maka zani a kasuwa sannan kuma yazo gida yace zai daura maka? Na dauka ma maganar wannan marar kunyar yaron zai yi miki. Wannan yaron ko maye ne shi to sai dai yaci kansa wallahi dan kin fi karfin sa".
Haka ta cigaba da maganganun ta ni dai har na gama cin abinci na na kammala shiryawa ta. Sannan ita na taci muka fito muka yi wa Aunty Hajjo sallama muka tafi. Tun a mota ta bawa Mustapha labarin nayi waya sa Uncle Ahmad, ina jinsa yana bata hakuri wai kar ta sawa kanta damuwa shine maganin daga Uncle Ahmad ɗin har Mukhtar. Ni dai bance musu komai ba duk kuwa da kokarin saka ni da suke yi a cikin maganar.
Muna zuwa asibitin muka tarar an yi discharging Daddy. Sun gama bashi duk wani treatment ɗin da zasu bashi babu kuma sauran wani abu da zasu iya yi masa. Wannan shine dama mostly abinda ake yi masa a duk asibitocin da muke zuwa. Sai dai suke mana muje gida in wani symptom din ya sake bayyana ko wani ya zama worst sai mu dawo. Amma cutar sa babu magani. Har yanzu ba'a samu maganin ta ba. Sai a lokacin nake jin ashe Daddy ya saka an kama mana apartment din da zamu zauna kafin sanda za'a yi min aiki. Plan dinsa dama shine in an sallame shi mu samu gida mu zauna baki daya har sai na rabu da cikin jikina sannan zamu koma Nigeria. Damuwarsa kuma har lokacin ita ce bai san yadda zaiyi da abinda za a ciro daga cikin nawa ba and definitely baya son mu zauna tare da abinda zan haifa. Bai san already na samo solution to that ba.
Sai da na bari ya tura Mustapha ya karbo sauran magungunan da akayi masa prescribing, Mommy kuma ta fita gurin nurses zata yi making some inquiries sannan na jawo kujera kusa da shi kaina a kasa nace "Daddy, Uncle Ahmad yace yana ta neman ka a waya baya samun ka". Ya bata rai "ina ganin kiran nasa ai. Me zai ce min? Ban dauka yana daga cikin wadanda zasu goranta min a duniya idan wata kaddara ta fada min ba". Na girgiza kaina "ba gori yayi min ba Daddy. Faɗa yayi min" ya dauke kansa yace "haka yace miki kenan? Da ke yake so yayi amfani ya dawo gare ni kenan. Na riga na yanke hukunci, in Allah ya sauke ki lafiya mun koma Nigeria zan karbe komai namu da yake hannunsa. In kinyi aure lokacin your husband can take care of everything for us" naji hawaye yana taruwa a ido na. Na sake cewa "Daddy, duk duniya fa bamu da wanda ya fishi. Blood is thicker than water" yayi dan karamin murmushi "haka yace miki?" Na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsuna ban ce komai ba. A lokacin na kammala yanke hukunci na. Na dago kai nace "Daddy na yanke shawara, akan zabin da ka bani"
Ya juyo yana kallona amma bai ce komai ba.
Nace "na zaɓi Mukhtar. Mukhtar zan aura".
****. ****. ****. ****. ****. ****.
A bangaren Gidado ya dan samu sauki, ba wai saukin zafin da zuciyarsa take yi masa ba sai dai yanzu iyayensa sun dan sauko duk da dai basu dawo yadda suke da ba. Still suna blaming dinsa for being negligent, for being vulnerable, for letting a small girl toyed with his emotions. Two days after zaman da suka yi dashi ne suka sake kiran sa suka gaya masa hukuncin da suka yanke a kansa.
"Ba za'a fasa haɗa bikin ka da na Mufida ba kamar yadda muka yi niyya. You are going to get married"
Ya dago kai yana kallon su, feeling confused. Abba yace "ka duba cikin yan'uwa, tun daga yalleman zuwa Kano zuwa Abuja, ka fitar da mata, cos you are getting married in the next two months".
Ya juya yana kallon Mama, hoping ko zai samu wani hope daga gare ta, amma sai ya ga taki yarda su haɗa ido kuma a duk sanin da yayi wa iyayensa duk maganar da daya yayi to dayan ma ita yake goyon baya.
Abba ya cigaba da magana "believe us Muhammad, it is going to be the best thing that has ever happened to you. Duk kan mu mun san bayan abinda yarinyar can tayi maka, it will take time for you to heal and trust women again, and from our experience, the best feeling ever is to fall in love after marriage. And it is the most easiest. To make things easier for you, mun baka zabi. Choose wadda duk kake ganin zaka iya so later on, mu kuma zamu yi wa iyayen ta magana and if bata da wanda take so, shikenan"
Gidado ya sake juyawa ya kalli Mama, ta fahimci yana bukatar ta, tayi ajjiyar zuciya tace "It is going to be okay Gidado. Wannan shine decision ɗin mu. Kuma sai da mukayi dogon tunani kafin mu yanke shi. And ba zamu taɓa yin abinda zai cutar da kai ba. Kuma in kayi biyayya a gare mu ba zaka taba nadama ba"
Ya sunkuyar da kansa kasa a zuciyarsa yana hoping ina ma dai shi mace ne, ina ma dai zai iya zama yanzu a gaban iyayensa yayi ta rusa kuka har sai sunce sun janye hukuncin da suka yanke.
Jin yayi shiru ya saka Mama ta sake cewa "ina fatan yarinyar nan bata saka dafinta a zuciyar ka har level ɗin da zai kai ka ga bujirewa maganar mu ba".
Ya dago kai yana jin zazzaɓi yana neman rufe shi yace "ɗan Allah Abba, ina neman alfarmar a bani lokaci in yi...." Mama tace "dawa zaka yi shawarar? Da ita?" Ya girgiza kai da sauri "ba da kowa zanyi shawara ba Mama. Zan dan tattauna maganar ne da zuciya ta. I just want to have some time to think " Mama ta sake cewa "babu komai a zuciyar ka Muhammad sai soyayyar waccan matar. I have seen the kind of messages da kake tura mata. I have read yadda kake begging dinta kamar wadda take rike da ranka a hannunta" ta karasa maganar cikin dacin murya and he can literally feel irin tsanar da take yi wa Safiyya.
Abba yace "tomorrow. You have until tomorrow".
Ya maimaita "tomorrow. Okay" sai kuma ya mike da sauri ya fita waje. Sai da yaje wajen sannan ya tuna babu abinda zaiyi a wajen. Babu gurin wanda zai je wanda zai iya hana iyayensa abinda suka yi niyyar yi. His grandparents will definitely back his parents up musamman in suka ji abinda ya faru, his auntie and uncles too, and then marriage proposals will start flying from alla angles. Babu irin tunanin da bai zo kansa ba. If only he can see Piya maybe he can convince her leave her husband tazo su yiwa iyayensa karyar cewa maganar da ma ba haka bace ba misunderstanding aka samu, and then get married.
Sai kuma ya dafe kansa yana tunanin ta yadda aka yi ma har yayi irin wannan tunanin. Lallai soyayya babu abinda bata sakawa dan a lokacin abubuwa kadan ne ba zai iya aikatawa ba dan ya samu Safiyya. Love yana kokarin turning the good boy he is into a bad boy. Ya dauko wayarsa and for the nth time ya kira number ɗin Safiyya.
"Common Piya" ya fada yana jin ransa yana kara baci. How can you love and hate someone so fiercely at the same time?
Ya buɗe motarsa ya shiga, ya kalli side ɗin da take zama hoping to see her appear ko da na second daya ne. Sai kuma ya dauke kansa ya tayar da motar ya fita daga gidan a guje. Sai dai kuma shi kansa bai san inda zaije ba. Bai san abinda zaiyi ba. MD University ya dosa, the first time da ya shiga tun ranar da suka rabu da Safiyya. Kamar yadda yayi tsammani babu mutane sosai a cikin makarantar saboda dalibai suna hutu, but yana hoping wanda yaje nema yana nan. Ko baya nan ma zai nemo shi duk inda yake. File din Safiyya yake so a dauko masa, address din ta yake so a bashi, kano zai je a yau yaga babanta or her husband, whatever the case maybe. In yaje sai ayi duk wacce za'a yi.
Ya dauko wayarsa da niyyar kiran wanda zai karbi informations din a hannun sa, sai dai garin neman number ɗin ya lura da notification din da ya shigo masa wanda bai ma lura da sanda ya shigo ba. A message from Piya 💝.
Wani faduwar gaba yaji, and then cikin rawar hannu ya bude message ɗin ya karanta.
"Dear Muhammad. I am very sorry for what happened. Please find it in your heart to forgive me ko ba yanzu ba. But for now, please stop trying to contact me. And don't look for me dan Allah. I have made a mistake naci amanar mijina with you. Now I have repented bana son in kara aikata kuskuren da na aikata a baya".
"Mijina bai san abinda nayi ba and I want to keep it that way. Bana son in breaking heart dinsa because I love him so much. Please, do not break up ny happy home. You will soon get over me and move on as I have gotten over you".
"Dan Allah, for the sake of the love that you have for me. Don't let my husband know".
Ya maimaita jaranta message din ya kai sau uku, sai ya rufe shi ya sake budewa hoping it will disappear amma still yana nan.
Wayar ta zame daga hannun sa ta fada kan kafarsa, yayinda shi kuma ya saka hannu biyu ya rungume kirjinsa dan ji yake yi kamar zuciyar sa zata fito. Sai kuma ya kifa kansa akan stirring motar.
Ya jima a haka kafin da dago, ya kunna motar ya jata a guje ya fita kamar yadda ya shigo a guje. Ya jima yana zagaya gari ba tare da yasan inda zashi ba, har sai da yaga rana tana neman faduwa sannan ya doshi gida, zuwa lokacin already ya yanke decision ɗin sa.
Yana shiga gida ya samu Mama a zaune a falo suna hira da Mufida. Suka bishi da kallon mamaki da kuma tausayin yanayin sa. Ya zauna daga can gefe sannan yace "Mama na yanke shawara akan maganar da kuka yi min dazu" ta gyara zama tana kallon sa tace "ba sai gobe ba?"
Yace "babu bukatar hakan. Babu bukatar jiran gobe. Babu abinda zan chanja tsakanin yau da gobe. Na amince da maganar auren da kuka yi. Allah ya sa albarka. Amma ina neman alfarma guda uku. Na farko ina so ku zaba min da kanku, bana jin zan iya zaba da kaina. Na biyu ina son dan Allah duk wadda zaku zaba ya zamanto ta amince da kanta ba takura mata aka yi ba, zan so kuma ace tana sona ne dama, at least that will make things easier. Na uku, Please, kar ku zaba daga cikin yan'uwa, nafi son bare".
Mama ta bata rai tace "why not? Me yasa bayan muna da yammata masu hankali da tarbiyya da ilimi, wadanda kuma muka yarda da su muka yarda da asalin su sai mu tsallake su mu tafi nema a wani wajen? Ta yaya gida bai koshi ba zamu bawa daji?"
Ya girgiza kai "Mama, there is a chance that this may not work. And I value zumuncin mu da yan'uwan mu a lot that bana son in zama sanadin samun sabani tsakanin mu. Please ku nema min bare yadda ko ba'a dace ba effects din ba zai zama da illa sosai ba".
Mama tace "to ni yanzu Muhammad ta ina zan fara nema maka mata a cikin dan lokacin da muke da shi. Yaushe aka samu matar har aka yi neman auren da bincike da komai?"
Mufida da take kwance tana jin su ta mike zaune tace "Mama in kin yarda akwai friends ɗina. Akwai wallahi da yawa da sun sha yi min maganar suna son sa ni kuma ban taba yi mishi magana ba saboda nasan ba kula su zai yi ba. Idan kin yarda sai in bashi pictures din su ya zaba, duk yayan manyan mutane ne, babu kuma wacce iyayen ta ba zasu iya aurar da ita a cikin wata biyu ba"
Ya sake cewa yana kallon Mufida"I don't want to choose" shi a cikin zuciyar sa gani yake yi kamar idan ya zaba yace ya zabi wance kamar yaci amanar Safiyya ne.
Mama ta kalle shi kawai tayi ajjiyar zuciya, bata jin zata daina tsinewa yarinyar nan.
Mufida ta sake cewa "to bara in nuna wa Mama ta zaba maka ita, ta san most of them already, har iyayen su ma ta sani" ta fada tana dauko wayarta. Sai kuma ta tsaya kamar wadda ta tuno wani abu tace "oh my God. Oh my God" Mama da Gidado duk suka juyo suna kallon ta. Gidado ya juya mata hannu alamar tambaya, ta koma ta zauna sosai tace "akwai wata yarinya, kusan shekara guda kenan tana yi min naci akan in haɗa ta da kai" ya bata rai yace "wacece?" Tace "I don't know her. Kawai a one of the northern blogs na Instagram naga ta tura irin hide my ID post din nan da hoton ka, wai tana cigiyar ka ko kuma wanda ya sanka, wai tana son ka. I commented cewa kai yayana ne amma already kana da wadda kake so. She followed me into my DM tana ta yi min nacin in bata ko da number din ka ne ta gwada sa'ar ta, na gaya mata ba zaka kula ta ba taki yarda, I gave her your number dan ta tabbatar da kanta. She later told me ta kira ka baka dauka ba, she sent you a message kace mata tayi hakuri kana da wacce kake so and you blocked her " Gidado yayi shiru yana tunani, ba zai iya gane wacece ba because a lot of that scenario has happened, yammata da yawa sukan gwada sa'ar su a kansa and all the times ya kan basu hakuri and then blocked them dan baya son ciwon kai.
Mufida ta cigaba "tun lokacin bata hakura ba. Har daina daukan wayarta nayi na kuma daina replying messages dinta amma bata daina kira na da kuma turo min sako ba. She even sent me some of her pictures wai in nuna maka. And she is beautiful gaskiya. Daga alama kuma yar manyan mutane ne ce. Let me see it I still have the pictures" ta fada tana bude wayarta
Gidado ya mike tsaye "unknown girl. With no link or connection to the family. She is perfect. Call her and ask her if she is still interested. And if she can get married in the next two months. Then get her information. Duk abinda ta gaya miki sai ki gaya wa Mama" ya juya ya fara tafiya zuwa bangaren sa.
Mama ta daga murya tace "haka kawai kake tunanin zamu aura maka yarinyar da ba'a san asalin ta ba, daga haduwa a social media?" Ya juyo yace "in akayi bincike za'a samo asalin ta. In asalin baiyi muku ba sai Mufida ta samo wata unknown din"
Yana jin ta tana cigaba da magana amma baya fahimtar me take cewa. Tafiya kawai yake yi yana jin zuciyarsa tana breaking into thousand pieces.
****. ****. ****. ****. ****. ****.
Assalamu alaikum masoya littatafan maman Maama, babu abinda zan ce muku sai godiya sai kuma ban hakuri. I have not been doing well with posting Safiyya na sani, and it has gotten worst. A yanzu haka kuma dole in sake baku hakuri dan zan ɗan dakata da rubutun Safiyya saboda abubuwa da yawa da suka sha kaina wadanda ba yadda zan yi da su.
Kuyi hakuri, kuyi hakuri, kuyi hakuri....
Dani da Safiyya da Gidado muna baku hakuri.
We will resume insha Allah as soon as nayi clearing issues ɗin da suke gaba na.
Please ku taya ni addu'a, I really need it because I am faced with one of the toughest challenges dana taba fuskanta so far. Allah ya bani sa'ar abinda yake gaba na a yanzu.
We will see the end of Safiyya together insha Allah.
Wadanda suka fara biyan sponsorship in suna sauri ne suyi min magana for a refund.
Nagode. Ma'assalam
[07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: *❤🩹Safiyya❤🩹*
*By*
*Maman Maama*
*Episode Eight: The Acceptance*
Free Episode
*Her🧕🏻*
Ya dago kai yana kallona da fuskar mamaki, nayi sauri na mayar da nawa idanuwan kasa tare da rike numfashi na dan na san abinda zai biyo baya "Mukhtar?" Ya tambaya cikin mamaki "Mukhtar fa kika ce? Are they blackmailing you? Cewa suka yi in baki aure shi ba zasu gaya wa duniya abinda kika aikata?" Na fara girgiza kaina amma ban ce komai ba, na fahimci dama tunda yana jin zafin uncle Ahmad dole zaiyi retaliating akan zabin nawa duk kuwa da cewa shi ne da kansa ya lissafa min har da Mukhtar din a cikin options dina. Amma ban dauka zai dauki zafi haka ba.
Cikin fada ya sake tambaya ta "baki bani amsa ba, are they threatening you?" Mommy ta shigo da takardu a hannun ta, ta tsaya tana kallon sa sannan ta kalle ni cikin alamar tambaya, ban ce komai ba ta mayar da tambayar ta kansa. Cikin dacin rai ya nuna ni yace "wai Mukhtar. Wai Mukhtar zata aura"
Ta zame ta zauna akan kujera tana dafe kirjin ta "na shiga uku ni Sa'adatu. I thought you hated that guy. You said it yourself several times." A hankali nace "I never hate him, he is my cousin. I just don't love him. Kuma har yanzu bana son sa. Bana masa soyayya irin ta aure amma duk kunsan cewa shi yana so na and at least that is something". Mommy ta nuna waje da hannun ta "and so does Mustapha. In dai soyayya ce Mustapha yafi Mukhtar son ki. Yafi su son mahaifin ki da yanuwanki. Yafi kowa dace wa da auren ki. Da kika ce ba zaki aure shi ba na dauka Abdul zaki aura knowing fully well cewa ba kya son auren Mukhtar. Ashe zaki iya zaben wanda kika ambata xewa ba kya so akan Mustapha? Gwara kikai kanki inda na tabbatar ba son Allah da Annabi suke miki ba akan ki zauna a inda za'a fi ko ina mutunta ki?.........."
Ta cigaba da fada muryarta har shakewa take yi yayin da ni kuma na saka hannayena biyu na toshe kunnuwana tare da rintse ido na. Da bi ar da nake yi a duk sanda ake kokarin chanja min ra'ayi akan abinda na riga na yanke shawara akan sa. Sai da naji na daina jin muryarta sannan na dube ido na ina kallon Daddy shima yana kallo na idonsa cike da mixed emotions. "Wani abun Ahmad ya gaya miki a waya sanda ya kira ki wanda ya saka kika yanke wannan hukuncin?" Ya tambaya muryarsa da sanyi akan dazu.
Na girgiza kaina tare da goge hawayen da bansan sanda na fara zubar da su ba nace "bani da wani zabin ne Daddy. Ba zan iya auren Mustapha ba. Abdul baya sona. Bazan iya auren wanda nake so ba. Bani da zabi Daddy" ya gyara zamansa "waye wanda kike so ɗin? Ki gaya min waye shi ni kuma zan aura miki shi in dai har na bincike shi naga ya chanchanta. Zan aura masa ke kuma in mayar masa da ɗan shi. Waye shi?"
Na mike tsaye "ba ɗan shi bane ba Daddy. Ba ɗan shi bane ba. Ban san waye uban ɗan ciki na ba amma ba nashi bane ba. Ba zan makala masa laifin da nake da tabbas ɗin ba shi ya aikata ba. Ba zan bata tsakanin sa da iyayensa in kuma bata masa suna a gari ba"
Ya dafa kujera ya mike shima, bacin rai yana sake dawowa fuskarsa "kina da shaidar cewa ba shi bane ba kenan? In har ba ki san waye ba zai iya zama shi ɗin ne kenan. Wato da ki bata tsakanin sa da iyayensa gwara ke kin bata da naki iyayen ko? Da ki bata masa suna gwara kin bata naki sunan kin zauna da tabo na har abada a tare da ke, gwara kin auri wanda ba kya so wanda shima kuma ba son Allah da Annabi yake yi miki ba, gwara kin zauna da ɗan da in ya girma ya tambaye ki waye ubansa baki da amsar da zaki bashi ko? Gwara kinyi watsi tare da fatali da duk sacrifices da mahaifiyar ki tayi domin ki, domin ki samu kyakkyawar rayuwa ko? She gave you everything, she gave her very life for you". Ya karasa cikin daga murya.
Nace "but I never ask for it. I never ask for any of this. I wish she didn't do what she did. I wish she let me die"
Na juya da sauri na fita daga dakin ina kuka, ina jiyo muryar sa yana kwalla min kira "Safiyya, come back here" ban waiga ba ballantana in koma.
A waje na samu kujera na zauna na kife kaina ina cigaba da rusa kuka na. Har cikin zuciya ta a lokacin fata nake ina ma dai Ammi bata yi duk abinda tayi ba. Da yanzu ban samu kaina a cikin wannan matsalar ba dan ko shakka babu abinda tayi din shine silar shiga ta halin da nake ciki.
Ina cikin kukan naji an zauna a kusa da ni. Ban dago kai ba thinking wani stranger din ne. Sai da naji an ambaci sunana "Fiyya?" Na dago kai da sauri na kalli side ɗin, duk da kuwa na gane muryar wanda yayi min maganar tun kafin in kalle shi. "Fiyya what happened. Me ya saka ki kuka har haka?" Na saka hannu biyu ina goge fuskata duk kuwa da cewa ba tsayawa hawayen suke yi ba.
"Fada muka yi da Daddy " na fada cikin sheshshekar kuka. Ya gyada kai "yes. Ina tsaye ai kika wuce ni baki ganni ba. Amma Fiyya mai zai kai ki fada da Daddy a halin da yake ciki? A halin da kike ciki? Me ya haɗa ku" ya fada yana miko min hanky. Na karba tare da kokarin tsayar da kuka na. Ya sake cewa "talk to me.... At least let it out of your chest " na girgiza kaina "ba zaka gane ba Abdul" ya gyara zaman sa "Try me. Wata kila zan gane har ma in baki shawara. And just so you know, Mama ta faɗa min komai a kanki. She told me about your situation. She said she wants me to marry you" na juyo ina kallon sa na fahimci da gaske yake abinda ya fada, but I still noticed the sadness in his eyes.
Na danyi murmushin tausayin rayuwata nace "Allah sarki Aunty Hajjo. Lallai ta cika kawai kwarai. Ammi would be very proud of her" yayi ajjiyar zuciya "yeah. I guess so" nace "but I will not marry you Abdul" ya jiyo da mamaki, nace "na riga na yanke shawara, Mukhtar zan aura. Hakan shine sanadin fadan mu da Daddy. And I am not changing my mind. Tunda ai shi ya bani options ɗin kuma na zaba" ya danyi shiru yana tunani sannan yace "but why him? Me yasa kika zabe shi? Why not me?" Nace "I am not sure why. Kawai dai nayi addu'a and naji a raina shi ya kamata in dauka. And personally, na farko I believe yana so na da gaske. Cos ya jima yana ta bina da maganar soyayya ina ƙi, nacin da yake yi min da kuma goyan bayan sa da uncle Ahmad ya fara yi shi ya saka na bar gidan su da zama a Abuja na koma hostel. Shi kuma Daddy ya goya min baya yace ba za'a yi min dole ba. Wannan shine silar fara rikici tsakanin Daddy da uncle. And secondly, ina ganin auren mu zai gyara tsakanin Daddy da dan uwansa. He needs him a yanzu. Su biyu iyayensu suka haifa, bashi da kowa sama da shi" Abdul ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 14