ta dawo gare ni, na dauke ta na rungume. Ya ce,
"Ina so in maye gurbin baban Fati ne Kausar idan za ki karve ni".
Na ce, "Na gode, amma ina bukatar lokaci in yi tunani Dr.". Ya ce, "Hakan yana da kyau, na ba ki daga yau har rana ita yau Kausar, Allah ya zama jagoran mu". Na ce, "Ameen".
Na dawo gida na shimfide Fatima wadda zuwa lokacin ta yi barci a kafaduna, nima na kwana cike da tunanin maganar Dr. Habibu. Alal hakika idan da wanda na taba jin zuciyata ta yi amanna da ya maye min gurbin Sageer, to Dr. Habibu ne.
Na farko dai ya mallaki hankalin kansa, na biyu yana da wadatar ilimi irin yadda nake so. Sai na uku yana da sana'a kwaqkwara mai tsabta wacce zai iya rike ni dan ita babu takura. Sannan daga sura har zuwa halayyarshi babu na kushe, don kowa yabonshi yake a tsangayar mu, musamman saboda kamewar sa.
Washegari muna kalaci Hajiya ke tsokana ta,
"Ko ke fa? Da alama shi wannan ya samu gwamnati, tun da aka share lokaci da shi". Murmushi na yi, "Malamin mu ne fa Hajiya". Ta ce, "Kai abu ya yi kyau, kinga sai ku yi ta karatun ku". Na yi dariya.
Mun yi waya da Mami a ranar kamar in shaida mata maganar Dr. Habibu, daga baya dai na yi tunanin in kyale ta kawai tun da ban ma gama tsai da hankalina akan maganar ba.
Wasa-wasa sai ga Dr. Habib na neman samun gurbi a zuciyata, na kan vata lokaci ina tunaninsa.
Da abu yai gaba kuma sai ya kasance har waya muke vata lokaci muna yi, yana fayyace min irin yadda yake so na da irin rayuwar da yake tsara mana. Mutum ne da ya san wani abu wai ilimi, domin gaba daya karatun shi a kasar Greece ya yi shi, sannan kuma ya jima yana aiki a nan jami'ar Bayero.
Yau ne cikar ranar da muka yi alkawari da Dr. don haka tun bayan isha aka shaida min isowarsa. Sanye cikin atamfa mai karshen tsada na cimma sa a dakin baki kamar wancan karon.
Tun kamin in zauna ya ce,
"Kin san Allah Kausar tun kafin ranakun nan su cika tunanin amsar da za ki bani nake, don na ga kamar na yi miki tsufa".
Murmushi na yi, "Ashe akwai batun tsufa a cikin aure?' Ya rausayar da kai ya ce, "Halin 'yammatan wannan zamanin ke nan". Na ce, "Gara da ka ce 'yammata, amma ni ba 'yammata ba ce. Kada ka manta har da Fati a kasa". Ya lumshe ido ya fadada fara'arsa, "Ke nan na samu karvuwa ke nan?" A kunyace na ce, "Kusan haka". Ya ce,
"Bani da kalmar da zan yi miki godiya sai dai addu'ar Allah ya barmu tare, ya kuma nuna mana ranar da zamu kasance mamallakan juna, ameen".
Tun daga wannan lokacin muka shimfida sabuwar soyayya ni da Dr. sai dai ta fi karfi daga gare shi.
Ba zan ce bana son Habib ba, sai dai ni a gare ni zanyi aure ne kawai domin cika sunnar manzo da kuma farin cikin magabatana. Don zamana haka a gidan su Sagir baya da ma'ana, sai dai in ce ina zaune ne saboda makaranta, in haka ne to ranar da aka kare karatun fa?
A son Dr. nan da watanni biyu masu zuwa ayi komaia gama, amma ni na nuna na fi son sai na kare karatuna tukunna. To ba shi da zavi ban da ya bi nawa zavin.
Ina kan hanyar komawa gida daga makaranta, Dr. ya kira ni na amsa, ya ce, "Kina ina yanzu?'
"Ina kan hanyar komawa gida". Ya ce, "To gani nan yanzu zan kawo miki Saddik". Na ce, "Ka taho mishi da kayan sawa tun da yake week end ne sai ya kwana da Fatima". Ya ce, "To muna zuwa".
Saddik kyakkyawan yaro dan shekaru ukku, ya ce, "Ke ce sabuwar Momina da Daddy ya gaya mani?" Na ce, "Ni ce Saddik, ajinka nawa?" Ya ce, "Ajina ashirin ko Daddy?" Ya ce, "Mantawa ka yi ajinka tamanin". Dukkanmu muka sa dariya.
A gaskiya ina matukar sha'awar tsarin rayuwar Dr. mutum ne mai sassaukar rayuwa da rashin hayaniya. Komi cikin ilimi yake yin sa, don haka ne nake tunanin rayuwar aurenmu za ta tafi yadda nake so.
Kwananan Saddik biyu a waje na ya zo ya dauke shi, ni da Hajiya muka hada mishi tsaraba niki-niki, na shi da na Hajiyar Dr. Da daddare ya zo ya dauke shi suka tafi.
Na dawo makaranta ranar wata lahadi na cimma Hauwa'u ta zo yi min kwana biyu, da yake ta kare S.S.C.E dinta. Ba karamin jin dadin zuwanta na yi ba, abinki da dan uwa, ba ta da aiki sai rainon Fati. Ta same ni da daddare cikin sirri take gaya mani babanta ya dage ta ci gaba da karatu bayan ita kuma aure take son ayi mata.
Na ce da ita, "Daddy yana da gaskiya Hauwa'u, bakya ganin yadda auren zamanin nan ya zama ne? Yana so ya gina maki rayuwa mai inganci ne fiye da a mai da ke bazawara da quruciyarki. Don sakin yanzu mazan sun dauke shi ba a bakin komi ba. Masu karatun ma ya suka kare balle yara sabon jini irin ku?
Hauwa'u ta ce, "Bana tunanin Yusuf zai kasance daga cikin irin wadannan mazan Yaya Kausar, wallahi ya san abin da yake yi, kuma dan babban gida ne, ya yi min alkawarin barina in yi karatun har sai na ce ya ishe ni, amma bayan munyi aure".
Na ce, "Kin tabbata zai barkin Hauwa'u? A ina yake, kuma yaro ne ko babba ne?" Ta ce, "Yaro ne sabon jini bai fi twenty seven ba, a Kaduna yake aiki da matatar mai (Petrelium refinery). Ni dai wallahi ina son shi sosai, na taho wajen ki ne don in nemi shawara Yaya Kausar, don Momi ma ko zancen ba ta son in yi mata, wai na yi kankanta. Shin ana kankanta da aure ne?"
Na ce, "Ina laifin su? Suna son gina miki rayuwa ne, ya yi haquri ya kara miki lokaci atleast ki fara kammala ko da level I ne".
Ta ce,
"Na yarda da shawarar ki, kuma zan wa Yusuf bayani. Kin san kuwa kullum sai na yi mishi zancen ki?'
"Zancena kamar ya ya".
"Na kan ce mishi wata sister na ce wallahi, one year of marriage mijinta ya rasu ya barta da baby, a kullum ina tausaya mata".
Na ce, "Nima ina tausayawa kaina Hauwa'u, amma da na yi haquri ga shi Allah ya kawo min makwafin sa, duk da na san ba zai taba maye gurbin Sageer a zuciyata ba, sai dai ya kwatanta. Amma an ce a rashin uwa akan yi uwar daki".
Ta ce, "Ina ma na san ki lokacin da kuke tare da Sageer?" Na yi murmushi, moment din na dawo min fresh, kamar ya shiga cikin asibiti ne zai je ya dawo.
Hankalina ya tashi kwarai ainun, sai da na dangana da kuka sannan na ji sassaucin zuciyata. Hauwa'u ta ce, "Da na sani da ban yi miki maganar ba". Ita ma sai hawaye.
Fatima ta shigo ta kama hannuwana tana ja wai Uncle diddi....... Wato Uncle ya zo. Nan na duba wayata, ashe yana ta kira bamu ji ba daga ni har Hauwa'u. Na gyara fuskata na zizira kwalli don kar ya gane na yi kuka, amma sai da ya gane din.
Ya ce, "Idan ke matar mamaci ce, nima mijin marigayiya ne. Don haka hakan ba zai dame ni ba a yanzu Kausar, amma muddin muka yi aure nima za ki dulmiyani cikin damuwa". Bai jima ba ya tafi, dama ya zo kawo min wani littafi ne, tun da kuma am not in the mood ya san ko ya tsaya ayi hirar ba za ta yi armashi ba.
Hauwa'u ta koma da sati biyu Yaya Hajara ta yi min waya take sanar dani an kawo kudin aurenta daga gidan su Yusif, kuma Daddyn ta ya karva, amma biki sai ta kare level one.
Nan take na kira Hauwa'u muka yi ta murna, ta kuma hada ni da Yusuf din muka gaisa. Na ce da ita kuma kinga lokacin tunda na kare karatuna sai mu sha biki. Ta ce, "Biyu za'a hada dukkan mu". Na yi murmushi, don ni yanzu na fara tunanin har sai na kare NYSC ma.
Muna falo ni da Hajiya tana karatu da medicated glass dinta, cikin littafin (Ahlari), ni kuma ina nazarin takardun karatuna. Aka sanar dani ina da bako wai dan uwana ne daga Bujawa, na sa lulluvi na fita.
Na sha mamaki da na ga Sale dan Inna Laminde, a hannunshi jakar bakko ce taf da tsarabar su gujjiya, daddawa, aya, kwan zabbi da sauransu, ya ce duk a kawo min in ji Inna, kuma tana gaishe ni. Mun dade muna hira a dakin baki, na shiga cikin gida na samo mishi abinci ya ci muka ci gaba da hira.
Sai goshin magariba muka yi sallama ya juya, bayan na ba shi kudin mota.
Munyi waya da Mami a ranar take sanar dani ta koma karatu a jami'ar Chicago, sannan su Muslim duk sunyi nisa da karatu. Mukhlis ya kare karatunshi yana tare da su, na yi mata murna sosai for the achievements'din da suke ta samu a rayuwa. Sai dai ko da wasa bama yin zancen M.K daga ni har Mami, na rasa dalili.
To sai kuma ga bikin bamu shaidar karatu ya matso, dole Hajiya ta aika ma Yaya Hajara. Baba Lawal da Inna Laminde, da iyalinta duk sun halarta a gidan Justice ana i gobe za'a gudanar da taron, in son samu ne dole su Mami su halarta.
Ni dai da kaina na ki in sanarwa Mami, don na san muddin Mami ta ji dole su rankayo gaba dayan su. Tun da na samu na yakice M.K daga zuciyata bana marmarin duk wata hanya da za ta sake hada ni da shi, ko da a mafarki ne.
Sai dai shima kamar ya san ra'ayina. A cikin satin Mami da yara ne suka taho, har da Mukhlis. Take gaya min in yi haquri da rashin zuwan Daddy, yana New York din shi bai taho ba, sakamakon ayyukan office da suka yi mishi yawa, amma yana yi mani murna, digirin Allah ya sa rai aka yiwa.
Ta kawo wani dan kit ta bani, gift ne in ji shi. 'Yar akwatin samfurin ‘polo’, ba komi bane a ciki face biro, agogon hannu, nail cutter, da inki da za a durawa biron in ya kara, duka design din ‘polo’.
"Wata kyautar sai manya". Na fada cikin zuciyata. Idan kin ga dalolin da aka narkar wajen sayen wannan tarkacen banzan sai ki rike baki.
Su huda duk sun zama 'yammata, su Muslim an zama samari, 'ya'yan Mu'azzam Kanti, wadanda ba daya suke da sauran 'ya'ya ba, wurin ilimi, nutsuwa da kyawun sura.
A ranar da suka iso ne su Hauwa'u ma suka iso, gidan Hajiya ya zama ba masaka tsinke. Mami ta kara kyau da gogewa alamun komi na rayuwa zam-zam. Hajiya ke ba ta labarin Dr. Habib, don ita ba ta san wai M.K ya so ni a baya ba. Yo wane mai hankali ne ma zai yi wannan tunanin? Sai mu dabbobi (ni da M.K) marassa hankali marasa sanin ya kamata.
Koma dai mene ne ni dai alhamdulillahi tun da Allah ya kawo min miji dai-dai ni, dai-dai da rayuwata, wanda zai rike ni da mutunci har illa masha Allahu.
** **
[1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: Filin 'Convocation Square da ke cikin jami'ar Bayero cike yake da motoci na zamani manya da kanana, su Dr. Habib na gefe suna kaiwa da kawowa kafin a fara taron. Taron da ya hada har da shugaban kasa da ministoci na ilimi, da wadanda ba na ilimin ba.
Nice mutum ta farko da aka kira a tsangayarmu, kuma ni kadai na fiddo second-class Honour (upper). Don haka idan ka dubi fuskar Dr. Habibu daga duba na farko, za ka fahimci tsantsar farin cikin da yake ciki, to haka 'yan uwa da masoyana cike suke da godiya ga Allah.
Mun dawo da daddare a dakina Mami ke tambaya ta wai wane ne shi wannan Dr. Habibun?
Na yi mata bayanin sa da abin da ya kamata ta sani game da shi. Ta ce, "Kin tabbatar kina son sa har cikin ranki?" Na ce, "Da bana son shi Mami ya za ai na bari har maganar aure ta gifta a tsakanin mu?" Mami ta yi murmushi mai qunshe da ma'anoni da dama, ta ce, "Uhm! Kausar ke nan, ban san yaushe za ki daina yin abubuwanki na quruciya ba".
"Mami ban gane ba?"
"Ba nufi na ki gane ba, amma ni na gane, damuwar ki yi auren ne don a daina yi miki kwakwazo ya sa kika fidda wannan mutumin. Amma ki nutsu ki bi komi a hankali, nima akwai abubuwan da nake dubawa ne a hankali komi za ya warware maki da yardar Allah".
Na yi nisa a cikin tunanin kalaman Mami, har ban san yaushe ta fita daga dakin ba ta barni da cunkushasshen tunani. Ta dauki Fatima dake ta rikici tasa zani goya ta a bayanta, suka nufi wurin Hajiya.
Wannan na nufin......... Mami ba ta goyon bayan tarayyata da Dr. Habibu? Wannan na nufin Dr. Habibu bai samu karvuwa a wajen Mami ba? Wannan na nufin ina shirme ne ba soyayya ba a ganin Mami?
To in ban yi auren ba me take nufi da in yi? Ba zan bari Mami ta yi min sakiyar da ba ruwa ba.
Sun koma America ranar lahadi, suka bar Mukhlis saboda za su je ya gaida dangi a Hadejia shi da Justice. Sai da suka je suka dawo sannan ya yi booking flight.
Ya leko dakina da daren ranar ya ce, "To Kausar da ALHERI, sai Allah ya sake dawo da mu". Na ce, "Safe journey Mukhlis". Muka dubi juna muka yi dariya cikin tuno quruciyar mu.
Da sati ya zagayo na soma hada kayana domin komawa Jos kamar yadda muka yi da Yaya Hajara. Hajiya ba ta ji dadi ba, to amma ba yadda za ta yi, domin zan fi samun sukuni a can din fiye da nan gidanta, ko dan Hauwa'u da ta lura tamu ta zo daya. Na kuma roqe ta da ta bani little Fatima in tafi da ita za mu dinga zuwa akai-akai tana ganin mu.
Hajiya ta ce, "Anya Kausar ba wani abu muka yi miki ba kike gudun mu?" Na yi dariya na ce, "Ni kuwa Hajiya me za ku yi min a duniyar nan da zan guje ku a kanshi?" Ta ce, "To ki bar min Fatima in dinga ganinta ina jin dadi". Dole dai don farin cikin Hajiya na tafi Jos ba tare da Fati ba.
Kwanana uku kacal Dr. ya zo, mun sha hira mun more. Da zai tafi ya ce ya dace cikin watan nan ya turo magabatansa a aje wata kwaqkwarar magana. Na ce, "Ba yanzu ba sai na kare NYSC, yanzu kuma da zancen ya je wa Justice ko Baffa Lawal duk cewa za su yi ayi auren yanzu. Ya vata rai sosai ya ce, "Amma dai ba haka muka yi dake ba ko Kausar?" Na ce, "Ka yi haquri Dr. gaggawar ce bana so". Ya ce, "Shekara guda muna tare Kausar ai ina tunanin ba mu yi garaje ba ko? Kina tunanin zan iya jiranki har wata shekarar again?" Na ce,
"Ba ka fahimce ni ba Dr. atleast in fara NYSC din ko ban gama ba idan na gamsu da lokacin da ya yi mani sai na yi maka magana". Ya yi shiru bai ce komi ba, haka muka rabu zuciyarshi babu dadi.
Bai yi fushi ba dai ya ci gaba da zuwa waje na a week-end, ni kuwa ina tunanin maganar Mami ne, na cewa in bi abin a hankali in yiwa zuciyata kyakkyawan jagoranci.
Posting dina na NYSC yfito,na samu an barni a arewa inda aka tura ni jihar Kaduna.
Na fara bautar kasa ta cikin kwanciyar hankali, a sakateriyar gwamnatin jihar Kaduna. Da muka samu sarari bayan watanni uku na je Kano na gai da Hajiya, na ga Fatima ta kara wayo. Dr. ya je har K.D wajen sau uku. Hajiya ta ce, "Haka tun barin ki gidan nan kafafunshi ba su bar kofar gidan nan ba yana zuwa yana gai da mu". Na ce, "Bawan Allah ke nan".
Na fiddo waya na kira shi na ce, "Yau dai gani a Kano". Ya ce, "Kai haba, to gani nan isowa yanzu".
Na cimma shi a dakin baki dauke da Fatima, tana ganin shi ta wangale baki ta ce, "Uncle!" Ya karve ta ya ce, "My dear Fatima matar Saddik". Na yi dariya na koma ciki don samo masa abin jika makoshi.
Mun nitsa da hira ya marairaice ya ce, "Saboda Allah Kausar ki tausaya mini a sanya ranar auren nan haka". Na ce, "Na amince Dr. Allah ya bamu sa'a".
Saboda farin ciki Dr. rungume ni ne kawai bai yi ba. Muka yi sallama ya tafi da niyyar a ranar zai kai zancen ga mahaifiyarsa don ta sanar da Baffaninsa.
Tun dai rabuwarmu da Dr. akan hakan to ban kara jin duriyarsa ba, har na koma Kaduna. Sai da na yi kwanaki bakwai da komawa ya kira ni a waya.
"Kin ji ni shiru ko Kausar?" Muryarshi kamar ta mai fama da mura, ban nuna mishi na damu ba, "Ah haba, na san yanayin aiki ne". Ya ba ta shiru na dan lokaci kafin daga bisani ya yi karfin halin cewa.
"Maganar dai ba za ta yiwu ta waya ba, zan zo on week end sai mu tattauna sosai". Jikina a masifar sanyaye na ce, "To". Don na fahimci ba lafiya ba.
Dr. bai zo ba sai ranar lahadi da yamma, har na fidda rai da zuwanshi, karfe biyar na yamma ya kira ni ya ce in same shi a inda muka saba tsayuwa.
Yana cikin motarshi Toyota Camry, kafarshi daya a ciki daya a waje, da waya a kunnenshi yana magana.
Tun daga nesa na fahimci Dr. ya rame ya fita hayyacinshi, kamar wanda ya yi kwana bakwai kan gadon asibiti.
Na bude daya kofar na shiga na zauna, tun kan na idasa zama na soma koro mishi tambayar dalilin ramar shi. Ya ce, "Kausar you are my life, idan na rasa ki ban san ya ya ragowar rayuwata za ta kasance ba.
Na samu Hajiya da zancen mu, amma ta nuna min ba ta amince ba........."
"Saboda me?" Na tambaye shi kirjina na dukan tara-tara ba uku ba.
Ya ce, "Zancen da zan yi miki ke nan, akwai wata yarinya Jamila, kanwar marigayiya matata (Madina), the same parents Da iyaye suka ga ya kamata na aura a can baya, har suka gabatar min da maganar. A lokacin na amince har na ce su jiraye ni zuwa wani lokaci, a lokacin ne kuma na gamu da ke, na ji nan duniya ke kadai nake so, a take kika sauya min akalar rayuwta
Don haka ranar da na kaima Hajiya zancen ki abin da ta fara tambaya na shi ne, ya ya kuma zancen Jamila? Hankalina ya tashi, don shaf na mance da ita, tun daga lokacin da kika shigo rayuwata.
Na yi kokarin in fahimtar da Hajiya amma ta kafe, karshe da na takura sai ta ce sai dai in hadaku ku biyu in aura".
Na yi saurin dako ido na dube shi, babu alamun wasa a zancen sa. Don haka na mai da kaina kasa na sunkuyar.
Ya ci gaba da cewa ba tare da ya saurari ta bakina ba, "Bani da zabi ban da in amince da hakan, saboda tsoron kar a hana mini aureki kwata-kwata.
Daga ni har shi shiru muka yi, cikin rashin sanin abin yi. Kai idan ka ganmu sai ka rantse mutuwar iyayenmu aka aiko mana. Daga baya Dr. ya bukaci jin ta bakina, na ce ya barni sai na yi shawara tukunna.
Da na je Jos a karshen satin nake gaya ma Yaya Hajara yadda mu kai da Dr. Ta ce, "Wannan shirme ne, sai dai in shima dama yana son yarinyar, in ban da haka babban mutum kamar shi, Dr. a ilimi a ce za'ayi mishi irin wannan auren ya yarda, ai ba zai yiwu ba. Shi dai yana so kawai. Don haka ya rage naki ki yarda ko a'a, tun da dai in kin ki shi ma wani mai matar dai za ki aura, tun da sunanki bazawara".
Na ce, "Ni fa Yaya Hajara ko dama can ba wata muguwar soyayya nake ma Dr. ba, kuma Mami ta fada dama dai kasancewar shi ba shi da matar ne ya fi jan ra'ayina. To tunda yanzu yana da mata ai ya zama daya da sauran zawarawana
Ta ce, "Abin da nake so da ke Lanto, ki dage da addu'a Allah ya kawo miki miji na gari, wanda zai so ki saboda Allah ba dan wannan baturiyar fatar taki ba. Maganar gaggawar yin aure ki ajiye ta a gefe ki fuskanci abin da ke gabanki, ki nemi zavin Allah amma ba zavin zuciyarki ba".
To da nasihar Yaya Hajra na yi amfani na soma yakice Dr. Habib, musamman da aka sha bikinshi da kanwar matarshi Jamila, suka tare a cikin gidajen malamai na old site. A yadda yake nufi shi ne, wai daga baya za a zo a yi nawa bikin idan na kare NYSC.
Don haushi na goge lambobinshi daga wayata, na canza layin waya duk saboda shi. Shima tun da ya soma dandanar zumar amaryarshi ko duriyar shi ban kara ji ba. Maza ke nan!!!
Don haka na dauki al'amarin mayaudaran mazan wannan zamani na aje a gefe, masu cika mace da dadin baki har sai ta ji kanta uwa mai kambun sarauniya, sannan su yakice ta.
Na kammala NYSC dina cikin nasara, na tattaro na dawo Jos cike da godiyar Allah.
A wannan satin zuwa Kano ya kama ni, domin zan karvi wasu takardu a makaranta. Don haka na nemi rakiyar Hauwa'u, wadda bikinta ya karato dai-dai wannan lokacin.
Mun tafi da alkawarta wa Yaya Hajara kwana uku kacal za mu yi mu dawo.
Muka shirya akwatun mu direba ya sanya a mota, da tsarabar himilin dankalin Jos da Yaya ta aike ma Hajiya. Tafiyar awanni uku kwarara ta kawo mu Kanon Dabo.
A gaskiya ina matukar son garin Kano, ko da yake a nan ne na yi kusan rabin rayuwata, na yi rayuwa da Mami da 'ya'yanta, na yi da Sageer. Ya ya kuwa ba zan so garin Kano ba?
Sanye nake da atamfa xclusive baka mai ratsin fari da ruwan kasa, yafe da mayafi ruwan kasa, wato brown. Na cure gashin kaina a cikin ribbom ya leko ta kasan kallabina, sai daukar ido yake. A kafafuna flat shoe ne kirar vincci, rataye da jakarshi su kuma farare ne.
Muka yi sallama a falon Hajiya, Hauwa'u ce a gaba ni a baya. Yana sanye da ruwan tokar shadda (Ghalila), karkar da ita kamar takarda, kamar yadda yake a al'adarshi (dinkin tazarce).
Ya kara fari ya kara mulmula kiba mai tsari da ban sha'awa. A fuskarshi gashin man's pride ne kwance lub-lub kamar ana shafe shi da mai, har sheki yake. Quruciyar shi ta dada bayyana a sarari.
Yana zaune kamar yadda yake zaman carpet dinsa, wato sai ya dauki kafa daya ya dora akan daya, M.K ne.
Wani irin motsi na ji har cikin kwakwalwata ya zagayo ya kashe lakar dake cikin gangar jikina. Ban yi tsammanin zan kara ganin shi a rayuwata ba, babu mamaki mafarki nake irin wanda na kan yi lokaci zuwa lokaci a kansa.
Jin sallamar mu da ya yi ya juyo a hankali, muka yiwa juna qurii da ido na 'yan dakikai. Ni na fara kawas da kai ganin ya kasa dauke ido a kaina.
Hajiya tana "Oyoyo! Da mutanen Jos". Muka karasa muka zauna a gefen ta.
Na russuna ina gai da Hajiya, sannan na dubi shashen da yake ba tare da na bari mun sake hada ido ba, na soma gaishe shi.
Ya yi gajeran murmushi, ya ce, "Ba zan amsa gaisuwar ki ba Kausar, sai dai in amsa na kanwarki".
Na yi wani irin murmushi cikin matukar jin nauyinsa, na ce,
"Dalili?"
Ya kai hannu ya shafi kwantacciyar kasumbarshi mai tsananin taushi da sheki. Ya ce,
"Zan iya tunawa, rabona da ke tun ta'aziyyar rasuwar marigayi, daga wannan lokacin ko waya ba ki taba yi min ba balle ki yi tunanin ki ziyarce mu. Alkawari, zumunci da aminci ba su ce hakan ba".
Hajiya