sun dauki hanya kuma sai Haidar ya fara dariya yace "ka san tunanin da nayi, ina ma ace tare da Aunty Hafsat muka je gidan nan matar nan tayi mana wannan mulkin" Gidado yayi murmushi yace "da anyi yaki kuwa. She will humble her. Zan so inga yadda zasu kare da bikin nan".
*Her* 🧕🏻
Kwanaki suna ta tafiya har ya rage saura sati biyu lokacin da likita ya saka za'a yi min aiki yayi, amma sai naji sam bana jin tsoron aikin da za'a yi min ban damu da cewa wai cikina za'a yanka a fito da ɗan mutum ba, ni dai kawai burina shine in rabu da mayataccen cikin nan ko na samu in shaki iska mai daɗi, ko na samu in dai na ganin disappointment a fuskar Daddy a duk lokacin da ya kalle ni, ko na samu in manta da abinda ya same ni.
Sai dai ni kaina na san cewa rabuwa da cikin ba zata taba goge abinda ya faru daga zuciya ta ba, babu abinda zai fari da zai saka in manta da abinda aka yi min. Zalincin da aka yi min. Babu kuma abinda zai saka in yafe wa wanda yayi min. Har abada.
A lissafin Daddy naji yace aiki na zai kama washegarin daurin auren Safina. Ni kam ban ma rike date din da aka saka na auren Safina ba. Dan ni ba ma na gane ranaku a yanzu. Akwai kawayen mu da yawa da suke ta yi min magana a chats akan bikin Safina, ni kuma na kan basu amsa da cewa nayi tafiya jinyar Daddy dan haka bana nan za'a yi. Safina kam sai shirye shiryen ta take yi. Ta kan turo min pictures na kaya tace in taya ta zaba, har kayan da zata saka na kowanne event da zasu yi sai da ta turo min, sometimes na kan yi ignoring dinta dan ni abinda yake gaba na yafi karfin zaban kayan sawa, sometimes kuma sai in bata amsa dan kar ta ga kamar dan nasan kudin indirectly daga gurina zasu fito shi yasa na ke wulakanta ta.
Kamar yadda nayi tunani, su yan uwan nata da ta tafi Katsina gurin su dan suyi mata aure babu abinda suka yi mata na kayan daki, haka a dole Mommy ta sauko daga fushin da tayi da Daddy ta dame shi da waya akan ya bada kuɗin da za'a yi wa Safina kayan daki, direct yace mata bashi da kuɗi, besides, ai tace masa Safina ba yar sa bace ba. Sai ta koma gurin Uncle Ahmad shi kuma yace mata ta tambaye ni amma sai ta kasa tambayar tawa ta cigaba da bin Daddy, har sai da Daddy ya tabbatar tayi laushi sannan yace da Uncle Ahmad ya bata. Haka suka yiwa uncle Ahmad bill tun daga kan kayan daki har zuwa kayan da zasu saka na fitar biki, shi kuma ya raba biyu ya basu rabi yace ba zai bayar ga baki daya ba. A lokacin ne Safina ta yi min dogon message akan maganar, wai uncle Ahmad zai saka suji kunya, wai tun yanzu ya fara nuna musu cewa su ba yanuwan mu bane ba, dan Allah inyi masa magana.
Banyi masa magana ba sai na yiwa Daddy magana, tunda na fahimci shi sulhu yake so yayi a tsakanin mu shi kuma uncle Ahmad so yake a raba gari kowa ya kama gabansa. A ƙarshe dai Daddy ya saka Uncle Ahmad ya cika musu kuɗin suka yi duk siyayyar su suka gama.
A ranar da yake saura sati daya aikina, na tashi da safe kamar yadda na saba na shiga kitchen na haɗa smoothie na sha sannan na shiryawa Daddy breakfast. Na dauka na kai masa dakinsa na tarar yana kwance idonsa a rufe amma daga gani na gane ba bacci yake yi ba. Na jawo table gabansa na dora abincin na zauna a gefe nace "Daddy ga breakfast. Ka tashi ka ci". Ya tashi zaune da kyar, na lura da effort din da ya saka yanzu gurin tashin yafi yadda yake yi da, ciwonsa yana kara cigaba a kwanakin nan fiye da yadda yake da.
Ya zauna ya debi oats din dana dama masa a hankali ya kai bakin sa, na kara lura da yadda hannunsa yake rawa sannan da kuma yadda ya hadiye abincin da kyar. Ya lura da kallon da nake yi masa yayi gyaran murya yace cikin muryar da ta kara zama weak "doctor yace nan da wata uku, that's idan na kai nan da wata uku, I will be needing a feeding tube, ba zan iya cigaba da hadiye abinci da kai na ba. Kin gane?" na gyada kai na da sauri tare da sunkuyar da kaina ina kallon ciki na da yanzu baya boyuwa a cikin riga ta. Ya kira sunana "Safiyya" na dago kai na kalle shi yace min "don't cry" na sake sunkuyar da kaina ina jin hawaye na suna zuba kan cinyata. Nayi saurin goge su. Sai ya sake kiran sunana "Safiyya" na dago kai, yace "munyi magana da Ahmad, za'a daura auren ki da Mukhtar washegarin da akayi na Safina, in anyi miki aiki da safe, da yamma za'a daura miki aure. Saboda baƙin da zasu zo na Safina ba sai sun koma ba sai a daura naki. Do you understand?"
Na sake gyada kaina ina rike hawayena. Sai na mike na yi hanyar fita, har na kai kofa ya sake kiran sunana "Safiyya " na juyo yace "kin fahimci dalilin yin auren nan ko?" Na sake gyada kaina ban ce komai ba na fita da sauri.
Daki na na wuce da sauri na rufe kofa sannan na zube a kan carpet din gaban gadon dakin na fara rera kuka. Kukan abubuwa da yawa. Kukan da ban san ranar da zan daina shi ba
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 14