Share this page
komawa bakin gadon nayi na zauna tare da saka hijab dina. Cikin wani munafukin na nutsuwa ya zauna yana sunkuyar da kai wanda a da can wani gani gani yakewa dakin idan muka zo, sai yau naga akasin haka. "Mama don Allah ki ce ta amshi yaran wallahi an kusan!" "A'a ba sai kun had'a ni da Alla ba ai bata kyauta ba, kawo su ku tafi kada a makara." Ta amshi yar hannun Safiyyudeen din ta kwantar da ita sannan ta mika hannu ta amshi Namijin da yake kwance a faddadar kirjin shi. "Don Allah ki roke ta, ta koma kafin ayi bikin shiga gidan gwamnati!" Ya fada yana mikewa cikin sanyin halin da ban san yaushe ya dauko shi ba yo ai ba halinsa ba. Kasa-kasa nace. "Sai dai a kai gawata gidanka, wallahi ba xan koma ba!" Nasan zai ji kuma bakiɗaya ma nasan zasu ji, na dauke kai kamar bani nayi maganar ba. Wayar Safiyyudeen ne yayi kara ya ga Mahmud tsaki yayi yana faɗin. "Muje!" Dakyar ya iya fita yana jin kamar an sauke mishi nauyin da yake kanshi. A gurguje suka nufi filin da za a rantsar da shi, daga shi har Safiyyudeen babu me damar magana hankalin kowa a tashe yake domin gani suke kamar an mishi wani ne. Gyara murya alkalin alkalai yayi sannan ta shiga maimaita alqawarin da rantsuwa da Aliyu Muhammad Jadda zai dauka, ya sha fararen kaya kanshi sanye da wata bakar hular zanna Bukar da tasha aiki me kyau, ana gama rantsar da shi ya shiga motar gwamnati kamar yadda kowani gwamna yake. A fusace Mama ta nuna min Yatsa, "kada ki sake fushina ya kwace akanki, kika sake raina ya b'aci zaki ga ba daidai ba" a matuƙar tsorace na hadiye duk abin nake ji na koma na nutsu tare da kame kaina Mama bata daukar reni tana cikin iyaye marasa daukar iskancin Yaransu. Fita tayi amma bakiɗaya ranta a b'ace yake haka ta hado ruwan zafi ta kawo dakin Allah Sarki Uwa me dad'i, hatta sabulun wanka ta hada, "Assalamualaikum, Hadiza ashe an kawo Yaran?" Inji Umma, murmushi tayi tana me faɗin. "Eh gasu nan zan wanke su." Waye bai san halin Umma ba wurin had'a wuri da son bin didigi, "Kai Hadiza ina laifin ki ce ni ko Yaya wata tazo ta wanke Ummu Hadiyya da jarirai ke da kanki zaki yi haka?" Cikin ko in kula ta ce mata mata. "Yanzu aka min jika abin cikin kwai, yafi kwai dad'i!" Daga haka Umma tayi turus, "Allah ya huci zuciyarki!" "Ai ba fada ba ne!" Mama ta fada tana cirewa Macen kaya, ta fara shafe ta da lalle da ta kwab'a da tazargaje, ta maida ita cikin abin ɗauka ta rufeta, sannan ta koma wurin wurin namijin shima haka ta shafe shi tas, har lokacin Umma ta gagara jan kafa ta bar dakin. Domin bata tab'a kawowa Mama zata gaya magana haka na. "Ummu babu inda yake miki ciwo?" Girgiza mata kai nayi sannan ta juya yana faɗin. "Sannu da arziki ashe har yan biyu ne." Gyada kai nayi a kunyance, fita tayi can bayan fitarta Mama ta dalla min harara. "Wallahi da kin sake wani ya san bar mishi Yaran kika yi da na sab'a miki!" Shiru nayi ban ce kome ba, saboda nasan zata iya nad'a min duka wallahi. Tana rufe bakinta sai ga makota sun fara shigowa. "ashe Ummu Hadiyyarmu ta sauka lafiya?" Murmushi Mama tayi domin Mama me Jama'a ce kuma Allah ya bata jama'a don haka ta ce musu "Eh wallahi!" Ta nuna musu Yaran da take gyara su, yadda Mama take hidima kawai ya saka ni jin tabbas ta jima tana shiri ba na wasa ba, domin tsakaninta da Allah take kome, kafin zuwa azhar gidanmu ya cika da yan barka da yan Allah ya sanya alkhairi. Wato a a tayani murnar samun nasarar da Tafida yayi har yau an rantsar da shi. Murmushi nake domin basu san me ke faruwa ba, da an buga ni a jarida. "Assalamualaikum!" Mama da take tsakar gidan ta amsa tana faɗin. "Malam Mudan!" "Na'am Mama, ga kayan Hajiya Ummu da wayarta." "Masha Allah, ka kyauta wallahi!" Zata amshi kayan Zakiya da itama shigowar kenan daga kofar gida ta amshi kayan tana faɗin. "Mun gode, Mudan yanxu dai zaka koma Government House kenan?" "A'a Hajiya Zakiya ina nan daram a tare da Hajiya Ummu!" "Lallai na zata can zaka koma ai." Dariya yayi yana faɗin. "A'a babu inda zani!" "Mudan kyale magananiya ga abincin nan!" "Hajiya Mama kin san gidan ana ta hidima Hajiya Maryam ta haɗa min kayan naci abinci." "Tow shi kenan." Sallama yayi na leko ina faɗin. "Mudan ka rufe min store dina!" "In sha Allah" ya fada yana me barin gidan. Mika min jakata Zakiya tai na na amsa ina bude jakar,wayata ce Samsung series X ina kunnawa na ga babu charger. "Zakiya?" Na kirata. "Na'am Aunty Ummu!" "Don Allah bude akwatin nan akwai power Bank a ciki bani!" "Tow!" Ya zuge akwatin na ciro, ta mika min ina sakawa a charger kamar abin munafunci sai ga kiran Tafida. Kamar ba zan dauka ba. Jin wayar tana ta ringing ban dauka ba, ta shigo dakin. "Kanki daya kuwa? Ba kiranki ake ba?" "Ayya Mama kin ga abin da nake yi basu mama nake fa!" Na fada kamar zanyi kuka, "kowa rai ya amfana baya ga me shi ne!" Daga haka ta fita wayar ya kuma ruri. Dauka nayi a fusace na ce mishi. "Me kake bukata?" "Ko ki kira ni!" "Akan me zan kira ka meye matsalata da kai da har zan damu kaina da kiranka!" Murmushi yayi sannan ya ce min. "Matsala ai babba ce tsakanina da ke, dama na kira naji yaushe zaki dawo ayi suna a government!" Ya fada a cikin sanyin murya da ni bako ne a gare ni. "Da bance ka zo ka ɗauke kayanka da ka kawo min ba?" Wani shiru yayi kamar baya rike da wayar na cigaba da cewa. "Idan ka sake raina ya b'aci kotu ce zata raba ni da kai." "Ummu Hadiyya duk akan me yayi zafi?" "Na gaya maka zama da kai ne ya kare ka fahimta mana!" "Ummu Hadiyya ni fa ban san me nayi kika dauka da zafi har haka ba." "Zaka sani daga baya!" Na kashe wayar har yanzu wani irin b'acin rai nake ji domin kaf wayata babu wanda ya kira ni a gidansu Aliyu Tafida ya min barka haka ya tabbatar min suna tare da Dan uwansu da Yar uwarsu, kuma nasan koda ina gidan haka zasu cigaba da harkansu babu wanda ya damu da ni. Murmushin takaici nayi ina kallon Yaran, wayata tayi ƙara dauka nayi ganin Kulsum. "Aunty Ummu Hadiyya ashe kin sauka." "Hmm eh Kulsum!" "Wayyo Allah nan nesa bata maganin kusa kamar nayi tsuntsuwa na zo na ga Aunty baby da Jaririnta kin san ma a ina na gani?" "Sai kin fada tsikallazi!" " A status din Mai girma gwamna, ya saka tare da cewa My beautiful kids from first lady!" Tab'e baki nayi ina cewa. "Sai dai wata faisi ladyn ba dai jinin Baburawa ba!" "Kai Aunty Baby!" "Meye nayi? Daga fadar gaskiya wallahi kuwa zai aiko min da takardana!" "Ba ruwana!" Jin ana kiran wayar nace mata. "Kashe Father inlaws yana kirana!" "Tow Maman twins daga Aunty Baby zuwa Maman twins!" Tana kashewa ina daukar kiranshi. "Abba kayi hakuri!" "Yarinyata ke xan bawa hakuri ashe babu wanda ya zo ganinki? Babu abin da aka kawo miki? Yarinyata wacce irin rayuwa kike yi ne haka? Kin ga haka abokiyar zamanki take yi ne?" Kafin nayi magana Hajja Ganaah ta ce mishi. "A'a Jadda kar ki ga laifin Yaron nan Hadiyya mutum ce guda, Yaron yana da kawaici kawai iskancin yan gidanka ne su ya dace kiyi musu fada ba Yaron nan Hadiyya ba, kuma kin ga hankalin kowa ya tafi wurin bikin rantsar da Tafida shi yasa aka manta.", ai kuwa ina ji ya juya mata kanuri shiru yayi domin a fusace yake, "Ga sako nan na turo zuwa an jima xan zo da kaina.;" "Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana, Allah ya biya da gidan Aljanna!" "Zan zo na ga yaran kin ji!" Nan ya shiga bani hakuri dama fa haka yake, Tafida da laifi shi da bada hakuri. "A'a Abba wallahi babu kome!" Kai mutumin nan da girma yake. "Na gode sosai! Allah ya muku albarka sai na zo!" Haka muka yi sallama na ajiye wayar kenan sai ga Kiran Aunty Maryam na dauka. "Ashe kin sauka lafiya!" "Eh wallahi!" "Tow sannu!" Ta fada a dakile kafin ta rufe baki na ce mata. "Yawwa!" Na kashe wayar, sake kirana tayi na dauka tare da cewa. "Kin yi mantuwa?" "Ban yi mantuwa ba, kada ki ga don Abba yana wani ji da ke ki dauka wata tsiya ce, domin talaka bai iya samun wuri ba!" Dariya nayi irin na cusa haushi nace mata. "Ke Yayar Aliyu ce shi yasa ba xan gaya miki me zafi ba, amma idan da gaske kina tare da dan uwanki don Allah ki ce mishi kafin faduwar rana zuwa hudowar na gobe ya sauke igiyoyin da ya zame mishi alak'ak'ai ya huta kuma ku huta da bakar kaddara!" Kafin ta gaya min abin da zai hana ni barci na katse kiran tare da sakata a blacklisted kowa ya huta, nasan ba irina suke bukata ba, shi yasa duk abin Tafida yayi min basu gani asalima gani suke kamar an tauye mishi hakkinsa na aura mishi. "Mama Amarya ga wata a kori kura da kaya wai an kawowa Aunty Hadiyya ne!" Shiru nayi ina zare idanu, bankado labule tayi na fara kokarin ajiye Jaririna zan mike. "Ban fahimci me Yaron nan yake faɗa ba?" "Dama-dama, Abban babansu twins ne ya ce za a kawo kayan abinci." Wani kallo ta zuba min na fara rantsuwa. "Wallahi ban roka ba." "Kada ki tara min mutane." Ta ja mayafinta, ta yafa sannan ta ce min. "Kika sake wani abu ya dawo daga hukuncinki wallahi zan saka kafar wando daya dake." Hadiye yawu nayi na wuce ban dakin da yake cikin dakinta na dawo dakin na tsiyayyi ruwan flast na wuce, Tabbas Abba ya turo da kayan abinci, babu abin da babu kama giron kunu, buhun sugar, katon din madara da Ovaltine, shinkafa, alkama, man gyada manja, da Naira dubu hamsin, wai a gaya min gobe za a kawo nama. Koda aka shigo da kayan, Hajiya Balki da Umma suka shigo. A fuskar Hajiya Balki da na hango sanyi na gaisheta. Cikin kulawa ta ce min. "Sai gashi har biyu kika haifa da kanki?" Komawa kujera nayi na zauna, domin girman Hajiya daban ne. "Kin zama Maman Yan biyu, bana nan tun asuba muka tafi gidan Taima kin san abin sai a hankali zama yaki dad'i kuma Babanku yaki magana akai shi yasa naje tun lokacin ina can. Ina dawowa Kawu Gwani yake gaya min kin haihu. Ikon Allah muna ta al'ajabin wannan cikin naki ashe kyautar Allah ne awurin." "Ya su Taima din da Yaranta?" "Suna lafiya, al'amarin sai a hankali uwar mijin taki a zauna lafiya yanxu haka dakyar aka shawo kanta!" Naji babu dad'i sai dai ita sharri haka take, "Allah ya kyauta ya daidaita tsakaninsu." "Amin Ummu ki yafe mana, sannan ki zauna a dakin Mijinki wallahi Allah ne ya d'aga darajarki amma tabbas halin ki da na mahaifiyarku abin koyi ne!" A hankali na d'ago kai na kalleta kafin ta ajiye Yaran ta ce min. "Daga yau zan cigaba da musu wanka, jin Yaran nake kamar Yaran kawu gwani!" Hawaye ne ya cika min idanuna. Nasan Allah ya haɗa ni da kawu gwani tun farko amma da Allah bai nufa ba haka kome ya tafi da tarin zunubi marasa dad'i, "Ba kome Ummi!" Yadda Yaranta suke kiranta. Har zata fita Mama ta shigo da ruwan wankan Yaran. Ta ce mata."kiyiwa ma mijinki da kishiyarki ni zan yiwa Y'ata." Murmushi Mama tayi tana faɗin. "Oho wato ke nan me gudun dangi har zaki guji miji da kishiya ki gyara yarki!" Abin da daure kai yaushe Mama da Ummi suka shirya? Wai meke faruwa ne a gidanmu waye zai gaya min wannan labarin? Ummu Rooman, tabbas ita ce zata bani labari haka Ummi ta kwashe ruwa ta kai ban daki ta saka na fito tayi min wanka tas, har da jijiiga min cikina sai ga jini da yake damuna. Kafin na fito ta koma bangarenta, ina ga girkin daren da tayiwa Baba shi aka zuba min yaji man shanu gijib, aka Mahira ta kawo, sai sannan ta ga Yaran dake irin yaran nan ne masu rawan kai, amma.tana tsoron Ummi, ta shiga daukar Yaran a hoto sannan ta daura a story dinta, da faɗin. *Alhamdulillahi Masha Allah tuburkallah, Yaran mai girma Gwamna Aliyu Muhammad Jadda Bro Tafida!* Kafin wani lokaci an cika mata waya da kira ana tambayarta da gaske Matarshi ta haihu? Komawa Whatsp tayi ta ce Yes Aunty Baby ta haihu. Ta faɗa tana murmushi. "Aunty Baby ni fa xan iya dawowa nan da dama saboda Yaran nan, wai ma ya sunansu ne?" "Mahira kina babbar Uwa ina ruwana da su!" "Ok bari mu zabi suna masu dadi!" mama da take shafe su da turare ta ce mana. "Oho garin saye sayen suna sai kun sakawa Yara suna cokali!" Dariya Mahira tayi tana faɗin. "Wannan sunanshi Mufid ita kuma Mufidah. " "Oho idan kunso ku saka musu muzuru da magege!" "Kai Mama kishinki yayi yawa!" "Idan ban yi waje dasu ba ku ba dame ni da maganar kishi!" Ta fita tana murmushi. "Aunty Baby kiyi hakuri ban shigo ba na tafi school ne kuma na dawo na kama aiki kiyi hakuri!" "Ba kome Mahira!" Shigowa Mama tayi da tukunyar miya, ta ajiye ta zubawa Mahira tace. "Ki kaiwa Umminku da Umma!" "Tow Aunty Baby sai gobe don karatu nake sosai mun kusan Exam!" "Allah ya bada sa'a!" "Amin Ya Allah!" Ta fada tana me barin dakin, zuba min nawa tayi can su Zakiya da Uwani suka shigo. Suka baje a dakinta. Nan muka shiga hira, muna haka Baba yayi sallama. Duk suka mike tare da komawa can gefe, ciki ya shigo yana faɗin. "Haka kawai naji ina cikin farin ciki ashe Ummu Hadiyya ce ya sauka, Masha Allah Alhamdulillahi Ubangiji me kyauta da kari." Ya taka har bakin gadon ya dauki yaran yana musu addu'a. "Wato kun zo ayi bikin Babanku ko?" Kaina a sunkuye ya kalle ni kafin ya ce min. "Sannu Ummu!" Ni dai kaina a sunkuye. "Dazun Alhaji Muhammad Jadda yake gaya min, Ummu Hadiyya ta sauka sai da na kusan shigowa gari yake gaya min yana ta bani hakuri yanxu ma yace bayan Isha yana hanya. "Tow Masha Allah!" Haka ya gama maganar sannan ya ajiye su ya fita after kamar minti talatin sai ga Amiru da katon leda, gasashen kaza ne har uku inji Baba. "Amma Alhaji ko? Zai gamu da ni!" Ta fada tana me faɗin.."Uwani dauko min tire da flat." Fita Uwani tayi sai gata da su, ta baje mana sannan ta zuba min nawa naci sosai don ma bakina ba dad'i. Wurin karfe takwas sai ga Sako Baba ya turo a gayawa Mama Alhaji Muhammad Jadda yazo. Sai da tayiwa yaran addu'a sannan ta dauki daya Zakiya ta ɗauki namijin, Uwani da katon tire an saka ruwa da kayan sha. Aka kai musu Yaran, dake ya saba duk inda zai shiga da Kannen shi nan guda biyu. Ba'agwe da Abbalawan, sune suka amshi Yaran yana zaune a kusa Baba da ya ajiye mishi kayan marmari gabanshi. "Ina Yarinyata ba wurin wadannan naxo ba!" Abba yana cikin mutane masu dattako da daraja, shi hankaka ne mai da dan wani naka, kuma har yau haka yake. "Bari na kirata!" mama ta kuma fita muka tawo tare na sha uban lafayya. Ina shigowa na zube zan gaida shi ya ce min. "Kul koma kan kujera, danyen jiki ne dake zauna a sama, Hajiya shigo mata da takalminta!" Kallon Abba Mama tayi yayi murmushi ya ce mata. "ki shigo da shi mana!" Haka ta fita ta kawo takalmin, ya ajiye min sannan ta cewa Abba. "Alhaji baka bukatar wani abu ne?" "A'a Hadiza me zan bukata yau ango nake nayi sabuwar Amarya shar ke da Balki da Yahanasu na ja muku layi." Ai kuwa farlon aka saka dariya ta fita tana murmushi, "Alhaji Bulama kayi dacen mata, haka nake mafarkin Aliyu ya dace da Hadiyya,matukar wancar matar da ta fita ita ta haifi Hadiyya tabbas Aliyu ya dace. Alhaji ka bawa Ummu Hadiyya hakuri na sani,.kuma nasan zata cigaba da yi. Murmushi Baba yayi ya ce mishi. "Alhaji sha'anin Yaranmu sai Allah amma nasan zuwa yanzu kome ya wuce ai, tunda gashi har da zuri'a." Wai ma tukun bikon Aliyu aka zo yi wato gani nan sakarya shine da zo a bani hakuri ban gama nazarin haka ba naji Abbanshi yana faɗin. "Nayi mata alkawarin kuma zan sauka akan alkawarina ba, Allah ya mata albarka ta kuma cika yar halak, ta nuna min ita haifafiya ce, Ummu Hadiyya ki tsaya akan kalamanki Allah zai tsaya miki, zan kuma koma gefe na zuba idanu. Idan Aliyu Tafida yayi nasara akanki zan baki boye kaina idan kika kai shi kasa da shi da yan barandanshi nayi miki alkawarin tsaya miki kai da fata, amma ki sani sai kin zama jajjurtacciya akan kome da kowa, Alhaji Bulama kayi hakuri amma akwai banbanci da can baya da yanxu domin ina bayanta ne a yanzu. Wannan shine dalilin zuwa ta. "Na zata kome ya wuce Alhaji!" Girgiza kai yayi yana faɗin. "Yanzu ne mafarin.... Anya Alhaji Muhammad Jadda Uban Aliyu Tafida ne kuwa.... Me yayi zafi har da zai hada kai da Matar dansa? 🥺 08130269641YAR MACE....🌺 *Mai_Dambu* Paid book 03 Duk da dai ban san dalilin Abba nayi haka ba, amma naji a jikina tabbas ko Abba da Baba su tsaya min ba, wannan shine karshen zamana da Tafida domin a duk lokacin da na tuna abun ya faru a baya tabbas Tafida yana buƙatar space me girman gaske, yana bukatar na bashi wuri ya sha iska, don haka na sunkuyar da kaina kasa, har Abbanshi ya gama bamu hakuri ya cewa Baba. "Ka kira Mamanta su maida su daki." Ya fada yana kallon Yaran da yake jin wani kaunarsu kamar ya tafi da su. "Tow Alhaji Muhammad, ayi ta hakuri dai domin shi rayuwar bakiɗaya akan hakuri yake." Haka ya kira Mama a waya suka tawo suka dauki Yaran ni kuma nayiwa Abba da Baba da yan uwan Abba sallama, koda muka koma dakin Mama ruwan zafi ta had'a min na danyen gasarar kunu da ta zuba sugar da garin yaji, ta dauko min namar da Baba ya kawo ta kara dumamin, sannan ta ajiye min tana faɗin. "Kafin ki kwanta ki sha ana bukatar yaran su wadata da ruwan nono kafin gari ya waye." Gyada kai nayi na cire kayan jikina, sannan na maida wanda na saka dazun na fara shan ruwan zafin ina cin namar, hira suke tun ina jinsu har barci yayi gaba da ni, dake na manta da wayata ban kashe ta ba, wurin karfe daya na dare naji wayar na ƙara, a matuƙar gajiye na dauki kiran. "Ya kike?" "Gaskiya ka shiga hakkina akan me zaka kira ni daidai irin wannan lokacin? Fisabiilillahi baka gane kana cutar da rayuwa ne? Ka je Allah yana nan baya barci." Na kashe wayar bakiɗaya na kwanta. Dakyar nayi barci don ma Mama tana dakinsu Zakiya. *Aliyu Tafida* Yau duk wani hayaniya da aka yi tare da bidiri a kasan ranshi Ummu Hadiyya ce, domin a matuƙar dame yake ya rasa yadda zai yi ne, amma dake Allah ya daura mishi zurfin ciki da juriya yasa bai wani nuna damuwa ba, amma tsakani da Allah yana hautsine akan abinda Ummu Hadiyya take nima, wunin yau bai da nutsuwa ga bikin da aka yi, bayan rantsar da shi. Duk yadda yaso ya yi magana Safiyyudeen ya hana shi, koda ya kira Ummu Hadiyya ma yana cikin mota zasu koma gida ne su uku Tafida, Safiyyudeen da Mahmud. "Ummu!" "Tafida zuwa karfe biyu na rana zan zo na hada maka kayanka!" "Deen!" "Na'am!" "Ka wuce da ni gidansu Hadiyya!" "Dare yayi kai ka gaya min tun karfe daya na daren jiya take abu daya yanzu ta samu zata huta kace a tafi a tadda ita kai ka ce baka tab'a sanin haka Mata suke shan azabar haihuwa ba, ka san me? Allah yana sonka da rahama ne har ya nuna maka yadda mace take nakuda." "Amma me yasa.!" Kafin ya kai Aya Safiyyudeen ya dakatar da shi da cewa. "Kada ka manta yanzu kai ne gwamnar Jahar Borno wai ma Tafida yaushe ka fara kananun magana?" "Tun ranar da aka aura mishi wancan me siffar dodon wasan Yara!" Inji Mahmud, kalamansa sun yiwa Aliyu zafi saboda ya san cewa shi ya bada damar haka amma bai taɓa kawowa zai iya cin mutuncin Ummu a gabansa haka ya basu damar fadar abin da yayi musu. "Wannan wacce irin hauka ne? Taya zaka fadi haka?" Inji Safiyyudeen yana tuki. "Kambu da kai nayi? Dan shigigi ko ance babu wanda bai san halinka ba ne." "Gara ni ba munafiki ne ne, gara ni bani da fuska biyu idan har bana son Abu bana wahalar da kowa sannu shugaban munafukai. " "Kai ya isa haka, don Allah meye haka ne? Tun muna Yara kuke wannan haukar har yau baku gane gaskiya kun girma ba ne!" "Shi zaka gaypawa dan matsiyata!" "Na gode sosai tunda arzikin ba ubanka yake rabawa nace ya manta da gidanmu ba, gara na zauna a tsiya da na zama me irin halinka!" "Zanci bura uban mutum!" Ya fada da karfi haka yasa bakiɗaya suka yi shiru. Wato shi Safiyyudeen kokari yake ya hana Tafida fadar sirrinsu yayi da Mahmud yake son yaji meke faruwa tsakanin Tafida da Ummu. Dukansu abokan Tafida ne tun suna Yara shi yasa kaf duniya bai da sama da su, amma don sirri da tattauanawa me muhimmanci bai da sama da Safiyyudeen domin shi Deen irin mutanen nan ne masu zafi da fada, yanxu sai ya iya kwaabewa ayi dambe da shi babu ruwan shi. Yayinda Mahmud baka tab'a sanin halinshi idan ka cire jaraban bin mata tow magana ya kare duk suna da kirki sai dai tsakanin Mahmud da Safiyyudeen shirinsu na lokaci ƙalilan ne zuwa wani lokaci sun hautsine don shi Mahmud yana da wani irin dabi'u saurin gori da nunawa yafi kowa yayinda Safiyyudeen bai da irin wannan halin sam, sannan shi kanshi Tafida yasan halinsu ya san abin kowanensu zai aikata. Kuma dukkansu babu wanda yake jin zai rabu da shi don halinsa sai dai kai ka rabu da Tafida don kanka. Sai da aka fara sauke Mahmud a gida ya tsaya a gefen motar ya ce. "Allah ya isana duk wanda yayi gulmana!" "Kai can ci ubanka!" "Na dai faɗa!" Ya juya tare da shiga get din gidansa. Murmushi Safiyyudeen yayi ya ja motar suka yi gaba. Tafida ya kwantar da kanshi. "Deen me yasa kake hanani magana!" Banza yayi mishi tare da mai da idanunshi kan hanya, wannan halin na Deen yana matuƙar burge Tafida domin Deen Allah ya mishi baiwar iya shariya musu ka tambaye shi abin da yasan ka sani ba zaka kulaka ba sai dai ya bawa banza ajiyarka banbancinshi da Mahmud shi a kodayaushe cikin zargi yake ana munafuncinsa. Sai da ya shigar da shi cikin gidan Mahaifinsa security da masu tsaron da suka hana binsu suka taso tare da lullube su. "Aliyu!" Juyawa yayi yana kallon Deen yana da kyau ka mutuntata darajar Ummu Hadiyya ko babu kome yanzu an zama d'aya, idan da hali kada ka bawa kowa damar cin mutuncinta, yarinyar nan ta rufa maka asiri sama da yadda zamu

Chapter 2 of 17