dai kasan mu mata muna da son yabawa, and when I walked in I noticed kana ta kallona, I thought na samu wani bangare na zuciyar ka" ya juya yayi hanyar fita, har ya kai bakin kofa sannan ya juyo yace mata "I was looking at you because I thought you were someone else, it turned out ba ita ce". Sai ya juya ya fita.
A waje ya hango Al'ameen yana waya, ya tafi gurinsa ya tsaya har ya gama, ya fahimci cewa da matarsa Humaira (read *Aisha Humaira*) yake magana saboda yadda yake ta zabga murmushi shi kadai, love is truly the most beautiful feeling ever. Sai da ya gama sannan ya juyo yana kallon Gidado yace "wai fitowa kayi ka bar ta ita kadai?" Yace "kai ma ba fitowa kayi ka bar ni ni kadai da ita ba?" Al'ameen ya danyi dariya "guri fa na baku ku gaisa sosai" Gidado yayo dan karamin tsaki "I can't stay inside with her. It is suffocating".
Haka suka cigaba da tsaiwa a waje duk su biyun, har sai da Mustaphan da ya dauko su dazu yazo yayi musu magana sannan suka koma ciki tare, basu tarar da ita ba. Ya zauna ya saka su a gaba sai da suka dan ci abinci kadan sannan ya nuna musu toilet suma yi alwala suka zo suka yi sallah, daga nan kuma ya fita sai gashi sun dawo tare da manya su biyu, wadanda duk suka baiyana wa su Gidado kansu a matsayin wan baban Safina da kuma kanin sa, suka tabbatar musu da cewa suna goyon bayan auren suka kuma bawa Gidado assurance ɗin cewa ba zai samu matsala da Safina ba.
"Tun tana jaririya mahaifinta ya rasu. Ni na rike ta tamkar ni na haife ta, ko bayan aure gurin na zaka zo akan duk wata bukata, kar ka yarda wani daga baya ya fito yazo yace maka shine yake da iko a kanta. Mune dangin ubanta mune komai nata" Babban cikin su ya faɗa. Da zasu tashi Al'ameen ya ajiye musu kudi masu kauri yace su sayi turare
Sai da zasu tafi sannan Gidado ya tuna da sakon ta da Mama ta bashi ya kawo mata, ya mika wa Mustaphan da yake tare da su yace ya kai mata, yayi dariya "kai dai kawai kace inje in kira maka ita kuyi sallama" ya kira wata yarinya "je ki cewa Safina tazo angonta yaƙi tafiya yace sai ya ganta".
Ba'a jima ba ta fito, ta yafa mayafi sosai wannan karon ta rufe jikinta. Gidado ya mika mata ledar hannunsa "inji Mama" ta karba tana murmushi "Nagode sosai. Zan kira ta inyi mata godiya" yace "good. Mu zamu tafi. Ki turo min sakon da nayi miki magana a kansa" ta girgiza kai "no ka barshi kawai. I already made plans" ya daga kafada "okay. Alright" har ya juya ssi kuma ya dawo "I just heard cewa babanki ya rasu, you never tell me" ta daga kafada itama "you never ask" yace "maman ki kuma fa?" Tace "tana Abuja. Da ya rasu ta koma gurin sister ɗin ta a Abuja. Yanzu ma tana can. A can zan sauka lokacin bikin. A can zata yi nata taron" ya gyada kai. "Okay. Alright. Am sorry for your lost. Allah yaji kansa" ta langwabe kai "Ameen. Na kusa daina maraici ai. Insha Allah. Am sure mijina zai kula da ni sosai".
Har suka je airport basu yi magana da junan su ba, har jirgin su ya tashi ya kuma sauka a Abuja basu tattauna akan komai ba. Gidado was consumed in his thoughts yayin da shi kuma Al'ameen ɗin ya rabu dashi dan ya fahimci baya cikin mood din maganar. Sai da suka sauka suka shiga mota zasu je gida sannan Gidado yayi wa Al'ameen magana "Ya Ameen, please tell me the truth, do you think I am loosing my mind and imagining things?" Al'ameen ya rage gudun da yake yi yace "i don't think you are loosing your mind. But I believe you are overthinking everything" Gidado yace "then advise me? How can I stop thinking? How can I stop thinking about her?" Al'ameen yace "I am not expert in this thing, amma ina ganin you need to get something that will keep you busy, wani abu da zai dauke maka hankalin ka daga tunani, maybe shine dalilin su Abba na yi maka aure thinking matar zata dauke maka hankalin ka, but I advise ka samu wani abu ka dinga yi, ka daina zama kai kadai, ka gajiyar da jikin ka da ƙwaƙwalwar ka yadda ko dare ne yayi kana kwanciya zaka yi bacci. Sannan get rid of anything da zai ke tuna maka da waccan yarinyar"
Gidado ya danyi murmushi yace "I tried doing that. But she is everywhere. Har cikin bacci na take shiga. I always dream about gani na da ita na karshe. And the more I saw her a cikin mafarkin the more I feel the need to get back to her. Gani nake kamar kokarin mantawa da ita da nake yi yanzu ba dai dai bane ba. Gani nake kamar nayi betraying dinta, she needed me and I shut the door on her face" Al'ameen ya tsayar da motar ya juyo sosai yana kallon sa "I can't believe this. You betrayed her fa kace? How? I thought ita ce ta yaudare ka ta saka kuka yi soyayya alhalin tana da aure? Ko kayi bincike ne ka ga cewa bata da auren karya take yi?" Gidado yace "she is married. Wannan bani da shakku akan sa a yanzu. But ....." Al'ameen ya bude hannu yace "but what Muhammad? She is married and pregnant for her husband. Kai kace min kaga cikin da idonka. For God's sake stop creating things in your head and blaming yourself alhalin kai ne victim din" Gidado ya dago kai yana kallon Al'ameen da wani irin kallo yace "ranar da tazo gurina na karshe, ranar da ta gaya min cewa tana da aure. She looked broken, sad, and devastated. She looked like a shell of her former self. Akwai wani abu da ya faru da ita, wani abu da ya mayar da ita haka. Ba haka take ba. She was the most cheerful person I have ever seen. And sanda na kore ta daga office ɗin, ta tsaya a bakin kofa ta miko min hannu and called my name, kamar tana neman taimako daga gare ni, but i did not listen. I shut the door. And now duk sanda na rufe ido na scene din da nake gani kenan. Har cikin bacci na nake jin tana kiran sunana"
Al'ameen ya dafe kansa tare da rufe idonsa, Gidado yace "you really think I am loosing my mind, right " Al'ameen ya bude idonsa yana kallon Gidado yace "no. I think you love that girl too much, and I think you need to see a therapist, you need to see Mammy".
Gidan su Gidado suka fara zuwa, suka yi packing Gidado ya bude kofa ya fita sai kuma ya dawo ya zauna yana kallon Al'ameen yace "one more question, ka taba ganin Safiyya, do you think she loved me ko kana ganin tun a lokacin she was playing me?" Gidado yace "guy! Anya kuwa kana kallon kan ka a madubi, anya ka fahimci irin haduwar da kayi? Bana jin a duniya da akwai wata ya mace mai jini a jika da zaka ce kana so kuma ya kasance bata son ka. Tabbas a lokacin da na ganku da Safiyya tana son ka. But that doesn't matter now. Don't tell that matter".
Gidado yayi murmushi fuskarsa tana nuna jin daɗin maganar yace "thank you ɗan uwa, I really appreciate this".
Forgive the typos please
Dan Allah kar kuce yayi kaɗan 😅🤫
Littafin Safiyya is 500 naira via
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Send the evidence via telegram or WhatsApp to
0704 203 0419
Posting of paid episodes will be on telegram only.
Dan Allah idan da akwai wadda ta turo evidence dinta ban saka ta a group ba should talk to me so that your message will come up.
Nagode sosai. I really appreciate all the love.
[07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: ❤🩹*Safiyya*❤🩹
*By*
*Maman Maama*
*Episode Thirteen: One Day Apart*
Free Episode
Littafin Safiyya is 500 naira via
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Send the evidence via telegram or WhatsApp to
0704 203 0419
Posting of paid episodes will be on telegram only.
Kwana biyu bayan zuwan su Katsina, Gidado ya saka Safina ta turo masa address ɗin matar da aka ce yaje ya gaisar anan Abuja, sunan ta Hajiya, kuma kamar yadda Safina ta gaya masa mahaifiyar ta ma tana tare da Hajiyar a lokacin. Dan haka ya shirya ya ɗauki Haidar suka tafi tare. Tun daga gate ɗin shiga gidan suka fahimci cewa wannan gidan masu kuɗi ne, real kuɗi, tsohon kudi.
A bakin gate mai gadi ya tambaye su gurin wanda suka zo, Gidado yace "Hajiya, ina fatan tana nan ai ko. Am sure ta san da zuwan mu" maigadin yayi murmushi yace "ko sirikin na mu ne? Tun safe Hajiya tace zata yi bako, tace mai neman auren Safina ne zai zo, ai Mommyn Safina ma tana gidan. Allah ya sanya alkhairi ya sa da mu za'a yi" Gidado ya danyi shiru yana kallon sa, babba ne sosai kuma daga ganin sa kasan ya san jiya ya kuma san yau, irin masu aikin gidan nan da suka zama yan gida. Sai yayi amfani da damar sa yayi kokarin sanin wani abu akan Safina. "ka san Safina kenan sosai" mai gadin yace "sosai ma. Safina ai kamar jika take a gidan nan. Mahaifiyar ta ma a gidan nan ta tashi tun tana karama har aka aurar da ita har yau kuma nan shine gida a gurin ta. Ai yayar mahaifiyar ta ce matar gidan nan. Kuma tunda ita ta rike ta sai ta zama kamar ƴa ce a gidan. Safina kuma kaga ta zama jika ce. Kai kuma ka zama sirikin mu. Allah dai ya sanya alkhairi" Gidado yayi murmushi "na kusa zama. Not yet. Nagode Baba. Ameen. Dan Allah a sanar musu mun zo"
Mai gadin ya bude musu gate suka shiga da mota sannan ya kira wata yarinya da tazo wucewa yace ta je ta gaya wa Hajiya baƙin ta sun zo. "Saurayin safina ne?" Yarinyar ta tambaya cikin rada amma su Gidado sunji, mai gadin ya fara yi mata fada "maza ki tafi aiken da nayi miki, ku baku da aiki sai shegen tsegumi".
Su Gidado suka fito daga motar a tare, Haidar ya zagayo side ɗin Gidado yace "tana nan ne?" Gidado ya kalle shi yace "wa?" Haidar yayi murmushi "ita ɗin dai" Gidado ya bata rai "zaka koma gida wallahi" Haidar yayi dariya "wai naga sai wani bobboye ta kake yi ne. I just want to see her in lissafa mata irin abubuwan da nake so da kuma wanda bana so. Kasan ana gama bikin ku can zan koma. Though ba Safiyya bace ba amma wancan alkawarin bai karye ba. Har na zaɓi daki ma" Gidado yace "tsakanin ku ne wannan, ni ina ruwa na?" Haidar yace "to ai baka haɗa ni da ita ba dan haka akwai ruwanka a ciki, dole kai zan bawa sako ka isar mata. Ina fatan ta iya girki, ina nufin girki irin five stars standard ɗin nan".
Kafin Gidado ya bashi amsa aka yi musu magana aka ce su shiga. Suka jera suka tafi, sai Gidado ya samu kansa da murmushi yana tuno irin soyayyar da take tsakanin Safiyya da girki. She and Haidar would have been friends. She even promised him that. Ya tuna da wani lokaci da tayi wannan alkawarin.
****. ****. ****. ****. ****. ***
Waya suka yi da safe a muryarsa ta fahimci cewa he was stressed. Da ta tambaye shi dalili sai yayi mata complain cewa aiki ne yayi masa yawa a office, har zuwa rana ma da suka kara wayar still bai kammala aikin da yake yi ba. Da yamma sai gata ta baro hostel dinsu ta dauko motar ta tazo har office ɗin sa ta kira shi a waya tace ya fito ya ga wani abu. He complain cewa aiki yayi masa yawa amma shi kansa ya san cewa ba'a cewa Safiyya "no" dan yanzu sai ta saka masa kuka. Dole ya rufe office ya fito ya same ta a mota, ta bude masa gaba tace "get in" ya shiga yana kallon ta "what?" Tace "to ka rufe motar mana so kake mutanen da suke waje su ga abinda zan nuna maka. Sirri ne" yayi ajjiyar zuciya "Piya! Aiki nake yi wallahi. Dole a yau zan gama aikin nan kuma ko rabi ban yi ba. Ko kina so a kore ni ne?" Tace "waye zai kore ka? Abba ko uncle Habib? You own dis school. Oya, close the door" ya jawo kofar ya rufe "yes ma'am" sai kawai gani yayi ta saka mota a giya ta fara tafiya, ya bude ido "what are you doing Piya? Ina zaki kai ni?" Tace "I am kidnapping you, kuma sai an biya ni ransom zan dawo da kai".
Ya gyara zaman sa yana kare mata kallo, abaya ce a jikinta da mayafin abayar a kanta. Fuskarta fes babu kwalliya, fatarta kamar kullum tana kyalli da daukan ido. Ta kalle shi ta gefen ido. "ka daina kallo na. Ko so kake inyi tuntube ne" yace "you are driving, not walking " tace "to in na buga motar fa?" Yace "tunda kin hana ni yin aiki na ba gwara in zauna inyi ta kallon ki ba, kar inyi biyu babu" tayi murmushi "believe me, you are going to enjoy this. Zaka gode Allah cewa I kidnapped you today" yace "zan rubuta a diary in ajiye wa yaran mu, in gaya musu maman su taje har office ɗina tayi man-napping ɗina" tayi dariyar kalmar da yayi amfani da ita a dai dai lokacin da suka zo gate din fita daga makarantar.
Sai da suka fita yace "seriously, ina zaki kai mu ne wai?" Tace "park. You need a rest. I couldn't take jin ka a gajiye. It doesn't suit you" ya bude ido "baby ni namiji ne fa? Dole sai nayi aiki. In banyi ba da me zan kula da ke da yaran mu?".
Sai da suka yi nisa sannan ya juya yana kallon seat din baya "wai abinci ne a bayan motar nan? Kamshi nake ji" tace "abinci ne mana. We are going to have a picnic. And I know ko lunch baka yi ba. Ya shafa cikin sa, ko breakfast din kirki bai yi ba kuma yanzu kamshin abincin ya kara masa jin yunwa. Ya juya yana kallon ta yace "you are amazing Piya. Thank you. Zan iya fara ci yanxu?" Ta girgiza kai da sauri "not in my car" ya daga hannu "nayi alkawari ba zan bata miki ba" and he knows he dare not. Dan muguwar tsafta ce da ita. A karshe dai haka ya hakura har suka je gurin. Shi yayi musu shinfida da abin shimfidar da tazo tashi, ita kuma ta jera musu abinci, sannan ta jera masa a plates ta ajiye masa a gabansa.
Farko har zaiyi mata dariyar ta zuba masa da yawa, saboda shi ba mutum ne mai cin abinci sosai ba, amma yana ci tana bashi labarin dramar da ake a hostel dinsu bai san sanda ya cinye ba sai gani yayi tana kara masa.
Ya hadiye lomar bakinsa yana jin daɗin abincin yace "Piya, duk sanda aka yi bikin mu, ina jin Haidar gidan mu zai dawo da zama" tana kallon sa itama tace "saboda me kace haka?" Ya nuna plate din abincin gabansa yace "abinci, saboda kaunar da yake yi wa abinci. Saboda ke kuma kin iya abinci" tayi murmushi fuskarta tana nuna jin daɗin maganar sa tace "bayan bacci, the second thing da na iya a rayuwata shine girki. I can cook. Irin I can really cook" yace "banda yabon kai dai. In mutum ya iya abu ai bari yake yi mutane su yaba ba wai shi ya zauna yayi ta yabon kansa ba" tace "saboda me? Abeg let me brag about my achievement tunda bani da abubuwan bragging for da yawa. I can cook. Na iya girki wato nake gaya maka" yace "there is something else da kika iya kuma ai, wanda ya kamata a baki medal a kansa" ta gyara zamanta tace "what? Tell me please, in kara shi akan list of achievements ɗina a rayuwa" yace "crying. You can cry for Africa. Ni ban taba ganin ma mai saurin kuka irin ki ba". Tayi dariya "haha. Duk kuka na ai mai dalili nake yi, is either an hana ni yin abinda nake so ko kuma an takura min sai nayi abinda bana so. In ba'a so inyi kuka kawai a barni in yi abinda raina yake so" yace "ai na fahimci haka. Kuma na fahimci laifin Daddy ne. Shi ya shagwaba ki beyond repair. Ni yanzu an barni da sabon raino. In mun haihu ban san wa zan goya ba, ke ko yaran" ta bata fuska "wanda kafi so. A lokacin zan gane matsayi na ai" yayi murmushi yana cin burger din daya ajiye masa a gabansa da zafinta, duk kuwa da cewa jin cikinsa yake yi kamar zai fashe. Yace "wai in tambaye ki Piya, yanzu in muka haihu, in yaron yana yi miki kuka ya zakiyi da shi?" Tayi shiru tana tunani sannan tace "zama zanyi nima in yi masa kuka" ya ajiye burger din yana dariya sosai, sai da ya gama sannan yace "I can't wait for that time. You will look so cute with kids" tayi murmushin ta mai kyau tace "I can't wait either. I love kids. Ban san yadda ake musu ba saboda gidan mu babu yara but I will learn. I will be the best Mom ever".
Sai da suka gama cin abincin sannan ya kira Haidar a waya. "albishirin ka. Ka kusa barin gidan Abba. Dan na tabbatar duk sa da akayi bikin mu da Safiyya gida na zaka koma" Haidar yace "saboda me?" Gidado yace "saboda ta iya girki. Kuma tana kaunar girki. She will just keep feeding you har sai ka kasa tashi. Nima abinda ya faru da ni kenan yanzu" sai kuma ya mika wa Safiyya wayar "gashi yace in baki" ta bude ido tana girgiza kai "in kuma suna tare da Mama ko Baba fa? Ai sai suce bani da kunya" yace "shi kadai ne fa" tace "to in ya basu labari fa? In yace musu munyi waya fa?" Gidado yayi ajjiyar zuciya "ba zai fada ba, zan gaya masa kar ya fada" ta langwabe kai "kayi alkawari?" Yace "yes, nayi alkawari" sai ta karbi wayar ta saka a kunnen ta, taji muryar Haidar yana dariya yace "nima nayi alkawari" sai taji kunya ta rufe fuskarta kamar yana gurin. Suka gaisa, yana ta tsokanar ta, sannan a karshe tayi masa alkawari "ka kusa dawowa gidan yayanka da zama. Kai zaka fara zabar daki a gidan. Abinci kuma sai wanda ka zaba za'a ke girkawa a gidan".
Sai da suka gama wayar ta mikawa Gidado sannan taga ashe shi kallon ta yake tayi, ta sunkuyar da kai tana jin kunya yace "you know what? I am glad you kidnapped me. And I am looking forward to you kidnapping me again. I get to look at you instead of papers.
****. ****. ****. ****. ****. ****.
Suna shiga cikin gidan wani katon parlor aka kai su. Suka zauna aka fara hidimar kawo musu fruits da snacks da drinks iri iri. Haidar zai fara ci Gidado ya harare shi sai ya koma ya zauna yana bata fuska. Basu jima ba wata dattijuwar mata ta fito tare da wata yar budurwa, yarinyar ta taimaka mata ta zauna a kasa sai su Gidado suma duk suka sauko suka zauna a kasan. Tace "bana iya zama kan kujera yanzu, ciwon kafa ya sako ni a gaba. Kun san jikin tsufa. Ko da yake ku ba zaku fahimta ba".
Suka yi murmushi sannan suka gaishe ta a tare, ta amsa musu da sakin fuska sosai tare da tambayar su mutan gida. Ta nuna Gidado tace "na gane mai gidan nawa, waccan marar kunyar ai takanas ta aiko min da hotonsa ta waya wai ta samu mijin xa yafi nawa kyau, ni kuwa na san ko a yanzu kuka jera kai da Alhaji sai yammata sun dauki Alhaji sun barka" ta karasa maganar tana dariya. Suma suka yi murmushi.
Ta cigaba "naji daɗin zuwa da kayi ka gaishe ni, hakan yana nufin ka girmama ni kenan. Ina kuma so ka dauke ni tamkar uwa ba ma kaka ba, ni uwar kowa ce. Ni ka ganni nan Allah bai bani haihuwa ba amma kuma yayi min baiwar mutane. Wannan ya sa gashi dai shekarun girma sun zo min amma bana kukan rashin yaya, yaran da na rike sun zama gata na. Yayan yanuwana da na mijina duk dauka nake yi in rike su kamar ni na haife su, sannan kuma in debo marayu in rike su suma in basu duk kulawar da ya dace iyaye su bawa yaya, ko yan aiki aka kawo min na lura basu da cikakken gata a gidajen su sai in mayar da su yayana in rike su har in aurar da su. Ba zan iya lissafa yan aikin da na rike ba, tun daga kan Safiya har zuwa wannan yarinyar ta gaba na Lubabatu. Allah sarki Safiya Allah ya kai rahama kabarin ta. Duk da bata raye amma har yanzu ina morar gatan da na yi mata".
Su Gidado suka ce "Ameen" ta cigaba "ina gaya maka wannan ne dan ka saki jikin ka, nan gidan mutane ne, kowa kuma namu ne ballantana kai da aure zai hada mu. Ka fahimta ai ko?" Gidado yayi gyaran murya yace "na gane. Na gode kuma sosai. Allah ya kara lafiya" tace "Ameen ya Rabbi. Ai an gaya min cewa kai jika ne a gurin marigayi ambassador Muhammad Dikko. Mutumin kirki. Allah ya kai rahama kabarin sa. Na san shi ai lokacin da yana da rai, na kuma san matarsa Hajiya Fatima, ban sani ba ko zata gane ni amma in kaje kace mata Hajiya Maryama matar Alhaji Nasiru Atafi tana gaishe ta" Gidado yace "insha Allah za'a gaya mata".
A lokacin wata mata ta sauko daga sama, kallo daya Gidado yayi mata ya fahimci cewa ita ta haifi Safina, kamar su daya sai dai safina zata fi ta farar fata sannan da kuma bambancin shekaru. Ta zauna akan kujera a gefen su Gidado, suka juya suka gaishe ta ta amsa musu babu yabo babu fallasa sannan tace "sai yau ka samu damar zuwa gaishe mu kenan".
Hajiya tace "menene haka Sa'adatu? Tunda yazo ba shikenan ba?" Tace "ni kinsan bana barin magana a ciki na. Amma muna gari daya ace sai few days to auren Safina sannan zamu ga mijin da zata aura? A hakan ma kuma sai da nayi waya nayi wa mahaifiyar sa korafi sannan yazo, da bai yi niyyar zuwa ba ai. Da sai dai ranar bikin muma mubi cikin mutane muna tambayar ina angon yake"
Hajiya tace "tunda dai ita amaryar ta san shi ba shikenan ba?" Sai kuma ta juya gurin Gidado tace "rabu da ita, ita in dai idonta ya ga abu sai bakin ta yayi magana, haka halinta yake, zaka saba da ita a hankali. Tana da kirki sosai sai dai zaka sha faɗa" Mommy tana daga gefe ta kuma cewa "an anyi abu ba dai dai bane ba ai nake yin fadan" Hajiya ta chanza maganar ta hanyar yi musu korafin ba su ci komai da aka kawo musu ba, su kuma suka bada uzurin cewa sunci abinci a gida kafin su fito. Amma duk da haka sai ta saka aka kwashe komai da aka kawo musu aka kai musu mota. Da haka suka yi musu sallama suka tafi.
Suna shiga mota tun kafin su bar gidan Haidar yace "I don't like wannan surikar taka" Gidado yace "that makes the two of us" bayan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 14