Share this page
masu bayani ya shiga rudu da tashin hankali ya dago yace “ina mijin nata to ranka ya dade ai huruminsa ne wannan" qasa Abba yayi da kansa yace “bayanan yana Abuja baimasan abinda yake faruwa ba Amma zamu sanar dashi yanzu dai kasa hannu a ceto rayuwarta yafi komai muhimmanci. Cikin sanyi jiki da mamaki ya sanya hannu jikin takardar daidai lkcn da taxi ta tsaya Ja'afar ya fito suka zubansa ido yana sallamar me motar ya nufosu Mai martaba gabansa ya fadi ganin irin muguwar ramar da dannasa yayi ga wani baqi da yayi qarasowa yayi ya russuna cike da ladabi ya gaida mahaifin nasa da surikinsa suka amsa tare da tambayarshi hanya yace “alhmdllh" Shiru ce ta dan ratsa kansa na qasa kunyar Abba yakeji tunaninsa ko yasan meye yake faruwa tsakaninsa da Rafi'ah ganin babu wanda yabi takansa yasashi miqewa ya matsa kusa da Innah ya zauna ya rafsa uban tagumi. Lkc yaja sosai sannan wata likita mace ta fito dauke da jaririn a towel me kauri tana zuwa ta tsaya tace “Waye Ja'afar M Wakil?" Miqewa yayi da sauri yace “Gag...gani" gabansa na faduwa ya nufi nurse din tayi ajiyar zuciya tace “petiant dinka ta farka tun dazun saidai bata cikin hayyaci sai yanzu muka samu ta dan samu so Kuma tunda ta farka take sharar hawaye munyi munyi ta fadi me take buqata bakinta baya fita sosai Amma na iya fahimtar tana cewa Ja'afar M Wakil meyesa kayimin haka me nayi maka alqawarin farin cikin da kayimin kenan irin tukuicin da na cancanta gareka kenan? Wadannan kalaman tuhumar su taketa maimatawa shiyasa naga ya kamata idan kana gurin kaje kaji meye take buqata" Numfashi ya sauke me qarfi tare da miqa hannu ya karbi bebien dake nade cikin towel ya bude fuskarsa yaja wata qaqqarfar ajiyar zuciya yace “barakallahu ahsanal khaliqin" kyakkyawan yaron me muguwar Kama da ubanshi saidai qanqanta kamar an fyatoshi a hanci. Juyawa yayi ya nufi dakin da yaga nurse din ta fito rungume da dannasu dan qarami kamar yar tsana, tana kwance saman gadon ya tsaya a kanta yanajin bugawar zuciyarsa da numfashinsa suna neman daukewa Koda bata cikin yanayin lfy da Kuma walwala ya sani Kuma ya shaida shidin rahama ce garesa a duk lkcn daya rabeta sai yaji nutsuwa tana wanzuwa a cikin ruhinsa. Idanunsa ya sauke saman nata da suke lumshe ruwan hawaye na kwarara, tausayinta ysna ratsa gabbansa ya rasa meye yasa ya qaurace Mata har tsayin lkc haka Kuma ya yanke duk wata hanya da zata sanya ta samu sauqi yanada tabbacin duk wannan halin da ta kasance a ciki shine sanadi domin da ace bashidin bane bazai kasance Abu na farko da zata bude baki dashi a wannan yanayin me hatsari ba tabbas aikine ja a gabansa ya dawo Mata da farin cikinta fiye da baya. Miqawa nurse din babien yayi yace “Asashi a Inquivertor" ficewa tayi shikuma ya tsugunna a gaban gadon ya riqo hannun Rafi'ah da yake daure da callular ya hada tafin hannunta da nashi ya matsa a hankali ya dora harshensa saman kuncinta yana lasar hawayen da yake zuba a idonta taja ajiyar zuciya tare da daga hannunta dayan ta dora a kansa sai ta fashe da kuka ta qanqamesa shima hawaye ne suka zubo masa ya janye da sauri yana qoqarin rarrashinta yace “kinga Rafi'ah ki bari kukannan Kinga aiki akayi miki baa buqatar yawan numfashi ma me qarfi balle kuka" Ajiyar zuciya tayi ta bude idonta akansa shima itan yake kallo cike da tausayi da kunya yace “please kada ki tuhumeni wlh bansan ya akayi hakan ta faru ba ki tayani da addu'a kawai" lumshe idonta tayi kawai kamar mai bacci Amma idonta biyu tabbas tuhumarsa takeson yi saidai ya riga ya katse Mata hanzari a hankali tace “ina fatan kana lfy ba wani abune yasa hakan faruwa daya shafi lfyrka ba" a hankali take mgnr wanda sai mutum yasa nutsuwa sosai zai fahimci me take fada tausayinta ya qara cika zuciyarsa yace “lfy Lau ki huta idan kinji sauqi zamuyi mgn na gde da kyautar dan da kikayimin mai kama dani" bata Kuma ce Masa komai ba suka zauna na kusan 15 minutes a haka kafin ya fita Innah ta shigo ita da su Mai martaba da Abba bude idonta tayi ta saukeshi akan mahaifinta shima Saida gabansa ya fadi ganin irin muguwar ramar da tayi, matsawa yayi ya riqota qoqarin hadiye damuwarta takeyi yace “anya babu wani abu a qasan zuciyarki uwar manya nasanki da baqin zurfin ciki menene waye?" Yana mgnr ne a rikice idanunta ta sauke akan Ja'afar da yake shigowa da kaya a hannunsa yaji tambayar da Abba yakeyi Mata hakan yasast saurin kadanta Kai ko bai haneta ba bazata iya fada ba a ganinta wannan sirrin gidanta ne tsakaninta da mijinta, ganin bazata fadaba yasa Abba furzar da iska yace “shikenan uwata banayi Miki dole Allah ya kawo Miki mafita" sakin hannunta yayi ya fice tabisa da kallo gabanta yana faduwa tasan bai gamsu da shirunta ba to Amma ya zatayi sirrin ciki sai hanji tasan babu abinda yàke tabbata a rayuwa dadi ko wuya komai me wuccewa ne zata hqr ta jurewa komai akan mijinta musamman da yake uban danta qaddara ta ko Ina ta hadasu batada yanda zatayi dashi bashida yanda zaiyi da ita dole su rufe sirrin juna, Kwananta uku a asibitin ta samu qwarin jikinta kullum suna tare a asibitin duk da ta lura har yanzun ba daidai yake ba Basu cika magana ba saidai kallo da ido amma yana kula da ita matuqa ya daukewa likitocin duk wani Abu daya shafeta su kansu suna jinjinawa qwarewarsa tare da mamakin yanda akayi hakan ta faru yana matsayin consultant doctor matarsa ta hadu da irin wannan matsalar me wuyar sha'ani wadda ko mutum ya warke idan ya shiga damuwa take taba tunaninsa. Ba huruminsu bane shiyasa basu zurfafa ba a fakaice dai suke bashi shawara suka sallamesu kwanaki biyar lkcn yaron yayi qwari sosai abu na masu abu kamar Wanda aka hurawa iska ya wani cika abinsa jajir dashi qirar ubansa duk Wanda yaganshi sai yace “masha Allah kamar ba bakwaini ba" daganan gdan sarautar akaso wuccewa ya tubure akan cewa shifa bazaa mayar da matarsa gidannan ba tunda dai ta haihu idanma can dinne baaso ya Gina Mata wani gdan akaita can zai zuba masu kula da ita Hajiya Innah ce ta dage itama akan cewa wlh bazaa kaita gidansa ba a dakinta zata zauna har sai tayi arba'in ita ba lfy ba shima Kuma ba lfyr ya cika ba kansa na cikin kwartanniya yace akaita can waye zai kula da ita da jaririn" Daurin gindi ta samu gurin Mai martaba dole ya hqr badon yaso ba suka wucce da ita fada ananma yaso hana kaita part din Hajiya Innah Amma Babu fuska yanaji yana gani aka wucce da ita bangaren Hajiya Innah daki guda ta ware Mata da parlour aka gyaranta aka zubawa jariri kayan buqatarsa shima wannan da yana ganin gata a gurin wannan family inda yake fuskantar adawar qarqashin qasa ta mafi yawan bangarori, Sunada wata Al'ada a gidan idan aka haifi jikin farko na da namiji qanne mahaifinsa ne zasu siyansa gadon bacci da kayan fitar suna harda bargon dauka a yanda tsarin yake idan baayi yaro hakan ba to qasqancine anayin wannan ne tun kwana biyu da haihuwa ko uku Amma shi gashi har kwana biyar duk Wanda ya kamata yayi Hajiya Fatsum da Hajiya Kaltume sun hanasu wannan Abu ya damu zuciyar Hajiya Innah da Ja'afar gashi ya siyo gadon anqi kwantar da yaron akai wai banasa akeso ba itakam rafi'ah bata wani damu ba saboda batasan zafin al'adar ba sai daren rana ta shidda da Ja'afar ya shigo dakin tana kwance tana feeding din yaronta ya zauna ya zuba musu ido duk ya susuce yace “ina cikin damuwa fah Rafi'ah meye yasa hakan take faruwa dana ya kasa samun gata a dangina idan har akayi suna baa kawo gadonnan ba shikenan bazai gaji sarautar gidannan ba meyesa komai daya shafeki yake zuwarmin a baibai Meye karfa Rafi'ah dazu Hajiya Kaltume take cemin wai duk matar data haifi Lil Prince aka kasa samun gadon baccinsa daga dangin ubansa to karface Kuma asalinta jinin bayice harma tana cemin indai akayi suna baa samu ba to wajibine a cireki daga cikin zuri'a domin zaki bata iri meye kalmar karfa take nufi ne....." _More comments_ _More typing_ *_45-46_* _____________________________ _____________________________ Duka na sosai kalamansa sukayi Mata Wanda suka sanya zuciyarta lugude itakam wannan abu na wannan fam yana bata ciwon kai ta rasa meye laifinta meye ta tsare musu, shirun da yaji tayine yasashi cigaba da cewa “Al'amura sai lalacewa sukeyi gashi wadda zatayimin wannan alfarmar daga Badi'ah sai Karimah to Badi'ah mahaifiyarta ta hanata dazun take fadamin ta siyi gadon Amma Hajiya Kaltume tace idan ta bada Allah ya daidaitata ita Kuma Karimah babu ita a jadawali saboda kasancewarta qarama a gidannan na rasa ta Ina zan bullowa lamarin nan  Allah kibani mafita" Numfashi taja tare da yunqurawa ya taimaka Mata ta tashi zaune ta dubeshi tace “in advise ka cire jinin bayi Kuma karfa daga sashinka hakan zaisa ka rinqa samun matifa cikin rayuwarka Ja'afar don Allah kayimin wannan alfarmar inaji ajikina idan naci gaba da zama matsayin mata a gareka zamu wanzu cikin rayuwar qunci Koda kasancewar nasan duk wani Abu daya fado rayuwata to yardar sarkin sarkice Wanda baa masa dole, Ja'afar bandamu da nakasance cikin farin ciki ba indai farin cikina zai tafa darajar wani shiyasa a rayuwata bancika damuwa da dole saina rabi wani ba tabbas abinda Hajiya Kaltume ta fada maka gsky ne Koda akasin hakan ne Toni na gasqata maka Ni yar bayice Amma ba qasqantattun bayi ba bayin Allah wadanda suke yarda da duk wani hukunci nasa a ban qasa Ina jiran ka yanke duk hukuncin da zaka yanke Allah na roqeka kada bakawa kowa ikon kawo gadon daraja idan hakan ta kasance ku koremu daga garin azare...." Saurin rufe Mata baki yayi yana girgiza Mata Kai ta zabura ta miqe cikin bala'in da baitaba tunanin ta iyaba ta nunashi da yatsa tace masa “saime Ja'afar shine me danka kirani baiwa kuka ka kirani karfa Ina taka baiwar daka halitta sannan Ina taka karfar to duk abinda zakace ko a fada  maka ka fadamin na shirya karbarsa Allah ya tsinewa Wanda ya fas...." Dauketa yayi da Marin daya sanyata kifewa a gadon daidai lkcn da Hajiya Innah ta shigo ta rafsa salati tace “meye hakan magaji bakada hankali zaka Kai hannunka jikinta yarinyar da ba lfy ta isheta ba meye ma ya farune" Huci yakeyi kamar Wanda ya hadiyi maciji ya sake nunata da yatsa kawai sai ya juya ya fice a fusace Hajiya Innah ta matsa da sauri ta riqo Rafi'ah tace “meye ya farune kun ninkeni baibai fah" cikin kuka ta rinqa zayyanewa Hajiya Innah abinda ya faru taja fasali tace “to shine zaki tada hankalinki har kina daga muryarki sama da tasa bayan kinsan halin mijinki ko qalau yake ba hqr ya cikaba balle yanzu da kansa yake dawa Rafi'ah dole ke hqr ya Kama domin ke aka cuta" Sosai ta rinqa kwantar Mata da hankali harda tayi shiru ta dauki jaririn ta fice dashi tunanin duniya ya damu Rafi'ah gabadaya komai ya daukar Mata zafi tanason ta samu wanda zatayi Hira dashi taji dadi babu Hajiya Innah ta saka Mata ido ko yan'uwanta ne sukazo bata barin dakin saboda kada ta fadi wata mgn da zata fallasa sirrin gidan sarautar tayi kuka kamar ranta zai fita ita daya kamata a rarrasa ita akewa tsawa harda mari saboda gskyrta wannan dare dukka bangarorin babu Wanda ya rintsa Ja'afar tunanin maganganun da Rafi'ah ta fada masa ne da Kuma mafitarsa da dansa ya hana idonsa rintsawa ita Kuma alhinin wannan jarabar rayuwa ta zaman qasqanci da boranci tun zamanin quruciya sune suka hanata rintsawa Hajiya Innah kuwa tunanin ta inda zasu bullowa wannan al'amari da yanda zaayi su samu gadon daraja ne ya hanata bacci inda Hajiya Fatsum Kuma bokanta yace daga ita har Ni'imah su tube tsirara kowacce a bangarenta su tsaya a tsaye su kwana a haka kada suyi gyangyadi domin sunayin bacci asirin da suka qullo na haukata Rafi'ah kansu zai koma itakuwa Hajiya Kaltume neman ta inda zata fara bullowa Ja'afar da iyalinsa ya hanata rintsawa Abu na farko daya kamata tayi shine tasan yanda zatayi ta qara shiga tsakaninsa da Rafi'ah sannan ta sace wannan jariri kafin wayewar gari. Kiran sallar asubar farko Rafi'ah ta tashi da wani matsanancin ciwon Kai ta riqe kan da sauri tare da fara karanta izaja'a ta dan samu relief daidai lkcn da taji an bude qofar an shigo kasancewar da duhu bataga me shigowar ba ana gama shigowa Kuma sai aka haskenta ido da wata fitila me masifar haske ta yunqura zata miqe abinka da mara cikkakiyar lfy sai tashin ya gagara ta rintse idonta daidai lkcn da taji an watsa Mata wani ruwa anyi baya da sauri. Aikuwa saita wani yi tsalle ta miqe ta qwallah qara tare da damqar jaririn ta qanqame Hajiya Innah da Ja'afar har gware sukeyi wajen shigowa, Hajiya Innah ta kunna glub ta rintse idonta da sauri saboda tashin hankalin data gani inda Ja'afar ya nufeta a guje yana fadin “ Innanillahi wa innah ilaihirraji'un Rafi'ah meye hakan lfyrki kuwa tsirara fa kikayi...." Daukeshi tayi da wani mahaukacin mari tana qara matse danta a qirjinta tana wata dariya me hade da kuka tana cewa “ina ruwanku munafukai azzalumai algungumai dukkanku saina kasheku duk Wanda yazo gurina saina harbeshi danane ni na haifi abuna babu me rabani dashi daga yau nasa masa suna mai martaba Muhammadu Mahir eh sunansa kenan sunansa kenan Allah sunansa kenan dana sunansa kenan Ja'afar ya mutu Mahir maraya ne hhhhhhh Ja'afaru ka mutu ka huta nima na mutu na huta kowa ya mutu ya huta..." Wani baqin tashin hankali da dimuwa Ja'afar ya shiga ya matsa gurinta saikuwa ta rarumi kaskon wuta ta jefosa dashi tana qyalqyala dariya tana cewa “bazan baka danaba nawane ni kadai kufice ku fice nace ku fice ko na yankaku na shanye jininku hhhhhhh suwaye nan kowa bayasona Ni inason kowa kowa bayaqina ni inaqin kowa..….." Tashin hankali yasa Ja'afar yin kanta a guje aikuwa suka Kama kokawa daqyar yayi nasarar karbar yaron ya miqawa Hajiya Innah da taketa sallallami da kuka ya dauki doguwar riga yasa Mata ta hankadeshi ta miqe ta nufi qofa a guje shima ya bita yasawa qofar key ya daka mata tsawa itama kuwa saita daka masa tsawa tare da fuzge ribbon din data kame gashinta dashi ta kurma ihu tana wani dukan iska tana cewa “ni kubani dana Babu inda zaa kaimin dana abani abuna ...." Hadata yayi da jikinsa ya rungumeta sosai a jikinsa kawai saiya fashe da kuka ya bude baki yace “wai... Waime kikeyi ne haka Rafi'ah meye yake damunki ne bakiga bakida lfy bane...." Hannunta ta dora a bakinta tace “shitttttt ni qalau nake nafika nafi babanka nafi babarka lfy ba sunana Rafi'ah ba sunana Deluwa yehhhhh Deluwa takan bola Deluwa takan titi Deluwa ta kowac...." Hade bakinsa yayi da nata ta kuwa gasa masa cizo ya janye da sauri harshensa har saida ya tsage ya koma gefe yana kallonta Hajiya Innah daketa salati ta Kiran sunayen Allah tsarkaka tace “sai hqr Ja'afar sun haukata maka Mata innanillahi wa innah ilaihirraji'un....." Dagowa yayi da sauri yace “wht hauka Kuma Innah wanne irin hauka" sake kwashewa Rafi'ah tayi da dariya tace “eh da gaske ni mahaukaciya ce daga yau sunana Deluwa mahaukaciya yar macukule........... Zubewa yayi rijib a qasa sumamme tsabar tashin hankali Hajiya Inna tayi wajen gdan a guje tana ihu tana Kiran a kawo Mata dauki nan hadimai sukayo ciki a guje daidai lkcn da Jamal ya shigo gdan shima isowarsa kenan daga Rasha ya tawo ganin dansa dan yayansa da matar yayansa da baitaba gani ba ya siyo gadon da aketa badaqala akan samuwarsa sannan ya hadowa matar yayansa kayan fitar suna akwatu guda. Tun daga bakin qofa yasan gidan babu lfy yana shigowa yaga wata mace ta fice qunshe da Abu a hijjabinta da mugun gudu ganin yanda gidan yake a hargitse ga Kuma gajiya yasa baibi takanta ba ya nufi cikin gidan inda ya hangi mutane dodo guda a qofar bangaren Hajiya Innah haka ya rinqa kukkutsawa har ya Isa cikin part din wata muguwar faduwar gaba yaji lkcn daya riski yayan nasa warwas a qasa kamar matacce aikuwa wata alkafura yayi ya dira kansa ya fara danna Masa qirjinsa tare da neman ruwa ya fara quga Masa tsayin lkc sannan ya fara sauke ajiyar zuciya ya bude bakinsa da sunan matarsa. Sai lkcn aka ankara da bata cikin dakin aikuwa nan aka bazama nemanta lungu da saqo Amma Babu ita babu lbrnta Jamal ne yace lkcn da Yana shigowa yayi karo da wata mace ta fice daga gdan a guje Amma baibi takanta ba ya zaci mahaukaciya indo ce, salati Innah da Mai martaba dama sauran mutanen dake gurin suka dauka Ja'afar kam hade Kai yayi da gwiwa duk wani tunani ya qwace masa baimasan meye zai tuna ba a hankali yace “suwaye suka haukatata me tayi musu suka azabtar da ita da ciwo me cin zuciya da lalata ruhi Ina zata Ina take me suke nema me tayi musu sun illatata......." _Hqr My Fan's am sick wlh_ _More comments_ _More Typing_ *_47-48_* _____________________________ _____________________________ Shiru ce ta ratsa gurin na dan wani dogon lkc kowa zuciyarsa na searching abubuwa da dama mabambamta, zumbur Ja'afar ya miqe ya nufi qofa zai fita Mai martaba ya rufa masa baya shima Jamal miqewa yayi suka fita daga gdan duk wani guri da suke tunanin rafi'ah sun kasa samunta wasa wasa sai ga lkc yanata tafiya har goma na safiya shikam Ja'afar ya zamana kamar wani robbot ko bakinsa bai iya budewa sai tafasa da zuciyarsa takeyi. Mai martaba ne yace da Jamal su juya suje gdansu Rafi'ah sugani ko taje can hakan ce ta faru suka nufi gidansu Rafi'ah Mai martaba yasa akayi masa sallama da Abba dake asabar ce Abba ya fito ganin Mai martaba da kansa yasashi qarasowa da saurinsa yanayi musu sannu da zuwa yanda yaga dum jikinsu  a sanyaye ya fadar masa da gaba yace “meye yake faruwa ne naga kamar Kuna cikin damuwa?" Ja'afar ne ya magantu a karon farko yace “Rafi'ah batazo ba ko Abba shikenan na shiga ukuna ta shiga duniya Ina zataje hannun wa zata fada....." Jiri Abba yaji yana dibansa yayi saurin matsawa jikin motar yace “ban fahimta ba Ina Rafi'an ta tafi da danyan jego?" Mai martaba ne ya zame rawaninsa ya goge gumi yace “wato yau mun tashi da wani iftila'i ne Alh Nuhu lfy Lau muka kwana da Yarinyar nan Amma da asuba sai ta tashi da wani yanayi me kama da samuwar tabuwar kwakwalwa hakan tasa mijinta yanke jiki ya fadi wai kafin a samu  a shawo kan tashi matsalar baa ankara ba ta sulale ta dauke danta ta fice munyi yawo sosai a garin nan tun asuba muke zagawa ko zamuyi katarin ganinta Amma Babu ita babu alamarta duk inda muka tambaya sai ace baa ganta ba to shine mukayi tunanin ko nan ta taho Kuma gashi alamu sun nuna batanan" Durqushewa Abba yayi yana furta Hasbunallahu wani'imal wakil cikin mummunan tashin hankali miqewa yayi ya bazama gidan da sauri ya zaro wayarsa ya fito suka sake fita sune police station sune transport agent Amma Babu wani lbr me dadi saina godiyar Allah kawai ranar yini sukayi ko ruwa basusa a bakinsu ba Basu suka hqr ba sai taran dare suka koma gda kowa zuciyarsa cike da matsananciyar damuwa suna komawa gida Ja'afar ya shige bangarensa abin mamaki saiya tarar da Ni'imah a parlourn taci uwar kwalliya tana jiran dawowarsa. Baikobi ta kanta ba ya shige ciki ya bude dakinsa tare da dauko key din daya dakin na Rafi'ah ya datse ya koma dakinsa ya haura kan gado ya hada tagumi yanajin wani zugi da radadin zuciya da bashi da misali baiji shigowarta ba saiji yayi tana wani shafa sumarsa ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur ya saukesu akanta take taji tsoro ya lullubeta Amma saita dake tace “we meye na tada hankalin hakane bafa wani hauka da takeyi tsabar iskanci ne dama ba sonka takeyi ba shine take neman hanyar rabuwa dakai cikin sauqi...." Dagowa yayi ya sake saita injin idonsa akanta sosai take a tsorace Amma batason tabar zuciyarsa ta zauna kurum kamar yanda mahaifiyarta ta qyara Mata idan ya dawo tasan duk yanda tayi tasashi jin haushin Rafi'ah ta hanyar nuna masa tana sane ta Kama hauka don ta samu damar guduwar masa da dansa, hawaye ta dauke tace “na dade Ina jiye maka zuwan wannan ranar saidai Kai ka kasa fahimta Koda yake nasan bayin kanka bane asiri ne ke dawainiya dakai badon haka ba mema zakacj da Rafi'ah Ja'afar nidai Ina baka shawara ka cireta a ranka muci gaba da rayu....." Tsawa ya daka Mata tare da daga hannu zai dauketa da Mari sai Kuma ya fasa ya miqe tare da shigewa bathroom ya sakarwa kansa ruwa yana furzar da iska ya fito tana zaune inda ya barta yaja dogon tsaki ya dauki doguwar rigarsa yasa ya fice daga dakin ya bude Wanda ya rufe dazun ya shiga ya tada sallar nafila ya nata jerawa ba qaqqautawa bayan ya idar ya jima yanayiwa Rafi'ah da Mahir fatan fadawa hannu na qwarai. Alqur'ani ya dauka fara karantawa zuciyarsa na karyewa sosai yanajin yanda ruhinsa ke ciwo tabbas yasan a zaman da sukayi da Rafi'ah wata ukune kawai sukaji dadinsu watanni biyar duk sun tafi a banza ne to ko watsin da yayi da ita da rayuwarta a lkcn da tana da cikin ne yasats yanke Masa wannan hukuncin na rabashi da kanta da gudar tsokarsa Mahir? Tambayoyine da bashi da amsarsu hakadai ya rinqa zauniya Koda yayi abinda ya sawwaqa cikin karatun qur'anin saiya rufe ya rafsa tagumi yanajin yanda jikinsa ke daukar zafi alamun damuwa ta fara ratsa bargonsa ta zuba Masa ciwon gabobi da zazzabi me zafin narkar da nutsuwar ruhi.Zamewa yayi ya haye gadon ya kwanta yanajin yanda jijiyoyin kansa suke wani tartsatsin wutar azaba qwanyarsa tana neman tarwatsewa gashi Babu mataimaki sai Allah yaji sanda Ni'imah ke buga qofar yayi Mata banza saboda baisan meye yasa ba tunda ya dawo Azare ya barota a Abuja ganinta ma bayason yi idanma ya kalleta gabansa faduwa yakeyi. ********** Baiwar Allah Rafi'ah kuwa lkcn data fita daga gidan sarautar da asuba ta yanki shara a guje gudu takeyi na wucce saa da danta qunshe cikin towel ta sake qudunduneshi da hijjab dinta haka taketa keta dajin batare dako takalmi a qafarta ba haka take gudu a jeji gar ta fita daga Azare gabadaya ta shiga wani jeji me surquqi ta rinqa gudu ba qaqqautawa tana cilla qafarta ko Ina qaya zafin Rana baisa ta sunkuya, babban tashin hankalin idan ta waiwaya baya sai taga wuta naci a bayanta ganga ganga tana lasota haka zata qara zabura ta kwasa da gudu tana abbaton ya Khaliqu yini tayi ranar tana gudu babu ci babu sha ga cikinta inda akayi Mata aiki daketa azabar ciwo Amma Babu hankalin ta tsaya Abu daya da ya kasa mantuwa a ranta shine tasan idan taji danta ya motsa ta qara matsesa hankalin ta bashi abinci kuwa babu. Ba ita ta samu ta daina ganin wutar ba saita ta wucce dambam ta shiga wani dajin shima shikuma ruwane yake binta da mugun gudu yanason cinyeta haka suka rinqa tsere da ruwan sai dare Allah ya kaita rugar wasu fulani da farko da suka ganta sun tsorata ita kuwa tana zuwa taga wata dattijuwa tana matsar nonon saniya sun hadawa shanu wutar jin dumi aikuwa sai ta nufi dattijuwar nan ta tsaya akanta matar ta miqe da sauri a tsorace ganin mutum a kanta murmushi tayi kamar me hankali sai ta yaye hijjab dinta ta budewa Mahir fuska ta miqawa dattijuwar ta bude baki zatayi mgn abin mamaki sai bakin ha harde ta kasa mgn. Tayi tayi tayi mgn ta kasa kawai sai hawaye ya wanke mata fuska ta zube a gurin tanata kakari a dole mgn takeson yi ta kasa Abu daya da idan ta dage

Chapter 15 of 19