zan aureta tunda baka bukatarta a rayuwarka ka sake ta ka ga ikon Allah!" "Deen!" "Eh zan mata da abotarmu, alakarmu zan aure ta a matsayin da duk tazo min kuma zan yanke mu'amala da kai saboda ex-wife dinka ce kada ka ketare min iyakata, sai ka zauna da ƙaruwar da take biyo namiji har gidan aurenshi akan idanun Matarshi, idan da kasan wacece yarinyar nan ko hada numfashi da ita ba zaka yi ba, Aliyu na gaya maka gaskiya ne domin ba zan koma baya ina cin dudduniyarka ba! Ka sani ba iya kanka kake jefawa bala'i ba innocent soul din da kake jefawa masifa shine tashin hankali, Tafida zina ko kusantarta masifa ce balle kuma Allah ya baka mace ta gari da take kara kame kanta, idan da yau duk abinda zaka yi iya kanka zai tsaya da sauki idan ita wani yayi attempt dinta saboda ka kusanci zina kayi mata adalci? " "Amma kasan ban tab'a zina ba ko?" "Taya xan sani bayan ka ajiye mace a dakinka kuna kwana daki daya, ita matarka ta sunna ka mai da ita hoto, kamar yadda kake da lafiya da kuzari haka take da shi kai ba Jahili ba amma kafin jahili jahilci zan gayawa Abbanka yasan irin ukubar da kake ganawa Ummu, tunda kai ka tashi daga sahun mutanen kirki ka koma sahun kasikai azzalumai masu cutar matayensu da danginsu."
"Deen " dakatar da shi yayi yana faɗin. "Ban gama ba, ita yarinya har abada ba zaka tab'a samun biyunta ba, ta rufa maka asiri ta saka ka boye macen da ta zo mata dadiranci sannan kayi tsammanin yarinyar nan har yau bata isa ta baka abinci ka ci ba, Yarinyar da ta rufa maka asiri idan wata ce tona maka asiri zata yi a gaban mahaifinka, amma ta nunawa maka kai mutumin kirki ne abin da ta gani ba zai hana ta rufa maka asiri ba, Ummu Hadiyya mace ce ya kuma me tarbiyyar da ake bukata don Allah idan ba xaka zauna da ita ba da kayi ta bata wahala ka sakota ni zan zauna da ita
Daga haka ya bar shi sake, sai dai yadda ya fadi haka sai yaji ranshi ya b'aci ba fa akan Ummu ba a'a shi kawai babban matsalarshi aibanta Saadi baby da yayi, bayan tafiyarsu ne ya shigo ya dauki abinci ya kai mata dakin, tana murmushi ta ce mishi. "Abba ya tafi ne?" "Eh ki koma gida yau, zaman ya isa haka!" "Ya Ali!" "Nace ki koma gida!" Jin haka yasa ya shiga hada kayanta tana kuka. "a yau xan koma Maiduguri!" Kallon agogon dakin yayi yana shafa kansa. "Zuwa gobe ki wuce!" Sannan ya fita, har dare bai kuma yin wani abu ba asalima ban san ya suka kare ba, washi gari da sassafe naji tana ta kuka tare da surutai, domin cikin dare da na fito na dibi tea saboda muran da yake damuna a parlour na ganshi ya kwanta, na dauke kai nayi kitchen. Ko bayan tafiyarta ban yi abin karyawa da wuri ba, domin nasan iya cikina ne. Sai wurin sha daya na dumama tuwon jiya naci, da rana nayi shinkafa da wake, na ci tare da barin sauran zuwa dare don nasan baya shigowa sai da barcin, haka muka cigaba da rayuwa babu me shiga harkan wani sai dai akwai wata yarinyar me suna Tina da ta dame mu da zuwa, idan tazo tun safe sai ta kai har karfe goma kafin ta tafi, na farko Ita ba musulma ba balle nace ba wani abu. Sai dai dake ban bata fuska ba. Tana zaune zama take a parlour idan yana gida suka yi hira, haka zata gayyato kawayenta sun mai da ni mai girkinsu. Sannan ban isa na ce yau ina ciwo ba domin Tafida da bai da uzuri yanzu sai ya fara fada. A hiransu na fahimci Babanta kusan gwamnati ne, sannan yana da kusanci da shugaban kasa, bayan nan Baban Tina Yana son Tafida musamman da yasan waye Uban Tafida, haka yasa shi kara son shi. Sannan wani abu da ya yarinyar tana da hankali da nutsuwa matsalarta shine yadda ta maida ni mai girkinsu.
Ranar wata Juma'a ina dan wake tazo, tana buga kofa naje na bude mata, "Amarya yau na zo miki da wani abu canka?" Murmushi nayi nace mata. "Kin ga na bar abinci akan wuta shigo!" Har ga Allah na gaji sosai, kamar na gudu gida haka nake ji, kwashe dan waken nayi na zuba a ruwa na karasa sauran jifan. "kin ga wannan wata kawata ce a kamfanin Maggi star, wai za ayi girki na gasa arewa da kudu shine na amsa miki Form!" Kallont nayi bakina sake."kika amsa min?" "Eh mana taya xan biya ki hidimar da kike mana, kin ga har da kyauta na san Amarya You Are the best, kuma abincinki ko uban waye yaci zai sara miki, manyan masu girki ake gayyata shine na gayawa Aliyos yace babu ruwanshi." Murmushi nayi tare da cewa. "Tow bari na gani xan gayawa Alhajinmu!" "Yawwa next week za a kira ku!" Ta mika min takardan yarinyar nan ba karamin kudi ta kashe ba, sai naji kunya ya kama ni. "dubu dari uku kudin shiga gasar!" "Kina tsammanin baki fi karfin haka bane?" "Na gode!" Na fada bayan na ajiye takarda na nufi daki na ji bakiɗaya kunyarta ya ishe ni. Na fito na zuba mata abinci, tana ci dai ga Tafida na shiga kitchen na dauke mishi takardan na ajiye mishi. "Me yasa kika kashe kudinki tina akan inuwar alli, ina ruwan kukun guntaye, don Allah dube ta da kaɗan tafi Mug tsawo!" "Aliyos wannan cin fuska ne." "I'm just joking ne fa!" "Wannan ba joking bane mock dinta kake, maybe a idanunka ne kake kallonta haka, amma tana da mutunci da sanin darajar kowa tunda nake zuwa bata tab'a gajiya da ni ba, sannan ko ya na kawo mutane zasu ji dadin zuwan Please bayan ni kada ka kara cin zarafinta haka, domin ni idan aka min zan iya mutuwa balle ita da haka.bai dame ta ba which mean ta saba da cin fuskarka. Addininku ya bawa mata kariya, ya kuma girmamasu. Sannan ya nuna musu muhimmancin mutanen, kai kana da kirki da mutunci amma Matarka ta wuce tunanin ka, da ce ni ce kai na sameta har abada ba xan yi wasa da damar da na samu ba, ita kamar haske ce a gidanka a lokacin darkness, tana da kirki Please ko ba yanzu ba kada ka taba yarda wani abu ya rabaka da ita don ba zaka tab'a samun kamarta ba" kasa magana yayi yana jin tinah har ta gama suka yi hira ta bar gidan, ina zaune ya d'aga labulen ya watsa min takardun yana faɗin. "Idan ma asiri kike yiwa mutane tow ki daina domin wallahi xan miki ba dad'i....
*Ni jikar na tsalle kwad'o yace. inji Aunty Hadiza 🤣😂 Tafida baka jin magana wallahi asiri kuma dai!*
#500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
Paid book
14
Hadiye yawu nayi ina kallonshi, kafin na ce mishi. "Kayi hakuri idan kace ma kada na shiga gasar zan hakura da shi!" Wani wulakantaccen kallo ya zuba min yana me kara shigowa cikin dakin. "Da kiyi da kada ki yi daya ne a wurina ko a kwalar rigana, ke idan kin son ki tafi tsirara babu abinda ya dame ni." "Na gode!" Na fadi haka tunda na samu wannan damar nayi alkawarin zan yiwa Aliyu biyayya koda kuwa zan rasa rayuwata ne, don na kara gane wasu daman baka tab'a samunsu haka kawai sai ta wani dalili me karfi dalilin kuwa shine auren Tafida, don haka na yarda da cewa Allah yana tare da ni shine wannan damar yazo min, bayan fitar shi na kira Mamana na gaya mata abinda yake faruwa, Abinda ta fara tambayata. "Mijinki ya amince?" "Eh ya amince!" "Tow ki kira Babanshi ki gaya mishi sannan ki gayawa Babanki da Babanku Bulama!" "Tow Mama!" Haka kuwa nayi na gayawa Abba yayi min addu'a sosai, sannan na kira Baba Bulama na gaya mishi, ya tambaye ni Aliyu ya amince nace eh, sannan yayi min addu'a. Can na kira Babana sai da muka yi dogon hira har katina ya kare sai gashi ya kuma kirana. "Babana!" "Na'am Ummuna!" Ya fada yana murmushi. "Dama wani gasar girkin zamani ne aka saya min Form din shine na ce bari na gaya maka ayi min addu'a." "Masha Allah Mijinki ya amince?" "Eh ya amince!" "Tow ya za ayi shi zai na kai ki ko kece xaki na zuwa don nasan ke bakuwa ce a abuja!" "Eh gaskiya yana fita da wuri ni kuma ban san yadda xan na fita ba." "Tow shi kenan zan nime shi muyi magana!" "Tow Baba!" Haka muka yi sallama, bayan Isha ina zaune na ji ana buga kofar gidan, zuwa nayi na bude Sa'adiyya ce, ban yi mamaki ba na bude mata kofar ta shiga tana yatsina fuska. Ban ce mata kome ba, wurin karfe goma ya shigo gidan ina dakina, buga kofar yayi na tashi na buɗe. "Uban waye ya ce ki hada ni da wadancan tsofi ukun!" "Kayi hakuri na gaya musu ne amma ba zan ƙara ba." "Sakarya kawai!" Ya fara tijaran da ya saba, koda yake kwana biyu bai yi ba amma yau kamar jira yake Sa'adiyya ta dirko gidan, haka ya gama ina bashi hakuri yana kara tinzura karshe na makale jikin bango kamar zai dake ni, yana gamawa ya fita. "Ya Aliy!" "Sa'adi yaushe kika zo?" "Dazun nan man!" Washi gari Tina tazo ta amshi Form din ta ga ban cika ba, ware idanu tai tare da cewa. "Aliyos bai cika miki ba ne?" "Eh kin san yana busy!" Amsa tayi ta buɗe jakarta. "Amma naji kamar kina mura!" Na tambaye ta. "Eh jiya nasha ice cream ne!" "Bari na dafa miki ruwan zafi da yar farfesu!" "Amarya bar shi na koshi!" Ya fada tana kallon dakin Tafida da Sa'adiyya ta fito. "Wacece ita?" "Yar uwarsa ce daga Maiduguri!" Dauke kai tayi tana wani haɗe rai. Kitchen na nufa na hada mata kayan kamshi ma dafa mata shayi, sannan akwai sauran nama da yake sayowa na mata farfesu me ruwa ruwa. "Amarya ya kamata ace kina da babban frij, wanda zaki na ajiye kayan abinci. Ba sai kullum za a na girki ba!" "Tow Tina!" Na zauna, ta mika min takardan har ta cike wurin girki ne ta ce min. "Zaki dauki na gargajiya ne domin an fi samun na sa'a akanshi." "Duk wanda kika zab'a min zan amsa!" Ina jin motsin Sa'adiyya a kitchen, har ta gama abin da take ta fito ta wuce dakinshi, dama ya tafi aiki. Kitchen na shiga nayi mana shinkafa da miya sai salat. "Amarya zaki kashe ni da dad'i." Haka muka wuni da dare aka zo daukarta, ta tafi da takardan, weekend bata zo ba duk sai na damu domin tun ranar Alhamis juma'a asabar da lahadi bata zo ba, yammacin Lahadi ina zaune ya shigo dakin yana me tsayawa a kaina. "Ki saka kaya ina jiranki a waje! Kuma kada ki sake ki saka min burma-burman kaya." "Tow!" Na fada sannan na mike, kayana na duba babu wanda yayi yadda yake so, sai kayan dinner da aka min shi bubu ne na saka tare da daura zani akan rigar. Sannan na dauki dan kwalin na kafa dauri. Mayafi fari na saka da takalmi fari saboda lacce din fari ne tas, kwali da man baki na saka fuskana kuwa sama-sama na shafa mishi hoda, na fito. A parlour na same shi da Sa'adi, kwashewa da dariya tayi tana faɗin. "Yau an saka a cuci maza kenan! Don wannan boons din ba naki ba ne!" Yana jin mu bai ce kome ba, haka na tsaya kaina a sunkuye. Domin naga yana shan abu ne da itama shi take sha. Mikewa yayi yana faɗin. "Muje!" Haka na bi bayanshi, abin mamaki a harabar unguwar muka samu Mahmoud ya zo, yana idanunshi kur a kaina. Parking yayi a gefen motar Tafida ya fito yana kallona. "Man ina zaku?" "Kasan yar gidan Mr Kayemi Tina ita ce yau take birthday ta ce na zo mata da wannan abin!" Murmushi Mahmoud yayi ya ce mishi. "Ko na raka ku ne?" "Me zai hana sai ka tawo da Sa'adi!" "Ba dai a motatta ba, domin na tsani yarinyar nan bata da kamun kai!" Ya fada yana hade rai. "Please mana!" Ya fada yana nufar motarshi. "Na gaya miki gaskiya! Ke tauraruwa ce a cikin taurari, haskenki daban yake shi yasa zan biku na kare martabarki kada wasu , su kallar min ke!" Ya fada yana rike da mayafina, kwace mayafin nayi kafin Tafida ya juyo ya ganmu. "Man bari na shiga na mata magana."
Kin yarda nayi mu hada idanu, har na shiga motar, muka bar gidan yadda Tafida yayi ta min kashedi kada na je nayi rawan kai, abubuwa iri-iri babu wanda bai min ba.
**
Lokacin da Mahmoud ya shiga ya samu Sa'adiyya ta shiga dakin Ummu zata saka abu. Kamar ance ya d'aga labulen kawai ya ganta tana niman inda zata saka abin. "Da kuwa naci Ubanki, munafika fito kafin na takaki." Yadda ya hauro mata yasa tayi baya, ya amshe layyar ya jefa a toilet ya tura ruwa. "Yar iska kika sake gobe na same ki a gidan nan sai na baki mamaki, kuma ki shirya mu bi bayansu jaka kawai!" Haka ta fita jikinta a sanyaye, ta shirya suka fita, tasha zagi da harara. Har gidansu Tina.
Lokacin da muka isa ana yiwa Tina kwalliya, janyo ni tayi tana faɗin. "Itama ayi mata amarya ce!" Murmushi nayi kawai,"shine baki gaya min zaki yi bikin Birthday dinki ba!" "Amarya ba zan so kiyi aikin wahala ba!" Ta fada tana murmushi ana gama mata aka yi min kwalliyar dan daidai. Ba yawwa ba hayaniya, a tare muka fito bayan an dauke mu hotuna muka zo wurin Birthday dake mayafina yana kafadana. Idanun Mahmoud yana kaina, duk inda nayi yana bina da idanu. Sa'adiyya abin ya d'aga mata hankali musamman yadda Tina take hada ni da kawayenta, take gaya musu ai ni matar Aliyos ne, haka suka yi ta taya ni murna tare da bani labarin kirkinsa. Haka aka tashi taron wurin karfe goma sha daya, na gaji don ma ban yi sake Sallah ya kwace min ba, don da nace zan yi sallah sake kiran me kwalliyar tayi bayan na idar da sallah ta gyara min fuskana. A hanya muna dawowa yake gasa min magana. Ni dai ban kula shi ba, don barci nake ji. Ban san me ya hau kanshi ba, amma yadda yake gaya min magana yasa na kauda kaina kamar bana jin shi, Sa'adiyya da ta rigamu dawowa ita da Mahmoud suna parlour muka shigo. Daki na shige ban kalle su ba, na kwanta don na gaji sosai. Washi gari da sassafe naji motsin ana jan akwati. Ban fito ba sai sha daya gidan babu kowa na fito daga ni sai riga da wando na barci da na saka da asuba, na fere dankali na fara soya naji ana buga kofar gidan da kirana. "Amarya!" Da sauri ba saka hijab da yake jikin kofar kitchen na fito. "kin manta ne?" "Na gaji ne har nayi barci ." "Shirya mu tafi!" "Ban karya ba!" "No need zan miki takeaway!" Haka na shirya sannan na saka doguwar riga da mayafi na nad'e kaina, muka fita ita ce ta kai ni har inda zamu yi taro na kwana uku. Tana kai ni ciki tace zata kawo min abinci. Ta tafi ta cika alkawarinta, ana fitowa tana mika min abinci. "Kin san na makara muje na ajiye ki!" Haka ta kawo ni gida, "ki zo muci mana!" "A'a na gode!" Ta tafi ina shiga cikin gidan, hadiye yawu nayi domin Mahmoud na gani zaune ya zuba min idanu. Wuce shi nayi na nufi dakina, ina shiga na rufe kofar na zauna tare da fara cin abinci na. "Ummu Hadiyya! Ina son ki bani damar miki bayani yadda zaki fahimce ni, Ummu ina kaunarki ni bana son muyi kazamar alaka ki amince min na tsaya miki, Aliyu ya sake ki mu gina rayuwarmu na jima ina niman mace irinki." Idan gidan zai amsa tow na amsawa Mahmoud ya gama haukarshi ko waje wunin ranar ban fito ba, washi gari da safe ina fitowa na ganshi zaune daga shi sai gajeren wando, dakin na koma na zauna. Can ina zaune na ga abin bana kare bane zan tafi wurin taro na fito nayi abin karyawa haka ya zo ya tsaya a kaina yana ta min magana ban kula shi ba, abin da nayi niyya da ya sake yayi min wani shirme man gyada xan watsa mishi. Sai bai fara ba, har ya bar wurin na gama kome na shirya na fito zan tafi Tina ta zo muka tafi a bakinta najin Aliyu da shugaban kasa sun yi tafiya zuwa Morocco. Haka yasa na fahimci shi yasa Mahmoud yake damuna, kuma da alamu tafiyar ya sati guda ce, don haka tana kai ni nace mata. "Ni naga gidanku yafi kusa da nan, me zai hana kawai na dawo gidanku da zama kafin mu gama taron!" " Da gaske?" "Allah da gaske!" "Tow shi kenan!" Nayi haka ne domin gujewa sharrin shaidan, ana tashi muka dawo tare ta jira na kwashi kayana muka bar gidan, dana san gida daya muke kwana wallahi da ban zauna har haka ba, haka na koma gidansu Tina da zama ban tab'a ganin mutane masu mutuncinsu ba, sun girmama ni da mutuntatta ni, kannenta da Yayunta da matan yayunta kamar su goya ni, abinci kuwa dani ake girkawa Yarbawa karshe ne a girki sai suka ga nima ba a bar ni a baya ba, ai kuwa suka shiga cewa Ayawo a bude mana restaurants a garin nan, a wurin taron ma Ni daya ce yar arewa. Haka muka yi taron kafin muka fara zuwa girki, anan na ga Hajja yar Shehun Borno, ai kuwa ta ji dadi domin tana cikin alkalan gasar. Kowa na gabatar da kanshi nima na gabatar da kaina da inda na fito. Cikin jin dadi ta ce min. "kenan ke yar borno ce amma nasan yan borno turare aka sansu da shi, ba abinci ba." Cikin girmamawa na ce mata. "Dukka muna da shi turare da abinci!" Murmushi tayi tana mana fatan Alkhairi, tunda muka fara gasar girkin nan bana barci, ina kiran Mama tare da tambayarta, sallah dare kuwa na kara akan nada, girkin zai dauke mu kwana sha hudu. Ashe Mahmoud ya kira Tafida ya gaya mishi bana dawowa gida, da kamar zai ce ina ruwanshi sai yayi tsaki yace mishi. "Tana tare da Tina k zauna abinka kafin na dawo!" "Wallahi na zata wani wurin ta tafi!" Tsaki yayi yana faɗin. "Tow ina ruwana taje duk inda yayi mata ita ta sani ba ni ba." "Ban gane ba!" Kamar wanda aka tsira mishi allura ya fara magana, har da rantsuwa ko kato ya gani akan Ummu zai iya dauke kai don ba zai ji kome ba don baya kaunarta gara mutuwa sai dubu da zaman da yake da Ummu. "Tow ka sake ta mana tunda abin ya kai haka." "Ba zan sake ta ba domin Alhaji zai iya tsine min albarka. "Ita kuma bai dame ka ba idan ta bi wani namijin?" "Ita ta sani tunda yar talle ce ta saba da tsalle tsallensu da maza a waje kai ka dame ni!" Kashe wayar yayi murmushi Mahmoud yayi ya nufi dakin Ummu da ya ɓalla dazun, ya dauki bra dinta da pant, dinta ya runguma yana me sakawa a fuskarshi kamshin turaren miski yake shaka. "Kamar yadda kamshin nan yake Allah yasa kome na jikinki haka yake Aliyu na rantse da Allah sai na baka mamaki!"
Kwananmu tara Tina ta gaya min zai dawo ranar, daga wurin gasar gida ta kawo ni, ina shiga gida Babana ya kira ni yana tambayata ya nake da abinda nake yi, na gaya mishi akwai me kai ni, "ki turo account dinki zan turo miki zakkar da na cire ne na ware miki naki!" "Babana na gode in sha Allah zan turo!" Muna gamawa na tura mishi, ashe a can gida Maiduguri ana saka gasar mu bayan sallah isha, yan uwa da abokan arziki, kowa yana gani a tv NTA Maiduguri suna sakawa, wanda hajja ta dauki nauyin shi tare da Maggi star. Wasa wasa Yan uwa Aliyu abin bai musu dadi ba, domin gani suke ban cancanci shiga gasar ba, Shuwa kamar ta mutu don bakinciki, Abba kuwa ana isha yake dawowa yana me zama a jikin tv, yana kallon girke-girken.
Sai bayan Isha Aliyu ya shigo gidan, tunda na ce mishi. "Barka da hanya ka dawo lafiya?" "Da ban dawo ba zaki ganni?" "Ayi hakuri! Masifatu!" Inji Mahmoud yana shigowa cikin gidan, basu wuri nayi na koma kitchen, ina dafa jollop din taliya, ina gamawa na zuba a kula na barshi a kitchen din na shige dakina. Bayan ya huta ne ya fito ya samu Mahmoud ya dauki abinci ya baza a tire, har ta fara ci. "kai bana son iskanci, gidana ne zaka zo ka juye abinci kana ci sonka!" "Ai naga baka damu da girkin ta bane shi yasa na juye idan kana so Bismillah!" Ba musu ya sauka ya fara ci ko cokali bai dauka ba, haka suka cinye ya nufi kitchen ya dauki tukunyar ya juye sauran ya fito suka cinye. Washi gari na fito na kwaba fanke, na koma daki kafin karfe shida ya tashi na koma na fara soyawa ina gamawa na dama kunu na tafi wanka. Nasan Mahmoud baya nan, sai dai ina fitowa na samu an sha kudin saura kaɗan a kasan kofi, fanke kuwa na rantse da Allah daya aka bar min. Raina ya b'aci haka juya abincin nan aka juye tas yau kuma an kara min haka. Haka yasa ban ce kome ba na kira tinah na ce ta zo min da abinci don Allah. Da abincin tazo min muka wuce wurin gasar na karya a motarta.
A hankali na fahimci wannan abin da ake min ya fara yawa, daga ni sai Tafida a gidan bayan shi ko Mahmoud naga baya nan yazo da alamu ya tafi gida, kwatsam Ranar asabar da safe na gama soya kosai, na shiga daki na fito ko ya dauka wanka na shiga kawai na zo na samu ya zauna yana cin kosan da kunu sauri sauri yana gudun kada na kama shi, juywa nayi dakin na barshi ya ci. Yana gamawa na ji motsin ya bar gidan. Tun daga lokacin ban kara yin abu iya cikina ba, sai na yi dayawa amma bai gane ba idan nayi dayawa sai ya kwashe ya tafi da shi, ranar da muka gama gasarmu, da ranar wani kunu nayi wanda ake yi da shinkafar tuwo, madara kilo, kimba, kanunfari, citta, da manshanu da sugar. Domin a cikin kwanakin nan da kuma yi ni daya ce ban maimaita abinci ba, kuma yau da nayi wannan bakiɗaya hankalin Alkalan yayi kaina. Tunda na wanke shinkafar tuwo na zuba da ruwa me yawa, sannan na zuba kayan kamshi kafin na barci yayi ta nuna ina ganin ya nuna sosai na bude na kara dama shi, sannan na kara masa ruwan dumi ya sake. Na rufe shi kafin na dauko garin madaran na fara zubawa ina damawa, sai da ya hadu tas sannan na sauke na zuba sugar na juya shi, sannan na zuba a yan kananun bowl da cokali na zuba manshanu a kai ba jera inda kowa zai dauka. Tunda na gama na wanke kayan na koma gefe ina goge hannuna. A yau aka bamu damar magana tare da nuna mana inda zamu zauna, Alkalai na cin abincin mu, suna mana tambaya. Wani dan china da yake
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 17