Share this page
ta katse shi "wannan shine abinda ta gaya maka? To bara in gaya maka gaskiyar magana. Babu wani gurin babanta da take zuwa. My guess is gurin mijinta take zuwa in anyi hutun. Yana kasar waje ita kuma tana nan tana karatu, in anyi hutu kuma ta tafi gurinsa. In ta dawo kuma kai gaka. Ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya". Gidado ya rufe idonsa yana tuno hotunan Safiyya da Daddyn ta, most of them a asibiti, ya girgiza kansa, baya son yayi tunanin abinda zuciyarsa take hasaso masa. Abba yace "to a karshe kuma ya akayi ka sani?" Ya bude idonsa yace "taje holiday kamar yadda ta saba, and she have been acting off for months, she came back tace tana son ganina, muka hadu a office dina, and she told me". Abba yace "and kai me kake tunani? Do you believe she is really married ko kuma she is lying tana so ne dai kawai ta rabu da kai?" Gidado yayi shiru because that was a million dollars question, bai san amsar ba, zai kuma iya bayar da komai dan yasan amsar. Cikin jikinta shi yake convincing dinsa akan cewa tana da aure din, amma kuma yanayin yadda tayi masa magana, da abubuwan da suka gudana kafin ranar, suna so su gaya masa cewa da akwai wata a kasa. Amma ya kasa fahimtar if those things are real ko kuma zuciyarsa da take cike da sonta ne take imagining dan ta bata kariya kamar yadda Ya Ameen ya gaya masa. Ya dago kai yana kallon Abba yace "I don't know Abba. I don't know what to think. I don't know what to believe " yayi shiru kuma sai yayi deciding ya gaya musu all he knows, idan akwai wanda zai taimaka masa kaf duniya to su ne. Sai ya kara da cewa "she is pregnant". Da sauri Mama tace "ita ta gaya maka?" Yace "gani nayi" tace "to wannan shine dalili, ta gaya maka gaskiyar ita matar aure ce saboda cikin jikinta. Shi ciki ai ba'a boye shi. Bata yi niyyar fada maka ba sai data tabbatar in bata fada ba ma zaka gani da idonka" Abba ya gyada kai cikin amincewa sannan yace "that will be all. Tashi kaje". Gidado ya mike, a ransa yana jin mix feelings. Na farko yana jin dadin iyayensa sun fahimce shi duk da dai har lokacin suna ganin da laifin sa a ciki, amma kuma yana jin babu dadin yadda suka dauki maganar, a gurinsu a yanzu babu halitta worst than Safiyya. Yana rufe kofa Abba ya juyo yana kallon Mama da bacin rai a fuskar sa yace "da ace nasan wacece yarinyar nan da ta mayar min da ɗa haka wallahi da sai na san waye uban ta a Nigeria" Mama tayi murmushin takaici tace "she can be traced, tunda daliba ce a MD, shima kansa Gidadon zai iya tracing danginta idan yayi niyya but to what end? Menene amfanin hakan? Allah zai saka masa kawai. What we should concentrate on a yanzu shine ganin ya dawo hayyacin sa". Ya gyara zamansa yace "abinda muka yi magana akai kawai shine" tayi ajjiyar zuciya tana girgiza kanta. "I don't know dear, what works for some might not work for others. Aure kuma is a life sentence. Bana son garin neman gira mu rasa ido". Ranar Gidado wuni yayi da wayarsa a hannun sa. Ya daina kiranta ya kuma daina tura mata messages amma wuni yayi yana kallon pictures da videos dinsu together, trying to figure out a ina hint din cewa tana da aure yake, trying to see beyond the obvious amma babu abinda ya gani sai soyayya, tsantsar soyayya. A karshe sa yaji kamar zuciyarsa zata fashe sai ya rufe wayar ya kuma rufe idonsa, a haka bacci ya dauke shi, cikin baccin ne yayi mafarki da Safiyya a tsaye a kofar office dinsa hannayenta biyu rike da cikinta, hawaye sharkaf a fuskar ta, ta mika masa hannu daya tana kiran sunan sa "Gidado please, I am sorry. Muhaammaaad...." Yayinda shi kuma ya saka hannu biyu ya hankada ta waje sannan ya rufe kofar. *Her* 🧕🏻 Kwanaki ukun nan sun wuce wa min very slowly. Bawai ina ganin rashin saurin kwanakin bane saboda kasancewarsu event-less, a'a, abubuwa ne da yawa suke faruwa not one after the other but all at the same time, abubuwan da suka cika min kwakwalwa ta har suka sa ka bata gane komai. Mommy ta saka ni a gaba da zancen auren Mukhtar, Mukhtar ya takura min da kokarin chanja min ra'ayi a kansa, Abdul ya cigaba da rokon na akan kar na zabe shi a matsayin miji, yayin da Daddy ya cigaba ta tambaya ta akan wanene zabina. Ni kuma a gurinta zancen aure shine least of my problems, babban matsalata shine lokaci yayi sauri yazo a raba ni da cikin jikina ko na samu freedom ɗin da zan ji daɗin jinyar Daddy, ko hakan zai bani damar rekindling relationship din mu. Sai dai kuma shi Daddy kullum maganar sa ita ce "bana son in tafi in barki a wannan yanayin Safiyya. So nake in gyara rayuwarki kafin in tafi in barki". And through all these, Gidado weight heavily in my heart.💜 Tunanin halin da yake ciki ya kara wa wuni na tsaho, mafarke mafarken sa kuma sun hana min bacci mai nauyi. A ranar da muka kwana biyar a garin ne na samu nayi dogon bacci da safe irin wanda na jima ban yi irin sa ba. Har Mommy ta tashi ta shirya ta tafi asibiti gurin Daddy ta barni bacci. San da na farka na danji dadin jikinta sosai, dan rashin baccin ma yana daya daga cikin abubuwan da suke toshe min tunanina. Na tashi nayi wanka na fito ina shirya wa ina tunanin yadda zan kai kaina asibitin tunda babu kuɗi a hannuna dan tunda muka zo ban yi chanjin kudi ba. Na zauna tana lissafe lissafen abun yi sai ga Aunty Hajjo ta shigo dakin. Na gaishe ta ta amsa sai naga ta samu guri ta zauna akan kujera, wannan ya saka ni feeling uncomfortable na sunkuyar da kaina, hoping cikina bai fito sosai ba. Sai naji ta fara magana "Safiyya dama ina ta so muyi magana da ke amma bana samun damar kasancewa da ke ke kadai, kuma maganar da zan yi miki da ke kadai nake son yinta. Na cigaba yin shiru ban ce komai ba, ta cigaba "Sa'adatu ta bani labarin abinda ya faru dake, ko kuma ince abinda ke kika gaya musu cewa ya faru da ke, dan a yadda na fahimta basu yarda da labarin ba nima kuma har yau labarin bai kwanta min a rai ba. Amma kuma na kasa ganin laifinki ballantana in zauna inyi miki fada ko inji na tsane ki ko inji ina kyamar ki. Hakan kuma yana da alaƙa da mahaifiyar ki. Allah ne shaida ta har ta rasu ina yi mata kallon yaruwa ta, in fact zan iya kiranta da role model dina dan nakan kwaikwaye ta akan abubuwa da yawa musamman harkar kula da miji da kuma nuna soyayya ga yaya. Ina iya tuno da sanda ta haife ki Safiyya, ina tuno irin tarin soyayyar ki da na gani a idonta a lokacin da naje yi mata barkan haihuwar ki. Ban yi mamakin yawan soyayyar ba saboda la'akari da nayi da jimawar da tayi tana neman haihuwa kafin ta same ki, na kuma kara fahimtar soyayyar sanda ta gaya min cewa likitoci sun tabbatar mata da cewa bayan ke ba zata sake haihuwa ba". Na saka hannu na goge hawayen da already ya fara bin fuskata, ta cigaba "ina kuma iya tuno lokacin rasuwar ta Safiyya, a gaba na aka yi mata sutura. Abinda nafi iya tunawa a lokacin shine sautin kukan ki. You were barely two years old. Kowa a gidan yayi kokarin ya rarrashe ki amma kina ta kuka kina kiran sunan da kike gaya mata 'ammi', abinda yafi tayar min da hankali a lokacin shine idan na kalle ta a kwance babu rai kuma na tuno da cewa ruhinta yana gurin kuma tana jin kukan ki amma bata da damar rarrashin ki duk kuwa da irin tarin soyayyar da take yi miki. It broke everyone's heart, musamman saboda yadda mutuwar tata ta kasance". Ta dakata tana kokarin daidaita muryarta, daga alama kuka ne yake kokarin kwace mata. Ta cigaba "wannan shine nightmare din kowacce uwa, and I couldn't help but think about dan karamin dana Abdul Hakim, na lissafa idan nice na mutu what will happened to him? Nayi kuma tunanin taki rayuwar ya zata kasance? Tun a lokacin na fahimci kina cikin jarabawa babba kuma kin rasa wani bangare na rayuwar ki da ba za'a iya replacing ba, amma kuma ban dauka gibin da aka samu zai kai ki ga matsayin da kike ciki a yanzu ba. I offered to take you, dan inyi kokarin cike wannan gibin, bayan ni mutane da yawa sunyi kokarin daukan ki amma babanki ya hana, yaki bawa kowa ke yace shi zai raini abarsa da kansa. Ina iya tuna wata rana da muka je tare da mai gidan nan dan mu duba halin da kuke ciki, muka tarar da shi ya goya ki da zani a bayansa kina tayi masa rigima, duk da ma'aikatan da suke gidan ku amma ba zai iya bawa kowa ke ba saboda girman soyayyar da yake yi miki". Ta sake yin shiru. Muka yi shiru baki daya sai sautin kuka na kadan kadan, ta cigaba "ban sani ba ko ma'anar labarin nan da nake baki tana fitowa, ban sani ba ko kina gane me nake nufi. But you are so precious Safiyya. You are far greater than yadda kika mayar da kanki. And you have enemies everywhere. Labaran da Sa'adatu ta bani akanki, ban san wanne ne gaskiya wannan ne akasin hakan ba. Ba zan kuma yi claiming nasan abinda yake zuciyar mutane ba. Ta gaya min cewa za'a hada auren ku ke da Mustapha idan kin haihu. Amma kuma mai gidan nan shima ya gaya min cewa suna son idan kun amince zasu hada auren ku ke da Abdul. Ban san wanne ne gaskiya ba. Amma ina son gaya miki har yanzu a raina ina da niyyar daukan ki in rike ki in dai har zan samu wannan damar. In kin zabi Abdul zan so hakan. In baki zabe shi ba kuma ina so ki san cewa I will be here for you whenever you need a mother". ****. ****. ****. ****. Ina yan kasuwar mu wadanda suke son samun more visibility for their kasuwanci? ina masu neman followers a social media pages din su? To ga dama ta samu. Ku sani cewa mai talla shi ke da riba. Come and advertise with me and I assure you that you will get value for your money. No matter how big your business is, dole kina bukatar advertisement dan samun cigaba a kasuwancin ki. Kar ki manta, hatta manyan companies irin su CocaCola, Apple, Dangote etc kullum suna cikin tallan hajar su so why not you…. Duk wanda yayi sponsoring episode zan yi masa tallan business dinsa in the episode which will be posted on whatsap, facebook, intagram and wattpad, zan kuma saka number dinsa da kuma links na social media accounts din business din sa, zanyi posting pictures and links din on my whatsaap, facebook and intagram stories for 24h. Kar ku manta, the advert on the pages will last for as long as social media exist, that means forever. I will come up with a method da zan tabbatar you get value for your money, in sha Allah. [07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: ❤‍🩹*Safiyya*❤‍🩹 *By* *Maman Maama* Daga marubuciyar: Maimoon A'isha Humaira Diyam Tagwaye Jidda And now..... Safiyya *Episode Seven: The Good and the Bad Choices* A ranar ban je asibiti ba sai dare, na zauna a daki ni kadai with my thoughts thinking in nayi spending a day with my self zan iya yanke wa rayuwata shawara. Amma sai dai har daren ban zamu na yanke din ba, sai dai kamar kullum, ranar ma nayi adduoi sosai akan Allah ya dube ni ya kawo haske a rayuwata. A ranar ne kuma na fahimci dalilin da yasa na kasa samun zabi a cikin samarin da Daddy ya lissafa min, dalilin kuwa shine Gidado. In dai har zan cigaba da yiwa aure hangen da muka yi masa ni da Gidado to kuwa sai dai in Daddy yayi zuciya ya zabar min da kansa dan ba zan iya zabar kowa ba. Amma kuma sai naji cewa ina ma dai zaiyi hakan? Da ya dauke min wani babban nauyi a kaina, da ya cire min guilty feeling da nake ji a raina a duk lokacin da nayi tunanin zabar wani ba a matsayin miji wanda ba Gidado ba. In dai har ba Mustapha zai zabar min ba to bani da matsala. Abdul na san idan na zabe shi bani da matsala da iyayen sa, dan maganar da Aunty Hajjo tayi min yau ta kuma tabbatar min da kaunar da take yi min, sannan Uncle Sufyan kuma zan iya kiran shi da second father dina dan duk duniya Daddy bashi da aminin da ya amince wa kamarsa. Amma kuma Abdul yana da wadda yake so kamar yadda ya gaya min baki da baki. Kuma experience dina da soyayya ya saka na fahimci cewa kowace ce ma yana kaunar ta sosai. Duk sanda nayi tunanin zabarta sai in hasaso cewa Muhammad ne sanda muke tare muke tsara rayuwar mu tare sai iyayensa su haɗa shi aure da wata saboda selfish reason ɗin su. It would have destroyed our lives. And I do not want to destroy someone else's life dan ni in samu farin ciki. Mukhtar on the other hand yana so na, dan yana daga cikin few mazan da suka taba physically confessing soyayyar su gare ni. Mukhtar ya jima yana so na, soyayyar da ni a gurina na fara daukan ta obsession har ta fara irritating dina kuma tasa yayi loosing girmansa na yaya na a idona. In na aure shi at least zan zauna da wanda yake sona ko da kuwa ni bana son nasa amma kuma iyayensa fa? Uncle Ahmad shine dan uwa daya tilo da Daddy yake dashi a duniya, komai namu a hannunsa yake tunda Daddy ya fara rashin lafiya more than five years ago, sai dai kuma tun ina karama nake samun problem dashi da matarsa dan suna min kallon spoilt girl da bata da tarbiyya, problem din namu kuma ya karu a shekarun bayan nan, sannan ya zama worst bayan bayyanar ciki na. Zasu karbi aure na dole, and zasu iya farinciki ma da hakan, sai dai hakan baya nufin zamu daidaita dasu ko kuma zasu kasa goranta min ko nan gaba. And Mustapha, in na zabi Mustapha rayuwa ta will be a disaster, dan ban taba tsanar mutum ba kamar yadda na tsane shi and there is no way da zan iya neman aljanna ta a karkashin sa. Sai dai kuma Mommy tayi min dukkan halaccin da mutun yake nema daga wani mutum, ba ita bama, danginta sunyi wa Ammi na halaccin da duk mutum yake bukata daga mutum, musamman wanda ba dan uwansa ba. Duk da dai nasan a yanzu ba wai dan soyayya ko halacci ne yasa suke son hadin auren mu ba, but I do not care about that, da ace zan iya 'managing' zama da Mustapha, da tabbas shi zan zaba. Kamar kullum tunda muka zo garin, sai na samu kaina da yin adduoin istikhara da neman Allah ya bayyana min zabin sa a fili ya kuma tsayar min da zuciya ta akan zabin nasa. Kwana biyu bayan nan, da dare ina kwance kamar kullum ina kallon ceiling na kasa bacci, a lokacin babu abinda nake nema irin abinda zaiyi taking ɗina away from my thoughts. Na tuno da twins sai naji guilty feeling dan tun da muka rabu a Nigeria bamu sake yin magana ba. Na dauko wayata na kunna ina lissafin time ɗin Nigeria amma sai na lura dare yayi sosai a can, maybe ma sunyi bacci. Amma sai nayi tunanin hawa online in duba su. Sai dai ina kunna data din wata ta naji gaba na ya fadi, sai a lokacin na tuna cewa banyi blocking Gidado from Whatsapp ba kuma na tabbatar ya neme ni ta can. Na bude Whatsapp din na tsaya ina kallon yadda messages din suke shigowa a guje, har suka gama suka tsaya. And like I  expected, akwai da yawa daga Muhammad. Na kasa bude sakon nasa saboda tsoron abinda zan gani, zuciya ta ba zata iya daukan wasu karin bakaken maganganu daga gare shi ba. Idan kuma rokona yake ba zata iya jure cigaba da butulce wa soyayyar sa ba. Sai dai kuma a lokacin na sani har cikin zuciya ta cewa rabuwa da shi shine abu mafi alkhairi da zan yi masa a rayuwa. I couldn't stain his clean life with my dirty and tragic life. Idan ma gaya masa gaskiyar abinda ya faru da ni ba zai taɓa rabuwa da ni ba, iyayensa kuma ba zasu taɓa amincewa ya aure ni ba, nawa iyayen kuma zasu kama shi da zargin yana da hannu a cikin abinda ya sameni. So in whatever way shine a ruwa. And I rather drown myself then get him wet. Wannan shine zurfin soyayyar da nake yi masa. Message dinsa na karshe kawai na karanta. "please Piya, I just want to know why". Na rufe ido na ina jin damshin hawaye na a akan kuncina na danne conversation din mu sannan na danna delete, knowing fully well that nayi deleting dukkan chats dina da shi. Sai da nayi deleting dan kar in karanta sannan na bude nayi masa reply, duk da ban san complete abin da yace ba. Na gama rubutawa na tura masa sannan nayi blocking dinsa from my Whatsapp chats. Na saka hannu na biyu na rufe fuska ta, nayi kuka na mai isa ta sannan na bude fuskar na goge hawaye na na cigaba da scrolling through the chats ko zan samu abinda zai dan kwantar min da hankali na ko yayane. A lokacin nayi karo da messages din Yaya Mukhtar. Na bude, duk kuwa da cewa a raina na san shima wani karin bakin cikin zai kara saka wa zuciyata. Maybe ma gorin cikin jikina zai yi min. Amma kuma sai na tarar hakuri yake bani "Fiyya ban san da wanne kalaman zanyi amfani ba in baki hakuri, daga ni har Abba na san mun bata miki, a lokacin da ya kamata mu zama mune masu share miki hawaye sai kuma muka zama mune masu saka ki kuka" "Kin san halin Abba, it was just his temper talking not him, and he loves you shi yasa yake takaicin halin da kike ciki. Please kiyi hakuri ki yafe masa" "And ni kuma. You of all people know what my problem is, kishi ne yake damuna ba wani abu ba. I know I shouldn't have said zan taimaka miki in aure ki because like you said, ni ne nake neman taimako a wajen ki, cos nine nake tsananin son ki. And it would be my pleasure to marry you ko da kuwa nakasa ce ta same ki. And whatever kika haifa, zai zama ɗan mu ne ni da ke babu wanda zai san abinda ya faru. This I promise you with my life" "Please Safiyya in kinga messages ɗina ki kira ni. Ko ki kira Abba if you are still angry with me. We are worried about you. Bama samunki a waya and Daddy baya daukan kiran mu daga ni har Abba". And the last message "Ki gaya wa Mustapha, duk sanda ya shigo Nigeria sai yayi regretting. Na rantse sai na chanja masa kamanni". Na ajjiye wayar tare da yin ajjiyar zuciya. Na rufe ido na ina jujjuya kalaman Mukhtar a raina sannan kuma ina tunanin abinda ya haɗa shi da Mustapha. Dama can basu fiya jituwa ba tun muna yara. Shi Mukhtar muguwar zuciya ce da shi irin ta Daddy da Abba, shi kuma Mustapha silent killer ne, da wahala kaga bacin ransa. Ga ladabi da biyayya a gurin manya. Da haka ya siye zuciyar Daddy. But only I know who he really is. Da safe na tashi nayi wanka ina shiryawa kenan yayin da Mommy ita kuma ta shiga wanka, sai naji wayata tana kara, sai dana dan tsorata dan na manta da cewa na kunna ta. Sai kuma na fara murna ina saka ran twins ne suka kira ni, amma dana dauki wayar sai naga Uncle Ahmad ne. Nayi ajjiyar zuciya na zauna a bakin gado sannan na dauka tare da sallama. "Abba ina kwana" Ya amsa "lafiya lau Safiyya. Tunda kuka tafi sai yau kika kunna waya ne?" Nace "jiya da dare na kunna" yace "saboda menene? Saboda kima ganin babu wanda ya damu da ke da zai neme ki a waya? Ke kin kashe waya shi kuma Yaya na kira wayarsa yafi sau cikin charbi amma ba'a barinsa ya dauka. Na san kuma matar sa tare da wannan tsinannen yaron Mustapha. Har Mustapha ne ni zan kira Yaya ya dauka yace min wai bacci yake yi yace kar a dame shi. Ni fa?" Na dafe kaina saboda already har naji ya fara yi min ciwo da safiyar nan. Nace "kayi hakuri Abba, in sha Allah yau in naje asibitin sai in kira ka in bashi wayar kuyi magana" Ya danyi shiru "eh ina son magana dashi sosai, ke ma kuma ina son magana da ke. Ina son in baki hakuri akan abinda ya faru ranar nan. Na fahimci shine dalilin da yasa Yaya yake fushi da ni. Ni ba dan wani abu nayi miki fada ba sai dan ina ganin na isa inyi miki fadan ne. Uwa daya uba daya ne suka haife mu ni da Adam. Ke a matsayin ƴa kike a waje na. Ban dauka dan nayi miki fada Yaya zai dauki fushi dani har ya daina yi min magana ba. Ban dauka dan nayi miki fada zaki je ki kai kara ta gurin sa ba". Na girgiza kai kamar yana kallona nace "Abba wallahi ban kai karar ka ba. Ba da niyyar kai karar ka nayi masa magana ba....." Ya katse ni "I know Safiyya. I understand. Wannan matar tasa ce zata hada. She have brainwashed you two ba kwajin maganar kowa sai tata. Ba kwa daukan kowa da mutunci sai ita da yayanta. Ni na san ita ce ta saka ki kike ta bina akan wai sai na dauki kuɗin ki na siya wa ƴaƴan ta motoci " na sake girgiza kaina "Uncle ba ita ta fada min ba, ni ce .." yace "ba zaki gane ba Safiyya. Ba zaki gane ba. Kamar yadda nace, she have brainwashed you". Nayi shiru ban ce komai ba a lokacin da Mommy ta fito daga toilet tana kokarin shiryawa. Yace "in kinje asibitin ki gwada hada ni da Yaya ko Allah zai sa ya sauko muyi magana. I am not feeling comfortable with you two tare da su. Hankali na ba'a kwance yake ba" na gyada kai ina kallon Mommy da ta tsaya da abinda take yi tana kallona. Nace "insha Allah, zan yi masa magana in naje. Insha Allah, komai zai dawo dai dai" yace "good. Idan kinyi haka kin kyauta mana gabakidaya. Dan duk duniya baku da wadanda suka fi mu. Muma kuma duk duniya bamu da wanda wadanda suka fi ku". Na cure wayar daga kunne na na ajiye ta a gefe, Mommy da har lokacin take kallo na tace "waye?" Nace "Uncle Ahmad ne " ta bata rai "Ahmad ba shi da kunya wallahi. Me kuma yake ce miki bayan irin wulakancin da yayi miki a cikin mutane? Me kuma zai ce miki?" Nayi shiru da farko, amma ganin alamar amsa take jira sai nace "yana so yayi magana da Daddy ne. Yace baya samun sa a waya" tayi tsaki, "to ba dole yaki daukar wayarsa ba. Ta yaya za'a yi mutum ya cire

Chapter 8 of 14