murna tare da ni.
Na lura jikinsa ya yi sanyi, ya kuma shiga cikin wani dan tunani. A satin gaba daya ban gane masa ba, ya birkice min kamar ba shi ba, ya zama wani irin mutum mara umh mara umh-umh. Sai dai yai ta bi na da kallo kamar yau ya fara ganina.
Na yi tunanin ko kin ba da goyon bayana da zuwa yi wa Daddyn murna ne ya vata mishi rai? Don haka na ce mu shirya muje, shi kuma ya ce "Fau-fau ya fasa".
Yana kwance cikin rest chair, bayan ya dawo daga aiki, rike da jaridar ‘Triumph’ yana nazari, na zauna dai-dai kafarshi ina mishi tausa a hankali, ya janye kafarshi ba tare da ya ce dani ko ci kanki ba.
Na kwace jaridar na ce, "Sagirrr!".
Da wasu irin rinannun idanu ya dube ni, kala bai ce min ba.
"Na rasa kanka cikin 'yan kwanakin nan, na yi tunanin ko na yi laifi ne ban gano ba? Na bincika ko daga ina kuskuren nawa yake in gyara, Allah bai bani ikon gani ba. Ina so ka gaya min don Allah don darajar iyayenka laifin me na yi maka?" Idanuna suka cicciko.
Kamar ba zai yi magana ba, tsayin mintuna a kalla goma kafin ya ce, "You want to know?"
"Eh, I want know my mistake for reconciliation".
Ya yi murmushi, "Meye dalilinki na qulla gaba da Daddy?"
"Gaba? Wace irin gaba?"
Ya sake murmusawa, "Gaba mana? A tunanina ke ce mutum ta farko da za ta fara yi mishi murnar abin alherin da ya same shi, idan ba bakin ciki kike ba meye hujjarki na kin son zuwa ki yi mishi murna?"
"Na ce da kai hakan?"
"Ba ki ce ba, amma yanayinki ya nuna, kuma masu iya magana suka ce, "Labarin zuciya a tambayi fuska".
"Tunda dai ban furta hakan ba, ba ka da hujjar da za ka ce haka. Mai yiwuwa ni wani abu daban nake tunani a lokacin".
Ya ce, "Ko?"
Ban amsa ba.
"To bani wayarki?"
Ba tare da wani tunani ba na je daki na dauko na ba shi. Ya shiga lalube-lalube wanda ban ga dalili ba, yana zargina ne da voye wani abu a cikin waya ko me?
Ya caje wayata tsaf, kamin ya miko min abata. Yana kallona da wani irin murmushi mai lankwashe da azababben kishi. Na kama shi ya janye, na rungume shi a gigice.
"Kada ka tayar min da hankali Sagir, mene ne?"
Ya angije ni, "Ni ba mahaukaci bane Kausar, meye dalilinki na kin sanya nambar Daddy a dukkan wayoyin ki? Kina nufin ba ki da alaka ne da shi ko ya ya sai matarsa?"
"To yanzu me ya kawo wannan tambayar, ina ruwana da nambar Daddy?'
Ya sake kashe ni da wannan kallon da bana so, kallo ne mai cike da tuhuma, zargi da rashin yarda. "Ba ki da abin da za ki ce ma M.K a matsayinshi na wanda ya rike ki har auren ki?"
"To me zance da shi? In mun hadu ai za mu gaisa".
"Haka kawai ba za ki iya kiran M.K ki gaishe shi ba?"
Frankly speaking na ce, "Ba zan iya ba".
"Dalili?'
"Nauyi yake yi min Sagir, ina matukar ganin girmanshi".
"Ni kuma fa?"
A fusace na ce, "Ka isheni da silly questions Sageer…………why all these?".
Yayi wani irin murmushi cike da KISHI idanun shi a karkace yace
"Bana nufin komai da ke sai ALHERI, kina son MU'AZZAM KANTI".
Na sunkuyar da kaina domin na kasa jure kallon kishin da yake jifana da shi, a sanyaye nace
"Ni na gaya maka?"
"Ba ki gaya min ba, don haka a barshi a hakan, tsinkaye na ne kawai nake gaya maki b,a kuma cewa nayi lallai ki yarda da ni ba, hakkannan ba jayayya nake so muyi ba ‘it is my observation’, ki yafe ni. Sai dai ni na san ba zan iya saki in bar mishi ba, don nima ina son ki…………!"
Sati guda muka kwashe cikin wannan takaddamar kafin Sagir ya sauko, daga baya kuma ya mance zancen shaf, don shi dama yana daga cikin irin mutanen da ba su fi ya sanya abu a ransu ba har ya zo ya dame su ya hana su aiyukan su. Musamman da wanda ake bidirin dominsa ya daga ya bar kasar shi da iyalinshi.
A wannan watan na lura ina fama da laulaye-laulayen shigar ciki, ni ce barci, kasala da kwarara amai. Gaba daya hankalin Sagir da kulawarshi sai ya dawo kaina. Ina matukar alfahari da samun Sagir a matsayin miji da babu ta inda ya rage ni. A haka na ci gaba da fama da karatu da laulayin ciki, har Allah ya sauke ni lafiya na samu Fatima-Binta, sunan da da gani har Sagir muka amince mu sanya mata ke nan.
Ai kuwa Sagir na yi mata albishir kafin suna da kwana uku sai ga ta ta iso da tsarabar baby rankatakaf, duk da ba abin da Sagir bai saya ba. Su Nur suna ta murnar samun kanwa.
A gidan Hajiya aka yin taron suna, wadda ta ce ba a kyauta mata ba tun da ba a yi mata kara ba, kanmu da Mamin mu kawai muka sani.
Ni da Sagir mu kai ta ba ta haquri da alkawarin next haihuwa idan mace ce ita ce, idan namiji ne Mukhtar ne.
Bayan haihuwar mai sunan Mami da watanni hudu, Sagir ya soma nuna min wasu abubuwa da bana ganewa. Alal misali, ya fi ya yi min zancen M.K da son gyara alakar mu da ta gurvata.
Abu na farko da ya fara yi shi ne, zuba min nambobin wayar M.K a wayata, ya kuma ce lallai a gabanshi in kira shi in gaishe shi, a cewar shi M.K bai cancanci gaba ba daga gare ni. Koma mene ne a tsakaninmu a can baya ya wuce. Sai a manta a fuskanci gaba.
Dole na yi dialling nambobin akan idonsa, kuma a hands-free. Ta jima tana ringing kafin ya dauka. Ya yi magana cikin muryar nan tashi mai rikita ni da gigita ni.
"Salam, wa ke magana?"
Na yi ajiyar zuciya mai nauyi na ce, "Kausar ce".
Shiru ya yi bai ce komi ba. Na yi ta maza na tattara nutsuwata musamman da na tabbata Sagir observing dina yake. Ya Allah ka cire min wannan masifar, da aure na da iyalina ina ruwana da mijin Mami? Ko ma dai mene ne bani da laifi shi ya sani, da baya yi min zancen da tuni na mance da M.K, don haka ko yaya ne laifin nashi ne.
"Cewa za ki yi Mrs. Sageer Mukhtar Mohd.anyway. Ya kuke? Ya uwargidata?'
"Duk muna lafiya".
Tsigar jikina ta ci gaba da tashi, kirjina ya soma bugu, abin da nake gudu ke nan, amma Sagir din da gangan ya ki ganewa.
A sanyaye na mika ma Sagir din, na miqe nai daki ya bi ni da kallo. Suka ci gaba da hirar su ta tsawon lokaci, kafin suyi sallama.
Haka muka ci gaba da zaman da dadi ba dadi, shi yana tuhumata da don me na san ina son M.K shi na aure shi? Wannnan yaudara ce. Ni kuma ina mai kalubalantarsa da cewa, ni da zuciya daya na aure shi, amma wannan rashin yardar da yake nema ya vullo da ita, ita ce za ta cuce mu gaba daya, tun da dai na riga na yi aure ai magana ta kare. Idan na yi mishi irin wadannan kalaman sai ya ji sanyi.
Fatima na da watanni bakwai na shirya zuwa Bujawa, Laminde ta karve mu sosai. Mun je gidan Baffa Lawal mun gaisa, ya ce, "Har yau babu labari, masu nemana daga dangin mahaifiyata ba su sake waiwayo wa ba". Ya ce, "Amma in kwantar da hankalina, in da rai da rabo". Na ce "Haka ne".
A satin ne tafiya ta kama Sagir da mahaifinshi daurin auren wani cousin din Justice din zuwa garin Hadejia. Ni dai haka na samu kaina da bana son Sagir da wannan tafiyar, shi kuma sai xoki yake, a cewar shi ya jima rabonshi da garinsu.
Ya gama hadewa cikin kaftan ina tsaye harde da hannuwa jikin kofa ina kallon shi, ya yi kyau matuka ta yadda har na kasa dauke idona a kansa. Sha'awar mijina ta tsirga mini har kashi da vargo. A duk sanda irin wannan ta same ni yana ganewa, ya san kuma ko zan mutu da sha'awar ba zan taba furta mishi ba. Ina kallon shi yana dariya kasa-kasa, kamar bai san halin da nake ciki ba. Na san a ranshi cewa yake, "Yau dai zanga iya gudun rowan ki……".
"Ni bani hanya in wuce, kin wani kankane min kofa…..".
Na bi shi da idanu, ya sake kashe ni da shegun lumsassun idanunsa, ban san sanda na kama shi na kankame ba.
Duk wata kwalliyar daurin aure mun hargitsata, anyi squeezing dinta. Sai da muka dawo normal ya duba agogo, ina jin tun auren mu bamu taba samun gamsasshiyar soyayya ba irin ta yau ba, it's among the moments of history..... those unforgettable moments...precious and remembered!.
Sagir ya kasa sakina, kissing ya ke babu kaqkautawa. Sai da wayar Justice ta katse shi, da kyar ya mika hannu ya amsa, inda Justice ya fara yi mishi fadan shanya su da ya yi.
Muka kintsa muka fito, sai wasu kayan ya sake don na cukurkuda wadannan. A kofar fita falo ma ya sake ban peck a kunci. To haka da ya shiga mota ya tayar ya ce.
"Dan kara miko min kadan".
Na zura kaina ta tagar motar ya ci gaba da romancing yadda ranshi yake so. Da kyar ya ja motar yana daga min hannu tare da fadin, "Take care of urself…….Lanto". Cikin murmushi nace
"I will, in sha Allah".
Haka na zauna shirim a falo abin duniya du ya dame ni. Mai sunan Mami tana wurin Hajiya yaye, tun satin da ya wuce. Haka nan dai na soma samun faduwar gaba lokaci-lokaci.
Na kunna tauraron dan adam don raba kaina da tunanin da ke addabata, amma bana fahimtar duk wasu programme da ake gabatarwa.
Karfe hudu na yamma sai ga Idi direban Hajiya, da ganin fuskarsa ka san a dimauce ya ke, duk da yana kokarin voyewa.
Muka gaisa a takaice, ya ce, "Dama Hajiya ce ta aiko ni cewa in zo in dauke ki".
"Ga shi Doctor ba ya nan, in kiran ba na sauri bane me zai hana idan Dr. ya dawo mu zo da daddare?'
"Ai Dr. din ta gaya mishi, kuma shi ya ce in zo in dauke kin".
Gabana dai bai daina faduwa ba, karewa ma faduwar gaban yanzun ta fi ta farko. Mayafi kawai na dauko na yafa akan doguwar rigar da ke jikina, na bi bayansa bayan na sa key na rufe kofar shiga gidan.
Tun daga farkon layin har karshen sa cincirindon mutane ne, kuma abin mamaki a kofar gidan su Sagir cunkoso ya fi yawa.
Da kyar nake iya daga kafa kamar ba a kan kasa nake tafiya ba, hankalin kowa ya dawo kaina, ban tsaya ba sai a falon Hajiya. Nan ma cike yake da mutane, aka ce in karasa cikin daki Hajiyar tana can.
A yadda na ga Hajiya abun babu dadin fade, ta ci kuka har ta gode Allah, idanuwanta kamar barkono aka gumbuda musu. Na zauna a gaban ta a galabaice.
"Hajiya me ke faruwa ne? A fidda ni duhu".
Ta kamo ni ta rungume muka ci gaba da kukan tare. Tun ma ban ji musabbabin ba na tabbata koma dai mene ne ba mai dadin ji bane.
"Ki yi wa Allah Hajiya ki gaya min abin da ya faru".
Amma Hajiya ko uffan ba ta ce mini ba.
Wani dan'uwan Justice ne ya shigo, "Ina Kausar din? Ta zo an hada shi ta yi mishi addu'a, kema Hajiya ki taso".
"Wa aka hada?" Na tambaya cikin karaji?
Hajiya ta ce,
"Duk wani mai rai mamaci ne Kausar, muma nan duk ita muke jira, Allah ya yi ma Sagir rasuwa akan hanyar su ta dawowa, sun samu accident a take Sagir rai ya yi halinsa, Justice kuma yana gadon asibiti ya samu karaya har biyu a kafa, ki yi dauriya ki je ki yi ma mijinki addu'a.
Ta kama hannuna muka miqe tare, har falon Justice, inda gawar Sagir dina ta ke. Na dai bude fuskar na tabbatar shi ne, ban kara tantance me ke faruwa a duniyar ba.
****
[1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: RAYUWA, JUYI
Sati biyu bayan rasuwar Sagir mutanen America suka koma, ko da yake shi Daddy dama kwana uku ya yi ya tafi ya barsu. Daddy ya zo har dakin Hajiya ya yi min ta'aziyyar maigidana.
Mami ta ce in ci gaba da zama nan gidan Hajiya in kare takabata kafin a san abin yi. Hakika mutuwar dan'uwanta ta doke ta fiye ma da Hajiya, ta rame ta yi fiyat.
Hajiya kuwa kullum karfafa min gwiwa take akan haquri da dangana. To Sagir din ne abin so ga kowa, kuma mijin da nake da tabbacin ba zan samu mai kaunata kamar shi ba. Don haka maganar wai in daina tunanin Sagir ko in daina yi mishi kuka abune da na tabbatar har abada ba zai taba yiwuwa ba…!
***
Daki guda Hajiya ta ware min nake zaune. Da na kare takaba na koma makaranta. Ina cikin shekara ta karshe ne, don haka al'amarina babu sauki. Mai sunan Mami tana debi min kewa, kullum na ganta sai in ga kamar naga Sagir saboda tsabar kamannin su.
Bana yin sallah in tashi ban rokawa Sagir rahama da gafarar Ubangiji ba, a matsayinsa na wani mutum da ya inganta rayuwata 'positively'. Wani al'amari wai shi aure ya fice min a ka, Sagir kawai nake so, kuma Allah ya karva.
Hajiya da Justice suka soma damuwa da karakainar zawarawa da tuzurai a gidansu, ina sawa ana korar su.
Rannan muna zaune a falo take yi min fada akan in yi haquri in fidda miji cikin su in yi aure ya fiye min kwanciyar hankali, don har yau, shekara guda da rasa Sagir, ban koma cikin nutsuwata ba.
Na ce, "Hajiya idan kina tunanin zan iya hada rayuwa da wanin Sagir kin yi kuskure....."
Ta ce, "Ba ki yarda da kaddara ba ke nan Lanto?" Na sa havar zanina na share hawayen da suka kawo min zarya, na ce, "Na yarda da kaddara, to amma Hajiya auren ne kawai bana marmari, bana sha'awa. Gatan da za ki yi min Hajiya shi ne kawai ki dinga sanyani cikin addu'ar ki".
Ta ce, "Ai kullum ina yi miki Lanto-Kausar, Allah ya zava mana abin da ya fi ALHERI". Na ce "Amin".
Muka samu hutun zangon karatu na farko, a wannan lokacin ya zamanto na samu kaina da son neman shiri tsakanina da dangin mahaifina. Don haka na sanar da Hajiya ina son zuwa Jos wajen Yaya Hajara, daga nan kuma idan na kwana biyu sai in wuce Bujawa.
Direba ya ajiye ni a kofar gidan Yaya Hajara da misalin karfe biyar na yammacin ranar litinin. Na tsaya a kofar shiga na danna kararrawa, wata yarinya budurwa 'yar kimanin shekaru goma sha biyar ta zo ta bude kofar.
Ko ba ta fada ba na gane ita ce Hauwa'u diyar Yaya Hajara ta fari. Babu alamun sanayya ta ce, "Shigo".
Na samu gefen kujera na zauna ina nazarin dakin, muka gaisa cikin rashin sanin juna. Ta ce, "Mama ta je ofis amma ki jiraye ta tana kan hanyar dawowa.
Na tambaye ta, "Dama Mama tana aiki ne?" Ta ce, "Ma'aikaciya ce a bankin G.T watau (Guaranteed-Trust)". Ta kawo lemu da snacks ta ajiye mini. Abinki da jini, nan da nan muka saki jiki da juna muka soma hira sosai. Dai-dai lokacin da sauran kannenta suka shigo daga Islamiyya.
Yaya Hajara 'ya'yanta biyar, Hauwa'u ce ta fari, sai Gaddafi, Fa'iz da Fa'iza, da autarsu Maryam.
Shida dai-dai Yaya Hajara ta iso, bayan ta yi parking motarta a harabar adana motoci, ta shigo rataye da jakarta. Sanya kanta ke da wuya cikin falon ta yi turus, "Wa nake gani haka kamar Kausar? Yau a gidana?'
Na sadda kai kasa ina wasa da'yan yatsuna, na ce, "Ni ce Yaya". Ga dukkan alamu jikinta ya yi sanyi, a take nadama ta zo mata.
Wato dan uwanka dan uwanka ne, no matter what, ita taki Kausar, yau ga Kausar din ta biyo ta da kafafunta.
Sai da ta shiga bandaki ta yi freshen up gajiyarta, ta iskeni a falon. A take ta sa Hauwa'u ta shigar min da jika ta dakinta. Ta samu kujera mai fuskantata ta zauna, ta dube ni da idanun basira ta ce,
"Ya ya hanya, ya kuma Hajiyar Justice da babyn ki?' Na ce, "Duk suna lafiya, kuma sun ce a gaida ku". Ta ce, "Ki yi haquri Kausar, tun bayan rasuwar Sagir ba ki kara gani na ba, aiyuka ne sun min yawa, duk da haka na san ban kyauta ba". Na ce,
"Babu komi Yaya, nima ina karatu ne shi ya sa bana samun lokacin zuwa".
Yaya Hajara ta kara gyara zama ta ce, "Kausar ki yafe ni, hakika a can baya ban kyauta miki ba. Nice wadda ya dace in dauki dawainiyar rayuwarki, amma shaidan ya sanya ni ban yi hakan ba, sai yau dana ganki kin zama mutum nadama mara amfani ta same ni. Babu abin da mahaifinki bai yi min ba a rayuwata, amma da rashin arziki na saka masa.
A yau na ji kunyar ki sosai Lanto, ina rokon ki ki yafe mini". Na share hawayen da suke yi min zarya, na ce, "Abin da ya wuce ya wuce Yaya, babu amfanin a dinga tayar da shi".
Ta umarce ni da in je in yi wanka in huta. Na sanar da ita ina tare da direban Hajiya a yau zai koma Kano, don haka ta umarci mai aikinta da ta kai mishi abinci.
Kwana biyu gidan Yaya Hajara ya haifar min da wani jin dadin cewa, nima fa mutum ce kamar kowa da ke da dangin uba, wadda kuma wannan shine pride na kowanne dan adam. Na saba da dukkan yaranta, musamman Hauwa'u da muke kwana mu tashi daki daya. Maigidan Yaya Hajara Alh. Aminu mutumin kirki ne, don yadda yake ja na a jiki kamar su Hauwa'u. Da na ce ina da bukatar zuwa Bujawa, Yaya Hajara ta ce sai dai mu tattara dukkan mu direba ya kaimu, saboda ita aikin ofis ba zai barta ba.
Sai ya kasance yau gani da kwana a dakin Inna Laminde ni da Hauwa'u da sauran yara. Washegari kuma gidan Baffa Lawal muka wuni, yana ta haba-haba damu, shima ya ce yana mai bani haquri, kuma har yanzu ba labarin Nasiru (mahaifina) suma turawan da suke nema na basu kara waiwayowa ba.
Bayan kwanaki uku muka sake komawa Jos. A kullum ita ma Yaya Hajara lallashi na take akan in yi haquri in yi aure, zaman haka bai kamace ni ba, tun da kuma ba rasa maneman na yi ba. Na kan kalle su ne kawai, amma can a karkashin zuciyata cewa nake ina zan kuma samun miji irin Sageer?
Sageer wani irin miji ne da samun kamar shi a wannan zamanin sai an tona. Mu yi wasa, mu yi dariya, mu yi girki, mu gyara gidanmu. Ya mai da kanshi bawa a gare ni, nima na sadaukar da kaina a gare shi. Yana tattalin farin cikina, yana bina da duk abin da nake so. Ya zamo wani bigire na zuciyata ta yadda faduwanshi ya kayar da zuciyata akan aure, na gwammace in yi ta yi mishi rainon diyarsa har illa masha-Allah.
Idan na yi wa Yaya Hajara wannan has ashen, sai ta ce, "Cikar imanin ki da mutuncin ki za ki duba Lanto, aure martaba ne, kina son mijin ko bakya son shi, ki yi haquri ki yi tawakkali, Lanto ki kasance cikin godiya ga Allah a bisa duk abin da ya zava miki".
Cike da kewar juna na baro Jos, saboda hutunmu ya kare. Yaya Hajara ta ce da zarar na kare karatuna wajen ta zan dawo, nima kuma na fi son hakan.
Na dawo ranar lahadi, washegari monday na koma makaranta. Mai sunan Mami na tare da Hajiya a kullum tana rainon ta, tana samun kyakkyawar kulawa, domin Hajiya ba daga nan ba, ta dauki son duniya ta dora akan Baby Fatima. Ta kan ce, "Ganin ta nake uwa Sageer".
Ranar wata lahadi ban iso makaranta da wuri ba, sakamakon tashi da Fatima ta yi da zazzafan zazzavin malaria, sai da na kai ta asibiti na mai da ta gida tukunna.
Don haka na iso a makare, already anyi submitting assignment wanda na kwashe kwana biyu ina hadawa cikin tsananin bincike a manyan littattafai. Don haka wata course-mate dina Blessing ta bani shawarar in je kawai in samu malamin a ofishinsa in ba da excusedina.
Sai dai kuma duk ajinmu ba mai iya tunkarar Dr. Habibu saboda thoughness dinsa, 'yan ajin da yawa sukan ce yana da jin kai, he is sticking on one word, (baya canja Magana), in ya karvi takardun 'yan aji ya karva ke nan, ba ya karvar excuse daga baya.
Na yi zurfi a cikin tunanin in je ne in ceci C.A dina ko ko in kyale? Daga baya na yanke shawarar in je din ko da kuwa zai kore ni ne.
Na yi addu'a kamin in yi sallama a kofar ofishinsa.
Na daga kai a jikin kofar shiga ofishin an rubuta Dr. Habibu Kofar-Sauri. Na yi qundunbala na shiga, bayan ya amsa sallama ta a ciki kamar baya so.
Ya yi min nuni da kujerar gefenshi na zauna, na fara gaishe shi, ya amsa. Kana na soma koro mai excuse dina cikin harshen turanci. Ga mamakina sai ya ce in ba shi takardun.
Na zage zip din jakata na dauko su, sai dai jikina ya bani ya qura min ido, ya sanya gilashi yana nazarin takardun, ya ce, "Kausar Nasir Bujawa?" Na ce, "Yes malam". Ya ce, "Shin ko zan iya sanin Kausar na da aure?'
Na rasa dalilin wannan tambayar, amma dai na nisa, "Maigidana ya rasu, shekaru biyu da suka gabata". Ya ci gaba da nazarin takardun kamin ya ajiye su gefe, ya ce, "Shi ke nan". Na taso na fito amma jikina ya bani kallona yake ba ya ko kiftawa.
Ina dakina da yammacin ranar ina harhada wani assignment din. Ayshe mai aikin Hajiya ta yi sallama a kofar dakina na amsa mata, ta ce, "Kina da bako a waje". Na yi tsaki cikin takaici na ce.
"Amma Ayshe sau nawa zan gaya miki idan an turo nemana a waje ku ce bana nan?" Hajiya ta jiyo mu daga falo, ban yi aune ba na ji ta yi kiran Ayshe ta ba ta makullin dakin baki, sannan ta ce, "Je ki bude mishi dakin baki ko wane ne ki ce gata nan zuwa"
Ta iske ni a daki ta ce, "Fita ki je, kina da bako ko nima za a aike ni a ce ba'a nan ne?" Haushi da takaici kamar in mutu, na zari zurmemen hijabin sallah ta na zurma na fita.
Sai me nake shirin gani ni Kausar? Dr. Habibu ne. Gwiwa a sage na yi sallama ya amsa. Ko da nake korar mutane na kasa korar Dr. Habibu saboda kwarjinin da ya yi min. Cikakken mutum ma'abocin wadatar ilimi da annuri, dan kimanin shekaru arba'in da haihuwa. Ta ko ina bai da makusa ko nakasu. A perfect gentle-man indeed!
Ya miqe tsaye cikin girmamawa, sai da na zauna sannan shima ya zauna. Ya yi murmushi ya ce, "Kina mamakin ganina ko Kausar? To kar ki yi mamaki, bincike mai zurfi na yi a kanki kafin in zo gare ki. Don haka daina mamaki, garin masoyi ba ya da nisa.
Na yi ajiyar zuciya ina kallonsa, ban ce kala ba. Ya ce, "Ina Baby Fatima?" Na ce, "Tana cikin gida". Ya ce, "To don Allah ko zan samu alfarmar ganin ta?' Ban yi magana ba na taho cikin gida na dauko masa ita.
Ya karve ta ya dora a cinyarsa ya ce, "Very beautiful baby, Allah ya ji kan babanta". Na ce, "Ameen". Idanuwana suka cicciko.
Ko mene ne Sagir duk kai ka jawo mini, da ka tafi ka barmu. Ba don haka ba wa ya isa kullum ya jawo jiki ya ce ya zo yana so na? Na yarfe wasu matsiyatan hawaye da suka tsatstsafo mini.
Ya yi murmushi ya ce,
"Ina da irin ciwon ki Kausar, don haka ba zan yi mamaki ba ganin kina kuka a gabana don na ambaci baban Fati. Matata Madina ta mutu a wurin haihuwa ta barni da jariri Saddik, yanzu haka yana hannun Hajiyata, zai yi sa'an Fatima".
"Allah sarki". Na furta a hankali. Haka kawai na ji jikina ya saki da shi, soul-mate' wato we have the same feelings. Fatima ta sauko daga cinyoyinsa