Share this page
hakan, suna shiga pharmacy din suka miqa takardar da aka rubuta maganin wani matashin saurayi da alamun shine mamallakin gurin ya karba ya dago ya sauke idonsa akan Mahir gabansa ya yanke ya fadi. Miqewa yayi da sauri yana kallon yaron, itama Bari'ah sai tabishi da kallon mamaki kawai sai taga ya miqowa Mahir hannu duk qwuiyar Mahir da baya daukuwa gurin kowa sai taga ya miqa hannu shima yana bangale Masa baki mamaki ya cika Bari'ah da Alh Hisham sukayi murmushi a tare Alh Hashim yace “hukuncin Allah sai sauraro kiga maquiyacin yaron nan yanda ya wani miqa hannu gurin bawan Allan nan" Murmushi yayi yace “fine boy Nima nayi maka kamar yanda kayimin ko?" Yaron da baifi 17 months ba ya daga Kai sukayi dariya mutumin ya zubawa yaron ido yace “wato Alh danaga yaron nan naku Saida gabana ya fadi tunda nake bantaba ganin kamantayyar halitta irin wannan ba tsananin kamarsa da yayana mamallakin wannan pharmacy din tasa gabana faduwa tare dajin qaunar yaron a raina" Batare da sunba abin muhimmaci ba sukace “ai dama haka Allah yake ikonsa" Jamal da Dan banzan surutu ya sake dubansu yace zaku bani dama na dauki hotonsa duk da nasan Prince baya cikin nutsuwa Amma zan nuna masa yaron nan nasan zaiji dadin ganin me kama dashi wlh tallahi shi da kuke ganinsa kungansa can a hoto" Nuna musu hoton yayi yace “ya rabu da matansa du daya ma ana kyautata zaton ta mutu dayar kuwa ranar daya samu lbrn mutuwar dayar ya saketa saki biyu so dama ya taba yanka Mata Kati sau daya yanzu haka baya qasarnan yana Canada sama da shekara daya babu Mata kullum mafarkinsa matacciya zata dawo" Dariya yayi sosai yace “Allah Sarki Yaya yaci engine brain am mema zaa baku?" Miqa hannu yayi ya dauko maganin tare da rubuta yanda ake amfani dashi yace “amma likitan daya rubuta muku maganin Nan babban likita ne saboda ba kowa yasanshi ba indai Kuna da rabon qara haihuwa zaku samu kwanan nan Allah ya kawo twince" Su dariya ma yake Basu duk ya susuce sai surutu yakeyi kamar zautacce Alh Hashim yace “nawane maganin?" Murmushi yayi yace “ah haba aini na zama dan gida in wannan ma ya qare ku dawo wlh kyauta zan baku albarkacin wannan zuqeqen yaron me kama da Prince am ni yama sunansa?" Alh Hashim yayi murmushi yace “Muhammad Mahir" wani ihu yayi yace “Allahu Akbar tudu biyu sunan ubana ne dashi Kai dole nayi maka kyauta kaida uwarka" Bari'ah ce tayi murmushi tace “banice mahaifiyarsa ba qanwata ce tana mota yaro kayi uba a sama dama uwarka ta damemu da kukan Mahir maraya ne" nandanan tausayi ya cika Jamal yace “Allah Sarki buwayi yanzu uban wannan kyakkyawan yaron ya mutu sannu kaji dole uwa taka tayi kuka ni wallahi kayimin yaro ka samu sabon uba kaji?" Kwantar dakai Mahir yayi a kafadarsa yana dan gwarancinsa saboda maganar Bata fita sosai a haka suka fito zuwa bakin motar Rafi'ah na tsaye tana danne danne da wayarta taji takunsu ta dago idanunta sanye da glass ta sauke idonta kan Jamal hakanan taji wata faduwar gaba ta sake saita idonta akansa shima abinda taji shi yaji tare da amsar wani rikitaccen saqo cikin sakanni numfashi suka sauke a tare itadai kallon sani takeyi Masa Amma takasa tuna inda tasan kamanninsa inda shikuma yake aika Mata da wani saqo. Kawar dakai tayi tace “mamaki maquiyacin dana a hannun baquwar fuska ya akayi haka?" Murmushi Alh Hisham yayi yace “muma haka mukasha mamakin Nan" mota ta shige tana cewa “wannan ya tabbatar muku Dana Dan gayene baya jituwa da yan gaya shiyasa baya yarda da kowa sai an Gaye" dariya sukayi Jamal yana qara saita idanunsa akanta yace “inason yaronki mamana" da sauri ta kalleshi tace. “Muryar dana sani Amma a Ina nasanta?" Kwashewa yayi da dariya yace “up ni a mafarki Mana tsuke fuska tayi tamai da kanta qasa shima baibi takanta ba ya matsa sukayi qusqus dinsu da Alh Hisham sukayi sallama ya leqo yace “hajiya ta zan kawo ziyarar gaisuwa gami da roqon iri inason nima asammin wannan kyakkyawan irin na yafa a gonata" Wani dogon tsaki taja daya daki zuciyar Jamal hakanan Allah yayisu basa qaunar tsaki, itakam Bata kobi takansa ba Alh Hashim yaja mota suka tafi tunda suka taho take huci tana mita tana cewa “kowanne dan iska sai yace yanasona bayan na fadawa kowa ni matar aurece don mijina ya mutu Yana nufin dole sai nayi wani auren ne to ai banga gawarsa ba balle nayi takaba sudai Basu kulata ba saboda sun saba jin wannan tufka da warwarar tata tace mijinta ya muta ta dawo tace ita matar aure ce. Suna zuwa gda ta fita a motar fuuuu ita a dole anyi Mata laifi Alh Hashim da Bari'ah suka kalli juna sukayi murmushi Bari'ah tace “wannan karon zanyi iyakar bakin qoqarina guy din ya hadu sosai da alamun zata samu nutsuwa idan ta amince dashi" fita sukayi suka rufanta baya kowa ya fara harkar gabansa bata ware ba sai washegari sukaci gaba da harkokinsu Bari'ah tace Mata zasuyi baqi yau suka kuwa bata lkc wajen shirya dinner itace harda zabar abincin da zaa girka duk Wanda ta zaba sai tace tasan Ja'afar dinta yanasonshi" Basu gama ba sai yamma liqis ta nufi dakinta tayi wanka sukayi magrib ta dauki qur'ani tana karatu taji an turo qofar ta dago ta kalli Bari'ah daketa murmushi tace “Yallabai yace kizo ki gaisa da baqin kafin su tafi" lifaya ce a nade a jikinta kawai ta miqe ta fito ta nufi parlourn baqin tare da sallamarta gabanta ya qara faduwa ganin mutumin jiya me muryar Wanda ta sani ta kuwa daure fuska Alh Hashim yace “zauna Mana Rafi'ah" tsuke fuska tayi ta zauna tana wasa da yatsunta inda Jamal ya kafeta da ido ganin yau sai taga ya qarayi Mata kwarjini fiye da jiya. Alh Hashim ne ya kawar da shirun da cewa dama haka Allah yake ikonsa qila dama rabon haduwarki dashine yasa tunaninki ya dawo kika tuna kinyi karatun medicine har kika tuna da maganin da yakamata ki taimaka Mana dashi kika rubuta mukuma muka tafi neman gaibu don Allah ya sani har mukaje pharmacy din farko ban yarda akwaishi ba saboda wani lkcn maganganunki suna sabawa da hankali Amma da mukaje akace akwaishi maganin sune dai nasu ya qare sai na samu karsashin daukarmu nakaimu R&j domin mu siyo kwatsam sai mukayi katarin haduwa da wannan bawan Allah so abinda nakeso dake Rafi'ah ki nutsu ki fahimcesa idan da hali ki buda zuciyarki kigani kozata karbesa kinji" qasa tayi da kanta tana matsar qwallah tace “amma Alh nasha fada maka Ni matar aure ce don Allah ku daina takurani nayi soyayya wlh bazan iyaba zuciyata shi daya takeso Kuma ya tafi yabarni idan bashi ba bazan iya rayuwa da kowa ba" Mamaki ne ya cika Jamal ya miqe yana riqe da hannun Mahir ya matso gabanta ya tsugunna Alh Hashim ya miqe ya fice, ajiyar zuciya yayi yace “da farko nayi Miki kallon tuhuma dana sani Amma dana tuna wasu abubuwa saina cire tunanin komai araina nasa a zuciyata Kama biyu kikeyi min tabbas hakane Rafi'an Prince ta mutu kwana biyu da haukacewarta an samo gawarta data babienta a dajin Dambuwa Kuma ke ance Mijinki mutuwa yayi so karna jaki da nisa My Raf inasonki Kuma aurenki na daura dambar yi duk da kasancewata saurayi hakan bai dameni ba domin sunnah zan raya ma'aiki shine yayi mana nuni da hakan zan aureki Rafi'ah da gaske wlh tun jiya na afka ki bani hadin Kai bada sauri ba mu fahimci juna ke nifa idan kika amince dani zaki aureni gobe zantada hankalin Azare baki dayanta sai an dauramin aure dake...." Wani Abu taji ya caki qirjinta da yasata dafewa tace “azare! Azare!! Azare!!! Kamar na tabajin sunan?" Dariya yayi yace “ya Kama babie kina qasar Hausa kice bakisan Azare ba ni dan sarautar Azare ne mahaifina shine sarkin Azare yayana daya namiji yana Canada shekara guda bashida lfy saidai yaji sauqi idan bege da shauqin rashin matarsa da dansa ya motsa Masa Kuma yayi kamar ba zaiyi raiba Ina tausaya masa sosai har kuka nakeyi Masa saboda magauta sun sashi a gaba kawai don ya kasance me jiran gado shi kansa anso haukatashi Allah Bai nufaba sai aka sa Masa tsanar qasar Nan gabadaya wannan dalilin yasashi komawa Canada dazama Amma dukiyarsa duka tana Nigeria duk wata jaha dake arewacin Nigeria idan kika shigeta zakiga R&J pharmacy mallakinsa ne sunansa ne da sunan matarsa marigayiya Rafi'ah....." _Comments_ _Share_ _Vote_ *_Ummuh Hairan_* [2/2, 6:28 PM] Real Oum Hairan: I think you'd like this story: "MY BESTIE'S HUSBAND" by realfauzahtasiu on Wattpad https://www.wattpad.com/story/252522858?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create_preview&wp_uname=realfauzahtasiu&wp_originator=YZa%2Bnq8Gv74dk%2Br3fmroHt2fOS%2BrJAgPESvojabuR6mlrCBKlGcg1k%2FY8%2FEhPI0MmEXId7KOWuX%2F9qb4sodRsV9pyRkdk1Kk%2Bbe1YCuenDmpizIAObNjZFqoveTxmA0%2B *_Mbh_* *_Ummuh Hairan_* *_Wattpad-realfauzahtasiu_* *_Telegram Link_* 👇🏻 https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7 *_53-54_* _____________________________ _____________________________ Shiru tayi batare da tace masa komai ba ya zuba Mata ido yana jiran tace Amma taqi cewa sai ya miqe yace “kiyi tunani akan manufata ta alkhairi ce gareki dani baki daya idan kin yanke hukunci zan kiraki sai naji ya ake ciki saboda nasan mataki na gaba" tabe baki tayi ta miqe itama yabita da kallon mamaki tunda yake baitaba ganin birkitacciyar mace irinta ba tama saurareshi din babu dama. Qwafa yayi daidai lkcn da Alh Hisham ya shigo suka qara gaisawa yace “yadai ta amince kuwa?" Murmushi yayi yace “aa batama cemin komai ba inaga barinta zanyi ta nutsu tukunna saita yanke hukunci" numfashi Alh Hashim ya furzar yace “haka takewa kowa bazatace maka komai ba saidai kawai zan baka dama ka turo magabatanka ayi mgn inaganin hakan zaisa ta samu nutsuwa" Kallonsa yayi da sauri yace “da gaske?" Murmushi yayi yace “eh da gaske mana" hamdala yayi yace “Amma naji dadi sosai gobe kuwa zan tafi Azare zan sanar da Mai martaba abinda ke faruwa idan ya amince jibi ma zamuzo" Jinjina Kai Alh Hashim yayi suka fita ya rakashi har gurin motarsa cike da kulawa inda yabar shirgin sha Tara ta arziqin daya hadowa mahir sun jima suna tattaunawa sannan sukayi sallama ya tafi Alh Hashim yana komawa gida ya Kira rafi'ah balbaleta da fada yayi abinda Bai tabayi Mata ba yana tuhumarta dalilin wulaqanta Jamal. Hawaye ta rinqa sharewa tsayin lkc yana fadan nasa kafin ya sauko ya zauna yanayi Mata nasiha taci gaba da matsar hawayenta kamar tana daukar abinda yake cewa, Saida ya dakata sannan ta dago tace “bazanyi jayayya da abinda ka zartar ba Amma inason ki fahimceni wlh bansan komai game dani ba inaji a jikina Ni matar aurece Amma bana iya tuna komai so kuyi hqr ki qyaleni na rayu a haka har zuwa lkcn da Allah zai kawomin qarshen matsala ta tabbas akwai wani Abu da kullum zuciyata ke qoqarin tunawa ta kasa" Shiru yayi na dogon lkc Itakam Allah yayi Mata baiwar saita kalami idan ya biyeta bazasu tsinanawa rayuwarta abin arziqi ba dubanta yayi yace “amma da sharadin zaki daina fita ko Ina don na gaji da mazan dakemin sinturi a gidana" saurin daga Kai tayi tace “na amince da hakan" dariya ma taso ta bashi saidai ya dake ya tashi ya shige ciki miqewa tayi ta shige ciki ta Kama danta suka kwanta ranar kwana tayi bata rintsaba ta takurawa kwanyarta son tuno abinda ya goge a cikinta hakan yake haifar Mata da matsanancin ciwon kai. Kwanaki suka rinqa tafiya cike da abubuwa masu rikitarwa duk yanda Jamal yaso ta bashi hadin Kai taqi yaje ya samu Mai martaba da maganar auren shine yace masa ya fara samun soyayyar yarinyar tukunna gashi abinda yake tunanin bamai wahala bane yayi masa wahalar samu, duk da bata bashi damar soyayya ba Amma tana sakin jiki dashi suyi hira. Abinka da abinnan da hausawa suke cewa me da Wawa soyayyar da yake nunawa Mahir tasa takejinsa a jikinta idan yaga haka yakan dauka fara sonsa tayi Amma da yayi mgn sai tace itafa uban danta kawai takeso bayanshi bata ra'ayin kowanne namiji a duniyaWannan kalma na Sosa zuciyar Jamal saidai bashida wata madafa shi s hakanma dadi yakeji duk da ya zurma da yawa yakan taushi zuciyarsa akam ta sassauta Masa kar yaje yayi saukon bukukuwa ya Gina zuciyarsa da qaunarta Rana daya ta juyansa baya Da wannan tunanin yake ragewa kansa shauqi game da ita Al'amarin Ja'afar kuwa tunda Rafi'ah ta Bata ya shiga kwale²n masifa tun suna sakaran ji ko ganinta har suka fara fidda rai tsayin wata guda shikam yaqi lfy kullum cikin faduwar gaba da ciwon qirji yake, dadin dadawa Ni'imah da taketa qoqarin dole wai ita saita gogensa tunanin matarsa da dansa yakanyi Mata kashedi me qarfi game da hakan saidai taqiji wannan yasa suka rinqa samun sabani idan taje ta isheshi da mita wani lkcn idan takaici ya isheshi ya ware qwanji yayi Mata mugun duka ranar saidai ta kwana a bangaren Hajiya Fatsum. Ana haka watarana ya zaneta cikin dare tazo ta isheshi aikuwa ba arziqi ta gudu bangaren Hajiya Fatsum tana kuka anan hajiyan take fada Mata tayi hqr bayin kansa bane aljani sukasa ya cire masa tunanin Rafi'ah sannan ya batar dashi shine suketa fada da zuciyarsa da aljanin idan ya ciks takurawa ma haukacewa zaiyi shima, suna tsaka da wannan tattaunawa kawai sukaga wani jan haske ya keto bango ya nufosu gadan gadan take suka watse suka rinqa tsere Amma Saida ya cimma Hajiya Fatsum kawai saiji sukayi ta fasa qara ta fadi qasa Tim tundaga wannan Rana ta zama kamar mutum mutumin babu motsi babu magana babu komai a wannan ranar ne Kuma bakin Rafi'ah ya bude, Sosai hankalin kowa ya tashi Amma banda Ja'afar da ya fara susucewa kullum cikin hada kaya yake ana riqeshi zaibar gari wata Rana da bazata goge ba cikin tarihin rayuwarsa yana kwance da dare kawai saiji yayi an qwala mass Kira ya miqe a firgice saijin murya yayi ana cewa dashi "Canada ka tafi Canada matarka da danka sunacan zaka ishesu acan" Aikuwa batare da tunanin komai ba ya miqe cike da farin ciki ya dauki passport dinsa da master card dinsa da wasu takardunsa masu muhimmanci ya sace jikids qafa ya fice ta bsyan gdan saboda masifa ma ta katanga ya haura Hajiya Kaltume tana kallonsa tayi dariya tace “shege da kace bakaji ya tafi inda ajalinsa yake" tunda ya fita bai tsaya a ko inaba sai a inda zaiyi Visa ta tafiya kudi ya saki sosai akan cewa shifa tafiyar gobe gobe yakeso sunyi iyakar bakin qoqarinsu suka sama masa ta jibi daqyar ya hqr ya karba ya fice ya nemi masauki ya qarasa kwana washegari kuwa kashe wayarsa yayi Bai budeta ba Saida ya sauka a Canada ya nemi mazauni ya huta sannan ya bazama gari neman farin cikinsa duk Wanda yagani indai baqar fatane saiya tambayeshi inda zaiga Rafi'ah a qarshe ma mutane sukamai dashi mahaukaci kwana da kwanaki yana bilayi daganan zuwa nan a kwana na sha biyar ne aka kirashi a waya ake fada masa anga gawar Rafi'ah da danta a jejin Dambuwa daga tsaye ya yanke jiki ya fadi shine har yau Bai qara lfy ba. Jamal ne ya biyosa yake jinyarsa kwanansa ashirin yaji sauqi sauqi aikuwa a ranar ya turawa da Ni'imah saqon sakinta uku harda qarawa da cewa “dama Ina zaune dakene arziqin Rafi'ah tunda na rasata kema dole kibarni nayi rayuwata ni kadai ki nemi miji kiyi aure Ja'afar na Rafi'ah ne ta mutu ta barni zan jira ranar mutuwata mu hade da ita a darussalam" wannan saqo ya rikita Ni'imah ta rinqa kwarara ihu an dauka na iskanci ne Ashe qaiqayine ya dawo kan masheqiya tun ana daukan abin yanzu anjima har Abu ya tatura ta fara surutan tonan asirin kansu tashin hankalin da kowa ya shiga ba kadan bane aka rinqa Allah wadarai da halinsu. Daqyar Abba ya rarrashi daddy Ni'imah ta koma gdansa Yana tur da Allah wadarai da halinta ita da uwarta aka rinqayi mata magani amma Babu sauqi Abu sai gaba yakeyi dole sai daki aka ware Mata aka rinqa Kiran malamai sunsyi Mata ruqiyya aljani kuwa yaci laya akan bazai barta ba tunda Rafi'ah tafi qarfinsa ai dama Saida sukayi sharadi shi baya zama hakanan batare da ya kada wani juji ba sukace sunji sun gani saboda haka Babu inda zashi Abu kamar wasa Abu sai gaba yakeyi takai tana tsigar gashin jikinta da kanta tana cinyewa kusan shekararta guda a haka sannan aka samu daqyar wani malami ya rabasu Amma me yana barinta ya koma kan Hajiya Fatsum. Tashin hankali Ashe ga inda ake hauka can tuburan rawa da juyi takeyi tana yagar jikinta tunda akayi katari ta falle daga gdan sarautar har yau baaji duriyarta ba, inda Ni'imah take cikin tsananin nadama mabayyaniya son zuciya da zugar jahilan iyaye takaita ta baro gashi tayi uku babu babu mijin da take hauka akanshi babu aminiyarta babu auren Kuma babu mutunci da qima saima tarin tsana da qyamata da take fuskanta gurin mutane. Tazamo kamar mujiya gurin dangi da mutanen gari daga ita har uwarta babu me musu dariyar rahama saidai habaici da shagube wannan abu nasata kukan tashin hankali takan dade tana tunano rayuwarsu ta baya da Bestienta da irin alqawuran da suka rinqa yiwa juna takanyi nadama tare da tambayar kanta meyesa tayi kaza meyasa ta yarda aka zugata tayi kaza ina zataga Bestienta da gaske Bestienta ta mutu ta sanadin mugun abinda sukayi Mata? Tana tuna haka saita qara rushewa da kuka itace asalin asararriya mara gatan rahama data shiga tsakanin ma'aurata ta zamo silar sanyasu baqin ciki tabbas ta Debi kaya me yawan da batada me sauke mata, gabadayanta tayi sanyi bata iya komai sai kuka takan tuna a baya idan ta shiga mawuyacin hali Rafi'ah ke Bata shawara yanzu babu Rafi'ah waye zai bata shawara takanji dama hqr tayi da Ja'afar tun a farkon farawa kafin ya aureta data gane qawarta yakeso tabarshi ya auri aminiyartata da yanzu duk hakan bata faru ba Amma son kanta yasata qin gane kuskurenta Saida ta aikata kuskuren daya zarta kuskure. ******** A bangaren Rafi'ah kuwa shaquwa qara shiga tsakaninta takeyi da Jamal dole tasa ya hqr da mgnr soyayya ya dauketa kawai matsayin qawa mamaki yakanyi da wasu abubuwa da takeyi daya shafi harkokin lfy yakance Mata a Ina tayi karatun medicine sai kawai yaga ta fashe da kuka tace “tabbas nayi karatu Jamal Kuma mijina ma babban likita ne Amma na kasa tuna wani Abu daya shafeshi ko ya shafeni Jamal mijina fitaccen mutun ne fah Ina tuna kamar ya mutu kamar Bai mutu ba" bayason yawan furta masa mijinta mijinta da takeyi shiyasa yake basar da zancen ya aunata a abubuwa da yawa sai yaga ta wucce tunaninsa. Yau tun safe yake tunanin meye yakamata yayi Mata Wanda zataji dadi, murmushi yayi yayi ya gama ayyukansa ya Isa gidansu tana harabar gidan tana wasa da danta Bari'ah daketa faman laulayi na gefe tanashan lemun tsami ya shigo ta tsaya da buga ball din yayi parking ya fito Mahir ya nufeshi da sauri yana kiran “Abba oyoyo" daukan yaron yayi yana cillashi sama ya zauna suka gaisa da Bari'ah ya dubi Rafi'ah yace “maman dana inason mgn dake" tsuke fuska tayi yayi murmushi yace “banan na nufaba hajjaju am ko kinada intereste akan aiki?" Saurin kallonsa tayi sai Kuma tayi dariya shima dariyar yayi yace “akwai sabon asibitin da Yaya Ja'afar ya bude anan jikin pharmacy dinmu Rafi'ah Memorial Hospital so muna buqatar ma'aikata shine nake ganin kamar kinada rawar takawa idan babu damuwa zan baki gurbi a asibitin kema kya rinqa rage kewa Amma me kika gani?" Wani ihu tayi ta rungumeshi tana dariya shima dariyar yayi yace “kinqi aurena Kuma kina susutani meye yasa Anya kinamin adalci" nandanan ta hadiye murnarta tace “bazaa aureka badin ni ta mijina ce shishi kadai" kawar da zancen yayi yace “zan gama Miki komai ranar litinin ki fara zuwa aiki kawai" sosai taji dadi Kuma tayi masa godiya har ya miqe tace “amma Jamal banida takarduna a hannuna da mijina ya tashi mutuwa dasu ya mutu" dariya sukayi duka yace “bazan baki inda zakike aiki me wahala ba saboda gudun shirme ni inaji ma a lab zan barki" dariya sukayi ya kalleta yayi murmushi ya shiga mota ya tafi. Binsa tayi da kallo Bari'ah tace “yana bani tausayi sosai Rafi'ah yaqi hqr da wahalta Miki ke Kuma kinqi hqr ki karbeshi don Allah ki bashi dama ko yayane" ajiyar zuciya tayi ta zauna tana matsa Mata qafa tace “uwar biyu bazaki gane ba ne kawai Allah bazan iya hada soyayyar wani data Abu Mahir ba ki barni kawai" sanin idan ta cika mgn fushi zatayi da ita yasata yin Shiru kawai sukaci gaba da hirarsu tna bayyana jin dadinta da aikin da Jamal yabata wannan kenan. _Comments_ _Share_ _Voting_ *_Ummuh Hairan_* *_Mbh_* *_Ummuh Hairan_* *_Wattpad-realfauzahtasiu_* *_Telegram Link_*             👇🏻 https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7 *_55-56_* ______________________________________ ______________________________________ Hakan ce ta kasance kamar yanda Jamal ya fada Mata ranar litinin dakansa yazo ya dauketa zuwa asibitin da safe tare da bata takardun daukar aikin ta cike tabashi duk da baa bata wani bangare ba, tunda suka shiga asibitin gabanta ke faduwa har suka shiga reception din tanabin hotunan da aka maqale a reception din da kallo tana sauke ajiyar zuciya batakai ga gama kallon hotunan ba taji murya a bayanta ance Mata “sannu" gabanta ne ya sake bada wani dam har saida tayi kamar zata fadi yayi saurin Kai hannu ya riqota taja wata wawuyar ajiyar zuciya tare da zuba idanunta kan fuskarsa, Murmushi ya sakar mata yace “wa kike tunani haka" numfashi ta sauke tare da janyewa daga jikinsa tace “ka tsoratani Jamal sainaji muryarka kamar ta JM dina" da sauri ya kalleta yace “waye shi?" Dago kanta tayi tace “Baban Mahir dina wani lkcn Ina tuna wasu abubuwa game dashi amma fah Raina yana fadamin ko ganinsa nayi bazan ganesa ba" saurin zama Jamal yayi saboda cikin kwanakin nan kalamanta suna sanyashi cikin tunani to Amma Alh Hashim yace itan qanwar matarsa ce to meyesa kalamanta suke Kama da wacce wani abunta ya Bata ne? Kullum tana saba lambobi idan an tambayeta sai tace JM dinta ya mutu Kuma idan tazauna sai take kalamin da suke nuna wani Abu sabanin haka. Zuba idanunsa yayi akan hoton Ja'afar dake maqale qato a reception din ya zubawa Mahir ido yana nazarin wani abu hakanan yaji zuciyarsa na raya Masa wasu abubuwa duk da ya dade yana qoqarin bijirar dasu Anna sunqi barinsa miqewa yayi ya dubeta ga mamakinsa itama hoton ta kafe da ido ko qiftawa batayi Kama hannunta yayi yace “kinsanshi ne?" Numfashi ta sauke me qarfi tayi murmushin yaqe tace “aa kawai Dana kalli hotonsa sai naga yanamin yanayi da wani dana sani shekarun baya Amma fah nakasa tuna inda nasanshi qila ma a hanya na taba ganinsa" Sake shiga rudani yayi bayan ya rakata office dinta ya koma nasa cike da tunani mamaki gamida zulumi wannan abin Yana bashi ciwon kai, wayarsa ya dauka ya lalubo number yayansa ya danna Masa Kira ring biyu ya daga muryarsa a kasalce yace “meye Kuma yake faruwa Jamal?" Ajiyar zuciya ya sauke yace “abubuwa da dama suna faruwa fah Prince kayi qoqari kazo 9ja gda ya rikice gefe Kuma da wani rikitaccen Abu da yake sani tunani da shiga zulumi" tashi yayi daga kwanciyar da yayi yace “jikin Barebarin ne ko kuwa wani abu ne daban?" Shiru yayi na dan lkc kafin ya dago yace “Mai martaba ya matsamin nayi aure har yana iqirarin idan ban kawo ba zai zabomin so nikuma wacce nakeso taqi bani dama a qarshe ma ta dasamin kokwanto Yaya inasonta sosai Amma nafijin tausayinta tayi loosing memory dinta gabadaya bata iya tuna abinda ya faru da ita shekara uku baya saidai wani lkcn takan so tuna wani Abu Amma Bata samun dama a farko Ina dauka kamace kawai kakeyi da Mahir Amma yanzu na fara tantamar hakan inaji a Raina kamar ba Kama bace jinine Yaya don Allah kazo ka ganta ko ka ciremin kokwanto nima na samu salama" Shiru Ja'afar yayi kamar bazaice komai ba sannan ya magantu da cewa “bana marmarin sake shigowa 9ja har qarshen rayuwata Jamal banida wani Abu da yayimin saura da zan kalla naji dadi komai na kalla damuwa yake qaramin am kaga ka manta da lamarin yarinyar ka nemi wata

Chapter 17 of 19