Share this page
later in life. And it did ... Sai dai kuma bashi da tabbas din zata ma tuna da shi ballantana har ta gane shi. Yayi reversing motar a hankali still yana kare mata kallo dan ya tabbatar da cewa ita din ce dan kar yaje yayi wa wata magana. Sai dai yana zuwa saitin ta sai ta kara yin gaba kamar bata san mota ta tsaya a gaban ta ba. Ya bude kofar motar ya fito still idonsa a kanta. Yana jin zuciyarsa wani iri dan shi dai bai taba ganin macen da ta yi masa kyau kamar ta ba, bai kuma taba tsayar da mace a hanya yayi mata magana ba. Ta ƙara bata rai tare da juya fuskarta daya side ɗin, daga alama kallon da yake yi mata ya dame ta. Ya tako zuwa gabanta, sai ta zaro wayar ta ta fara dannawa kamar bata san dashi a gurin ba. Yayi mata sallama. "Assalamu alaikum" ta amsa, amma shi kansa da yake kusa da ita motsawar bakinta kawai ya gani amma baiji muryar ta ba. Ya danyi shiru yana tsoron kar ta wulakanta shi amma kuma yana son gwada sa'ar sa, ya dan leka fuskarta a hankali yace "Piya?" Ta dakata da danna wayar da takeyi ta dago kai tana kallon sa da alamar tunani a fuskarta, lokaci daya kuma sai yaga recognition a fuskarta, and farin cikin da yaji a ransa was more than he thought. "Malam Muhammadu dan fillo?" Yayi dariya, dariyar da yaji ts wanke dukkan tsoronsa. Ta nuna shi da dogon yatsan ta "Washington DC" ya girgiza kai "no. Manchester" tace "yeah. Right. Manchester. What are you doing here? How are you here?" Yace "ke zan tambaya. Never thought I will ever see you again" tace "me too. It has been five years?" Yace "seven" tace "wow. How time flies. Kayi girma sosai" ta fada tana kallon sa tun daga kan takalmin kafarsa har zuwa yalwatacciyar sumar kansa da bai rufe da hula ba. Ya shafa kansa "ke ma haka". Suka yi shiru duk su biyun, kowanne su trying not to look at the other. Sai kuma suka kalla a tare, suka hada ido, and then they smiled together. "uhmm ...... Trouble with the car?" Ya tambaya yana nuna motar da take tsaye a gabanta. Ta bata fuska "wallahi... Ta mutu.... I don't know why. Ina tafiya kawai ta mutu. Na kira kuma an hada ni da mechanic har yanzu kuma bai zo ba" yace "why not leave the car here in yazo ba sai ya dauka ba. You shouldn't be here standing under the sun" ta daga mishi key din motar "sai yazo zai karbi key ai" ya girgiza kai "still sai yaje gida ya karba. You shouldn't be here alone" tayi ajiyar zuciya bata ce komai ba. A hankali yace "can I take you home?" Ta juya ta kalli motar ta, sannan ta kalle shi fuskarta kamar zata yi kuka, yace "sai in dawo wa da mechanic ɗin key din, in bai zo ba kuma I can get another one for you" ta girgiza kai "ba wannan ne damuwa ta ba. Uncle Ahmad will kill me today. Yace kar in fita da mota. Yace ban iya mota ba. Baya son a bani mota ni kuma so nayi in nuna masa na iya" Gidado ya mika mata hannu yace "mu ga key din" ta bashi, hoping motar lafiyar ta kalau itace dai bata iya din ba. Ya bude ya shiga yayi ƙoƙarin tayar da ita amma sai yaji yana murda key din tayi wata irin kara. Ya fito yana kallon Safiyya yace "key starter din ta ta lalace. Maybe kinyi ta murda key din ne" ta fara bubbuga kafa a kasa "to ba ita ce taki tashi ba" yayi dariya "tuba take yi. Now call the mechanic and tell him key starter issues ne, tell him kuma zaki tafi gida yazo gida ya karbi key ɗin". Tayi abinda yace sannan ya bude mata passenger's seat din motarsa ta shiga ta zauna shi kuma ya zagaya ya shiga seat din driver. Suna kama hanya ya lura duk ta zama uncomfortable, sai yayi kokarin yi mata hira "you look good. You look really good" ta danji kunya "thank you. You too" yace "so... how have the 7 years been going?" Tayi ajjiyar zuciya "like the blink of an eye" yace "na dauka ba zaki gane ni ba fa, I was praying kar ki yarfa ni" tace "nayi niyyar yin hakan fa. But sai kuma ya kasance kai ne. Ni ma nayi mamaki dana gane ka. Amma kai ya akayi ka gane ni?" Ya daga kafada "ina da saurin gane mutane. Besides, I have thought about you a lot within these years. Ke fa" tace "ina tuno da kai ne kawai idan na shiga jirgi na hadu da me aerophobia" suka yi dariya a tare. Wayarta tayi kara, ta dauka. Shi kuma ya samu damar cigaba da kare mata kallo "Yaya Mukhtar na bar gurin fa. Na kira shi nace ya same ni a gida. Alright. Don't tell Uncle please. Thank you". Ta ajiye wayar tare da ajjiyar zuciya yace "I like the way you talk" ta juyo tana kallon sa tace "what?..." Ya maimaita "I like the way you talk. I am not sure if it is the way your lips moves or the sound of your voice or the body language, ban sani ba. I just like it. It is therapeutic" ta sunkuyar da idonta kasa tana murmushi, ya kara da cewa "and the way you smile too". Sai ta ja mayafin ta ta rufe fuskarta. Ya tsaya yana kallon dogayen yatsun hannunta. Aka kira wayar sa, ya dauka direct yace "kai na fasa zuwa fa. And don't call me again". Ta bude fuskar ta tana murmushi tace "babu kyau karya alkawari fa" yace "ba alkawari nayi ba  fa. Besides, there is no where I would rather be then here". Motarsa ce tayi wata yar kara sannan ta mutu. Suka juya suka kalli juna. Yayi kokarin sake tayar da ita amma taki tashi. Safiyya ta rufe fuskarta tana dariya yayin da shi kuma ransa in yayi dubu ya baci. Ta bude fuska tace "it is official. Yau da rashin sa'a na tashi" ya juyo yana kallon ta yace "ni kuma yau sa'ar dana tashi da ita bata ma misaltuwa". Tace "I am not sure. Maybe this is a sign that we are not meant to be together" ya bude kofa ya fita yana girgiza kai da sauri. "No. This is a sign that we will walk the path of Destiny together" ta fito itama tace "walking? Not driving" yace "I am ready to do it if you are" ta saka hannu tana kare rana tace "under the sun?" Ya zagayo gaban ta ya tsaya, jikinsa yayi blocking mata hasken rana yace "I will shield you". Suka fara tafiya a hankali, side by side, enjoying each other's company, breathing in each other's scent, suna kuma updating juna akan abubuwan da suke faruwa a rayuwar su. A lokacin ne ya gaya mata karatu dama yaje yi Manchester, kuma ya gama degree dinsa na daya dana biyu, ya kuma yi service. Ya kuma sanar mata da bukatar mahaifinsa akan yaje yayi aiki a ƙarƙashin sa, da kuma shi burinsa na yayi aiki a sabuwar jami'ar da baban masa da siblings dinsa suka bude in memory of mahaifinsu ambassador Muhammad Dikko, M.D University Abuja "ina so nima in bayar da tawa gudummawar wajan kafa jami'ar". Ta fahimta, sannan itama ta bashi nata labarin. Family dinta mazauna garin Kano ne. Ta gama Sec school dinta three years back, amma kuma sai babanta ya fara rashin lafiya. Jinyar sa ya saka bata fara jami'a ba saboda basa zama a kasar ko da yaushe suna yawon kasashe neman magani, sai yanzu ne yayi insisting dole ta dawo Nigeria ta zauna a gidan Uncle din ta anan Abuja ya nema mata admission a daya daga cikin manyan private universities ɗin da suke garin. Last week ta zo garin. Kuma already ta gaji da garin. A lokacin suka kai karshen junction ɗin suka hau kan babban titi. Suka tsaya suna kallon juna yace "we did it. The path was rough, tiring and very sunny. But we arrived at the destination, together" Kafin tayi magana mota ta tsaya a gabansu. Aka sauke glass din wani ya leko "Fiyya. There you are. Na kasa hakura shine na biyo bayan ki. Let's go home kafin ya dawo ya ga bakyanan" tayi ajjiyar zuciya, daga alama ranta bai so haka ba. Ta so su ci gaba da tafiya a kafa ita da shi. Duk da dai cewa a kwai wahala, but with him by her side, zata jure. Ta juya tana kallon Muhammad tace "cousin dina ne. Gidan su na sauka. Kafin kazo dazu shi na kira na gaya masa inda nake" Ya gyada mata kai "go" tace "okay. Zamu yi magana" yace "yes. I will call you" ta danyi shiru tana kallonsa. Ya sake ce mata "go... Rana tana dukan ki. It is not good for your skin" tayi murmushi. Ya bude mata kofar motar. Har zata shiga ta kuma juyowa tana kallon sa tace "are you not forgetting something?" Yayi shiru yana tunani sannan yace "no. Me na manta?" Tayi murmushi tace "I don't know. Kawai ji nayi kamar kayi wata mantuwa" na motar ya leko. "common. Let's go sauri nake yi fa" ta shiga reluctantly ta zauna, Gidado ya ja baya tare da yi mata alamar I will call you. Ta yi murmushi. Sai da motar tasu ta ja sannan hankalin sa ya dawo jikinsa. Sannan ya fahimci abinda take cewa ya manta. "God damnit" ya fada da dan karfi. "Damnit" Ya maimaita yana saka yatsun hannunsa duk goman a cikin gashin kansa yana jin kamar ya fincike gashin ya zubar. Bai karbi number wayar ta ba. ****.    ****.    ****.     ****.    ****.    ****.    Ina yan kasuwar mu wadanda suke son samun more visibility for their kasuwanci? ina masu neman followers a social media pages din su? To ga dama ta samu. Ku sani cewa mai talla shi ke da riba. Come and advertise with me and I assure you that you will get value for your money. No matter how big your business is, dole kina bukatar advertisement dan samun cigaba a kasuwancin ki. Kar ki manta, hatta manyan companies irin su CocaCola, Apple, Dangote etc kullum suna cikin tallan hajar su so why not you…. Duk wanda yayi sponsoring episode zan yi masa tallan business dinsa in the episode which will be posted on whatsap, facebook, intagram and wattpad, zan kuma saka number dinsa da kuma links na social media accounts din business din sa, zanyi posting pictures and links din on my whatsaap, facebook and intagram stories for 24h. Kar ku manta, the advert on the pages will last for as long as social media exist, that means forever. I will come up with a method da zan tabbatar you get value for your money, in sha Allah. [07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: ❤‍🩹*Safiyya*❤‍🩹 *By* *Maman Maama* Daga marubuciyar: Maimoon A'isha Humaira Diyam Tagwaye Jidda And now..... Safiyya *Episode Six: Mother* For sponsorship, contact 0704 203 0419 on whatsap or send a dm to my Instagram page https://www.instagram.com/maman.mamas.words?igsh=MW5yaXFqOHhubnIwaQ== Save my business number 0704 203 0419 and say hi on whatsap dan inyi saving naku. Please, dan Allah, abeg, ban da kira Free page...... Knocking kofa ne da dawo dashi daga tunanin da yake yi. Ya mike ya koma kan kujera ya zauna yace "yes". Mama ce ta turo kofar amma sai ta tsaya daga bakin kofa tana karewa dakin kallo tace "ina Al'ameen ɗin? Ko ya fita bai yi min sallama ba" Gidado yace "ya fita, maybe ba kya kusa" ta karasa shigowa da bacin rai a fuskarta tace "ko bana kusa ai sai ya neme ni, saurin me yake yi? Ni fa na kira shi kuma sai ya tafi ba tare da na sallame shi ba" Gidado bai ce komai ba amma ya san shi ya jawowa Al'ameen wannan fadan tunda shi yace kar ya gaya mata maganar da suka yi, ya san kuma Al'ameen ya gudu ne dan baya so ta tambaye shi ya suka yi. Ta shigo ta zauna akan gado tana kallon sa tace "ya jikin?" Ya ajiye carbin hannunsa tare da safa addu'a a fuskarsa yace "da sauki Mama, kar ki damu da ni. Zan je asibiti anjima" ta bata rai "in kaje asibitin me zaka ce musu? Ji nake dazu da na tambaye ka abinda yake damunka cewa kayi kwakwalwar ka ce take ciwo, haka zaka ce musu a asibitin? ta yaya zaka ce kar in damu? Ki yadda ka koma cikin kwana biyu, me yasa ba zan damu ba? Akan ka aka fara faɗa da budurwa ne wai?" Gidado ya dago kai yana kallon ta, ya bude baki sai kuma ya mayar ya rufe. Shi bai san me zai ce mata ba. Baya son ya gaya mata abinda ya faru tsakanin sa da Safiyya saboda baya son ta tsani Safiyyan, duk kuwa da cewa bata san ta ba. Wannan shine zurfin soyayyar da yake yi mata. Yin shiru sa ya saka ranta ya kara baci. "Kai ba zaka gaya min ba kuma shima dana turo ya tambaye ka ya tafi bai gaya min ba. Wani abu ne mai muni ya faru? Ko wani laifin ka aikata kake boye min?" Yayi saurin girgiza kai tare da bude ido "no, Mama babu abinda nayi fa. Babu abinda ya faru, kawai bana jin dadi ne. Kuma zanje asibiti in an jima". Ta dauki wayarsa daga kasa ta mika masa tace "idan har babu wani abu da ya faru kira Safiyya ka bani ita mu gaisa" ya rike wayar yana jujjuya ta. "Bata kasar, kiran ba zai shiga ba" tace "WhatsApp call nko? Shima ba zai shiga ba? Ko kuma da ta tafi wata kasar a matsayin ka na mai neman aurenta bata baka layin da take amfani da shi a can ba?" Ya ajiye wayar akan cinyarsa tare da sunkuyar da idonsa kasa, abubuwa da yawa suna yawo a ransa. Ta kuma daukan wayar and kafin ya fahimci me yake faruwa sai ta kama hannunsa ta saka fingerprint dinsa ta bude wayar. Ya dago kai da sauri yana kallon ta, trying to process abinda yaje faruwa "Mama! Mama Please don't!" Ta juyo tana kallon sa tace "ko zaka kwace wayar ne? Ko kuma akwai abinda kake boyewa ne wanda baka son in gani? I cannot just seat idle and watch you turn into this, sai dai in abinda yafi karfina ne". Yayi shiru tare da saka hannu biyu ya dafe kansa, shi dai yasan babu wani abin ashsha da yake cikin wayarsa wanda ba zai iya budewa a gaban ta ba, abu daya ne baya so ta gani wanda kuma ya san shine abinda take after, chats dinsa da Safiyya. Tun shekaran jiya Safiyya tayi blocking din calls dinsa, amma kuma ta manta bata yi blocking dinsa a WhatsApp ba, wanda dama shine kadai social media app din da yake yi anan ne kuma suka fi yin hira. Tun shekaran jiyan kuma yake tura mata sakonni, amma ya fahimci kamar data dinta a kashe take gaba daya dan sakonnin basa zuwa gare ta, amma hakan bai hana shi rubuta wa ba, hakan bai hana shi gaya mata duk abinda yake zuciyarsa ba, all the things that he wanted to say to her, hoping that zata bude ta karanta ko da ba yanzu ba ne ba. Ya tabbatar kuma idan Mama ta karanta sakonnin zata fahimci gaskiya abinda ya faru tsakanin sa da Safiyya, zata fahimci cewa Safiyya matar aure ce kuma har tana dauke da ciki. Bata jima tana danna wayar ba kuwa ta ga abinda yake boyewa, tun daga expression din fuskarta ya gane ta gani.  Da sauri take karantawa harshenta har yana hardewa. Wadansu maganganun a fili wasu a zuciyarta. Har tazo kan wanda ya warware mata warware mata damuwarta ya kuma ɗora mata wata damuwar data ninka waccan. "I only want to know me yasa kika yi min haka, me nayi miki da zaki yi min haka, how can you let me fall this deeply in love with you alhalin kina matar aure?" Mama ta saki wayar daga hannunta ta fadi akan carpet, "Muhammad!" Ya jawo hannayensa daga kansa ya rufe fuskarsa da su yana jin wani zazzaɓi mai zafi yana saukar masa. "Matar aure fa Muhammad. Yanzu Gidado dama da matar aure kake tare? Matar wani?" A muryar ta yana jin irin zafin da yake zuciyarta and how much disappointed she was in him. Ya zame daga kan kujerar ya sauko kasa "Mama.... Mama wallahi..... Na rantse miki wallahi ban sani ba" ta mike tsaye sannan ba tare da tace komai ba ta yi hanyar fita. Ya mike shima ya bita a baya da sauri "Mama, Mama" bata waiwayo ba har suka zo suka wuce Mufida a falo , Mufida ta bisu da kallo cikin tunanin abinda ya faru, har sai da ta shiga dakin ta sannan ya samu ta juyo ta kalle shi, sai dai ganin hawaye a idonta ya saka ya ji kafafuwansa sun kasa daukan sa. Ya zame ya durkusa a gabanta "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Mama dan Allah kar kiyi kuka a kaina. Wallahi ban san tana da aure ba. Boye min tayi" ta juyo da tsawa tace masa "ka tashi ka fita ka bani guri, ka tashi in daina ganinka a gaba na kar kasa inyi maka abinda ni da kai gabakidaya zamuyi nadama" ya mike da sauri ya fita, ta turo kofa ta rufe, amma sai ya kasa tafiya ya jingina da jikin kofar sannan ya zame ya zauna a gurin, babu abinda bakinsa yake furta wa sai innalillahi wa inna ilaihir rajiun, shi kansa ya kasa tantance me yake faruwa da rayuwarsa, a cikin kwanaki biyu rayuwarsa ta juya daga good zuwa bad and now it has turned to terrible. Tun tasowarsa he has always been Mama's boy, akwai shakuwa da fahimta sosai a tsakanin sa da ita. She raised him and his siblings with love, da soyayya ta raine su da soyayyar kuma ta tarbiyyan tar da su. Tun tasowarsa kuma ba zai iya tuna ranar da ya ganta cikin bacin rai irin na yau ba. He has always been a good boy. Da wahala yayi laifin da zata daga masa murya ma ballantana har ta kai ga zubar da hawaye a kansa. Ya tuna da maganar da Ya Ameen ya fada masa dazu, cewa Safiyya is not worth bacin ran iyayensa, a lokacin maganar bata dake shi sosai ba sai yanzu da yaga bacin ran na gaske. Yana nan zaune har Mufida da ta ji su shiru ta taso ta biyo bayansu, a lokacin ne ta ganshi a zaune a kasa a kofar dakin Mama, hankalin ta ya tashi dan bata taba ganin yayan nata a cikin irin wannan halin ba. Ta durkusa a gabansa tare da dafa kafadarsa "Hamma? Lafiya? Me yake faruwa?" Ta fada muryar ta tana rawa kamar zata yi kuka. Ya dago jajayen idonsa yana kallon ta yace "Mufida. Kiyi min addu'a. In kinyi sallah kiyi min addu'a" ta rike kukan da yake neman kwace mata tace "kullum ina yi maka addu'a dama Hamma, amma yau zan tashi cikin dare zanyi sallah musamman dan kai, zanyi maka addu'a, insha Allah Allah zai yaye maka dukkan damuwarka". Ranar cin abincin daren su sam bai yi armashi ba a gidan. Dan yau damuwar Gidado tafi ta kullum yawa, Mama ma kuma juya abincinta kawai take yi ba ci take ba. Daga baya ma sai ta tashi tace musu zata je ta kwanta. Gidado ba haka yaso ba, so yayi tayi masa fada, so yayi ta gayawa Abba in yaso sai ya samu damar yi musu bayani tare da kare kansa, amma maimakon haka sai ta bashi silent treatment. Kwanan su biyu a cikin wannan yanayin. A rana ta biyun ne Gidado ya samu Mama a kitchen tana aiki tare da Mufida ya ajiye mata wayarsa. "Mama dan Allah in ba zaki saurare ni ba ma fa wayar tawa nan ki duba, ki karanta sakonnin gabaki daya zaki fahimci gaskiya ta" ta juyo ta kalle shi, zuciyarta tana yi mata zafi akan yadda dan lelen dan nata ya koma saboda mace, tace "bana bukatar duba wayarka, na riga naga abinda nake bukatar gani. Kaje kawai, zanyi addu'a akan ka zan kuma yi tunani, sannan zan gayawa mahaifinka halin da kake ciki dan ya damu da ya sani, abinda duk muka yanke a kanka kuma dole shi zaka bi". Ya gyada kai cikin amincewa. Shi indai zata daina fushi da shi to kowanne hukunci ne ya yarda zai dauka. Washegari ya fahimci cewa ta gaya wa Abba abinda ya faru, dan sanda ya gaishe shi bayan sun dawo daga masallacin sallar asuba kin amsawa yayi, rana ta farko a rayuwarsa daya gaishe da mahaifinsa bai amsa masa ba. Wannan ya sa a ranar ko dakinsa bai koma ba anan falo ya kwanta anan falon yana jiran Abba ya shirya ya fito ya sake gwada sa'ar sa ko zai samu ya kula shi, yayi masa fada, kai ko dukansa ne ma ya yarda yayi in dai zasu daina fushi da shi. Yana nan kwance Mufida ta fito, yaji tazo tana taba wuyansa sannan ta koma suka dawo tare da Hafeez, yana ji suna ta maganganun su sannan Hafeez din ya tafi suka dawo tare da Abba. Yaji Mama tazo itama. Ya tashi zaune yana jin sanyin acn falon tayi masa yawa a jikinsa. Abba ya aika Mufida yace ta kawo masa abinci daga nan kuma sai ya sallame su ita da Hafeez. Gidado ya dauki cup din tean da aka ajiye a gabansa ya kai bakinsa amma bai kurba ba sai ya ajiye shi, pretending kamar yasha. Mama tace "dauki ka shanye" babu musu ya dauki kofin ya shaye tas duk da kona mishi baki da yake yi. Abba ne yayi magana yace "mamanka ta bani wani labari da ban taba tunanin jinsa ba. Tace min yarinyar da kake ta maganar za'a je nema maka auren ta, Safiyya, matar aure ce, haka ne" Gidado ya gyada kai, har lokacin zuciyarsa ta kasa sabawa da jin sunan Safiyya tare da kalmar matar aure a hade a sentence daya. Abba yace "to me zaka ce game da haka?" Gidado yayi gyaran murya yace "ban san haka bane ba. Sai last gani na da ita take gaya min hakan" mama tace "take gaya maka me?" Yace "tace min..... Tace she is married". Abba ya gyara zama "amma kai tun da kuke da ita ba ka taba gane cewa matar aure ba ce ba? Ta yaya? Kana me zata ninke ka a baibai tsahon lokaci baka gane ba? Wanne irin so kake mata da zai rufe maka ido from the obvious?" Gidado yace "Abba ban san ya zanyi bayani ku gane ba. Da ace kun santa zaku fi yarda da magana ta. Babu wani alamun aure a tare da ita. Ban taba zuwa gidan su ba ballantana in gane daga nan...." Mama tace "baka taba zuwa gidan su ba? All these while har ka yi gini ka saka ni hada kayan lefe amma baka taba zuwa gidan su ba?" Gidado ya dafe kansa "how foolish he might have looked a idon iyayensa, how foolish duk wanda yaje abinda ya faru zai dauke shi, amma kuna it is easy to judge idan har abin bai faru da mutum ba. Yace "Mama, Safiyya student ce a MD, a hostel take zaune, asalin iyayenta yan Kano ne, mahaifinta ba mazauni bane kusan ko da yaushe baya kasar. Duk sanda akayi hutu itama tana binshi whichever kasa yake a lokacin. A cewar ta kullum tana kokarin samun chance idan yazo gari ta kaini. Tace bata son kaini gurin kaninsa, wanda yake zaune a garin nan, tafi so in ganshi direct because of some family issues that she didn't mention. I didn't push sosai saboda baban bashi da lafiya, kusan ko da yaushe yana asibiti. She ......" Mama

Chapter 7 of 14