dauka da "hello! Waye?" "Kiyi tunani Ummu Hadiyya me kyau ga dambuna ya kare waye zai min irin naki?" Kashe wayar aka yi, ya kira yaji wayar a kashe bakiɗaya. A can dakin kuwa yana jin motsin fitarshi ta farka tare da bin shi ta makale tana me saka kunnenta. Jin sunan Ummu abin ya bata mamaki, wannan wacce irin masifa ce haka? Tana Barka an rabu da bukar ashe an haifi habu. Kwafa tayi tana me barin jikin kofar ta kwanta karshe barcin da bata yi ba kenan har sai.da ya shigo a saninta shi din yana da bukatar mace a koda yaushe, amma sai ta ga tun barin Ummu Hadiyya gidan ya rage sosai asalima tana zuwa dakin zai dauki pillow ya shimfida bargo ya kwanta a kasa. Wannan abin ya mata ciwo ko yana mata ciwo kamar wacce tayi mishi wani abu bakiɗaya ya janye daga kulawar da yake bata. Dakyar barci yayi gaba da ita cikin takaici.
***
"Waye ya kiraki a wannan daren!" Kallon Mama nayi kafin nace mata. "Tafida!" Sannan na gyara kwanciyana. "Yaron nan yana ta kokarin ya ga kun daidaita amma kin ki ban san wani irin taurin kai yake damunki ba, amma ba xan daina gaya miki gaskiya ba domin kuwa shi ne gatan da zan miki." Kasa magana nayi ina kallon gefen da take kwance, a hankali naji alamar barci ya ɗauke ta.
Gyara kwanciya nayi ina son na tuna me yasa na rasa wanda zai tsaya min akan abinda Tafida yayi min? Me yasa Mama take niman juya min baya? Me nayi da zafi haka da kowa yake ganin kada na rabu da Tafida.
-
Sunana Ummu Hadiyya a sanina ni agola ce Mama ta auri Baba Alhaji Bulama bayan ta yaye ni. Alhaji Bulama yana da mata biyu da Mama uku Hajiya Balkisu ita ce uwar gida kuma me manyan Yara dakinta tana da yara biyar, Ahmad Bakura yana aiki a abuja yana da mata daya da Yara biyu, sai Muhammad sani Kawu Gwani sai Salman Bamai, sai Safina wacce ake kira Taima.....
N500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
*Assalamualaikum don Allah kada a tura payment ta GTBANK babu network zan saka Opay dina*
Paid book
08
Sai Saratu wacce ake kira Kwaise, ita ce autarsu. A gaban Hajiya Balkisu akwai Yar kaninta wanda ya rasu ya barta wato Mahira Hajiya Balkisu wato Ummi ita ta fito ƙabilar barebari ce wato kanuri kamar Hajiya Bulama Hajiya Balkisu tana da zafin kishi shi yasa kome nata ya banbanta da na kowa hatta Yaranta ba yarda su tafi . Sai Hajiya Karima wacce muke kiranta Umma, Yaranta uku duk mata ne , kuma kowacce tana gidan, Sadika, ita ce babba yaranta hudu, sai Asiyah tana da yara biyu sai Azizah ita ce har yau Allah bai bata haihuwa ba, dukkansu ukun nan suna aure cikin manyan ahali.
Mama ce matar Baba ta uku, lokacin da aurenta ya mutu ta bar garinsu tazo wurin Kanin Mahaifin ta zauna. Mama yar kabilar Baburawa ce. Anyiwa Mama auren dole ne da Babana wanda ya kasance malamin makarantan secondry school, Babana ya so Mama amma saboda kiyayar da take mishi taki zama, haka yasa dole aka raba auren lokacin ban wuce wata goma a duniya ba, shine ta dawo garin Maiduguri wurin Kanin Babanta da zama, matar kanin Babanta Mama Yahanasu gidanta cike yake da Jama'a kasancewarta tana sana'ar sayar da abinci a bakin kasuwar Monday market, wuni ake ana shiga da fita. Anan suka hadu da Alhaji Bulama, wanda ya nuna soyayyarshi a gareta kuma ba a wani sha wahala ba ta amince mishi.
Manya suka shiga cikin maganar, haka aka yi daurin auren ta tare, kasancewar ta san dadin niman kudi bata yarda ta aure shi ba sai da ta ce mishi zata fara sana'arta, shi kuma a bangaren Alhaji Bulama abin da ya kara bashi sha'awa da Mama ta gama secondry school, haka yasa shi kara bata kwarin gwiwa ta fida poly tayi diploma, wanda ta fara shi tana da cikin Ummu Kulsum, har aka haifeta ni a lokacin ina wurin Hajiya Yahanasu, duk da ban wani girma sosai ba, sai dai ina da matukar wayo a lokacin, bayan shekaru biyar a lokacin ina da shekara bakwai a duniya na koma gaban Mama, sakamakon rasuwar Hajiya Yahanasu, da Babana yaso amsata amma fir taki amincewa haka yasa saboda kaunar da yake mata ya hakura na zauna a hannunta, Mama uwa ce da ta tsaya min a ko ina, duk da kuwa ina shan gori a wurin yaran gidan amma haka bai hanata nuna musu ina da gata ba, ban san babana ba amma a yadda nake jin tana bada labarin Babana yana da rufin asiri. Har tana fadawa mutane yadda duk bayan wata shida yake min aike ita ce ta hana saboda bata son kome daga gare shi.
Duk yaran gidanmu suna da ilmi. Hatta kannena suna da kokari idan ka cire ni, duk yadda naso nayi karatu domin Mama dai ba tayan baya ba ce a ilimi, sannan tana aiki da local government. A lokacin Mama ta fara deciding fara yin abincin sayarwa saboda ta fara amma ta ajiye sakamakon aikinta, kuma tana sayan kayan abinci tana rabawa ma'aikata karshen wata su bata kudinta. Tunda muka fara abin karyawa na sayarwa idan muka tashi tun 4:30am muka fara aiki ba zamu koma.ba sai karfe sha daya na dare sakamakon yadda ake wuni sayar da abinci,ana sauke abinci karfe shida na safe, kafin karfe bakwai na safe ya kare an daura na rana. Ni zan tafi makaranta ita Mama aiki. Sannan akwai masu mana aikin wake-wake da daura abincin rana saboda zan dawo, ina da shekaru goma a duniya Mama ta sake min ragamar girkin abincin sayarwa tare da bani damar na cigaba da kula da kome tana lissafi, ba don kome ba sai yadda ta fahimci ƙwaƙwalwata bata iya gane kome sai sarrafa tukunya da kayan abinci, Mama tayi kokarin nayi karatu amma Allah ya gani bana ja bana iya kome ban san kome ba idan ba girki ba, tayi min nasiha har dukana sai da tayi amma ban fahimci kome ba. Alhaji Bulama da kanshi ya dakatar da ita ya ce ta yiwu bani da wani abin da zan amfana ne a can, sai ta saka ni a high Islam, na fara gara shi kan ba laifi na maida hankali sosai. Sannan a unguwar mu ina zuwa tahafiz kada ku sha mamaki yadda nake iya karatun Alqur'ani amma boko kamar zan mutu ko hala ban da rabo ne cikinshi. Mu hudu Mama ta haifa Ni ce babba sai Ummu Kulsum, sai Ummu Rumana, sai Ahmad domin Ahmad biyu ne a gidan mu, Baba Bulama yana da rufin asiri sosai, domin babu abin matanshi da yara suka nima suka rasa, Ummi wato Hajiya Balkisu turare take sayarwa shine sana'arta Umma kuwa yar zaman banza ce, sai gulma bata da aikin.
Akwai wani abu da nake kara jin dadi da tausayinsa a raina farkon dawowata gidan yadda Yaran gidan suka tsane ni, idan na cire Sadika wacce ta girme ni sosai, amma Asiya,Azizah, Taima, duk sa'o'i muje sai Yaran riko da Ummi da Kuma suke daukowa, saboda ni da Baba ya bar Mama ta dauko ni. Suna irin na cin mutuncin da cin fuska babu wanda ba a saka min a gidan ba, an saka min yar duna jikar masu daddawa, Mama ta tsaya kai da fata ita da Baba da Kawu Gwani wanda Allah ya haɗa jininmu, suka kashe sunan. Bayan nan aka sake saka min African queen, Kai har sai da sunan ya fita waje Baba ya samu me unguwarmu aka kashe sunan, sai da aka saka min suna yafi kala goma Mama da Baba suna kashewa domin akwia wani yaro me suna Farouk da ya saka min cinnaka baki san na gida ba, sunan har makarantarmu ya tafi, Mama ta wanke kafarta har gidan iyayen Yaron ta ce bata yarda ba. Shine aka dawo aka saka min Baby. Kun san dalilin, kasancewata yar karama domin bani da girma sannan ni baka ce ina da dan auki sakamakon yadda Mama take fada ai ni bakwaini ce shi yasa nake da karamin jiki.
A lokacin da na cika shekaru goma sha biyar, ina dab da gama high islam. A wannan lokacin Baba ya bude gadon sayar da Abinci ya ce min yaga ina da kokari na cigaba da sana'a. Haka na cigaba har muka yi sauka,.inda na kara kankaro mutunciwa Mama, domin idan ka cire mazan gidan duk sun sauke Matan ne sai a hankali domin suna da shegen kyau fa farin fata. Wannan kyan nasu yasa suke min izgilanci bai taɓa damuna ba, domin bani nayi kaina ba, abu daya na sani duk da wannan kyan nasu kafin su saka suturar da nake sakawa sai an shekara, ba wai ko lokacin bikin sallah ba a'a, akwai wata bayarabiya da take zuwa daga Lagos, wurin aikin Mama take duk karshen wata uku tana zuwa ta kawo kayan sayarwa daga kwatano haka yasa Mama take saya mana kaya, Mama har Kano wani lokaci tana zuwa ta sayo mana kaya ta ajiye a gidan Hajiya Amina sai dare yayi ta saka ni da su Ummu Kulsum da Ummu Rooman mu je mu kwaso kayan, wani ma daga can muke kaiwa wurin tela wata yar kalaba me suna Maman Chioma, haka yasa duk iskancin yan matan suke d'aga min kafa, kuma babu yadda suka iya dani, koda nazo na gama high Islam na kara rungumar, gashi mun shaku da kawu gwani wanda haka yasa aka.fara zargin soyayya muke.
A wurin aikinsu aka kawo tallar wani makarantar girki, kafin ya dawo ya saya min Form ya cika min sannan ya kawowa Mama ta gani, ban ji dadi ba amma kuma ganin shine ya kawo min na mai da hankali na shiga makarantar, tabbas akwai inda zaka rena kanka, domin ina shiga makarantar na hadin gwiwa wasu mutanen kasar waje ne, larabawa da turawa, sai Hajja Yaana wacce ta bukaci so tayata budewa, ita din Yar shehun Borno ce. Haka yasa muka mai da hankalinmu. Shekara daya muka yi akan girki amma kafin na gama na samu satifiket a bangarori na makarantar da dama, saboda kwazona da mai da hankali akan abinda ya shafe ni, haka yasa muna gamawa na kara mai da hankali na rike baiwata gam.
Ana haka aka yi bikin Bakura da Sadika. Muka sha biki sosai amma sai da aka yi ta girma domin kawai Baba ya dauki hidimar abinci ya bamu, karshe sai da Mama ta dauki kayan abincin ta maidawa Baba case ya mutu, sai dai Baba da yayi walima mune muka hada mishi kome sannan muka samu kanmu. Haka rayuwar gidan yake. A hankali aka yi ta bikin yan matan gidan har aka zo ɓangarenmu. A lokacin ne aka yi bikin Ummu Kulsum da Ummu Rooman, hankalin Mama ya tashi domin lokacin da Baba yayi maganar hada ni da kawu gwani hankalin Hajiya Balkisu ya tashi inda tace ko a fada auren ko ta tsine mishi albarka, haka ya bar ni ya auri wata yarinya Mariya, bayan nan aka yi auren Salman Bamai, babu kowa sai yayan rikon Umma da Ummi.
Nasan Mama tana cikin damuwa amma Allah ya gani ba ni ce na hana kaina miji ba, domin ana haka nayi ta samu manema sai sun zo zasu gudu, wani ma sai anyi maganar aure rimi-rimi har manyan sun shiga an kawo sadaki za a fasa, sau uku ana haka kawai sai na daina bawa kowa fuska. Akwai wani taro da aka yi a unguwarmu, wanda ya janyo aka yi ta zuwa sayan abincin, maza ne guda uku suka shigo shagon abincin nasan dayan yana yawan sayan abinci da safe. "Barka dai Hajiya kwana biyu bana ganinka!" "Aunty Baby nayi tafiya ne!" Dariya nayi ina faɗin. "Har da kai a cikin masu kirana aunty!" "Eh mana!" Ya fada cikin dariya. "Me za a zuba maka!" "Shinkafa da wake, da soyayyen kifi ayi min hadin kullum dai!" Shinkafa da wake yake saya, sai salat da kifi, sai tsimi. Haka kullum yake saya kuma za ayi mishi takeaway guda ɗaya. "Jamilu anan nake cika cikina!" "Hmm na ga alama!" Ya fada yana bin inda nake da kallo. "Me za a saka maka ka fada?" "Idan akwai tuwon alkama miyar kuka! Sai mana wani iri suke da shi!" "Aunty Baby wani irin nama kuke da shi!" "Akwai na kaza, na rago da na saniya!" " A saka min kirjin kaza!" "Tow!" Shigowa Uwani tayi tana faɗin. "Aunty Baby an gama dan waken da alalen!" "Tow zo ki mika musu, na dauko." Shigowa tayi ta mika musu na shiga cikin gidan na kwaso kayan na kawo. Ina kawowa kuwa aka.fara shigowa ana karban abinci, Mudan yana ta zuwa yana kaiwa kasuwa musamman wadanda suka yi booking. " "Alawan anan suke abincin ne?" "A cikin gidan nan mana, gidansu ne kuma ko yaushe ka zo zaka samu abinci da dumi. Babu abinda basu sayarwa domin local food ne amma kuma luxury restaurant ne da sai ka jijjiga aljuhunka!" Ya fada yana shan ruwan tsimin. "Aunty Baby a bani takeaway na ga kudin abincin!" Ya mika mata kuɗin su bakidaya.
"Na gode sosai!" Na saka mishi wanda yayi guzirinsa, haka rayuwata take tafiya. Sannan a gefe guda wannan Jamilun a nan yake karyawa, abincin rana da na yamma da Uwani take yi. Wasa gaske sai gashi yana niman shigo min da zancen soyayya. Duk yadda na kaucewa soyayyarshi haka ya takura min, ban san ya aka yi ba wata juma'a bayan an sako masallaci ina ta fama da almajirai da wani ya saya musu abinci ina raba musu, dan gaba da mu, ana daurin aure ne. Unguwar an cika sannan wasu na ta shigowa na sayan abinci, sannan duk ranar juma'a an fi yin abinci dayawa saboda sadaka. Sannan an fi cika gaskiya. Kaina yayi zafi ina fama da jama'a. "Assalamualaikum ina niman Aunty Baby!" "Na'am gani nan!" Na d'ago ina kallonta. "Jidda ki fito mana da shegiya karuwa!" Kallon wacce aka kira da jidda nayi na ce Mata. "Ki ce musu tayi hakuri zuwa gobe yau ina da jama'a ne!" Ihu ta wajen tayi ta fara zage zage da cin mutuncina, ban kulata ba sai da na ga haukar tayi yawa na fito an cika ga yan aurin aure sun fito ana ta tsayawa. Zakiya da bata da hakuri ta nufe su na riko hannunta. "Uwani ita ɗaya ce kyale su!" "Baiwar Allah ban san wacece ke ba, amma kiyi hakuri idan na b'ata miiki rai." Na juya riko rigana tayi ta baya. Na juya zan kwashe da mari sai kuma na fasa musamman yadda na ga an cika a wurin ana bata rashin gaskiya. "idan akan Alhaji Jamilu ne ki je bana bukatar shi, domin bai isa da ke kuma kin nunawa duniya cewa ke mahaukaciya ce, wacce ta fi karfin Mijinta. Ban tab'a rigima da kowa ba a unguwar nan tun tashina, idan don shi ne ba zaki mai da ni karya yar uwarki ba, ki je da Mijinki Allah ya baku zaman lafiya!"
Na juya ina me komawa shago, rintsa idanuna nayi,ina kallon mutumin a cikin idanuna wanda girmanshi da kwarjininsa ya hana ni marinta, "Malam Inuwa wacce yarinyar nan?" "Agolan Bulama ce." "Amma tana da tarbiyya sosai!" "Ai don ma baka zauna da ita ba ne, yarinya ce matuƙar hankali da sanin ya kamata." "Hmm ko ban zauna da ita ba zan bada labarin haka a gaba, yadda ta d'aga hannu zata mare ta kallonta nayi ta sauke hannun. Irin wannan yarinyar nake ta nimawa Tafida wacce ta san idanun da darajar na gaba, Alhamdulillahi na samo mishi ita."
Kwana biyu a tsakanin muna cin abincin dare aka kira ni wai Jamilu yana kirana, na san ina son nayi aure duk da ba wani jimawa nayi kawai hankalin Mama da yake tashi ne yasa nake ganin gara nayi auren, tunda na fita yake bani hakuri amma ban ce mishi kome ba,.yana gamawa na ce mishi. "Kayi hakuri kawai, Allah ya baka wacce ta fini." Na juya na koma gida, ni a zatona zai bar ni ne a'a haka ya cigaba da zuwa shigona. Bana kula shi abinci yake zuwa ya saya ya tafi. Bayan kamar wata biyu ya daina daga nan na sakawa raina hakuri babu amfanin saka kaina hakuri da mai da kome ba kome ba, duka-duka shekarunta ashirin da biyar ne zuwa da shida kawai ganin kannena duk sun yi aure yasa Mama take cikin damuwa. A duk shekara akwai wani Alhaji Mu'azu yana daukar nauyin girka abincin bude baki da na asuba ana rabawa sadaka. Sai da ya rage wata daya za fara azumi Allah ya mishi rasuwa, a wurin rasuwa mabukata ke ta kukan rashin da aka musu, bayan anyi jana'izar shi wasu daga cikin Yaranshi suka dauki nauyin abincin kamar yadda Babansu yake yi, bayan sun gama kome da aka share makoki suka ce sun fasa. Domin basu gayawa mana sun fasa ba sai da azumi ya rage saura sati biyu a lokacin yake bada kudin kayan abincin wata guda. Abin ya dame ni sosai domin raina yayi masifar b'aci, ana cikin wannan yanayin aka ce an samu wani ya dauki nauyin abincin. Kuma yazo yana wurin Baba. Sai a lokacin Mama take ta zolayata. "Ummu ina zaki kai son kuɗi ne haka?" "Allah Mama ba wai don kudin da nake samu ba ne kawai sadakar yana da amfani. Sannan ina shan addu'a a wurin Mutane." "Allah yasa mu dace!" "Amin nace mata!" "Hadiza!" Muka tsinkayo muryan Baba yana kiranta, mikewa tayi ta fita can ta kuma dawowa suka fita da shi. Koda ta dawo ban kuma bin ta kanta ba, sai dai na ga ta fita zuwa gidan Mama Amina. Ban san me ya faru ba na ga dai sun dawo tare suka tasani a daki ana ta min wani irin bayani da ban gane kanshi ba. Ni lissafi idan ba na abinci ba ai gani nake kamar bata lokaci ne. Ni dai washi gari na shiga kasuwa nayi sayayya sosai sannan na dawo muka ci aiki kamar ba gobe.
Har ana gobe za a fara azumi bamu daina aikin ba, da yamma muna busar waje aka shigo mana da nama, wai Alhaji da ya dauki nauyin abincin azumi ne ya turo da namar, ni dai haka muka gyara aka saka a firji, washi gari aka fara azumi duk fadin duniya muka yi kunu da kosai, sai shinkafa da mita wanda yaji nama. Idan aka gama muna sakawa makota da mutanen gidanmu, duk da Mama ta gaya min nayi harkan gabana kada na damu da kowa nayi abin da na ga xan iya shi yasa ban tab'a kallon yan gidan mu a cikin rayuwata ba. Duniyata da Uwata da kannena sune a gabana domin ko lokacin da kanina Ahmad ya samu scholarship ba karamin artabu aka yi ba wai Baba yana fifita yan dakinmu. Haka ya zuba musu ido. Ahmad ya tashi a tsakaninmu duk abinda ya gani na hidimar gida da kome sai ya kira ya gaya min sannan ta tura min ta facebook din Uwani domin ni dai irin wannan haukar bai dame ni ba, sai daga baya wani zuwan shi hutu ya zo min da waya waya. Anan yake turo min da kayan kitchen mu kuma da mama muna tura mishi kudi, idan ya saya dayawa sai ta turo min ra cargo. Idan aka kawo gidan Hajiya Amina muke kaiwa tana da extra daki da take zuba min shirgina. Hatta kayan gado a can ya saya min aka kawo min. Sannan a gidanmu ana ganin duk wahalar da nake yi ba mamaki idan bikina ya tashi nauyin zamu daurawa Baba shi yasa ake yawan samun rigima akai na. Azumi yana kawai goma da safe na je gaida Baba yake gaya min. "Hajiyar tuwo da miya, bayan tarawi akwai bakon da zaki yi don Allah a tsaya a mutunta shi kamar yadda na san ki da halin ƙarammaci!"
"In sha Allah Baba!" Daga nan na dawo daki ko Mama ban gayawa ba, haka muka yi ta aiki bani da kuzari, bayan ana sha ruwa ina kwance yaro ya shigo . "Aunty Baby ana sallama da ke!" "Tow gani nan zuwa!" Na fada ina kwance. "Tashi ki je mana!" "Tow Mama!" Ma fada ina jin damuwa, haka na shirya na fita akan zan musu iso zuwa parlourn baki. Ina fita na hango su a jikin Motarsu, domin nace haka ne saboda dayannsu da ma gani cikin motar karasawa nayi zan musu sallama daya ya ce min. "Kanwata don Allah ki shiga gidan can ki kira mana Ummu Hadiyya!" Sai naji na diririce, baki na yana rawa na ce musu. "Ai ai ni ce!" Yana latsa waya ne bai san lokacin da ya d'aga kai yana kallona ba. Karewa kunna torching wayar yayi yana haska ni daga kasa har sama kafin suka kwashe da dariya, su biyu shi wanda yayi min magana bai yi dariya ba, sai cewa yake. "Meye haka Tafida Mahmoud Meye na biye shi kuna dariya." Idanuna ne suka cika da kwalla san lokacin da hawaye ya zubo min ba. Ina tsaye sai dariya suka tare da faɗin. "Wai Tafida kayi kamuwa wai ina ruwan kashi da rai! Ka ga hancinta kuwa ina ruwan mitsil!" Wani irin kuka ne ya zo min. Har jikina yana rawa, na juya xan tafi shi wanda ya haska ni ya ce min. "ke Ummu kike? Tow ki gayawa Mutumin da ya zo gidanku idan ya sake zuwa ki ce ni tafida ban miki ba." "Dalla me yasa kake yin haka ne? Mahaifinka ne fa kake cewa mutumin da yazo kamar wani sa'anka!" "Deen babu ruwanka da ni, ya ga Yan mata kalar gari a hada ni da wata kucaka wacce bata da bambancin da yar kauye. Idan kai haka ka shirya rayuwarka ni tawa da banbanci....
#500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
Paid book
09
"Kyale shi Tafida idan kana niman bagidaje ka samu Deen ai magana ya ƙare, banza ko shi aka hada da wannan me magana busashen kifi ba yarda zai yi ba, don Allah duba ta kamar wacce aka gama rabon halitta aka manta da ita sai daga baya aka yi karo-karo..." Bangaje kafadarshi mutumin da yake musu fada yayi yana faɗin. "Sannu Ubangiji da ya iya tsara halittar kowa!" "Kada dai ka fita musulunci don na lura ba Tafida aka turo ganin yar baby ba kai ne" ya kwashe da dariya, yana.nuna Deen din. "Kanwata" ko sauraronsu ban yi ba na nufi gidan a zaune na durkusa na fashe da wani irin kuka, na kai minti ashirin a wurin kafin na mike zuwa cikin gida sai da na wanke fuskana, sannan na shiga dakin Mama na ce mata. "Na dawo Mama" na fada zan fita daga dakin. "Ya kuka yi?" Na ji ta tambaye ni. Bakina yana rawa dake ban saba mata musu ba na ce mata. "Allah yasa haka shine mafi alkhairi!" "Alhamdulillahi Ubangiji ya tabbatar da alkhairi." Juyawa nayi zan fita ta ce min. "Ummu Hadiyya Yaron yayi miki?" A hankali na kara juyawa hawaye na zuba min. Na ce mata "hm!" "Ki kwantar da hankalinki in sha Allah lokaci yayi da zaki tafi dakinki,masu ganin ba zaki yi aure ba su sha mamaki." Hawaye ne ya kara zubo min Mama bata damu da nawa damuwar ba bukatattar nayi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 17