MAMI ma’abota karamci da kyautatawa ga wadanda ke karkashinsu??
Da wannan tunanin da wani sabon tsanar kaina da ya dirar min na angije M.K, daga qarqashin maqogaro na na ce "M.K Mami……….".
[1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: Ya ce "Kausar…….. Mu'azzam, shima mutum ne abin a tausayawa, da da yadda zaiyi da haka bata faru da shi ba, sai ki zaba, UWA ko MIJI?"
Ya ci gaba da yin abin da yake yi din (passionate kiss) kamar maganata ta kara mishi qaimi ne maimakon ta ankarar da shi, babu inda baya karkarwa a jikinsa, ni kuma na yi saranda na miqa wuya da duk abinda Allah ya hukunta a gare ni.
Cewa yake cikin kankanuwar murya,
"In ta hana ni auren ki Kausar ....... ai ba za ta hanani wannan ba………!"
Kalami na karshe kenan da Fatima-Binta ta tsinkaya cikin kunnuwan ta. Bayan kyakkyawan ganin data yi, ta yi saurin juyawa kafin kowannen mu ya ankara da ita, ta yi dakinta ta bame kofa.
Karar rufe kofar tata ne ya maido mu cikin hankulanmu, duk da cewa a hankali ta rufe.
"M.K don Allah.......don rasulillahi.....ka fita rayuwata, ka tuna wacece Mami agaremu nida kai, ka taimaki rayuwata kada ka raba ni da Mami, banida kowa sai ita, ta yi min komai a rayuwa....". Na fadi cikin matsanancin kuka tareda sulalewa a kasa na zauna a dandaryar kasa.
"Ke ba ki san soyayya ba ruwanta da wannan……....? Yau da addini ne yace babu aure a tsakaninmu Kausar zan bi umarnin ki, I know my wife just give her time".
"Na ji, amma ka fita, ko ni ka barni in wuce, idan Mami ta dawo ta tadda mu fa?"
"Mamin ta sani, ta san ina son ki, kuma da sannu za ta fahimce mu, saboda ita mutum ce mai tausayi da jin qai……".
"Ka yi min alfarma.... na hadaka da girman iyayenka, ka daina yin abin da kake yi dinnan a kaina..... ka daina shiga rayuwata, ka taimake ni ka taimaki Mamar mu……..".
"Nima ki taimake ni Kauthar, ba ni na sanyawa kaina ba, kuma bani kadai na ke son ki ba. Sai dai ki ce pretending kawai kike yi wanda ni na kasa….". Sai na rushe da kuka.
"Abu daya nake so da ke Lanto, idan Fatima ta tambaye ki kina so na ko bakya so na? Ki dubi Allah ki fada mata gaskiya……".
A razane na kara cira kai na dube shi, ya daga min gira. "Eh, ita din yadda kika zace ta ba haka take ba, mace ce mai dimbin kauna da alfarmomi a gare ni, farin cikinta shi ne nawa, ita ma farin cikina shi ne nata.
Da sannu za ta yarje mana muyi aure mai suna aure kin ji Kauthar? Ki kwantsr da hankalinki. Sai ku ci gaba da zamanku da babbar hujja, in ba haka ba ke da itan masu rabuwa ne tun da ko ba dade ko ba jima gidan auren wani za ki. To gida bai koshi ba kinga ya dace a kai dawa?"
Takaici, bakin ciki da tausayin Mami suka kara dabaibaye ni, kamar in dora hannuwa aka in ce wayyo Allah! Ya fahimci ya gama hada min zafi, don haka ya juya ya fice yana kara jaddada min tafiya dani Turkiya babu fashi.
Can ya cimma Mami a daki zaune tsakiyar gadonta ta hada kai da gwiwa ta rasa abin da ke mata dadi a duniya, ta nemi digon hawaye a idanunta, ta rasa.
Namiji! Sai a barshi.
"Wa ya tabo min uwar Mukhlis ne…..".
Sauran maganar makalewa tayi a makogaronsa sakamakon kallon da Mami ta cira kai tana yi masa. Ji take kamar ta kashe shi ta huta, so yake ta kori Lanto, so yake ya farraqa wannan yardar da wannan amincin da sunansa na Da namiji kusan zuma, to ta kore ta ta je ina? Kishi bazai sa hankali da tunaninta da tausayinta su gushe ba. Ita din ma'abociyar, hankali da imani, tausayi da sanin ciwon kai ce.
Ya karaso gefen gadon ya zauna, ya kamo hannuwanta ta fincike. Bai yi aune ba sai jin saukar lafiyayyen mari ya yi a kuncinsa, sannan ta bi shi da muguwar shaqa.
"Gara in kashe ka kafin ka kashe ni……!'
"Saurara Fatima in miki bayani……".
"Bayani? Bayanin me? Na karerayi da yaudararka? Allah ya sa idona ya gane mini ba wani ne ya zo ya gaya min ba, balle ka ce anyi maka qage………".
"Na ji ba ai min qage ba, kuma na rungumi 'yarki, na tsotsi bakinta. Bayan wannan Binta banyi komai ba. Sai dai nima ban san me ya kaini ga yin hakan ba, soyayya .......Mami. .....soyayyah!"
"Soyayya M.K?"
Jikinta ya saki yaraf kamar kayan wanki, yau ita M.K yake gaya mawa yana yiwa wata diya mace soyayya kwatankwacin wadda yake mata. Ya ya sunan maza ne? Mugaye, Mayaudara, Marassa Hankali, tun da basu san ya-kamata ba……….
Ta cika shi ta koma gefe ta soma rera masa kuka. Ya sake bin ta cikin lallashi ya kwantar da kai a kafafunta,
"Na haqura Binta, na haqura Fatima, wallahi ba zan aure ta ba.
Kin fiye min kowa Binta, bayan mata ta sunna ke UWA ta ce, data bani dukkan kauna a sanda bani da iyaye, ta tallafe ni a sanda bani da komai, ta auri marayan da ba Uwa ba Uba, alhalin tana cikin gatanta. Uwa-uba ta haifa min iyali son kowa, tare da ba su tarbiyya abin alfaharin kowanne Uba. Tun da na kasance mai bata miki rai da cin fuskarki haqiqa na yi asara!
Magana ta karshe Fatima ki dauki Kausar ki mai da ta inda kika dauko ta shi ke nan, zan yi kokari in yi ma zuciyata linzami.
Amma idan har tana tare damu bani da tsimi bani da dabara akan al'amarin da ke faruwa da ni".
Ta kama mijinta ta rungume, tana addu'ar kada Allah ya nuna mata ranar da za ta raba su, ko ta maimaita kuskuren da ta yi (marin mijinta).
"Forgive me M.K?"
"Na yafe miki duniya da lahira, nima ai rannan na mare ki, ramawa ki ka yi".
Ta ciro kanta daga kirjinsa,
"Kaima ka rama".
Sai ya rama mata da fatar bakinsa.
"Ni kuma ba zan kori Lanto ba, she mean a lot to me….".
"Shi ne dalilin da ya sanya ita bakya ganin laifinta sai nawa?'
"Me ta yi wanda zan ga laifinta? Waya take maka ko binka take yi? Kula ka take ko ita ta ce ka dinga yin abin da kake yin? Gaba kake da ita ka fi ta shekaru da tunani, kai ne ya kamata ka yi wa kanka birki, don ba zan taba iya hada shimfida da 'yata ba, sai dai ka zaba ko ni ko ita?'
"Na zabe ki Fatima-Binta, wallahi na zabe ki. Tafiyar ma an fasa da ita, na rantse miki na haqura da Kausar har duniya ta nade."
Suka koma ma abin da ya fi komi muhimmanci a gare su, har wayewar garin ba wanda ya kuma jin duriyar su, ko abinci ba su nema ba.
****
Sun tashi kasar Istanbul a washegari tareda dukkan ‘ya’yansu, gida ya rage daga ni sai Baba Larai. A washegari ina falo ni kadai ina aikin assignment na tsinkayi dirin mota, kafin kararrawar kofar shigowa ta ankarar dani akwai baqo mai son a bude mishi kofa.
Sanye nake da wani bakin material mai laushi, dauke da dinkin da bai kama jiki ba, riga da zani da kallabinsu.
Na bude, muka yi arba ni da wani mutum, saurayi mai matukar kwarjini, fari sol, ko ko in ce, jajawur. Sai dai kuma abin da ya shagalar da idona ga kallonsa shi ne, komi da ke zane a fuskarsa, wato hanci, ido, baki irin na Mamin Yara ne.
Ya karasa shigowa fuska a sake, da ganin shi ka ga mutumin da yake jiqe cikin ingantaccen ilimi na addine ne ko na bokon? Akwai fara'a da faram-faram a tattare dashi, don a take ya sakar min murmushi.
Na ba shi hanya ya wuce har tsakiyar falo, muka gaisa cikin mutunta juna. Ya ce, "Ya na ga gidan kamar ba kowa?"
"Eh, sunyi tafiya ne zuwa kasar but Turkiya".
"Dubo Mukhlis ke nan?"
Na gyada kai.
Ya ce, "Ni sunana Sagir, kanin Mami ne Uwa daya Uba daya. Ke kuma fa? Don ban san ki ba".
Na zauna a kujerar da ke fuskantar tashi,
"Anya hakan zai yiwu? Kana dan gidan su Mami ba ka sanni ba?"
"Allah sarki, shekaruna takwas rabona da gida, dawowar ke nan jiya-jiya na ce bari in zo in ga 'yar'uwata, don tun jiya nake neman layinta ba ya shiga. To ashe ba ta kasar ne".
Na mike zuwa kicin ya bi ni da kallo, na juyo kadan ya yi saurin kau da kansa. A niyyata in kawo mishi lemo da ruwa, amma sai wata zuciyar ta ce,
"A'a, na koma inda na tashi na zauna".
Ya yi murmushi ya ce
"Ba lemo za ki kawo min ba? Kawo min mana?".
Cikin mamakin yadda aka yi ya karanci zuciyata na mike na isa ga kicin, na dauko gwangwanin lemon Rany mai sanyi da gorar ruwan Eva, da tambulan na aza a karamin tray, na karaso mishi da su.
Ya ce, "Thanks".
Ya bude ya juye a cup din ya kai bakinsa, kurba daya-biyu-uku ya ajiye.
"I would like to ask, wace ce ne?"
"Hadimar Mami ce!".
"Hadima kamar ya ya?"
"Eh, to hadima zan ce, tunda ni ke kula da hidimar yaranta ina kuma taimakonta a kicin, ita din kuma tana min riko na uwa da 'yarta, ta yadda idan na ce ni hadimarta ce ranta yake baci. Don haka zanyi mata karar, har a bayan idonta kamar yadda take so, in kira kaina, 'Yar Mami".
Ya yi murmushi ya ce, "Wonderful. Karatu kuma fa?"
"Ina shekara ta farko a jami'ar Bayero". "Ana karanta mene?"
"Microbiology ne".
Ya sake cewa, "Wonderfully good, Allah ya sa mu a danshin ma'aikata kiwon lafiya".
Wasa-wasa sai ga shi na sake da Sagir muna ta hira, hirar da ban taba sakin jiki na yi da wani da namiji ba. Sagir akwai fara'a, saukin kai da son hira. Har labarin iyayena na ba shi da yadda a kai na zo gidan Mami. Sai dai na lura yana da wata al'ada guda daya wadda bana son ta ga da namiji, watau smoking.
Ya gaya min ya kare karatunshi a kasar Moscow, ya fito da kwalin likitancin yara, ba da jimawa ba zai fara neman aiki.
Mune da hira har karfe tara na dare, shakuwa da aminci mai tsanani Allah ya hada ya qulla a lokaci guda. Da kyar ya duba agogo ya ce,
"Kausar kina da dadin hira, kin shantakar dani kada Hajiyata ta yi min fada".
"Ta yi ma fada? Sai ka ce wani yaro karami?'
"Babba ma ana mishi fada Kausar idan ya yi abin da bai kamata ba, tun da cike take da dokin ganina".
"Allah sarki, haka ne kuwa?"
Ya fiddo kan wayoyin shi guda uku daga aljihu, ya ce, "Ungo wannan muke communicating ko? I found a good friend".
Na yi murmushi,
"Ina da waya, sai dai in ba ka nomba".
"Bana son wayarki, da tawa nake so ki dinga amfani. Ko kina tsoron kada saurayinki da ya ba ki ya tuhume ki?"
Na kai hannu na toshe baki cikin dariya, "Kai Uncle Sagir, ni bani da wani saurayi, Mami ce ta saya min Allah".
Ya sauke wani asirtaccen numfashi, ya ce,
"In haka ne karbi wayata. Mami ba za ta ce don me ba".
Na miqa hannu na amshi lafiyayyar wayar da ban saba gani ba, sai ko a hannun irin su Daddy, na ce,
"Na gode".
Ya dau nambarshi ya zuba a ciki, ya sanya sunan "Uncle Sagir" yai saving. Haka muka yi sallama kamar ba za mu rabu ba, da alkawarin gobe in Allah ya kaimu tunda yake lahadi ce da wuri zai zo ya tayani gadi, tun da nazama 'yar gadi, amma fa idan hakan ba zai zama takura gare ni ko karatuna ba".
"Zai zama kam, amma ga karatun nawa, gab muke da fara jarrabawa".
Ya ce, "Shi ke nan, Allah ya ba da sa'a, am not in a hurry, daga nan har a kare jarabawar ma dinga gaisawa ta wayar".
Na ce, "Wannan din ma kam ban saba ba, kuma zai dinga raba min hankali"
"To ni kuma Kausar ya ya za ki dani?"
"Ban gane ya ya zanyi da kai ba, goyo?"
Ya yi murmushi, ya ce, "Tukunna, ki dai yi min wannan alfarmar ki dinga daga kirana".
Na gyada kai kawai. Ya ce, "Mu kwana lafiya".
"A gai da min Hajiya da kyau".
"Za ta ji".
Har bakin motarshi na raka shi muna daga ma juna hannu har ya fice a gate.
Abun kamar sihiri, tun daga ranar muka zama wasu irin gam-da-gam ni da Sagir, a waya kawai. Ban kuma bari wayarshi ta shafi karatuna ba, mun qayyade lokacin waya kamar wasu mata da miji, da safe da daddare kawai. Sai next da yake yawan aiko mani, ba dare ba rana. Wanda hakan ya haifar da wata matsananciyar shakuwa da kauna a tsakanin mu.
Bayan dawowar su Mami a ranar Mami ta ganni da sabuwar waya, ta nemi jin ba'asi.
"Ya ce shi kaninki ne, the same parents, ya zo mun sha hira, yace ya dawo karatunshi daga Moscow".
Ta rungume ni ta ce "Sagir is back?'
"Eh. Sagir ya ce mani sunanshi".
"Tashi maza shirya mu tafi, yau gidan Hajiya za mu kwana, hira da dan'uwana".
Daddy ya balla mata harara
"Ai sai ki je ki kwanan, tunda ke ce ke auren kanki".
Ta langabar da kai,
"Don Allah M.K?'
"Wallahi ba za ki kwana ba, ku je dai ki yi mishi sannu da zuwan ku dawo".
Muka shirya fes, dukkaninmu kowa ya yi kyau, ba ga yaran ba ba ga manyan ba. In da ni ce Mami, nake haifar da wadannan zuka-zukan 'ya'yan banga abin da zai sanya ni yin wani family planning ba, watakila kuma daga ita har maigidan ra'ayinsu ke nan? Allah masani.
Hajiya ta rasa ina taka-saka-ina-taka-aje da 'yan jikokinta. Jin ana oyoyon zuwan Mamin yara Sagir ya iso dakin Hajiyar, in da a can kowa ya baje suna ta zubawa Hajiya labarin kasar Turkiya, wai Yaya Mukhlis ya zama qatoto. Ta kawo musu wannan ta kawo musu wancan.
Hada idonmu ke nan muka sakarwa juna ni'imtaccen murmushi. Ya ce
"Kausar din Mami". Nima na ce, "Sagir din Hajiya".
Kowa yai dariya. Hajiya ta ce,
"Wai ni Binta sai yaushe za ki aurar da diyar taki ne?"
An soso ma mai gyambo inda ke mishi qaiqayi, ya zauna dab dani yana wani kankance ido, duk kunya ta kamani, musamman da na fahimci Mami na kallon mu, ta yi uwa ba ta gane kome ba, ta ce
"Sai randa Allah ya kawo mijin ina ce? Wannan ba ta da saurayi ko daya bakin jini ne da ita, ko za ki sa a dinga yi mata rubutun farin jini ne?"
Sagir ya qyalqyale da dariya,
"Amma Mami kin yanki gayu".
"Yo wannan wani gayu ta iya? Ita ke nan kullum cikin Pakistani da Abayat, ko irin dan fente-fenten nan da 'yammatan zamani ke yi su zama kamar turawa ba ta iya ba, wa zai taya? Don ma Allah ya taimake ta fara ce, da abun ba zai yi mata kyau ba".
Sagir dariya yake sosai, nikuma na ya mutse fuska ina kallon Mami, ya ce
"Hajiya ba sai kun wahalar da kanku ba wajen yin rubutun farin jinni, ga miji Allah ya kawo ma Kausar har gida........" Ya nuna kansa.
"......Ko ba kya so na Kausar?'
Da-dai na ga in na zauna mutumin nan zai ci gaba da tsinkani da yawa, sai na tashi na bar musu dakin. Daga ganin fuskar Mami da Hajiya ka san sun matukar jin dadin wannan al'amari.
Mami ta ce, "Da gaske kake Sagir? Bana son wasa".
"Babu wasa cikin maganata, da zarar na samu aiki na yi settling komai nawa zan auri Kausar, idan har za ku bani ke da M.K?". Ta ce,
"Me zai hana?"
****
Muje ga littafi na biyu wanda tare suke da dan uwanshi don muji shin wanene mijin Lanto? MK din ko Sagir din?
[1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: ALKAWARI BAYAN RAI ASALINSU
Asalin su Mami mutanen garin Hadejia ne, mahaifinsu Justice Mukhtar Muhammed aiki ne ya kawo shi Kano. Jin dadin zaman garin Kano ne ya sa ya baro mahaifarsa ya zo nan Kano ya sayi gidan da suke ciki a yanzu.
Su biyu kacal iyayensu suka haifa, kuma shekaru biyu ne kacal a tsakaninsu, wanda Bintan ta bawa Sagir.
Rayuwar Justice Mukhtar Muhammed da iyalinshi rayuwa ce abar koyi mai tsari mai ban sha'awa, babu abin da yake gabansu kamar kula da cigaban rayuwar su da neman na kansu. Ko da suke manyan 'yan boko, basa wasa da kasuwanci da garin Dubai. Don haka asirinsu a rufe yake babu abin da suka nema suka rasa a rayuwarsu.
Sun kuma dauko 'yan'uwansu na kauye marasa aikin yi sun dora akan kasuwancin su cikin amana, don wanda ke kula da shagon Mami ma kanin Justice ne uwa daya uba daya. Ita kuwa Hajiyar Mamin nata shagon na turaruka ne ‘Haramain’ da na wuta da su gawayin Dubai a kantinan dake layin Sabon Gari na Kano. Tun haihuwar Sagir ta samu matsalar da dole aka juya mata mahaifa.
A shekararta ta biyu a jami'a ne ta hadu da Mu'azzam Kanti, a lokacin shi yana karatun ‘master’ duka a Jami'ar Bayero, yana karatun kimiyyar sadarwa tana nazarin kasuwanci.
Rannan ne ta je cin abinci shagon ‘Al-Amir’ da ke cikin B.U.K suka hadu a kujera mai fuskantar juna, da ganin shi kaga irin daliban nan da basu da komi sai karatun, jeans din jikinsa kodadde kuma dan gwanjo. Ba a maganar kodaddiyar shirt dinsa. Haka nan Allah ya kimsa mata kaunar sa, ta samu kanta da biyan kudin abincinsu su biyu.
Ya dube ta da kyawawan idanunshi ya ce, "Ya ya za ai haka?"
Ta ce "Babu komi, niyya na yi".
Ya ce "To na gode, amma next timekar ki sake".
Ta yi murmushi ta ce, "It's my pleasure in sake next time din, sai idan bamu hadu a ‘restaurant’ din ba".
Ya ce "gashi ni kuma dama ba al'adata ba ce shiga ‘restaurant’ din ba, ni nake dafa abincina da kaina, yau din ma a masifar yunwace nake, shi ya sa".
Ta ce "Shi ya sa nake sha'awar rayuwar Campus, saboda irin wadannan experiences masu koya ma mutum rayuwa ta dogaro da kai".
Haka suka ci gaba da hirar Campus har tsayin wani lokaci. Su kai exchanging phone no da address na gida. Shi yana zaune ne a cikin quatersdin malamai gidan wan babanshi, wanda ke rike da shi tun rasuwar iyayensa a hatsarin mota tun yana karami.
Ba shi da komai sai kokari, kuma ba dan kowa ba. Irin daliban nan ne gifted da malamansu ke alfahari da su, don kuwa duk tsangayar su shi ya fiddo first class a zamanin yaye su daga digiri na farko.
Wasa-wasa sai abin nasu ya rikide zuwa mahaukaciyar soyayya. Ya san bashi da abin da zai auri Binta a yanzu, dama ko wacce mace tun da bai da madogara, sai Allah.
A lokacin da ta shiga mataki na uku mahaifinta ya uzzura da son yi mata aure, ko don ta raba shi da mazan da ke kara-kaina a kofar gidansa.
Kai tsaye ta gabatar mishi da da Kantin a matsayin wanda take son aure, duk kuwa da irin 'ya'yan manyan da ke rububi a kanta, da 'ya'yan abokan Babanta.
Mahaifin nata ya bukaci ganawa da shi, ya kuma amsa kiran.
"Binta ta gabatar min da kai a matsayin wanda take son aure, na sa anyi min duk wani bincike da ya kamata in sani game da kai na kuma samu daddadan feedback, how do you see it?'
Ya lankwashe 'yan yatsun hannunshi cikin na juna, a ladabce da kunyace ya dukar da kai, ya ce,
"Da gaske nake ina son Binta, sai dai bani da halin aure a yanzu, ina neman aiki ne, ban kai ga samu ba".
"Me ka karanta?"
Ya ce
"Kimiyyar yada labarai ne(mass comm.)".
Ya ce
"To a kawon takardun in gani ko zan iya taimakawa, nima in tayaka neman aiki".
Har gobe ba zai manta da Justice Mukhtar Mohd ba, wanda ya zamo silar duk matakin da yake da shi a yanzu.
Hatta gidan da za su zauna a ciki shi ya ba su a nan kusa da su, ya ce kafin Allah ya ba shi halin sayen nashi. Ya sama mishi aiki a N.T.A Abuja da albashi mai tsoka.
Shekaru uku da aurensu ya sayi gidan da suke ciki a yanzu, ya bai ma Justice nasa. A lokacin sun haifi Mukhlis. Rayuwarsu ta ci gaba da mikawa har zuwa matakin da suke kai a yanzu.
Yana aikin ya nemi izinin tafiya karo karatu a Jami'ar Harvard. Da ya dawo aka kara mishi matsayi, duk wasu kwasa-kwasai da ya yi bayan nan wajen aikin ne suka tura shi.
Don haka Kanti Mu'azzam har gobe yake tunawa da wadannan alfarmomi na Mami da iyayenta, ba ya da kamar su, ko shi butulu ne ya hakura ya barma Mami 'yarta.
To idan shi din ya hakura ya tilasta kansa da hakurar ita natacciyar zuciyar fa? Soyayya ce wadda ta fi karfin tunaninsa, ta shallake saninsa, wadda bai taba ji a diya mace ba. He is sorry to say it again "INCLUDING MAMI". Addu'a yake yi akan Allah ya cire mishi amma kullum kamar yana kara izata.
** **
Ya koma bakin aiki ranar lahadi da yamma, kuma a ranar ne da daddare Sagir ya zo da shirin samartaka. Duk budurin nan bai san ana yi ba, ita Mamin ba ta gaya mishi ba ko da wasa.
Ya kasa haquri da karasa jarrabawar tata, soyayyar Kausar ta yi mishi mugun kamu. Support 100% daga iyayensu da Yayarsu.
A galabaice ya zauna cikin 3 seater din Mami, a sa'ilin da ni kuma ke bisa kilishi ina cin abinci. Muka yi ma juna kwal da ido kamin mu saki dariya sassanya a tare.
"Na kasa haquri ne Kausar, jarrabawa ta ki karewa, har yaushe ne?"
Ya sauko ya sanya hannu cikin plate dina muna ci tare.
Haka ya mai da gidan Mami wajan hirarsa, dandalin soyayyarsa da walwalarsa. Ya yin da Mami ke kara jika mana soyayyar da goyon baya, da shawarwari na yadda za mu kaima cikar burin mu. Kullum ba zai zo ba sai ya qunsowa su Nur chocolate da Ice-cream, don haka ya sa suka manne masa uwa babansu, saboda ba sa ganin hakan a mahaifinsu,verystrict, though, unsocial person.
Cikin nasara Sagir ya samu aiki da AKTH bangaren yara (paediatric). Soyayyarmu kuwa sai abin da ya yi gaba, sai dai ya rage zuwa saboda aikinsu na dare da rana, sai a waya muke haduwa.
Ranar wata sunday ya samu rangwamen aiki, daga hospital din bai koma gida ba kai tsaye ya taho saboda akwai muhimmiyar maganar da yake so su tattauna shi da 'yar'uwarsa.
Da ganinsa ka ga Dr. Sageer Mukhtar Muhammed, irin mazan nan ne masu razana mata da kwarjinin da Allah yai musu.
Rataye a hannunshi na hagu lab-coat dinshi ce. Ni dai na san ina da kyau, amma har sai nake ganin Sagir din yafi karfina.
A gajiye yake muraran, Daddy na gida ya kara yi ma Allah godiya. Daddy ya dube shi ya ce,
"Da alamun the Doctor is hectic". Ya ce "Ba wani abu yunwa ce kawai, ya ku ke?'
"Kowa lafiya". In ji Mami.
Mintuna wajen talatin suna ta hira shi da Daddy, yana ta zuba ido ya ga giftawa ta ban fito ba, ya dubi Mami, "Wai ina mutuniyar ne?'
Mami tace "Tana daki, ban san me take yi ba, yarinya sai ka ce huda-huda, ban taba ganin ta babu takarda da alkalami a hannunta ba".
Daddy ya ce
"Doctor Sageeruaure sai yaushe ne? Ina ganin lokaci yayi da zaka aje iyali.
Ya ce "Bari in fito, sai in ba ka bayani".
Nan ya ajiye coat dinsa ya karaso dakinmu.
Muka sakarwa juna soyayyen murmushi, ya zo ya zauna dab da ni ya tankwashe kafa, ya kai hannu ya zare biron da ke hannuna ya soka min cikin gashin kaina, wanda ko kallabi babu. Gashin yala-yala mara tsaho yake kallo cikin al'ajabi, bai taba sanin haka gashin yake ba. Ya rufe text book ya hada da jotter ya dauke su ya yi baya da su.
"A dinga hutawa ana bai ma maigida haqkinsa, wannan ko karatun likita kike sai haka, haba Kausar, kar ki bari kwakwalwarki ta motsu da karatu mana?".
Na yi murmushi kawai, Allah na tuba idan ban yi karatu ba me zan yi? Ba uwa ba