Share this page
11 / 12
ba sa'anninta ba ne, ba zata iya shiga cikin rayuwar mu ba balle har ta fara tunanin kishi da mu" har suka kai aya Umma na kallonsu Jikinta yayi sanyi Zahra wacce ta tsaya a bakin ƙofa da ruwa a kofi, bata san sanda ta tsaya cak ba idanu ta zuba musu itama Azrah kuwa daga cikin ɗaki ta ji komai jikinta yayi mugun sanyi Zuciyarta ta cika da fargaba da nauyin abin da ke faruwa ga kuma wani tsoro da lokaci guda ya dira zuciyarta Ba tare da jiran ko tsammani ba matan suka juya suka fita, da suka kai bakin ƙofa suka ci karo da Mama da tun shigowar su ta fito jin abin da ya kawo su ta nufi bakin kofa da sauri shine zasu fita suka ci karo Mama ta ja su gefe cikin rawar murya, amma tana kokarin yin magana da ladabi, wani kallo suke mata wanda a cike yake da wulakanci, ta ce "Kuyi hakuri ku saurare ni... Ni ma lokacin da aka kawo ita mahaifiyar Azrahn sai da nayi kusan barin gida, saboda kwatakwata ko kallo ban ishe Malam ba, gani yake ya dauko mace mai karatu sannan kyakkyawa kuma yadda zai iya nunata a kamfafoninsa, amma haka na tashi na fara neman mafita har daga karshe na samu mafita har zuwa yanzu... yanzu idan har kuna da ƙarfin hali, ba wai na kuɗi ba dan nasan kunfi karfin wannan toh kuyi iya kokarinku ku hana auren, kafin komai ya wuce gona da iri ko kuma a ɗaura auren ku shiga uku dan asiri baya cin su" Amma Hajiya da co-wife ɗinta suna kallonta da wani irin kallo na kyama da wulakanci Kamar dai "wacece ke da zaki bamu shawara?"  Mama dai bata damu ba ta juya ta shiga cikin gidan, tana girgiza kai kamar wacce ta bata san komai ba Bayan tafiyar su Hajiya da Hajiya Rabi Umma ta zauna dirshen a ɗakinta, zuciyarta cike da raɗaɗi ta dade a wajan ba tare da ta ce uffan ba, kafin ta kalli Zahra da ke tsaye gefe tana kallonta tuntubi ta ce "Har ga Allah wannan abin kunya ne, toh me su kuma na zuwa da kansu? Ashe haka auren mai mata yake jawo wa? Wataƙila ba mu yi tunanin daidai ba tun farko..." Ta faɗa cikin tausayin ƴar uwarta Azrah ta fito a daga ɗakin duk tayi kalar tausayi idonta har yayi mugun ja, Bata kalli kowa ba ta zauna kusa da Umma, sannan a hankali ta ce "Umma ni bazan ci gaba da wannan ba, Zuciyata ba za ta iya jure irin wannan wulakanci ba Idan har auren Honorable ke nufin raini da tozarci daga matansa to ni na hakura ko da kuwa me zai bani ne" Umma ta kalleta da idanu masu cike da ƙauna da tausayi amma gaskiyar magana kenan itama hakan ne a zuciyarta tun farko, amma bata so ta hana ‘yarta farin ciki dan bata san ko tana son Honourable ɗin ba, kawai ta ɗan dafa kafaɗar Azrah da murmushin amma dan bata san me zata ce mata bane cos she's speechless.... Bayan Magrib kamar yadda honorable ya saba zuwa haka yau ɗin ma yazo kamar koda yaushe, yayi parking motar sa ya sauka sannan ya karasa zauren gidansu ya kirata a waya Azrahn dake gefen Umma har sannan babu wanda yace wani abu cikinsu taji wayanta yana ringing kallon Umma da Zahra ta yi, Umma ta mata alama data yi picking, bayan su ɗanyi magana sai kuma ta wuce ɗaki ta saka Hijab ɗinta sannan ta fita Bayan sun gaisa ta kasa haɗa ido da shi har sai daya ce yau lafiya? Tana kallonsa sai kuma ta sauke ido ta ce "Alhaji don Allah ka gafarce ni Na yanke shawara… bazan iya cigaba ba, ka hakura da Ni dan Allah" ya dinga kallonta da mamaki duk yadda yaso ta faɗa masa dalilin haka ki tayi daga baya ganin ba zai hakura ba yasa ta faɗa masa cikin tsoro.... Ta karasa ta ce "kuma gaskiya tsoro nake ji, Ni ba zan iya zama cikin matanka ba harga Allah" Honorable ya tsaya yana kallonta da mamaki da kuma tausayi ya ce "Azrah… listen to me, duk abinda suka aikata sunyi shi ne without my knowledge... I've been trying to protect you shiyasa banma taɓa faɗa musu wani abu game da ke ba" Amma kafin ya gama magana ta fara girgiza kai hawaye na gangarowa daga idonta ta ce "Bazan iya ba wlhi ni yarinya ce ba zan iya zama da manyan mata ba... Zuciyata ta gaji kuma Please… just let me go" Wani irin shiru ne Honorable yayi ya tsaya yana kallon ta kamar yana neman kalmomin da zasu sauya zuciyarta… amma babu wata da zata shige zuciyarta a lokacin Azrah ta share hawaye a hankali, sannan ta kalli Honorable da ido masu ɗauke da tsoro "A'a" ta ce cikin murya mai sanyi "Ni ba zan iya zama da matanka ba Sun fi ƙarfi na, Rayuwarsu da tawa ba iri ɗaya bane, Wayon su da salon su sun sha banban da ni, Bazan iya rayuwa a cikinsu ba, kayi hakuri kawai ka kyaleni ko dan saboda Umma ta" Honorable ya langwabar da kai yana kallonta ya ce "Azrah please, give me a chance to explain bazan bar ki haka ba saboda ina ƙaunarki, and I promise you, zan kare ki" "Ka riga ka kasa kare ni!" Ta katsesa cikin sanyin muryanta da kuma wani confidence ɗin magana "Ka gani fa! Sun zo har gida, Ina laifina anan da nayi har hakan ya shafeni pls? Why not su fara maka magana tunda ai kai kace kana so na" Sai ta fashe da kuka ta juya tana kokarin shiga ciki Honorable ya tsaya cak, zuciyarsa na kuna, amma ya kasa cewa komai. Ya sauka daga matakin kofar, ya rigata shiga cikin gidan zuciyarsa a matuƙar ɓace Yana shiga ciki, ya hangi Zahra na alwala, ya dakatar da ita a hankali "Zahra jagoranceni zuwa dakin Umma mana" Zahra ta kalle shi da damuwa bayan ta gaishe sa sannan ta tafi cikin zuwa ta faɗa wa Umma. Bayan ƴan mintuna ta fito ta ce "Zaka iya shigowa" Honorable ya shiga ya gaishe da Umma cikin ladabi sannan ya zauna "Wallahi Umma, ban san abinda ya faru ba sai da naji, Ina neman afuwa a madadin matana, nasan bai dace hakan ba it's sign of disrespect nayi alkawarin kuma hukunta su" Umma ta gyara zama tana dubansa cikin natsuwa ta ce "Ba komai Honourable, wlhi komai ya wuce sannan dan Allah Karka musu magana balle wai hukunci" yayi shiru yana kallon wani waje haka kawai yaji ya kasa maganar da yayi niyyar mata kawai ya miƙe ya fita daga ɗakin Yana wucewa bakin kofa, yaga Azrah tsaye  har yanzu tana bakin kofa, idonta jajir. Bai tsaya ba, ya wuce kai tsaye zuwa motarsa, ya shiga ya tada motar zuciyarsa cike da haushi da damuwa Azrah ta juya jiki a sanyaye, ta shige ɗakin Umma. Umma ta bita da kallo na tausayi, sannan ta sauke ajiyar zuciya Zahra tana gefe ta ce "Allah sarki shi. Wallahi yana da hali na mutanen kirki, amma matansa... Allah dai ya kyauta" Umma ta ɗan murmusa "Zahra, har yanzu ke yarinya ce ba zaki fahimci komai yanzu ba" Yana isa gida, Honorable bai zauna ba ya nufi ɗakin uwargidansa rai ɓace "Big shame on you, idan banda jahilci da rashin sanin menene hankali ina ku ina zuwa gidansu yarinyar? Ni na kai kaina shine laifi ya zama nata? I'm warning you idan bakuyi hankali ba wallahi You will definitely regret" Uwargidansa ta zabura tana kallon sa da mamaki "sbd ita har zaka iya gaya mana magana Alhaji? Yanzu sbd wata banza" "Sure! And mind you, wallahi hakan bai isa yasa na fasa ba, sannan rashin hankalin ku zai iyasa ku tunzura su" murmushin takaici yayi kawai yabar ɗakin zuciyarsa cike da takaicin su. This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256. Episode 18:The Breaking Spell Kamar yadda yanda rana ke fitowa ba tare da izinin kowa ba, haka ne ma rayuwa ta ci gaba da juyawa tsakanin su Azrah da Honourable ba tare da wani communication ba, dan tun daga wancan ranar bai sake zuwa ba sai dai yakan kirata lokacin zuwa lokacin wanda kwata kwata ya kasa gane kan Azrahn, kana ganinsa kuwa kasan yana cikin damuwa wanda hakan bai fasa bayyana a fuskarsa ba Kamar koda yaushe Hajiya Maryam ta fito cikin ƙasaita da izza irin nata, makullin motar ta a hannunta sannan ɗayan hannun nata tana riƙe da fashion designer bag, tana sanye da sun glasses, ta wuce inda Mijinta ke yawan zama a backyard dan wajan shan iskansa kenan, ɗan taɓe baki tayi tana kallonsa tana ayyana damuwar daya sama kansa saboda wata banza can, ta karasa inda yake ta ce "Darling" a ɗan firgice ya juyo alamun ta yanke masa tunaninsa ya ce "Azrah!" Ɗan dakata wa tayi tana kallonsa da mugun mamaki, wani murmushin takaici da kuma bama kanta tabbacin hanyar da zasu bi yanzu shine best way out, dan tana da tabbacin cewa idan har ya auri Azrah, zata ɗauke musu matsayin su gaba ɗaya a zuciyar Honourable, Zuciyarta taji ya buga cike da tsoro, kishi da fargaba, Honorable kuwa shi bai san ya ce Azrah ba kallon yadda ta faɗa duniyar tunani yake ya ce "Maryam zaki fita ne?" Sai sannan ta ɗan kalle sa sai kuma ta ɗauke kai ta juya ta bar shi zaune baki buɗe haka ya bita da kallo sai kuma ya ɗauke kansa daga kallonta ya jingina kansa a resting chair dake zaune akaj Tana parking a kofar gidan ko kashe motar bata yi ba ta ɗauki handbag ɗinta, wayanta ta ciro a Jakkan sannan tayi dialing numbernta tana ɗaga wa ta ce "Ina bakin gate ɗinki" daga haka ta katse kiran tayi cilli da wayar a wajan mai zaman banza ta kifa kanta da steering motar tana jin wani zafi a ranta, Allah ya gani dan co-wife ɗinta ma ba yanda zata yi ne amma da zata zauna da kishiya ne? Balle mace irin Azrah, ɗan tsaki ta jaa, can sai ga Hajiya Rabi'a ta fito tana karasowa ta buɗe front seat ta zauna tana kallon Hajiya Maryam ta ce "Shine ba zaki shigo ba?" wani kallo ta mata sai kuma ta ɗauke kai ta ce "Bamu da lokacin ɓata wa, kuma Kinsan kauyen nisa gare sa amma kike wasting mana time da nasan wajen da tuni nayi gama abuna ai" Hajiya Rabia ta gyara zamanta ita kuma Hajiya Maryam ta tada motar suka bar unguwar.. suka tafi wani kauye a can cikin wani gari dake cikin jihar Katsina can wani tsohon daji suka nufa, wanda ba kowa ke iya shiga ba sai wanda suke shawara da shaidan ko suke bin huɗubar shaidan, bayan sun yi parking suka sauka suka fara nufa wani hanyar da zai sada su da fadan Mutumin wanda ba zaiyu su shiga da mota ba dole sai da ƙafa, Suna isa wajen wani dattijo mai murya katti wanda kallo ɗaya da zai yi ma mutum zai karanta zuciyarsa, kallonsu yayi ya kwashe da wata kalan muguwar dariya irin ta bosawa sannan ya nuna musu inda zasu zauna, Hajiya Rabia ta fara magana "Mun zo ne domin wata yarinya me suna Azrah, tana bamu sleepless night.. yarinyar kyakkyawar ce, kuma harga Allah muna son a nisanta ta da Mijinmu, dan ya kwallafa rai a kanta yana son aurenta mu kuma gaskiya ba zamu iya juren wannan bakin cikin ba" Dattijon ya yi dariyar da ke tsoratarwa ya ce "Wannan yarinyar ba mai sauƙi bace, ta gina kanta da addu'o'i da azkar, sannan kuma tun daga can garinsu an dafa naman su da magungunan kariya, toh kunga ba wani tsafi da zai yi tasiri a kanta idan kuma kuna so za'a iya mata wani aiki amma aikin zai yi wahala sosai sbd Akwai hatsari ana samun matsala kaɗan zai juyawa kanku" yana kare maganar ya sake shekewa da dariya mai tsoratarwa, kallon juna suka yi sannan suka sake maida kallon su ga Mutumin,yana wani irin abu tare da bubbuga kasa ya ce "Idan kuma kuna so tunda ita akwai hatsari akan ta, Amma mijinku fah? Nan da nan aikin zai kamasa" Nan take suka yarda, suka bada kuɗi masu yawan gaske sannan sun bi dukkan umarnin da aka dinga ya musu, ya ce "Za'a fara da cire Azrah daga tunanin Mijinku ? Za'a rufe zuciyarsa da rashin sha'awar ta balle tunaninta kuma, za'a mayar da tunaninsa bisa ga abubuwan daban-daban sannan za'a saka masa ƙiyayyarta mara adadi a zuciyarsa......" Tun bayan da suka dawo daga wannan ƙauyen nan, kamar ranan aka fara musu aiki dan tun daga wannan ranan honorable ya daina kiran Azrah, da farko ta ɗauka ko yawan aiki ne na office sai kuma taga shirun yayi yawa, duk da bata son sa amma sai kuma haka kawai ta fara jin wani iri kuma da shirun nasa.. Azrah ta fara jin zafi a ranta. Tun abin na damu ta har ta mayar da hankalinta ga karatunta da kasuwancinta, ta fara rubuta WAEC ɗinta cikin natsuwa, tana kuma aikace-aikacen gida sbd yadda Zahra ma ta mayar da hankalinta ga karatunta,  Mama da yaranta kuma basu fasa ci gaba da wurga masu Umma da Azrah habaici habaicen da suke musu ba... Wata rana da yamma Bappah ya dawo daga inda yake zama ya shiga compound ɗin da sallama Azrah ce kaɗai ke tuka abinci ta gaishe shi ya amsa har yayi gaba sai kuma ya tsaya ya ce "Azrah idan kin gama inason ganin ki ko?" Ta ce "Toh Bappah" bayan ta gama komai ta ɗauki abinci ta kai cikin ɗaki tana kallon Umma ta ce "Umma barin je Bappah na kirana" Umma ta amsa mata da 'Toh' Tana shiga ɗakin Bappah tayi sallama ya amsa mata ta shiga ciki ta zauna ta ce "Bappah gani" ya ce "Azrah me ke faruwa tsakaninki da Honourable ne? Ban sake jin labarinsa ba daga gare ku, kuma yanzu na daina kallon sa yana zuwa wajan ki lafiya?" Azrah ta dan yi murmushi mara sauti ta tsunkuyar da kanta kasa sai kuma tana wasa da fingers ɗinta ta ce "Bappah Inaga ba Alkhairi ne shiyasa, dan yanzu ya daina kirana kuma Nima na mayar da hankalina ga karatuna siyasa banma bi ta kansa ba, kuma yama daina kiran at all" Bappah ya girgiza kai "To cire shi a zuciyarki, Allah zai kawo wanda yafi shi, sannan zan kirasa muyi magana idan har ya fasa ne sai ya janya a maida masa sadakinsa dan ba'a nema akan nema, Kada ki damu zamu taya ki addu'a Ni da Umman ku" Azrah ta amsa da "Amin" kanta a kasa har Sannan... Rayuwa ta ci gaba da tafiya, Azrah ta ƙuduri niyya ta tabbatar da cewa ba aure ne rayuwa kaɗai ba, Duk wata mafarkin da take da shi game da Honourable dama akan Umma ne sbd lafiyarta Ta mayar da hankali sosai wajen ganin karatunta ya tafi successful tana komawa gida kullum cikin gajiya amma hakan baya karya mata gwiwa ba, Azrah ta daina jiran sakon Honourable, ta mayar da gaba ɗaya hankalinta wajen nasara ne wanda dama tun tasowanta takan dage kan karatu da kuma sana'a A bangaren Honourable kuwa, tun daga wannan lokacin duk sanda ya fara tunanin Azrah haka kawai tsoro ke kama sa, duk sai yaji kamar a birkice yake, duk da cikin duhun da yake, amma can ƙasan zuciyarsa bata daina tunanin ta ba kuma baya iya kiran ta duk da wata tsanarta da yake ji a ransa, amma bai san dalili ba, haka kawai ya fice daga hayyacinsa.. Kamar kullum yau ma ta taso daga makaranta tana hanyar gida kamar yadda ta saba tun tana karama kanta a kasa yake idan har tana tafiya, tazo zata tsallake babban titin wajan kamar ance ta kalli gefenta kawai ta kalli Ya Saif ya fito a motar sa yana tsayan abu, nan da nan murnan ta ya dawo ta ma manta cewa ta gaji ashe da gudu ta karasa jikin motar ganin kamar komawa motar zai yi tana isa ta sake masa murmushi ta ce "Barka da Rana Ya Deen" Saif ya juya yana mata wani irin kallon sannan ya bita da kallo ya ce "Ke lafiya zaki wani zo min jikin motar?" Ta ɗan kallesa sai kuma ta dake ta ce "I'm Azrah sir, baka gane Ni bane halan, please numbern Mummy da Anty suhaila zaka taimaka ka bani lokacin bani da waya amma yanzu an tsiya min Dakata wa yayi daga shiga motar yana mata wani irin banzan kallo ya ce "Malam lafiya? Ko dai kina Bara ne ban sani ba?" Azrah ta tsaya kallonsa with shock sai kuma a hankali ta ce "Bara kuma akan me? Ko kaga na maka kama da mai raba ce ban sani ba?" Wani kallo yake binta da shi ya ce "Zaki matsa min ne da kazantar ki ko sai na hanɓare ki kin faɗi tukun nan?" Ja da baya tayi tana kallonsa sai kuma tayi murmushin takaici a ranta tana ayyana cewa da badan Mummy bace Mahaifiyarsa ba, ba abin da zai sa ba tafa faɗan masa bakar magana ba, ko sake kallon direction ɗinsa bata yi ba tayi gaba abinta Da daddare ta fito daga ɗakin Umma tana haɗa kayan wanke wanken da zata yi and gobe tana da exams da safe, bayan ta ɗibo ruwa ta fara kenan sai ga Mama ta fito daga ɗakinta, Azrah ta ɗan Kalle ta sai kuma ta mayar da hankalinta ga abinda take yi ta ce "Barka da dare Mama" Mama dake murmushi ta karasa har wajan da take ta ce "Yauwa Azrah, wanke wanke kike yi kenan? Ba zaki bari da safe ba" Azrah ta ɗan tsaya tana kallonta saboda sai taji wani iri da yadda Mama ta mata response sbd gaisuwar su ma is hardly ta amsa balle harta nuna wani concern akan su, a hankali ta sauke idon ta kasa ta ce "Eh da safe ina da jarabawa ne Zahra ma itama tana da makaranta shiyasa" ta gyaɗa mata kai ta ce "Ayyah, ai naga dare yayi ne shiyasa nace da kin hakura, amma tunda zaku fita da safe gwara kiyi abinki yanzun" Azrah tayi murmushi dan Allah² take Mama ta bar wajan dan kawai ta samu kanta not comfortable, Mama ta gyara tsayuwarta ta ce "Nikam yaushe ne ma bikin naki? Ko da shike ance kina gama Wannan jarabawar da sati ko? Saura mako nawa yanzu kenan?' Azrah ta sauke idon ta kasa ta ce "A'a ina ga yanzu ba zai yiwu ba" Mama ta zaro ido irin with much concern ta ce "Ban gane ba? Wani abu ya faru ne? Ko kuma canza ra'ayinki kika yi?" Azrah tayi shiru dan bata san me zata ce mata ba dan basu saba magana da Mama cikin lumana ba balle har su ɗauki more than a minute suna magana, Mama ta ce "Kinyi shiru Azrah" "A'a Inaga ya fasa ne, kuma Nima na fasa shiyasa" Azrah ta bata amsan a takaice, Mama tayi wani murmushi tana ta bin Bappah ya gaya mata yaki gashi yanzu cikin ruwan sanyi ta samu amsar tambayarta, wani murmushin ta sake yi tunawa da shawarar data bawa Matan honorable wanda yanzu ta fara tunanin sune suka bi, daga haka ba tare data sake ce mata komai ba ta wuce ɗakin ta murna fal ranta sai yanzu taji watse A kwana a tashi a sarar mai rai.. har ta gama rubuta exams ɗinta successful, sanan an saka graduation date wanda yanzu gobe za'a yi.... Ana gobe graduation ɗinsu gida ya dauki salo na dabam, duk yadda Umma da Zahra suka so ta ɗanyi wani abu ki tayi amma daga karshe haka Zahra ta haɗa mata wasu abu ba tare data bari Azrahn ta sani ba, Umma ma gani take atleast ta ɗanyi wani abu tunda abu ne na once in a lifetime, Sannan kuma tana so taga kullum tana cikin walwala ne Da daddare suna zaune kana ganin Azrah kasan tana cikin farin ciki, Zahra ta ce "Umma dan Allah ki je tare da mu gobe!" Umma ta mata wani kallo ta ce "Yau naga ikon Allah" ɗaukan wani kayan Umma tayi daga cikin kayanta mai kyau tana warwarewa ta ce "Umma sai fah kinje Kinga yanzu ma zan saka miki kayan ki a kabbasa tare dana Yaya" Umma ta ce "Toh Uwata Zahra'u" Azrah dai murmushi tayi tana kallon draman Umma da Zahra Zahra ta gyaɗa kai ta ce "Yauwa koke fah Umma, ai hakan yafi" Azrah ta fito da dukkan kayan da Anty Suhaila ta bata ta ce "Zahra wannan yayi ko?" Zahra ta mata wani kallo ta ce "Ke kike sa a raina ki, me na ɗaukan wannan, sai kinje an kira ki cikin taro aji kunya" ta fizge wannan kayan ta ajiye a gefe wani haɗeɗɗen lace daga kayan da Aunty Suhaila ta ɗauka tana warwarewa ta ce "Wannan ya fi" Azrah ta dinga kallonta ganin ɗan gyallen sa karami ne ta ce "Ke Zahra veil ɗin kayan ɗan karami ne sosai" Zahra ta ce "And so?" Umma tayi murmushi tana kallon yaran nata Episode 19: Tears of Joy and pride Yau tunda asuba Azrah ta farka daga bacci and it didn't feel like an ordinary day, today was more than just a day it felt like a milestone, sbd wannan shine take gani a matsayin nasararta na farko, Ranan gama sakandari, lumshe idonta tayi, a moment she had been anticipating for what felt like forever. Cike da godiya ga Allah she whispered the morning Du'a 'Alhamdu lillahi-ladhi ahyana ba'da ma amatana wa ilaihi-nnushur' buɗe ido ta tayi bata san sanda murmushi yayi escape daga fuskanta ba as she felt a sense of peace wash over her, sake murmushi ma kanta tayi feeling a mix of excitement and nervousness about the day ahead. Bayan gari ya gama waye wa har Maman Azizah ta iso tare da 'ƴarta Baby, duk suna zaune ɗakin Umma, Zahra ce ta fito cikin wani sihirtaccen kyau sai zuba kanshi take ba zaka taɓa cewa a wannan arean take ba dan bata yi kama da su ba saboda yadda suke behaving da tsantsan ilimi Azrah kuma an mata wani irin make-up na nutsuwa, wanda ya fito da kyawunta kamar tauraruwa a sararin dare yadda take haskawa, tana sanye da riga da skirt na lace mai ɗinkin zamani da touch na India embroidery, gashinta a nade cikin kwalliya, fuskarta a cike da annuri da kunya, Zahra ta tsaya tana kallonta ta ce "Ya SubhanAllah.... My very own Azrah idan nace kina kama da ƴan Bollywood! don't say No, pls" Kowa dariya yayi Mama Aziza ta ce "Wannan kenan, ai dole Honourable ya ƙellara ido yace shikan ya kyasa dan wa zaiga Azrah ya hakura da ita idan ba sai dai babu kuɗi garesa" Duk suka fito zasu filin taro, hatta Umma ta kasa ɗaga ido akan Azrah sai taga yau Azrahn ta mata kama sak da mahaifiyarta nan da nan taji hawaye ya taro mata da sauri tayi saurin riƙewa to be sure kar ya gangaro balle ta ɓata wa Azrah rananta... Mama suka kalla tana kan ɗaura abinci, Umma bata yi mamakin rashin ganin Maman Asabe da bata yi ba, Umma ta ce "Maman Abdul barkan mu da safiya" Mama ta ɗaga kai ta mata wani matsiyacin kallo, Maman Azizah ce ta yanke ma Mama tunanin da ta fara a rai ta ce "Mun tashi lafiya?" Mama ta taɓe baki ta ce "Klau, wato ke da kike can nesa har an sanar da ke amma mu da ake gani zamu ma yarinya baƙin ciki ko kuma musa a fasa taron ai gashi muna gida ɗaya ko sani bamu yi ba" Umma ta ce "Dan Allah kiyi hakuri, wallahi Nima ban ɗauka zani ba sai Jiya da daddare yara suka sakoni gaba akan lalle sai naje shiyasa" Mama tayi wani humming irin cike da takaici Umma ta ce "Kuma munyi magana da Bappahn su ai yace ya sanar da ke, maganar gaskiya kuma harga Allah kamata yayi na faɗa miki da kai na amma na mance" Zahra ta tamke fuska tana kallon Umma ganin banda ɓata musu lokaci babu abin da Mama ke yi yasa ta ce "Umma bari mu fara gaba kar Yaya ta makkara" wani kallon tsana Mama ta bi Zahra da Azrah da shi, Mama Azizah ma data ga ba amfanin mata baya Ni ta ce "Toh mu mun tafi" sai kuma ta maida kallon ta ga Umma ta ce "Mu je kar yarinya ta makkara" daga haka suka nufi kofa Mama ta bi su

Chapter 11 of 12