Share this page
1 / 12
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels About the Author Hauwa Jibrin Sulaiman (Jiddatulkhayr Writes) is a Nigerian writer, poet, teacher, and author known for her inspiring stories and contributions to Hausa literature. Born and raised in Maiduguri, she studied Biochemistry at Bauchi State University and currently resides in Bauchi. Hauwa has a passion for encouraging young writers and uses her writing to explore novels, poetry, and nonfiction that resonate with readers. Connect with her on Instagram, Facebook, and TikTok: Jiddatul-khayr Writes. BEYOND THE VEIL Hauwa Jibrin Sulaiman Jiddatul-khayr writes Young talented writers association (YOTA) All praise is due to Almighty Allah who has granted me the strength, time, nd inspiration to write again. It's by His mercy that I return to u my beloved readers with another story frm the depths of my heart. To everyone who supported my previous works, thnkyou for walking this journey with me. Your love, your feedback, and your encouragement continue to fuel my passion. Now, I come back with something new a different style, a fresh voice, and a story I hope will touch your soul in ways words alone cannot explain. I pray you receive it with open hearts, just as you’ve welcomed me before. Before diving into the story, I want to express my deepest appreciation to *Na'ima Sulaiman Sarauta (Nimcyluv)*.  Her thoughtful suggestions and careful edits have greatly improved this work.  I am truly grateful for her time, encouragement, and belief in my vision.  Thank you Shugaba Nimcyluv, and I Love you so much. Wannan littafin kuɗi ne, 500 ne as ongoing book, idan ya kammalu kuma 1k ne document ɗin, thank you. Free page Episode 1: Unspoken possessiveness Tana dukunkune cikin duvet ɗin ta, saboda ruwan da akayi jiya da daddare wanda yasa garin ya ɗauki sanyi, buɗe idanun ta me cike da bacci tayi, ta ɗan yaye duvet ɗin da ya rufe mata har kan ta, agogon ɗakin ta kalla, da sauri ta miƙe zaune cikin muryan ta mai daɗi tace "SubhanAllah, it's already 6:30am? Oops.., I woke up late today" sai kuma ta fara karanta addu'an tashi daga bacci, sauke kafafun ta masu laushi da haske tayi ta saka Indoor slippers daga haka ta mike tsaye, ta yaye Night cap ɗin kanta saboda takurawa gashin ta da yayi tana yamutsa fuska, hakan ya ba ma gashin na ta damar sauka har gadon bayan ta, gƴara tsadaddan gadon ɗakin nata ta shiga yi, bata ɗau lokaci ba kuma ta gama, wardrobe ta wuce ta buɗe wani kimono ta ɗauka ta sa akan sleepwear ɗin jikin ta ta sauka kasa da sauri, kitchen ta shiga don haɗa breakfast, cikin sauri take haɗa Sandwich ɗin wanda bai ɗauke ta wasu lokuta ba ta gama, ta tafasa tea ta juye a tea flask, daga haka ta kai su kan dining, ta haura sama da sauri dan yin wanka. Bata tsaya shafa mai ba, kawai ta wuce ta ɗauki simple Abayan ta ta sanya, ta ɗauki Office bag ɗin ta ta rata ya, ta juya tana kallon fuskar ta a madubi, ganin pink lips ɗinta sun fara bushewa yasa ta shafa lips balm Cikin sauri yake shiri, mamakin kansa yake yi dan is hardly ya makkara, bayan ya fito parlorn yana gyaran neck tie ɗinsa daga haka ya wuce kitchen yana bin gurin da kallo ko zai samu abin sawa a cikin sa ganin kitchen ɗin alamar anyi girki yasa ya wuce dinning Luckily ya ga Sandwich dake cikin plate rufe da mesh food cover, ya ja ɗaya daga kujerun dining ɗin ya zauna ya yaye laidar ya taɓa flask jin akwai tea ya juye a cup sannan ya fara breakfast hankalin sa kwance yet in a hurry way, bayan ya gama ya koma parlorn dan haɗa kayan da zai tafi da shi office Tun daga sakkowan ta daga stairs take kallon sa sai kuma ta ɗauke kai, ya ɗan kalle ta shima sannan ya ɗauke kai, dinning ta wuce, da sauri ta kalle sa ganin ya gama breakfast da kayan da ta gama making ta sake kallon waste plate ɗin, ta ɗaga kai ta kalle sa sai kuma ta ce "Wait, is it the breakfast I just prepared that you ate?" Ba tare da ya Kalle ta ba ya ce "What are your eyes telling you? I ate it because I saw it was already prepared." Ɗan tsaki ta ja, saboda ran ta yayi mugun ɓaci ta ɗan saci kallon sa ganin zai fita ta ce "Amma ai wannan bai dace ba, dama kana cin abincin gidan ne ko kuma neman magana ne?" Ba tare da ya Kalle ta ba ya ce "This is my house, and I will do as I please, so stop asking me whether I ate or not, I will do whatever I see fit." Ta ɓata fuska tana kallon sa har ya fita sannan ta bi sa da harara, ta ɗauki Officebag dinta ta bi bayan sa ta samu already har ya shiga Mota itama wajan nata motar tayi kawai ta tsinci muryar sa "Kar ki kuskura ki fita da wannan kayan jikin naki, you're behaving like someone who isn't married." Ta ɓata fuska ta kalli agogon hannun ta, sai kuma ta Kalle sa taga mugun kallon da yake mata, kawai ta samu kanta da juyawa ta wuce cikin gidan, ba'a ɗau lokaci ba sai gata ta sake fitowa da Hijab a jikin ta, ganin shigar ta yasa ya fara tada motar sa, ita kuma ta wuce wajan motar ta, ganin tayan a sace yasa tayi wajan sa da sauri dan har ya fara reverse Ta ce "Wait.. mota na da matsala barin bika kawai" Wani kallo ya mata sannan ya wuce ta ya fita, ta tsaya baki a bude, kawai tayi ordern bold Tana zaune a office ɗinta tana aiki a system ɗin gaban ta wani ogan ta ne ya shigo da sallama a bakin sa, ta ɗaga kai tana kallon sa sai kuma tayi murmushi ta ce "Good morning, sir." ya ce "Morning, hope kin gama da aikin jiya?." Ta ɗan buɗe baki tana kallon sa sai kuma ta miƙe ta ce "I'm so sorry, wallahi Jiya saboda hadari na manta but I’m going to do the work now." Ya juya ba tare da ya ce mata komai ba ya fita daga office ɗin nata, ta bisa da kallo sai kuma ta miƙe ta buɗe wani File cabinet  ta Ciro wani paper tana duba wa sannan ta ɗauki wayanta ta shiga e-mail tana kallon ko yayi daidai daga haka ta miƙe zuwa wani Office ɗin. Ba tare da tayi knocking ba ta buɗe kanta tsaye ta shiga, Ajiye cup ɗin hannun sa da yake sipping yayi yana kallon ta da mugun mamaki, ta taɓe baki kamar ba shine ya gama cinye mata breakfast a gida ba amma gashi yana sake wani breakfast ɗin a Office Ya ce "Don't you know how to knock or say hello before coming in?" Dama da haushin yaki mata left take, ta Kalle sa kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta ce "Aikin da Jiya kaki ka min ne yanzu Oga Mahmud yace nayi na kai masa" Wani kallo ya mata sai kuma ya cigaba da aikin gabansa ba tare da ya sake bin ta kan ta ba Ta tsaya for almost 5 min ba tare da ya sake ko kallon ta ba hakan yasa ta jawo system ɗin gaban sa ta gyara zamar ta ta soma aikin operating system ɗin nasa With lots of shock yake kallonta ta ya buɗe baki zai yi magana a fusace aka buɗe kofar office ɗin, duk suka juya lokaci guda ta miƙe tana washe baki ta ce "Baba!, Welcome" Ta kasan ido ya Kalle ta sai kuma ya maida kansa kan mutumin da ya shigo ya ce "Good morning, sir." Mutumin ya karasa har cikin office ɗin ya zauna har sannan da murmushi shinfiɗe a fuskar sa cike da dattako ya ce "Daughter, I hope you’re doing well" Ta ce "Alhamdulillah Baba" kallo ɗaya ya masa ya ce "Baka ga message ɗina bane? Ko kuma kiran nawa ne zaka ce baka gani ba?" Ɗan sotsa kansa yayi ya saci kallon inda take sai kuma ya maida kallon sa ga dattijon ya ce "I'm very sorry, Sir. Actually, I had some work I needed to finish first, then I planned to come over har gida na same ka, shiyasa sir" Ya miƙe ba tare da ya ce masa komai ba yana kallon ta ya ce "Daughter idan aiki ba zai miki yawa ba akwai special assignment da zan baki tunda mijin naki baya maida hankali ga aikin sa" Da murmushi a fuskarta ta ce "Alright Baba, nayi alkawarin maida hankalina na gama cikin kankanin lokaci" Murmushi ya mata daga haka ya fita, dama supervising company ya zo yi, duk inda ya shiga gaishe sa ake cike da girmamawa Sauke ajiyan zuciya yayi ba tare da ya ce komai ba, idon sa na kanta har ta kammala aikin da zata yi ta miƙe Ya ce "Bana bukatar sake ganin ki anan please" Ta juya tana masa wani kallo ta ce  "Haba? Toh ka rantse naji?" Wani kallo ya mata, ta taɓe baki ba tare da ta sake kula sa ba ta fita, first floor ta wuce rike da papern da ta gama printing ɗin su out, a bakin Office ɗin Oga Mahmud ta danna door bell, bayan an bata izini yasa ta shiga ta same sa ga kuma Baba dake gefen sa yana duba wani files ta ce "Here's it sir, Na gama" Karɓa yayi yana dubawa ya ce "Well, thank you" Daga haka ta fita daga office ɗin zuwa nata office ɗin. Da Yamma bayan karfe 4pm duk yawanci ma'aikatan duk sun fito da niyyar tafiya gida Hango sa da tayi yasa ta fara tafiya da sauri dan ta rantse a motar sa zata koma gida Ta tsaya tana magana da wata ma'aikaciya ganin ya nufa motar sa yasa tayi wani murmushi dan ta kasan ido take kallon sa ganin ya shiga yasa tayi wajan da sauri ta buɗe kofar gaban motar Shi da yake shirin tada motar ya ɗaga kai yana kallon ta da mamaki ya ce "Are you out of your mind opening my car without permission?" Ta ce "Why would I need permission when it’s my husband’s car?" He gave her a sharp look ya ce "Alright then, get in let's see." Ta ce "Yanzu ma kuwa" ta zauna har da gyara zamanta ta saci kallon sa taga wani irin kallon da yake mata ta ɗaga kafaɗa ta ce "Baba ne ya ce kar na hau bold tunda ga ka, siyasa ban masa kardama ba, amma ka ce na sauka wallahi sai na je na faɗa masa" Hango Baba da yake saukowa tare da guards ɗin sa hakan yasa ya tada motar ba tare da ya sake kallon ta ba, ta taɓe baki ta toshe kunne ta da Bluetooth dan bata bukatar jarabar sa A hanya taga ya parka dai dai wani babban eatry ya sauka ya shiga ciki, bai wani dade sosai ba sai gashi ya fito rike da laidar takeaway ta dinga kallon sa har ya karaso motar tana mamakin takeaway ɗaya da ta gani, tayi kwafa har sai daya ɗan Kalle ta. Bayan sun shiga cikin parlorn na su, yana gaba tana baya, ya wuce dining ita kuma ta wuce sama, yana ajiye takeaway ya wuce dakin sa dan canza kaya, tana laɓe a stair wall ganin har ya rufe dakinsa ta fito da sauri tayi dining ta ɗauke takeaway ta haura sama da gudu tana dariya, tana shiga dakin ta ta danna masa key, kan tsadaddan bedside dinta ta ajiye sannan ta cire kayan ta ta wuce toilet dan yin wanka. Bayan ya sanya jallabiyar sa ya fito, bai lura da babu komai a dining ba sai daya karasa, sake baki yayi yana kallon kan table din sai kuma ya shafa kansa bai san sanda murmushi yayi escape a fuskar sa ba ya shafa fuskarsa ya wuce kitchen dan duba wani Alternative ɗin. Yau tun da ta tashi haka kawai take jin bata son wannan family meeting ɗin nasu, haka kawai take jin fargaban haɗuwa da sauran family member ɗin sa. Kamar kullum ta ɗaura 'yar karamar kimono akan sleepwear ɗin jikinta ta sauka ta girka breakfast har da shi bayan ta gama ta jera su a dining sannan ta wuce sama dan wanka. Bayan ta fito a wanka ta shafa tsadaddun lotion ta feshe jikin ta da expensive Perfumes sannan ta saka tsaddadan lace tayi daurin daya amshe ta ta daura laffaya ta dauki flat shoe da wani dan karamin hand bag, ta saka Black space sannan ta sauka. Tun daga stairs yake kallon ta, He couldn't take his eyes off her har ta karasa dining ɗin, sannan ya sauke ajiyar zuciya Ba tare da ta Kalle sa ba ta jawo flask din tea ta zuba, ɗan daga idon ta tayi suka haɗa ido yayi gyaran murya ya ce "Baki iya gaisuwa ba ne?" Ta Kalle sa ta ce "Idan na gaishe ka ɗin amsa wa zaka yi?" Yayi kasa da murya yace "Don't please" ta Kalle sa sai kuma taji ba daɗi Har suka gama breakfast ba wanda ya ce da ɗan-uwansa kala, bayan sun fita ta ɗauka a motar sa zata bi sa, sai kuma taga ya nuna mata nata motar, ta ɗan kalli wajan sai kuma taga har an gyara mata hakan yasa ta koma cikin gidan dan dauko nata keyn. A Babban compound ɗin da ya gaji da kyau aka yi decorating, a tsare wajan zaman suke, ga su VIP chairs ga kuma reserved seats, wanda wannan taron once in a while ake yin shi sbd Extended family gare su, wanda already mutane sun fara taruwa kowa yana zama a spot din sa Amira ta kalli Zainab ta ce "Kin san wa nake son kallo?" Zainab ta ce "Nope, sai kin faɗa" Amira ta ce "Matar Crush ɗina mana, ina so naga da me ta fini, naji ance ƴar ghetto area ce kuma She came from a poor background" Zainab ta yamutsa fuska ta ce "ƙaryan tsiya anan ya kare ai, I doubt she can speaks or understanding English, yanzu idan ya tashi tafiya business trip ɗin sa sai muga yadda zai yi da mata 'yar ghetto" Duk kwashewa suka yi da dariya Wata cousin ɗin su ce tazo wucewa tana cewa "Yanzu Yaya zai shigo da matar sa" Juyawa suka yi suka Kalle ta, Amira tayi saurin cewa "Hajara wait.. wai Yaya ne zai shigo yanzu?" Kai ta gyaɗa mata ta ce "Sure! Harda Matar sa, kinsan ba'a san ta ba" Tana kai wa nan tayi gaba ta bar su, Amira ta miƙe ta ce "Zee, ta shi mu je can gate na ganta da kyau kar sai ta zo nan mutane su hanani kare mata kallo" Zainab ta miƙe tana cewa "haka ne fah" Hajara dake waya da Yayan ta ta ce "Okay Yaya, yanzu haka ina car park Ina jiran shigowar ku" Bayan sun isa can farkon compound ɗin suka tsaya, basu wani daɗe ba sai ga motar sa ya kuso kai Zainab ta kalli Amira ta ce "Wallahi dama a cikin mu ya ɗauka, gamu duk final year student a uni, bari dai yau mu kare ma matar nasa kallo tass" Amira ta mata wani kallo ta ce "Dama Ni ya ɗauka ko mu?" Ta karasa maganar da harara Yana gama parking Hajara ta karasa tana masa Sannu da zuwa, hakan yasa su Zainab karasa wajan suma Amira ta kashe murya ta fara magana cike da shagwaɓa, Hajara ta ce "Yaya Anty Azrah fah?" Bata kai ga rufe baki ba sai ka motar ta ta shigo compound ɗin, Amira duk suka mayar da hankali su kanta dan ganin ta wato har mota ta iya yanzu Bayan tayi parking ta buɗe motar wanda tuni Hajara ta karasa wajan dama kiran da ya mata kenan akan ta shiga da ita saboda rashin sanin ta da aka yi, sauke kafafun ta tayi kasa wanda take sanye da flat shoe red henna kafarta ya karama kafar nata kyau da haske, Amira suka kalli juna da Zainab Ta karasa fita a motar wanda fuskar ta yana ɗauke da murmushi ganin Hajara, sai da numfashin Amira ya kusa ɗauke wa sanda idon ta ya faɗa kanta, Zainab kam tuni ta manta wani class ta sake baki tana kallon ta Zainab ta juya tana kallon Yayan su da ya fara gaba ta ce "Yaya ina Matar ka? Ko ba zata zo bane"?" Pointing mata inda Hajara ke rufe mata motar yayi, da sauri ta juya tana kallon Amira data gama mutuwar tsaye Hajara na rike da ita suka karasa har in da suke ta ce "Hey Cousins, ga Matar Yaya" Duk sun kasa cewa komai hakan yasa Hajara taji wani iri daga haka suka wuce wajan taron Amira ta kalli Zainab wanda har sannan idon ta ya gama cika da hawaye ta ce "I doubt ba ita bace" Zainab tayi dariya dan ta fahimci kishi ne ta ce "Sai kuma ya manta matar ta sa? Ita ɗin ce sai dai ba yadda muke expecting bane kila karya Anty ta mana" Amira ta bar wajan dan bata jin zata iya sake tsayuwa a gidan nan. #Jiddatulkhayr 08110615256 *BEYOND THE VEIL Hauwa Jibrin Sulaiman (Jiddatulkhayr) Young talented writers association (YOTA) Free page Episode 2: A Glimpse into Azrah's Life Tsane ruwan dake zuba daga kanta tayi, ta ɗaura ɗan karamin towel ɗinta sannan ta sanya hijab a jikinta, ta dauki shower gel ɗinta da shampoo dake kan tagar ban-ɗakin wanda ko plasta babu balle window, tura kofar ban-ɗakin tayi ta fito cikin ɗan matsakaicin compound ɗin nasu, Mama dake kwashe abincin talla tana zuba wa a cikin robar tallan ta ɗaga kai tana mata wani banzan kallo ta ce "Ace yarinya ƴar gidan talakawa amma ki dage ke lallai sai da wannan sabulun turawan zakiyi wanka ke ga ƴar gold ko? Mu da muke wanka da Omo ai mutuwa muka yi" A hankali ta buɗe baki ta ce "Mama bani fah aka yi, bawai nace nafi karfin wanka da Omo bane" Mama ta bita da wani kallo ta ce "Ai karya zan miki, ba abinda kika iya banda yawon iskanci, yo yawan iskanci mana wai ke gaki ƴar boko ko?" Azrah ba tare da ta sake kallon direction ɗin Mama ba ta wuce zuwa ɗakin dake kusa dana Mama ta shige ciki Umma ta ɗaga kai tana kallonta ta ce "Sai dana ce miki ki daina fita da wannan sabulun ruwan amma baki ji" kallon Umma tayi cike da mamaki sai dai bata ce komai ba ta wuce daki direct dan sanya kaya Bayan ta gama shafa lotion dinta ta dauki well ironed uniform dinta wanda daga gani kasan ya gama koɗewa ta sanya sannan ta fito rike da jakka a hannun ta, tana kallon Umma ta ce "Ina Zahra Umma?" "Na aike ta ta tsiyo sigari" Umma ta mayar mata da amsa Ta ce "Toh Ni zan wuce makarantar kar na makkara" Umma ta ce "Toh Allah ya bada sa'a Azrah, ki kula da kanki" ta gyaɗa mata kai daga haka ta nufi compound ta samu Mama da wata makwabciyar su da alama magana suke yi Mama tayi wani murmushin takaici ta ce "Wato ke Azrah baki da aiki sai zuwa makaranta saboda baki son aikin gida ko?" Makwabciyar ta su wanda ake kira da Maman asabe ta ce "Toh ai sai ku hana ta ai tunda bata isa ce muku A'a ba, dan Ni banga amfanin wani makarantar boko ba" Mama ta ce "Yo dama me suke koya a makarantar idan banda iskanci? Nawa zaki ga yarinya wai ita boko daga karshe shikenan ta koma karuwar gari" Tuni Azrah ta fita ba tare da ta sake waiwayosu ba ko tanka musu Gidan su kawarta Fatima ta tsaya, tana sallama sai gata ta fito itama cikin shirin makaranta daga haka suka wuce zuwa makaranta Bayan ta dawo daga School babu kowa compound ɗin su ta wuce dakin Ummanta ta shiga da sallama, Zahra dake jikin Umma tana cin abincin ta ɗaga kai tana kallon Azrah ta ce "Sannu da zuwa Anty Azrah" Azrah ta gyaɗa mata kai tana kallon Umma ta ce "Barka da rana Umma"  Umma ta ce "Yauwa Azrah, ya karatun?" Ta ce "Alhamdulillah Umma" daga haka ta miƙe ta wuce ta shige dakin da yake nasu bata daɗe ba sai gata ta fito tana sanye da doguwar riga da hijabi Umma na kallon ta ta ce "Ba zaki ci abinci bane zaki tafi?" Azrah na Murmushi ta ce "A'a Umma nasan abincin ba yawa idan naje gidan Mummy ba zan rasa abin da zan ci ba, amma wannan na bar muku ke da Zahra" Umma tayi shiru tana kallon 'yar nata cike da tausayi Azrah ta yanke mata tunaninta ta ce "Toh Umma na tafi" Umma ta gyaɗa mata kai ta ce "Allah ya tsare" Zahra ta miƙe ta raka ta har bakin kofa sannan ta koma Wani babban gidane wanda ya gaji da kyau a Barhim estate, dake jihar Katsina, a bakin gate ɗin tayi knocking mai gadi ya leƙo ganin ta ya wangale mata gate ɗin ta shiga tana mai gaishe sa ya amsa mata, daga haka ta nufi cikin entrance ɗin gidan, a balcony taga Ya saif na zaune Ta ce "Ina wuni Ya saif" Ko kallon ta bai yi ba balle tasa ran zai amsa mata kuma bata yi mamaki ba dan idan da sabo ta saba dama ba gaisuwar ta yake amsawa ba, tana shiga parlorn taga Mummy na zaune ga kuma Suhaila a gefen ta tana shan fruits, duk ɗaga kai suka yi suna kallon ta har ta karasa cikin parlorn ta duka jikin wani kujera ta ce "Ina wuni Mummy" Mummy da murmushi shinfiɗe a fuskar ta tace "Lafiya kalau Azrah, ya su Umman ki?" Ta ce "Alhamdulillah" ta maida kallon ta ga Suhaila ta ce "Ina wuni Anty Suhaila" itama da murmushi shinfiɗe a fuskarta ta ce "Lafiya Azrah, kar

Chapter 1 of 12