Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 10
na yau bane tun kamin aurenta na fari ne, tana kafa hujja da ni. To ni din na amince na yarda mu hadu mu rungume M.K ni da Kausar, amma ban san dalilinta na kin amincewa ba take neman hada kanta da ciwon zuciya". To wai an ce labarin zuciya a tambayi fuska, kuma soyayya ba ta tsufa, sai dai masoyan su tsufa. To balle kuma mu da muke kan gavar ganiyar quruciyar mu. Ba abin da za mu ce da Mami daga ni har M.K, wadda ke tsaye don nema mana farin ciki da zuciyarta daya, sai dai mu bi ta da addu'ar alheri. A take Justice ya sanya hannu cikin aljihu ya kirgo sadaki a matsayinshi na waliyyin M.K, Baffa Lawal ya amsa. Aka ci gaba da gudanar da daurin auren kamar yadda shari'a ta tsara, bayan dukkanin mu mun bar falon. ** ** Babu kacaniyar biki, daurin aure kawai ya wadatar da daga amaryar har angon. Sai cuku-cukun neman ‘visa’ ta da M.K ya maida hankali, a karshen satin cikin qudurar Ubangiji muka daga New York. Gida ne na hawan bene sama da kasa, a sama dakuna ne biyu da falo da toilet, to haka a kasan ma. Kicin din gidan da ya kasance guda daya makeken gaske ne a kasa yake, mun sauka birnin New York lafiya. M.K ya zava min zaman kasa Mami a sama, dakin su Nour ma a kasa yake. Ni dai tun da muka iso aka nuna min daki, alwala na dauro bayan shower na sauke sallolin da ke kaina, na bi lafiyar gado bayan na kulle dakin, ban san halin da jama'ar gidan ke ciki ba. Ya cimma Mami a dakin barcinsu tana kiciniyar sauya kayan jikinta zuwa nighties sanye yake cikin pyjamas masu taushi, bai taba yi mata kyau irin wannan ranar ba. Kai kayan ma bai taba sanya su ba sai yau da ya dauko sabuwar amarya (a tunaninta). A take kumallon matan ya motsa, ko kallon shi ba ta yi ba balle ta nuna ta san Allah ya yi ruwan tsirarsa a dakin. Ta ci gaba da abin da take, tunaninta wai yau M.K ne zai hada jiki da wata mace bayan ita, macen ma wadda ta raina, ai abin da takaici. Sai hawaye shar-shar wasu na korar wasu. "Mami ya zaki sa ni in yi abu, kuma ya zo ya dame ki? Da kin san hankalinki bai kwanta da al'amarin ba, don me za ki ce a yi?" Ta kai hannu tana yarfe hawayenta, "Ka yi sacrifising saboda ni, ya ya ba zan yi sacrifising saboda kai ba?" Ta valle da kukan da yake girgiza masa zuciya. Ba ya son ganin kukan mace, balle kukan Mami. Ya gigice ya rikice ya rasa inda zai sa kansa. Da zai iya sakin Kausar din a wannan daren da ya yi, amma ina, shima yasan ko bindiga za’a daura masa a makogaro ba zai taba yin hakan ba. Burin shi na shekara da shekaru yau Allah ya karba yaya zai yi sake da ni’imar da Allah yai masa? Ganin halin da yake ciki ne ya sa ta share nata hawayen, ta ce, "Muje in raka ka wajen matarka". Ya ce, "Ba inda za ni Mami, you are ok for me, hadama ce kurum irin tamu ta maza, amma ai kema kanki kin san kin ishe ni rayuwar duniya da lahira". Ta dage sai ya tashi, in ba haka ba za ta fice ta bar mishi dakin. Ji ya yi kwata-kwata ba ya son Lanto, tun da hakan vacin rai ne ga Mami, to ya hakura. "Kafin ki bar min dakin ni zan bar miki kayanki, amma na rantse Binta ba zan taba cin amanar ki ba". Dariya ya ba ta sosai, M.K ya mai da kansa kamar wani yaron goye, sai dai kuma daga ganin shi ka san mahaukaciyar soyayyar amaryarshi na dawainiya da shi. Ya juya ya fito ya koma nashi daki. Haka kawai ya hada ma kanshi zafi, ashe haka zama da mata biyun yake? Amma ya yarda ya amince cewa ba yin kansa ba ne yin Allah ne. Kwanaki bakwai duk yadda Mamin ta yi don ta shirya mu abin ya ci tura, abin ma ya fi karfi daga gare ni, ko son ganin M.K bana yi, bana fitowa main parlour balle in hadu da M.K din. Na nemi duk wata soyayya da na ke mishi na rasa, kunyar Mami ta hana ni sukuni. Amma ga Muslim, Nour da Huda wannan abin farin ciki ne a wurin su, sun fada sun kara, "Daddy mun gode da dawo mana da Auntynmu, Mami ta gaya mana ba za ta sake komawagidan Hajiya ba, tun da ka aure ta". Sai ya yi murmushi. Shi Mukhlis tuni ya koma Turkey haxo kwalin shi na biyu. Ko abinci bana fitowa nema balle in yi arba da kwayar idon Mami, to amma ai an gudu ba a tsira ba, saboda ita da kanta take kawo mini ko Baba Larai. Ina ganin kaina as a betrayer, sai dai kuma duk da hakan koma ya ya ne na sani na hakikance, na tabbata dai-dai da rana daya ba zan iya daina son M.K ba. Don haka har wa'adin da Daddyn ya deba a wurin aiki da sunan amarci ya cika, Mamin ta kasa qulla komi a tsakanin mu. Kuma a dai-dai lokacin ne bikin 'yar kanwar Justice ya kama a Hadejia, don haka ta samu mafaka ta yi amfani da damar ta bamu excuse na tafiya Nigeria biki ita da yara". "Amma Mami ko Huda ce ki bar mini". Ta valla min harara. "Ba zan bar miki Huda ba, tunda kin zama mai kunnen kashi, ban isa in saki abu ba ki yi, ai sai ki yi ta yi. Ba ni kike kwasowa alhaki ba kanki ne. Kausar aure ba abin wasa bane, duk yadda kike tunanin shi ya zarce. Kin yi watsin Allah-tsine da mijinki, ni ban yi kishin ba sai ke ce za ki yi halin tsiya. Tun da gidan kike so in bar miki ki sake da mijin ki, to ai ga shi nan zan bar miki". "Wallahi ba haka bane Mami". Sai hawaye shar-shar! Ta ce ba tare da ta dube ni ba, ta mai da hankalinta wajen troller da take shirya kaya. "To ya ya ne idan ba hakan bane?" "Yanzu Mami me kike so in yi?" "So nake ki kama mijinki, ki yi masa duka bin da mace ke yiwa mijinta. Sannan ne zan shirya da ke". A haka ina ji ina gani suka tafi airport suka yi tafiyarsu. ** ** [1/1, 14:08] Nrs Zainab A S: Na zauna zugum ni kadai a falo ina tunane-tunane yadda za mu yi rayuwa daga ni sai M.K cikin gidan nan. Ina jiyo motsin Baba Larai a kicin tana ta kiciniyar gyare-gyare. Na dau waya na kira Hauwa'u muka shiga hira, da yake bikinta ya matso. Baba Larai ta leko daga kicin tana tambaya ta abin da zan ci. Na ce, "Ta bari kawai zan zo yanzu da kaina in yi girkin Daddy sai in ci, ta nemi wanda za ta ci kawai". Bayan na kare shirya tebur na fada toilet din dake makale da dakina, na shirya cikin riga da siket din versace, ina tazar gashin kaina da hand-dryer na ji shigowar motar M.K. Ko kamin in idasa in cimmasa ya bayyana cikin dakin, hannunshi na dama rike da brief case, ya yin da na hagun ke rike da falmaran din suit din shi, ya watsar da su ya iso gare ni ya miko hannu ya rungumo ni ta baya. Kafin ya juyo ni all overya hade da jikinshi yana sauke wani irin wahalallen numfashi. Atlast! Allah ya cika mana burinmu na shekara da shekaru, me za mu ce da shi ne, ban da mu gode masa. Mun dade cikin wani hali, cikin wata irin rayuwa da ban taba tsintar kaina a ciki ba. Cikin wata duniya da ban taba shiga ba ko da a mafarki ne. Har lokacin sallar magariba ta wuce bamu ankara ba, da kyar na kwaci kaina a hannun M.K muka fada toilet. Wanka na taimaka mishi ya yi kafin da mu hau tebur. Muna manne da juna kamar masu tsoron kada wani abu ya ratsa a tsakaninmu. *** Idan wannan ita ce soyayya, to ban taba jin ta a SAGEER ba, idan wannan shi ne AURE, to ban taba dandana shi a SAGEER ba, idan wannan ita ce KAUNA, to ban taba dandanata a rayuwata ba. At last! Allah subhana ya dube mu da kyakkyawar niyyar da ke zuciyoyin mu ya mallaka mana juna. Kanwa ta kar tsami kwannafi ya kwanta, sai fatan Allah ya ba da zuri'a masu albarka. Ya kwantar da kai a masangalin wuyana, ya ci gaba da fassara min wane ne MU'AZZAM? Kuma mce ce soyayyar?? ** ** Har muka share sati biyu muna varzar amarci ba mu sa Mami a ido ba, sai dai na san koma dai yaya ne cikin juriya da dauriya take, don cikar farin cikinmu. Alas! A yanzu kam ya samu nutsuwa ta har karshen rayuwar shi, wato mata biyun nan da yake matukar so a duniya da lahira (Mami da 'yarta). Don haka a dawowar Mami wani abu wai shi KISHI ba mu san shi ba, Allah subhana ya yaye mana tun da ya dubi zuciyoyinmu na ALHERI ne ga junan mu. A ranar da Mukhlis ya dawo da kwalinshi na Lauya, wato (LLB) a ranar ne na haifi Mukhtar (Justice) bayan shekara guda Mai sunan Hajiya ta biyo baya. Ko da Mukhlis ya tsinkayi aurena da mahaifinshi jinjina kai ya yi, wato abin nan da ake cewa fadan da ya fi karfinka…... Sai dai kuma shima ya so hakan, kamar yadda ya ce fiye da a ce a waje Daddy ya je ya dauko musu. Soyayyarshi da Fa'iza diyar Yaya Hajara kanwar Hauwa'u ta yi nisa, don haka shi din yanzu cikakken mutum ne mai hankali, ya daina duk abubuwan da yake yi na quruciya. Bikin Hauwa'u ya tashi, don haka dukkannin mu muka tattaro muka yo Kano, daga nan muka wuce Jos inda Daddy ya samu halartar daurin aure. Ba kuma tare da zaton kowa ba ya biya sadakin Mukhlis da Fa'iza, don haka muka kece da biki babu kama hannun yaro. Kowa yana sha'awar tsarin rayuwarmu ni da Mami da maigidanmu, sai fatan Allah ya ja da rai ya kuma raya mana zuri'a, ameen Rayuwa ta ci gaba da mika mana yadda ba mu zata ba. Da ci gaba da nasarori ta fannoni da dama. Mu'azzam Kanti Mu'azzam mutum ne da kafin a samu kamarshi cikin dubban maza sai an tona. Ga dai adalci, ga kuma soyayyar, kulawa da iya tafiyar da rayuwar iyalinshi ta yadda babu wadda ta isa ta yi complaning kan cewa ba a kyauta mata ba. Sai kuma ya yi katari da wata irin uwargida mai rahama a gare shi, har gobe ba zai daina alfahari da FATIMA-BINTA ba. Kamar yadda nima har jibi ba zan daina alfahari da ita a matsayi guda biyu da zuciyata ta bata ba, musamman da ta hada har da Fatima cikin iyalinta. Wato UWA kuma 'YAR UWA , sannan abokiyar shawara amma ba KISHIYA BA. Masha Allahu laquwwata illa billah. Takori An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 10 of 10