da su.
A duk lokacin da na ga za'ayi zaman cin abincin zan shige toilet in yi zamana ko ba abin da zan yi. Ko sun gane ba su gane ba bai dai kara takura ni da zancen zaman cin abinci ba.
Baiwar Allah Mami, ta shigo dakinmu niki-niki da kayan tsaraba, ta samu gefen karamin gadona ta zauna, wanda ke fuskantar na Baba Larai. Ta jima tana nazarina a hankali kamar ranar ta soma ganina, duk na bi na tsargu, dama an ce mara gaskiya........
"M.K ne ya ce in canza miki daki, ya kamata a raba muku daki ke da Baba Larai, ya kika gani? Kina so ko ba kya so?"
Hankalina ya kara tashi, na yi tsumu-tsumu dani kafin na yi karfin halin cewa,
"Duk yadda kuka zartar a kaina dai-dai ne".
Ta cem "To babu laifi, zan sa a gyara miki dakin can da nake zuba kaya na kusa da dakin su Nur, ko za ki dinga kwana tare da su, yaya?"
Na ce, "Na fi son kwana tare da su din".
Ta ce, "Babu laifi, yanzu dai ki je ki fidda masu kayan wanki anjima mai wankin zai zo dauka".
Na yi mata godiyar tsaraba fal, ta ce, "Babu komi, ni ke da godiya Kausar, yadda kika tsaya kike kula min da 'ya'ya da zuciya daya nima hakan zan tsaya miki cikin kowanne hali".
Daddy bai bar Kano ba sai da ya tabbatar na koma dakin su Nur da kwana.
A satin nan ne muka fara zana NECO, don haka na dauki hankalina baki daya na miqa ga karatuna. Na kuma kirkiro ma kaina hanyar da zan dinga kauce ma haduwa da M.K a duk week end dinsa, ta hanyar komawa bayan gida da karatu inda suke yin kiwon fararen agwagin ruwa cikin swimming karami da aka tanada musamman don agwagin.
Don haka na ci gaba da zana jarrabawata cikin kwanciyar hankali, shima M.K bai kara nema na ba, ko ya neme ni bai ganni bane yana kuma kunyar tambaya oho?
Sai dai ni kaina ina yaudarar kaina ne da gangan, na san ganin shi ya fi min rashin ganinsa salama. Ni kadai na san yadda nake azabtuwa a zuci da gangar jiki da soyayyar mijin Mami.
****
Mu'azzam Kanti Mu'azzam ne zaune a makeken ofishinsa cikin ma'aikatar N.T.A Abuja, tulin aiki fal a gabansa ya kasa cimma komi.
Tunanin 'YAR MAMI? Yes! Tunanin 'YAR MAMI!! Tunanin ‘yar Mami ne ya addabe shi.
Kada ayi aikin rashin kyautawa, kada ayi aikin rashin dacewa, kada ayi aikin dana sani.
Zuciyarsa ta ankarar da shi, amma duk da haka wata kalmar nata yawo a zuciya da kirjinsa.... AURE? Eh, yana son auren 'yar Mami ko a gobe ne, idan har Fatima-Binta za ta ba shi hadin kai.
Mazaaa! Sai a barsu. Suka ce "A'ah, kar a barmu. Ba mu bane muke sanyawa kanmu soyayyar da ba ta dace din ba Takori. Sannan idan ku mata kun dauki auren wanda ka ji ranka, zuciya da gangar jikinka na matukar so, ba tare da la'akari da kusancinka da shi, ko da matarka ba, a matsayin CIN AMANA, to mu ba mu dauka a hakan ba.
Ya fiye mana da mu neme su da ZINA. Babu wanda ya isa ya sanya ma kanshi soyayya, Allah ne yake sawa! Shi ya ke dasa mana ita har ta yi rassa!! Tayi yabanya ta murqushe zukatanmu mu daina ganin dacewa ko rashin dacewa.
Ya muskuta kadan, ya yi juyi cikin lallausar kujerarsa. Shi ne zai karanta labaran wannan makon baki daya, amma ya gaza tattara bayanai. Yana tsoron kada rashin nutsuwarsa ya shafi aikinsa, da yadda shugabansu yake muhimmanta labarun wannan satin. Yana neman wanda zai fasawa cikinsa ko ya huta, a kalla ko bai samu goyon baya ba, ya rage nauyin dake gallabar zuciyarshi.
Ya tabbata bai taba fadawa a irin wannan soyayyar mai takura zuciya ba, a kafatanin rayuwarsa.
Ya rasa ta inda zai bullowa Mami ta yarda da shi, ta amince da hujjojin sa. Yana da hujjojin da zai iya auren 'yarta a shari'a da addini. Sai dai bai san yadda al'ummar al'ada za ta dauki abin ba.
Babu ta inda Fatima-Binta ta rage shi, amma yana son kari, karin kuma ba da kowa bane, da 'yarta.
Inama Fatima za ta yi mishi wannan alfarmar, ba tare da ta qullace shi ba? Ba tareda ta dube shi da wata fuska daban ba bayan wadda take duban sa da ita ta miji masoyi mai amana? She mean a lot him………!
Bayan kasancewarta uwar 'ya'yan da baya da ya su a duniya,ita din nagartacciyar matar aure ce.Mai kirki mai addini, abun alfahari ga mijinta, abun koyi ga mata 'yan'uwanta, kuma mai son shi tsakani da Allah........
A duk sanda yai wannan tunanin ne gwiwarshi take sanyi. Anya Mamin ta cancaci wannan SAKAYYAR?
Ya kifa kai jikin teburinshi, yana mai da numfashi a hankali, he must be a betrayer! A Real betrayance!!Sai dai kuma yana ji a jikinsa baxai iya haqura da Kausar ba no matter what!.
[1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: Ya riga ya yi nisan da har baya jin kira. Bai damu da duk abin da za a kira shi da shi ba, ya shirya, ya dauka, ya runguma da duk wata fuska da al'umma ko ita Mamin za su kalle shi, ko su alakanta shi da ita.
Ba zai zauna ya kashe kansa a banza ba, ko ya kamu da ciwon zuciya a karon banza da wofi saboda tsoron bacin ran Binta ita kadai ranta. Bai kuma ce baya son ta ba, ko ta gaza gare shi ta wani bangare, soyayya ce matsananciya daga indallahi ba daga yin kansa ba.
Da ya koma gida ya kira Mami, ya ce ta saya ma Kausar waya. Mami Ta ce,
"Dalili?
Wa take da shi da za ta kira?"
"Ba ta da kawaye?"
"NAMIJI MUNAFIKI………!"
FATIMA-BINTA ta furta a zuciyarta, tare da kai hannunta ta yarfe wasu matsiyatan hawaye da suka tsattsafo cikin kwayar idanunta.
A wannan dare Mami ba ta yi bacci ba, hankalinta a tashe matuka. Me take shirin fahimta ne? Me M.K ke nufi? Wannan sabuwar kulawa da yake yiwa Lanto, ta magani da mece ce? Me ke shirin faruwa a idanunta ne? Ba ta da amsa.
Ni dai sai na ga Mami da sabon kwalin waya, ta iske ni a daki ina taya Muslim home-work, ta samu gefen gadon su Huda ta zauna tana wasu 'yan nazarce-nazarcen da ita kanta ba ta san na mene ne ba.
Na dago a hankali ina gaishe ta, ta amsa fuska a sake, ta ce,
"Ga waya Lanto?"
Na ce "Me zan yi da ita Mami? Kawaye gare ni? Kuma tunda muka kare paperkowacce ta kama gabanta, kuma ko adireshinsu ban karba ba balle kuma nambar waya. ‘Am anti-social".
Ta dage sai na karba a hakan, ba ta kuma ce dani M.K ne ya ce ta saya min ba.
***
Aiki ya kacame ma Mu'azzam Kanti, ayyukan da yake tarawa, bai yi ba. Don haka a ranar alhamis ya mai da hankali ya hattama su. Gida yake son tafiya, babu abin da yake matukar son ji irin sautin Lanto. Ya kuma rasa yadda zai yi ya tambayi Mami nambar wayar.
Ya aje biro a hankali ya kama kanshi da hannunshi na dama, deep in thought! Ya ya zai yi ne? Soyayya da 'yar da Mami ta riqa a matsayin 'yar cikin ta???
Ta daina baima Kausar aikin komi, cewa take "Kin fi karfin wanke-wanke da shara a gare ni. Babbar Yaya ce ga 'ya'yana, mai taimaka min wajen hidimarsu,tarbiyyar su, da kula da su da jin dadin su".
Su yi girki tare, su yi shawara tare, su tattauna akan matsalolin kowannensu.
"Ya Allah ka agaje ni, ka fidda ni da Lanto, daga butulci da karya zuciyar Fatima-Binta. Ba ta cancanci wannan ba…….!!!”
A fili Mu’azzam Kanti yake fadin haka.
Don haka ya yi juriya cikin fin karfin zuciya, a kokarinsa na yakice Kausar daga tunaninsa da zuciyar sa. Zai karya zaman lafiya da kwanciyar hankalin da yake samu a gidansa ne kawai muddin Fatima-Binta ta fahimci halin da yake ciki.
He don't want to break his home. Yana da yakinin itama Kausar-Lanto, ta fada a kwatankwacin halin da yake ciki a yanzu. Dole ya yi wa tufkar hanci, don taimakawa rayuwar Mami, amma ba don yana jin zuciyar, ruhin da gangar jikin sun haqura da Kausar ba.
Ya mika tunanin shi ga al'amuran Ubangiji masu ban mamaki, Ubangiji duk yadda ya so haka yake yin al’amarinsa, babu wanda ya isa ya hana shi. In haka ne ke nan ba shi da laifi, ba yin kansa bane halin da ya tsinci kansa; Ubangiji ne ya assasa masa, bai kuma san yaya zai yi da qaddarar sa ba.
Haka ya dawo gidan a wannan satin sukuku da shi!. Duk irin shirin da Mami ta yi domin tarbarsa, kalailaye jiki, gida, toilet, ingantacciyar cima wadda ko a hotel albarka, tura yara da Lanto lesson don kar su dame shi, ingantacciyar tausa, mai warware jijiyoyin jiki da gusar da gajiya, ba ta burge shi ba, bata tafiyar da damuwar da yake ciki ba.
"In faranta min kike son yi Fatima- Binta, ki barni na auri abin da raina ke so……. don samun tabbatacciyar nutsuwata……………".
Haka yace can a qarqashin ransa
Shi da Mamin ne zaune a falo, shi a kishingide cikin kujera, ita a zaune dai-dai santala-santalan kafafunshi.
Huda, Muslim da Nurr suna a gaba, kamin in maro musu baya. Duka suka diba...
"Welcome Daddy……….".
Suka ruga aguje suka dabaibaye shi.
Hankalinshi na kaina, a sadda na tsuguna nake yi mishi barka da zuwa, qokarin kau da kai yake, kar mu hada ido, balle kuma ni da nake jin inama kasar ta tsage in shige, don tserar da kaina daga kaifafan idanun Mami, wadanda ba ni kadai suka razana ba har ma da shi kanshi.
Bani da zabi banda na kwashi matacciyar gwiwata da jiqaqqiyar kafata in doshi daki. Soyayya ba ta taba boyuwa no matter what a kwayar idanu ne?? A gangar jiki ne??? A baki ne ko a hanci wajen shaqar numfashi?? A reaction ne ko a emotion? Haqiqa Mun tabbata qasurguman maciya amanar Mami.
Bai fasa ba, ai namiji ne, kunyarsa ragagga ce, and he is selfish by nature.
Suna bisa tebir domin cin abincin dare, ya dubi Muslim,
"Kirawo Aunty Kausar ta zo ita ma a ci abincin da ita".
"Daddy na kiranki Aunty Kausar".
Wata irin matsananciyar faduwar gaba ce ta same ni mai keta zuciya. A sanyaye na tambayi kaina, mai ya sa Daddyn ya damu dani yanzun? Kada dai in ce abin da ke damuna shi ne ke damunsa? Idan haka ne mun kyautawa Fatima Binta? Dole nima in yiwa tufkar hanci, ta hanyar cewa,
"Ka ce sai anjima zan ci, bani tare da yunwa".
Muslim ya sake dawowa
"Mami ta ce ki zo".
Kamar in ce wayyo Allah! Ko kallabi ban daura ba saboda gigicewa, na bi bayan Muslim, kai da ganina ka san babu nutsuwa ko kankanuwa a tare dani.
Ban san sanda na zube a gabanta ba, a hankali na ce,
"Ga ni Mami".
Komi ma ta fanjama-fanjam, in ji ‘yan Magana. Bani da ilimi, bani da sani, bani da tsimi, bani da dabara sai abin da Allah ya hukunta a gare ni.
Iyakaci Mami ta kore ni, in ta fahimci ina son mijinta, karshen ta kenan. Ta riga ta bani tsanin rayuwa, tushen ilimi, zan iya karbar rayuwar a duk yadda ta zo mini.
Ban iya na dago na hada ido da M.K ba, wanda ke cin abincinshi cikin sukuni da kwanciyar hankali wanda na alaqanta nan take da ganin Kausar da yayi.
"Daddy ya ce ki dinga joining dinmu, ki daina tsawwalawa kanki zaman daki. Ni na lura ma wani ba dai-dai kike ba, wot's wrong?"
Na girgiza kai, babu amsa, don nima din ban san abin da ke damun nawa ba.
Bani da zabi ban da in hau tebir. Feeling somehow a betrayer. Na sanya serving-spoon ina dibar abincin daga cikin warmers, wadanda na tabbata babu inda zan kai shi.
Haka muka tsatstsakuri abincin daga ni har ita, uffan M.K bai ce mana ba, miskili ne na karshen-karshe.
Mami 'yar bokon zamani,
“tun da ba za ku bude baki ku furta ba, na dade da gano ku, bari in bi ku in ga iya gudun ruwanku………...”.
Abin da kowannen mu ya fahimta daga gare ta ke nan.
Don haka shima M.K a darare ya aje cokali, ya mike. Ko sashen da nake bai kalla ba. Ya koma cikin kujerar falo ya kishingida hankalinshi akan zaben tashar tabijin (ko zaben mata za’a ce tsakanin Fatima da ‘Yarta?) oho shi ya bar ma kansa da zuciyarsa sani.
Nima mikewa nayi jiki a sabule, na nufi hanyar daki, jikina ya bani Mami bin mu take da kallo, daga ni har shi.
Mace ma'abociyar ilimi da aiki da hankalinta, duk kam da al'amarin nan na ci mata rai, na dunqule mata a kahon zucci, to amma ya za ta yi da mu? Kowannen mu mahaukaciyar tsimagiyar soyayya ta fyade shi, mugun fyade kuwa.
Duk hukuncin da za'ai mana ai mana, ai dai ba mu furta ba, don haka ba ta da hujjar cewa soyayya muke ko jin nauyin juna? Tun da a da can, ai bama shiri.
Ta kuma lura tun dawowarta daga Dubai ne al'amarin namu ke neman sauya taku, ni dai na tabbata, bani kuma da shakku akan rantsuwata, na rantse ko zan mutu ba aure, ko soyayyar za ta kashe ni, ba zan taba auran MK ba, domin Mami Uwa ce a gare ni, uwar ma irin Mami? Idan har zan auri M.K, ashe kuwa zan auri Baffana,Jibir mai rasuwa, da kuma mijin da mahaifiyata ke aure.
****
Duk yadda ya yi don ya wanke zuciyar Mami da matsananciyar soyayya a wannan daren, Mamin ta bijire, ta ki ba da hadin kai, abin da ba ta taba yi ba ko da wasa.
Lallashi na duniya, ban baki na duniya, kwantar da kai na karshe ga macen da ake matukar so Mu’azzam Kanti ya yi, ko a jikin Mamin.
"Sati guda…! We’re not together, alhalin kinsan ke kadai gare ni…..Mami ki taimaki mijinki mai kaunarki...........Binta…...".
"Kauna Mu’azzam? Wace iri kenan?”
Ta fada cikin matsanancin kuka wanda a yau ya fasa sirrin dake zuciyarta.
"Kada ka mai dani mahaukaciya mana? Na ganka sanda kake lalube min waya ka dauki nambar Kausar, haka ne ko ba haka ne ba?"
"Ba haka bane, ke dai kawai tsarguwa ki kai. Yau ne na fara taba maki waya? Laifin me ma na yi miki ne at all Binta ban sani ba!".
"Kana son sani? To bari in gaya maka abin da na dade da sani. Ka gurbata min 'ya da soyayyah…… ka hanata sukuni. Kana son ruguje min ginin da na yi shekara da shekaru ina yi akanta.
Ido baya boye soyayya ‘no matter what…, to haka reaction and emotion. You are in love Ibraheem…... (Sunan da ba ta taba kiranshi da shi ba). "…….Unimportant luv kuma.
Tun da za ka hada mu ka aura ne? Shi ne abinda ban sani ba. Nake kuma son in sani? In haka ne ashe za ka iya auren Houda? To na gode! NAGODE MU’AZZAM!!!".
Ya yi qokarin kamo hannunta, ta fizge, ya kai mata runguma ta goce, ya kai mata kissing ta hankade shi....
"Tsakanina da kai Ibrahim…..sai Allah ya isa……..!!!"
Ba ta yi aune ba, ta ji saukar wawan mari akan lallausar kuncin ta. Jin ta da ganinta suka gushe na wucin gadi. Ta kai hannu za ta rama wata zuciyar ta ce "A'ah". Ta sauke hannun ta kasa a hankali.
Ganin haka kuma ya kamata ya qanqame da karfi, dukkanninsu nishi suke saki a jikin junansu. Kamar wadanda su kai gudun 1000m. Duk yadda ta yi don ta qwace kanta ta kasa, karfin ba daya ba. Sai ta sa kuka, kukan da ta dade tana hana kanta yi akan Da namiji.
Ya sassauta rikon da ya yi mata cikin kirjin shi irin na larabawan Casablanca. Zuwa lokacin ta soma nutsuwa, ko ba komi ta samu ta furta masa abin da ke cin ta a zucci.
"Ki gaya min me na yiwa 'yar taki na soyayyar? Idan na yi zan ce, na yi, idan ban yi ba zance ban yi ba.
Akan me za ki yi min Allah ya isa? Akan laifin da ban sani ba? Ki kira ta ki tambaye ta, cewa nayi ina son ta?!"
Mace mai rauni da saurin yarda da mijinta, a hankali ta soma yarda da dadadan kalamanshi, gami da azababbiyar soyayyar shi. Sai ta soma tunanin lallai laifin na Kausar ne, tun da ita ce mai tsananin jin nauyin shi, jin nauyi kuwa alamun so ne. In haka ne kuwa za ta iya karkato da zuciyarta a hankali zuwa karatu, har yanzu tana cikin shekaru na kuruciya, ‘in her teens’ ba ta isa a kira ta mace ba.
As a mother, she can control her. Ba za ta barta ta ruguza rayuwar ta da soyayya a banza ba.Soyayya wadda bata da riba, soyayyar da aka gina akan kuruciya da sha’awa. A ganin ta Lanton, bata kai wannan gejin ba.
Ko daya ba ta ga laifinta ba, ba kowacce mace ce zata iya kau da kai akan Kanti Mu'azzam ba. Tana kuma da yakinin cewa, tashen balaga ke damun Kausar, amma ba soyayyah ba. A tunaninta fa ke nan.
Cikin wannan week-end din gaba daya tattalin Mami yake kamar jaririya, duk abin da ya san yana bata mata rai ya guje shi, ya daina cewa Lanto ta zo su ci abinci, ya daina hira da ita, ya daina neman ta cikin gidan idan bai ganta ba.
Gare ni na ji dadin hakan, ko yaushe ina cikin daki ina karance-karancena cikin text books na abin da nake son karanta, watau kimiyya.
Har ya koma wannan satin bai kara yin abin da zai bata ran matarshi akan Kausar ba, duk wani feeling ma da yake da shi akan Kausar ya neme shi ya rasa, wanda ke tabbatar mishi da cewa, kwanciyar hankalin Fatima-Binta shi ne nashi.
****
Sai ya zamanto duk zuwan da ya yi in bai ganni ba baya nema, nambar wayar ma da ya sata a wayar Mami ya goge ta daga cikin wayarshi, amma bai goge ta daga cikin kwanyar kansa ba, yayi-yayi kokarin hakan ya kasa. Sai dai kuma bai taba gwada kira ba ko da wasa. Nambar ta zauna ne kawai daram a cikin kansa.
Iyakacin ganin shi da ita idan sun shigo daga lesson ne da suke yi a karshen sati in zasu wuce dakin su, ko da Mami a wajen ko babu za ta gaishe shi ya amsa, ita ma Mamin ta daina daura ido.
Jarrabawarmu ta fito, na yi matukar qokari fiye da zaton Mami, babu abin da na fadi. Ba da jimawa ba na samu admission a jami'ar Bayero, duk da yadda admission dinsu yake da matukar wuya kuwa a wancan lokacin sai mai sa'a. Ta hanyar lashe jarrabawar ‘screening’ da suka kira ‘post-UME’.
Sai dai maimakon kwas din da na nema watau MBBS, Microbiology suka bani. Na amsa na karba cike da godiya a raina a matsayin shi ne zabin Allah.
Na soma daukar lectures cikin nasara tare da fatan Allah ya taimake ni in fita kunyar iyayen dakina. Domin tun daga farkon farawa na fahimci abun da kamar wuya.
****
Daddy ya shirya mana kai ma Mukhlis ziyara kasar Turkiya a karshen shekararshi ta biyu a can, ni kuma a zangon karshena na shekarar farko a jami’a.
Ina daki muna ta aikin makaranta ni da Muslim, don Huda da Nur suna Sultan Road wajen Hajiyar Mami. Na yi saurin dawowa ne yau daga makaranta don ko jiran direba ban yi ba, taxi na hawo drop har kofar gida, sakamakon rashin zuwan lecturer.
Don haka Mami ba ta san ina nan ba, don sanda na shigo tana toilet tana wanka.
Kuma ko da na ji murda kofarta da fitowarta falo ban fito ba, don hankalina ya tafi ga tattara assignment da nake yi cikin littafin Anatomy. Magana take a waya wadda Allah ya bawa kunjuwana ikon zuqowa.
"A wane dalili za ka ce in kaita passport, me za ta yi da shi? Mu tafi da ita Turkiya akan me? Karatun ta fa? Har a week end ba su da hutu……!”......... “Zan kaita M.K, me ya yi zafi? In ka yi hukunci bani da qauli".
Hankalina ya tashi matuka, wato da gaske Daddy ba zai daina abin da yake yi din nan ba? Da gaske burinshi ke nan ya assasa kiyayya tsakanina da Mami? Eh, burinshi ke nan, tun da ya san abin da yake yi din nan ba kyautawa yake yi ba.
Washegari Mami ta ce dani in shirya za mu dan fita. Kai tsaye ‘Nigerian Immigration Service’ muka nufa, aka yi min duk abubuwan da ake yi don karbar fasfo, aka ce mu dawo bayan kwana uku mu karba.
Ni kuma na rantse in har tafiyar nan da M.K a ciki, to ba zan yi ta ba. Already su Huda duk suna da fasfon, don ba yau suka fara fita kasashen qetare ba, duk sanda M.K ya dau annual leave waje suke fita su huta, duk da ba kowace shekara yake daukan ba.
Haka a zamana a gidan sun fita ya fi a kirga, to amma shi da Mami kadai, ni da yara ake bari a gida. Ban ga dalilin da za a ce yanzu dani za ai ba, salon in hana su sakewa su da iyalinsu, nima in takura kaina. Mukhlis din ma da ba wani shiri yake yi dani ba.
Ana i gobe tashin Daddy ya iso, Mami ba ta nan ta je (Zainab Saloon), inda ake wanke mata kai. Baba Larai ma ta tafi cikin gari ta gano 'yarta, yau throughout bani da lecture, don haka ina kicin ina harhadawa Mami kayan girki waje daya kamar yadda ta umarceni kafin ta fita.
Sallamar Daddy cikin kasaitaccen sautin sa wanda ya fi na Cyril Stober (NTA Abuja) amo da fidda sauti rangadadau, ta tsinkayi kunnuwa na.
A zuci na amsa cikin damuwa, da tasowar wani abu mai ta da tsigogin jiki. Koko wani warkakken miki daya rigaya ya warke a jikin dan adam. Ya Allah ka cire min soyayyar wannan bawa naka, ko na samu sa'ida.
Har kicin din ya biyo ni, ya tsaya daga bakin kofa shi bai shigo ba shi bai fita ba, hannun damanshi dafe da qyauren kicin, na hagun rike da suit din shi, jikin shi sai 'yar cikin da zanzarewarsa.
Ya yi matukar kyau kamar yau ya fara sanya suit, kuruciyarshi ta kara bayyana, kai ba ka ce shi ne ya haifi Mukhlis ba. Sai dai ka ce Yayan shi ne.
Ni dai na san shi mutum kullum shekarunshi gaba suke, yana kara tsufa. Amma Mu’azzam Kanti sai ka rantse da Allah kullum kara masa kuruciya ake.
A hankali na juyo na dube shi, tsigar jikina ta tashi yarrr! Har zuwa yatsar kafata. Ya karasa shigowa ya iso inda nake har muna hada kafada, na yi saurin ja da baya, ya sake biyo ni na kara ja da baya.
Haka mu kai ta yi har na tadda bangon kicin na yi tuntube da lokas, ya sanya dogayen hannuwanshi duka ya sanya ni a tsakiya ya hana min hanya ya kankane kowanne bangare.
Kamar in yi kuka, shima kamar ya yi kuka. Na ce.
"Mene ne hakan Daddy?"
Ya langabar dakai abin gwanin ban tausayi, kamar ba Mu'azzam Kanti Mu’azzam ba. Anya ko M.K din Mami ne wannan???
"Na daina yaudarar kaina Kauthar da cewa wai zan iya haqura da soyayyarki, qarya ne wannan!".
Na soma qokarin sunkuyawa ta kasan hannunshi in wuce don tserar da rayuwa ta, ya kamo ni ya qanqame ya mamaye ni cikin wasu irin abubuwa da ban taba tsintar kaina a ciki ba, ko a mafarki. Ban kuma san ana yi ba a duniya.
Tunani da hankalina suka gushe na wucin gadi, bana ji bana ganin komai a duniya ta da kwakwalwata da ruhina bakidaya sai Muazzam Kanti Mu’azzam. Hakan bai hana positive sashe na zuciyata gayamin haramcin hakan ba a addinin mu (kissing) tunda ba aure ne tsakaninmu ba, kuma ba da kowa ba sai da mijin Fatima-Binta? Matar data tsamoni daga qangin rayuwa ta mutunta ni ta martaba ni, martabawar da jinina basu yi min ba, ta gina rayuwata positively! Ashe a duniya babu sauran amana indai akan soyayya ne? Shin kasa rike ragamar zukatanmu da mukayi akan soyayya da manta halacci bazai dakusar da zuciyar taimako da aminci ba a zuciyar mata irin