Share this page
kokarin kar ya kalli cikina, yace "ina jin yau kusan shekaru biyu kenan da na fara gaya miki abinda yake zuciya ta. So kin riga kin sani. Ina so ne in gaya miki cewa babu abinda ya chanja a zuciyata a game dake duk da rejecting dina da kikayi the first time. Babu abinda ya chanja a zuciyata duk da wannan abin da kika yi" ya fada yana waving hannunsa around cikinta ba tare da ya kalli cikin ba, naji zuciyata ta tattare ta dawo wuyana, na nade hannuna a kirjina nace "what do you want, Mukhtar?" Ya dago kai yana kallon cikin idona, nima ban dauke nawa ba, yace "you know exactly what I want" nace "no, I don't. Just skip the whole preamble ka gaya min direct. Menene kake bukata daga gare ni". Ya sauke idonsa kasa yana hadiye yawu yace "idan kin amince ..... A matsayi na na dan'uwanki na jini, ina so in kin haihu, zan taimaka miki in aure ki, har abada babu wanda zai san me ya faru. Har abada babu wanda zai san me kika yi" na kankance idona a kansa nace "Mukhtar, a tsakanin ni da kai tabbas akwai wanda yake bukatar taimako, kuma daga ni har kai mun san waye". Na juya da sauri na bar inda yake, raina a matukar bace, blindly nake tafiya ina magana da kaina kasa kasa, ban ankara ba sai gani na nayi a gaban Uncle Ahmad, na dan ja baya sannan na gaishe shi a diririce "uhmm. Uncle. Ina kwana" yana danna wayarsa ya amsa. "Lafiya" har na wuce shi sai kuma na tuna da alkawarin da nayi wa twins dan haka na dawo da baya. "Uncle.....dama ina so zanyi maka magana ne ... Dazu munyi magana da twins akan cars din da nace a siya musu. Shine nace bara in tuna maka maybe ka manta ne". Wani mugun kallo daya watso min ne ya saka a lokaci daya naji ina ma dai jiya da na kwanta bacci yau ban tashi da rai ba. Na ja da baya taku biyu cikin sauri dan a tunani na rufe ni zaiyi da duka amma instead sai yace cikin daga murya "Safiyya? Yanzu rashin kunyar taki har ta kai haka dama? Zamani har ya kai haka lalacewa? Ke sam baki ma damu da wannan abun kunyar da yake jikin ki kike yawo da shi ba har kina da karfin halin tsayawa a gaba na da abun kunya a jikin ki kina bani umarni?" Na juya da sauri na yi gurin motar mu ina jin kafafuwa na suna harhadewa a cikin juna, ina kuma jin idanuwan duk mutanen da suke gurin a kaina. Kafin in kai mota hawaye sun jika fuskata, ta gefen idona na ga twins sun taho gurina amma sai nayi sauri na bude kofar gidan gaba na shiga sannan na rufe da karfi, still ina cigaba da jin muryar Uncle Ahmad yana cigaba da fadar bakaken maganganu a kaina. "Kaf dangin mu ba'a taɓa yin irin wannan abun kunyar ba. Saboda daurin gindi amma wai har tazo ta tsaya a gaba na tana gaya min maganar banza" na saka hannayena duk biyun na toshe kunnuwa na tare da kifa kaina akan dashboard ina cigaba da rusa kuka kamar wadda aka aikowa sakon Daddy ya bar duniya. A cikin kuka na naji shigowar Mommy cikin motar ta zauna a baya tayi min magana amma banji me tace ba, sai dai na dago kaina na fara kokarin goge hawayena. Yaya Mustapha yazo ya bude daya kofar bayan ya taimaka wa Daddy ya zauna sannan ya rufe ya dawo seat din driver ya zauna. Na cigaba da ƙoƙarin tsayar da kuka na dan sam bana son Daddy ya san abinda ya faru ballantana ransa ya baci. Sai dai yaya Mustapha yana tayar da motar naji Mommy tace "ki daina wannan kukan haka tun kafin ki saka wa kanki wata cutar kuma, ki gaya wa Daddyn ku abinda ya faru" nayi shiru ban ce komai ba, sai naji muryar Daddy yace "menene ya faru?" Na sake yin shiru amma kuma sai hawaye na ya dawo sabo. Ya sake magana cikin tsawa "magana nake miki Safiyya, menene ya faru?" Cikin kuka nace "Uncle Ahmad ne yayi min hayaniya a cikin mutane" yayi shiru kamar bai ji ne nace ba, sai kuma yace a hankali "me yace?" Nayi shiru a raina ina jin nauyin maganar. Mommy tace "zagin ta yayi, ya goranta mata akan abinda ya same ta, a gaban duk yaran gidan nan" Daddy ya sake yin shiru, amma duk da ban kalle shi ba nasan ransa yayi matukar baci, ni kuma abinda nake gudu kenan. Har yaya Mustapha ya ja mota sai Daddy yace "tsayar da motar nan Mustapha, zo ka kama ni in fita". Nayi sauri na juyo ina kallon sa hankali na a tashe. "Daddy please" Mommy ma ta rike hannun sa da sauri. "Dan Allah kar ka fita, dan Allah kar ka kula shi. Abinda yake so kenan dama. Mu lafiyar ka tafi mana komai. He isn't worth it. Ko babu komai yanzu mun san inda ya sa gaba". Daddy ya karbe hannun sa da ta rike ya kama handle din kofar yana kokarin budewa. Na juya na kalli yaya Mustapha cikin tashin hankali nace "rufe lock ɗin. Ja motar mu tafi" yayi abinda nace muka bar harabar gidan a guje. Har muka yi nisa babu wanda ya kuma yin magana. Sai daga baya naji Daddy yace "Mustapha kira min Ahmad a wayar ka ka bani shi" na dafe kaina. Ba zai hakura ba dai. Wata irin zuciya ce da Daddy da sam baya barin magana ta wuce sai ya rama. Ina kallo yaya Mustapha ya daukl wayar sa yayi dialing sannan ya saka a kunnen sa, aka dauka sai yace "Uncle Ahmad, Daddy ne yake son magana da kai" sai kuma ya mika wa Mommy wayar ita kuma ta bawa Daddy, ya karba direct yace "kar ka biyo ni airport, bana son rakiyar taka. Allah yayi min komai, bana bukatar komai daga gare ka". Daga haka ya ajiye wayar. Mommy tace "kash. Ni dai ban so ka kula shi ba wallahi" amma a raina sai nayi mamakin abinda yasa naji kamar farin ciki a cikin muryar ta. Bamu jima a airport ba aka kira jirgin mu, na rungume twins da suka biyo mu har airport a baya muka yi sallama, na tabbatar sunyi sallama mai kyau da Daddy sannan nabi bayan yaya Mustapha da yake tura Daddy a wheelchair zuwa cikin jirgi. Sai dana tabbatar Daddy ya zauna comfortably sannan na nemi seat dina na zauna nima tare da sauke ajjiyar zuciya. Bamu dade da zama ba jirgin ya tashi, daga can nesa dani na hango wata ta kankame hannun kujerarta. Nayi murmushi tare lunshe idona ina kallon seat din kusa dani wanda babu kowa a kan sa. Sai kuma na tuno da fuskar sa jiya. How hurt and broken he looked. Na kuma mayar da idona na rufe a fili nace "I am sorry Muhammad. Ina yi maka son da ba zan iya staining white din ka da datti na ba. Allah ya baka ikon cin wannan jarabawar. Allah ya baka wadda ta fini". Sai kuma naji ina jin kishin wadda Muhammad zai samu bayan yayi healing daga abinda nayi masa. Ina kishin rayuwar da zasu yi. Rayuwar da Gidado ya shirya mana zamu yi ni da shi, yanzu dole da wata zaiyi. Dole da wani zanyi. Zuciya ta naji tana tafasa, gashi na kasa cire tunanin daga cikin ta. Na dauko headphone a handbag dina na saka a kunne na na kunna karatun Alkur'ani tare da rufe idona a hankali ina motsa bakina ina bin kira'ar, da fatan zai sanyaya min zuciya ta. Ban san tsahon lokacin da na dauka a haka ba naji an taba ni. Na bude ido naga Mommy a tsaye a gaba na, tayi min murmushi sannan ta taba wuya na tana testing temperature dina. Sai kuma ta zauna a kujerar kusa dani tace "nace Mustapha yazo ku zauna tare ya debe miki kewa yace in ya zauna ma faɗa zakuyi" nayi shiru bance mata komai ba ido na a kasa. Ta cigaba "me yasa kuke rigima ne kullum wai Safiyya? Akwai abinda yake yi miki wanda ba kya so? In akwai ki gaya min ni zanyi miki maganin sa kinji?" Na gyada kai na kawai bance komai ba. Sai tace "ki je gurin Daddy, yace yana son magana da ke". Na mike da sauri tare da cire headphone ɗin kunne na na ajiye, ta rike hannu na "ki bi a hankali kar ki fadi" na sake gyada kai sannan na wuce na tafi inda Daddy yake. Ina zuwa ya dago kai daga karatun magazine din da take hannunsa, ya kalle ni, kallon da ya fi min ciwo akan komai sannan ya mayar da idonsa kan takardun hannunsa yace "seat" na zauna a kujerar da Mommy ta tashi daga kai ina wasa da yatsun hannuna ban ce komai ba. Ya ajiye magazine din yace "kin dai san maganar da nayi miki akan aure ko?" Na gyada kai, yace "baki da baki?" Na amsa da sauri. "na sani Daddy" yace "good. Da nayi niyyar sai dai kawai kiji an daura miki aure, banyi niyyar sanar da ke komai a kai ba. Amma ban san me ya hani ni yin hakan ba. Ban san me yasa nake tausayin ki ba, duk da kuwa cewa ke ba kya tausayi na, ko kadan" bance komai ba, dan ji nake yi duk duniya tayi min kunci. Jin banyi magana ba sai ya cigaba. "Ina tunanin mahaifiyar ki ce. Memory dinta ne yake hunting dina yake hanani aiwatar da duk wani hukunci da nayi niyyar yankewa a kanki. Komai nayi niyyar yi sai inyi tunanin in tana raye zata yarda? Kullum sai nayi tunanin in tana raye wanne hukunci zata dauka akan ki" ya yi ajjiyar zuciya yace "but I guess I will find out soon enough" na dago kai da sauri na kalle shi amma sai yayi sauri ya juya kansa gefe, ya cigaba "babban burina kafin in tafi din shine in ga rayuwar ki ta daidaita, yadda at least ubangiji zai rangwanta min akan  laifin negligence a kula da amanar da ya bani, yadda at least zan samu abinda zan gaya wa mahaifiyar ki idan na haɗu da ita a can". Na goge hawayen kan kuncina a hankali na fadi kalmomin da suka zamar min kamar karatun sallah a cikin watannin nan "Daddy I am sorry". Ya cigaba "wannan dalilin ne yasa nake son yi miki aure as soon as possible. Bana so in tafi ba tare da na yi miki aure ba Safiyya. Bana so in tafi ba tare da rayuwar ki ta daidaita ba. Wannan shine abinda nake tsoro fiye da mutuwar ita kanta" yayi ajjiyar zuciya ya cigaba "nayi magana da likitan da zai cigaba da dubaki a Germany, ya gaya min cewa zasu iya cire cikin idan yayi wata bakwai ba tare da illa ga ke ko babyn ba. Wannan shine abinda za'a yi. Ina so a rabaki da cikin nan ina raye. Sai dai kuma ban san yadda zanyi da babyn ba idan an cire shi. So for the last time ina sake tambayar ki Safiyya, waye uban cikin nan?". Na girgiza kai na da sauri amma na san yin shiru na zai kara bata masa rai, kamar yadda nasan abinda zan fada ɗin shima bata masa ran zaiyi. "Daddy wallahi ban sani ba" na fada cikin rawar murya. Yayi ajjiyar zuciya. "I thought as much. Kamar yadda na fada, ni ina tausayin ki amma ke ba kya tausayi na. Okay let's assume gaskiya kike faɗa. Ba ki san waye ba. Amma ai na tabbatar da cewa kin san waye saurayin nan naki ko? Ko shima ba ki san shi ba" na girgiza kaina sai kuma nace "na san shi Daddy " yace "okay, let's go over the whole story kamar yadda kika bamu. Kince a ranar da abin ya faru you were with him throughout the evening, har dare kuna tare. Haka ne?" Nace "haka ne" ya cigaba "da dare you look him to an eatery. Kuka ci abinci tare daga nan sai aka kira ki, someone claiming to be Mustapha, and that's when it happened. Ko?" A hankali nace "haka ne" yace "okay let me break it down for you maybe ko zaki iya bude idonki beyond soyayyar da kike yi masa ki ga gaskiya. You told him cewa a ranar zan zo gari. Haka ne?" Nayi tunani, tabbas na gaya masa, we were so excited saboda na gaya masa a matsayin another birthday gift da zan bashi, zan kai shi gurin Daddy idan yazo. Nace "haka ne" yace "kuma shi kadai kika gaya wa ko kin gaya wa wani?" Nayi tunani, ni bani da wasu friends da nake wata personal magana da su, na girgiza kai na "ba wanda na gaya wa" Daddy yace "good. And ya san bani da lafiya?" Nan ma na amsa in the affirmative. Ya kuma tambaya "kuma ya san kina da dan'uwa Mustapha, ya san tare zamu taho da shi?" Nayi shiru a raina bana jin dadin direction din da wadannan tambayoyin suke tafiya. Ya katse min tunani na "yes or no" nace "yes, ya sani" yayi murmushi "tambaya ta karshe. Sanda aka kira ki aka yi pretending to be Mustapha, yana zaune a gurin ko ya tashi?" Nayi shiru ban ce komai ba, zuciyata tana bugawa kamar zata bar kirjina. "Answer me!" Ya fada da muryar fada. Na tuno abinda ya faru a lokacin, muna zaune aka kira Gidado a waya, ya dauka baya jin abinda ake cewa sai ya tashi looking for network, and then my phone rang. Na lumshe ido na a hankali nace "baya gurin, ya tafi yin waya" Daddy ya sake yin murmushi yace "and you still think ba shi ya kira ki ba? You still think ba shi bane ba?" Na girgiza kaina "Daddy bashi bane ba" Ya dafe kansa da hannu daya, ina jinsa yana karanto addu'a a hankali, maybe addu'ar Allah ya sanyaya zuciyarsa kar ya rufe ni da duka a cikin jirgi. Ya bude idonsa at last yace min "okay. A cikin biyu akwai daya. It is either duk wannan labarin da kike bayarwa karya kike yi, ko kuma kin san shi ɗin ne and you are doing everything in your power to protect him" na sake girgiza kai stubbornly "bashi bane ba" "Tashi ki bani guri" Daddy ya fada cikin tsawar da nasan mutanen gurin sunji. Na mike da sauri jikina yana rawa, sai kuma yace "A cikin mutum uku ina so ki zabi daya. Ko Mustapha, ko Mukhtar, ko Abdul". Na durkusa a kusa da kafarsa ina kallon yatsun hannuna bance komai ba, tunani na yana rarrabuwa. Farko nayi tunanin already Daddy ya yanke hukuncin aura min Mustapha, tunda har shi kansa Mustapha din ya shigo dakina jiya yana min kurari akan hakan, Safina ma kuma tayi min magana akan hakan in another way, ashe su maganganun su kawai suke yi Daddy bai tsayar da magana ba, ban taba tunanin zai bani zabi ba, ban saka ran zai bani zabi ba, dan haka ban auna choices ɗin nawa ba. Nace "ko Mukhtar ko Abdul, duk wanda zuciyarka tafi amincewa da shi Daddy, ko ba su ba ma kowane ne, anyone but Mustapha. Dan Allah banda Mustapha" "Zauna" yace min yana sake nuna kujerar da na tashi daga kai. Na koma na zauna. Ina ganin yana kokarin daidaita numfashin sa sannan yace "me yasa kika ce banda Mustapha?" Nayi shiru ina wasa da yatsun hannuna. Ba zan iya gaya masa dalili ba, kamar yadda na zan iya gaya masa dalilin da yasa na dage akan ba Gidado bane uban cikina. Akwai wadu abubuwan da ƴa ba zata iya gayawa mahaifin ta ba, mahaifiyarta ta ke bukata, ni kuma bani da ita. Jin nayi shiru ya cigaba. "Mahaifiyarsa tana kaunarki sosai. Ta kuma dora ranta sosai akan auren ku. Asalima dagewarta akan abun yana daga cikin dalilin da yasa na baki zaɓi dan na fara tunanin wani abu daban. Amma kuma Mustapha is like a son to me. No na bashi tarbiyya, kuma yanzu ni nake morar sa fiye da wanda ya haife shi. Shi nafi tunanin zai rike min ke amana akan sauran. Musamman yanzu after what Ahmad did to you". Jin bani da niyyar yin magana ya sake cewa "tashi ki tafi". Na mike na koma gurin da na zauna da farko, na tarar Mommy tayi bacci, na gyara mata kwanciyar ta sannan na zauna na mayar da headphone dina ina lissafa maganganun da muka yi da Daddy. Naji dadin zancen cire wannan kaddararren cikin da yace za'a yi at seven months, meanin6ina da sauran just a month and a half tare da cikin kenan. Na biyu kuma hujjojin da Daddy yake neman kafawa akan Gidado. Daddy was right, kowanne evidence yana pointing directly at Gidado, amma bashi bane ba, na sani in my bones and soul cewa bashi bane ba, amma bani da shaida. How I wish cewa shi ɗin ne ma. It would have made all these easier for everyone. ****.    ****.     ****.    ****     ****.    **** Ina yan kasuwar mu wadanda suke son samun more visibility for their kasuwanci? ina masu neman followers a social media pages din su? To ga dama ta samu. Ku sani cewa mai talla shi ke da riba. Come and advertise with me and I assure you that you will get value for your money. No matter how big your business is, dole kina bukatar advertisement dan samun cigaba a kasuwancin ki. Kar ki manta, hatta manyan companies irin su CocaCola, Apple, Dangote etc kullum suna cikin tallan hajar su so why not you…. Duk wanda yayi sponsoring episode zan yi masa tallan business dinsa in the episode which will be posted on whatsap, facebook, intagram and wattpad, zan kuma saka number dinsa da kuma links na social media accounts din business din sa, zanyi posting pictures and links din on my whatsaap, facebook and intagram stories for 24h. Kar ku manta, the advert on the pages will last for as long as social media exist, that means forever. I will come up with a method da zan tabbatar you get value for your money, in sha Allah. [07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: ❤‍🩹*Safiyya*❤‍🩹 *By* *Maman Maama* Daga marubuciyar: Maimoon A'isha Humaira Diyam Tagwaye Jidda And now..... Safiyya *Episode Four: The Choices 2* For sponsorship, contact 0704 203 0419 on whatsap or send a dm to my Instagram page https://www.instagram.com/maman.mamas.words?igsh=MW5yaXFqOHhubnIwaQ== Save my business number 0704 203 0419 and say hi on whatsap dan inyi saving naku. Please, dan Allah, abeg, ban da kira ****. ****. ****. ****. ****. **** Awa 8 da rabi mukayi muna tafiya kafin mu isa garin Berlin, Germany. Daddy ya zaɓi Berlin ne saboda anan ne babban abokinsa Uncle Sufyan yake zaune da iyalinsa. Akwai kuma likitan da ya kware akan ciwon Daddy wanda zai kula dashi a tsahon lokacin da zamu zauna a can. It was almost 8 o'clock pm when we landed a birnin na kasar Germany. Already muka tarar da Uncle Sufyan da dansa Abdul suna jiran saukar mu a airport. Muna haduwa da su Uncle Sufyan ya tarbe ni da murmushi "Safiyya, as beautiful as ever" na sunkuyar da kaina ina murmushi sannan na gaishe shi, duk sanda muka hadu dashi haka yake yi min, ya amsa tare da miƙa wa Daddy hannu at the same time yana cewa "duk sanda na ga Safiyya sai na tuna da Safiya, a rear gem. Har yanzu banga mace irin ta ba. Allah ya kai rahama kabarin ta". Mommy tace "Ameen ya Rabbi. Safiyya is a photocopy of her ai" Daddy ya dago yana kallo na yace "anya kuwa, sunyi kama dai a fuska, amma hali kam basu da dangantaka" na kalle shi muka haɗa ido nayi sauri na mayar da ido na ƙasa. Abu biyu na karanta a idon Daddy a lokacin, akwai grief, wanda duk sanda akayi maganar ta sai na ga yanayin sa ya chanja, wannan yana daga cikin abinda yake kara min fahimtar irin soyayyar da yayi mata, yadda har yanzu, more than 20 years da rasuwar ta, amma bai daina jin mutuwar ta ta ba. Abu na biyu kuma wanda yafi daga min hankali shine disappointment. Daddy was really disappointed in me. Gani yake kamar duk duniya bashi da wani disappointment da ya wuce ni. Naji duk gwuiwowina sun sage, kamar kullum naji babu abinda nake so irin barin duniyar. A lokacin babban concern dina shine Allah ya sa hijab dina ya boye cikina tunda bani da tabbas din hosts din mu sun san da maganar cikin or not. Daga nan muka wuce zuwa inda suka ajjiye motar su, sai da muka je na fahimci cewa motoci biyu suka zo dasu. Daddy ya juyo yana kallona yace "ki shiga motar abdul ya kai ki gidan su ki huta, mu zamu wuce asibiti" na tsaya ina kallon sa idona yana cikowa da hawaye dan naso ace na bishi asibiti anyi komai a gabana, amma kasancewar yanzu bana iya yi masa musu sai nace "okay Daddy". Na tuna da Safiyyan da, da ace seven months back ne, da zan iya rusa kukan da zai tara masa mutane a airport din idan yace ba zan bishi ba. Da ba karamin aikina bane in zauna dirshan a kasa in rike kafafuwansa ina kuka da dukkan karfina, amma yanzu sai nayi taku biyu baya na tsaya ina kallon sa ina kokarin rine kuka na. Ina kallo aka saka Daddy a bayan mota daya, Mommy ta shiga kusa da shi, yaya Mustapha ya shiga gaba sannan Uncle Sufyan ya zauna a drivers seat, aka barni a gefe ina rarraba ido. Mommy ta sauke glass ta ce min "ki kwanta ki huta in kunje, ki sha maganin ki kuma, zan zo gidan in anjima" na gyada mata kai, Daddy kam ko kallo na bai yi ba suka tafi. Sai da motar su ta bar gurin sannan Abdul ya ce min "okay. Daddy's girl. Nasan yanzu zaki kama kuka. Let me take you home tun kafin ki rikice min". Na goge hawayen da ya fito tare da ƙirƙirar murmushi nace "I am not crying" yace "of cause you are not. Maybe someone is cutting onions around". Ya bude min kofar motarsa na shiga sannan ya rufe ya zagaya ya shiga side din driver muka dauki hanya. A hanya yana ta kokarin nuna min gurare amma ni bani da wani interest akan buildings and monuments dinsu, rayuwa ta kawai nake lissafa wa. Har sai da muka yi packing a gaban gidan su sannan ya juyo yana kallona yace "Safiyya, I want to use this opportunity da muke alone muyi magana. Magana nake so muyi as civilized people. Daddy na yace wai sun fara magana da Daddyn ki cewa akwai yiwuwar zasu yi mana aure" yayi shiru yana so yaga reaction daga gare ni sai yaga babu komai, ya cigaba, "so you knows about it kenan. Look, I want you to understand cewa I have nothing against you as a person, I like you. You are very beautiful and intelligent and I am very sure that akwai maza da yawa da suke layi suna son ki zabe su as your life partner. You can have any man you want. Wannan yasa na kasa gane dalilin su Daddy na bullo da wannan maganar. Gaskiya ni dai I don't want arrange marriage. Na fi son inyi aure for love. And I am sure ke ma haka. I know yadda daddyn ki yake son ki ba zai taba yi miki dole ba, and that's why I am begging you. Please idan an tambaye ki kice ba kya sona kamar yadda nima zanyi kokarin nunawa nawa daddyn haka. Let's join hands and fight this battle together. In kika yi min haka I will forever be grateful to you. I am sure kema kina

Chapter 4 of 14