tace.
“Hajiya sannu da zuw...." Tsawa ta daka Mata tace “dakata irin tsiya barden goyo karki kuskura wannan bakin naki na gadon maita ta ambaci sunana na lalace kamar yanda wannan dan asarar ya lalace waike makira wacce ta tsotsi kirsa a nonon uwa kinzo daga zuwa kwana hudu kin kanainaye komai wato har tafiyar da aka dade da shiryata da yarinyar nan yar albarka kin hana yanzu dake zaayi ko aikuwa indai nice na haiheka bakai ka haifi kanka ba to baka Isa ka tafi da yar iskar yarinyar nan ba saidai ka tafi da Ni'imah itace ma ta dace da tafiyar domin ita tayi kalar turawan wannan me baqin jiki da baqar zuciyar bata dace da zuwa canba ka bari idan zaka Niger ko Africa ta kudu ko Kenya saika tafi da ita nanne ya dace da ita, sannan Abu na gaba wannan cikin dake maqale a mararta ban yarda dashi ba ba naks bane dashi tazo dan bazance a waje kayi Mata ba domin kanada Mata inda kanada rabon a kusa da tuni kasashi a inda ya dace"
Tunda Hajiyan ta ambaci cikin suka kalli juna tana rufe baki sukace “ciki?" a tare kallonsu tayi da sauri domin tayi subutar baki saita waske da cewa “eh jiya Ni'imah take cemin tana kwance batada lafiya to inba ciki ba menene?" Ajiyar heart yayi ya taka ya qarasa gaban Rafi'ah dake durqushe ya dagota yace “ok babu mamaki ai abin rabone Hajiya am ki manta kawai dama ita Ni nayi Mata dole bason tafiyar takeyi ba saboda haka kowacce ta zauna kawai zanje na dawo lfy dama wata kwangila ce da zanyi da wani campony so shine nakeson zuwa na gama komai kafin tsakiyar shekara Amma tunda abin ya zama haka zanyi qoqari na dawo nanda 2 mouths insha Allah"
Harara ta watsa masa tace “ba haka nace ba cewa nayi ka tafi da Ni'imah" qasa yayi da kansa yace “nifa wlh bazan tafi da itaba batada wani amfanin da zatayimin mace sai rakin masifa daka tabata tace ta gaji Hajiya babu ruwanki fah da harkar cikin gidana abinda ya shafi matana kowacce nasan amfaninta saboda haka babu me tsaramin yanda zan rayu da iyalina"
Fuuuu ya juya ya haye sama yana masifa muqus Hajiya Fatsum tayi saboda sanin halinsa ba mutunci ne dashi ba ko kadan juyawa tayi ta kalli Ni'imah dake tsaye riqe da qugu tama manta da Rafi'ah a gurin tace “wannan shegen yaron bayajin bari saidai Kai ka bari Kinga muje kawai waini wannan lemon kuwa kinbawa shegiyar nan Tasha?" Harara Ni'imah ta watsawa Rafi'ah ta waske da cewa jiya fa saboda wannan snatcher din yace na zauna a gidanmu ni wlh Hajiya na fara gajiya da wulaqancin danki idan bazaki iyaba ki qyaleni na tafi Mana saikace dole"
Ranqwashi ta zuba Mata tace "babu inda zaki kinanan Wai an dorawa kwado tanki wato so kike kibarwa baqar ashana gdan ta qoneshi ta qone me gidan ai kece mafitarsa idan ba hakaba kuwa to ganinsa ma saiya gagareni am ki barni da yar shegiyar nan da qafafunta zata tafi ai duk Wanda yaci tuwo Dani miya yasha ba Amina ba ko Niger ce gabadaya qarewar buzu shegiya me idon aljanu wlh a gidan dana dai baki Isa ki haihuwa saidai kita asarar qwayaye su lalace a banza"
Saukowarsa ne yasa su saurin juyawa suka fice tananan durqushe inda yabarta ba maganar Ni'imah ce ta batanta Raina ta Hajiya Fatsum ita a komai nata tana hqr Amma batason ana taba Mata martabar iyaye domin batada na biyunsu a duniya, sosai kuka takeyi harda shassheqa tana tambayar kanta ita wannan wanne irin aurene takeyi kowa baya qaunarta meyesa qaddararta tazo da wannan simatsin?"
Jitayi ya dagata cak ya nufi saman da ita bai direta ko inaba sai gado ya lullubeta da qirjinsa ta sakarwa kukanta jiniya tana cewa “don Allah ka qyaleni banaso Ja'afar wlh banason...." Rufe Mata baki yayi yana tsotsa yana sauke numfashi yana tura Hannunsa cikin sumarta tare da dora dayan a qirjinta ta rintse idonta ta tureshi ya fadi gefe kafin ya taso ta tashi a guje kamar walqiya ta shige bandaki shi dariya ma ta bashi yayi dariyarsa me isarsa ya miqe ya fice daga dakin sake shiryawa yayi ya hade abinda yasan zai buqata ya dawo ya ajiye Mata kudi masu yawa a saman bedside ya fice bangaren Ni'imah ya shiga tananan zaune sai chat takeyi daure da towel da alamun daga wanka ma ta fito murmushi yayi yace “kinji dadi ko kin hadani da mahaifiyata to meye ribarki don kinsa ta hanani tafiya da Rafi'ah?"
Tashi tayi zaune tace “ko banza munyi biyu babu ai Kuma sai aje a rungumi pillow abinda akewa bazaa samu ba saidai aci na kwararo" badan ya shirya tsiya ba da kwade bakinta zaiyi Amma dake yasan meye ya taka sai kawai yayi murmushi ya zaro kudi ya doranta a jikinta yace “kinyiwa kanki"
_Sorry yau banida charge shiyasa bakujini ba kuma banyi long typing ba_
*_Continuation 35-36_*
____________________________
____________________________
*_Cigaban na jiya_*
Ficewa yayi ya koma bangaren Rafi'ah dakinta ya shiga ya dauki qaramin akwatu ya zuba Mata kayanta bai bita kanta ba yaje yasa a mota ya dauki wayarsa ya kirata Saida tayi ring sai uku sannan ta dauka yace “ki fito Ina jiranki a parking space" yana fadin hakan ya kashe wayarsa yabarta tsaye sake da baki zuciya na raya Mata kartaje sanin da tayi cewa hakan zai bata ransa yasata daukar mayafinta ta zura takalmi riqe da wayarta ta fita bude Mata yayi ta shiga yatada ta kalleshi da sauri tace “hajiya fah tace kada ka tafi dani" Saida suka fice a get din ya waiwayo ya dubeta suna hada idanu sai hawaye sharr.
Tsuke fuska yayi yace “ikona ne hakan ba ikon Hajiya ba bata Isa ta yankamin yanayi da iyali na ba" daga haka Bai qara cemata komai ba itama taja bakinta ta tsuke sukayita sharara tafiya sune har Abuja a mota kafin sukai Abuja tayi bacci yakai sau hudu ita da kanta tana mamakin yawan baccin nata cikin sati guda da bikin nasu data zauna sai gyagyadi sai bacci.
Suna Isa gdan yayi parking ya sabi abarsa a kafadarsa ya shiga da ita ciki ya kwantar da ita a kujera ya zuba Mata ido lkcn da take bude idonta akansa murmushi ya sauke mata yace “baccinki yayi yawa saikace kasa Anya kuwa bansa babyn ba ta mafarkin na Hajiya" turo baki tayi tace “ni banida komai kawai gajiyar bikincan ne" ya bude baki zaiyi mgn tace “wayyoh kaina..." Saurin riqe Mata yayi yace “meye ya samu kan?" Harararsa tayi tace “ina ka kawoni?" Tambayar taso bashi dariya ya gimtse tare da daure fuska yace “au bakisan Ina satar mutane ba ai satoki nayi zanyi camping naki nayita baki aiki bazaki koma Azare ba saida kyautar babie"
Duka takai masa da pillow ya goce yana dariya ta miqe suka fara zagaya parlourn shammatarta yayi ya fada wani daki ya maqale jikin qofa tabisa ya kuwa rufe yace “masha Allah abani abinci na ko nayi aiki da qarfin da ilahi yabani na qwata" kukan shagwaba ta fara harda su dire diren qafa ya cafketa sama ya watsata gadon yabita ya turmushe sosai sukaba sama hayaqi suka jiyar da junansu dadi inda kowa yake baje fasaharsa wajen sarrafa dan'uwansa duk da bajin dadin abin takeyi ba har yanzu wuyar budurci bata barta ba Amma takan daure tunda ta fahimci mijin nata bamai takura bane indai kabashi yayi yanda yakeso to kaima zaka samu sauqi hakan yasa take sakar masa jiki tare da tayashi duk abinda ya dauko wannan Abu yayi mugun qara Mata martaba a idanunsa soyayyarta take qara narkewa a ruhinsa ta yanda take batattakar duk wani diso na son wani Abu bayan ita.
Wannan dare an more sosai washegari tashin asuba jirginsu yayi zuwa Mexico itadai bazata iya Dorar da tsayin tafiyar ba saboda wani irin yanayi da take a ciki ita ba me lfy ba ita ba mara lfy ba, sosai sun qoshi da tafiya tunda suka fara keta sararin samaniya take lefe a jikinsa shikuma sai shafa bayanta yakeyi inda suka bawa na kusa dasu aikinyi sukayita kallonsu suna shauqin jin dama sune, lkcn da suka sauka suka hau mota zuwa masauki sanyi kamar ya kasheta bata tabajin sanyin azaba irin na qasar ba ganin yanda take rawar sanyi yasasa kunna Mata room hitter.
Tare da bata wata Madara tasha ta haye gadon dake kusa da ita ta qudundune shima shiga yayi saboda ba qaramar gajiya yayi ba suka Kama bacci tsayin lkc sannan suka tashi tare sukayi wanka suka shirya ya bata wasu kayan sanyi da aka Basu a hotel din tasa shima yasa yabata coffee sukasha tare da cin abinci ya dauketa suka fice darene Amma kamar Rana tsirarun mutane sunata harkokinsu ta dade da lura da qasashen turawa da larabawa sunfi harkokinsu da dare,
Wani shagon siyayya suka shiga ya lodo Mata kayan sanyi suka fito ya sake biyawa wani gurin ya siya musu hot coffee sannan suka nufi masauki suka fara sabuwar rayuwa dakanta ta fahimci Ashe sunso suyi ganganci subarshi ya taho shikadai itama da take mace yanayin azabar sanyin yana sata shiga yanayi bare shi namiji lafiyayye dole ya buqaci dumin mace a jikinsa aikuwa tanacin ubanta babu qarya danma yañada tausayi idan yaga ta shiga yanayi yakan qyaleta.
Satinsu biyar a qasar Mexico ta fara rashin lfy ta gaske da farko ya zaci weather dince ta dameta ya rinqa lodo mata kayan sanyi yana siyo Mata duk wani nau'in abinci da zaisa ta rage jin sanyi Amma daga bisani saiya fahimci ita sanyin ma takeso batada aiki sai kwanciya a qasa shan ice da sauran abubuwan sanyi ga rashin cin abinci sai tayi kwana uku bataci abinci ba saidai ice ki jus sosai ya shiga damuwa,
To yauma tun safe ya fice sha'anonin daya kawosa qasar ya matsu ya gama su tafi shi tunaninsa duk wannan yanayin ne yasata shiga ha'ula'iYana wajen harkokinsa yaji hankalinsa yayo wajenta ya dauki wayarsa ya kirata bugu kusan biyar bata dagaba abin ya tsumashi dole ya ajiye komai ya nufo hotel din da sauri ya haura saman ya bude dakin ya shiga bata parlourn hakan yasashi fara kiranta Amma Shiru bude qofar dakin yayi gabansa ya yanke ya fadi hangota da yayi kwance a qasa a sume bakinta sai fitar da kumfa yakeyi,
Da mugun gudu ya qarasa gareta ya ciccibota jikinsa yana Kiran sunanta a gigice yana jijjigata cikin tashin hankalin dabai taba shigaba, dagata yayi cak ya fito waje da gudu da ita ya nufi emergency care din cikin asibitin suna ganinsa suka tareta aka dorata a gadon tura marasa lfy suka shiga da ita wani daki suka dorata a gado tare da jorner Mata na'urori shikuma sai danna qirjinta yakeyi, jinyeshi likitocin sukayi duk da kasancewar bangarensa ne tashin hankalin da yake ciki bazai barshi ya bata taimakon da take buqata ba,
Duk wani taimako na gaggawa Saida suka gama batashi ta fara sauke numfashi sukayi ajiyar zuciya tare da likitocin dashi ya matso yana zana musu irin sign din da ciwon ya fara bayarwa kafin ta kwanta hakan yasasu fara bincikarta cikin saa kuwa bincikensu ya nuna musu ai shigar ciki ke gareta na wata daya da awanni goma sha daya.
Wani ihu Ja'afar ya saki tare da yiwa Allah godiya ya rungumeta sai hawaye sharr ya sumbaceta yace “ni...Ni dama nasan aurena dake akai wani Abu me qarfi Allah baya hada lamarinsa a banza Allah na gde maka daka azurtani da samun qaruwa da mace mafi soyuwa a Raina Allah ka kareminsu ka tsareminsu daga sharrin duk wani abinqi" sake matseta yayi a jikinsa hawaye ya kwaranyo mata tun dirarsa ya tasheta taja ajiyar zuciya tare da qara gasqata girman Ubangiji tabbas Allah buwayi ne gagara misali burin Ni'imah kenan da anyi aurenta da Ja'afar ta samu ciki ta haifi Lil Prince Ashe ba haka Allah ya shirya ba ita da bata taba zataba bare ta kawo ita qaddara ta zaba a lissafin da likitan yayi ma ranar farko daya Santa mace ranar cikin ya shiga tabbas girman buwayar Allah abar jinjinawa ce.
Dagota yayi jikinsa cikin sanyin murya yace “har yanzu bakya sona Rafi'ah meyesa kika kasa koyawa zuciyarki son mijinki me sonki da qaunarki uban yayanki Ja'afar haba Rafi'ah me nayi Miki da kika kasa yafemin ne" rungumeshi tayi ta saki wani Kuma me ciwo tace “ni...nifa ba sonka ne banayi ba inajin tsoron Hajiya ta gane da gaske inada cikinka a jikina JM kasheni zatayi bata qaunata...."
Rufe Mata baki yayi da nasa ya lumshe qananun idanunsa itama ta lumshe nata sun jima a haka kafin su saki bakin juna yaja numfashi yace “bandamu da kowa ya tayani sonki ba nidai inasonki Kuma nine zan rayu dake matata ki cire kowa a ranki don Allah ki manta da kowa kinji?" Dagansa Kai tayi yayi murmushi yace “bari nayiwa Hajiya Innah albishir nasan zata tayamu farin ciki" da sallama ya fara wayar suka gaisa yace “wlh tananan da sauqi muna asibiti ma batada lfy Lil Prince yana wahalar da ita" dariya yayi yace “aa Innata kawai dai na fadane ko Prince ko Princess duka Wanda Allah yabani Ina murna" sun jima suna waya tanayi masa fadan rage zafin zuciya me ciki batason yawan fada da fushi hakan yana dabi'antuwa ga yaron dake cikinta idan San samune ma zaifi su yawaita karatun qur'ani hakan zaiyi tasiri wajen halittar yaro zai dabi'antu da hakan sosai.
Godiya yayi Mata ya miqawa Rafi'ah wayar a kunyace suka gaisa tayi Mata fatan alkhairi suka aje wayar ya sake Kiran qaninsa Jamal ya fada masa amaryarsa tanada ciki steel ya sake Kiran Muhseen ya sanar dashi kafin dai wani lkc mgnr cikin ta cika wannan family Hajiya Fatsum itace qarshen Kira dake taji lbrn gurin Jamal saitaqi daga wayar sai text ya tura Mata tayi tsaki tace _“tsiyar zanwa fatan alkhairi?"_ tura Masa tayi ya duba sosai zuciyarsa na tafasa cije lips dinsa yayi yace “tsiya! tsiya!!" Numfashi ya sauke ya miqe ya fita bai jimaba ya dawo yana kallonta tayi qasa da kanta yayi ajiyar zuciya kallonta kawai yana kwashe masa damuwar da yake ciki zama yayi a gabanta yace “bansan me bebie na yakeso ba a fadamin na tafi ns Nemo" Lumshe idonta tayi tace “Abbansa yake feel....."
_More comments_
_More typing_
*_Ummuh Hairan_*
*_37-38_*
_____________________________
_____________________________
Abin ya bashi dariya sosai yayi abarsa ta zuba masa ido yayi qiba sosai ya qara haske abinka da farin mutum ta sauke ajiyar zuciya tanajin wani yanayi game dashi, batayi aune ba taji ya dagota cak ya dauketa kamar babie ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta ya sauke Mata kiss me zafi yaja numfashi yace “bansan me zanyi ki gane irin farin cikin da nake cikiba Rafi'ah inason babien nan na cikinki tabbas shine asalin raba gardama ga duk me hankali yasan cewa zafin rabo shine ya rinqa azalzalar zuciyata Saida na mallakeki sonki da sha'awar kasancewa dake suka hanani duba kowace irin alaqa tabbas inajin cewa da wani qaddara ta gifta dana kasa samunki da zanyi Miki fyade Kuma zaki samu ciki to sai Allah ya dubi kyawun niyyata ya qadarta zamowarki matata mace mafi daraja aguna"
Lumshe idonta tayi yayi murmushi tare da direta a gadon yace “inasonki Rafi'ah kema kinasona?" Rufe idonta tayi da hannunta tana dariya shima dariya yayi ya miqe yace “har yanzu nakasa samun wannan kalmar kina Sona ya gagareki furtawa ko?"
Ficewa yayi ta miqe ta shiga bathroom tayo alwala ta dawo tana duba alqibla ya shigo da kaya a Hannunsa ajewa yayi yana kallonta ta tayar da sallar bayan ta idar ya matsa gabanta ya fito da kayan daya shigo dasu tarkacen ciye ciyene ya rinqa bata wanda zata iyaci ta karba Wanda bazata iyaba ta kawar dakai da haka saida ta qoshi sannan ya qyaleta.
Likitan ya Kira yabasu sallama suka fito tana kwance a jikinsa suka shiga dakinsu suna shiga ta fada gado duk jikinta batajin qarfinsa shikuma ya fada wanka lkcn daya fito har tayi bacci ya dubi agogo 10:30pm ajiyar zuciya yayi ya haye gadon ya janyota jikinsa ya matseta yana shafa bayanta zuwa mazaunanta ta sauke ajiyar zuciya tare da bude idonta Dora bakinsa yayi saman idon nata yace.
“ke kikace babie na ni yake buqata" turo baki tayi tace “aa nifa wasa nakeyi maka banajin feel naka..." Rufe mata baki yayi yace “ni inaji" daga haka Bai qara bata damar mgn ba ya kashe musu fitila sosai ya sanyata nishadi salonsa yana tsaya Mata arai bata iya bijire Masa dadine me ratsa kwanya yake bata itama tana tayashi Saida suka samu nutsuwa sosai sannan sukayi wanka suka kwanta.
Wayarsa da tun farko fara harkokinsu take ruri ya dauka ganin number Ni'imah yasashi tsaki kawai ya sata a silent ya koma ya kwanta ya sake rungume matarsa wayarta ce itama ta fara ruri gashi ya hanata tashi bacci ne ya sakeyin dama dasu Basu suka tashiba sai asuba sukayi sallah suka sake kwanciya 11:00am suka tashi sukayi break ya fice ita Kuma ta danyi abinda zata iya ta sake kwanciya tare da janyo wayarta.
Missed calls tagani sunfi hamsin ta fara dubawa kusan duk na Ni'imah ne tayi murmushi tare da latsa layin Kira daya ta daga tace “sai yanzu kikaga damar daga wayar tawa?" Murmushi tayi tace “wlh kinsan dake ba zaman kaina nakeyi ba lkcn da kika Kira Ina tare da mijina shiyasa..." Wata dariya Ni'imah tayi tace “kaji fah masu miji mijine dake ko farka da akaga dama aka baki aronsa to bari kiji na fada Miki wani abu dole idan Mai fili yazo me trader ya dauke abarsa domin kuwa shi kansa yasan bazaiyi jayayya dame contenar ba to kamar hakane tsakanin ni dake nice me Ja'afar nice matarsa ta farko saboda haka shidin nawane ko kina da ja?"
Rafi'ah bataso kulata ba Amma idan ta barta haka tabbas zata siyawa kanta raini numfashi ta sauke tace “tabbas hakane kece matarsa ta farko bazaa taba canzawa tuwo suna ba saidai kinyi zuqu baki tsaya a iyakar matsayinki ba kinaso ki shiga nawa bawai Ina fada Miki bane dominsa aa Ina fada Miki ne domin ki kiyaye harshenki Ni'imah Ja'afar nawane zuciyarsa da ruhinsa dukka mallakinane domin ni aka haliccesa ki riqe wannan aranki akwai ranar da zaki maimaita dakank....."
Katseta tayi da cewa “hhhhh taqamarki waike kinyi ciki ko lallai yarinya to bari kiji wlh sai naso zaki haifesa banza sakarya yar fashin miji kawai"..... Qit ta kashe wayar murmushi kawai Rafi'ah tayi tace “shashasha kawai" Kiran Anti Raziqa tabi tana dagawa tace “uwar hudu tun jiya nake kiranki baki dagawa saraki ne ya hanaki ko?" Murmushi tayi tace “aa a silent na sata sai yau dana danji qwari naketa bin Kira kema ya fada Miki kenan"Sun jima suna waya sukayi sallama ta sake Kiran ta Ammi itama dai murnar samun cikin tayi Mata kunya kamar ta nutse Ja'afar bashida kunya duk ya gama bazata a duniya yanzu kowa yasan meye sukayi har suka samu cikin, sosai Ammi tayi Mata nasiha akan ta qara kwantar da hankalinta su zauna lafiya da mijinta da abokiyar zamantasannan tace abbanta yana gaisheta shima jiya bayan Ja'afar ya kirashi ya fada masa ya kirata Bai sameta ba, a kunyace suka gama wayar bata qara tsinkewa da lamarin Ja'afar ba Saida wata wayar ta shigo ta daga tare da sallama jin muryar babban mutum ya amsa yasata shan jinin jikinta,
Gaisheshi tayi ya amsa da muryar Isa ya jima sannan ya sake jan numfashi yace “Sannu Rafi'atuh dama haka Allah yake ikonsa Allah ya rabaku lfy yabaki lfyr shayarwa da tarbiyya Allah ya tsareku da tsarewarsa jiya magaji yake fadamin na kirashi ban sameshi ba idan yazo kice nace munason takwara idan namiji ne idan macece Kuma to munason princess dinmu ta zama tayi halin uwarsu Innah saboda haka munason asa Mata Nana Hafsatu" itadai a kunyace take amsawa sosai Mai martaba yayi musu addu'a sukayi sallama Saida ya aje wayar sannan ta kashe tata cike da mamaki Ja'afar yawucce tunaninta.
Nan ta yini zaune waya ta ko Ina yimata akeyi hatta Hajiya Kaltume Saida ta kirata tayi Mata fatan alkhairi kowa a gidan murna yakeyi zasu fara samun jikan da namiji Lil Prince zaizo qasan zuciyar Kaltume baqin cikine fal duk qudurinta ya rushe idan har ta kuskura tayi saken da Ja'afar ya fara haihuwa shikenan mulki zai koma gurin Zuri'ar Fatsum sukuma sun tashi a tutar babu kenan, tashi tayi tana kaiwa da komowa tabbas dole tayi wani Abu akan Wannan lamari dole zataja Rafi'ah a jikinta ta hakane zata samu cikar burinta Ja'afar ya jima yana bata barkono ya jima yana cizon zuciyarta idan tabarshi yashata bisillah ta cutu batada hanyar ramawa saita hanyar raba tsakaninsa da Rafi'ah domin ta fahimci duk duniya babu abinda yake qauna kamarta Rafi'ah itace jarrabarsa ita kadaice zaa taba duniyarsa ta girgiza.
Murmushi tayi tace “Kulsum matanadar makirci Ja'afar lkcn daukar fansa yayi tabbas zaka gane ka tabani" mayafinta ta dauka ta fita ta shiga bangaren bayi ta Kira jakadiya tayi Mata ihsani tace Mata lallai yau tanason ganin Mai martaba, dariya jakadiya tayi tace “ai kin biya uwar dakina jeki jirani yanzu zan dawo da sakamako" murmushi Hajiya Kaltume tayi ta koma ta zauna tana karkada qafa awa daya bata cika ba saiga Jakadiya Indo tana rawa tana juyi tace.
“Anyi nasara uwar dakina ki shirya kije kawai" tafawa sukayi tace “ki jirani gobe zamu tattauna dole wannan aikin sai kin shigo ciki so nake na tarwatsawa Magaji farin cikinsa gabadaya na hanashi samun nutsuwa a duniya kamar yanda ya hanani amaryarsa tanada ciki nasan kin samu lbr don jiya yini akayi ana celebrating a gdannan zanyi duk me yuwuwa na zuge Mai martaba yasashi dawo da ita amaryar gidannan ta hakane zan samu damar janta jikina so nake nayi amfani da ita wajen ganin bayan mijinta"
Jinjina Kai Jakadiya Indo tayi tace “zaki iya uwar dakina Amma fah ance yarinyar batada sabo naji suna fada"
Murmushi Hajiya Kaltume tayi tace “babu ruwanki da rashin sabonta ki bari na gama aikina sai na baki naki kedai kiyi qoqari kiga kina nadomin abinda waccan makirar take ciki idan nasan abinda suke shiryawa shine nima zanyi amfani da hakan nayi nawa cikin sirri" Jinjina Kai Jakadiya tayi sukayi sallama ta tafi.
Itakuma ta fara shirin tafiya gurin me Mai martabaBayan ta gama komai ta hada masa zobo me dadi da sanyi ta nufi turakarsa sai zuba qamshi takeyi ta qwanqwasa yayi Mata iso ta shiga yana zaune saman sallaya yana lazumi ta samu guri gefensa ta zauna ya dubeta ta sunkuyar dakai yayi murmushi ya ajiye carbin ya dubeta yace “Uwar gida saqonku ya ishemu dazu ta wajen su Jakadiya muna fatan dai lfy?"
Qasa tayi da kanta ta tsiyaya lemon a Kofi ta miqa Masa ya karba tayi farr da ido tace “lfy ranka ya dade kawai dai inason ganawa dakai ne saboda an kwana biyu baa zauna ba balle a shawarci juna" shanye zobon yayi yace “wannan gaskiya ne Kaltume to ai kudin ne kun fiye rigima shiyasa muka rabu daku" dariya tayi tace “to ranka ya dade ai baayi haka ba tunda Allah yabaku amanarmu ai sai kunyi hqr damu"
Murmushi yayi yace “hakane Allah ya qara Mana hqr" Hira sosai ta barke tsakaninsu inda cikin hirar ta lura duk Rabin maganarsa akan cikin da matar Magaji ta samu ne ba wani dadin hirar takeji ba Amma haka ta rinqa daurewa tana nuna masa dokinta akan cikin nandanan zuciyarsa tayi wasai saboda duk Wanda ya nuna yanason cikin jikin amaryar dannasa dadi yakeji, Nan ta samu dama tace “am dama Mai martaba nikam idan ka bani dama na kawo mana wata shawara Mana" dubanta yayi yace.
“To kaltume muna sauraronku" numfashi taja tace “duba da yanayin auren Yarannan Rafi'ah da Ja'afar da Kuma quruciya ni sai nake ganin tunda muna raye baikamata abarsu a gefe ita dashi suyi rainon cikin nan ba yakamata manya su shiga ciki domin zatafi samun kulawa ita da jikanmu dake cikinta" Jinjina Kai Mai martaba yayi yace “gaskiyane" sake qass tayi dakai tace “Me zai hana ya dawo da ita cikin gdannan idanma bazai bari taje wani bangaren cikin gidan ba tayi boffiɗonta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 19