wani guri aka bashi ya shanye har wani qara shigewa kake jikinta to ka hadiyeta mana qarewar so da kewa munafiki mara adal...."
Hannu ya daga zai kwada Mata mari Rafi'ah tayi saurin riqe Hannunsa tace “Don Allah ka rinqa tausasa zuciyarka mijina ai namijin gaske baa sansa da fushi a gidaba idan kana fushi meye sauqinmu ne muda zamu rayu a qarqashinka please yi Mata uzurin nan daka saba da wankama nakeso na tayaka kayi nasan ka gaji Amma naga tumbinka ya sauka ba haka na saba ganinsa ba muje na ciyar dakai yanda zaifimin dadin shafawa" ta qarasa tana shafa tunbinsa murmushi yayi ya dagata cak ya direta a kujerar dinning din takaici ne da baqin cikin abinda bata taba tunani ba yasa Ni'imah juyawa zata fice har takai bakin qofa yace “dokace ba umarni ba kin saba taka dokata Ina qyaleki wannan bazanyi uzuri ga kowa ba"
Sumsum ta dawo taja kujera ta zauna Rafi'ah tai murmushi ta hadawa kowa abincin ta turawa kowa gabansa ta diba a cokali zatakai bakinta ya riqe tasan me yake nufi ta matso da kujerarta ta rinqa bashi tuwon Cous-Cous ne da miyar kubewa da yaji bandar kifi sai fatan doya da yaji hanta babu kunya Ni'imah da ganda tasata yiwa kanta horon yunwa ta zage ciki ta nadi tuwon tasha hadin lemon da Rafi'ah tayi musu na kankana ta miqe ta Kama hanya zata tafi Ja'afar yace “ki jira na gama na rakaki tunda cikinki ya dauka a qa'ida ma fah ba ita zatake girki ba ke zakikeyi mana tunda ita sabon hannu ce da wanne zataji saboda haka daga gobe zaki fara aikinki zuwa sati" ta hadiya iyakar hadiya wai tayi musu girki suci tab aikuwa zaayi zaman yunwa a gdan to ita da wanda zataci ma batason girkawa itace zata girkawa qarata biyu abinci tab zaayi bala'i kuwa" a tsaye ta tsaya taqi zama shima Kuma yaqi tashi saijan Rafi'ah yakeyi da hira itace taga tsaiwar tayi yawa tace “am dare yayi zata gaji da tsaiwa ka tashi ka rakata" juyowa yayi ya dubeta ta kumbura fuska yayi murmushi yace “wlh na manta dake a tsaye sorry muje na rakaki" miqewa yayi itama Rafi'ah ta miqe ta rakasu har bakin qofa tace “asuba ta gari Best...."
Wata uwar harara da yayi Mata tasata juyawa da sauri ta fara harhade kayanta sake gyara parlourn tayi ta kunna turaren wuta a burner ta haura saman shima ta sake Masa sabon gyara tayi alwalar isha tara harta wucce tayi isha tayi shirinta na kwanciya gabanta na faduwa batason nacinsa cikin saa daya shigo din shima bai wani takura Mata ba sukayi baccinsu salamun salamun washegari litinin ta roqeshi alfarmar zataje tayi C.A a school da farko cewa yayi bata isa fara yawo ba Saida yaga ta marairaice masa zatayi kuka sannan yace ta shirya yakaita suna fitowa Ni'imah ma tana fitowa da alamun fita zatayi iyakar son tuno abinda ya wucce dinsa yakasa tuna sanda ta tambayeshi fita Koda yake dama tunda aka fara mgnr aurensa da Rafi'ah bata tambayarsa zuwa unguwa saidai ya dawo ya tarar batanan.
Ya shirya Mata mugunta saboda haka ya nufeta da sauri yana zaro kudi a aljihunsa yace “Au na manta yau zanyi baqi daga Gombe ki bawa Yahaya kudi gasu ya siyo kifi nasan babushi a kitchen dinki wancan kin barsa ya lalace kiyi mana farfesu sannan kiyi mana tuwon alkama miyar kalkashi ki tabbatar kin gama kafin azahar zankai Rafi'ah makaranta May be tare zamu dawo da baqin"
Bai jira cewarta ba ya juya yana murmushi ya shige motarsa yaja har suka fita takasa motsawa tashin hankalinta yanda zatayi wannan wahalallan girkin daya sata ita tunda take a gidansu bata taba ganin anyi tuwon alkama ba Amma wai yau ita zatayisa harma da tagomashin miyar kalkashi ga gyaran kifi da kullum ta gyara sai yace bata iyaba gdanta yana qarni, zubewa tayi a gurin ta dora hannu aka tanaso ta zunduma ihu Amma ta kasa daqyar ta miqe kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta koma ciki ta rinqa zagaye parlourn tana tunanin ta inda zata fara kiran Hajiya Sahura ne ya shigo ta daga da sauri tace “ya munata jiranki boka yace dole sai kinzo aiki zaiyi yadda akeso ke Kuma kina bata Mana lkc" sai yanzu ta samu damar fashewa da kuka tace “Mom wannan dan gadon masifar ne ya hadani da aiki wai baqi zaiyi shine yace nayi masa tuwon alkama miyar kalkashi sannan nayi masa farfesun kifi harda cewa saina hada masa lemo don Allah ki turomin Marawiyyah nasan ta iya tunda girkinsu ne na yan qauye wlh idan banyi ba akwai matsala" Hajiya Fatsum ce ta karba tace
“Ke shashasha ce to ki fito mana idan aka gama abinda zaayi minti nawa ne zaki dawo kiyi masa inma kafi tuwon alkama ne Kuma ma idan ansamu yadda akeso ai bai Isa yace qala ba" dadine ya cikata tace “ok hakane ganinan" daukar Jakarta tayi da mayafinta ta fice tana dariya tana cewa “Ja'afar Wakil ka bonu ka lalace a gurina" mota ta dauka ta nufi qauyen tana zuwa ta tarar da uwar mijin nata da uwarta sunyi gurfane kamar masu neman gafara.
Dariya boka na gangare ya sheqe da ita yace “shegiya haihuwar asara ta sabawa umarnin miji ta fito toke an fada Miki wannan yarinyar a zaune take ai munafurtarki takeyi tana zagayewa tana bin manyan bokaye yo baki ganiba ko a yammatancinku tafiki farin jini ke Saida aka rinqa hadawa da layu da guraye sannan aka samu aka hadaki da wannan kaffafen mutumin da kurwarsa taqi juyuwa to ai baki sani bama tuni burinki yana gaf da rushewa ke wata biyar yana baki kinaqin karba ita kuwa tun ranar farko ta karbe yanzu haka da cikin yariman Azare me jiran gado a jikinta....."
Zaro ido sukayi tare da dafe qirji dukkansu Hajiya Fatsum tace “ciki Kuma daga zuwanta haba boka sake dai dubawa ni dana bashida wannan azarbabin" tsawa boka ya daka Mata yace “ankare nutsu tsinanniya wacce ta fatalar da aljannarta na rantse da bukkata Rafi'ah amaryar danki Ja'afar tanada shigar ciki saidai a dauki mataki Amma cikikam akwaishi abinda yasa naqi yarda na rusa aurennan kenan na hango rabo me zafi yana yawo inma baayi aure ba to zaa lalace ayishi a titi yanzu mafita dayace idan bakwa buqatar cikinnan zanbaku wata laya kusan yanda zakuyi ku haqa saitin inda kukasan koba kullum ba wataran dole sai tabi gurin ku binne to indai kukayi haka duk sanda ta samu ciki ko ya Isa haihuwa indai ta taka gurinnan saiya bare hhhhhhhh tsinannu Kuma karba fa zakuyi ku?"
Tsoro ne ya shigi Ni'imah tace “kayy aa gaski....." Bige bakinta Hajiya Sahura tayi tace “aa ubanki ai dole mu karba ke baki kishin kanki baki fatan ki zama uwar sarkin wataran" kallon Hajiya Fatsum Hajiya Sahura tayi duk hatsabibancin Fatsum tana shayin Sahura take tace “abamu boka nima banason shegiyar yarinyar nan ta hada iri da dana wlh irin Hajiya Amina ai irin masifane buzuwa ce fah tsafi sukeyi su bama asiri ba".............
_More Comments_
_More Typing_
_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad- realfauzahtasiu_*
*_Gmail-fauzahtasiu41@gmail.com_*
*_YouTube- Open eyes multimedia_*
*_Telegram_*
👇
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7
*_33-34_*
_____________________________
_____________________________
Dariya boka ya sake sheqewa da ita ya dauko wata laya ya miqawa Hajiya Fatsum yace “to debabbiya wacce ta saki danta ta Kama gaibu wannan asan yanda zaayi a binne ta da an binne mgn ta qare ciki zai lalace duk lkcn data tsallaka gurin da aka binne amma ayi takatsantsan kada ido ya gani" murmushi Barebari tayi tace “haba boka yau muke tare mukayi aikin da yafi wannan wahala ma bare wannan gashi shekaru sunata tafiya 38 years taqi fasuwa kawai kabar komai a yanda yake ni zanji da komai"
Ashar ya qunduma Mata yace “hhhhh shegiya yar fashi da dabara ashefa ke har fashin rayayye kikeyi ki sanya matacce a wannan aikin bazaiyi Miki wahala ba dama na irinku ne marasa imani kije kiyi yawwa sai wannan ruwan rubutun duk yanda zaayi yau yakai cikin Rafi'ah kota abinda zataci ne indai batayi Bismillah ba to aikin gama ya gama sauran bayanin zakugani da idanunku Amma fah kubi a sannu idan kika kuskure kwabarki zatayi ruwa asirin da kika Dade da binnewa zai fasu" tsawa ya daka musu suka firgita yace “ku tashi tsinannu uku wadanda basuda rabon lahira" tashi sukayi da baya da baya suka fita daga bukkar bokan suka nufi mota kowanne da abinda yake aunawa itadai Hajiya Fatsum tunanin abinda kaje yazo takeyi tunda take da Ja'afar iyakar sonta data mallakeshi ta kasa ta kashe millions of Naira don kawai ta cire masa jin Hajiya Innah aransa Amma ta kasa saima ya zamana kamar qara musu shaquwa takeyi yanzun ma game da abinda ya shafi Rafi'ah tafi tsoron Hajiya Innah fiye da ita kanta Rafi'an domin ita tasan an gama da ita indai maganin nan yaje cikinta to mgn ta qare sallar farillah ma sai anyi da gaske zatakeyi bare nafila.
Cikin saa har suka koma qarfe daya da rabi Ja'afar bai dawo ba da sauri suka nufi qofar bangaren Rafi'ah dake Intalok ne basusha wata wahala ba suka qwaqule daya daqyar sukayi haqa suka jefa layar gashi kuwa sun iya saiti dake tsofaffin mushirikai ne bayan sun gama suka mayar da abinda suka bambare suka debo farin yashi a waje suka zuba suka sake zuba ruwa suka saki ajiyar zuciya tare,
Bangaren Ni'imah suka shiga suna mayar da numfashi Hajiya Fatsum ta dubi Ni'imah tace “ah ke abin naki harda qazanta Magaji ya tsani qazamin mutum gsky ki zage wajen tsafta idan ba hakaba kina ganinsa zaiyi Miki fintinkau" yatsina fuska tayi tace “to Hajiya ga yan aiki harsai wani nayi aiki girman ma ai yanada halin da zai nema mana kuku tunda dama babu inda akace na rinqayi masa girki" tabe baki Hajiya Fatsum tayi tace “ai gakinan gashi ni Ina ruwana" kitchen din suka shiga su uku sukayi Mata tuwon alkamar da miyar kalkashi sai farfesun kifi cikin lemukan ne tace a hada na kwakwa a zuba rubutun a ciki saboda duk lemukan duniya Rafi'ah tafi sonshi, aikuwa suka zage suka hada ta dauka tasa a freegde suka tayata ta gyara bangaren su kansu ba wani iya gyaran sukayi na tsanaki ba andai burbura sukayi suka tafi saboda basason yauma ya dawo ya tarar dasu a gidan ita Kuma Ni'imah ta fada wanka ta kashe kala ashe iskanci ke hanata kwalliya ta iya,
Dawowa tayi parlour ta harde abinta Ja'afar ya shigo gdan bai shigoba sai bayan la'asar sosai suka shigo shiga Rafi'ah ya daukota daga makaranta tunda suka shigo taji gabanta na faduwa ta fara karanto addu'o'in neman tsari ya bude Mata motar Ni'imah na kallonsu ta window ya riqe Mata jakar ta fito ta sunkuya ta karba ya lakace Mata hanci sukayi dariya ya Kama hannunta suka shiga ciki,
Suna shiga suka fada wanka yau wankanma tare akeyinsa itadai duk a kunyace take Amma batada mafita hàka sukayi suka fito ta shiga kitchen da sauri dama tanada miya data soya jiya ta dafa musu farar shinkafa ta hada salat ta zubo musu suka baje a parlourn sunaci suna Hira tuni ta manta da komai ta zage tana bashi lbrn irin wahalar da tasha jiya da irin ciwon da kanta keyi bayan sunci abincin ya dauko Mata paracetamol a clinic dinsa na cikin gdan yabata tasha ta miqe da gaske yau taci biro da yawa kanta sarawa yakeyi ta shige daki ta kwanta
Sannu ya rinqayi mata yana tofa Mata addu'a a goshinta hardai ya samu bacci ya dauketa wannan dalilin ne ya hanata zuwa dinner lkcn dinner tanata baccinta yana jiran ta tashi har Tara na dare gashi Ni'imah ta dameshi da kira kawai saiya tashi ya tafi shi kadai tana ganinsa shi kadai tace “ina take?" Yanda tayi tambayar yashi qara saita injin idonsa akanta yace “wa kenan?" Qasa tayi da kanta tace “Rafi'ah Mana naga kun shigo tare Kuma naga yanzu kazo Kai kadai ita bazakayi Mata dole tazo taci abincin anan ba?" Murmushi yayi yace “bayin kanta bane yanzu hakama tana bacci kantane ke ciwo sosai karki damu ita batada matsala"
Shiru tayi zuciyarta cinkushe da takaici da baqin cikin yanzu idan batazo ba duk shirinsu ya rushe" kallonsa tayi tace “Amma daka tasota ai qila ta yini bataci komai bane batason cin abinci idan abinta ya motsa saita kwana uku bataci wani Abu me nauyi ba" baice Mata komai ba yayi Bismillah ya faracin tuwon yana korawa da lemon abarbar duk da bayajin yunwa Amma yaci da kirki ya dago ya kalleta sai juya cokali takeyi ta kasacin abincin yace “bake kikayi abincin nan ba dandanon girkin ba naki bane na Barebari ne"
Da sauri ta dubeshi yace “banason musu akan abinda nariga nayi yaqini akansa kodai kinje ko Kuma tazo wanne ne ya faru a ciki?" Hade rai tayi ta fara qunquni yayi murmushi yace “bazaki nutsu ba da kinkwantar da hankalinki sai yar uwarki ta koya Miki da muka tafi nake fada Mata cewa tayi zakisha wahala na kiraki na fada Miki ki jira ta dawo sai kuyi" harara ta watsa masa tace “sai Kuma nace Ina neman taimakonta"
Ganin ta juyawa zancensa ma'ana yasashi jan bakinsa ya tsuke ya tashi yayi gyatsa yayi hamdala yace “babu wani Abu ko zan tafi?" Miqewa tayi da sauri tace “bari na baka wannan lemon kwakwar nasan tanaso Kuma zataji dadinsa kasa Mata a freedge idan ta tashi saitasha" yaji dadin nuna kulawarta ga abar qaunar tasa ya karba yayi kissing nata yace "kin fara hankali Saida safe" ficewa yayi yabarta tsaye cikin jin dadi tasan indai Rafi'ah taga lemon to bazataqi shaba da zaran Kuma Tasha to aikin gama ya gama zasu kassarata cikin sauqi
Koda ya koma din tana kwance har lkcn bata tashiba shine yaga baccin yayi yawa ya tabata yaji ta sauke numfashi tare da bude idonta tar akansa ya sauke Mata murmushi yace “ya kannaki?" Lumshe idonta tayi ta bude tare da miqewa zaune tace “yayi sauqi shine baka tasheni ba akayi magrib har akayi Isha" Hannunsa ya dora bisa goshinsa yace “sorry my heart nabarki ki hutane yanzu tashi kiyi" miqewa tayi yabi bayanta da kallo yanajin wani yanayi a jikinsa tausayinta yake hanashi takura Mata ya lura itan tanada wani hali ko zatasha wahala indai tasan Abu haqqinka ne to bazata hanaka ba wannan dalilin ya darsa masa tausayinta,
Baiji fitowarta ba saiji yayi ta ja hancinsa ya sauke numfashi tare da zamewa ya kwanta yana kallonta har ta idar da sallar ta zauna tana lazumi ta dade sannan ta tashi ta shiga wanka ta fito tayi Shirin kwanciya yace “au na manta qawarki tabani coconut Just tace na kawo miki" murmushi tayi tace “na gde Amma yanzu banajin sha'awar komai wani baccin nakeji zansha da safe Ina fatan kasamin a freedge?" Janyota yayi yace “bacci bacci dai Rafi'ah kodai har mun samu qaruwa ne"
Kunya mgnrsa ta bata ta sinqe Kai a qirjinsa tana yar qaramar dariya shima dariyar yayi yace “to muka sani ko mudin special ne one bugu one dauka" Shiru tayi masa tanaji yayi ajiyar zuciya yace “da Kinga qauna kuwa zan hanaki ko sanya kaya da kanki zanyi tattalin unborn dina fiye da tunanin me tunani itadai Rafi'ah batace masa komai ba tanajinshi yana hura Mata iskar a kunnenta tare da sanya harshensa cikin kunnen nata yana yamutsa gashin kanta da Hannunsa qamshin gashin nata yana qara hargitsa masa lissafi yana qara matseta qanqameshi tayi saboda tsoron da takeji sosai karo biyun taji a jikinta shiyasa da ta fahimci inda ya dosa jikinta ya dauki rawa.
A hankali cikin rawar murya yace “ki...kisaki jikinki bazakiji zafin ba a hankali zamuyi kinji" daga Masa Kai tayi idanunta na kawo ruwa yass harshensa yana lashe hawayen nata yana shafa shaffafen cikinta a hankali zuwa mararta tare da zare Mata rigar jikinta ya zubawa qirjinta ido yanajan wani rikitaccen numfashi tare da Kai Hannunsa ya kashe musu fitilar wani al'amari me tsayawa arai shine ya wakana a wannan dare yayi mamakin yanda ta rinqa taimaka masa wajen samun nutsuwarsa ta rikitashi ta dimautashi ta jiyar dashi dadi tabashi nutsuwar da baitaba samu ba a rayuwarsa duk da shi kansa yasan taji a jikinta Amma bai hanata bashi farin ciki ba,
Daren ya tsaya masa a ransa darare biyu da bazasu goge ba a tarihin rayuwar aurensu daren farkonsu da wannan daren me cike da ni'ima Ubangiji ma yasan daren na musamman ne a rayuwar bayinsa shiyasa ya qara Masa armashi da saukar ruwan sama sosai Ja'afar ya rikice ya rinqa sanya Mata albarka yana shafa bayanta inda itama tayi luf a qirjinsa tanajin azaba amma shafa sumarsa takeyi.
Bacci ne yakeson daukarsa yaqi bari Saida ya tasheta sukayi wanka suka tsaftace jikinsu sannan suka kwanta suna manne da juna washegari ta tashi da dama jikinta sosai tayi abinda zatayi a gurguje ta fice daga gdan shine yakaita Koda yakaita baibaro makarantar ba Saida ya shiga ya fita duk wani Abu daya dace ayi game da tafiyarsu yayi sannan ya dawo ya jirata suka dawo gidan lkcn da suka dawo Ni'imah batanan yayi qwafa ya shige ciki itama ta shiga da kitchen ta fara indomie ta dafa don da gaske yunwa takeji ta zubo stew akai ta fito ta zauna shikam baici ba cewa yayi abincin yarane taci abincinta ta haye sama tayi wanka ta sauko ta isheshi Ashe fita yayi ya dawo da ledoji a Hannunsa ta karba tana me yimasa sannu da zuwa ya amsa da nishadi yace “naga yau kin gaji ga yar uwarki batanan shiyasa nayo Mana take away godiya tayi masa ta hada masa ta lura ransa a bace yake tunda suka shigo gidan yake qwafa itadai tana sallamarsa ta haye sama ta dauki book ta fara nazari bai hauro saman ba sai goma da rabi lkcn har tayi bacci.
Tashinta yayi yace “da mutuncina da komai bazai yuwu nakebin mace dakinta ba kisawa ranki indai inanan bangaren to dolene a dakina zakike kwana ko security ma ai yafi"
Bata tashiba saima gyara kwanciya da tayi yasa hannu ya dagota cak ya nufi dakin nasa da ita ya kwantar da ita daidai lkcn da wayarsa ta hau ruri yana dubawa yaga sunan surukinsa mahaifin Ni'ima yayi kamar karya daga saidai yaga Rashin dacewar hakan ya daga suka gaisa Dad yace “Ja'afaru yanzu nakeji a gurin Mata Wai kace da Ni'imah ta zauna a gda har sai ka nemeta meye ya faru ne?" Numfashi ya sauke yace “Dad ka qyaleta kawai duk sanda ta nutsu ta gane zamaba takeyi ba zaman kanta ba ta dawo ace mace kullum batada aiki sai yawo Kuma yawon ma bazata sanar da mijiba saidai kawai na duba naga ta fice haka ake aure ko kuwa itane take aurena haba Dad wannan ai zubarmin da qima takeyi a garinnan waye baisan itan matata bace ko an fada Mata zan dauki iskanci da gantali ne?"
Numfashi Dad ya sauke yace “ni dama nasan da hankalinka bazaka barta ta rinqa yawon nan ba duk da bani nake ganinta ba Amma megadi ya fadamin kusan kullum sai tazo yanzu dai Ja'afar baza ayi hakaba kayi hqr zansa driver ya dawo da ita idan ta qara wlh komai kaga ya dace kayi"
_More Comments_
_More Typing_
*_34-35_*
_____________________________
_____________________________
Numfashi yaja yace “shikenan Dad Babu komai Amma aja Mata kunne abubuwa da yawa Ina hqr dasune dominka kada takai hqr na qarshe" godiya Dad yayi masa suka aje wayar ya zubawa Rafi'ah ido tayi luf da ita ta lafe a katifar yanayinta ya kalla kawai ya fahimci da abinda yake damunta Amma dake miskili ne saiya shige bathroom ya fada wanka sanda ya fito tayi bacci,
Shima kwanciyar yayi yanajin yanda dumin jikinta yake hauhawa da hakadai shima bacci ya daukeshi washegari taso zuwa school ya fitittike ya rinqa ruwan bala'i waishi yayi aure Amma bazai samu lkcn matarsa ba da anyi mgn sai tace school, dole tanaji tana gani ta hqr aikuwa ranar tasan ta zauna a gda duk wata nutsuwarta Saida ya rabata da ita ko bakin qofar dakin yaqi zuwa wannan Abu ya dameta hakadai taketa daurewa har yammaci yayi wanka ya fice itakuma ta gyara bangaren ta sake kwanciya.
Yinin ranar sur bataji Motsin Ni'imah ba to dayake itama taji maza batako leqoba har dare yayi da daren ne ya shigo da murnarsa ya zauna a parlour yana shafa fuskarta ta bude idonta akansa yayi murmushi yace “ina fatan kin gama ready na tafiyarmu jibi zamu tashi" lumshe idonta tayi kawai batare da tace masa qala ba lamarin daya bashi mamaki yasan dai ba wani Abu ya fada Mata da zai dameta ba farin ciki ma ya kamata tayi.
Juyowar da zaiyi yaga hawaye yana zuba a idanun nata dagota yayi da matsanancin mamaki yace “mene Kuma ya faru daga mgn?" Hawayen ne ya qara qarfi tace “amma dai nazaci kasan cewa Ina karatu Kuma kanada lbrn burina akan karatuna meyesa ka dage saika tafi dani bayan bani kadaice matarka ba meyesa bazaka dauki Ni'imah ba tunda ita free take Ni ka qyaleni na qarasa karatuna kace 3 mouths kafin three months munyi exams mun gama don Allah ka qyaleni badon...."
Abinka dame zuciya a kusa sosai ranshi ya baci Amma Bai nuna Mata ba ya miqe ya haye sama tabisa da kallo jin shirun tayi yawa bai dawo ba itama ta miqe ta nufi saman ta bude dakinsa ta hangesa kwance kan gado matsawa tayi ta zauna kusa dashi ya zubawa selling ido Kama Hannunsa tayi ya janye ta bude baki a hankali tace “bansan bazaka fahimceni ba da ban fara fada makaba kayi hqr...."
Daganta hannu yayi yace “fita Rafi'ah" da sauri ta dago ya tashi zaune yace “ki ficemin a daki nace" miqewa tayi a tsorace ta fice daga dakin da sauri ya furzar da iska me zafi ya tashi ya kulle dakinsa nata dakin ta shiga ta fada gado tayi kwanciyarta zuciyarta na tafasa ta tsani mutum mara fahimta a rayuwarta, da wannan tunanin ta tashi kawai ta dauka qur'ani ta fara karatu ta Jima tana karatunta sannan ta bari ta koma ta kwanta aikuwa bacci ya dauketa me dadi hankalinta kwance bata farka ba sai asuba tayi sallarta ta fito parlourn ta fara shirya breakfast tana kitchen din taji saukowarsa ta fito ya zubanta ido harta qaraso kusa dashi ta durqusa tace masa “barka da fitowa" wani gwauron numfashi ya sauke komai na me ilimi dabanne da oo ce sai suyi sati suna gaba da juna Dagota yayi ya hadata da jikinsa yace “na fahimcek...." Rufe masa bakinsa tayi tace “na hqr da karatun kayi duk yanda kakeso dani" wani dadine hade da tausayinta ya mamayeshi ya qara matseta da jikinsa yace “are you sure?" Dagansa Kai tayi yayi murmushi me sauti ya sauke lips dinsa a goshinta yace “Allah yayi miki albarka zuciyata tafi aminta dana tafi dakene saboda inads tabbacin zamu qara samun kusanci da fahimtar juna bazan katse Miki karatunki ba jiya na gama Miki komai insha Allahu wannan daya dai bazai hanaki samun abinda kika Dade kina muradi ba sai kinzama doctor din da zaayi alfahari da ita a fadin Nigeria ki shirya yau zamu wucce Abuja gobe saimu tafi kinji amaryata?"
Yar qaramar dariya takeyi tana shafa qirjinsa ya sanya hannu ya balle bottle din rigarsa yajata suka zube a kujera ya sanya bakinsa ya Kama ZIP din rigarta na gaba ya zuge ta tsorata da inda taga ya nufa amma bata Isa nunawa ba yanzu sai rai yazo yana baci hakanan tanaso bataso suka bata lkc wajen romance din juna suna a haka sukaji ana buga qofar da qarfin gaske kallon idonta yayi itama shi take kallo ya janye yana mayar da numfashi yace.
“Uban waye zaizo yanamin bugun nan da sassafe?" Bude qofar yayi yana huci kawai sai ganin Hajiya Fatsum yayi tsaye tanata huci saurin saita kansa yayi yace “da safennan Hajiya sannu shig...." Daukeshi tayi da mari tace “da saikamin iso zan shiga munafuki Koda yake zama ka iya korata kace bacci zakasata sallamamme asararre" shigewa tayi daidai lkcn Rafi'ah ta gama zura hijjab dinta dan batamasan inda ya cilla Mata rigarta ba a dan darare
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 19