Share this page
tsakiyar titi numfashi ya sauke yaja motar ya qara gaba. Shiga fadar sarkin qofar bangaren nasa ya bude Masa ya shiga yayi parking ya bude motar ya fito taka qafar da zaiyi yaji kansa ya sara gabansa ya yanke ya fadi take yaji zuciyarsa tana tafasa “ Innanillahi wa innah ilaihirraji'un" ya rinqa karantawa har ya murda qofar ya shiga ko Ina na gdan qamshi yakeyi yanason Rafi'ah komai da yakeso a cikin watanni hudun ta gama karanceshi tsaf baiji fitowarta ba saiji yayi ta rungumeshi ta baya tana yar qaramar dariyarta me sanyashi nutsuwa tace “Ur are welcome My life...." Ajiyar zuciya yayi yana shaqar qamshinta ya juyota yayi kissing kumatunta yace “inasonki fatan kina lfy" qasa tayi da kanta tace “ina lfy kamar Kai" kalmar ta bashi dariya yace “haba yarinya da wannan dumar da ta fara girma a tumbinki zakiyi lfy kamar tawa?" Dagansa Kai tayi tana shafa mararsa yanajin wani irin yanayi ta dago ta dubeshi ya wani lumshe ido tace “zuciyar Rafi'ah da alama kanajin yunwa me kakeson ci na sama maka banson zaman gwarzon maza da yunw...." Bata qarasa ba ya hade bakinsu guri daya suka zube a kujera tasan yau ta ballowa kanta ruwa da alamun dama kadan yake jira daqyar ta qwaci kanta shima Saida ya samu nutsuwa tayi luf a jikinsa son mijinta takeji a hankali yana mamaye duk wani gurbi na qiyayyarsa na baya Ashe takusa ta cuci kanta da ta yarda son farin cikin wata ya hanata karbar nata farin cikin. Dagota yayi yace “me kike tunani?" Murmushi tayi tace “son mijina nake fasaltawa a zuciyata nakasa gane yanayin girmansa da matsayinsa na yarda na mutu dakai mijina kaifa?" Farin cikine ya cika masa ruhi ya rungumeta yace “na dade da yarda da hakan Rafi'ah tun kafin kisoni nasoki Kuma zan mutu da soyayyarki" luf tayi a jikinsa sun jima a haka Bai zaci zata sake magana ba yaji tace “kayimin uzuri a duk lkcn da na bata maka mijina bazan taba furta ko aikata abinda zai taba farin cikinka a halin Ina sani ba" sanyi jikinsa yayi ya sunsuna sumarta yace “Insha Allah" miqewa tayi tana takansa rawa yayi murmushi komanta dabanne ya dagata cak suka shiga ciki wanka yayi ita ta qara gyara jikinta ya fito ya canza kaya suka fita bangaren Hajiya kaltume suka shiga tana parlon tana ganinsu ta miqe tana washe baki tace “tun dazu naso zuwa naga lfyrki Dije tace baki tashi ba to sannu kinji yarnan Magaji meyesa baka kirani nazo mun gaisa ba me ciki batason yawo balle ita da ba lfy ce ta isheta ba" dadi yaji sosai a ransa ya zauna yace “hakane Hajiya shima motsa jikin yana da amfani" zama tayi suka gaisa ta miqe tace “bari na kawo miki wani Abu nasan jikalle na zai soshi" Kitchen ta shiga bata jima ba ta fito dauke da wata kula ta bude wata lafiyayyiyar gurasa ce ta alkama da aka mulketa da Zuma sai kunun tsamiya sai zuba qamshi yakeyi" kwantar da kanta tayi a jikinsa ya dago kanta yaga yanda take hadiyar yawu sukayi dariya shida Hajiya Kaltume yace “ta koma kamar mayya komai tagani tanaso tunda mukaje Mexico take sani barnar kudi a Rana sai tace tanason abu kusan kala talatin" Zaro ido tayi sukayi dari dukansu Hajiya Kaltume ta kirawo Jakadiya Indo tace “ki dauki wannan kayan ki kai bangaren magaji" gdy Rafi'ah tayi Hajiya Kaltume tayi murmushi tace “Ah haba babu komai ai dole mu kula dake haqqi ne akanmu am don Allah Ja'afar duk abinda ya faru baya a manta dashi ya wucce har abada Rafi'ah duk abinda kikeso ki aiko a karba Miki bani da wani amfani sai hidimarku" Jinjina Kai Ja'afar yayi yanajin dadi a ransa idan aka nuna anason Rafi'ah da cikin jikinta ji yàke kamar yayiwa mutum kyautar duniya, miqewa yayi ya kamo hannunta yace “bari mu qarasa ciki mun gode da kulawa" fita sukayi tanata zubawa Rafi'ah sannu" suna fita ta kwashe da dariya tace “zakuci ubanku waikai ne Mata ita Kuma me ciki har wani godiya kakemin kamar ka mantani nice dai Ummu kursumu yar mage baki dadin goyo sai baqin naci har wani proud akeyi Wai batada sabo tunda ta samu kwadayayyen ciki ai dole ta saba dani zan shekara yi Mata hidima domin Rana daya tak yahudu tuba babu hhhhhhhh" ta qara kwashewa da dariya. Bangaren Hajiya Innah suka shiga anan ya tafi yabarta saboda Hajiya Fatsum batanan anan ta kusan yini ita da Karimah qanwarsa yar wajen Hajiya Innah sunata hirarsu dake dama basufi sa'anni ba sai yammaci ta tafi bangarenta ta shiga hadimai sai hidimarsu sukeyi tayi wanka ta baje a qaramin parlour Dija ta kawo Mata kunun da gurasar tayi Bismillah taci tayi hani'an sauran tasa a freegde tayi alwala tayi sallar magrib ta kunna kallo anan yazo ya isheta shima yabiyeta sunata hirarsu abin da yakebashi tsoro da mamaki idan baya tare da ita sai kewa da tunaninta ya damesa Amma idan yazo sai ysji duk ya gundura duk wani motsi da zatayi maimakon birgeshi da yakeyi da yanzu haushi yake bashi, Sai darema da sukaje kwanciya yini yayi yana feeling nata Amma yanzu sai yaji duk haushinta yakeji gashi shi baiga wani laifi da tayi masa ba balle yayi fada yaji dadi duk wani Abu da tasan zai sanyashi farin ciki shi takeyi, itakam batajin komai a ranta kawai dai yanayinss ne yake bata mamaki sai ya kwanta ya tashi ya sake kwanciya ya tashi Saida yayi haka sau uku tanajinsa batace komai ba taji ya miqe itama saita tashi ta rungume pillow a qirjinta yakai ya kawoya tsaya a gabanta yace “na rass meye yake damuna wani haushinki nakeji Rafi'ah Kuma wlh bakiyi min komai ba" Allah sarki sai kawai tayi murmushi ta miqe ta dauki qur'ani ta dawo ta rusuna ta miqa Masa yasa hannu ya karba tace “a duk lkcn da najini a irin wannan yanayin nakan bar duniya da abinda yake cikinta ta na koma ga Allah ta hanyar ambaton sunayensa tsarkaka da Kuma karanta zancensa me dadi da sawa zuciya haske mijina kaima kayi haka nasan zakaji sauqin abinda kakeji...." Ajiye qur'ani yayi ya matso gabanta yana huci kamar wacce ta zagi uwarsa ya dago kanta kawai saiji tayi dauketa da Mari ya hankadata a gado ya hau bala'i yana cewa “wato saboda kin rainani harni zaki fadawa yanda zanyi idan Ina cikin yanayi ai ba duniya ce tayimin zafi ba kece kikayimin Kuma wama yace Miki banayin karatun qur'ani ko yau da asuba saida nayi nifa banson kirsa waike ta Allah to fadamin wanda yake bautar ubanki..." Fuuuu ya fice daga dakin yana cewa haba nima da jarabata in Banda qaddara ma mezanyi dake nifa baa hakicceni domin wahala ba ke kika rasa ba yar iskar da zata doramin hawan ruwa sakarya kawai" miqewa tayi da sauri ta leqa ta window jin tashin motarsa agogo ta duba 1:49am kawai saita dora hannu a ka ta rushe da kuka ita ba cin mutuncin ne ya bata Mata raiba aa fitarsa a wannan lkcn gashi gda basu kadai ba kowa da abinda zai fassara ta jima tana kuka ganin bazai kaita ba ta tashi tayi alwala ita ta rungumi qur'anin da aka mareta dominshi tana karatun tana hawaye tunda take baa taba wulaqantata irin wannan wulaqancin ba harda zagin ubanta wai JM da bakinsa yake ce Mata yar iska, sake rushewa tayi da kuka tare da daukar wayarta ta fara kiransa Kira daya tayi masa ya daga shassheqar kukanta yasashi saurin cewa “kinga don Allah kiyi Shiru wlh bazan iya kwana a gidannan ba zuciyata tafasa takeyi kaina kamar zai tarwatse Rafi'ah bansan meye yake damuna ba na kasa jurewa idan na cika takurawa cutuwa zanyi"........ _More Comments_ _More Typing_ *_41-42_* _____________________________ _____________________________ Numfashi ta sauke tana qoqarin shanye kukanta tace “amma me nayi maka JM don Allah kayi hqr tun kafin ka fadamin laifina inasonka bazan iya jurewa wannan sauyin da kake neman wanzarwa tsakaninmu ba" numfashi shima ya sauke yace “calm down please ki kwanta ki huta babienmu nason hutu da safe zamuyi mgn" Bata iya jayayya ba hakance tasata cikin sanyin murya tace “shikenan kayi bacci cikin aminci Allah ya tsaremin Kai" kashe wayar tayi ta koma ta takure a saman gadon tana saqe saqe ta rasa tuno abinda tayiwa mijin nasu kwanciya tayi tana shafa cikinta da ya fara motsi jiya ta sauke ajiyar zuciya tanajin qaunar abinda ke cikinta a wannan daren dai daga ita har Ja'afar babu wanda yayi bacci shima din daya fita bai iya nufar gidansa ba asibitinsa ya nufa yayi parking a mota ya qarasa kwana saida yayi sallar asubz sannan ya juyo ya dawo gidan sarautar, a fada ya tsaya akayi zaman fada dashi sannan ya shiga gidan tana kitchen sanda ya shigo ya shige ciki yayi wanka ya canza kaya ya dawo parlon ya zauna, Saida ta gama shirya breakfast dinta ta fito tana jerawa a dinning taji gyaran murya juyawa tayi da sauri suka hada ido ajiyar heart tayi ta fadada murmushinta ta nufishi duk wata gaba ta jikinta tana rawa tana zuwa ta zube a qasan carpet din ta Kama kyawawan yatsun qafarsa tace “barka da safiya mijina" janye qafarsa yayi yace “ki bani abinci yunwa nakeji" miqewa tayi ta nufi dinning din ta hado masa kunun gyadar da tayi ta dauko masa doya data soya sai farfesun kifi tarwada ta kawo masa ta ajiye a gabansa ya sauko qasa cike da zumudi ya faracin abincin, cokalinsa uku a kunun ya ture ya sake Kai doyar bakinsa ya furzar tana kallonsa gabanta na faduwa ya ja farfesun yakai bakinsa kawai sai taga ya ture plate din yaja tsaki ya miqe ya shiga ciki. A mamakance Kuma a tsorace ta miqe tabi bayansa ta bude dakin ta shiga ya juyo ya kalleta itamma shi take kallo ta matsa a hankali dan nesa dashi saboda har yanzu tanajin Marin da yayi Mata jiya tace “kace kanajin yunwa naga Kuma bakaci abincin ba ka tashi" a hasale ya dago yace “me kikasawa abincin nan yake daci..." Da sauri ta kalleshi ya dakanta tsawar da Saida tasa dan cikinta ya dunqule yace “magana nakeyi Miki kin kafeni da ido" idonta ne ya cicciko da ruwa tace “wlh bansa komai ba...." Figarta yayi yace “qarya kikeyi kice bakisa komai ba kinsa komai muje kici kiji" a gaban abincin ya dangwarar da ita yace “kici kiji" daukan kunun tayi takai bakinta tasha ita bataji dacinba ta dago tace “ni banji ba" masifa ya rinqayi ta inda ya shiga ba tanan yake fitaba itadai babu abinda takeyi sai kuka ya juya zai fice tabishi da sauri ta riqoshi ta fada jikinsa yasa hannu ya rungumeta sukayi Shiru na dan lkc kafin ya dagota yasa bakinsa yana lasar hawayenta yajata zuwa ciki ya zaunar da ita yace “me kikewa kuka?" Kwantar da kanta tayi a jikinsa tana shafa bayansa ya gane abinda take nufi hakan yasa ya dagata cak ya nufi ciki da ita ya kwantar da ita ya kwanta a gefenta ya zubawa fuskarta ido. Murmushi yayi yace “meyesa ne Rafi'ah" a hankali ta bude idonta tare da janyo jikinta ta hade bakinta da nasa ya sukaja numfashi tare sun dade a haka tana shafa sumarsa shima yana shafa nata sosai suka tsuma juna kafin su Kai ga cimma burinsu sun jima sosai sannan suka saki juna suna mayar da numfashi ya shafa fuskarta yace “so sweet babe" murmushi tayi masa a rayuwarta batason fada balle mara dalili irin nasa hakanan dai babu wata walwala suka yini Abu qalilan ya rufeta da fada hatta Hajiya Innah data shigo duba lfyrta Saida ta fahimci akwai matsala Amma bata zurfafa ba dake dama tasan fadan halinsa ne, da dare suna zaune duk ta takura saboda Motsin kirki idan tayi rufeta zaiyi da fada wajen Tara na dare wayarsa tayi ring ya wani zabura ya miqe ya Kara wayar a kunnensa bataji me akace ba taji dai yace “to angama ganinan 20 minutes" miqewa yayi ya fice batare da ko ya kalleta ba taja ajiyar zuciya. Miqewa tayi ta gyara gurin ta shiga daki tayi wanka ta shirya cikin kayan baccinta ta sanya hijjab ta dauki hisnul muslum tana dubawa tana daukan addu'o'i ta Jima zaune sannan tayi addu'a ta kwanta, Shiru goma sha daya har daya bataji Motsin Ja'afar ba wayarta ta dauka ta danna numbersa ta kirasa har tayi ring Bai dagaba sake Kira tayi. Taji an daga taja ajiyar zuciya tace “Allah yasa dai lfy kake najika Shiru...." Jitayi anyi murmushi sannan akace “dake zama kikayi kina jiran dawowar abinda aka baki aronsa to ai dama kwanciya kikayi kikayi bacci zaifi Miki sauqi Ja'afar kam yayi nisa saidai Kuma gobe idan naga dama na baki aronsa, sorry fah babie" Qit aka kashe wayar taja numfashi tare da tashi tsaye cike da al'ajabi a ranta take tambayar kanta to dama ana haka kenan? Batada me Bata amsa hakan yasata ta koma ta sake kwanciya kishi na azalzalar zuciyarta hawaye nabin idonta tana karanto addu'ar annabi Yunus “ La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin" dahakadai daqyar bacci ya saceta itakam tana ganin rayuwa to me tayiwa Ja'afar haka ne daya fara juya Mata baya yana kantafi da mutuncinta. Washegari har hudu bai shigo gidan ba batayi zuciya ba ta Kira wayarsa akayi rejected takaici ya kamata Amma saita dake saboda kullum Amminta tana fada Mata ibada batada sauqi aljanna ce me sauqi idan ka iya sarrafa zuciyarka tare da naiman daukin Ubangiji a duk lkcn da wani Abu ya kulleka. Text ta rubuta Masa da zafafan kalamai da tasan zasuja hankalinsa Amma har dare babu reply hakan yasa ita da kanta ta fara zargin ko wani laifi tayi masa ta sake rubuta Masa saqon ban haquri ta tura Masa bai biyota ba har wayewar gari idan barawo ya rintsa itama ta rintsa. Da sassafe saiga Hajiya Kaltume suka gaisa tace “ina me gidan ko ba anan yake bane?" Qaqaro murmushi tayi tace “Eh ba anan ya kwana ba" murmushi tayi tace “nikam Rafi'ah Anya bazan baki shawara ba a zaman da nayi dake na fahimci kinada tsayawa akan addini sosai alhmdllh Zaki dace a rayuwa Amma fah sai kin tashi tsaye, in baki wani lbr Mana surkarki da tatafi Damagaran bafa kowa take dashi ba neman asiri ta tafi na mallakarwa kishiyarki mijinku ta yanda da quruciyarki da komai zaki zama bora bance kiyi shirka ba Amma ki dan tashi tsaye ki tallafawa kanki rayuwarnan ta yanzu baa zama wlh duk wanda kikaga yana fantamawa to ya miqe" Kallonta takeyi da rashin fahimta tace “ban gane ba Hajiya" miqewa tayi ta rufe qofa ta dawo ta zauna tace “saboda munafukai masu fakar ido am Rafi'ah da Hausa nayi Miki bayani ki miqe ki dage ki zama tauraruwa a gurin mijinki ta hanyar yan shige² nifa bance ki fita ba aa ki barmin komai zanyi Miki nidai hadin kanki nakeso" Saurin girgiza kai tayi tace “astagfirullah Hajiya aa bazan iyaba nikam babu wanda nake dashi daya wucce Allah shine zai iyamin" Shiru Hajiya Kaltume tayi tana nazarin mgnrta kafin tace “Eh hakane kam kin Kama dahir Allah yasa mu dace" miqewa tayi tace “zan wucce kidai duba maganganuna akwai gyara a rayuwarki idan ba hakaba kinaji kina gani Zaki zama yar kallo" sallama sukayi ta tafi Rafi'ah ta tabe baki tace “dama Hajiya Innah ta fadamin ba Allah ne take kawoki ba kaji mace yar kalan masifa zata liqamin tsiya ta jamin raba tsaba da mahalicci na" shigewa tayi daki tayi duk abinda zatayi dare yayi tayi addu'o'inta kamar yanda ta saba ta kwanta tanajin cikinta yanata motsi tasan harma da yunwa kasancewar damuwar rashin mijin nata ta hanata cin abinci. Ita burinta bai wucce ko a waya taji lfyrsa ba inda ya kasance duk Kira ana rejected haka ta wanzu idan taga dare yaqi tafiya takan tashi tayi alwala ta nufi mahaliccinta da, da yamma ta gama duk wani shirinta na karbar miji har dare tana tsara girkinta ta kashe lkcnta wajen shirya masa abinci tagama ta dauki wanka ta harde tana duba agogo takwai Tara goma sha daya Shiru. Cikin tsananin mutuwar jiki ta dauki wayarta ta katsa numbersa gabanta na faduwa ta Kira cikin saa ya daga batare da yace komai ba taja fasali tace “barka da yini" qaramin tsaki yayi yace “inajinki" a sanyaye tace “lfyrka nakeson ji kwana uku bamu gaisa ba" wata qaramar dariya yayi yace “idan banida lfy nan nake jinya saboda haka indai Ina wajen gdannan kikajini Shiru to qalau nake" Shiru tayi maganganun nata suna hautsina nutsuwarta ta hadiye wani Abu me ciwo tace “ba nufina kenan ba gani nayi baka nemana idan na kiraka ma sai kayi rejected don Allah ka yafemin Best wlh nakasa tuna kuskurena gareka iyakar sanina dakai cikin watannin da mukayi baka iya barin Abu a ranka wannan ba dabi'arka bace tawace nima Kuma kullum Ina addu'ar Allah ya sassautamin nauyin baki saboda gudun kamuwa da wani ciwon akan matsalar da zan iya maganinta da harshena" Maimakon yaji kalamanta sunyi tasiri a zuciyarsa saima tafasa da yaji zuciyar tasa tanayi yace “saime idan kin kamu da ciwon bake kika dorawa kanki ba kwanane yau ban shirya yinsa anan ba ni bama na Bauchi Ina Abuja Kira Kuma banaso ki daina idan kinqi kuwa ranki ne zai baci a banza sakarya kawai...." Ajiye wayar tayi da sauri saboda a duniyarta takan hadiye kowacce irin damuwa Amma banda cin mutuncin iyaye shikuma ta lura hakan yafi Masa komai sauqi, zuciyarta suya takeyi sosai nadamar Kiran nasa takeyi da tasan abinda zai fada Mata kenan, kuka kam har saida taji jijiyar kanta na daurewa ta hqr tasha magungunanta ta kwanta zuciyarta nayi Mata wani irin zafi. Abu kamar wasa tafiya sai qara miqawa takeyi daga sati antafi wata babushi babu alamarsa waya kam tun ranar da ta kirashi yaci mutuncinta take tsoron kiransa Amma ta wajabtawa kanta kullum saita tura masa saqon barka da safiya dana Saida safe shi kansa abin na damunsa sosai yarasa ya zaiyi ne wani sharadine Ni'imah ta gindaya masa wai idan ya kuskura taji lbrn yaje inda Rafi'an take sai tasa ya saketa shikuma tsoro ya shigeshi wani mugun tsoronta yakeji saiya daga waya zai kirata sai ya tuna cewa idan tasan ya kira Rafi'ah cin mutuncinsa zatayi hakan duk zafin kansa zai hqr ya share, wasa wasa har gashi da wata biyu a Abuja. Yau tun safe ya tashi dajin wani qwarin gwiwa nason ganin Rafi'ah yana qissima watannin cikinta fitowa yayi daga daki ya tarar da hakimar tasa a zaune tanata fama da tuffa ya dubeta yayi mata murmushi yace “gimbiya yau watanmu nawa rabonmu da Bauchi ne?" Dagowa tayi ta dubeshi a banzace tace “wata biyu da sati biyu mana wani abune?" Gabansa ne ya fadi yace “aa kawai dai na tambaya ne" yatsina fuska tayi tace “ok na dauka tunanin waccan yar iskar yarinyar kakeyi" dagowa yayi da sauri sosai kalamin ya tabashi Amma suna hada ido sai yayi qasa dakai yace “ah haba dai kawai dai tunanin cikin jikinta nakeyi" Wani banzan kallo tayi masa tace “to ko zakaje ne" qasa yayi da kansa yana wasa da yatsunsa kamar wani qaramim yaron da yaje jiran umarni ta daka masa tsawa tace “tambayarka nakeyi ko zakajene?" Saurin girgiza Kai yayi tare da dagowa kawai sai idonsa ya ciko da qwallah ya miqe da sauri ya haye sama ta sheqe da dariya tace “sakaran banza da kace bakaji saura shegiyar baqar kadarar can labarinta ma saiya shafe a duniyar mutane daga ita har cikin jikin nata muga ta tsiya _More Comments_ _More Typing_ *_43-44_* _____________________________ _____________________________ Tunda ya shiga dakin ya hade Kai da gwiwa kuka yakeyi sosai kamar yaron goye zuciyarsa na azalzalar sa ya tafi Azare ya gano lfyr matarsa da cikin jikinsa Amma babu dama tsoro yakeji kada Ni'imah ta fahimci inda ya dosa ji yake kamar idan ya bata Mata rai qonashi Ubangiji zaiyi dabara ce ta fado masa ya miqe da sauri ya rufe qofar ya shige bandaki da waya a Hannunsa ya fara duba number Rafi'ah Amma Babu a wayarsa tsoro ya qara cikashi gami da mamaki duk inda zai duba baigani bs hakan yasashi kiran Hajiya Innah ta jima tana ring sannan ta daga daga yanayin muryarta yasan akwai damuwa. A gaggauce yace “Am Innah Ina Rafi'ah?" Numfashi taja cikin tausayawa halin da dan nata yake ciki tace “anya magaji kana addu'a kuwa" katseta yayi da cewa “inayi Inna please kibani Rafi'ah magans nakeson yi da ita" murmushin qarfin hali tayi duk jikinta yayi sanyi tabbas akwai alamun nasara wata biyu an tafi uku ita kanta baya kiranta tunda ta kirashi tayi masa nasiha tare da fada masa halin da matarsa take ciki na yawan damuwa da kuka ga ciwon Kai daya sata a gaba ko abinci tasa a gaba saita kasa ci idan ta tambayeta sai tace ita ba damuwarta yazo gareta ba damuwarta ya daga wayarta taji lfyrsa Amma yayi block contact nata kota Kira baya shiga. Sake katse Mata tunani yayi da cewa “don Allah Inna kibani ita wlh inajin idan banjita ba komai zai iya faruwa Inna ko wani abu ya farune?" Numfashi ta sauke tace “akwai damuwa me tsanani a tattare da Rafi'ah yanzu dai ma kar naja maka zance bata gidannan tana babban asibitin Bauchi suna treatment nata sakamakon jininta da ya hau yaqi sauka yau kwana uku batasan waye akanta ba Amma sunankia take ambata dazu ma da mai martaba yazo sunce indai jininta bai sauka zuwa wayewar gari ba to zasuyi Mata Cx su cire cikin jikinta me watanni bakwai saboda idan aka basshi zaa iyayin biyu Babu ba itan babu shi...." Katseta yayi da cewa “Wht Innah Amma shine baku fadamin ba" murmushinsu tayi na manya tace “ai Wai da mukaga ba sune a gabanka ba Ja'afar duk da nasan wani abun bayin kanka bane Amma yana ishe hali nidai banga abinda yarinyar nan zatayi maka ba ka dauki wannan matakin akanta kafi kowa sanin yanda akayi auren nan bataso iyayenta basaso rabone kawai me gaggawa ya baka saar mallakarta Amma tazama abar wulaqantawarka kada ka sake kakai hqrn mutum me haquri da zurfin ciki qarshe idan ya kwance maka rawani duk duniya babu Wanda ya Isa ya daura maka so ka kiyaye" Kashe wayar tayi ta shiga dakin da Rafi'ah take kasancewar itace a gurinta taqi bari a fadawa iyayenta abinda yake faruwa koda sukazo asibitin kafin jikin ys rikice tace kada a fadawa Abbanta idan yaji akwai matsala, hakan tasa sukayi Shiru Mai martaba da Hajiya Innah da Karimah sune suketa jele sai Badi'ah yar Hajiya Kaltume ce Amma itama zakkace batayo halin uwa ba zuba Mata ido tayi cike da tausayi duk ta kumbura ta dashe kamar bayan hawan jinin ma akwai wani abin dayake damunta daidai lkcn ta wani zabura alamun allurar ta saketa idonta a rufe Amma sai bige bige takeyi ta qarasa da gudu ta riqeta abinda ya janyo hankalin Karimah ta shigo da sauri ganin yanda matar yayan nata ta datse harshenta tana make make jikinta yana jijjiga yasata fita a sukwane ta Kira likita ya biyota da sauri suka shigo daqyar ya samu yayi Mata allurar kashe jiki sannan ya Kira sauran ma'aikatan ya dubesu yace. “Wannan bazatakai gobeba a yau ayi Mata aiki arabata da cikin nan idan ta qara awa daya zata farka alamominta sun nuna zata iya kamuwa da ciwon jijjiga Wanda zai iya haifar Mata da depression domin kuwa akai damuwa danqare a zuciyarta" Babu bata lkc suka sanya Mata kayan theater suka turata suka shiga da ita dakin theater sai a lkcn ne Hajiya Innah ta Kira Mai martaba ya daga take fada masa halin da ake ciki tare da cewa “Ranka ya dade fah abinnan yafi qarfin Shiru a fadawa iyayen yarinyar nan likitoci sun shiga da ita dakin aiki Amma sunce sai wani shaqiqinta ko mijinta ko mahaifinta yasa hannu sannan zasu tabata" miqewa yayi daga kishingidar yace “to bari yanzu zan fito" dakansa ya tuqa mota hankalinsa a tashe sai office din Abba ya rakitosa suka tafi asibitin Abba baisan meye yake faruwa ba Saida sukaje likitan yayi

Chapter 14 of 19