Share this page
3 / 12
dawo bai sake kula Sagir ba, bayan ya sauka zai kulle car door din Sagir ya ce "Good night Aboki, please be guided" Sadeeq ya tsaya yana kallonsa sai kuma ya ce "Look! Idan har ba zaka daina shirmen nan naka ba wallahi ba zan sake haɗa hanya da kai ba balle wani aiki ya sake haɗa mu" Tun kafin Sagir yayi magana ya wuce zuwa babban gate ɗinsu wanda gidan sai ka ɗauka a wata kasar take. Umma sai kallon Azrah take wanda tun ɗazu tayi tagumi, kana ganin ta kasan yau tana moody, Umma ta ce "Damuwar me kike saka ma kanku Azrah? Kina bukatar wani abu ne?" Azrah ta sauke hannunta da tayi tagumi tana kallon Umma ta ce "Nothing fah Umma, kawai dai na gaji ne" Umma ta ce "Toh tashi kije ki kwanta, Kinga ƴar uwarki kam ai ta kwanta kuma ke kike bukatar hutu" ta girgiza mata kai ta ce "Idan na kwanta kuma aka zo siyan abu kuma fah Umma?" Umma ta ce "Sai na fita na bayar" Azrah tayi murmushi dan ita a kalan tausayin Umma da take ji ba zata bari tana aikin wahala ba saboda kar kanta ya fara ciwo balle har taje ta fama ma kanta matsala, ga kuɗin aiki wajan 30Mil ta'ina zasu fara, kamar Umma tasan tunanin da take yi ta ce "Ai ba zan yi hayaniya ba balle har kan ya fara ciwo Azrah, balle ma kwanan nan ma ai kan yana ɗan ciwo amma ai yana tafiya kuma ba tare da ciwon ya ta shi ba" Azrah ta ce "Toh Allah kara miki lafiya Umma, burina nayi karatu na samu kuɗi da za'a rabaki da wannan ciwon ne" Umma ta ce "Amin, Allah cika miki buri". Har Azrah ta kwanta amma kuma sai ta kasa manta da maganar wannan strangern ga kuma Ya Saif, haka kawai taji ta tsane su with passion, wato talaka bashi da wani ƙima ko daraja kenan? Wato talaka bashi da aiki sai zama mutumin banza? Wannan ne babban burinta na son cinma buri a karatu saboda ko dan kujewa irin wannan wulakanci, tasa hannu ta share hawayen fuskanta sannan ta miƙe zaune tayi addu'an bacci ta gama shafe jikinta ta kwanta. Washe gari tun safe Mama ta ɗaurawa Habiba tallah, wanda Siyama na gefenta suna dafa abinci da itama zata fitar tallah. Azrah dake kallon Umma ta ce "Umma toh barin tafi kasuwan ko da wani abun da kuma zaki bukata?" Umma ta ce "A'a babu Azrah! Allah tsare min ke" ta amsa da "Amin" a compound taga Mama da Siyama suna ta girki suna magana, a hankali ta ɗaga kai tana kallon Mama ta ce "Ina kwana" Mama ta ɗago tana mata wani kallon banza ta ce "Karki fita ko ina, ki dawo dan yau dake za'a je tallah gareji sai dai ki mutu amma sai kinje" Azrah taji hawaye yana shirin taruwa mata, amma ta hana kanta haka, tayi wucewar ta kofa ba tare da ta sake kallon Mama ba dan tana jin wallahi ko dukan mutuwa za'a mata ba zata tallah gareji ba, sai kace ƴar iska mara kunya. #Jiddatulkhayr 08110615256 Free page Episode 4: Beneath the surface Mama tabi Azrah da kallo baki buɗe har ta fita, ta fara tafe hannu tana salati ta ce "Yau Ni Azrah zata ma rashin kunya? Har ina mata magana zata iya tafiya ta barni tsaye? Saboda ganin bani na haifeta bane ko kuma so take ta nuna min cewa ban isa da ita bane" Siyama ta ce "Ai dama za'a rina, yanzu gani take ai tafi ƙarfin tallah balle tayi, mune dai ya zama mana dole" Mama ta ce "Wallahi bari Bappahn ku ya dawo, zanyi maganin ta sai dai idan har ta daina cin abincin gidan nan ne" Siyama ta ce "Toh Kema Mama ai Kinsan ba zata ba kika tsaya ɓata bakin ki a banza, baki ga kalar fatarta bane, ai gani take ita ƴar hutu ce mune dai ƴan wahala" Mama ta tamke fuska ta ce "Toh me a fatar nata?" Siyama ta ce "Yanda yake sheki mana, Kema Kinsan Manyan maza ne ke siya mata waɗannan sabulun turawan mai uban tsada, kuma Kinsan maza basu kashewa mata kudi haka kawai wlhi" Mama ta fara dariya ta ce "Ai kuwa Nima har sannan mamaki baya barina sai na ratsa aina take samun su, Ahap ba sunce ita ƴar boko ba? Muna nan mu zuba da su saita kawo musu abin kunya, waye kuma bai san Matan boko ba?" Siyama ta miƙe tana faɗin "Ai muna kallon su kuwa". Ba Azrah ta dawo gida ba sai wajajen karfe 11am a mugun gajiye ta karasa cikin gidan nasu wani almajiri yana biye da ita rike da wani bakko a kofar ɗakinsu ta ajiye na hannunta sannan ta karɓi na hannunsa ta fara kaiwa ciki, ta kuma fitowa ta basa laɗan aikinsa sannan ta karasa ciki ta zauna kan laidar dakinsu tana kallon Umma dake zaune tana karanta wani lissafin musulunci, Umma ta rufe littafin tana kallonta ta ce "Sannu Azrah, kinsha wahala kam" ɗan murmushi tayi ta ce "Sannu da hutawa Umma" fara cire kayan bakkon tayi tana nunawa Ummanta kayan da tayi tsari tana faɗa mata kuɗaɗen su Umma ta ce "Ɗazu naji kamar kun sami matsala da Mama?" Nan da nan annurin fuskarta ya washe tana kallon Umma ta ce "Kiji fah Umma, wai tallah gareji zata bani na kai mata, nikuma nasan ba zanyi ba shiyasa kawai nayi tafiya ta" Umma ta ce "Kinyi min daidai dan Banga dalili ba, idan Nima ina son na saki tallan ai da tuni na fara turaki amma dake bana son yarana suna tallan shiyasa ban fara barinku kuna yi ba tun farko, sai dai kawai yadda naga tana masifa na san dole zata haɗa ki da Bappahn kune sai kisan me zaki ce masa" Azrah ta ce "Toh shikenan" Umma ta ce "Miƙamin laidan sai na fara kulla busheshshin kayan miyan, kawai ke kije ki shirya ki tafi gidan da kike aiki Karki yi rana tunda yau baki je boko ba, danma suna hakuri ne kawai wlhi" Azrah ta miƙe ta bawa Umma laidar daga haka ta wuce cikin ɗaki ta fara shiryawa, har zata sa wani ƙuncen Abayan Anty Suhaila data bata sai kuma ta fasa tunda aiki zata no need kawai ta sanya wani riga da skirt ta ɗaura hijabinta daya ɗan koke ta fito tama Umma sallama sannan ta fita. Tunda ta shiga parlorn taga Saif yana zaune babu kowa hakan yasa ko kallon direction ɗinsa bata yi ba ta kama hanyar kitchen ya ce "Ke kuma haka aka baki tarbiyya baki iya gaisuwa ba?" Tayi kamar bata ji sa ba, cos kawai dan tana aiki a gidansu ne kuma yaron Mummy ne amma da sai ta faɗa masa bakar magana akan bakar maganar daya gaya mata jiya dan sai yanzu abin ke kara jiƙa mata kuma ta ɗau alwashin koda wasa ba zata kara Gaishe sa ba balle ya sake cewa tana son jan hankalin sa ne gareta, attention ɗinsa take nema, harta shige kitchen bata Jiyo ba ya bita da kallo baki buɗe, sai kuma yaji takaicin magana da yayi dan wannan raini ne ma gashi baya so wani abun ya sake haɗasa da ita, yayi dana sanin maganar da ya mata yafi cikin ƙwando Harta gama girki ta fitar kan dinning bata ga Mummy da Suhaila ba, hakan yasa kawai ta girka abinda tayi kwana biyu bata dafa musu ba, tana gama duk wani activities dinta na gidan ta fito parlorn da niyyar tafiya, idonta akan na Saif dake dining ɗin yana cin abinci ya faɗa, da sauri ta ɗauke kanta daga haka ta fita a Parlorn tana mamakin ai kyankyaminsa na banza ne, idan har yana kyamarta akan meyasa zaina cin girkinta ita wannan abin ne yafi bata dariya da tasa kalar saftan. Tafiya kawai take abinta ba tare da komai ba, sai dai kawai tunanin yaushe zasu gama wannan wahalar a duniya? Few houses da gidan Mummy ta kalli wani mota na parke shima gidan ba karya ya haɗu fiye da tunanin me tunani maza uku na jikin motar da alama dai hira suke, ita dai kullum ta shigo unguwar nan sai tayi fatan suma Allah ya basu koda ƙwatan waɗannan ɗinne. Kamar ance ɗaga ido kawai idonta ya sauka a cikin nasa, ta gane sa clearly, dan babu ko wani doubt tasan shine tamke fuskanta tayi zata ɗauke kai sai kuma ya sauka a cikin idon Sagir, wanda shima clearly ya gane ta, da sauri ya taɓa Sadeeq ya ce "Be guided please, gata can" sai kuma ya kwashe da dariya dan shi abin na mugun basa dariya dan duk duniya babu me iya faɗawa Sadeeq magana sai Mami, amma sai gashi ƴar yarinya ta faɗa masa, kuma babu shakku balle nadama saima lots of confidence da take dashi A fusace Sadeeq ya zuya yana ma Sagir wani kallo ya ce "Enough please, wait... Do I have any business with her? Ko dai kana neman hanyar da za'a haɗa ka da ita ne?" Sagir kallonsa kawai yake ganin How serious he is Al'amin ya ce "She's beautiful, girlfriend dinka ne Sadeeq?" ya kare maganar in very calm tongue, Dan shi bai san abinda ke wakana ba, a mugun fusace Sadeeq ya shige motarsa ya kunna motar wanda kawai figarta yayi da gudu har sai da Al'amin ya matsa masa ganin zai iya buge su, ya bisa da kallo sannan ya maida kallon sa kan Sagir ya ce "Me amfanin hakan da yayi?" Sagir ya ce "Alakanta sa da ita da kayi ne ya basa haushi, baka ji yana tambaya yana da business ne da ita ba?" Al'amin ya taɓe baki ya ce "So? And isn't she beautiful ko dan nayi admiring ne yaji haushi? Sagir ya ce "Nace maka dan ka haɗasa da ita ne fah yaji haushi" taɓe baki Al'amin yayi ya ce "Then, shi yaji wajan, amma ai wannan tafi ƙarfin sa". Azrah dake tafiya taga wucewar motarsa kamar wanda zai tashi sama dan bata san sanda ta koma gefe da gudu ba, sai kuma ta bisa da harara tana taɓe baki. Da yamma tana karatun babu kowa a ɗakinsu dan Ummar da Zahra sun fita, a cewar su tana ɗan zaga unguwar kar zaman gida kullum kuma ya jawo mata wani ciwon gwara tana excerses Muryan Mama taji ita da Bappah ga Habiba ma dake sa baki, amma ta gagara sanin akan me suke magana, haka kawai yaji hankalin ta bai kwanta da wannan maganar nasu ba saboda yadda tasan yau kuma ita da Mama sai Allah, rufe littafin tayi ta maida hankalinta tana sauraron su, Bappah ya ce "Toh ke Fatsuma ai shikenan tunda taki tallan kawai ki kyaleta" Mama tayi wani ashar ta ce "Kana nufin duk iskancin data min da nuna min ban isa da ita a ya tafi a banza kenan? Harda buga ɗan karamin kofar mu da muƙe managing ɗinsa fah, ace ai ko bata sanni ba bai kamata ina mata magana tayi wucewarta ta barni tsaye ba, Ni kayan takaicin ma yadda ta gaggayamin magane yafi komai ɓata min rai" Bappah ya ce "Bansan sau nawa kuma zance kiyi hakuri ba, maganar tallah kuma tunda tun farko Uwar bata so shikenan, amma dole zan ɗau mataki akan yadda tayi miki ai" Mama ta masa wani kallo ta ce "Toh gaskiya Malam sai dai Matar ka da yaranka su fara girkin su amma Ni gaskiya nagaji, Ni nawa yaran ba sonsu nake ba da nake tura su tallah ai, wato nata yaran ne ƴaƴan gata ko? Wallahi na daina saka musu abinci daga yau ɗin nan" Bappah ya ce "Haba ke kuwa Fatsuma, ai abin duk bai kai haka ba, tallah kuma tunda kince sai sun fara zuwa ai wannan dole ne, dole ne sai sunje amma sai dai kar ana shiga hakkin lokacin karatun su tunda suna zuwa makaranta" sai kuma ya shiga ƙwalawa Azrah kira "Ke Azrah! Kina ina ne ina magana ba zaki fito ba" Azrah dake sauraron su ta ajiye littafin hannunta ta share hawayen daya gangaro mata she wish Umma na nan, ta miƙe jiki babu ƙwari, jin ya sake doka mata kira yasa ta ce "Na'am Bappah gani fitowa" Muryan Mama ne ya biyo bayan nata tun kan ta rufe bakin nata ta ce "Dan uban ki ana magana ba zaki fito bane ko sai na shigo na fito dake" buɗe labulen kofar tayi ta fito koda wasa bata kalli direction ɗin Mama ba tana kallon Bappah ta ce "Bappah gani" Bappah ya ce "Kema yanzu kin canza hali ko? Akan wani dalili zata na faɗa miki magana kice mata A'a sannan tana miki magana kawai sai ki tafi ki barta a tsaye? Haka ake yi ko kuma Uwarku ce ta koya miki" Azrah ta share hawayen daya gangaro mata tana kallon Bappah ta ce "Bappah nifa ban mayar mata da magana bafa, kawai nace Ni ba zani tallah bane kuma wai tallan a gareji ba zan iya zuwa bane Bappah shiyasa nace A'a , amma kuyi hakuri dan Allah" Bappah na mata wani kallo ya ce "Kin kyauta ma kanki, yanzu daga yau zaki fara tallan kema kinji? sai kar kuyi nisa" "Babu tallan da zata yi dan Banga wanda zai ɗaurawa Azrah tallah ina da rai ba" Murya Umma ya dake kunnuwan su wanda basu lura da shigowa nata ba ga kuma Zahra a gefenta, karasa cikin sakar gidan tayi tana kallon Bappah da mamaki dan tasan shima baya son tallan nan amma ji lokacin guda ya yarda, Mama ta katse mata tunanin ta "Ai ita take ɓata yaran Malam, ba'a isa a ɗau mataki akan su ba sai tace ita kaza, ga ita mai ƴara ba" Mama ta kalli Zahra dake gefen Azrah ganin yayarta na kuka yasa itama farawa ta ce "Azrah kama hannun kanwarki ku wuce ciki" Azrah ta juya Zahra na biye da ita a baya Umma tana kallon Habiba dake zaune sai washe baki take tana dariya ta ce "Kema Habiba tashi ki wuce ciki" Habiba ganin Bappah yasa ta ɗan ɓata rai ta wuce ciki tana gunaguni Mama na kallon Bappah ta ce "Malam kayi hakuri amma gaskiya I'm very disappointed in you, ace har zaka yarda a tura yaranka tallah? Idan har ina son suyi tallah da tuni na fara ɗaura musu, ko Azrah dake sana'a iri da kala naga a gida take yi sai dai wasu lokutan a fitar kofar gida amma rana tsaka kace zata fara fita tallah" Mama ta riƙe kugu tana kallon Umma ta ce "Toh sannu Uwar Agwagwa, ai ta gwada bata so ina Kema zaki so" Umma ta ce "Tabbas kuwa ba zan so ba" Bappah yana kallon dukkan su ya daka musu tsawa, Mama ta ce "Shikenan Malam tunda har abin haka ne, Ni kuma daga yau na daina abinci dasu, su koma girka abincinsu su daina dogara da Ni" Bappah zai yi magana Umma ta rika sa "Baki san abinda nake addu'a akai ba kenan? Dama taya idan banda zalunci ace kece zaki na girki sai kinga dama ki tsokara mana sannan kuma ki haɗa da gori, wallahi tafi Nono fari a waje na" Bappah ya ce "Yanzu ke da kike murnan an raba girkin ya zakiyi, kin samu ana rufa miki asiri shine kike da bakin magana ko?" Ta ce "A'a ta rufa maka asiri dai, sannan ai dama cinmu da shanmu a kanka yake Malam, dan haka sai ka fara providing mana muma" Mama da shock take kallonta dan bata ɗauka hakan daga gare ta ba, taso ta bata hakuri ne Ita kuwa daga haka ta juya ta wuce ciki, tana shiga Azrah tayi kanta da sauri tana faɗin "Umma kiyi alwala ki zauna da shirin ki ana magrib sai ki kwanta ki huta Kinga kinyi magana dayawa Ni tsoro na ma kar ciwonki ya tashi ne" Umma na Murmushin karfin hali ta ce "Karki damu Azrah, ba zai tashi ba In Shaa Allah" daga haka ta wuce ta kwanta akan dadduman dake shimfiɗe a Parlorn. Har dare yayi Mama bata kawo musu abinci ba, Azrah dake zaune ta kalli Zahra ta ce "Zahra zo ki raka Ni" Zahra ta mike tare suka wuce kitchen ɗin, tuba tsohuwar mukubur ɗinsu sukayi suka fito dashi fili, Azrah ta ɗauki gawayi a wanda take sayarwa ta hura wutan, ta wuce ɗaki bata daɗe sosai ba ta fito tana mika ma Zahra kuɗi ta ce "Zahra je ki tsoho mana taliya laida ɗaya sai a sa miki mangyaɗa gwangwani ɗaya kinji? Kiyi sauri dan Allah" Zahra ta amsa da "toh" ita kuma ta zauna nata cigaba da fifita wutan. Bayan sun gama girkinsu suka shiga ciki da shi, mikawa Umma suka yi, Umma ta ce "Amma mayasa kika tsaya Azrah? Azrah ta ce "Toh haka zamu kwana da yunwa Umma? Ai abinci dole ne" Umma ta ce "Toh ai naga a cikin kudin kine Azrah, kuma bana son kina taɓawa saboda gaba" Azrah ta ce "By then, Allah zai kawo mana wani In Shaa Allah" Umma tayi shiru tana kallonta, suna kan cin abincin sai ga Bappah ya shigo, Umma ta ce "Sannu da zuwa" ya amsa da "yauwa" yana kallon su Azrah ya ce "Ku shiga ciki ko?" Ta shi sukayi suka wuce ciki, ya maida hankalinsa ga Umma ya ce "Amma mayasa zaki ce kina son zakuna girkin ku?" Wani murmushin takaici Umma tayi ta ce "Toh dama ai ba zamanta nake ba, kuma ai ba ita ya kamata ta ciyar da mu ba" Bappah ya ce "Toh ai zamana kike kuma Ni na tsara hakan" Umma ta ce "Yanzun saboda gudun karka na tsiyo mana kayan abinci ne yasa kake son naje na bawa matarka hakuri Malam? Lokacin da ka dauki kuɗin da ka siyar da machine dinka ka bata da niyyar tana juyawa ana samun wanda za'a ci Ni ka tambayi shawara balle kuma ka bani Nima ina juyawa? Amma ai gashi kullum gori da kuma gadara da akan ita take ciyar damu ya ishe Ni, kaima sai kayi hakuri akwai ka cigaba da siya mana namu muna yin sa daban" Bappah yayi shiru yana kallonta. Duk kallon Daddy dake bayani suke, a hankali Saif ya ce "Amma ai Daddy Suhaila ya kamata ama magana saboda Normally mata na riga maza aure amma tana her late 20s sai ni kaɗai" wani kallo Daddy ya masa, Mummy ta ce "Deen yaushe zaka daina haɗa kanka da kanwar ka ne wai?" Daddy ya ce "Saboda ita macace idan miji bai zo ba ba ita zata je ta nema ba, kai kuma na miji ne, a haka ne kake son na ɗaura ka akan business Dina ba tare da kana da aure ba? Ai hankali na ba zai kwanta ba ina turawaka different countries" ya ɗan kalli Daddy shi ya tsane anything pertaining wannan so called company, ya fiso independent life ne amma ba zasu gane ba. #Jiddatulkhayr 08110615256 *BEYOND THE VEIL (LABULEN SIRRIN)* YOTA ID/026 Wattpad © Jiddatulkhayr Instagram © Jiddatulkhayr writes Free page Episode 5: When hope seems lost Azrah data fito sanye da uniform ɗin makarantarta tama Umma sallama harta tafi bakin kofa kuma ta tsaya ta juyo tana kallon Umma ta ce "Dan Allah Umma kar kice zakiyi girki ko wani aiki, Kinga ba'a son wani abu da zai sa ciwonki ya tashi ko ya jawo miki ciwon kai" Umma tayi murmushi ta ce "Naji Azrah, Allah muku Albarka, ki tafi kar kiyi latti ko?" Azrah ta gyaɗa ma Umma kai ta nufi kofa. Azrah tunda ta isa makaranta, ta lura da yanayin da ya ɗan sauya, An taru a harabar makaranta yayin da Principal ke magana da ɗalibai "Ku sani tun kafin ku shiga SS3, dole ne a biya kudin candy, Wannan tsarin ne tun daga sama, kuma ba za mu ɗauki ɗaliban da ba su biya ba idan har an rufe" Maganar tayi nauyi sosai a zuciyar Azrah. Candy din dai wani nau'in horo ne na makarantarsu kafin jarrabawar WAEC, kuma kudinsa yana da ɗan yawa sai dai bai kai kuɗin WAEC ba, amma idan mutum yaci za'a tura sunan sa ga gomnati ya biya masa WAEC da NECO Sai dai kamar yadda aka santa, Azrah bata bari damuwarta ta bayyana a fuska ba. Ta cigaba da sauraro cikin natsuwa, amma zuciyarta cike take da nauyi tana kokarin hana kanta hawaye, Gaba ɗaya wannan ranan haka ta wuni a school babu wani laƙƙa a jikinta dan ita sanmaninta sai anyi 3rd term ne zasu biya. A hanyanta na komawa gida, bata ma lura da abinda ke faruwa a gabanta tafiya take absent-minded ko hirar da kawarta Fatima take mata da 'Em.. eh.. A'a" take amsa mata ba tare da tasan tana hakan bama. Kamar wacce aka kunna ma zuciyarta wuta ko aka zare fahimtarta" Tana isowa gida, taji aroman girkin Umma, ta karasa ɗakinta, ta aje jaka da schl stuff, sannan ta fito da sauri zuwa kitchen dan bata ga Umma a main spot ɗinta ba, A nan ta tarar da Umma tana tuka tuwo "Umma! Na gaya miki fa ba'a so ki na aiki! Kina so ki fama ciwon kai naki ne? Dan Allah ki daina! Ki ƙoma ciki ki zauna ki huta mana!" Umma ta juyo da murmushin mai laushi ta ce "Na gama yanzu. Bari na koma daki Azrah" Azrah ta ɓata fuska tana kallon Umma dake mata murmushi Da ta juya ta fita, Azrah ta bi bayanta cikin sauri, tana shiga ɗakin, ta zauna kusa da Umma tana kallon ta idon ta cike da damuwa ta ce "Umma yau a makarantar mu wai mu tanadi kuɗin candy saboda a wannan term ɗin zamu yi kafin mu shiga SS3 duk wanda yaci shi gomnati zai biyawa kudin jarabawar waec da neco" Umma tayi murmushi ta ce "In shaa Allah kina cikin wanda zasu ci Azrah, na yarda da addu'a sannan na yarda da ke" Azrah na kallon Umma kamar bata fahimci me take nufi ba, a hankali ta ce "Umma kamar baki gane ba, zamu biya kudin candyn ne yanzu fah, toh ni da nake tara kuɗi akan sai na shiga ajin karshe ne, amma yanzu zamu biya" Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Azrah, ki kwantar da hankalinki kinji? Ai tunda Bappah ya ce ya bawa Mama kudin WAEC ɗinki, danta juya jari dashi ai akwai sauki, Zamu samu mafita in shaa Allah" Azrah ta ɗan saki ajiyar zuciya "Toh Umma, ni dai na yanke shawara zan fasa asusun nan nawa, Ko da bai ishe ni ba, amma zan yi ƙoƙari, Ni bana so wannan damar ta wuce ni saboda kuɗi" A dai-dai lokacin Zahra ta turo ƙofar da sallama a bakinta, bayan ta gaishe su ta tsaya binsu da kallo sai kuma tayi dariya ta ce "Kamar dai magana mai muhimmanci kuke ko?... Me ke faruwa?" Azrah ta ɗan ƙalleta, bata da niyyar faɗa, sai dai Zahra ta matsa har taji labarin Zahra ta haɗa gira ta ce, "Ai ni dai bazan lamunci a hana Azrah karatu ba saboda kuɗi, dole Mama ta amo da kuɗin da Bappah ya bata tunda ya hana miki Umma, ko kuma wallahi shi Bappahn zai sake bada wani" ta kare maganar ranta a ɓace Azrah ta dubi 'yar uwarta, zuciyarta na sauƙa kaɗan Kodayake har yanzu bata da tabbacin yaya zata magance matsalar candy idan Mama ta ce 'Aa' kuma tasan zata iya dan bata damu da karatun nata yaran bama, idan Bappah ya ce bashi da kuɗi kuma fah? amma kalaman su Umma da Zahra sun rage mata nauyi a zuciya. Da Rana bayan ta dawo daga makaranta, tana cikin shirin fita gidan Mummy sai Umma ta kirata ita da Zahra, suna zauna ita da Zahra a dakin suna kallon Umma, Umma ta kalli ‘yayanta da nutsuwa ta fara da "Ku sani rayuwa ba zata taɓa zama daidai da yadda muke fata ba, ku kalli mahaifinku a baya da yadda yanzu kuma rayuwa ta canza masa, Amma duk da haka, kada ku taɓa rasa bege, Idan kun wayi gari da lafiya, ku gode wa Allah, sai dai yana da kyau kuma addu'a da positive thoughts, Rayuwa karshen ta ba komai bane, komai sai dai a barshi..." Muryarta ta yi rauni yayin da kalmomin ke fita kamar ana taune su, Zahra ta lumshe ido, Azrah kuwa bata ce komai ba, amma zuciyarta cike take da ɗumbin damuwa, Kalaman Umma sun shiga zuciyarta fiye da yadda take sammani, amma gaba ɗaya sai suka sinci kamar wani abu na shirin faruwa dasu ne, A haka ta tafi gidan Mummy kamar kullum, tana shiga compound ɗin, sai ga Saif, yana shirin fita, matsawa gefe tayi ta wucesa ba tare da ta gaishe sa ba, with shock ya dubeta

Chapter 3 of 12