An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: ALKAWARI BAYAN RAI SHIMFIDA
Na sha tambayar kaina mai ya sa wasu mutane, ko ko in ce Hausawa, ke daukar matsalar banbancin kabilanci, addini da al'ada da matukar zafi, har hakan ya shafi rayuwar yaron da aka haifa?
A ganina duk auren da aka gina a matsayin aure na addini, aka kuma bi ka’idar da addini ya shimfida wajen yin sa aure ne, da ya cancanci a karbe shi kamar sauran aurarraki, a kuma karbi dan da amana kamar sauran 'ya'ya ba tare da la’akari da wadannan banbance-banbancen ba. Amma ni ba haka bane a tunani da ra'ayin dangin mahaifina ba.
Ni dai na taso da tabbacin Baffa Jibir ne kadai ke so na. Bani da kamar Baffa. Don haka har kullum nake kara bin shi da addu'ar tsahon rai da lafiya dauwamammiya.
Ba wai Baffa ne kadai nake da shi a duniya ba, a'ah, ina da kannen Uba, wadanda ban san da sunan da zan kira su ba. Sai dai in ce tsana da tsangwamar da suke yi min, yana da nasaba ne daga mahaifiyata da su ke ce dan'uwan su ya guje su a dalilinta.
Duk da haka ina jin dadin rayuwar tawa a hakan. Rayuwar 'talle’ ba? Idan an dawo makaranta. Yo me ya kai ta dadi a wajen yaron karkara? Abubuwa iri daban-daban babu wanda Inna Laminde ba ta dora mini.Tun daga kan dafaffiyar gurjiya, rogo, dafaffen makani, kumurci, soyayyar gyada (marau-marau), tubis-tubis da dangogin su. Da abin ya ci gaba ne aka koma dafaffen kwai. Babu kuma abin da Inna za ta dora min ban siyar na kawo mata cikakkun kudi da faranti ba.
Don haka Inna take tsammanin ko wani maqarqashiya nake da shi na samun ciniki? Ta sha cewa, loko ake ja na ayi min juye a bani kudi, koko ta ce maza ke ja na zaure. Wanda a zahiri ba haka bane, mutanen gari kadai ke so na,a sabili da banbancin kalar fata da gashin kaina.Wanda ya banbanta da nasu. Don haka ne sau tari suke rububin sayen abin hannu na.
Babu yadda Baffa bai yi da ita akan ta dena dora min tallan nan ba, sai ta ce, kudin kayan aurena nake tarawa da kaina. Idan ba haka ba uban wa nake tsammanin zai yi min kayan dakin? Baffa bai da 'ya mace, kuma ba zai fara a kaina ba.
Yo meye amfanin diya mace a karkara? Idan ba ta yi talla ta samo abubuwa guda biyu ba? Mijin aure da kudin kayan daki? Ko ita ta haifi mace iyakacin gatan da za ta yi mata ke nan. Amma kullum Baffa ya ce, ba ta yi dai-dai ba, don ana son a goranta mata cewa ni din ba 'yarta ba ce.
Iyayen nawa na so na, suka watsar dani suka haure? Don haka idan ba a gode mata ba, to ba za a kushe mata ba.
Baffa kan ce "Amma sabida Allah Laminde, ba ki ganin hakan ya tauye karatun muhammadiyyarta?" Sai ta ce
"Idan ba za ka gode min ba, to ka dauke ta ka kaita duk duniyar da kake tunanin dai-dai ne da rayuwarta!".
Sai ya murmusa ya koma ba ta hakuri. Don daga ni har shi bamu da wata powerin dai akan Inna Laminde ne.
****
"Gafara dai! Gafara dai!! Ko masu gidan basa nan ne?"
Daga can kuryar daki Laminde ta amsa, "Muna nan, karaso ciki Hajiya Hajara".
Ta ce "Dadina da ke Laminde daukar murya".
Ta yi murmushi, a dai-dai lokacin da ta rage tsawon ta don shigowa dakin wanda ke dauke da'yar kankanuwar kofa, tun irin ginin nan na iyayenmu da kakanninmu.
Laminde ta ce "Mutanan birni ke nan, ashe talaka na ganin ku?"
Ta ce "Sai idan talakan bai so ba".
Ta zauna bisa tabarmar karaunin da ke shimfide tsakar dakin suka soma gaisawa, gaisuwa irin ta kanwar miji da matar wa da suka dade ba su ga juna ba.
Dai-dai lokacin na dawo, duk kafafuna sunyi futuk. Na aje farantin na karasa dakin da sallama, don in mikawa Inna cinikinta na kwan zabbi da na sayar tas. Zuwa lokacin zuciyata fari kal take, don na tabbatar yau zan samu abinci in ci in koshi, tun da na sai da kwan duka. Gobe kuma ranar fita da gasara ne, wadda kuma ba kasafai nake sayarwa duka ba.
A tsarin Inna Laminde kuma, iya yawan cinikina, iya yawan abincina.
Har kasa na tsuguna ina mikawa Inna kudi, ba tare da na lura da Yaya Hajara da ke zaune a gefe ba. Ba ta karbi kudin ba ta bi ni da kallo, kana ta jinjina kai cikin takaici, ta ce "Lanto!".Na ce "Na'am Inna".
Ta kama kunnuwana duka ta murde iya karfinta, ta ce "Har yaushe ne?
Kullum ina gaya miki in za ki fita tallan nan ki dinga daura zanin arziki kin ki., kin nacewa wannan kodadden bambalastan, kina min bakin ciki kada ki samo min wanda zai kawar da ke. To ni na gaji, da rikon mai kama da maraya, komi na yi a ce ban yi dai-dai ba, ko kin ki, ko kin so, aure zan sa ubanki ya yi miki in huta. Allah ya gani na gaji, na yi iya bakin kokari na".
Ban tanka ba, har ta gama sababin ta uffan ban ce mata ba. '”Bace min da gani, tun ban yi kwallon albarka da ke ba". Ko kafin ta idasa maganar ta, tuni na wuce, don na san kadan da aikinta.
Kicin na wuce na samu abincina an rufe da faifai. Nan na zauna akan dutsen da Inna ke amfani da shi wajen girki, na soma cin abincin, danwake ne da mai da yaji, an yayyanka tumatir da albasa a kai. Na tsince albasar na zubar, kana na soma ci.
Daga nan inda nake ina jiyo sauran bala'in Inna, duk akan rikon mai kama da marainiya da aka dora mata, ga shi na rasa miji, ta rasa yanda za ta yi da ni.
Yaya Hajara ta kyabe baki ta ce "Ba don kar a ce na yi karambani ba, koko a ce nima din bani da kirki, da sai in ce ki kaita wanke-wanke da shara birni kawai ki huta, don ni kam ba zan daurawa mijina rikon da Allah bai sa shi ba. Nima ‘ya’ya ne a gabana ba daya ba ba biyu ba, don haka bana neman kari. Can ma kuma kinga ai neman mijin ne, ga kuma kudi da za su ba ta duk wata ki samu na yi mata kayan dakin".
Laminde ta ce "Wannan Uban nata da ke sonta fiye da 'ya'yansa zai amince ne?"
Hajara ta ce "Barni da shi". Ta ce
"Ni yadda yake kaffa-kaffa da ita ai ya fi Uban da ya haife ta. Idan ba ta je birni ta yi wanke-wanke da sharar ba ni ban ga amfanin ta ba, tun da bakin jini gare ta, babu wanda ya taba shinshina ta.
Babban tsoro na ma ko wasu na janta zaure, ta yo ciki a dora min jafa'in da ban ji ba, ban gani ba. Gara dai ku dangin nata........."
"Dangin wa?" Hajara ta tare ta... "Ba dai ni Hajaru ba, don ni ban hada dangi da jinin yahudawa.......".
"Au....abin haka ne? Shi ne ni kuka hada mini? To ku san yadda za ku yi da kayar ku, amma wallahi ba zan rike ba, nayi na Allah nayi na annabi, wanda na daure ma nayi tsayin shekaru goma da doriya, Allah ya amfana!".
Dariya ta kama Hajara, ta yi mai isarta ta ce, "Shekaru goma kina rike da kayarki Laminde,babu wanda ya taba jin kan ku, ki daure ki karasa ladan ki.......shekaru nawa ya rage a kaita gidan miji? Musamman ku nan a kauye?".
Ta ce "In wannan ladan ne ban so, kuma nace dake bakin-jini gareta ba wanda ya taba shinshina ta, ku dau abinku ku karata da ita, ba neman diya mace nake ba don ina haifar maza". Hajara tace
“ki bar lamarin a hannu na, dama wata ‘yar uwar Baban su Hauwa’u na ji tana cigiyar yarinya kamar ta”.
Yaya Hajara ce a dakin Baffa, ta kwantar da murya cikin hikima tana rokon sa ya ba ta Lanto, za ta rike mishi amana, za kuma ta samar mata aikin yi a can Kano.
Baffa ya ce "Aikin yi? Wane irin aikin yi? Da dai makaranta za ki sanya ta Hajara da na fi jin dadi. Shekaruna sun tura, ina da burin samar ma Lanto, kyakkyawar rayuwa kafin in bar duniya, da abin da za ta dogara da shi, ko da ba ta tadda samun ganin iyayenta ba".
Sai Hajara ta koma lallami cikin ha'inci, ta tabbatar mishi cewa ba za ta bar wata rayuwa maras kyau ta faru da Lanto ba, ita ma tana da hakki a kanta.
Dole Baffa ya yarda, ya umarce ni da in hada kayana mu koma tare da Yaya Hajara. Hajara ta ce "Ai sai zuwa gobe za mu wuce, ba ta gama halartar 'yan'uwa ba".
Da daddare Baffa ya kirani, na koma gefe na zauna cike da damuwa, wanda kullum ya ke bina da ban hakuri kan in jure, wata rana sai labari da halin matarsa.
Ya ce "Lanto ki kara hakuri akan naki na da da rayuwa, wata rana sai labari, nima hakuri nake yi da ita, saboda 'ya'yanta, ta zame min dole. Duk abin da ya yi farko yana da karshe, duk yadda za ta yi dani ba zan taba ba da ke auran sadaka ba, yadda take so, sai sadda Allah ya kawo miki miji mai son ki, mai kaunarki.
Ai alhakinki ke bibiyar ta, ga nata 'ya'yan nan duk sun ki karatu, sai gantali a titi, ke kuma da ta hana karatun Islamiyyah ko a gidan mijinki idan kina da rabo sai ki yi, tun da kin samu ilmin firamare ai an gode Allah, daga kowanne mataki na rayuwa za ki iya dorawa".
Ire-iren maganganun Baffa ke nan gare ni a kullum, idan ya ganni cikin damuwa. Kowa ya san dai shi din bai je makarantar boko ba, amma cudanyar shi da al'umma daban-daban, ya sanya kanshi a waje yake, wato,abin nufi, ya san abubuwa na zamani da dama.
Na mike zan fita, bayan na yi wa Baffa sallama, a bakin kofa muka yi karo garammm! Ni da ita, ta ce"To ka da ni ki ji dadi". Na ce "Allah ya ba ki hakuri, Inna".
Kwana na yi ina tunanin wannan sabon al'amari, watau bin Yaya Hajara birni. Kafatanin dangin mahaifina babu wanda ya fi tsanata irin Yaya Hajara, na san kuma ba ta nufi na da alheri a wannan tafiya. Don ba tun yau ba Laminden ta ke mata tayin ta dauke nin tana ki, duk akan kiyayyar ta ga mahaifiya ta.
Sai yanzu kuma rana tsaka, ina auna wacce irin rayuwa zan yi da Yaya Hajara, wadda a zahiri ta nuna min ba tun yau ba bata kauna ta.
Karfe goma na safe na shiga don in yi wa Baffa sallama. Eh, a wurina Baba ne, tun da wan Babana ne. Dogom mutum mai babbar sura, wato babban jiki. Kowa ya kwana ya tashi a kauyen Bujawa, ya san Mallam Baffa Jibir Bujawa, saboda shahara da ya yi akan sana'arshi ta kiwo yana sayarwa. Wadda ya girma ya tashi a kanta.
Can na iske, Inna Laminde, ta kai mishi abin karyawa, na tsinkayi kalaman ta na karshe.
"Me zan yi da abin da za ta samo? Illa iyaka in mata tarin aure da su, duk da dai ake cewa bani da kirkin ban iya zalama ba sai neman zama lafiya. Idan kuwa yarinyar nan tana cikin gidan nan, ba zan taba zama lafiya ba,.....
Kai ana nuna maka samun sauki kana kawo qabli da ba’adi, wa ya ki rayuwar sauki?'
Baffa ya ce "ba na son saukin, ni nafi son a bar min ‘ya ta nan a gabana, nafi amincewa, banda dai da ni da Hajara duk daya ne......shine kawai yasa na amince, amma ba don ina neman wani sauki ba. Ita dinnan kwaya tal ta fiye min taron yuyuyin ki, koko in ce taron tsintsiya ba shara. Ba don Hajara bace wallahi da bazan amince ba”.
Wani sanyi ya tsirga a zuciyata, domin idan da akwai abin da nake so a rayuwata, a halin yanzu bai wuce barin gidan nan ba, ko don kunnuwana su huta, su sami rangwame daga sababi da bakaken maganganunta, wadanda take saki babu kunya, babu kawaici a kunnuwana.
Baffa ya ci gaba da cewa
"Don ba zan bari ba Lanto, a yi miki abin da ba kya so ba, domin ke din nan duk da nake wan mahaifinki, amana ce ke a hannuna, wadda idan na ci ko ya ya sai Allah ya hukunta ni".
Na ce, kaina na sunkuye
"Na amince Baffa, da kai da Yaya Hajara ai duk daya ne".
Ya ce "To Allah ya sa hakan alherin mu ne baki daya".
Haka na ci gaba da sake-saken abin da zan je in taras a gaba a cikin raina. Allah ya sa hakan alherin nawa ne kamar yadda Baffa ya ke fata.
** **
Karfe goma na safe muka bar Bujawa ni da Yaya Hajara a motar mijin ta, kayana cike taf cikin shudiyar Ghana Must Go, kafin karfe daya mun iso Kanon Dabo, Jalla babbar Hausa, yaro ko da me ka zo an fi ka. Direba na jan mu. Ni dai na san Yaya Hajara mazauniyar garin Jos ce ita da mijinta da 'ya'yanta, don haka na sha mamaki da na ganmu a Kano. Ba don na san Kano bane, a'a, sai don ji da na yi suna furtawa ita da direbanta.
Kamin mu taho sai da Baffa ya kara kira na dakin sa ya ci gaba da yi min nasihar na zauna da kowa lafiya, in kiyaye sallah, in kyautata alaka ta da kowa.
Shiga nan, bulla can direban ya iso gida mai lamba ashirin da daya a cikin Nassarawa G.R.A. Gidan yana nan a Abbas Road kwatankwacin sauran gidajen manyan ma'aikatan gwamnati da ke layin. Muka fito muka karasa ciki.
Allah sarki, me zumunci ya zama ne a wannan zamanin? Ko da ya ke a cewar su (dangin mahaifina) suna da hujja.
Yaya Hajara da ta ke matsayin kanwa ga mahaifina, ba za ta iya rike ni cikin iyalinta ba, ta gwammace ta kawo ni gidan dangin mijinta in yi ta aikatau. In hakan ta faru su dai sun rabu da alakaqai sun huta.
Tarba ta mutunci matar ta yi mana, tana lale da mu. Ta danna wani abu sai ga wata dattijiya ta fito daga wata kofa da na yi tsammanin madafi (kichin) ne, sakamakon qamshin girkin abinci da ke busowa daga kofar, da ya bakunci hancinan mu.
Ta umarce ta da ta kawo mana dan abin jiqa makoshi.
Suka ci gaba da tattaunawa a kaina ita da Yaya Hajara, ga dukkan alamu sun jima da sanin juna, to alhamdulillahi na samu karbuwa wajen uwargijiyar tawa.
Sai bayan la'asar Yaya Hajara ta yi shirin tafiya, tana mai kara ja min kunne kan yiwa uwargijiyata biyayya.
A cikin hirar tasu ne na fahimci cewa, a wani biki ne da suka hadu ita da Hajiyar ta ce da Yaya Hajara idan ta je kauyensu ta samo mata 'yar yarinya karama da za ta dinga taimaka mata. Na kuma fahimci ita matar gidan dangin mijin Yaya Hajara ne.
Bayan fitar Yaya Hajara muka yi shiru daga ni har ita, tana ta danne-danne cikin wannan wayar ta zamani, wadda ko a Bujawa na ga ta zama ruwan dare. Sai da ta kare ta kira wannan dattijiyar ta ce "Sunanta Baba Larai, za ku zauna tare, sai dai kowanen ku aikin shi daban.
Tana kula da kichin ne, ke kuma ba zan ce ga hakikanin aikinki a cikin gidan nan ba. Bayan taya Baba Larai aiyuka da wanke-wanke da share-share, akwai kula da yara.
Babban aikin ki shi ne shirya su kullum da abincin da za su tafi da shi makaranta, duk Baba Larai za ta koya miki har ki saba. Sunana Hajiya Fatima-Binta, ke kuma fa?" Na ce,
"Lanto".
Ban taba haduwa da mutumin da na ji ya shiga raina farat daya irin Hajiya Fatima-Binta ba, ga dai kirki ga fara'a, ga mutunci da saukin kai, sune halayen da na fassarata da su a lokaci daya.
Ta ci gaba da cewa "Za ku zauna daki daya da Baba Larai, ki kula da kanki, ki kula da tsafta sai mu yi zaman mu lafiya mu taimaki juna. Yarana duka kanana ne, suna bukatar wata wadda za ta dinga kulawa da al'amarin su bayan ni a ko,'ina.
Ni 'yar kasuwa ce, ina da manyan hidimomi a kaina shi ne dalili. Ina fatan za ki zauna damu cikin amana mu hadu mu taimaki juna?"
A hankali na ce "Na yi wannan alkawarin Hajiya......". Ban idasa rufe baki ba suka yiwa falon tsinke, suna ta tadin su na yara 'ya'yan gata. Duk suka baibaye Hajiya suna ta shara mata labarin abubuwan da suka faru da su a yau. Ta ce
"To ga kawa na kawo muku, kuna so ko ba kwa so?"
Gaba daya suka juyo suka dube ni, babban ya yamutsa fuska, sauran ukun suka amsa cikin jin dadi "Muna so, Mami".
A kyamace babban ya ce
"But she is dirty Mami?”
Ta yi murmushi, "Cikin kwana biyu za ta yi fes, Mukhlis".
Ya kyabe baki "In dai wannan ce kawar da kika ce za ki nemo, to bana so, ina da kawaye na a school sun ishe ni".
"Kaifa Muslim?"
"Ni ina son ta Mami".
"Huda fa?"
Ta ce, "Nima ina sonta Mami, za ta goya ni irin goyon da Baba Larai ke min?"
Ta ce, "Kin yi girma da goyo, Baba Larai ma ta tsufa balle ta goya ki, balle wannan 'yar mitsitsiyar? Nour fa?"
Da ganinta ka ga 'yar auta, saboda yadda ta bi take lafe jikin Mamin, ta ja bakinta ta tsuke ba ta ce komi ba, duk sai ta ba su dariya. Daga nan ta umarci Baba Larai da raka ni dakin mu in ci abinci in huta.
A hankali Baba Larai ke koyar dani duk abubuwan da Mami ta ce a koya min, musamman shirin su Nour zuwa makaranta.
Cikin sati daya kacal na gane komi ta fannin kula da su wajen tafiya makaranta da shirya musu abinci cikin akwatin tafiyar su (lunch box), saboda Mami ba ta fitowa sai karfe goma.
Ban da abu irin na su na masu akwai, ni ban ga wani aiki a nan ba da har sai an nemi mai yi. Amma ga Mamin tana ganin hakan taimako ne ake mata, tun da kuwa yanzu ga shi tana samu ta yi baccinta mai isar ta.
Mun shaku da Nour da Huda sosai, cikin 'yan kwanaki kalilan, na rasa mene ne dalilin da ya sa Mukhlis ya ki jini na, tun da in dai don qazanta ce yanzu bana tare da ita, na yi fes na yi shar kamar ba ni ba. Kyawuna ya bayyana a sarari, hatta sabulun wanka na musamman Mami ta sai mini, wanda daga kwalinshi na lura ya fi na Baba Larai mukami.
Cikin watanni biyu kacal na zama 'yar gida, na yi dace da uwar daki ta gari, kuma ta qwarai mai nuna nata ba nata bane, ta hada ni da 'ya'yanta duka ta rike tsakani da Allah.
Duk wani abu da zai bata ni a wurin wannan iyali ina gudun shi, don haka ne na zamo mai kaffa-kaffa da al'amarina. Ba na shiga shirgin Mukhlis ko kadan, shima ba ya shiga nawa shirgin. Zama da su sau dubun-dubata ya fiye min zama da Inna Laminde ta kowanne fanni, na kuma kara zage damtse wajen kyautatawa Mukhlis dan kimanin shekaru goma sha hudu, kuma babban da ga Mami.
Bana jin kiwar yi wa Mami kowane abu da ta sa ni in yi, don a gani na ‘as rainon kauye as I am’ zan iya yin fiye da haka, kafin nan ma, ita ba ta sani abin da ya fi karfina.
A shekara guda kacal ni kaina na san na samu sauyin rayuwa da ci gaba ta kowanne bangare, don Mami ta umarce ni da in dinga zama wajen lesson din su da yamma wanda wani Bayerabe yake zuwa kullum daga karfe hudu zuwa shida, wato bayan sun dawo makarantar boko sun huta.
Ba zan iya cewa ga hakikanin shekarun Mami ba, sakamakon alamun jin dadi da suka boye hakan, suka mai da ita kamar 'yar shekaru ashirin da biyar, bayan a zahiri ta baiwa talatin baya.
A kullum kalaman Mami gare ni su ne.
"Jin ki nake kamar 'yar da na tsugunna na haifa Lanto, ki ci gaba da zama dani da iyalina cikin amana".
Ranar wata lahadi mun dawo daga daukar lesson, kowa ya kama harkokin gabansa, Mami na lura yau sai bi na take da kallo duk in da na gitta. Ta kare ta ce "Lanto zo nan".
Na matsa na zauna bisa carpet a gabanta, a ya yin da take zaune cikin lintsimemiyar kujerar falon. Ta ce
"So nake ki bani tarihin ki a taqaice".
Nan da nan hawaye suka balle, yi nake ba sassautawa. Ta ce "Ba kuka na kira ki ki yi min ba, ina so ne in sani su waye iyayenki na hakiqa, don mutumin da ke zuwa duba ki nan (Baffa) jiki na ya bani ba Babanki bane. Haka Hajara idan 'yar'uwar mahaifinki ce ta hakiqa, zuwa yanzu ya dace a ce ta waiwaye ki, at least ta ji lafiyar abin da ta kawo ta ajiye, ko da ba mutum bane……".
Na ce
"Eh, Baffa ba Babana bane, mariki na ne kuma wan mahaifina".
"Wan Uba na asali?"
"Nima ban sani ba, na dai taso na ganni tare da shi, yana kyautata mini, kamar diyar cikinsa, ko ma in ce, fiye".
"Kuma bai taba