Su Abba sunce daurin aure kawai zasu yi, ba sa son anything that will call attention na mutane kan mu, amma ni ina son ki samu everything da kike da burin yi a auren ki. Amma baki taba fada min ba ko akwai wani abu special da kike so?" A hankali nace "ni babu abinda nake so. In an daura auren kawai shikenan". Ya danyi shiru "i know ba kya so na, but this is not about me but about you. I want you to have all your heart desires. I know mata da son biki, am sure you had plans....." Na katse shi "mata daban daban ne ai, kowa da akwai abinda take so. Ni bana son biki. Bana son yin komai" na fada ina jin raina yana kara baci. Ya sake yin shiru. Sai kuma a hankali yace "I am sure da shi zaki aura da baki bata rai dan ance ki fadi events din da kike son yi ba. I am sure da Gidado ne da kin fi kowa murna........" Na mike tsaye kamar wadda aka yi wa allura "don't" na fada cikin sarkewar murya, "don't you dare mention his name ever again" ya danyi dariya kaɗan "okay, okay. Na daina. I just want you to talk kin barni ina ta magana ni kadai shi yasa na dan taɓa button ɗin da yake activating ɗin ki. Amma nima kishi na ba zai barni in kuma ambatar sunan sa ba. Kin san...."
Na kashe wayar nayi jifa da ita kan gado sannan na koma na zauna tare da dafe kaina, wani irin bacin rai nake ji, wani irin ciwo zuciya ta take yi min. Na san Mukhtar ya san Gidado kamar yadda shima Gidadon ya san shi, amma basu taba magana da juna ba kuma wani daga cikin su bai taba yi min maganar dayan ba. Ban san mai yasa jin sunan Gidado a bakin Mukhtar ya bata min rai har haka ba. Na jawo wayar tawa ina kallon hoton kan screen din. Hannun Gidado ne a ajjiye akan steering motar sa "Allah sarki Muhammad" Na fada a fili "Allah ka dubi bawanka".
Na sani, ina son Muhammad son da ba zan iya kwatanta shi ba, na kuma sani shima yana min son da ban taba ganin irin sa ba. Na tuno da haduwar mu ta uku, na tuna da yadda ta kasance.
****. ****. ****. ****. ****. ****
Tunda muka rabu da shi a ranar da muka yi haduwa ta uku zuciya ta bata samu sukuni ba, naji haushin sa sosai a ranar, haushin rashin karbar number ta da baiyi ba, na kuma ji haushin kaina akan me yasa ni ban karbi tashi ba tunda shi ya manta bai karni tawa ba? Amma kuma ni nasan kaina, nasan pride ɗina na ƴa mace ba zai barni in karbi number ɗin saurayi ba ko kuma inyi making first attempt, na san cewa na kamu da son sa, duk kuwa da cewa a lokacin ban san so ba amma nafi so ace shine da kansa ya fara ambata min yana sona ba ni ba.
Wani lokacin kuma in ina tunanin sa sai inji haushin kaina, ina ganin kamar shi bashi ma da interest a kaina shi yasa ma bai karbi number ɗin ko kuma ya nemi address dina ba. I mean wanne saurayi ne zai ga budurwar da yake so suyi magana sosai kuma har su rabu amma bai karbi number ɗin ta ba, who does that?
Tun ina daukan abin wasa har ya zamar min gaske, kullum in ina zaune ni kadai shi nake tunawa, sai inyi ta bitar maganganun mu a raina ni kadai ina murmushi. In kuma na kwanta bacci Muhammad sai ya bini cikin bacci na, amma a baccin nawa yana karbar number ta har ya kira ni a waya muyi ta hira, ina ta murna, sai na farka sai inga ba haka bane ba.
Lokacin dama Daddy ya kawo ni Abuja da niyyar uncle Ahmad ya nema min jami'a a cikin manyan jami'o'in Abuja saboda in samu in zauna a guri daya in daina binsa ƙasa ƙasa, uncle Ahmad ɗin kuma yayi kokarin samar min admission ɗin, jira kawai yake a fara registration ya kaini inyi, a lokacin ne wata dabara tazo min.
Ina tunawa a cikin maganganun da muka yi da Muhammad ya fada min family dinsa sun bude sabuwar jami'a in honor of his late grandfather. Ya kuma shaida min yana son yin aiki a can. Duk da dai lokacin da muka yi maganar bai fara aikin ba. Sai na yanke shawarar why not in saka a nema min admission a makarantar, maybe mu sake haduwa a can. Maybe ma in ganshi a aji a matsayin malami na. Na tuna sunan makarantar "MD University". Naje na samu uncle Ahmad da maganar "uncle wata sabuwar jami'a da aka bude kwanan nan, MD University, can nake so a nema min" ya bata rai "ban gane ba. Ita kuma wannan da aka nemar miki menene matsalar ta?" Nace "babu komai uncle, kawai dai ni nafi son waccan ne, akwai kawayena da suka ce min can zasu je, kaga zan samu abokan karatu". Haka nayi ta bugawa amma uncle Ahmad yaki yarda, ranar nan ma cewa yayi in na sake yi masa maganar sai ya kwada min mari. Mukhtar yana ta yi min dariya. Ni kuma naki hakura dan gani nake makarantar ita kadai ce chance ɗina na haduwa da Muhammad again.
A haka Allah ya kawo savior dina kasar, Daddy, ai kuwa ranar da yazo da maganar na tare shi, "Daddy ni MD University nake son a nema min, ni bana son wannan da aka samu" ya juya yana kallon uncle Ahmad "wacce ce kuma MD?" Uncle Ahmad yace "kar ka biye mata yaya, wata sabuwar jami'a ce da ko kafuwa bata yi ba ballantana musan kyanta ko akasin haka. Wannan shekarar fa suka fara daukan daliban su na farko" na zamo daga kan kujera na fara kuka "ni wallahi Daddy ita nake so. Dan Allah ni dai a kaini can. Allah in ba'a kai ni ba ba zanyi karatun ba" Daddy ya fara fada "ba za'a kai ki ba ɗin. Wannan da aka samo ɗin ita zaki je".
Amma daga ni har duk wanda yake gurin mun san cewa kamar an kai ni ne an gama.
Wata guda bayan nan har na gama registration na fara zuwa lectures.
Tun daga nan kuma sai na fara abinda ya kai ni makarantar, neman Muhammad. Farko na fara neman sa a cikin malaman department din mu, amma ban same shi ba, sai na fara nema a na sauran departments amma na rasa a ina zanyi concentration neman tunda ni ban ma san me ya karanta ba ballantana in san me zai koyar. Sai na fara shiga cikin yan wani department din da ba nawa ba, in ana hira sai ince something like "ai naji labarin wannan malamin naku Muhammad Lawan, ance bashi da kirki" and they will be like "mu bamu da malami Muhammad Lawan" and I will be like "Okay ba department din ku bane ba ashe".
A haka har sai da na fara fitar da rai, thinking ko ya chanza shawara bai karbi aikin ba. Amma kuma na kasa hakura. A haka har semester ta kare aka fara shirye-shiryen exams. A lokacin ne kuma naje zanyi submitting wani assignment ɗina a office ɗin wani malamin mu. A lokacin ne kuma na ganshi.
Building din hawa biyu ne, duk offices din lecturers ne, office ɗin wanda zan kaiwa yana sama, ina hawa hawa saman idona ya sauka akan Muhammad a kofar wani office yana budewa. Sai dai bai ganni ba ya bude ya shiga ciki sannan ya mayar ya rufe. Na karasa da sauri ina jin wani irin excitement amma kuma zuciya ta tai yarda da cewa shi din ne. Naje kofar office din da ya shiga na tsaya na karanta sunan jikin office din "Muhammad Lawan Muhammad" naji wani dadi ya rufe ni kamar in taka rawa a gurin. Amma kuma what next? Gani dai gashi, katanga ce kawai a tsakanin mu amma me zanyi kenan? Shin zanyi knocking ne in ya buɗe ince hi? Ko kuma shiga kawai zanyi inyi pretending kamar batan kai nayi ba nan zan shigo ba, in yaso sai in nuna mamakin ganin sa a office ɗin. To amma kuma ai ga sunan sa nan baro baro a jikin kofar, in na shiga dole zai gane neman sa nake yi. Na dafe kaina, ga koshi ga kwanan yunwa.
A karshe haka ina ji ina gani na wuce office din ban shiga ba naje nayi submitting assignment dina na sake wucewa na koma gida. Amma hankali na ya kwanta tunda na ganshi na tabbatar yana makarantar, sai na kudiri aniyar zan san yadda zanyi ya ganni kuma ya fara yi min magana.
Daga nan na fara monitoring dinsa, na lura da sanda yake shigowa makarantar da kuma sanda yake fita. Sai na shirya plan dina. Sai da na daidaici lokacin da yake fita sannan na kwashi littattafai da takardu na tafi kan stairs din offices din nasu na baje wai ni lallai karatu nake yi. Ina zaune da uban takardu a gaba amma hankali na yana kan duk motsin da za'a yi a sama. A haka har na ji taku, na dan duba ta gefen ido na ga shine sai na dauke kai na cigaba da bude littafin gaba na amma ina jin zuciya ta tana ta bugawa da karfi. Ban ankara ba sai gani nayi yazo ya wuce ni ba tare da ko kallon inda nake yayi ba, yaje ya shiga motar sa ya tayar ya fice daga makarantar. Naji takaici ya kama ni. Amma na gaya wa zuciya ta cewa bai gane ni ba musamman saboda bayana zai gani sanda yaje saukowa.
Sai na chanja shawara.
Washegari takanas na samo kujeru guda biyu da dan karamin table na dasa a direct opposite stairs din su. Na baza takardu sannan na sawa kofar office ɗin sa ido, a haka har naga ya fito ya rufe kofa sannan ya fara saukowa, sai da naga ya kusa gama saukowa sannan nayi dabara na zubar da takardun gaba na, kamar irin iska ce ta zubar da su ɗin nan, ko bai ganni ba na san hasken takardun zai dauki hankalin sa.
Naji takunsa ya doso inda nake, ina jin kamar a cikin zuciya ta yake taka kafafunsa, sai kuma ya tsaya a dai dai sai ti na. A lokacin na tabbatar cewa ya ganni kuma ya gane ni amma ban kalle shi ba sai na cigaba da bude pages din littafin da yake gaba na. Naji Muryar sa "oh my God" still ban daga kai ba. Ya kara matsowa "oh my goodness. Piya? It is really you" na dago kai ina bata fuska, sannan na bishi da kallo tun daga kan takalmin kafarsa zuwa fuskarsa da take reflecting wani irin annuri da farin cikin da zuciyar sa take ciki.
Na bayyana mamaki a tawa fuskar "wow. Malam Muhammadu dan fillo. What are you doing here?" Ya ja kujerar da dama dan shi na ajiye ya zauna "ke zan tambaya Piya, what are you doing here? How comes? Taya kika zo nan? Shin ko mafarki nake yi ne?" Nayi murmushi ina nuna masa takardun gaba na "karatu nake yi. Anan makarantar nake. Kai fa?" Yace "I work here. Ga office dina can. I can't believe this. You have no idea yadda na sha wahalar neman ki a garin Abuja" a raina nace "taka wahalar ka sani ba ka san tawa ba".
Yace "ranar nan was the best and the worst day of my life. I can't believe I let you go ba tare da na karbi number ɗin ki ba. I went back to your car na zauna jiran mechanic dinki yazo daukan mota in karbi number ɗin ki a hannunsa, amma that good for nothing mechanic bai zo ba, anan nayi sallar la'asar da magrib" na rufe bakina ina dariya, shima yayi dariyar "stop laughing at me. Nasha wahala fa. Har dare bai zo. Da sassafe kuma dana koma gurin already har ya dauke motar".
Nace "to ai Allah ya yi yanzu, gashi mun sake haduwa" bai ce komai ba sai ya dauko wayar sa ya ajiye min a gaba na "i won't repeat the same mistake. Dauki ki saka min number ɗin ki" na dauka na saka, na mika masa amma sai yaki karba yace "save it" nace "okay, me zan saka maka yadda zaka gane. Safiyya Adam Muhammad kamar yayi tsaho, ko in saka maka Fiyya?" Ya girgiza kai "Piya. You will always be Piya to me" nayi murmushi ina jin zuciya ta fari kal. Nayi saving da Piya💝 na mika masa still sai yaki karba yace in kira, sai dana kira ya tabbatar ta shiga sannan ya karbi wayarsa. Na dauko tawa wayar a jaka nayi saving tasa number ɗin, farko na saka Muhammad, sai kuma na goge na saka "Pyar💝"
Forgive the typos
Say Hi to this number so that your number can be saved.
We are almost done with free pages insha Allah.
0704 203 0419
Yan kasuwa kofa har yanzu a bude take. Advert your markets with Safiyya and Gidado.[07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: *❤🩹 Safiyya ❤🩹*
*By*
*Maman Maama*
*Episode Twelve: Twisted*
Free Episode
Masu bude telegram musamman saboda su karanta Safiyya, you guys have a special place in my heart. I really appreciate the love and support. Dan ku na kasa daina rubutu 😍💕
Gidado yayi taku biyu baya yana kallon hannun da mutumin ya miko masa, sai kuma ya kalli fuskarsa kamar mai kokarin gane wani abu "Mustapha? Mustapha kace" mutumin ya sauke hannun sa ganin gidadon bai yi shaking ba, Al'ameen yace "eh Mustapha yace, ka san shi ne?" Wani murmushi Gidado yayi, a zuciyarsa yana jin kamar an dauke masa wani babban dutse, yace "no. Ban san shi ba. At least not yet" mutumin ya mayar masa da murmushin sa yace "Yes. I believe we will soon know each other a matsayin in laws".
Yayi gaba su Gidado suka bishi a baya zuwa mota, sai a lokacin suka lura da cewa su biyu ne suka zo. Suka gaisa da dayan shima sannan suka shiga bayan motar su kuma suka shiga gaba, wanda ya kira kansa da suna Mustapha yana driving. Gidado ya juya kansa yana kallon waje yana jin daɗin iskar da take dukan fuskar ta sa, iskar yanci. Yanzu tabbas yana da tudun dafawa. Safiyya tana yawan ambaton Mustapha a maganganun ta kamar yadda take ambaton Safina. Ya kuma san cewa shi Mustapha ɗin yayan Safina ne uwa daya uba daya. It cannot be a coincidence ace wannan yarinyar sunan ta Safina sannan kuma tana da yaya Mustapha.
Ya san idan ya tabbatar wa da Mama cewa Safina yar uwar Safiyya ce to tabbas zasu yarda a fasa auren, ko ba dan komai ba ya san yanzu babu halittar da suka tsana irin Safiyya. Ya juyo da kansa, fuskarsa still dauke da murmushi, Al'ameen da yake ta kallon sa ya yi masa alamar tambaya "what?" Dan ya san ba da irin wannan fuskar suka taho ba. Amma Gidado bai kula shi ba so yake yi suje gidan ayi maganar a gaban Safina a gaban kuma Al'ameen yadda Al'ameen din zai zamo masa shaida a gurin iyayensa. Dan yanzu duk wani abun da ya shafi Safiyya ba yarda suke yi da maganar sa ba.
Basu yi nisa sosai ba suka sauka daga kan titi suka shiga wani layi sannan suka shiga wani gida. Gidado ya bude ya fito yana kallon gidan, gida ne na masu rufin asiri, not luxuriously rich but middle class rich. Daga gani kuma gida ne mai mutane da yawa a cikin sa. Wadanda suka kawo su suka yi musu jagora zuwa bayan gidan, sannan suka shigar da su wani ƙaramin parlor. Suna fita Al'ameen ya tambayi Gidado "what? Menene kake ta fara'a haka? Don't tell me daga ganin yayanta har ka matsu da ka ganta" ya karasa cikin tsokana "Gidado ya zauna ya dora kafa daya akan dayar yana jujjuya ta yace "yes, in a way zaka iya kiran abinda nake ji a raina haka. Kai dai ka jira. You will be surprised with the outcome of this visit" Al'ameen ya zauna, trying as much as he can to be comfortable akan kujerar yace "to Allah ya sa muji alkhairi".
Basu dade da zama ba wasu samari suka shigo su biyu suka fara jera musu kayan ciye ciye bayan sun gaishe su. Gidado ya yi tilting kansa yana kallon yaran kokari yake lallai sai yaga kamannin Safiyya a tare da su, sai da suka gama sannan yace "are you guys twins?" Suka juyo suna kallon sa sannan suka kalli junan su suka yi dariya. "no" daya yace dayan kuma yace "a'a. Abokina ne wannan. Dan makotan mu ne". Gidado ya koma ya jingina kansa a jikin kujera tare da rufe idonsa, yana jin al'ameen ya bawa yaran wani abu suka yi masa godiya suka fita. Sai da suka fita Al'ameen yace "kannen ta ne twins din da kake nema?" Bai bude idon ba yace "kannen Safiyya ne" Al'ameen yayi ajiyar zuciya yace "Gidado, gidan su Safina muka zo nan ba Safiyya ba. What is wrong with you" gidado ya gyara zama yace "na sani, akwai abinda nake tunani. You will understand idan ta fito.
Ba'a jima ba kuwa ta fito ɗin. Kamshin turaren ta ne ya fara iso musu kafin ta karaso. Kyakkyawace son kowa kin wanda ya rasa. Fara tas mai cikar jiki da shape mai kyau wanda ta tabbatar ya fito a cikin doguwar rigar lace ɗin da ta saka, ba irin fitowar da za'a kira da tsiraici ba amma irin fitowar da zai dauki hankalin duk wanda ya kalle ta. Fuskarta da kwalliya dai dai gwardado. Tayi daurin dankwalin da ya zauna ɗas a kanta ya kuma bayyanar da yalwataccen gashin kanta ta baya. Ta yafa mayafi a side daya ya rufe rabin kirjinta.
Ta tsaya a bakin kofa tayi sallama. Suka amsa mata a tare sannan ta shigo kanta a kasa ta zauna a kujera ta gaishe su "sannun ku da zuwa. Da fatan hanya bata gajiyar da ku sosai ba" duk suka yi shiru babu wanda ya amsa. Kowa yana saka ran dayan zai amsa. Sai kuma suka kalli juna a tare suka amsa "lafiya lau" "yauwa".
Suka sake yin shiru gabaki daya. Ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da fingers dinta, Gidado kuma ya tsare ta da ido a ransa yana son ya ga ko zai iya tuno kamannin Safinar Safiyya, maybe ko ya taba ganin ta a hoto amma ya manta, yayin da shi kuma Al'ameen yake kallon Gidado da mamakin kallon da yaga yana yiwa Safina. Al'ameen ne ya katse shirun ta hanyar yin gyaran murya tare da cewa "malama Safina ya shirye shirye?" Ya fada already feeling awkward, dan shi ba gwanin magana bane ba musamman ga wadanda bai sani ba. Ta dago ido suka hada ido da Gidado, tayi murmushi tare da sake mayar da idonta kasa sannan tace "alhamdulillah. Ya naku?" Kafin ya amsa mata Gidado yace "ina twins?" Ta sake dago ido tana kallon shi, shi kuma yayi kokarin studying fuskarta yana neman yanayin mamaki amma sai yaga confusion. "Twins kuma? Wadanne twins?" Yace "naga Mustapha shi ya dauko mu dazu, na dauka tare da twins suka zo" ta sake bata fuska tare da girgiza kai "still ban gane abinda kake nufi ba. Mustapha daga ina yazo? Ai dama yana nan. But ka san shine wai?" Yace "shi Mustaphan ba yayan ki bane ba?" Ta gyada kai still cikin nuna rashin fahimta tace "eh yaya na ne, dan kanin baban mu ne. Ka san shi ne?"
Gidado ya mayar da kansa baya tare da rufe idonsa, yana jin dutsen da ya daga daga kan zuciyarsa dazu yana komawa yana cigaba da danne ta. Al'ameen yayi saurin cewa "kamar naga kin kawo mana snacks, ɗan zuba min" ta mike da sauri ta dauki dan karamin plate ta na zuba masa samosa amma hankalin ta yana kan Gidado, ta durkusa ta mika wa Al'ameen still tana kallon Gidado tace "is he okay? Ko baya jin dadi?" Al'ameen yace "fine, he is fine, akwai serviette ne?" Ta dudduba gefe sai ta mike tace "bara in kawo".
Tana fita Al'ameen ya ajiye plate din da ta bashi ya taba kafadar Gidado yace "kai lafiyar ka kuwa? What are you doing. What is with wani Mustapha and twins" Gidado ya bude idonsa, duk annurin da ya sauka a fuskarsa dazu ya kauce yanzu, yace "Piya tana da step sister mai suna Safina, and a step brother mai suna Mustapha. When I saw that guy yace min shi yayan wannan Safinar ne kuma sunan sa Mustapha, I thought......" Al'ameen yace "Muhammad! Must you relate everything to her? Komai na rayuwa sai ka jingina da ita sannan zai baka ma'ana. Are You telling me kazo gurin yarinyar da zaka aura and the first thing da kake kokarin tambayar ta shine ko ta san dangin tsohuwar budurwar ka? Does that even makes sense to you?"
Gidado ya dauki robar ruwa ya bude ya daga ya shanye gabaki daya sannan ya ajiye robar. Yayi murmushin takaici yace "maybe I am loosing my mind. But yes. To me everything relates to her. Nothing makes sense to me in dai ba'a haɗa da ita a ciki ba" Al'ameen yace "then I don't think you are fit to marry " Gidado yace "ha! Finally someone ya fahimta. Go and tell that to Abba and Mama watakila su ma su fahimta"
A dai dai nan Safina ta dawo hannunta rike da sabuwar serviette. Ta ajiye a gaban Al'ameen amma shi kuma sai ya mike. Tace "ba ka ci samosar ba" ya kalli samosar, shi ya manta ma ta ajiye masa, yace "thank you, zan dan je waje ne inyi waya" yana fita ta zauna akan kujerar da ya tashi daga kai tana kallon Gidado cike da damuwa tace "Habibi, kamar ba ka jin dadi ko? Ko tafiyar ce ta gajiyar da kai?" Ya dan juyo ya kalle ta "am fine. Kar ki damu. Yanzu zamu ga su baban? Gwara mu gama mu zo mu tafi"
Ta dan bata rai "tafiya fa ka ambata, yanzu fa kuka zo and ko gaisawa bamu yi ba sosai musamman tunda yau muka fara haduwa. Ya kamata mu danyi hira ai ko?" Ta karasa tana langwabe kai gefe. Ya gyara zamasa yana kallon ta yace "hira? Okay what do you want us to talk about?" Tace "at least ka fada min ya ka ganni? Tunda yau ka fara ganina. Gwara in san cewa nayi maka ko ban yi maka ba. And maybe tell me abinda yake damunka, watakila ina da maganin sa" yace "does that really matter? Kina ganin ra'ayi na akan ki yana da muhimmanci?" Ta mike ta ta bi ta gabansa zuwa inda kayan abincin suke ta zubo masa juice ta hado da snacks a plate ta dawo inda yake ta durkusa a gabansa ta mika masa juice din sannan ta koma ta zauna ta dora snacks din akan cinyarta tace "ra'ayin ka a yanzu shine yafi komai muhimmanci, musamman ni a gurina. Abinda kake so shine abinda zan saka a gaba na, abinda ba ka so shine abinda zan fi ki fiye da komai" yace "tell that to my parents" ya kurbi juice din ya ajiye yace "send me your account details, zan turo miki kuɗin da zaki yi hidima, am sure kina shirya wani abu da kike so kiyi. And if you need anything, message me".
Ranta ya baci har fuskarta ta nuna, tace "yanzu dai ba zanji cewa nayi maka ko banyi maka din ba? Duk wannan kwalliyar da nayi?" Ya mike tsaye "ban boye miki komai ba Safina. And you agree to take your chance with me. Wannan shine dai dai lokacin da zaki fara hakurin da kika yi alkawarin zaki yi" ta mike ita ma "kayi hakuri. Kar ka bata rai dan Allah. Kawai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 14