Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 10
uba babu dangi, sai dosanannen danagi. Tun ina sa ran watarana zan ga iyayena ko su su neme ni har na fidda rai. Ya ya za a yi Sagir din ya aure ni bai ga iyayena ba? Karatunnan shine gata na shine rufin asiri ga rayuwa ta. Wannan tunanin kadai ya sanya jikina yai matukar yin sanyi. Ya lura da hakan, don haka ya kai hannunvshi bisa havata ya dago ni mu kai facing juna, hucin numfashinsa na dukan hancina. Dukkanmu bamu ankara ba sai ganin Mami da Daddy mu kai a kanmu, bai razana ba, bai kuma canza daga yadda suka same mu ba. Ya juya ga Mami ba tare da ya cika havata ba, ya ce "Mami me ke damun 'yarki?" Daddy kallon mu yake cikin rashin fahimta, gaba daya fuskarshi ta sauya. Ya juya ya fita, Mami ta bi bayan shi ba tare da ta ce uffan ba. "Me kuwa ke damuna? Ban da soyayyar Sagir da fargabar ba zai iya aurena babu iyaye ba". "Ki dubi Allah Kausar ki gaya min me ke damun ki? Kada ki manta aure za muyi, idan kuma kina da wani ne da kike so ki gaya min mana, domin farin cikinki da kwanciyar hankalinki shi ne nawa. Kausar ba zan takura miki ba idan ba ki na'am da ni ba". A matsayina na mai son nesanta kaina da al'amarin Mu'azzam Kanti, dole in ba da goyon bayana ga Sagir, don cimma rayuwa mai amfani, amma ba don soyayyarsa ta dada ni da kasa ba. Na fi kwatanta shi da aboki mai dadin mu'amala fiye da masoyi. Idan kuma ni din har mace ce mai lafiya a jiki, kuma wadda ke da bukatar da kowanne dan adam ke da shi, to zan iya auren Dr. Sagir mu kuma zauna lafiya cikin mutunta juna, amma ba cikin soyayya ba. Bani da excessive love feeling a kanshi irin wanda nake da shi akan mijin mamata. So daya ne rak, na Mu’azzam Kanti ne. To amma ya za ai na furta mishi wannan? Don haka na furta wadda nake ganin za ta fisshe ni. "Ina tunanin iyaye na ne, Doctor Sageer, ba zan iya aure ba tare da su a kusa dani ba". "Ni kuma a shirye nake da na aure ki ko da a ce ba ki da iyayen, ko da a ce daga sama kika faxo. Iyayena duka sunyi na'am da ke, haka 'yar'uwata ko ba'a san iyayenki ba, ke an san halinki, a kalla an zauna da ke shekaru masu yawa anyi miki kyakkyawar shaida. Don haka daga Hajiya har Justice sun yadda da ke. Kuma ai ba haka za a yi mana auren ba a nemo dangin mahaifin naki ba". Hankalina ya nutsu da kalamin shi, na yi murmushi. Ya ce "To ya ya? kin amince ko a'ah?" Gyada mishi kai na yi. Ya matso dai-dai kunnena na dama ya rada min kalmar "Lanto, na gode". Ya cimma Daddy a falo, wanda har zuwa lokacin bai koma dai-dai ba, ita kanta Mami ta kasa gane mishi, wani kallo-kallo ya ke wa Sagir kamar a wulakance,kuma kamar a rashin fahimta. Shi Sagiru kam bai kula ba, ko kuma ya kula din ya yi mishi ta 'yan boko oho? Gabanshi ya zube ya ce, "Daddyn yara, maganarmu ta dazu, na ce bari in shiga in fito sai in baka bayani". "Wacce ke nan?' "Ta cewa da ka yi ya kamata in aje iyali". "To ka samo din?" "Eh, na samo, kuma a karkashin ikonka, gidanka da yardarka....." ........"Wa ke nan?" Babu haufi dircct ya ce "Kausar Mu'azzam Kanti". Yake ya yi, wanda aka ce ya fi kuka ciwo. Kafin ya tattaro nutsuwa da hankali ya dura a zuciyarsa, ya daure matuka ya yi saranda, da kyar sautin ya fito daga bakinshi. "Kausar din 'yar makaranta ce ina ce?" "Eh, 'yar makaranta ce, Baban yara, amma ai karatun baya hana aure. Ca nake kai da Mami ma haka ku kai, ba ta gama karatun ba ka aure ta?" "Anyi haka, amma ka bani lokaci in yi nazari, ita ma Kausar din akwai bukatar in tattauna da ita, don mun ji ta bakinka, ita ba mu ji nata bakin ba. Mai yiwuwa kai din ne ka gani kana so, ita ba ta ce tana son ba, kuma ba za mu yi mata auren dole ba a matsayinta na amanar Allah a hannunmu". Jikin Sagir yai sanyi lakwas, don ya lura kamar Kanti bai yi na'am da zancen ba. Ba haka yake gani a sauran mutanen da ya yiwa wannan albishir din ba. "Har zuwa wanne lokacin Mu'azzam?' "Bani nan da sati daya". "Ya yi min nisa". "Ka daure da hakan". "Shi ke nan, Allah ya jishshemu alheri". ** ** [1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: "Ban gane abin da kake nufi ba?' Ta fada dai-dai lokacin da ya shigo dakin barcinsu yana kokarin yi masu light up. Ya kashe ta kunna, ya sake kashewa ta sake kunnawa. "Tun kafin in ci kwalarka, ka gaya min me kake nufi akan kanina? Kana tsammanin yana da wata manufa ne ko wani mugun hali da za a hana shi aure a kansu?" "To ki ci kwalar tawa man sannan in gaya miki. Mtss!" Ya ja wani matsiyacin tsaki ya juya zai fice ya bar mata dakin. Ta sha gabansa. "Wallahi sai ka gaya min me kake nufi da Kausar kafin ka bar dakin nan". "Kada in mare ki Binta………". "Ka marenin mana, ai ba yau ka fara marin nawa akan Kausar ba……….". Karfi ya sa ya angije ta yai ficewarsa. Mami ta zauna a nan bakin kofa ta dinga rusa kuka. Ba ta tausaya ma Kausar kamar yadda take tausayin Sageer, yadda ya dauki son duniya ya dora a kanta. It wlll be a heart break, idan ya ji cewa wai shima surukin nashi sonta yake yi, mai yiwuwa ne ya janye ya ce ba zai hada hanyar neman aure da shi ba. Dole ta shigar da manya a zancen dan abin ya shallake tunaninta. Washegari ta shirya sai New-Site (gidajen malamai na jami'ar Bayero wajen Baffan M.K.). Bayan sun gaisa da Karima matar Baffa, ita kanta ta lura Bintan na cikin damuwa. Ta ce, "Ta zo ganin Malam ne". Ta ce, "Kash! Yanzun nan ya shiga cikin makaranta, amma ya ce ba jimawa zai yi ba". Don haka ta ci gaba da zaman jiran sa, suna ta hira da Karima har malam din ya dawo. "A'a-a'a! Yau Maman Mukhlis ce a gidanmu, jiya-jiyan nan na gama magana da shi a waya, yake ce dani karatun saura shekara biyu". Ta ce, "Haka abin yake, shekara kwana". Ya ce, "To Allah ya bamu sa'a, amin. Ya maigidan to? Kwana biyu ban ji duriyarsa ba". Ta ce, "Ai zancen shi ne ma ya kawo ni". Aunty Karima ta basu waje. Ta kwashe komi ta gaya mishi tun daga dauko Kausar da ta yi, ta kare da cewa, "Babban abin da nake gudu shine, kada yaran su farga da rashin amincewar sa hakan zai karya masu zuciya". Malam ya dube ta sosai ya ce, "Ni kam Binta, da za ki bi shawarata sai in ce ki kyale Mu'azzamu ya auri yarinyar nan, tun da dai ba haramun bane. In kin hana shi auren wadda kika san halinta ai ya kwaso miki fitsararriyar da za ta zo ta wargaza miki gida, maza ba a yi mana haka ki barmu da abin da muka gani muna so. Gara wannan kin santa, kin san halinta ciki da bai dinta, idan ita ma tana son shi, kinga kin zalince su". Gaba daya jikinta ya yi sanyi, hankalinta da nutsuwa suka zo mata, ba ta san sanda ta bude baki cikin fadin "Har ga Allah na amince M.K ya auri LANTO". "Ba sai na shiga lamarin ba ke nan?" "Ba sai ka shiga ba, ka barni ni da kaina zan gyara kurakuraina zan shirya komi". Ya ce "To Allah ya yi miki albarka, ya daukaka zuri'arki, ya kare ku daga sharrin makiya da mahassada. Na ji dadi kwarai da kika dauko al'amarin kika kawo gare ni, ba ki kai inda za a ba ki gurguwar shawara ba. Daga yau duk abin da yai miki na vacin rai ko na nuna fifiko a kan yarinyar ki zo ki gaya min ki ga yadda zan yi da shi, sai ya gwammace uwarshi ba ta haife shi ba. Saboda mu ba butulu bane, sai dai aure sunnar ma'aiki ne, bai kamata ki yi shisshigi da nuna iko a cikin lamarin aure ba, ki mutu su ki bin ki da addu'a, su zo suna cewa gara da kika mutu, kuma suyi aurensu su zo suna cewa da ba ki mutu ba da ba su samu wannan 'yancin ba". Ta kara razana, hawaye fal idonta. Ta ce, "Wallahi tallahi malam na yi nadama, na tuba Allah ya cire min kishin". Ya dauko biro ya dinga rubuta mata addu'o'i nagartattu na neman yardar Ubangiji, kasancewar shi H.O.D na Islamic Studies ne. Ta dawo gida cike da wata irin nutsuwa da karin imani, cike da tunanin hanyoyin da za ta bi ta kara musu soyayyar wadda ba da dadewa ba take fatan suyi aurensu, Kausar ta ci gaba da zama a dakinta a matsayin matar gida. Hakika tana tunanin dama ranar da Sagir zai dauke Kausar ya barta ita daya, ba za ta taba samun mataimakiya irin Lanto ba, tabbas Kausar din ALHERI ce a gare su. Wancan abin kai mai kama da jela shi ake ma kishin, bayan kuma Kausar din ba gutsire mata shi za tai ba, to taimakon da Lanto ke mata fa? Duk da suma suna taimaka mata ne amma ba za su iya biyanta da zuciyarta da amanarta data mallaka musu ba. To amma sai me? ** ** Baje suke a falon shi da Sagir da tarin envelop suna ta rattaba sunaye. A fitar da Mamin ta yi wadda ya tabbatar ba ta dadi ba ce ya san kararshi za ta kai, shi kuma idan akwai abin da ya tsana a rayuwarshi bai wuce a ce yau ya vatawa Baffan nan nashi da ba ya da kowa a duniya sai shi, ya gwammace in karar ce to ta kai ma Justice fiye da ta vata shi a wurin ubanshi, don bai iya daukar zafi ba. Tana fita dakin Lanto yai sallama, daga bakin kofa ya tsaya ya harde hannuwanshi a kirji, idanuwanshi sun kada sunyi jawur, jijiyoyin jikinshi duk sun miqe musamman na kansa sun yi rada-rada kamar mai fama da matsanancin ciwon kai. Ya ce, "Wurin ki na zo, Kauthar!" Na dago a hankali na dube sa, ganin tension din da yake ciki gaba daya na tsure, tsorona Allah kar a maimaita 'yar gidan jiya wanda har yau ban daina istigifarinsa ba. "Sagir ya gabatar min da yana neman aurenki, kina son shi ko bakya son shi?" Babu haufi, babu dogon turanci na ce, "Eh, inason Doctor Sageer". Yanayin yadda na bada amsar gatsar babu kunya ya bala’in bashi mamaki. Ya qura min ido kamar yai kuka, idanunshi a kaina still ya ce, "alright, game da lokacin aure ko kina da wani lokaci da kika ware da nufin yin aure a cikinsa?". "Yanzu ma a cikin hutu nake?" "Which mean....?' "……, am ready". Ya lumshe ido, a hankali yai murmushin da bai taba yi ba, yayimin kallon sakaryar banza kafin yace "……Allah ya ba da zaman lafiya Kauthar!" Daga haka ya juya ya fita. A take ya kira Sageer ya ce, "Ya je ya bugo invitation card na daurin aure yanzu-yanzu, next weekyake so a daura auren". Abinki da mai neman kuka……, amma ya danne zalamarsa. "So soon haka?" "Haka nai niyya, in kuma ba ka yi sai ka bar masu yi suyi". Ya ce, "Na tuba na bi Allah na bi umarninka, yanzu zan je na sanar ma Justice, daga nan zan biya wajen masu bugun I.V". Ya ce, "To ka hanzarta dai". Kafin Mami ta dawo sai ga Sagir da bandiran katina da albishirin Daddy ya amince a daura aure sati mai zuwa. "What a sacrifice?' Mami ta furta a hankali, a yayin da hawayen idonta suka zubo, ta yi kokarin kar su zubo amma sai da suka zubo din a tafin kafar Kanti Mu'azzam, wanda ya fada ya rame ya bushe a lokaci daya. "Kada ayi haka M.K…..". A yayin da ta dauki katin daya tana dubawa bayan fitar Sageer. Ya kamo matarshi ya rungume, cikin dauriya yace "………Zan iya barin komi don in faranta miki Mami, kada ki karya min gwiwa, support dinmu suke nema……". Shi kuka ita kuka, abin gwanin ban tausayi. Washegari ya tattara ya koma bakin aikinsa, da cewa duk abin da ake bukata a sanar da shi ta waya ba zai zo ba sai friday wato ranar daurin aure idan an sauko daga sallar juma'a kamar yadda aka rattaba a jikin katin. Ta ce, "Su kuma Dubai za su wuce domin sayayyar kayan aure". Hakan kuwa aka yi. Bayan mun auno kayan mun dawo, nake gaya ma Mami bana son taron biki daurin auren kadai ya wadatar. Ta ce, "Saboda ba ki da kewaye? To ni ina da su, don haka sai na shirya liyafa. Ana i saura kwana biyu daurin aure ne muka yi shirin tafiya Bujawa. Ni, Mami, Sagir da wani abokin Justice Alkali Muhyidden. In ban da faduwa babu abin da gabana ke yi, don ban san irin tarbar da Laminde za ta yi musu ba, tun da a tsayin shekarun da Baffa ya rasu ban zo na duba ta ba, sai yanzu da nake neman madaurin aure. Amma akasi ga tunanina, Laminde ta yi mana kyakkyawar tarba, ta yi mana shimfida ta kawo mana ruwa a kwanon sha mai tsabta. Ta ce, "Uhm! In gaya miki Lanto, watan da ya wuce wasu turawa suka zo neman ki, sun ce su dangin uwarki ne, don Haladu dan gidan Malam Mummuni na kira ya yi mana tafinta. Na nemi Hajiya Hajara na rasa, dan ita kadai ta san inda kike, sai kuma marigayi. Ala dole suka hakura suka koma, amma sun ce duk ranar da Allah ya kawo ki na karvi adireshin inda kike na ajiye musu watarana za su dawo". Dukkanmu mun kidime, barin ma Sagir, ya ce, "Amma dai Inna kin san tana garin Kano, Kano kuma ba vuyayya ba ce". Ta ce, "In na san tana Kano na san inda take a cikin Kanon?' Haushi da takaici ya ishi kowa. Ta sake cewa, "Tun da Baffanki ya rasu ba ki kara leko mu ba, idan ni ba 'yar'uwarki ba ce a kalla zan ci darajar riko, kuma ki yi zumunci da 'yan'uwanki". Kowa ya ce, "haka ne, Kausar tana ba ki haquri Inna". Ta kira Sale ta ce, ya je ya kira Baffa Lawal mai bin Yaya Hajara. Gidansa babu tazara sosai tsakaninsa da gidanmu. Baffa Lawan ya iso yana ta lale da baki, ya ce, "Lanto ba ki kyauta ba, saboda ni ba Baffanki bane tun da Baffan naki ya mutu ba ki kara gaishe mu ba". Na sunkuyar da kai na yi ta ba su haquri, ya ce, "A to, kanki ki kai wa. Arniyar uwarki ta turo neman ki ba mu san inda kike ba". Na ce, "Babu komi, inda rai da rabo watarana za mu hadu". Ya ce, "Haka ne". Mami ta gabatar da Sageer a matsayin mai neman aure na. Baffa ya sanya albarka, aka qulla komai na aure bisa al'ada da addini, muka baro su cikin dadin rai, bayan Sagir ya bi duk ya cika su da toshi. An rabu akan ana saura kwana biyu direba zai zo ya dauke su. Har kuma Hajara da ke Jos za su tura mata ta taho. M.K bai iso ba sai ranar daurin aure wato friday, ya hade cikin lallausar shadda fara kal, wadda kallo daya ya ishe ka kimanta daraja da qualitynta, sai walkiya yake duk inda ya gitta, sai ka ce shi ne angon. Sai dai kuma ya saya kwayar idonshi cikin dark space na ‘Prada’, ta yadda ba za ka gano halin da zuciya da kwayar idanunshi ke ciki ba. Na sha tambayar kaina shin maza irin su MK nawa ne a duniya? A komi MK daban yake, a duk inda ya shiga baya da na biyu, wannan kuma baiwa ce daga Allah. Irin wadannan mutanen dai-daiku ne a cikin al’ummah, Daurin auren da aka yi a masallacin da ke cikin unguwar Nassarawa ya tara albarkar al'umma da dama, duk daga bangaren su Sagir da mahaifinsa, sai 'yan tsirarun abokan Daddy. Ba yadda Baffa Lawal bai yi da M.K ba akan ya karvi wakilcina amma ya ki, sai shi Baffan ne ya amsa akan sadaki naira dubu hamsin kacal. Da yamma ne aka wuce 'Alliance Francais’ inda Mami ta shirya liyafa, ta yi min ado cikin laffaya ruwan sararin samaniya, kai ka ce baquwa ce daga kasar Mouritania. Aka ci aka sha aka yi videos da photo, amma ba a dauko mai kida ba. Abin ma da babu wasu 'yan mata duk kawayen Mami ne, yawanci 'ya'yansu ne su kai min kawance, sai kuma course mates dina da muke mutunci, don ni kam bani da wata shakikiyar kawa, kowa abokina ne. Shi kansa Sagir din ai a matsayin aboki nake kallon shi, bani dainfatuated feeling a kan shi. Shima angon yana can shi da nashi abokan suna tasu walimar a gidan Justice, wadda aka bankare raguna uku aka gashe, aka kyafe, sai naso suke, kuma duk abin da aka ci daga Chines Restaurant aka yi odar shi. Sai da duhun dare ya shigo idanuna suka raina fata, yau fa ake yin ta, zan bar Mami, kannena da kyakkyawar rayuwarmu? Ina! Sagir ya sake tunani, na aure shi ba don ya rabani da Mami ba, sai don ci gaban abotarmu, ya ci gaba da zuwa gidan mana kamar yadda ya saba muna hirarmu". Na furta ga Mami cikin matsanancin kuka, A yayin da ta karkace tana yi min kwalliyar amarci da wani farin cotton lace mai kananan duwatsu. Ya bi jikina ya kwanta saboda laushinsa. Ta kawo turaren 'fahrenhiet' ta feshe ni da shi. "AURE YAKIN MATA….." In ji Mami, wadda kuma can a karkashin zuciyarta wata irin voyayyar nadama ce. Motocin daukar amarya suka iso, to nan fa ake yin ta. Nur da Huda, sun kama bakin kofar dakinmu sun kankane ba inda za ni, sai da aka ce har da su za a tafi sannan suka hakura. Gidan da Justice ya saya ma Sagir yana nan a Hotoro G.R.A, gida ne flat mai dakuna ciki uku da falo biyu, kicin da store da study room. 'Yan kawo amarya suka watse, Mami ta lallava su Nur suka bi ta da alkawarin gobe za ta sa direba ya kawo su. Aka barni daga ni sai halina, ji na yi kamar kabari aka kawo ni aka binne, kowa ya watse. Sagir da abokan aikinshi Doctors suka cika falon, ina jin su suna ta daru wai su lallai sai sun ga amarya, shi kuma ya dage ba wanda ya isa ya gane mishi mata. A karshe dai su sukai nasara, don sun ce ba inda za su idan ba su ga amarya ba. Ya yi sallama a dakin ina takure gefen gado, kaina cikin gwiwoyina, in ban da rabzar kuka ba abin da nake. Ya zo ya zauna dab dani ya mika hannu ya ciro kaina daga cikin gwiwoyina, ya sa harshe yana lashe hawayen. Ya ce "Wa ya tavo min my babe?" Abu ne wanda ban taba ji ba, kuma ban taba gani ba. Sai da ya yi mai isarshi tukunna ya koma cikin nutsuwarshi, ya ce "Taso muje ku gaisa da Doctors, sun dage sai sun ganki, na yi na yi su tafi sun ki". Na miqe na gyara lulluvina, hannuna a cikin nasa muka yiwa falon kawanya. '"Fantastic!" In ji daya daga cikin su, "Allah ya bar kauna ya sanya alkhairi". Sagir ko kunya babu ya ce "Amin". Ya soma gabatar min da su, "Wannan Dr. wane ne, likitan ka za ne, wancan Dr. wane ne, likitan kaza ne". Wani a cikin su ya ce, "Kai kuma fa?" ya nuna kanshi Ya ce, "Ni Dr. Sageer Mukhtar Mohammed ne, likitan yara ne". Aka kyalkyale da dariya. "Amma by now na koma likitan soyayya". Suka ce, "Allah ya ba da zaman lafiya Dr Soyayyah". Haka suka fice suna ta kwarara mana addu'a. ** ** [1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: Ba zan iya cewa ga abin da zan dorar a first night dina ba ban da azaba. Amma a hakan ne Mami take ce dani wai auren abun so ne? Ina kalubalantar Mami. Idan wannan azabar ita ce auren, to lallai zan koma inda na fito. Ga Sagirun ko a jikinsa, annashuwa yake yana kara zafafa soyayya. Albarka na shata fadi yake, wai 'yar jami'a ta kawo budurci gidan miji. "Am proud of you Lanto, may ours be among the bests!" Daga ranar kuma bai sake kulani da wannan ba, don ya lura a matukar tsorace nake da shi. Sai bayan sati guda bayani ya sha bambam, aka koma 'yar gidan jiya. "Da na san kai dan iska ne ma mugu, wallahi da ban amsawa M.K aurenka ba". Dariya ya yi cikin matsanancin nishadi, ya ce, "To say I love you is not a way to express a feeling……". "Wata sabuwar kalma ce wannan a cikin soyayyar wadda ban sani ba ko me?" "Yeah, ba ki sani ba, bara in koyar da ke daki-daki, dalla-dalla……..". Kamar ba Sageer ba, ban san ina ya koyo wadannan al'amuran ba. Ko naki ko na so cikin dan lokaci dole Sagir ya soma samun kyakkyawan matsugunni a zuciyata, fiye da matsayin da na aure shi a kai. Iskanci kuwa (kamar yadda nace) bai rage ba sai ma abinda ya karu.Maimakon tsana, sai ma hakan ya rikide ya koma sayo masa matsananciyar kauna a zuciyata. Lallai miji ba wasa ba. ** ** Satinmu uku da aure muka tattara muka koma gidan da asibiti ta bai ma Sagir cikin AKTH. Sagir ya ci gaba da aikinsa cikin nasara da kwarewa, yayin da nima na ci gaba da karatuna cikin kwanciyar hankali. Sau daya na je gidan Mami ban kara ba, saboda yadda su Nur ke rikicewa idan zan tafi. Ita Mamin tana zuwa a kai a kai, ko ina da wata damuwa? Tana so ta ji, in akwai in fada mata, ta yi min maganinta, in babu in ce mata babu. Yo me Sagir din ma zai yi min na rashin kyautawa? Kullum cikin tattalina yake da tattalin farin cikina. Miji ne na fita rsara kuma abin alfahari, don haka a kullum kara son shi nake. Ko da wasa Mami ba ta taba yi min zancen M.K ba idan ta zo, ban kara jin duriyar shi ba, kuma nima ban tambayeta ba. Na tuntuvi Mami ko za ta sake neman mai taimaka mata ne? Ta ce, "Baba Larai ta isheni 'after all', yara duk sun girma sun iya kula da kansu. Wani zubin ma kafin in tashi daga barci sunyi shirinsu sunyi tafiyarsu". Nima din ko da wasa ban taba gwada tambayarta M.K din ba. Katsam Mami ke gaya mani aikin da M.K ya nema da gidan talabijin na CNN ya fito, za su koma kasar America da zama, sabon wata mai kamawa. Duk inda hankalina yake to ya dugunzuma ya tashi, na yi ta kuka kamar raina zai fita, na ce, "Ni sai dai in bisu, na fasa auren". Ta ce, "Kar ki damu kanki Kausar, ga Hajiyarmu ga Justice suma iyaye ne a gareki. Uwa-uba mijin da ke matukar son ki, ki rike su kamar mu, babu abin da muke yi miki da ba za su yi miki ba". Haka kukana da tashin hankali na bai kara ko ya rage komi daga hijirar su ba. A kullum kokarin Sagir shi ne ya faranta mini, ya dadada mini da soyayya da kulawa. Nima kuma ina iya kokarina wajen kyautata mishi, sai dai can a karkashin raina wani gyambo ne wanda har yau bai warke ba, ban kuma san ranar warkewar sa ba. Don haka na tattara al'amarin na mika ga Allah, ina mai rokon shi jagoranci a rayuwar aure na. Duk wani masoyin M.K na gaskiya ya taya shi murna da samun wannan aikin, ya kuma yi tattaki har gida ya je ya taya shi murna. To haka Sagir ya ce in shirya ranar asabar da daddare mu je muma mu yi wa Daddy congratulations. Ni kam da Sagir zai yi shawara dani sai in ce da bai sani cikin 'yan taya murnar nan ba, bana son duk wata alaka da za ta sake hadani da Mu'azzam Kanti. Tun da na yi aure bamu kuma haduwa ba, kuma bana son haduwar tamu. Allah shi ne kadai masanin wannan sirrin, don haka shi kansa Sagir ya lura da sauyawar da fuskata da gangar jikina ma gaba daya da ya yi zancen zuwa yi ma Daddy

Chapter 6 of 10