na tafi na bi yan gaisuwa. Na bar masa Matarshi a lokacin sun tafi yawon campaign, tunda na isa a matuƙar wahale, haka ta tsaya a kaina duk da itama bata da lafiya, ba karamin tausayi ta bani ba Allah yasa nazo da kudi, Yaranta mata kamar ba Uwarsu ba. Tafida baya gari lokacin da ya dawo yaji labarin na tafi ranshi ya b'aci . Yana kirana na ce mishi. "Kazo ka ɗauke ni kawai idan kayi niyya!" Kamar wanda na bashi umarni ranar addu'ar bakwai ya shigo cikin gidan. Ina zaune a wurin suyar masa, ya shigo ya zabga min harara. "Wannan uban nisan kika kwaso katon cikinki salon ki haifa min Yara a gefen titi ko? Ummu baki gane condition dinki bane? Fisabiilillahi idan wani abu ya same ku fa? Kin san yadda aka yi na dauki kwanaki ina zulumi? Idan wani abu ya same ki ba zan yafewa kaina ba, kuma wallahi ki daina min shishigi!" Kuma kada kuyi tsammanin a kebe yake maganar nan. Deen yana bayanshi yana murmushi. "Ummu don Allah a me kika bashi ya zama bita-zaizai haka?" Yana dariya. Ni kan kunya ya kama ni, na tashi da kyar ina faɗin. "ku shiga Hajiya tana ciki, zan kawo muku abincin karyawa." Riko hannuna yayi yana faɗin. "a'a muje ki zauna ki huta waye ya sani ko tun zuwanki kike musu aiki!" Ya fada yana hararata. Har cikin dakin na kai su suka zauna suna gaida Hajiya na fita na fara hada abincin yan uwansu da suke abokan wasa Sai tsiya suke min. "Ummu gaya mana gaskiya me kika bashi ya sha!" Dariya nayi na zuba musu kunu da masar. Na kai dakin, sannan na fito na dauki miyar da haka kawai nayi tun jiya ina fatan kada ya bani kunya Tafida yaki zuwa. Cikin hukuncin Allah sai gasu da safe sun shigo ashe tun daren jiya suka shigo. Sai nafi Hajiya Murna, kallonshi take cike da so da kauna. Bai tab'a zuwa ba ko wancan zuwa da yan uwansa suka zo bai zo ba. Yana cin abinci Rukayya ta shiga. "Tafida bamu da kudin mota. Ko zaka taimaka mana ne?" "Rukky ina zaki kai kudi ne? Ina baki kudi amma kamar ina baki kasa? Fisabiilillahi."
"Shi kenan kada ka bani ka kunyata Ni a gaban makiyana!" Murmushi nai tare da barin dakin ta ja tsaki. "Bana son haka, kada ki d'aga min hankalin matatta jininta ya hau." "Sannu yaushe ta samu zama a ranka!" "Aunty Rukayya kefa babba ce! Yarinyar nan tana mutuntatta ki sai zubda mutuncinki kike akan idanunta!" Inji Deen.
"Hmm!" Dake tana son Abu a hannun Tafida kuma tasan matukar yana tare da Deen baya barinshi haka sai ya saka yayi mata. Shigowa nayi da kofin tea har biyu na ajiye musu. "Gashi babu dambu nasan kana so da bread!" Murmushi yayi yana faɗin. "akwai sauran na ai na zo da shi!" Mika min key motar yayi ya ce. "Je ki dauko min!" Make kafadarshi Deen yayi yana faɗin. "Sannu uban yan son zuciya, tunda muka shigo take shiga da fita, dan banza zata kuma fita har waje tayi wani aikin!" Karban key din yai ya fita. "Ayya Yayana da ka bari na tafi na dauko!" Haka ya share ni, ya dauko bokitin, yana kawowa na zuba mishi na raba biyu na bawa Hajiya tayi ta godiya. Bayan la'asar aka yi addu'a, tun da yazo muka kebe na mishi magana akan Hajiya itama bata da lafiya. Ya share ni. Jan hancina nayi ya d'ago kai yana kallona. "Yaran Dady kun ga zata fara ko? Ni dai ban mata kome ba kawai ita ce dai da rikicinta." Ai kuwa na fashe da kuka, "ya isa me kike so?" "Abinci da kulawa kaga mijinta yanzu baya raye sannan Yarann sabira zata rike su a rage mata dawainiyya!" Sosai goshinsa yayi yana faɗin. "hmm! Naji!" Ya fada yana mikewa. Ya dawo gabana ya durkusa yana kallon cikina. "Yarana kuna kewata ko?" Ya fada yana shafa cikin. "Zan kawo Nanny har biyu su taya ki reno, domin naga ke baki da lokacin kula dasu. Sannan ba zasu sha nono ba saboda!" "Saboda ni yar karamar gajeruwar mace ko?" "No ba haka ba ne!" Hmm Tafida ba zai tab'a canjawa ba. Haka na gayawa raina ba zai canja ba.
Haka muka kwana da zan fita ya mika min kuɗi yace min. "Wannan ki bawa Hajiya, wannan kuma ki bawa Rukky!" "Allah ya saka da alkhairi!" Na fita na nufi cikin gidan, na samu suna ta mita. Mika musu kudin nayi na nufi Hajiya na mika mata nata, na ciro wanda na riko mata na mika mata. "Hajiya xan bisu ya ce, Allah ya ƙara miki hakuri!" Godiya take min kamar ta durkusa min. Muna haka ya shigo ta kalle shi a raunanane ta ce mishi. "Allah ya saka da alkhairi! Na gode Allah ya biya maka bukatarka na alkhairi ya baka sa'a da nasara akan abinda kake nima, ka rike Ummu mace ce ta gari tana da mutunci kuma ta fito daga gidan da ya dace kayi hakuri Baba Ali kayi hakuri da yan uwanka kai ne karami kai ne babba Allah ya baka matsayin ne don ya jaraba imaninka!"
"Amin Amin Amin!" Deen yake faɗa yana kara fada "Tafida ni gaskiya ku xan bi ke bashi kudinsa" inji Aunty Maryam, itama Rukayya, haka ta hakura amma ta ki bada kudin, ya ce musu. "Kada ku takura mata domin ni gaskiya muje tasha nayi shatar mota ku tafi ni kwanciya nake son tayi saboda Yarana." Ai kuwa tashar ya kai su tare da ɗaukar musu mota nasu iya su, haka muka bar garin cike da kewar Hajiya. Maryam bata so ba don haka ta gayawa drive yayi ta bibiyar su Tafida. Haka kuwa aka yi duk inda aka tsaya sai sun tsaya domin ayi musu abinda ake min. Haka muka shigo Maiduguri ya kai su gidajensu.
Lokacin da muka dawo Abba da kanshi ya zo gaida ni, nayi ta dariya ina faɗin. "Abba na dawo babu tsaraba!" "A'a da kika dawo lafiya ma ai arziki ne!" Haka ya gama gaida ni ya fita. Bayan na dawo na zata zan huta ashe ba haka ba domin kuwa Sa'adiyya da Uwarta suka saka ni a gaba, na farko cikin ya hanani barci, haka yasa cikin dare zan ga Sa'adiyya ta shigo dakina tsirara musamman idan baya gari, ganin haka na fara daina barci nima sai na maida hankali wurin raya daren, amma a haka nake jin kamar na bar gidan. A hankali na je na gayawa Mama ranar a naje awo nace Sagir ya kai ni gida, lokacin da muka isa Mama ranta ya b'aci don bata son alaka.da nake da yan uwan Babana. Da na kwanta ina nishi. "Mama bana son tashin hankali, amma ina ganin ya dace ki tsaya min na samu yancina, Mama gidan Tafida jin shi nake kamar wuta ake hura min wura min." "Nayi miki alkawarin tsaya miki gabanki da bayanki, amma dole kiyi hakuri." Wannan shine karo na uku da take min alƙawarin. Sai yamma da suka dawo campaign yazo ya dauke ni, yana ta Godiya. "Wai Ummu meye matsalarki ne?" Ya kalle ni yadda na lalace!" "Zaman gidan ne bana so." Shafa kaina yayi yana shiru kafin muna isa ya raka ni cikin gidan, sannan ya wuce wurin Abba, ban san me ye matsalar ba sai dai tun ranar ya fara kawo min ruwa a goran swan yana kawo min, ashe rubutu ake da Farin zuma ana wankewa da ruwan zam-zam. Tunda na fara sha barci ya fara zuwa min, ina hutawa shima ya rage yawan tafiyarshi, sannan cikin dare zai dawo ya kwana a gida domin lafiyar cikina.
Ana haka zabe yazo aka yi cikin kwanciyar hankali aka fara na shugaban kasa, sati biyu a tsakani aka.yi na gwamnonin. A nan Borno Tafida da wani Yaron Alhaji Mansur Goza aka yi takarar kuma Allah ya ba Tafida sa'a. Koda yake Sa'adi ta fita campaign amma ni ko waje ban fita ba, wani labari me dad'i shine yadda yan ƙaramar hukumar biu suka zaɓi Tafida saboda yana aurena. Tun daga nan Tafida ya kara ganina da kima. Tun da aka fitar da sakamakon nake nakuda a tsaye, mun yi sintirin asibiti har na gaji. Haka muka hakura jiran ciwon.
Wani abin mamaki kiri-kiri yan uwanshi da wanda suke uba daya suka koma gindin Sa'adiyya, musamman yadda ta fita campaign sai suke ganin ai ita tafi dacewa da zama First Lady, ni dama bai dame Ni ba ina dalili. Tinah ta kirani tana taya ni murna, a wannan lokacin Abba hakuri yake bani domin tunda aka ce shi yasa ci ya dan rage bani lokacinsa. A haka Shuwa tana ganin kamar sun shiga tsakaninmu ne.
A hankali kome ya zo karshe zuwa daren da za a kawo ni asibiti, yaso ya gayawa yan gidan nace a'a muje kawai. A lokacin da muka je Dr Sagir baya nan. Nabila ne a daren har wurin asuba kafin Allah ya sauke ni lafiya..
****
Dawo labari
Ajiyar zuciya na sauke ina jan kukan da y zo min, "Wai Ummu saboda nace ki koma dakinki kike wannan kukan? Ummu idan don haka ne Ummu ki zauna muna goga kafada da kugu wuri guda, kowa yana dakinsa yana rufawa kanshi asiri ke zaki tona min asiri a saka ni a gaba da habaici da gori?" A hankali na bude idanu na kalleta, kafin nayi magana ta dasa da cewa. "Ba zan takura miki ba, amma ki sani har abada ba zan tab'a farin ciki ba idan kika kashe aurenki!" Tashi nayi zaune idanuna sun yi fulu-fulu, don kumburi gashi babu barcin da nayi, hasken da nake gani ya fara daukewa a hankali na dunguro daga gadon ai kuwa ta sake salati.......
*Wash hannuna! Anan na kawo karshen free Page na labarin Ummu da Tafida! Hmmm Ga Ummu Hadiyya ga Tafida mai girma Gwamna! Wannan ba labarin soyayya ba ne kamar yadda kuke gani labarin gidan aure ne da yadda ake gwagwarmayar gidan aure. Yes ba labarin da zan cika ku da soyayya kiss! Sex scene da sauransu wani bangare ne na wata rayu idan har soyayya zata biyo baya tow ba mamaki farin ciki zata wanzu a zukatan masu hakuri da Imani! Ina labarin Mahmoud? Shin ya hakura da kudirinsa ko har yau yana bibiyar motsin Ummu! Shin Ummu zata hakura ta koma dakinta ko zata rabu da Tafida kamar yadda ta ce! Shin Tafida zai sake ta kuwa ko zai cigaba da riketa kamar yadda ya fada, Mahmoud zai samu biyan bukatarshi akan Ummu kuwa! Ya Tafiyar Sa'adiyya da Yan uwan Mijinta? Shin zasu dawo jikin Ummu? Ya Mahaifiyar Tafida Ummu zata iya dawowa Hajiya dan ta kuwa? SHIN AKWAI SOYAYYA? INDAI AKWAI SHIN WAYE ZAI iya amayar da nashi don.a koma sabuwar duniya! Tafida zai iya rike Borno kuwa a matsayinsa na gwamna! Sa'adi ta saka smarty ya lalata fake soyayyar Ummu da Tafida shin wai me zai faru? Hmmm wannan labarin ko? Ban yi kome ba domin idan tafiya yayi tafiya gumurzu zai fito rikici da soyayya zai jagoranci Yar Mace, wacece Yar macen nan ne?......*
TAFIDA
UMMU
DEEN
MAHMOUD
SA'ADIYYA ...... ALL IN YAR MACE kowa da kuka gani zai taka nashi matsayin don haka ku biyo alkalamin Uwar Muwaddah Ammyn Anum! Mai rikon Walid 😂🐐🤣
500
NE MALAMA IDAN KIKA GA LABARIN NAN A WAJE TOW SATOWA AKA YI Yawwa na gaya muku na kudi ne..
Zan tafi hutu sai Friday zan cigaba in sha Allah....
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76https://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw
*R&U BAG's GALLERY! Wai da gaske kun manta ne na gaya muku? Tow R&U ta kara dawo muku da kayan ado da kawwa wanda Ummu First Lady take amfani da su, tow dai Ummu tace na gaya muku a sirrince! Kawo kunnunku 🙉 a wannan R&U BAG's GALLERY babu abinda babu domin kamar kanti kwari ne a gidanki! Muna da kaya irinsu Atamfa, lace, shadda! Karewa dai har da lefe, kayan fadar kishiya, kayan Fitar suna na mai jego, kayan toshi na wanda saurayi zai kaiwa budurwa! Waya miyar sai a mota, muna bada dai-dai har da sari ku shiga domin tabbatarwa idanunku*
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 17