rububin sarauta ba, sai domin cancanta
bisa gaskiya, a wajena da kai da Yarima Zaid duk daya ne banbancin
bature
52 Page
53 Page
da zai kalla a tsakaninku waye shugaban waye adalcinsa ya fi
tabbatuwa ga Al'umma saboda haka ina bayanku, aikin ka na kwarai
shi ne zai banbanta kada shi, dan haka ina bayanku ku duka Allah
mafi sani ya zaba mana mafi alkairi, abu daya ne yanzu yake
damuna, lallai idan ka je kasar