Share this page
rufa maka, ta boyewa duniya waye kai ta kuma maida ka mutum sama da kasa, don Allah ko ba don ita ba ko don albarkacin Yaranka ka girmama lamarinta, ba ina gaya maka haka don akwai wani abu ba, kai mutum ne da yayi approaching siyasa yanxu kada ayi amfani da abinda ka aikata akanta ayi kokarin b'ata maka siyasar ka." "Nagode sosai Deen in sha Allah zan kiyaye kuma ina son idan na samu lokaci zamu je gidansu." Murmushi Deen yayi ya ce mishi. "Sai da safe!" Daga haka Aliyu ya fito a motar ya cewa Security din. "Ku Kai shi gida!" "Yes sir!" Suka fada tare da bin motar Deen. A hankali yake takawa jikinshi na matukar mishi ciwo, ya shiga har cikin gidan ya samu babu kowa bangarenshi ya nufa ya samu Sa'adiyya tana zaune waya a hannunta, sanye take cikin kyakkyawar shigar kayan barci. Sau daya ya kalleta sannan ya dauke kai kamar bai dangata ba. "Ya Tafida!" Kallonta yayi kafin ya ce mata. "Au kina nan ne ashe?" "Zaman jiranka nake?" "Ni kuma? Ai da kin kwanta abinki!" "Wani irin kwanta na gama shirin na tayaka murnan samu nasarar zama Gwanma kace nayi barci." Yadda take surutu ba karamin haushi yake bashi ba, Sa'adiyya ita ce irin choice dinsa amma yawan maganarta yasa yake jin babu dad'i akanta ta bude baki zata yi magana ya ce mata. "Please na gaji hutawa zan yi!" Ya wuce dakinsa wanda yake kusa da na Ummu Hadiyya, sai yanzu yaji bakiɗaya kome ya tsaya mishi. Gabanshi ya shiga faduwa da gaske Ummu Hadiyya tafiya tayi? Kurawa dakinta idanun yayi sannan ta wuce dakinsa, duk yadda yaso ya samu hutu ya kasa dole dakin Hadiyya ya dawo ya kwanta. Kamshin turarenta da yake cike a dakin kamar yanzu ta saka ya sashi lumshe idanu. Yana kwance a wurin har aka kira sallah asuba, dakyar ya tashi yayi sallah anan ya baje bai farka ba sai wurin karfe daya na rana. Shima kiran sallah azhar ya farka. Ban dakinta ya nufa yayi wanka sannan ya dauro babban towel dinta. Ya nufi waje sake da baki Sa'adiyya tayi da take waya da kawarta ganinnshi daure da Towel din Hadiyya, bata san lokacin da ta kashe wayar hannunta ba. "Tafida meye haka? Ko tsari babu." Banza yayi mata ya wuce dakinsa, tana biyo bayanshi ya ce mata ya ce mata "Get out!" Juyawa tayi babu shiri, tasan ba karamin aiki bane ya maketa kamar zata yi kuka ta kira Uwarta. "Ammi anya kuwa mun samu Tadda yadda muke so kuwa?" Ta fada kwalla na cika mata idanu. "Kul ki sake fadar haka ki zo muyi maganar mu biyu ban da waya." Kashe wayar tayi tana jin wani zafi da kishin Tafida a ranta, bata gaya masa ba ta shirya ta nufi cikin gidan. Shi kan yasan abincin gidan tunda Ummu ta bar gidan shi kenan ta kare mishi. Don haka ya nufi bangaren Inna sanye yake da gezner skyblue shaddar har wani sheki take takalmin kafarshi hafcove ne na kamfanin Dolce de Gabbana, sai hular da ya murza akanshi tangaran ce tayi bala'in mishi kyau. Ta babbar kofar gidan ya shiga cikin gidan, kamshin turarensa ya sanarda yan gidan da masu aikin gidan ga Tafida nan ya shigo, wani uwar gud'a da Mama indo ta buga yasa shi sake fuskar shi. Ta shiga mishi kirari. "Mama indo bakya gajiya ne?" Dariya tayi tana faɗin. "an gaida Uban Yan biyu, Uban Mutanen Borno. " Hannu ya saka aljuhunsa bai san iya adadin abin da ya ciro ba ya mika mata, ya wuce sai godiya take. Yana barin wurinsu ya haɗe rai kamar bashi ba, ya nufi bangaren Abbanshi. Da sallama ya shiga farlour ya samu Yayunsa maza suna zaune a kasa Abbansu yana kan kujera. Cikin nutsuwa ya zauna bayan yayi sallama. "Ina kwana Abba!" "Lafiya lau, ya aka ji da Jama'a?" "Alhamdulillahi!" Ya fada yana sosa giransa ya kalli Yayunsa cikin dan sake fuska. "Ina kwana ya Abubakar? Ina kwana Ya Umar!" "Lafiya lau Mai girma gwamna!" Murmushi yayi suka su bakiɗayansu. "Aliyu!" Alhaji Muhammad Jadda ya kira sunansa"Na'am Abba!" "Jiya Allah ya nufa an rantsar da kai a matsayin Gwamnan jihar Borno ko?" Cikin nutsuwa ya gyara zaman shi. "Eh Abba." "Masha Allah!" Abban ya furta a hankali, sannan ya ce mishi. "Nasihata gare ka ka ji tsoron Allah, ka tuna abun da ka dauka na kamar matsayin senata ba ne a baya, ba matsayin wakilin shugaban kasa ba ne, Aliyu ka tuna nauyi ne na al'ummar jahar Borno bakiɗaya, ya zaka ji idan Allah ya tsayar da kai karkashin alarshinsa yana tambayarka shin ka sauke nauyin da ya daura maka?" Sake sunkuyar da kai yayi yana jin wani irin yanayi yana rab'arshi. "Aliyu ni mutum ne da nayi aikin gwamnati tun daga matakin karamar hukuma har zuwa matakin federal nayi gwagwarmayar da yan boko da yan siyasa, kuma an waye da ni lafiya Aliyu kada ka shiga rigar gwamnati ta yi abinda zai saka ni jin kunyar kaina da a Mutanen da suka yarda da ni! Aliyu shugabanci yana da matukar wahala, na rike shugabancin jami'o'in kasar nan, na rike shugaban jami'a, na rike shugabancin hukumar zab'e, na zama me baiwa shugaban kasa shawara, nayi aiki da ofishin jakadanci, Alhamdulillahi duk wannan aikin da nayi ban tab'a dukiyar gwamnati da na Al'umma ba, Aliyu kada ka sake wani ya tab'a dukiyar al'umma da saninka ba tare da ka janye shi a tafiyar ka ba. Aliyu zuwa yanzu zaka ga masoya da makiya ka tuna da abokan da kuka tashi tun Yaranta kada duniya ta sa ka manta da su. A cikin hakkinka kayi kyauta kayi sadaka kada ka tab'a hakkin Al'umma, kada ka yarda wani ya baka shawarar gina kanka domin masifa ce idan kayi hakuri, wannan albashin da ake biyanka ya ishe ka kai da iyalinka da sauran dangi. Aliyu yan uwanka da sauran dangi kada don ka samu duniya ka manta da su, Aliyu kada don ka zama wani abu ka manta da kamsuna salawati, babu babban tashin hankali kamar kayi ta wasa da Allah, domin daga nan ne ake fahimtar waye mutum, Aliyu ka rike Allah cikin lamarin ka Allah zai tsaya maka kana nan ko baka nan, babu wanda ya isa cutar da kai face Allah ya rubuta a kaddaranka! Aliyu bakiɗaya shekarunka Arba'in ne cif a duniya kada ka yarda ka lalata alakarka da Allah, domin shine abu mafi muni da tashin hankali. Abubakar Umar ku zama shaidana ba bawa Aliyu Shawara akan rayuwa da mulki, Allah kana ganin na sauke nauyin da yake kaina. Duk abinda yayi na sauke nawa, saura shi ya sauke nauyin da Allah ya daura mishi, Allah ta tayaka riko, ka ga dai yadda kuka yi da Alhaji Mansur Goza!" Yayunsa ma suka mishi nasiha kafin suka shiga taya shi murnar samun karuwa da yayi na haihuwar da aka mishi, abinci aka kawo mishi daga ɓangaren Inna. Anan ya ci yana faɗin. "Gaskiya Inna tayi kokari." "Yawwa ya batun suna ne kayiwa Yaran suna ne?" Gabanshi ne ya fadi yana kallon Abbanshi. "Ban yi musu suna ba, rabona da su tun jiya." Ya zaci fada daga Abbanshi sai ya ga akasin haka ya nuna ma bai damu ba. "Yaushe zamu je a gansu? Ko zasu dawo ne?" Umar ya tambaye shi, "Hmm ban sani ba ko zata zo ayi suna anan ko a can zata yi sunan." "Abba baka ce kome ba?" Inji Ya Abubakar, "da aka yi me?" Ya tambaye su, "Akan matar Tafida, za ayi sunan ne nan ko a can?" "Ya je ya same ta a can su shawararsu." Shiru Tafida yayi domin ya fara shakkar Abbansu nan, don haka ya mike jiki a sanyaye ta nufi bangaren Inna ya shiga ya gaida ita tana karyawa Ita da Yar uwarta. "Tafida kin kira Yaron nan Hadiyya?" Zama yayi yana kallon Hajja Ganaah ya ce mata. "Ban kira ta ba!" "Baki kira Yaron nan Hadiyya ba? Anya Tafida kina tsoron haduwarki da Allah Yaron nan ya haifa miki Yara biyu shi ne ba zaki kira shi amma Tafida zaki ci mutum har buzunsa." Gajiya yayi da maganar Hajja Ganaah ga Inna taki cewa Uffan, haka ya ƙara saka shi cikin tashin. Muryan Deen yaji yana dariya a tsakar gida Hajiya Kaltuma tana faɗin. "Yanzu fa kuna tarewa a government house ba zamu kara ganin ku ba, sai an cika wasu takardu da sharuddan ko?" Dariya yayi ya ce mata. "Baba ina ba muda inda yafi nan, don haka ki kwantar da hankalinki. Muna nan fa babu inda yallabai zai koma." "Masha Allah, sai gashi an samu karuwa bana nan wallahi daren jiya na dawo!" "Ba kome Allah ya raya mana su tafarkin addinin Muslunci." "Naji ance ya shigo cikin gidan nan ko?" "Eh!" Hajiya Kaltuma Amarya Abbansu ce kafin ita akwai Hajiya Hawwa tana nan itace Uwargidan Alhaji Muhammad Jadda, sai dai dukkanninsu Mahaifiyarsu Tafida ita ce Babba amma aka samu rabuwa, tana Njamaina na kasar Chadi. "Inna baki ce kome ba?" Harara ta watsa mishi ta ce mishi. "Ke Tafida ki fita idanuna na rufe wallahi kika sake raina ya b'aci sai na miki shegen duka." "Assalamualaikum! Dama nasan za ayi haka kazo wurin uwargida sarautar mata ne?" "Hmm!" Ya fada yana mikewa ya ce . "Muje ka kai ni gidansu wancan yarinyar!" "Wacce kenan?" A hazuke ya dannawa Deen zagi. "Bana son kutma uba, Black gidansu zaka kai ni!" "Ai kuwa ban san hanyar gidansu ba!" A fusace ya sa kai zai fita Deen ya riko shi. "Kada ka sake ka fita wani ya kai ka gidansu Ummu a wannan lokacin, ka san waye kai yanzu? Ya kamata ka iyawa kanka haba don Allah, wai me Ummu ta tsare maka ne?" Buge hannu Deen yayi yana faɗin. "Zanci ubanka wallahi xan maka rashin mutunci ni zata hada da iyayena?" Ya fada da karfi, "matsalarka kenan baka da hakuri, kowa ya raina matarka saboda a gaban kowa zaka ci zarafinta." "Safiyyudeen zan maka rashin mutunci wallahi!" Ya fada cikin fada kafin ya daura da cewa. "Don ina binta ba yana nufin ina sonta ba ne, Yarana ma da ta zuba min zan je na amso su wallahi na fasa bar mata su, har Ni zata hada da iyayena!" Kafin kace kwabo an taru a tsakar gidan, ran Alhaji Muhammad Jadda ya kara b'aci amma yayi murmushi irin nasu na manya ya kalli Hajiya Kaltuma ya ce mata. "Dole sai ya biya abin da yayi Kaltuma." "Aliyu bai da laifi fa, har yau ina kan bakana da ace lokacin da ya rasa Uwa Inna tana nan da zai samu sauƙin haka, kai ka yanke hukuncin rabuwa da Aisha, sannan ka kwace shi kasan illar da ka mishi? Ka saka ya tashi mara hakuri, Eh Aliyu yana da zurfin ciki domin babu wanda yasan irin ukubar da ya sha a hannu Hawwa da shuwa, don haka bai tab'a gayawa kowa ga damuwarshi ba, akan Ummu Hadiyya ne baya iya hakuri, akan Ummu Hadiyya ne baya boye b'acin ransa, domin duk abin da ya faru kai ne sila, ban da Allah ya taimaka Uwarshi bata barci a kanshi har yan uwansa ai da abin da Aliyu zai zama sai yafi haka tow Allah baya barci kuma shi ba azzalumin sarki ba ne. " ta fadi haka tana fitowa waje, ganin yadda aka tsatssya yasa ta cewa. "Da alamu matsalar gabanku bai ishe ku ba ko ? Har sai kun kara da na Tafida!" Tuni kowa ya watse, ta shiga dakin har lokacin bai daina fada da masifa ba. "Deeni kyale shi ya je, tunda har Ummu Hadiyya ta iya tsallake Yaranta a gadon haihuwa babu abin da zai bata mamaki ko tsoro ya je ya tunkare ta, har yaushe zaka girma Baba Ali? Yaushe zaka yi hankali? Tow zuwa yanzu Borno da Al'ummar borno suna kanka sai ka cigaba daga inda ka tsaya, Amma hargowa da hargagi ba zai kara maka kome ba, sai dariyar waɗanda basu son kayi gaba. " daga haka ta juya ta bar dakin Inna, a can bangaren Shuwa daurawa suke suna kuncewa domin Aliyu dai irin mutanen nan ne da yau aka yi aiki kansu gobe zai iya yin sanyi ko ya lalace. Don haka koda Samha ta gaya mata Ya Tafida yana can yana fada akan Ummu taki zaman dakinta tayi jego wani murmushi ya kwace mata, "Alhamdulillahi ta nan muka yi nasara......🤔YAR MACE....🌺 *Mai_Dambu* Paid book 04 "Ke tashi aikinmu yayi kyau!" Girgiza kai Yarta Sa'adiyya tayi tana faɗin. "Ba dai akan Tafida ba, na san waye shi na kuma san me yake yi a cikin kashi goma na aikinmu dakyar daya yake kama shi, tow bari na gaya miki a dakinta ma ya kwana karewa kenan kin ga kenan babu batun wani aiki yayi kyau. Ni na gaji da zubawa yan iska kudi ki nimo wata hanya amma Tafida baya cikin mazan da asiri ko tsafi zai kama su, domin nayi imani da Allah kaf gidan nan babu wanda ya kai shi ibada da tsayuwar dare, lalacewa da ake kallon yayi yafi wadanda ake musu kallon kintsatsu sannan ke kanki shaida ce yadda na gama lalacewa da bin maza ina amsar kudi tow Tafida a idanunku yake mutumin banza amma a zahirin gaskiya yafi kowa samun Allah, sannan ban da sharrin da muka mishi bana jin har akwai abin da zai kama Tafida tunda kowa ya ga abin da ya faru hatta matarshi ta gani amma ta kare tana zama da shi a haka ne dai ki nimo wani hanya idan har haka zai saka ya rabu da ita wallahi bar ganin yana ihu na rantse da Allah son da yake mata ya wuce baki ya faɗa, domin kuwa na gani akan idanuna." "Ke kada ki mai dani yar iska, kina nufin Aliyu yana son wancan bakar Yarinyar?" "Kwarai da gaske, baya sonta zai dinga hawa kanta yana sauka? Baya sonta zai dirka mata ciki? Baya sonta zai haukace ta ce ta dawo dakinta tayi suna? Jiya fa har na shirya zan bishi ya ce kada na sake yaga kafata a wurin bikin rantsar da shi tunda bai min alƙawarin nice first lady ba, gaya min wacece First Lady?" "Ke mana, ai ya gayawa Babanki tuntuni ke zai bawa wannan matsayin." "A'a ba dai haka aka yi ba, sai dai idan kune kuka roka min ya bani!" "Ke ki min shiru yarinyar da kike magana akai ko jami'a bata shiga ba balle ayi maganar wani matsayi. Nasan nan duniya babu wata first lady sai ke!" Mikewa tayi zata fita domin ita kan Sa'adiyya bata jin zuwa yanzu zasu sake samun kan Tafida don yayi gaba. "Ina zaki bamu gama magana ba!" Juyawa tayi idanunta cike da kwala ta ce mata. "Watannin baya kin san dalilin da yasa Tafida ya kora Hadiyya gida?" Girgiza kai tayi tana kallon yarta da take ciki da mamaki. " murmushi Sa'adiyya tayi tana faɗin. "Nice nan na saci kudinsa na yi amfani da shi, kuma nasan bayan shi da Hadiyya babu wanda yasan inda yake ajiye kuɗi, na kwashi sauran na kai dakinta na boye." Goge hawaye tayi tana kallon Hajiya shuwa da kyau, "amma kin san me? Da yazo yana bincike na ce ban sani tunda ban san inda yake ajiyar ba, hmm kiran Hadiyya yayi ya ce ta tafi gidansu sai ya zo da kanshi. Bayan yasan ko me zai ajiye ba zata tab'a dauka ba. Tana barin gidan ya turke ni sai da na gaya mishi gaskiya ya kyale ni kin san me ya ce min? Kin ga wancan yarinyar da muke renata ko me na ajiye idan ban ce ta ɗauka ba da shi da banza daya ne, wallahi kin yi na karshe kada ki sake raina ya kuma b'aci wallahi kika sake na kuma kama ki sai na wulakanta ki!," murmushi tayi tana share kwalla ta cigaba da kallon Hajiya Shuwa. "Kina tsammanin zan kyale ni ne idan ya gano abubuwan da nake aikatawa na son rai!" Daga haka ta juya huci Hajiya Shuwa take tana jin lallai koda zata yi yawo tsirara sai yarta ta zama first lady na Maiduguri. --- *Ummu Hadiyya* Cikin barci naji wayata tana kara, a hankali na lallubeta na saka a kunne. "Assalamualaikum!" "Waalaikumun salam, Ummu Hadiyya!" Bude idanuna cikin nauyin barci nace. "Na'am?" "Maman Ilham ce, gamu a unguwarku ban san inda xan fara ba ne!" Tashi nayi zaune nace mata. "Aunty Saimah! Ki ce a nuna miki gidansu Aunty Baby'sMama kitchens!" "Ok!" Tashi nayi zaune ina me tattara sumar kaina, domin na wanke dazun da safe, na saka ribom na kama shi, sannan na shiga ban daki na kama ruwa na fito, ina kokarin zama naji sallamarta. "Assalamualaikum! Ikon Allah matar nan ashe har kin haihu? Ni da nace ki gaya min idan haihuwar tazo muje asibiti." Murmushi nayi ina sosa kaina, ina kallon Yaran. "Ikon Allah dama biyu ne Abban Ilham yaki gaya min, lallai zai sani." Ta fada tana shigowa dakin. "Aunty Saima zauna mana!" Na fada ina kokarin saka hijab xan fito waje. "Idan ta ni ce koma ki zauna sai da naci abinci kafin na fito kin san ba don rantsar da Tafida ba ni da borno sai kin haihu!" "A'a bari a kawo miki ruwa!" Haka na fito na samu Uwani ce a tsakar gida tana tattan kunun yamma. "Uwani ki had'a min kome ina da bakuwa!" "Tow Aunty Baby!" Na koma ciki, ina hada faɗin. "Kawai sai kuka ji labari ba!" "Wai kawai ashe ke da Aliyu kuka tawo asibiti!" "Eh wallahi kin san Hajiya Kaltuma bata gari tafi bikin yar Yayarta kuma kin san hidima baya karewa a familynta. Kin ga Inna kuma girma ya cimmata town waye zan kira a wannan daren?" "Hajiya Hawwa da Shuwa fa!" Murmushi nayi bance kome ba domin bana fatan na fadi kome har abada tsakanina da su idanu. "A'a kawai Ni ce nace muje asibitin idan ban haihuwa ba a nimo su." "Amma Ummu baki dauki kasada ba?" "Salamun alekum!" "Uwani oho Assalamualaikum ake fada fa!" "Tunda kin gane ba shi kenan ba, ke dai akwai son gyarawa mutum abu!" Dake abokiyar wasata ce yar Kanin Mama ce na kuwa ce mata. "Ai kuwa kina yin kuskure zan gaya miki katuwa kawai!" "Eh na yarda ke kuma Yar mitsila!" Dama can tun fil azal haka muke da ita. Ta juya tana kallon Yaran ta ce min. "Allah yasa kada kuyi halin Aunty Babyn roba!" "Allah ya taro mana ke!" Na fada ta juya ta gaida Aunty Saimah. Dalilin shiririnta Uwani aka share batun haihuwa, muna cikin hira sai ga Yayun Aliyu mata da biyu, Aunty Maryam da Aunty Rukayya, kallon Maman Ilham suka yi. "Eh ba dai Ya Abubakar ya baki labari ba ?" "Eh ai kunsan haihuwa da mutuwa bata boyiwa kafin ya gaya min makotana daga Abuja suka kirani suna min barka ashe har IG an daura yaran Baby'sMama kitchens." Tab'e baki Aunty Rukayya tayi tana latsa wayarta. "Ina wuninku!" Na gaishe su, a lalace suka amsa. Ban damu ba itama kuma Maman Ilham abin ya bata haushi tuni ta hade rai, ta dauki zobo tana sha. Taki mika musu Yaran. "Uwani!" Na kirata. "Aunty Baby gani nan ba sai kin fada ba, the first lady of Borno state." Kallon juna muka yi da Maman Ilham muka saka dariya. "Wato Uwani nan taku yar gari ce." Shigowa tayi da katon ture ta ajiye musu cikin zolaya ta ce min. "Banda mugun hali irin naki, kiri-kiri kin hanani ganin kyakkyawar mijinki, ki rage kishi, sai dai ya kashe shi da soyayya da shagwab'a. Don Allah kada ki saka yaje office yana kasa aikin al'umma." "Uwani zanyi zagi!" Tab'e baki tai tana faɗin. "Idan kin zage ni ma kin yi a bawo, domin nice zan shiga gidan mai girma Gwamna a ta uku!" Ko su Aunty Rukayya da Maryam basu yi niyyar dariya ba, suka kwashe da dariya. Yarinya ce Uwani amma ta iya mu'amala da mutane ga kayan saka dariya. "Kada ki damu indai tafida ne kamar kin ganshi."inji Maman Ilham, murmushi tayi ta fita kamar ba zasu sha ruwan ba suka sha Aunty Rukayya ta ce min. "Sai mun roka ne zaki bamu Yaran!" "Amma a bisa alada ba ita ya dace ta mika muku Yaran ba" ta fada tana mikewa ta dauko yaran ta basu. "Ikon Allah! Maryam yaran nan kamar lokacin da Hajiya ta haifi Tafida sak-sak da shi,.ina da hoton har yau." "Wai ni kuna jin labarin Hajiya kuwa?" Inji Maman Ilham, kallona suka yi suna jiran karin bayani. "Baby ya labarin Hajiya?" Hmm kusan wacece Hajiya? Mahaifiyarsu ce fa, idanuna ne suka cika da kwalla na ce mata. "Hajiya tana lafiya sai dai kuma bata jin dadi gaskiya." Na fada ina dauke kaina. "Allah ya bata lafiya!" "Amin Ya Allah!" Na fada bayan sun hade baki sun mata fatan sauki, hira suke jefi-jefi Mama tayi sallama ta shigo. "Oyoyo Mamana!" Dakin ta shigo tana me sallama. " Sannu ku da zuwa. Uwani baki kawo musu alele ba sai kayan ruwa ba kome a gabansu baya akwai alele da dan wake da doya da kwai maza a kawo musu ga babba me shiririnta da ta kasa magana, a zuba musu farfesun kajin nan maza don me Alhaji da Babanku suka kawo ba don a ciyar da masu zuwa Barka ba, maza a kawo musu abincin." Ta fada tana me kallona. "Kin ci abinci? Jego ba zai yiwu ba sai ciki ya dauka musamman wancan cinye du din don yafi yar uwarsa cin abinci. Maza hada shayin kisha." "Mama nasha fa bakina ne ba dad'i." "Ayya Ummuna daure kisha idan baki ginu ba, ba zaki iya daukar wani laluran nan kusa ba, amma idan kika ginu nan da wata shekara wani labrin ake." Mamaki ne ya maka su yadda suka ga Mama tana ritita ni, haka Uwani ta shigo musu da abinci, tana ajiye musu Mahira tana kawo min tuwon alkama miyar kuka danya wacce aka daketa kamar karkashi ta sha kayan kamshi, ta ajiye." "Aunty Baby Yan grp suna gaida ke, wai sun yi kewarki don Allah yaushe zaki cigaba da sanwata alfaharina!" "Ke Mahira yafi can kyaleta da wayarnan!" Dariya tayi tana faɗin. "Sweetheart kuna barci ko? Sai kun tashi xan zo muyi wasa;" "Sai ki hada har da kasa da yashi a bude muku fili Sabuwar uwa ta fara hauka!" Ta fita tana dariya, duk kin Allah aunty Rukayya sai gashi ta sake suna cin abinci hankali kwance. Fita Mama tayi ta bamu wuri can sai gata da wani kofi dauke da dafaffen madara. "Mama yanxu nasha tea." "Ungo naki, gyaran jiki babu ruwansa da kin sha ko baki sha ba, maza sha." Haka na amsa ina kallon madaran har mai mai yake yi kamar zan yi kuka na fara sha. "Wallahi kin more, irin wannan kulawar waye zai samu ji yadda Mamanki take kulawa dake!" Inji Maman Ilham, dariya nayi kaina a kasa na sha rabin madaran na ajiye. "Kin san nice Babba kannena duk ba ita tayi musu jego ba, asalima ba a dauko wanka a gidan nan, nice dai nazo da kaina!" "Assalamualaikum Mama ga sako daga Baba wai dafawa Aunty Ummu Baby!" "Sai dai Uwar baby yanxu ta tashi daga baby ta koma Uwar baby." Murmushi Aunty Maryam tayi tana faɗin. "Kanwarki nan akwai abin dariya!" "Uwani ba, ai ba ita ɗaya ba ce a kofar shiga kun wuce wata tana sayar da abinci a shago. Zakiya kenan Yaranta ne anan suke zaune abinci suke sayarwa idan sun yi aure ko kafin su yi aure za a kawo mata wasu." Ware idanun suka yi. "Kamar Ya?" "Kusan dake mu talakawa ne amma muna da burin mu cigaba idan har zaki iya hakuri ki kuma kame kanki zaki nime kudi Mama bata da matsalar kome, yanxu ita Uwani public health ta karanta, kuma next year zata gama,

Chapter 3 of 17