Share this page
2 / 12
dai yauma takowa kika yi da ƙafa?" Azrah murmushi kawai tayi, Suhail ta ce "Ke baki ganin nisan unguwar taku ne? Ace tun daga Kofar Marusa har nan Barhim estate ki tako a ƙafa?" Azrah murmushi kawai tayi dan yanzu har ta daina ganin nisan Mummy ta ce "Ai yabi jikinta ba zata iya dai nawa ba" Azrah ta miƙe ta fara tattara parlorn da ba wani datti sosai yayi ba tana gamawa ta wuce kitchen Nan ma ta fara gyara kitchen ɗin bata dau lokaci ba ta gama sannan ta tara kayan wanke wanken a sink ta fara yi cikin kankanin lokaci ta gama ta daura abinci, Mummy ta shigo kitchen ɗin tana bi da kallon, ɗaya daga cikin abin da take son aikin Azrah kenan tana da tsafta yarinyar sannan bata da gandan aiki shiyasa kawai take managing duk da Azrah idan ana School ba da safe take zuwa ba, ta juyo tana kallon Mummy ta ce "Mummy kina bukatar wani abun ne na kawo miki?" Mummy ta ce "A'a yi aikin ki kawai, zan dauki abu ne" Azrah ta gyaɗa mata kai kawai ta cigaba da aikin gaban ta Sai karfe biyar ta gama aikin gidan tass da abincin, ta duka a parlorn tana kallon Mummy ta ce "Mummy zan tafi gida" Mummy ta ce "Toh shikenan Azrah, sai gobe ko?" Ta gyaɗa mata kai, Suhaila ta ce "Gashi nan dubu uku ne, kiyi using ma week din nan kina hawa keke ki daina wannan takowan da ƙafa dan Allah", Azrah ta sa hannu ta karɓa ta ce "Nagode sosai Anty Suhaila, Allah ya biya ki da Aljanna" ta ce "Is Okay Azrah, Amin thank you" daga haka Azrah ta bar parlorn Suhaila ta kalli Mummy ta ce "Wallahi Mummy ina son ganin rayuwar yarinyar nan yayi kyau, Allah bata miji mai kuɗi da zai iya riƙe ta sakani da Allah" Mummy ta ce "Wallahi Nima ina mata sha'awar gidan Hutu, gata da hankali ga kuma ilimi kamar wacca ba makarantar gomnati take ba" Suhaila ta ce "Wallahi Nima ilimin ta dai mamaki yake bani, ga kyau kamar wacca ita tayi kanta, kwatakwata bata yi kama da 'yar gidan talakawa ba" Mummy ta ce "Dan kawai naga Yayanki basu shiri ne amma da wallahi na masa maganar ya aure ta dan banga wani abu na qualities ɗin mace ace bata da shi ba" Suhaila ta ɗan yi frowning face ɗinta ta ce "Shi ya sani, ai na taɓa masa maganar kamar wadda na kara masa tsanarta a zuciyar sa, wallahi duk macen da zai kawo dakyar ta wuce Azrah da wani quality ɗin wallahi" Mummy ta miƙe tana hanyar bedroom ɗinta ta ce "Zan gwada masa magana gaskiya idan har zai yarda" Suhaila ta ce "Hmm" ta cigaba da danna wayan ta. A gajiye Azrah ta isa gida, ta shiga dakin Umman su da sallama a bakin ta, Umma dake koyawa Zahra Tauhidi ta ɗaga kai tana kallon ta harta karasa cikin ta zauna tana sauke ajiyar zuciya dan ba karamin gajiya tayi ba, Zahra ta miƙe ta fita daga ɗakin, Azrah ta ce "Barka da yamma Umma" Umma na kallon ƴar nata cike da tausayin wahalar da take sha ta ce "Sannu Azrah, Allah miki Albarka ya baki future mai kyau wanda ba zaki sha wahala ba" Azrah ta ce "Amin Umma"  Zahra ta shigo da ruwa a hannunta ta karasa inda Azrah ke zaune ta miƙa mata ta ce "Gashi Anty Azrah" karɓa tayi tana faɗin "Nagode Zahra" Kafa kofin ruwan tayi a baki bayan ta sha ta sauke tana kallon Umman nasu ta miƙa mata kuɗin da Anty Suhaila ta bata Umma ta ce "Kuɗin me kuma Azrah?" Azrah ta ce "Anty Suhaila ce ta bani wai na daina tafiya da ƙafa shine da zan dawo naki hawan a daidaita nace sai a biya ma Zahra kudin Islamiyyanta sai ta koma ko?" Umma na kallon ta hawaye yana cikowa daga idon ta dakyar ta maida sa dan bata son yaran nata su fahimci haka amma zuciyar ta cike take da tausayin irin wahalar da Azrah zake ciki ta ce "A'a Azrah, gaskiya ne ki daina wannan takun kinga wajan da nisa sosai kawai ki ajiye tare da ke sai kina amfani da shi wajan tafiya ko?" Azrah ta girgiza mata kai ta ce "A'a Umma, har dubu uku ne fah" ta zare dubu ɗaya ta miƙa ma Zahra ta ce "Gashi gobe ki kai kudin makarantar ki saiki fara zuwa ko?" Zahra ta karɓa ta ce "Nagode Anty Azrah, Allah ya mayar miki" Azrah ta harareta sai kuma ta mayar da kallon ta ga Umma ta ce "Ina ga ba zan saka a asusu ba kawai zan nema abin da zan kara na sana'a ko Umma, sai wannan ya zama kamar naki ne" Umma tayi shiru tana kallon ta Azrah ta mata murmushi ta kalli agogo ganin Magrib ya kusa yasa ta miƙe ta ce "Bari nayi shara sai na ɗaura abincin dare" daga haka ta wuce cikin compound ɗin na su. Da daddare bayan sallahn Isha'i sai ga Bappah ya shigo gidan Mama na zaune a tabarma tana lissafin Kuɗi, ga kuma Habiba da bata daɗe da dawowa daga talla ba, ganin Bappah yasa ta tura kuɗin kasanta tana "Sannu da zuwa Malam" Habiba ta ce "Ina wuni Bappah" Bappah ya karasa ya zauna yana faɗin "Fatsuma ba zaki daina tura yaran nan talla ba ne?" Tayi kicin kicin da Idanu ta ce "Haba Malam, ina yanzu tallan ne ke rufa mana asiri, ina daga kai har matar ka duk da shi kuka dogara amma sai kana wani maganar kuma" wani kallo yake mata sai aka doka sallama daga bakin kofar, ya miƙe yana amsawa daga wajen mutumin ya ce "An kawo gawayi ne, muna sauri zamu yi gaba" Bappah ya kalli Mama data taɓe fuska, sai ga Azrah ta fito Zahra na biye da ita a baya suka yi gate ɗin da sauri tana faɗin "Ku shigo min da shi, gani zuwa" Bayan ta karasa fita ta samu suna kokarin shiga da shi, matsa musu tayi har suka shigo mata da shi cikin compound ɗin ta irga kuɗin su ta miƙa masa, karɓa yayi ya irga ganin ya cika ya juya ya ce "Toh sai da safe" sai sannan ta lura da Bappah dake tsakar gidan da murmushi a fuskarta ta ce "Sannu da zuwa Bappah" Zahra ma ta juya tana gaishe sa. Juye gawayin dukka tayi akan wani buhu ta shiga aikin kullawa a laida ita da Zahra, can Mama ta gagara hakuri ta fara masifa "Gaskiya za'a daina kulla mana gawayi a gida, dubi yadda ake ɓata mana gida da gawayi" Daga Azrah har Zahra ba wanda ya tanka ta Suna aikin su cike da nishaɗi, can sai ga Siyama ta shigo tana waka da kayan tallah a hannunta, kamar wata ƴar tasha ta zuɓe akan tabarman tana faɗin "Gaskiya yau nagaji Mama, dole gobe da safe ki barni nayi bacci gaskiya" Mama ta ce "Dan uwarki tallan ma kice ba zaki ba daya fi miki" taɓe baki tayi tana kallon Habiba ta ce "Ke tashi kije ki sako min abinci mana" Habiba ta ce "Toh shine zaki wani cemin ke sai kace baki san sunana ba" ta karasa maganar cike ta tsiwa, Siyama ta sake baki tana kallon ta zata kai mata duka sai ga Bappah ya fito daga ban ɗakin hakan yasa ta miƙe zuwa ɗebowa da kanta tana faɗi "Zan kama ki kuwa dan Uwarki" Azrah har suka gama kulla gawayinsu ba tare da sun kalli direction dinsu ko kulasu ba Tana shiga ta same Umma na zaune tana jan carɓi har sannan, Umma ta ɗaga kai tana kallon su ta ce "Sannu da kokari, kuyi hakuri da rayuwar da kuke ciki yanzu, wata rana sai labari In Shaa Allah" Azrah taji hawaye na taruwa mata girgiza mata kai tayi ta ce "Ki daina cewa haka dan Allah Umma, Ni buri na kawai ki samu lafiya ne" miƙewa tayi tana kallon Zarah ta ce "Muje mu kwanta ko?" Zahra ta miƙe tana bin bayan ta suka wuce ɗakin su. Kamar kullum Azrah ta gama duk wani aiki da tasan tana yi, ta kawo duk wani abu da Umma zata bukata ciki, kallon Zahra tayi wanda itama ta fito cikin shirin makaranta ta ce "Dan Allah Zahra kuna tashi ki dawo gida kar ki tsaya a hanya saboda Umma ko?" Zahra ta gƴaɗa mata kai ta ce "Toh Anty Azrah, ba zan tsaya ba" Ta na kallon Umma ta ce "Umma Ni zan tafi, idan ana bukatar gawayi yana waje" Umma ta ce "Toh Allah bada sa'a, Allah yayi muku Albarka" duk suka amsa da Amin sannan suka fita Mama dake zaune tana abincin tallan ta ce "Wallahi yau bari Bappahn naku ya dawo anjima, gaskiya ba waccan zata sake fita a gidan nan da sunan wai zata makaranta, dan Banga dalili ba ace sai nine zanna ciyar da ku" Gaishe ta suka yi, ta bi su da harara basu kuma bi ta kanta ba suka fita, Azrah ta kama hanyar makarantar su haka ma Zahra. Mummy na kallon sa ta ce "Magana fah nake maka Saif" Saif ya tamke fuskarsa jin maganar da Mummy ta gama dan ko kaɗan be kawo abinda zata ce masa ba, Suhaila dake danna wayanta ta ɗan saci kallon sa sai data kusan dariya dan ganin reaction ɗinsa, saidai ta ɗauke kanta ta cigaba da danna wayanta, Mummy ta ce "It's Okay tunda ba zaka iya bani amsa ba, ka mayar dani banza ai" ya tsosa kansa ya ce "Haba Mummy, how on earth zaki haɗani da wannan low class din, for that matter ma wannan teen ɗin" Sahulai bata san sanda ta fara dariya ba wani kallo ya wurga mata Mummy ta ce "Ka dai bi duniya a sannu da hankali, dan naga kamar ka ɗauke ta da zafi nikuma dama shawara na kawo maka ganin yarinyar tana da hankali ga tsafta kuma kyakkyawa ce" taɓe bakin sa yayi ya miƙe ya bar parlorn, Suhaila ta ce "Dan Allah Mummy karki sake ce masa komai, zamu ga kashen classic babe ɗin nasa ai" "Hmmm" kawai Mummy ta iya cewa. Yau ma kamar kullum, bayan ta dawo a makaranta ta gama shirin tafiya gidan Mummy ta fito tana sanye da Hijab ɗin ta, Zahra ta ce "Anty yaushe zaki sake illoka? Kinga yadda ake tambaya a ajin mu kuwa?" Murmushi tayi ta ce "Maybe idan na dawo yau, dan bana son kashe kuɗin" gƴaɗa mata kai tayi, mayar da kallonta ga Umma tayi ta ce "Umma bari na tafi ko?" Ta ce "Sai kin dawo, ki kula da hanya sannan ki kula da kanki dan Allah" kai ta gƴaɗa mata ta ce "In Shaa Allah Umma" Umma tana miƙa mata ɗari biyu ta ce "Gashi wannan ki hau abin hawa tunda Kinga jiya sunyi magana" Jim kaɗan tayi tana kallon Umma sai kuma ta miƙe tana faɗin "A'a rike kuɗin ki Umma, akwai ɗari biyu a waje na" daga haka ta musu sallama ta fito ɗan karamar tsakar gidan na su, sai da gabanta ya faɗi kallon step bro ɗinta Abdul dake tsaye a kofar Mama yana binta da wani mayen kallo, tunda ta Kalle sa sau ɗaya ta ɗauke kai dan bata kuma bukatar ta sake haɗa ido da shi, sai data zo fita ba tare da ta Kalle direction ɗinsa ba ta ce "Ina wuni" bata jira amsar sa ba tayi fice warta, wani a daidaita data gani yazo zai wuce tayi saurin taran sa da faɗa masa inda zai kaita dan ta gama tsorata da Abdul dukda bata yi niyyar tafiya da keke ba #Jiddatulkhayr 08110615256 BEYOND THE VEIL Hauwa Jibrin Sulaiman (Jiddatulkhayr) Young talented writers association (YOTA) Free page Episode 3: Ghetto, But not broken Knocking babban gate ɗin tayi, gatekeeper ya leƙo ganin ta yasa ya buɗe mata, ta shiga tana "Ina wuni Baba" ya ce "Lafiya lau Azrah" daga haka ta shige A daidai kofar shiga parlorn taci karo da Saif da shima yake ƙoƙarin fita daga parlorn littattafan hannunsa yayi watsi a ƙasa, da sauri taja baya tana zara ido dan bata san yana fitowa ba, ganin papers ɗinsa a kasa yasa da sauri ta duka ƙasa tana faɗi "Dan girman Allah kayi hakuri Ya saif, wallahi ban sani bane" Shi kam Saif with shock har sannan yake kallonta har ta gama tattara masa sannan ta miƙe cike da ladabi ta miƙa masa ganin bai karɓa ba yasa ta ɗaga kanta for the first time bayan incident ɗinsu ta Kalle sa, ganin wani irin kallo da yake mata yasa ta sake furta "Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan kana fitowa bane" cike da izza sannan da tsansan kyama ya ce "Are you doing this just to seek attention? So, ki cire ranki idan har wannan ne ke knocking a kwakwalwar ki, saboda ba zan taɓa cewa ina sonki ba, Stupid" ya ciro Handkerchief a aljihun sa sannan yayi wrapping hannunsa kafin ya karɓi papers da take miƙa masa ya bar wajan Azrah tafi minti 2 kamar tana processing maganar sa, sai kuma ta juya ta bi inda ya bi da kallo sannan ta harare wajan sai yanzu maganarsa yake jiƙa mata dan ita ko kaɗan yadda ya nuna kyamarsa gareta bata damu ba ɗan karamin tsaki ta'ja sannan ta karasa cikin parlorn da sallama Suhaila ta gani zaune tana danna system ɗinta da murmushi a fuskarta ta karasa ciki ta duka ta ce "Barka da warhaka Anty" sai sannan Suhaila ta ɗaga kanta tana kallon ta amma har sannan wannan murmushin beyi fading daga fuskarta ba ta ce "Sannu Azrah, ya hanya da su Umma kuma?" A hankali ta ce "Lafiya klau, duk Alhamdu Lillah" Suhaila ta ce "Ma Shaa Allah" Azrah zata miƙe Suhaila tayi saurin cewa "Wait.. ke da waye ne? naji kina bada hakuri?" Azrah ta Kalle ta sai kuma ta ce "Ya Saif ne, ban sani bane na buge sa" Suhaila ta jinjina kai daga haka Azrah ta wuce kitchen dan ganin aikin da zata fara Suhaila ta bita da kallo tana cigaba da murmushi dan tasan dole Saif zai ɗauka da wata manufa tunda ɗazu Mummy ta gama masa maganar Azrahn. Har Azrah ta gama aikinta tana jinta moody kuma tasan definitely abinda ya faru tsakanin ta da Ya Saifuddeen ne ya canza mata yanayi haka ta karasa aikinta sannan ba tare da walwala ba, bayan ta fito daga kitchen yayi daidai da shigowar Mummy, Azrah ta karasa tana karɓan kayan hannun Mummy meanwhile tana gaishe ta, Mummy ta amsa da fara'arta tana tambayar ta ya aiki. Bayan ta gama ajesu a position ɗinsu ta koma parlorn tana kallon Mummy ta ce "Mummy zan wuce gida" Mummy ta ce "Miƙomin wayata akan Centre table na kira Suhaila ta kaiki naga garin da hadari sosai ne" Azrah ta wuce inda wayar Mummy yake ta ɗauka ta kai mata, Mummy na karɓa tayi dialing numbern Suhaila tana ɗauka ta faɗa mata tana neman ta a parlorn, ba'a ɗau lokaci ba sai ga Suhaila ta fito daga ɗakinta tana kallon Mummy ta ce "Gani Mummy" Mummy ta ce "Dama wai ko zaki kai Azrah gida ne naga garin da hadari" Suhaila tayi shiru ta ce "Why not Yaya Deen Mummy? Kar na fita kuma ruwa ya sauko kuma Kinsan jikina baya son sanyi" Mummy ta ce "Eh kuma fah haka ne" tun kafin ta karasa rufe baki Azrah ta katse ta da "Mummy ina fita zan samu abin hawa Karki damu" Mummy ta ce "Toh shikenan, Allah ya tsare" da Amin ta amsa sannan ta musu sallama ta fita. Kura ake yi ga garin ya fara duhu sakamakon hadarin, a haka ta dinga tafiya tsoron kar ayi ruwa yasa kawai ta tsare keke ta shiga, tana isa unguwarsu ta samu already su har an idar da ruwan da aka musu, ta shiga cikin gidan nasu babu kowa a sakar gidan haka yasa ta wuce ɗakin Ummanta kawai, da sallama ta shiga ta samu Ummar na kwance Zahra na zaune gefen ta tana karatu da sauri ta karasa ciki tana faɗin "Umma baki da lafiya ne?" Murmushi kawai ta mata ta ce "A'a Azrah, kawai dai mura ne yake damuna Maybe saboda ruwan da akayi ne" Ayrah na kallon Zahra ta ce "Zahra ko zaki tsiro mata magani ne?" Zahra ta ajiye littafinta a gefe ta miƙe zata zo karɓa kuɗin sai kuma Ayrah ta ce "Barshi ma kawai bari naje da kaina dama ranan da na tsiyama Umma magani ina binsa canci" Umma ta ɗaga kai tana kallon Azrah da har ta miƙe ta ce "A'a Azrah ke da ko hutawa baki yi ba kuma ace zaki sake fita? Ki bari nace miki sanyin garin ne ya sake tado min da muran' Ayrah bata ji zata iya ba gaskiya kallon Umma kawai take yi. Tunda hanya ta biyo da su wani ghetto area dake Kofar Marusa yake ta masifa yadda kasan wanda ke driving ɗin ne ya lalata hanyar can wanda ke driving ya ɗan juya ya Kalle sa ya ce "Dan Allah Karka isheni da jarabarka, sai kace Ni na ɓata hanyar" Sadeeq a ƙufule ya ce "Amma kuma ai kaika biyu da mu hanyar ko? Babu wani hanyar da zamu bi ne sai wannan for that matter?" Sagir ya ce "Enough please, Ina kace kana sauri shi yasa na biyu da kai ta shortcut amma ji yadda kake ɗaga jijiyan wuya sai kace wanda na maka laifi" tsaki Sadeeq yaja ganin yadda motar nasu ke wani hawa da sauka suna wani rawa a motar sabar yadda suke bin ɓacaccen hanyar, can motar su ta kafe taƙi tafiya, Sagir ya juya yana kallon Sadeeq ya ce "What is it?" Wani banzan kallon Sadeeq yama Sagir jin banzan tambayar da yake masa Sagir yayi murmushi ya ce "Ina ji motar gaskiya ba zata iya tafiya ba sai mun sauka a ga menene ne" Sadeeq yayi humming kawai ba tare da ya Kalle Sagir ba sai ma danna wayan sa da yake yi, ganin haka yasa Sagir shima ƙwafa ya gƴara zaman sa a motar ya ciro wayansa yana ayyana a ransa yau zai gwada ma Sadeeq bashi kaɗai keda miskilanci da izza ba, they were like that for almost 10 mins Can Sadeeq ya ɗaga kansa yana kallon Sagir ya ce "Let me have the key tunda baka ga damar kaimu ba" Sagir ya masa wani kallo yana danne dariyarsa ya ce "So, dama ka iya magana ne? Lokacin da nake tambayen ka ya zamu yi ai shareni kayi" ɗan kallon sa Sadeeq yayi ya ɗauke kai, jin ana shirin tada sallahr Magrib yasa ya Kalle Sagir ya ce "Idan zaka iya sauka muje muyi sallah sai mu san matsalar motar toh" daga haka ya buɗe kofar ya fita ba tare da ya san ko Sagir ɗin zai sauko ba, Chemist dake gabansu ya nufa dan tsiya musu pure water da zasu yi alwala dan they're not sure ko masallacin da ruwa. Azrah tafiyanta take a hankali tana bitan haddan da zata bada ran Saturday, hanyan Chemist ɗin ta nufa dan tsiyama Umma magani, gaba ɗaya she's out of thoughts dan can kasan zuciyarta tana tuna mata next year zata shiga SS3 ya zata yi idan kudin WAEC da NECO ɗinta bai cika ba, wani mota ne da yayi kanta horn ɗin da ya danna ne yasa ta yin tsalle dan kaucewa motar saidai ta faɗa cikin wani ruwa da-ya taru a kasa sakamakon ruwan saman da aka musu, ruwan yayi salle ya fesu a jikin Sagir, da sauri ya ja baya yana me buɗe baki yana kallon ta da mamaki ganin yadda ta ɓata masa kaya, Sadeeq ya taɓe baki ya ce "This is just a glimpse of what the ghetto girls do, that’s why I hate interacting with them" (wannan kaɗan daga cikin abinda ƴan matan ghetto zasu maka kenan, shiyasa na tsani abinda zai haɗani da su kenan) Azrah ta ɗaga kai tana kallonsa cike da ɓacin rai, dan ba kaɗan ba maganganun sa sun daketa ta ce "Wait... Don't insult anyone, because not everyone would do such a thing, Poverty is not madness pls, Even me, it was a mistake and I only did it to save life not intentionally, Be guided, please"(Dakata... Kada ka zagi mutumin da baka sani ba, domin ba kowa ne zai aikata irin hakan ba, Dan talauci ba hauka bane, don Allah, Ni ma kuskure ne kawai nayi, kuma nayi shi ne don ceton raina ba da gangan ba, kasan me zaka faɗa gaba) sai kuma ta kalli Sagir dake tsaye shock clearly written all over his face ta ce "Dan Allah kayi hakuri, bansani bane nayi hakan ne danna kaucewa motar ne" kai kawai ya gƴaɗa mata dan ya rasa ma me zai ce sai kuma ya kalli Sadeeq wanda yake tsaye har sannan shock dinta bai barsa ba ya kyalkyale da dariya ya ce "Be guided please" sai kuma ya sake kwashewa da dariya, Sadeeq ya tamke fuskarsa ko alamar wasa bai bari ba, yana kallon mai shagon ya ce "Ka bamu ruwan mana kar sallah ya barmu" Mai shagon da shima dramar su ya masa daɗi dukda cewa shi ma kame-kamen turancin yake amma saf ya fahimci duk abinda ke faruwa kuma yaji daɗin amsar da ta mayar masa ya ce "Ai ranka shi daɗe kaff unguwar nan babu wanda ya kai yarinyar nan ilimi da iya turanci dukda a makarantar gwamnati take amma wallahi daban take, kar kayi mamaki dan kaga ta mayar maka amsan da Turanci" Sadeeq ya juya zai bar wajan mai Chemist ɗin yayi saurin cewa "Yi hakuri Alhaji, ga ruwan abin duk bai kai ga haka ba" Har sannan Sagir bai daina dariya ba dan shima bai ɗauka tana jin turanci har haka ba, dukda ma shi akama laifi amma shi yanzu incident ɗin dariya yake basa ya sake kallon Azrah sannan yayi wajan mai Chemist ɗin ya karɓi ruwan yabi bayan Sadeeq da sauri dan ganin har an kusan ruku'u. Azrah ta karasa wajan mai Chemist ta ce "Maganin mura zaka ɓani da canci na da nake binka kwanaki" yana kallonta ya ce "Nawa ne ma? Sannan wani irin maganin mura?". A hanyar su ta komawa gida duk kalan masifan da Sadeeq yake ma Sagir akan yadda ya dinga ɓare baki yana dariya kamar wawa shine yafi bashi takaice, yana masa fighting right dinsa amma jibi yadda at long last ya basa kunya Sagir ya ce "Like seriously yarinyar bata burgeka ba?" Wani kallo Sadeeq ya wurga ma Sagir wanda shi hakan dariya ma yake kara basa, dakyar ya sauya kansa meanwhile yana tuki ya ce "And she's so beautiful ya Allah" Sai sannan Sadeeq ya Kalle sa ya ce "Toh ai ba muyi nisa ba zamu iya komawa wajan mai Chemist ɗin sai ya kaimu gidan su yarinyar ko?" Sagir ya ce "Wallahi zan so fah, da gaske na juya kan motar zuwa wajan?" Wani kallo da Sadeeq ya sake jefa masa yasa ya fara dariya ya cigaba da driving ɗinsa kawai. Tun daga bakin kofar gida Bappahn ya fara doka sallama har ya shiga cikin ƴar sakar gidan nasu wanda duk sanda ya shigo yana doka sallama sunsan wani abu ne ya faru "Fatsuma!" Ya daka ma Mama kira wanda hakan yasa ta fito da sauri tana kallonsa ta ce "Lafiya Malam?" Wani kallo yake mata ya ce "Ina Abdul yake?" Ta buɗe masa hannu alamar bata sani ba ta ce "Kaga Malam rabona da shi fah tun da safe" Bappah ya ce "Toh ki sani ki jama ɗanki kunne idan ba zai natsu ba zai barmin gida gaskiya, ace kullum idan aka tashi kwatancen yaran unguwar nan marasa jin magana toh Abdul na ciki, yanzu ace wai Jiya da daddare ashe sunyi kokarin shiga gidan wani fah? Hakan ya dace ne Ni shikenan bani da ƙima balle daraja a idon duniya?" Mama dake masa wani kallon sha tara ta ce "Haba Malam sai ka gama tiririn ɗan naka ne a duniya kafin ka rufa masa asiri?" Ya ce "Toh shikenan, ki cigaba da zancen rufa masa asiri wallahi Karki sa baki a mummunan matakin da zan ɗauka a kansa" daga haka ya wuce fuuu sai ɗakin sa. Siyama ce ta shigo da sallama kamar mara gaskiya tana bin gurin da kallo ganin baya nan ta ce "Mama ina Bappahn?" Mama ta taɓe baki ta ce "Ke kuma me na wani abu kamar mara gaskiya" ta ce "A'a nikam ki kyale Ni, bana son jaraban Bappah" daga haka ta wuce ciki ta bar Mama da bakin cikin abinda Bappah ya gama mata kuma tasan definitely Umma ta ji su, wani dogon tsaki taja sannan ta wuce cikin dakin ta. Har kofar gida Sagir ya sauke Sadeeq wanda har suka je inda zasu suka

Chapter 2 of 12