cikin alkalan ya ce min. "Wannan abincin naki ban tab'a ci ba sai yau! Sannan dayawanku da kuka tsallake zagaye na biyu kun sake maimata girki ke kuma tunda kika fara baki maimaita ba me yasa haka!"
Rike abin maganar nayi na sake murmushi, sannan na fadi sunan makarantar Yar shehun Borno inda na samu diploma a girki abin da suka koya mana da kuma ni kaina tun ina shekara goma nake koyan girki , sannan muna yin abincin sayarwa wanda a rana guda muna abinci sama da kala biyar zuwa shiga, haka yasa na kara sanin yadda zan kaucewa maimaici. Sannan na gaya musu iya abincin gargajiya da nayi ba arewa ne, ban dauko wani abu daga kudu ba, masa, dan wake, sinasir, kindirmo da dambunshi, tuwon alkama, fumkasau, dambun cus-cus, biski, da sauransu. Karshe na rufe da wannan girkin. Sun jinjina min hadin aka fara fitar da sunayen wadanda suka yi nasara ban kawo zan yi nasara ba, haka yasa ana gamawa hira damu aka fara kiran waɗanda basu yi nasara ba ana basu shaidar kwarewarsu, a cikin mu goma aka sallam shida, ya rage saura huɗu. Na hudun sha fara kira aka bata kyauta. Sannan aka kira na uku namiji ne, sai na biyu na miji ne, sai gaba na ya fara bugawa. Lokacin da alkalan suka kira na biyu zuba min idanun suka yi yadda na kasa nutsuwa, na rasa waye zai tsaya min a lokacin. Tina ce ta fito wurin ta rike hannuna. Hawaye ya zubo min. "ba gani a tare dake ba, zaki iya na gaya miki yanzu zasu kira ki!" Lokacin da suka kira suna na, kawai ban san lokacin da na zube ina me sujada ba, domin sun tabbatar da cewa idan nayi nasara akwai wasu kamfanoni da zasu dauke ni nayi musu talla sannan akwai gasar girki na duniya a garin dubai wanda za ayi December, ni ce zan wakilci Nijeriya da jahar Borno. Yadda nai sujada nan ina tashi da kuka na tashi Tina ta rike min hannu muka je aka bani lambar yabo da kuma kyautar miliyan biyar. Kuka nake idan na tuna irin kokarin Mama akan girkin. Sai na rasa abin cewa haka aka tashi taron.
"Kai shegen sama ina ka boya ne?" "A wannan lokacin da yarinyar nan tayi nasara ya dace ace kai ne a gefenta, amma Tafida ka barwa Tinah matsayinka, Haba Aliyu Haba Aliyu me yasa ne haka? Me yasa ko ina sai ka nuna baka kaunar Ummu, me tayi maka da zafi haka? Aliyu Allah yana sonka ne ya baka Ummu amma wallahi muna nan dayawa da muke addu'ar Allah ya bamu mata nagari, Aliyu har cikin raina nake son zamanka da ita, yanzu ka ga yadda take kuka tana bukatar wani a gefenta iyayenta ko mijinta, amma ta rasa kowa sai wata da bata hada kome da ita ba zata tsaya mata abin nan duk Najeriya ake kallo haba Aliyu abokan aikina dayawa sai da suka fadi cewa ina mijinta yake ba an ce matar aure ba ce, haba Aliyu, don Allah don soyayyarka da Annabi Muhammad ka saketa kaji ka sake ta don Allah tayi wani auren ko zata samu wanda zai kula da ita!"
Nan ya hau fada tare da gayawa Deen cewa. "Ina da nayi tafiya na bar mata Mahmoud ya na kaita wurin tattarawa tayi ta koma gidansu Tina shi yasa na barta da Tinan!"
"Mahmoud ka barwa Ummu yana kaita wurin ? Tafida anya mutane ne aka haifeka? Kai da kanka kasan Mahmoud ko bunsuru ya ganshi ya barshi shine zaka ce ka bar mishi yar mutane Innalillahi, gara da ta bar gidan Allah ya mata albarka ya bata yadda zata yi amma tabbas Allah sai ya saka mata domin nayi Imani da wanda rayuwata da mutuwata take hannunshi Mahmoud ya mata akunyaci yasa ta bar gidan Wayyo Allah kai dai Allah ya wadaran halinka, duk amintatta da Mahmoud ba zan bar mishi ajiyar mace ba kai mace ko ta kare balle macen mutum ba zan barwa Mahmoud ba, kai bari na gaya maka ko macen alade ba zan taba barwa Mahmoud ba balle macen bil adam wacce ta hada sura da zati irin na Hadiyya wallahi ba zan bar masa ita a gida ɗaya ba ko a mota daya ba zan bari ba, kayi a hankali da rayuwa idan kasan fitar rana baka san inda zai fadi ba.......
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
Paid book
15
"Wallahi baka yiwa kanka da rayuwarka adalci ba, kasan waye Mahmoud? Koda yake ba mamaki kai da shi kwarya sama ce ta daki na kasa, amma nasan haka kawai ba zan barwa Mahmoud diya mace baliga ba, idan baka sonta fine amma barin Mahmoud a jikin mace baliga masifa ce kuma na gaya maka gaskiya tunda kai dan banza ne!" "Ya ishe ka zagina!" "Hmm wata rana zaka yi kuka da fatan Ummu ta saurare ka." "Allah ya min tsari kada ya nuna min wannan ranar ya raba ni da mugun ji da mugun gani!" Duk wani masoyina ya kirani a waya anyi min fatan Alkhairi, na rasa inda Deen ya samu number na sai gashi ya kira har da fatan alkhairi. Haka na samu damar shiga cikin mutane, a wannan lokacin na ga kokarin shi na yarda ya kai ni irin tarurruka da aka yi ta yi akan nasarar da muka samu, sai dai abin da ya fara damuna yadda kiri-kiri yake gaya musu ai kawai girkin na iya amma ai kaina babu kome a cikinsa sai yadda ake abinci.
Kusan sai naji abin ya fara fitar min a rai, ya zamana ko taro ne bana son zuwa sai ya saka ni a gaba da dariya. Ana haka kwatsam tafiya ta kama shi Maiduguri, ya tafi da safe da yamma sai ga Mahmoud tunda na ganshi ta window naki bude kofar, yayi kiran duniyar nan naki budewa nayi kamar ma bana gidan. Kawai ya kira Tafida ya gaya mishi ai yazo bana nan. Aikuwa ya fara fada kamar ya shigo wayar.
**
Deen yana jinshi bai ce kome ba, saukar wayarshi yayi ya turawa Mahmoud sako. *Kabar gidan Tafida kafin na shiga wurin Mahaifinsa na gaya mishi yadda kake kokarin niman Yar Mutane!* Sakon na shiga ko minti ɗaya ba ayi ba sai ga kiran Mahmoud. "Zan ci abu kazan-kazan Ubanka Ni zaka mayar dan iska nace maka ina niman matar aure ne!!" "Kai ka sani idan kaso kada ka bar wurin sauran Alhaji zai ji da shi." Ya kashe wayar. "Kai da waye?" "Ni da wani dan akuya ne da yake bin matar wani jaki shine na mishi kashedi ya biyo ni!" "Shi mijin dakikin ina ne da yana zaune wani na niman Matarshi?" "Ai bayi da banbanci da maloho irinka, da ka bar Ummu Hadiyya a abuja har wani yana ce maka matarka bata nan? Anya Tafida tsinuwar Annabi ba zai kama ka ba kuwa? Tow zan gayawa Abba domin iya adalci nayi maka ina tsoron kada wata rana wani ya keta alfarmarta saboda kai " "ban gane ba kana nufin Mahmoud yana niman Ummu?" "Ni na gaya maka? Rufa min asiri wallahi ban isa ba!" "Lashe bakinshi yayi yana faɗin. "Tow shi kenan!" Kwananshi biyu a Maiduguri da zai dawo tare da Deen suka zo saboda akwai wani workshop da zasu yi, tafida yaso ya sauka a gidan amma yaki, ya ce." Zan na zuwa cin abincin dare dai!" Da haka kuwa aka bar zancen, an bawa Tafida kaya amma yaki ikon Allah da Deen ya shiga yin sallama da Abba ya bashi kayan ya zo min da shi. Nayi murna domin kusan kayan Mama ce ta turo min, haka na gyara abuna na cigaba da mana girki. Kullum na kira Babana ko Abba nasiha suke min tare da tambayana ko akwai abinda nake so, nace musu a'a babu kyautar da Abba yake bani har mamaki yake sani jin ga Babana ma haka, Mama itama nayi hakuri na zauna . Baba Bulama shima ba karamin kokari yake ba, abin da na kara fahimtar iyayena da na Tafida suna son mu zauna a inuwa guda amma shi fa yaki sam yaki maganar a zauna.
Haka lokaci ya tura har muka fara kusantar watan azumi, wanda yasani jin kamar nayi kuka don ina son nayi azumi a Maiduguri, haka muka fara azumi ranar da aka ɗauki azumi daya ranar ya shigo dakin ya ce min. "Ke ki shirya Babanki ya ji zan tafi Umara ya biya miki!" "Babana?" "A"a Babana!" Ya fada yana watsa min harara, haka na saka hijab muka tafi aka mana kome har da passport, muna dawowa muka samu Tinah, murna kamar zai yi yaya ta kawo min kaya ne , wai ashe ta tafi Dubai ne sai gata da kaya niki-niki, tsaki yayi yana faɗin. "Tina kina bata yarinyar nan da kyauta fa,.ni bani da halin yi mata abinda kuke mata ke friend dinki!" "Aliyos ba zaka gane ba ne, Ummu tana da kirki shi yasa bana jin zan iya samun abu ban bata ba." Dogayen riguna kala uku sai takalma heel , masu kyau kafa hudu da jakunansu. Sai wani Musulmin lace me kyau kala biyu, "Gashi kin zo muna azumi me zan miki?" "Tafiya xan yi idan za a sha ruwa xan zo!" Haka na rakata ina ta godiya, har zata shiga Mota ta ce min. "Akwai wata yar ghana tana sayar da mai da sabulu xan karba miki." Dariya nayi nace mata "a'a bana son bleaching!" "No ba zai kara miki haske ba amma zai gyara miki fata!" "Tow shi kenan amma zamu tafi Umara duk da bai gaya min lokacin ba!" "Zan kawo miki an jima! Ni dai turaren Maiduguri nake so ga gidan ki nan mutum ya rasa wani irin kamshi yake yi!" "Kai Tina zan a kawo miki!" Haka muka yi sallama ta tafi,na shiga aiki kamar kafafuna zasu yanke. Ana shan ruwa Tina ta kawo min kayan na ciro mata kula masu kyau na zuba abinci a ciki ta tafi da su don saurayinta ya kawo ta, an fara azumi da kwana bakwai muka bar Nigeria zuwa Saudiyya. Lokacin da na ganni a dakin Ka'aba sai da nayi kuka nayi kuka nayi farinciki nayi addu'a na kai kuka na wurin Allah. Sai da aka sha ruwa na koma hotel dinmu, hmm Tafida tunda muka yi wanka muka tafi harami ban kara ganinshi ba, wasa gaske sai da muka sati Daya na ganshi tare da Sa'adiyya. Kallo daya nayi musu na dauke kai, ko ya sha jinin jikinshi ne, da asuba lokacin Sahoor sai gashi. Sau daya na kalli inda yake na kauda kai. Koda muka yi Sahoor kowa kama gabanshi yayi, na nufi masallaci, shi kuma yana me budar hotel din da ya sauya dukkanmu a nan haramin muke, haka ma da muka tafi Madina, sau na ganshi sai na dauke kaina, lokacin da naje rauhda. Anan ne naji kuka ya zo min, na tafi gaban Kabarin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, na zauna cikin kuka nace. "Ya Rasulullahi, ka sauke dukkanin sakonka ka yanta mu daga duhu zuwa haske ka cire mana rigar jahilci ka saka mana naka me haske da kamshi, Ya Rasulullahi kace muyiwa Mazajenmu biyayya su kuma su riƙe mu da adalci Ya Rasulullah na kawo kukana gare ka." Ban sani ba ko damuwar Tafida da ne yasa nake surutai ko bakinciki ne yasa nake jin kamar ban isa kome ba,amma zamana a rauhda yasa ni jin sauki da kuma surutai da nayi tayi sai naji kamar na yantu na samu sauki a zuciyata, na roki Allah ya cire min tashin hankali da damuwar Tafida. Har muka gama umara, sannan muka yi sayayya wanda ana jibi zamu bar maka yazo ya watsa min kudi na kalle shi nayi murmushi tare da cewa. "Ni bana bukata, ita wacce ka dauko ka kai mata ta fini bukatarshi ita tana jiran naka ne ni wanda iyaye suka bani ya ishe ni!" Ware idanu yayi tare da shigowa dakin zai hayayako min nace mishi."ina azumi bana faɗa!" Ina fadar haka ya dakata. "ina dakin Allah bana son na tafi na bar zunubi, kaima ina maka fatan shiryar Allah. Domin ka b'ata da yawa." Na fada ina me shigewa ban daki, wanka nayi tare da alola na fita nayi sayayya a kantin da naje sayayya, nayi ta sayan kananun kaya, Allah ya taimaka ina dan iya fahimtar larabci saboda mun yi tajewid, haka na gama sayyana lafiya lau na fito. Har nuna ni larabawa ke yi wai sun sha mamaki da nake iya fahimtar larabci da kuma kokarin da nayi. Turare na sayawa Abba biyu Babana biyu. baba bulama biyu sai Hajiya Kaltuma da Hajiya Salamatu, sai Maman Tafida da na saya mata kaya itama, ina dawowa na same shi a bakin kofar dakina. "Ga kudin nan Abba ya turo na baki wai na kayan sallah ki ne!" Saka hannu nayi na amsa ina faɗin. "Allah ya ƙara mishi lafiya da nisan kwana!" Na shige abina ina me rufe kofar, zama nayi ina nazarin kudin nan idan na canza shi Maman Tafida ya dace na bawa tai ko jari da shi ne gaskiya matar tana bukatar taimako sosai. Ranar da muka bar Makka muka wuce jidda, ina kallon tsiyarsu. Jirgin Maiduguri muka hau amma zai sauke mutane a Kano, haka muka bar kasar cike da kewarshi. Mun isa Kano, daga nan ban kara ganin Sa'adiyya ba, murmushi nayi domin naga sai lokacin ya nutsu da bai da nutsuwa bakiɗaya, haka muka taso bayan mun sha ruwa muka iso Maiduguri Deen yazo ya dauko mu, sai tsiya yake mana wai mu gaya mishi gaskiya ko mun dauko dan Makka da Madinah ne! Ni dai ban ce kome ba, ban san wani irin mutum ne Tafida ba, amma bai iya boyewa Deen matsalarshi. Domin anan ma gaya mishi yayi tare da Sa'adiyya suka tafi Umaran, bayan sallah nan zai gabatar da ita a wurin Alhaji . "Yayi kyau ai, amma ka sani yadda ka saba lalata da ita a waje idan ka shiga cikin gidan ya." "Bana son iskanci wallahi ban tab'a wuce gona da iri ba, iya kata." Sai juyawa muka haɗa idanun ganin murmushin da yake kan fuskana ina sauraron karatun Alqur'ani, domin akwai earpies, shiru yayi yana faɗin."ashe tana jin abu ne!"
"In sha Allah sai Allah ya saka mata!" Kafin mu isa gida sunyi fada kaca-kaca kamar zasu daku,. Har cikin gidan Deen ya dauka min kaya, ina jin yana faɗin. "Muje na ajiye miki zan tafi wurin budurwata!" "Kai ba zaka ɗauka min kayana ba!" "Saboda tsine min Ammah tayi?" "Hmm Dan iska!" "Ni bana wuce iyakar Allah!" Ya fada yana shigar da kayanmu, ni kuma na wuce cikin gida, dakin Inna na fara shiga ina faɗin. "Hajiya Innata gani nan!" "Ummu kai ne kazo!" "Eh nice Innata!" "Sannunka Yaron nan Ummu sannu da zuwa!" " yawa Inna! Da fatan an sha ruwa lafiya, mun same ku lafiya?" "Alhamdulillahi, ya Tafida take?" Murmushi nayi ina faɗin. "Duk muna Lafiya!" Sannan na mata sallama na wuce wurin Hajiya Salamatu na gaidata, ta ji dadi sosai. Ina fita na shiga dakin Hajiya Kaltuma, Uwar dakina nan na bararraje muka sha hira kafin na wuce wurin Abba, wasa wasa zai da muka share awa biyu hiran da nasiha yake min. Sannan nayi mishi sai da safe na.dawo bangarena. Dakina da gidan na ga an share min shi tas an goge an gyara ko ina, wanka nayi da ruwa me dumi ina fitowa nayi sallah Magariba da Isha na bi lafiyar gado, da zan yi sahur nayi wani mafarki me ban Mamki, Tafida ne ruwa yake tafiya da shi Ikon Allah hajiyarsu tayi kokarin janyo shi amma ina ruwan yaci karfinsa, ban san ya aka yi na fada ruwn ba na shakka wuyarshi, amma wasu mata da bansan su ba suka hanamu fita, wani katon maciji ya fasa kai yana bude baki, ganin haka yasa nayi ta jan Tafida amma Macijin nan yana bin mu, duk wanda ya nufe mu xan ga macijin nan ya nufe shi baki bude da wannan tashin hankali na farka jikina yana rawa. Ban daki na shiga nayi alola sannan na nufi parlour yana zaune shi da Sa'adiyya, ban yi mamaki ba don naga yana cin abinci, sai hira suke abin su zuwana Umaran nan na koyo shan shayi na fito da dauke da kofin tea domin jiya bayan dawowa na daga cikin gidan Deen ya buga mana kofa ya bashi yace. "Kai bawa Ummu na ta ne!" Don har da Nama yana zuwa ya ajiye min a bakin kofar, wani ikon Allah ban tab'a jin nayi magana akan Abinda yake min ba, haka kwanaki suka zo suka wuce , aka zo bikin sallah nayi abinci na kai, anyi sallah da kwana biyu kamar an bashi ina kwance a dogon kujera ya shigo yana faɗin. "Idan kin gadama ki shirya muje ki ga yan gidanku!" "Da gaske?" Na tambaye shi, "Ni abokin wasanki ne?" Yadda yayi min maganar na fahimci babu wasa da sauri na shiga daki sai ga Ni dauke da katon akwati, na tsarabarsu dama na cirewa Abba da na yan gidan, sannan na daura laffaya. Ina jan akwatin haka muka fita, a waje muka samu Deen ashe har da shi gaban motar ya shiga, "Ummu inji Ammah wai ta gode, abincin sallah sai sun cinye suka hanani. Gashi ko abokaina ban yi musu kome ba, don Allah na kawo cefenen ki musu girki wancan yarinyar ba zata iya fitar dani kunya ba!" "Ka turo ta mana muyi tare sai kace mata tazo na tayata babu dad'i tana matar da zaka aura amma ce ka kawo min abincin da zaka ba abokanka, sannan gasu Jalila ba zaka basu su maka ba?" "Ammah zata min sinasir, Jalila me ta iya ban da iyayi." "Shi kenan!" Na fada ina dariya, haka muka isa gidanmu, Wayyo dadi tunda muka shiga cikin gidan, na nufi parlour Baba na gaishe shi tare da Tafida, sannan na wuce wurin bangaren Ummi na gaida ta ita da Umma kafin na wuce bangaren mu, ina shiga na ga irin kallon da Tafida yake yiwa bangaren mu, kamar ya ga kashi. Mama kuwa sai hidima take mishi, Deen sai godiya yake mata. A yau nakara jin wani irin tsanar Tafida, domin babu dan da za a yiwa iyayenshi haka ya ji dadi. Ko ruwa bai sha ba ashe bani daya abin ya dama ba,.har da Deen. Suna gama gaisawa ya fita Deen ya zauna yaci abinda aka ajiye musu, ya ce mata. "Mamanmu ni fa zan tafi da kayan dadin nan wallahi!" " za a zuba maka ka tafi da shi!" Nan ya sake narkewa da murna, ita kanta Mama ta ji dadin Deen domin ta fahimci abokin Aliyu ne na amana. Bayan ya gama ya fita nima muka yi ta hira, na tura mata tsaraban ina mata bayani, ta amsa tayi godiya ta kuma ce zata raba gobe in sha Allah, "maza tashi ku tafi Allah ya miki albarka." "Amin Mamana " haka ta zuba min kayan ciye-ciye, na fito da shi, anan take gaya min ai Uwani ta tafi sallah gida , nayi fatan Allah ya dawo da ita lafiya haka muka bar gidan, tun a mota Deen yake faɗin. "Ummu Mamana ta ce min zata baki kayan dadina!" "Da dai kayi hakuri muje gida na diba maka!" "A'a gudun kada a sake samun dan fashin da yake juye nama ya kuma juye min kayan dadina ne wallahi ba zan yarda ba!" Ashe ya gaya mishi ya juye min nama, mutum sam babu sirri koda yake na lura tsakaninsu su biyun nan babu sirri suna gayawa juna kome, idan ka cire Mahmoud da basu irin wannan maganar da shi. Koda muka dawo na diba mishi nashi ya tafi, na bari a kitchen ina fitowa na samu ya dibo ya zuba a flat suna ci da Sa'adiyya sai santi take. Washi gari na kara kiran Mama na gaya mata ina son turaren wuta zan kaiwa Tina da yan uwanta da kawayenta, ta ce zata saya min a wurin Ummi. Kwana biyu Abba ya ce na shirya Tafida zai kai ni Biu.
Haka na roki Hajiya Kaltuma ta bani aron Nabila muka shiga kasuwa nayiwa Babana sayayya, muka yi cin-cin da cake. Sai nama wanda Abba ya bamu na sallah na soya na saka rabi a firji domin a zaman shekara kusan daya na gano lagon Tafida yana son nama kamar yayi hauka, zai iya cin nama da bread ya sha ruwa ya koshi, don haka na saka mishi wani a langa tsirara. Da kanshi da rakiyar Deen ya kai ni har kofar gidanmu, wannan karon an karbe shi a matsayin d'a ne da zai tafi ba karamin hidima aka mishi ba, Babana har kudin mai ya bashi ya mishi alkawarin zai saka a kawo ni har gida, haka kuwa aka yi na kwana biyu a garin Biu, mahaifina da danginsa kamar su lashe ni domin duk abinda na kawo ya saka an rabawa dangi kaf sai kaɗan Mamawo ta ajiye mishi, nima da zan dawo kamar wacce nace musu bani da kayan abinci, kuka, kubewa busashe, barkono, albasa, daddawa, garin kunu me kyau, kai tsaraba sai da aka cika min bayan mota da shi, kaji kuwa yanka min su aka yo aka gyara aka fasa ƙanƙara a kai, domin nace dambu zan yi. Mun iso da la'asar ban huta ba na hada wuta na daura dambu. Ya kwana washi gari na tuke shi tass. Alhaji ya kara turo min da nama danye yace na soyawa Tafida, haka na dafa na soya shi cikin langa tsirara, Mama tayi min cin-cin da kayan ciye-ciye sosai domin wannan karon mota zamu bi, sai da na gyara gidana na cirewa yan gidan tsarabansu ana gobe zamu tafi da dare Aunty Rukayya ta zo, ina jin yana gayawa mata shi ya gaji da bin shi da zan yi yayi magana Abba ya fara faɗa. Shine ta shigo dakin ina zaune da littafin addu'a. "Ummu Hadiyya ki gayawa Abba ba zaki bishi ba, don ai wannan takura ne ke baki ji kunya ki bishi ba." D'ago kai nayi na kalleta kafin nace mata. "Aunty Rukayya ke me zai hana ki samu Abban da kanki!" "Ni sa'anki ne?" "A'a na gaya miki abin da ba zaki iya ba tow nima ba zan iya ba, ba haka aka koya min ba, ba a nuna min musu da babba ba!"
Fita tayi jikinta a sake, can ya shigo.ya fara zagina ina ga Sa'adiyya tana parlourn don naji muryanta Aunty Rukayya tana bata labarin har ya gama ban d'ago kai na kalle shi ba, yana fita na rufe kofata. Jin Muryan Deen yasa ni fita muka gaisa nace mishi. "Don Allah ina son magana da kai idan da hali!" "Ok!" Ya tashi muka fita waje mika mishi kudi nayi nace mishi. "Don Allah ga number Mamanshi ka tura mata kudin nan, " "ke kika yi niyya ko tambayarki tayi?" Murmushi nayi nace mishi, "Bata tambaye ni ba idan ka canza a tura mata don Allah!" "Allah ya tsare gabanki da bayanki, lallai na yarda akwai abinda Abba ya hango ne." Amsa yayi ya saka a aljuhun shi, koda ya koma ciki share shi Tafida yayi wai akan ya kula ni hala, shi kuwa dan ya kular da shi sai dariya yake irin na niman fada.. da fada suka rabu, washi gari muka bar Maiduguri da assuban fari ana kiran assalatu, wannan dawowar da nayi abuja ya saka ni jin na tsani kome na duniyar nan, ya sakani cikin tsoro da wani irin fargaba. Domin kuwa Tafida ya barni ina rayuwa kamar bani da yanci.
Tunda muka dawo Mahmoud ya saka ni a gaba ko a ina ya samu numberta kullum sako kullum kiran waya, idan nayi blocking dinsa zai kuma kirana da wani layin.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 17