kawo min kayan. Dake ni da Uwani muka fita, ita ta amshi kayan. "Hajiya Ummu ni sunana Deen shi kuma wannan.." "Mahmoud ko?" Na tambaye shi, a dan razane shi Mahmoud din ya kalle ni. "Ya aka yi kika san sunanshi." Murmushi nayi nace mishi. "farkon zuwanku!" Gyada kai yayi ya ce min. "haka ne kiyi hakuri wakili zai zo amma sai ana jibi biki!" "Ba kome na gode! Sai an jimarku!" Na juya na koma gida domin tunda aka saka bikin na rage saka manyan hijab wanda yake nuna kankantatta.
"Deen gayen nan ya samu mace, asalin yar dakar idan kana jin mace yar dakar yarinyar nan ce. Idan ya sake ya rabu da ita ni zan shiga na fita na aureta domin irinsu Ummu Hadiyya ba matan su Tafida ba ne." Sake baki Deen yai yana kallon Mahmoud. "Kana nufin zaka iya cin amanarshi kenan!" "Idan ya bani kofar haka zanci domin shima yaci Amanar iyayenshi wurin amsar zabinsu!" Naushi Deen ya kai mishi me karfin da sai da ya fasa mishi baki. Dariya yayi yana faɗin. "Ko zaka kashe ni wallahi ba zan barwa Aliyu Ummu ba domin matsiyaci ne da bai san darajar Iyaye ba, idan ka isa ka dakatar da ni." "In sha Allah, matukar ina Numfashi ba zan tab'a barin Aliyu ya rabu da Ummu ba matuƙar ina raye sai na kare martabar Aurensu ko haka zai zama karshen rayuwata." Dariya Mahmoud ya cigaba da yi yana faɗin. "Muje bingo! Amma ka sani matukar kudi na aiki sai na raba su dama daya tak nake nima na bawa kowa mamaki! Tafida Tafida kowa tafida kowa Tafida kowa tafida kowa, Nasara Tafida iyaye na gari Tafida wife material Tafida, Aboki irinka tafida , degree da Masters Tafida. Ni ne koma baya babu wanda yake fadar Mahmoud." "A'a Mahmoud muna sonka kada ka lalata mana abotarmu ta yaranta don Allah kada ka zama me son kai!" "Wani irin kuna sona? Kai ka raba Ni da yardan tafida baya shawara da ni bata gaya min kome akanshi, sai dai na ji kuna tattaunawa a sirri. Haka shine abota? Haka shine aminta? Dama an fada abota ta mutane uku tow akwai munafiki a cikinsu kuma ba kowa ba ne sai kai!" Ya share gefen bakinshi da ya fashe yana faɗin. "Na jima da sanin kome kuka saka a gaba sai kunyi nasara, kai kana aiki a state University Maiduguri, shi yana tare da shugaban kasa, ni kuma Uwar me kuka mai dani?" Ya fada da karfi Deen sai yaji kamar da gaske sun yiwa Mahmoud kuskure. "Mahmoud babu wanda yaki ka, Mahmoud ka san ba karfi iyayena suke da shi ba, wannan matakin da nake Allah da gwamnatin jahar Borno suka kawo ni wurin, wallahi ban tab'a maka kallon wanda ya gaza ba, Please na haɗaka da Allah kada ka shiga wannan zabin da Abba yayi mishi wallahi Tafida yana buƙatar mace ta gari, kai kanka kasan gidansu ba barin shi suka yi haka kawai ba don Allah mu taya Hajiya karkato da hankalinshi" yadda Deen yake magiya ya ce mishi. "Ya wuce na hakura! Na bar zancen." Ajiyar zuciya Deen ya sauke, sannan Mahmoud yasan ko mutuwa yayi Deen ba zai tab'a fitar da maganar nan ba domin mutum ne mai mugun sirri da zurfin ciki.
Duk wani abun da ake na al'adar kanuri babu wanda ba ayi mana ba, Baba ya tafi har wurin Mahaifina ya gaya mishi kome da kuma Maganar auren da cewa za a kawo daurin auren wurinshi. Cikin girmama lamarin juna, sannan ya dauko kudi kusan miliyan daya ya bawa Baba Bulama ya ce mishi. "tun daga ranar da aka haifeta nake ajiyar shi nasan mace ce kuma Yar hidima ce wannan ku kara da shi, sannan akwai kayan gara. Domin nasan kabilar da tayi aure cikinsu mutane ne masu matukar girmama lamarin Gara!" Duk da Baba Bulama so hana shi, amma yaki. "Ita ce daya tal min a duniya don ma Hadiza ta hanani ita, na gode sosai da irin dawainiyya da kayi min wallahi ka biya ni, amma don Allah ka turo min mijin na zaga da shi wurin yan uwnaa!" A take Baba ya kira Alhaji ya gaya mishi har ya haɗa su da Baban suka yi magana, Alhaji ya jaddada mishi gobe tafida zai zo kuwa. Sannan Baba Bulama ya ce mishi. "Zasu zo tare da Ummun In sha Allah!" Koda Baba ya dawo haka ya sami Mama da maganar, bata ki ba ta gaya min, na dauki kayana kala biyu domin Baba ya ce na kwana a can ranar daurin Aure za a wuce da ni gidana. Mama kan bata so haka ba amma yadda Baba Bulama ya fada bata kauce zancenshi, haka ni da Uwani muka shirya domin ban yi a raina Aliyu zai zo ba. Haka na kwana ina juya zancen, da safe wurin karfe takwas sai ga sallamarsu har cikin gida suka shiga suka gaida Baba dasu Ummi da Umma, yan matan da suka.fara zuwa hidimar bikin da yan uwan Mama sai aka fara surutu dama wannan Ummu zata aura. Lokacin da ya iso part dinmu ya samu Mama tana ta lissafin kayan abin da za a sayo a kasuwa. Cikin sakin fuska Deen yake gaida kowa yana me godiya da fatan Alkhairi. Shi kan ina hango shi ta window yadda yake yiwa Mama wani irin kallo irin na renin hankali. "Aliyu kake ko? " ta nuna Deen girgixa kai yayi yana murmushi yana nuna tafida da ya sunkuyar da kai kamar mutumin kirki, "Allah ya shiga lamarinku bakiɗaya ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyiba! Ku tafi kada rana tayi muku!" Ta fada tana me kallon Uwani da ta fito dauke da jakarmu. "Uwani maza ta fito ku tafi!" Ina jinsu, sai da Uwani ta kara kirana na fito ina me zama a kusa da ita. "Mama!" "Meye kuma Ummu? Bana sallame ki ba!" A hankali na gyada kai zan yi magana kuka ya kwace min. "Mama idan nayi miki wani laifi don Allah ki yafe min, ki saka min albarka kamar yadda Mahaifiyar Nana Mariam ta saka mata don Allah ki albarkaci rayuwata da yawun bakinki, Mama don Allah ki yafe ." Cikin dauriya ta ce min. "In sha Allah ko kare kika rike Ummu sai ya miki biyayya sai ya soki domin Allah yana son masu biyayya ni kuma me zance bayan wanda kika min, Ummu idan har yawun bakina zai zama albarka da alkhairi in sha Allah babu abin da zaki tab'a Allah bai albarka ce shi ba, Ummu Hadiyya in sha Allah ba zaki tab'a baya ba sai gaba, kiyiwa aurenki biyayya ki kuma rike shi Ibada Allah zai cike miki duk wani gurbin da zaki rasa Ummu Hadiyya in sha Allah ba zaki tab'a danasanin auren nan ba, ko zaki yi na lokaci ƙalilan ne. Aliyu ga amanar Ummu Hadiyya, sannan zan gaya maka gaskiya idan ka sake wani abu ya rabaka da ita ba zan mata dole ba zan tsaya mata gabanta da bayanta, kai kanka da danginka xaku yi alfahari da samunta a matsayin Mata da suruka. Sannan ban da duka" d'ago kai yayi da sauri yana kallon Mama. "Eh ban da duka na fada maka, ka dake ta wallahi sai na rama mata." Sai kuma ta sake yar dariya kafin ta shafa kaina tana faɗin. "Gudaliyya ba zata yi abin da za a dake ta ba sai dai a rashin sani. Ku je Allah ya muku albarka!" Ina kuka haka muka bar gidan cike da soyayyar mahaifiyata itama ina barin gidan sai share kwalla take, tunda muka dauki hanya Deen yake tsokanata. "Yau naga shagwab'e Hajiya Ummu ba naji kina da kanne ba, Yan mata ina kune kannenta?" Tab'e baki Uwani tayi tana faɗin. "Idan shagwab'e Aunty Baby ya motsa ina ga ko yaron da aka yaye ya salama mata, ina dalili ya sani jin kishinta!" Uwani bata da mutunci, amma tana da kirki.
Garin Biu.
Anan Babana yake kasancewar shi, dan kabilar Babura ne, lokacin da muka isa gidan wanda Uwani ta sani amma ni ban sani ba, domin ban tab'a zuwa ba. Babban gida ne me cike da ahali. Lokacin da muka iso kofar gidan da jama'a tun kafin motar ta tsaya sai ga Babana ya taso yana me murmushi, anan na fahimci yanayin jikina daga gare shine, don ma shekaru sun ja. Bakine amma dogo kasancewar ni kuma Yar guntuwa, siriri ne amma kana ganinshi ka ga wanda ya wadatu da rayuwa me kyau. "Ummu Hadiyya;" ya bude motar cike da farin ciki da zumudin ganina. "Yarinyar da ta aka tafi da ita tana tsumar goyo yau gata mijin da zata aura ya kawo min ita. " ya fada cikin farin ciki da raha. Fitowa Deen yayi shi da Aliyu suka gaida shi, sannan muka shiga cikin bayan mutane na ta mika mana gaisuwa, sannan wasu sun ji labarin ai wanda yar shi zata aura wakilin shugaban kasa ne, Babana shine Sarkin noman biyu. Domin tun daga zauren gidanmu zaka fahimci Babana attajiri ne, don alkama ce aka yi ta jerata ya kai buhu sama da arba'in har sai da ta tab'a silif din zauren, da muka shiga babban parlour shi, ridine a cikin buhu har sai da ta cinye rabin parlour. Cikin murmushi ya ce mana. "Parlour yayi kaɗan ko? Tow ya za ayi store ya cika da kayan abinci, shi yasa aka saka wasu nan." Sannan ya kalli Tafida da yake ta kallon hoton parlour, kafin ya saukar da idanunshi ƙasa. "Yarona sannunka da kokari." Kafin ya ce min. "Tashi muje cikin gidan ki gaida iyayenki!" Haka muka shiga cikin gidan, a hanya na ga ana ta wucewa da tire manya-manyan ana wucewa parlour Baba da shi, dakin Uwargidanshi muka nufa tana ganina ta mike. "Ikon Allah! Yau ga Ummuna Hadiyya a gidan nan!" Murmushi nayi nan aka yi ta shigowa ana min Barka da zuwa ashe ni yar gata ce, na tuna lokacin da na tab'a tambayar Mama Ubana ta mare ni. Haka suka cika min gabana da abinci, Uwani tana tab'awa ta gudu gidansu. Bayan nayi sallah aka ce naje parlour Baba na tafi, nan baba yayi min nasiha tare da su Aliyu, wai zasu tafi. Bawan Allah nan da kokari yake domin kajin gida guda biyar manyan zakaru sai zabbi guda biyar da katon toron agwagwa ya saka musu sai madaran saniya danye da galan din zuma. Ya saka aka hada musu. Har wurin mota muka rako su bayan sun gaida yan gidan tare da bin gidajen Yan uwan Baba ya gaishe su. Cikin gidan na koma. Baba ya ce na zo parlourn shi muka ta hira, yana bani labarin kanshi da hotonsa lokacin yana aikin gwamnati. Da kuma dalilin rabuwarsu da Mama. Na sha kuka domin Babana yana son Mama har gobe, sannan yadda yake nuna min haka daga kalamansa na fahimta, yayi aure aure amma Allah bai bashi haihuwa ba sai akan Mama ita kuma bata sonshi haka Allah ya ƙaddara aka haife ni. Sannan ya ce min. "Duk abinda nake nima dominki nake yi. Kaf wannan hatsain da kome naki ne. Ni ban da wata bukata na dai ajiye su ne ko wata rana zaki zo ko ce min kina son wani abu, sai na fahimci Hadiza ta toshe wannan hanyar da zaki nime abu a wurina. Alhamdulillahi da bata miki rikon uwar wani ba, ta rene ki a matsayin nata amma naji ba dad'i da kika ki karatun boko!" Sosa kaina nayi ina dariya. Sallah ya tashe ni na tafi cikin gidan, abin da na fahimta suma gidan hidimar bikina ake, da dare sai sha biyu ya rako ni dakin Mamawo, uwargidansa na kwanta. Tun asubar fari aka fara hidima, bayan nayi sallah asuba aka ce naje yana kirana, ina zuwa ya zuba min kaya ya ce min. "Sunce aurin aure karfe sha daya ne ina son mu tafi ne yanzu domin mahaifiyarki ta bukaci a kai ki wurinta!" Girgiza kai nayi nace mishi. "Na rayu a gabanta, yau daya ta bar ni ka raka ni ka ji!" Na fada ina kallonshi hawaye ya cika min idanuna. "Tow taya ni zabar kayan da zan saka to!" Wata farar gizne na nuna mishi wanda ya sha aikin hannu, ya ce min. "Shi kenan!" Haka na fito ina jin shi yana fadawa Mamawo. "Idan an daura auren zan gaya muku sai ku taso! Ina Ummu Hadiyya!" Na fito ina faɗin. "Na'am baba!" "Yawwa babu abun da kike bukata ko? Mamanku zata baki sako zamu tafi Allah ya miki albarka." Gyada kai nayi kaina a kasa. "Allah ya tsare!" "Amin Ya Allah " suka fita, ina komawa ciki wata yar Kanwar Baba suka zo da Mai lalle, ta zauna da min ja hannu da kafa, yarinyar me suna Raliya ta ce min. "Aunty Ummu an miki kitso kuwa?" Girgiza kai nayi. "Zan iya bude kan?" Ya tambaye ni, murmushi nayi na ce mata. "Aljanuna zasu tashi!" Dariya yayi tana faɗin. "Sai mu musu turaren barkono!" Zame hular kaina tayi tana faɗin. "Masha Allah!" Ba kome ya saka ta fadar haka ba, sai yawan gashin da Allah ya min wanda na fahimci zuriar Babana ne na gado, domin Babana gashi har wutar shi alamar genen dinsu yana da karfi. Itama Raliya tana da gashin. "Yanzu haka zamu kai ki babu gyaran gashi wannan amarya da kayan ban mamaki kike! Bari na kira Bintu me gyaran gashi ta gyara kan nan!" Ta fada tana zungure kaina!" Can sai ga matar tazo sai dai ba wuta. "Mamawo a saka mai a inji a gyara mata gashinta!" "Ki kira Sama'ila ya tashi injin akwai mai ai ko jiya da ita aka kwana!" Man wanke kai aka saka domin ta tambaye ni relax nace mata a'a don haka man gyaran gashi aka dauko na kayan auren Raliya sai mamaki nake ina son magana ta hanani. "Zan gayawa Baba Malam zai mai da min wasu balle ma idan auren yazo zai min wasu kayan, kema ai an bada kudin kayanki tun da aka fadi maganar aurenki idan zamu kai ki za a kawo kayan." Murmushi nayi domin na fahimci Babana yana son ganin farin cikin duk wnada yake tare da shi. Kafin karfe goma an wanke min an ja min gashin, sannan na gaban goshina aka gyara min su tass.
--- A Maiduguri tunda Aliyu suka dawo yake wani niman hanyar rigima, Deen ya kyale shi yayi yadda yake so, a parlour Hajiya shuwa suka hadu shi da su Maryam da Rukayya,sai zuga shi suke akan kada ya sararawa Yarinyar. "Yar matsiyata kin ga wani gidan da muka je ban da noma babu abinda ake yi!" "Ayya My Son bana son abin da kike yi, tunda Alhaji ne ya zab'a maka ita haka zamu riketa hannu bibbiyu."
"Haba Mama waye zai yi farin ciki wannan auren ga Sa'adiyya Yar dangi waye zai ji dadin auren Aliyu da yarinyar kabilu ne fa!"
"Allah yasawa auren albarka!"
"Ya kike son kawar da zancen Sa'adiyya idan aka kwana biyu dole ya auri wacce muke so, wallahi ba zamu tsaya muna kallon ki gama wahalar shi wata can ta more shi, ko Hajiya albarka abin da kika yiwa Aliyu Allah ne kaɗai zai biyaki!" Inji Rukayya. Haka suka gama zuga Aliyu ita Shuwa tana dai gefe amma ranta yayi dubu ya b'aci, tunda Deen ya shigo da kayan da aka basu Alhaji yake kara jadaddawa Deen ya taya shi rikon auren Aliyu ya saka idanun a kanshi.
Biki me sunan biki aka yi a gidansu Aliyu, a ranar asabar al'ummar musulmi suka shaida auren Aliyu da Ummu. Wanda ya samu halartar manya mutane, yan siyasa, mai martaba shehun Borno, a wurin aurin auren Baba Bulama ya gabatar da Baban Hadiyya ga Abban Aliyu abin mamaki, sai gashi ashe abokai ne da suka yi barewa College, sai kuma lamarin ya koma na zumunci, aka yi ta tattaunawa har shi kanshi Shehun Borno ya san Baban Hadiyya Alhaji Kabir Biu. An yi daurin aure an tashi taron lafiya.
-
Tun karfe daya na rana, aka gama shirya kome tare da zabar mata hudu da zasu rako ni. Sai Raliya Uwani haka muka taso har da Mamawo da karfe shida muka iso sannan aka sake shirya tafiyar aka kawo ni gidansu Aliyu da yake Polo.....
N500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
Paid book
11
Zan iya cewa dukkaninmu a wannan duniyar muna da kalubalenmu, sannan kowani mutum da nashi ƙaddaran nawa shine ya hankad'oni duniyar Tafida, tun kafin mu iso an gyara inda zamu zauna da abincin da zamu ci babu abin da muka nime tunda muka iso domin wasu mata biyu daya me yawan fara'a ce, tana da matsakaicin jiki. Sai daya da babu yabo babu fallasa, suka yi ta hidima damu sannan a bangaren guda akwai wasu mata biyu da suke ta shiga da fita. Wanda suka juya harshe shuwa, don ma akwai masu ji musamman Kulsum da take auren shuwa, a take ta fara shan jinin jikinta tana kallona. "Aunty Baby wannan dangin Mijinki suna maraba dake kuwa?" Bance kome ba kaina a sunkuye. Haka suka fita babu abinda muka tab'a sai sallah da muka yi Rooman ce ta kira Kulsum tana tambayarta batun dinner da aka shirya ashe ita mijinta can ya wuce da ita. Mu kuma nan an bar mu a zube babu wanda ya kara mana maganar fita wani wurin.
Shi da yan uwansa suke shirya abinsu lokacin da muka shigo lokacin suka fita wurin shagalinsu, inda suka maida wata wai me suna Sa'adiyya a matsayin Amarya.
---
"Mahmoud ina Deen yake?" "Hmm ina zan sani na kira ya ki ɗauka!" Tsaki yayi yana zaune a cikin motar, gefenshi Sa'adiyya ce ta cab'a kwalliya. "Muje idan kace zakai ta jiran Deen ranka ne zai b'aci muje next wifydinmu!" Inji Mahmoud, haka suka fito a motar rike da hannun juna, har cikin hall din. Inda yake cike da jama'a. Anyi hidima sosai, duk da haka hankalinsa baya kwance ya kira Deen ya kai sau dari amma bai dauka ba, karshe kashe wayar yayi abinsa. Rooman tana ganin abin da yake faruwa ta ja mijinta suka bar wurin sai fada yake tayi, ita kan bata ce kome ba. "Fisabiilillahi a rasa wanda za a bawa Aunty Baby sai wannan dan iskan Yaron mara mutunci wanda kowa yasan.kaf garin nan bai da da'a kaf gidansu babu wanda yake da bakin mutane kamar Yaron nan, rashin auren Baby ba yana nufin rayuwarta zata kare a haka ba ne Allah ya gani naji zafin wannan auren yaron nan bai da kunya." Ita kan bata ce kome ba,.har suka iso gidansu Aliyu. "Bappa zan kwana Please!" "Idan aka samu matsala ki kira ni don Baby zan barki amma.da wani ne ba zan barki ba!" Ita kan godiya tayi mishi tare da shiga cikin gidan, da taimakon Uwani ta shiga cikin inda muke, tana faɗin."Ban tab'a ganin aure irin naki ba, wallahi taya ga Amarya anan wata ta zama ke a can? Idan baya sonki me yasa zai yarda a aura mishi ke wannan cin mutuncin da me yayi kama?" Turo kofar dakin aka yi daya matar me fara ce ta ce mata. "Ba ance babu dinner ba?" Zata yi magana nayi saurin dukar gefen cikinta. Ashe matar ta lura. Murmushi tayi ta ce mata. "Anyi dinner ne?" Kallona Rooman tayi tana me kallon matar ta girgiza kai tayi. "Ba zaki fada ba kenan?" "Tow me zance? Amarya anan ango a can da wata mace? Yayata ce fa?" Rufe bakinta nayi bayan na cire mayafin . "Ya isa haka!" Na rungumeta domin kuka zata yi. "Me yasa daga kawo ki sai tozarci?" Inji Kulsum. "Don Allah ki bar maganar nan, don Allah?" Nasan zan ga abin da yafi haka amma bana son tashin hankali. "Kuyi min alƙawarin Mama ba zata ji ba!" "Munyi!" Suka fada har da Raliya da Uwani. Don iya su suka tsaya min. "Don Allah Hajiya a bar maganar nan ba wani abu ba ne da zai zama babba a wannan lokacin. Don Allah!" Na fada ina kallonta. Murmushi tai sannan ta ce min. "Sunana Hajiya Kaltuma nice Amaryan Alhaji Muhammad Jadda, na ji dadi da Aliyu ya same ki a matsayin Matarshi, amma ban ji dadin abin da ya faru ba. Kiyi hakuri da abin da zai biyo baya amma nima uwa ce ina da Yaran da na rike ba xan so ayi.musu abin da aka miki ba, sai da safe." Haka ta fita tare da barin dakin, rufe kofar nayi na zauna a jikin kofar na hade kaina da gwiwata, "Aunty Baby!" D'ago musu hannu nayi nace musu. "Ku kwanta kawai!" Na cigaba da zama a wurin. Ban san me nake ji ba amma har karfe daya na dare lokacin da suka dawo ina zaune a banki kofar dakin. Can naji ana ta fada a cikin gidan bakiɗaya, tashi Kulsum tayi tana me kallona har lokacin ina zaune. "Baki kwanta ba ne?" "Bana jin barci ne!" "Meke faruwa?" "Ban sani ba!" Tsaki tayi ta kwanta domin muna jin hayaniyar amma da kusan shuwa ake yinsa. Kuma muryan na mace ce ba namiji ba. Ban daki na shiga nayi alola na fito na gabatar da sallah ina sallah naji ana buga kofar wurin karfe uku da wani abu. Haka na yi sallama na bude kofar. Gabana ne ya fadi nayi baya ina hadiye yawun bakina. "Fito munafika!" A hankali na ja kofar domin yayi maganar yadda iya ni zanji. Cafko hannuna yayi tare da fitar dani daga cikin gidan, wurin motar shi ya kai ni ya wurga ni cikin motar ya shiga. "Ke jakar ina ce? Ke wacce irin dakikiya ce dabba mara hankali? Matsuyaciya mara hankali har kin isa ki hada ni da mahaifina? Wallahi kika sake kuskuren shiga tsakanina da shi mutuncinki wawuya sakarya dabba kawai" tunda ya fara zagina kaina a sunkuye yake ban iya motsawa ba domin ji nake duniyar tana min yawo. "fita min a mota tinkiya kawai!" Wani irin zazzaɓi ne ya rufe ni, Dakyar na bude motar na fito jikina yana rawa, ga sanyin alfijir da ya fara ketowa wanda ya haɗa min wani irin zazzaɓi da tashin tsigar jikina. Dakyar na koma dakin, ban iya kuka ba domin na nime kukan na rasa. Har aka kira sallah asuba ina zaune a wurin Dakyar na tashi nayi na koma na kwanta bayan na tashi Kulsum. Tun da na kwanta ban farka ba, sai karfe biyu na rana. "Amma lafiya dai ko?" Hajiya Kaltuma ta tambaye ni bayan na farka. "Lafiya lau!" Na fada ina gyara zama. "An kai miki ruwa ki shiga kiyi wanka. " haka na tashi jikina babu kwari, na wuce nayi wanka da alolan azahar na fito nayi sallah aka kawo min kaya na sakanOllfaya. Ina zaune aka kawo min abinci,kaɗan naci domin bani da dandano a bakina. Haka na ci na bar sauran, yamma can aka fara hidimar biki sosai a gidan, yan gidan mu duk sun iso dama tun bayan daurin auren aka kawo gara da yasa èduxl k masu adawa da lamarin a jikinsu yayi sanyi, a da can shi yaso ya kama haya ne amma Abbanshi ya hana ya ce ya fara xama a gidan ya ga yanayin zamanmu, dangin Mama da yan uwa babana sun zo a kai ni cikin gidan wurin Abba, bawan Allah nan dattijon kwarai ne, domin ya amshe ni hannu bibiyu sannan ya hada ni da matanshi biyu hajiya Salamatu da Hajiya Kaltuma. Sannan aka fito dani aka yi budar kai. Anyi hidima sosai wnada yasa abin da Mama tayi ita da Mijinta da Mahaifina ya kashe karfin zukatar yan uwansa. Sannan aka dauke ni zuwa bangaren da zamu zauna wanda tunda aka yi jere babu wanda ya kara shiga sai yau da za a mai dani bangare na. Anyi hoto ko nace ni nayi nawa da yan uwana da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 17