Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 10
ta ce, "Ba ku gayyace ta garin naku bane don haka ban ga laifinta ba, tun da dai ba fifffike za ta yi ta je mukun ba". Ya yi murmushi, "Kin yarda da batun Hajiya Kausar?" Ni dai murmushi na yi. Ya ce, "To yanzu muna gayyatarki, ki bani passport dinki da na Hauwa'u, sai mu koma tare". A wannan lokacin ne na yi magana, "Ka yi haquri Daddy, za ni amma ba yanzu ba, idan lokacin da na ga ya yi min ya yi zan sanar". Ya ce, "Ba wani nan, ke dai bakya son yin nisa da bazawarinki malamin jami'a, shine kawai dalili". Hauwa'u ta ce, "Wane malamin da tuni ya yi aurensa?" Bai ce uffan ba, sai dai an ce labarin zuciya a tambayi fuska. Hidima sosai Hajiya ta shirya ma M.K, don tun da muka zo ba ta barmu mun huta ba. Wani aiki ne ya kawo shi Nigeria na tsayin sati guda, don haka dawainiyar shi na wuyan Hajiya. Da daddare har dakina ya cimma ni, ina jera kaya cikin wardrove, Hauwa'u na daura ma Fatima pampers. Ya tsaya daga bakin kofa ta tokare hannunshi na dama jikin kofar. Ya ce, "Kausar". Na bar abin da nake na fuskance shi cikin rashin sukuni. Ya ce, 'Ko zan samu 'yan rakiya zuwa Abuja gobe da safe?" Cikin mamakin sa na ce, "Kaima ka san hakan bai kamata ba". Ya ce, "Ko da Hauwa da little Fatima ne?' Na yi shiru don ban san amsar da zan ba shi ba. Ya ce, "Already na sanar da Hajiya, kuma ta amince don haka ku shirya da wuri, by (6am) za mu dauki hanya". Babu yadda na iya, a washegari muka tashi tun asuba muka kintsa, na samu Baby bag na shirya kayan Fatima da duk abin da za ta bukata. Karfe shida da rabi muna kan hanyar Abuja. Hauwa'u da Fati da ke a kujerar baya ba'a jima da fara tafiya ba barci ya dauke su, sanyin A.C da ke cikin motar ya yi yawa. Ina so in ce da shi ya rage ko don Fati bana son yin magana. Ya yi min matukar kwarjini, don haka na samu kaina cikin rashin sukuni da rashin sakewa gaba daya. Ba a jima ba na soma rawar dari nima, ya lura da hakan, ya mika hannu ya rage A.C, ya kuma ciro coat din da ke jikinshi ya mika mani, na amsa da sauri na zira hannayena. Ba mamaki don shi mazaunin kasar sanyi ne shi ya sa sanyin bai dame shi ba. Mun yi nisa sosai har mun kusan shiga jihar Kaduna, ya dau C.D ya sanya na kira'ar Ahmad Suleyman, cikin suratul Taubah. Mun nitsa a sauraron karatun ya ce a hankali, "Kausar". Na cira kai na dube shi ba tare da na amsa ba. Ya ce, "Lokaci ya yi da za mu daina yaudarar kanmu, bayan rasuwar Sageer na yi kokari matuka wajen ganin na fidda ke a raina, amma na gaza. Duk wasu hanyoyi da ya kamata in bi wurin kauce ma hakan na bi duk a banza, jikina yana bani we are meant for each other, amma idan kina ganin wani abu akasi da yadda na fada, to ki bi. Wallahi ba za ki yi nasara ba kamar yadda kika fara rasa mai shirin auren ki, alkawarin Allah ba ya tashi, amma idan kina ganin ba haka bane, to ki ci gaba da gwadawa". Na yi shiru kamar ruwa ya cinye ni, alal hakika lokaci ya yi da ya kamata a ce ina gidan aure kamar kowa, sai dai ya ya za'ayi in auri mijin Mami? Wallahi ko zan rasa miji a duniya kamar yadda yake ikirari ba zan iya ba. Ya yi murmushi, "Kina da hujjar ki Kausar, wato (Binta) nima kuma ina da tawa. Aure na da ke ba haramun bane, sai dai kawai ki ce min al'adarki ce ta haramta shi. Kausar I love you and I connot afford losing you, ki yi tunani sosai, ki taimakemu mu baiwa zuciyoyin mu abin da suke so da kanmu ba tun yau ba. Ina bayanki daga kowanne kalubale za ki fuskanta, balle ma Fatima ta yarje min aurenki ba tun yau ba, hankalinta da tunaninta ba daya bane da na sauran mata. A da kam ta dau abin da zafi, amma yanzu ta fahimta. In gaya miki abin da ba ki sani ba, da yardarta da amincewar ta na taho nan neman auren ki a karo na biyu. Ta san cewa ko ba dade ko bajima idan na so zan iya kara auren ne, ta ce kuma da in kwaso mata wadda ba ta san halinta ba, sau dubu gara in aure ki. Tun da duk mun san halin juna, sai mu yi haqurin zama da junan mu. Don haka ni yanzu amincewar ki kawai nake nema, Kausar ki dubi Allah kada wannan karon ma ki ce min a'a......." Na ce, "M.K ‘give it a thought’, idan ita za ta iya ni ba zan iya ba" .......” "Saboda me?" "Saboda uwata ce, kuma idan ita ta yarda su Mukhlis fa? Don Allah M.K ka bar wannan zancen, ka bar ni in yi aure na a inda zan samu kwanciyar hankali, ka barni in zauna da iyayen goyo na lafiya ba su cancanci wannan sakayyar daga gare ni ba". Zancen ke nan har muka dawo gida, shi yana a bisa ra'ayinsa, nima ina a bisa nawa. Wanda daga baya abin ya zame mana rigima sosai. Ban san ya aka yi ba, da daddare lokacin Justice ya dawo, Hajiya ta shigo dakina fuskarta babu annuri, ta ce, "In same su a dakin Justice". Hankalina idan ya yi dubu ya tashi, ban san sanda na soma yarfe hawaye ba. Shi ke nan ya rabani da su kamar yadda nake gudu, ya rabani da martaba ta a idanun su. Na yi sallama a kofar falon Justice ya amsa mini, sanye nake da bakar abaya da mayafinta, idanuwana sunyi zuru-zuru na rasa inda zan sa kaina saboda kunya. M.K na fara yin tozali da shi, ga dukkan alamu shi kam ba abin da ya dame shi. Na koma gefen Hajiya na zauna ban san sanda hawaye suka keto mini ba, wane bayani zan yiwa su Hajiya da zai nuna babu hannuna a cikin wannan al'amari? Na kai gefen mayafina ina sharewa, Justice ya ce, "Kausar? Haba Kausar? Ashe ba ki dauke mu iyayen ba kamar yadda mu muke tsammani? Na dauka zuwa yanzu da Fatima diyar Sageer take raye a duniya still kina nan a 'yarmu, ko da a ce kuwa kin yi aure ne a waje ba a cikin gida ba? Mene ne banbancin ki da Mamar Mukhlis da za mu ki yi miki auren da Allah ya halatta? Sai dai kuma idan bakya son Mu'azzam ne, to nan bamu da ta cewa". Shiru na yi cikin rashin sanin abin cewa, ta wani bangaren kuma cike da mamakinsu kamar ba su san ya ya muke da Mami ba, ko ba su san wace ce Mami a gare ni ba. Su dinnan mutane ne extraordinary samun irinsu a wannan zamanin yana da wuya, mutane ne masu zuciya ta gari. To har kwanakin da M.K ya diba zai yi a gida Nigeria suka cika bai samu wata kwaqkwarar amsa daga gare ni ba, daga shi har su Justice. Sai dai ya ce ya bani daga nan har wata mai zuwa in yi tunani na karshe, shi kam yana nan akan bakansa, babu gudu babu ja da baya. [1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: Na zauna zugum ni kadai a falo ina tunane-tunane yadda za mu yi rayuwa daga ni sai M.K cikin gidan nan. Ina jiyo motsin Baba Larai a kicin tana ta kiciniyar gyare-gyare. Na dau waya na kira Hauwa'u muka shiga hira, da yake bikinta ya matso. Baba Larai ta leko daga kicin tana tambaya ta abin da zan ci. Na ce, "Ta bari kawai zan zo yanzu da kaina in yi girkin Daddy sai in ci, ta nemi wanda za ta ci kawai". Bayan na kare shirya tebur na fada toilet din dake makale da dakina, na shirya cikin riga da siket din versace, ina tazar gashin kaina da hand-dryer na ji shigowar motar M.K. Ko kamin in idasa in cimmasa ya bayyana cikin dakin, hannunshi na dama rike da brief case, ya yin da na hagun ke rike da falmaran din suit din shi, ya watsar da su ya iso gare ni ya miko hannu ya rungumo ni ta baya. Kafin ya juyo ni all overya hade da jikinshi yana sauke wani irin wahalallen numfashi. Atlast! Allah ya cika mana burinmu na shekara da shekaru, me za mu ce da shi ne, ban da mu gode masa. Mun dade cikin wani hali, cikin wata irin rayuwa da ban taba tsintar kaina a ciki ba. Cikin wata duniya da ban taba shiga ba ko da a mafarki ne. Har lokacin sallar magariba ta wuce bamu ankara ba, da kyar na kwaci kaina a hannun M.K muka fada toilet. Wanka na taimaka mishi ya yi kafin da mu hau tebur. Muna manne da juna kamar masu tsoron kada wani abu ya ratsa a tsakaninmu. *** Idan wannan ita ce soyayya, to ban taba jin ta a SAGEER ba, idan wannan shi ne AURE, to ban taba dandana shi a SAGEER ba, idan wannan ita ce KAUNA, to ban taba dandanata a rayuwata ba. At last! Allah subhana ya dube mu da kyakkyawar niyyar da ke zuciyoyin mu ya mallaka mana juna. Kanwa ta kar tsami kwannafi ya kwanta, sai fatan Allah ya ba da zuri'a masu albarka. Ya kwantar da kai a masangalin wuyana, ya ci gaba da fassara min wane ne MU'AZZAM? Kuma mce ce soyayyar?? ** ** Har muka share sati biyu muna varzar amarci ba mu sa Mami a ido ba, sai dai na san koma dai yaya ne cikin juriya da dauriya take, don cikar farin cikinmu. Alas! A yanzu kam ya samu nutsuwa ta har karshen rayuwar shi, wato mata biyun nan da yake matukar so a duniya da lahira (Mami da 'yarta). Don haka a dawowar Mami wani abu wai shi KISHI ba mu san shi ba, Allah subhana ya yaye mana tun da ya dubi zuciyoyinmu na ALHERI ne ga junan mu. A ranar da Mukhlis ya dawo da kwalinshi na Lauya, wato (LLB) a ranar ne na haifi Mukhtar (Justice) bayan shekara guda Mai sunan Hajiya ta biyo baya. Ko da Mukhlis ya tsinkayi aurena da mahaifinshi jinjina kai ya yi, wato abin nan da ake cewa fadan da ya fi karfinka…... Sai dai kuma shima ya so hakan, kamar yadda ya ce fiye da a ce a waje Daddy ya je ya dauko musu. Soyayyarshi da Fa'iza diyar Yaya Hajara kanwar Hauwa'u ta yi nisa, don haka shi din yanzu cikakken mutum ne mai hankali, ya daina duk abubuwan da yake yi na quruciya. Bikin Hauwa'u ya tashi, don haka dukkannin mu muka tattaro muka yo Kano, daga nan muka wuce Jos inda Daddy ya samu halartar daurin aure. Ba kuma tare da zaton kowa ba ya biya sadakin Mukhlis da Fa'iza, don haka muka kece da biki babu kama hannun yaro. Kowa yana sha'awar tsarin rayuwarmu ni da Mami da maigidanmu, sai fatan Allah ya ja da rai ya kuma raya mana zuri'a, ameen Rayuwa ta ci gaba da mika mana yadda ba mu zata ba. Da ci gaba da nasarori ta fannoni da dama. Mu'azzam Kanti Mu'azzam mutum ne da kafin a samu kamarshi cikin dubban maza sai an tona. Ga dai adalci, ga kuma soyayyar, kulawa da iya tafiyar da rayuwar iyalinshi ta yadda babu wadda ta isa ta yi complaning kan cewa ba a kyauta mata ba. Sai kuma ya yi katari da wata irin uwargida mai rahama a gare shi, har gobe ba zai daina alfahari da FATIMA-BINTA ba. Kamar yadda nima har jibi ba zan daina alfahari da ita a matsayi guda biyu da zuciyata ta bata ba, musamman da ta hada har da Fatima cikin iyalinta. Wato UWA kuma 'YAR UWA , sannan abokiyar shawara amma ba KISHIYA BA. Masha Allahu laquwwata illa billah. Takori [1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: Sati biyu da komawar shi sai ga Mami katsahan, babu zaton mu ba tsammani. Daga ni har Hajiya mun yi mamakin zuwan ta, kasancewar Daddy bai jima da komawa ba. Mami ta same ni a dakina da daddare fuska babu sukuni, ta ce, "Wurin ki na zo Kausar". Na ce, "Ai gani Mami". Ta ce, "Kina son ki kashe min miji ko? Daga ni har ke mu yi asara?" Na girgiza kai cikin tashin hankali. Ta ce, "In ba haka bane mene ne? Kin ce don ni kika ki auren M.K, to ni din gani na zo in shaida miki cewa, da amincewa ta da yarda ta....." Na cire kai a hankali ina kallon ta, magana take baka da zuci (heart and soul). Na bude baki in yi magana amma harshena ya yi min nauyi. Da kyar na samu furucin ya fito daga saman harshena, "Mami ke da bakin ki kike cewa kin amince in auri mijinki? Kina ganin hakan ya kamata?" Idanun ta suka ciko ita ma, ta ce, "Ni na yarda da kaddara Kausar, na yarda idan tun fil'azal Allah ya rubuta ku mamallaka juna ne ni ban isa in ce a'a ba, sai rabo da haqki ya kawar dani kamar yadda Allah ya kawar da Sageer don ya nuna ku din ALKAWARIN Allah ne. Kishi aikin banza ne Kausar, idan babu zuciyar mijin da kwanciyar hankalinsa me nake tutiya da shi? M.K ya rasa walwala, ya rasa sukuni, ya rasa kwanciyar hankalinsa duk a dalilin rashin amincewar ki. Da aje a kwaso min wata wadda ban sani ba ban san halinta ba gara mun zauna tare. Bana son cewa da kike yi din nan wai saboda ni ba za ki auri Mu'azzam ba, alhalin kina son sa yana son ki, ba za ki jawo min abin da haqki zai yi sanadina ba". Daga baya kuma ta koma lallashi, ni Mami har mamaki take bani, kamar ba mijinta ba. Irin wadannan matan ma'abota jin kan mazajen su da jiye musu feelings din su tsiraru ne a cikin al'umma. Lallashin duniya da ban baki Mami ta yi har ta koma bani tausayi, don haka na ce, "Kamar yadda su Justice suka bani lokaci in yi tunani mai zurfi, ita ma ta bani lokaci". Don haka har ta koma fushi take yi dani. Sai na gwammace ta yi ta fushin dani da dai in yi abin da daga baya zan zo ina nadama, wato auren M.K, duk kuwa da cewa shine kadai wanda zuciyata ke ciwo domin sa. Na yi lalube cikin duniyar baki dayanta, mai ya sa ba zan so wani a duniya irin yadda nake son M.K ba? A iyaka lalube na babu, na gwada ban samu ba, domin ba ko wadanne mutane ne masu nasibin M.K ba. Ya kama zuciyata ya dabaibaye da al'amarin da ba zan iya fassarawa ba, abin da zan iya cewa kawai shine, M.K nake so har kashi da vargo. A karshen satin muka tattara muka koma Jos, ba tare da su Justice sun samu wata sahihiyar magana daga gare ni ba. Justice da Hajiya sai suka koma bani mamaki kamar ba su suka tsugun suka haifi Fatima-Binta ba. Allah kareem! Mun je kasuwa ni da Hauwa'u mun yo ma Yaya Hajara cefanen sati, Hauwa'u ke jan motar, muna shigowa harabar gidan muka yi arba da wata galleliyar mota kirar ‘Giuleitta’ baka sidiq fake a rumfar adana motoci. Na dan tsaya ina kare ma motar kallo cikin nazari. Wane ne mamallakin wannan motar? Tun kamin in shiga babban falo na soma jiyo muryar Inna Laminde da Baffa Lawal, na yi sallama Hauwa'u na biye dani rike da sauran ledoji. Gaba daya mutanen falon suka amsa sallama ta, a ya yin da idanuwana suka gane min wani abin al'ajabi. Sanye take da bakar abaya da mayafinta kirar Omman, fara ce sol har ta soma jaja-jaja don fari, ba za ka ce ga hakikanin jinsin da ta fito ba tsakanin larabawa da turawa. Idan har ba idanuna ne suka yi min karya ba ita ce wacce ke jikin hotona da aka kira 'Grace' da nake kwana da wuni kallon hotonta. Mutumin da ke zaune a gefen ta kuma ba shi da maraba da Baffana da Baffa Lawal, sai gogewar jiki da ya fi su. Sai na tsaya kikam a bakin kofa, ni ban shigo ba kuma ban koma ba. Miqewa ta yi ta iso gare ni, ta rungume ni, kafin nan ni tuni na sulale a kasa sumammiya. Ko da na dawo hayyacina ban gasgata al'amarin ba, in rungume ta in rungume mahaifina na rasa inda zan sa kaina don farin ciki. A karshe kuka muka saka dukkanin mu mai gigitarwa. Ta yi min nuni da kanne na su biyar a zaune, daya bayan daya muka yi ta rungumar juna cikin matsananciyar kauna. Mus'ab, Khairat, Bilal, Nusaiba da Ikhlas. Shi ya sa Ubangiji (S.W.A) ya ce, "Kar ku fidda rai daga rahamata". Addu'ata ta shekara da shekaru yau Allah ya karva, ba da dabarata ba, ba daga sanina ba, ya kawo min su baki daya a lokacin da ban zata ba. Sai da komai ya lafa suka nemi mu tafi Kano wajen iyayen goyona. A can ne Hajiya ta yi wa su Mami waya, cikin kwanaki biyu rak sai ga su sun iso har da M.K. Na samu kaina a karo na farko da yi wa M.K waya ina gaya mishi abin alherin da ya same ni, ya taya ni murna kwarai tun kamin su iso. Don haka a tsakaninmu Mami ta shirya mana liyafar taya murna. Mun ci mun sha mun yi hani'an cikin godiyar Allah, Justice ya rufe taron da addu'a. Gaba dayan mu Justice ya shirya mana motoci muka rankaya Abuja don gano muhallin su, da kuma kara dankon zumunci a tsakanin su. ** ** Gida ne babba, dai-dai misali a unguwar Maitama. Motoci har guda uku a rumfar adana motoci 'yan uban-ubansu. Rayuwar su cikin tsari mai ban sha'awa da sanin ciwon kai, daga su har 'ya'yansu. Daga baya ne Abban yake gaya mana shi babban likita ne (Consultant) a babban asibitin Abuja bangaren zuciya. Tarba ta bajinta Grace (Maimunatu) ta shiryawa Mami. M.K da iyayen su. Sai da aka ci aka sha aka yi nat, sannan Mami ta fara koro musu labarin tun ranar da Yaya Hajara ta kawo mata ni, har kawo aurena da Sageer, da rasuwar shi. Kowanne ya jinjina, aka yi ma Sageer addu'a da fatan nima Allah ya kara min dangana. Mami ta ce, "Ita kam tana son ta ji ya ya a kai suka tafi suka barni hannun Inna Laminde?" Suka dubi juna ita da mahaifina suka yi murmushi, kafin ya soma Ni dai sunana Nasir, dan asalin garin Bujawa ne ta jihar Katsina, cikin maraici na uwa da uba muka taso ni da 'yan uwana, don haka ne muka taru muka dunqule cikin sanannan hadin kai da kaunar juna. Baffa mai rasuwa shi ne babba, sai ni, Hajara ta biyo baya, sannan Lawal. Amadu autan mu shima ya rasu tun da quruciyarsa. Tun ina karami Allah bai sa min son sana'ar mu ta gado ba, wato kiwo da noma, wadda muka taso muka taras mahaifinmu na yi. Na fi sha'awar in yi karatu, musamman da turawan wayar da kai suka iso Katsina, bayan kammala karatuna na sakandire na samu tallafin gwamnati zuwa kasar Bulgeria inda na fara karatun MBBS. Ita wannan Grace (course mate) dina ce, ajinmu daya. Da farko abota ce a tsakanin mu wadda daga baya ta rikide ta koma soyayya, soyayya ce irin ta zamanin da, wadda babu ha'inci ko yaudara ko son zuciya a cikinta. Sai dai na san ba yadda za'ayi dangina su mara min baya, saboda ba musulma ba ce kuma ba yarenmu ba, baturiya ce tsantsa. Yadda nake maraya haka take marainiya, ba uwa ba uba. Iyayenta sun rasu a wani Air-crash da ya rutsa da su a yankin kasar ‘Athens’ tun tana sakandire. Don haka muka nemi madaura aure suka daura mana, da yake Hausawa ne mazauna can. Shekarun mu biyu da aure muka haifi Kausar a kasar Bulgeria, ni na zava mata suna Kausar, amma mahaifiyarta na kiran ta Lilian. Ban takurawa Grace cewa lallai sai ta musulunta ba, don na lura ba ra'ayinta bane, ta fi sha'awar addininta na kirista. Da muka kare dukkan karatun mu, ya kama dole zan dawo gida. Na dauko Grace da Kausar muka taho, nan gidan Baffa mai rasuwa muka sauka. Suka yi ta ina aka saka ina aka aje da baturiya, sai dai bayani ya sauya daga lokacin da na sanar da su ita baturiyar matata ce, wannan 'yar kuma tawa ce, sannan Grace tana cikin addininta na kirista. A nan gidan marigayi Baffa aka ware mana bangare guda dabayan gida da madafi, daki ciki da falo kamin Allah ya sa in samu aiki. Yadda ta yarda ta baro danginta, kasarta da daular da take ciki saboda soyayyar da take yi min, haka ni kuma na dauki alwashin kyautata ma rayuwar Grace duk yadda za'ayi dani kuwa, don kiri-kiri suka nuna min basa son ta. Suka kira taron tattaunawa (meeting) a tsakanin su. Har da Hajara, akan auren da na jajibo musu. Ba yadda ba su yi dani ba kan in sake ta, ta koma kasarsu su sama min yarinya in aura na ki. A cewar su wai za su bani diyar abokin mijin Hajara in aura, wadda wai ita ma kamar baturiya take, idan farar fata nake so. Na kafe akan cewa idan ba za su karvi Grace a matsayin matata ba, to su kore mu tare mu koma inda muka fito. Don haka suka hade kai su da matansu suka fara yi ma Grace kisan mummuqe ida bana nan, su da 'ya'yansu da su Laminde suka hana ta zaman lafiya. Izayar yau daban ta gobe ta gobe daban. Da abin ya ishe ta ban sani ba tattara yanata-yanata ta yi tafiyar ta kasarsu ban sani ba, ba kuma tare da ta yi shawara dani ba. Nan ta ajiye Kausar wadda ke da shekaru biyu a lokacin. Da dai na gane Grace ta barni saboda 'yan'uwana na qudiri aniyar nima ba za su sake ganina ba. Na yi iya cuku-cukuna na bi bayan Grace. A gidan iyayenta na gado muka ci gaba da zama, muka koma karo karatu da hanyoyin kasuwanci kadan. Da na kare karatu na muka dawo gida Nigeria da yaranmu uku, da kwalayena na babban likitan zuciya, haka ita ma Grace. Muka sayi wannan gidan da muke ciki, muka kuma watsa takardun neman aiki. Na yi aiki da asibitoci da dama a nan Abuja, a karshe dai muka samu aiki da National Hospital wanda har yau muke a kai, to kun ji". Mun dade muna tunanin muje mu dauko Kausar muna daga lokacin, sai yanzu da abubuwa suka yi mana dai-dai. Don haka ina godiya gare ki Hajiya Binta da iyayenki, mun gode Allah ya ji kan Sageer. Kowa da ke falon ya ce, "Ameen". Kana ya zuki numfashi ya fesar. Mami da kanta ke sunkuye tana murzar 'yan yatsunta, ta dago a hankali ta dubi mahaifina, ta mai da kallon ta ga M.K suka qura ma juna ido tana nazarinsa, ganin yadda yake ta rama kullum a dalilin rashin kwanciyar hankalin soyayyar Kausar. Ta ce, "A matsayina na marikiyar Kausar, idan na nemi wata alfarma za ku yi min Daddy?" Kowa ya juyo ya dube ta, musamman M.K. Ya ce, "Wace alfarma ce Binta? Bana zaton akwai wani abu da na mallaka ko nake iko da shi da ba zan iya yi maku ba, haka nan bani da kalmar da zan yi muku godiya sai fatan Allah ya saka maku da mafificin alherinsa. Don haka ki fadi ko mene ne ina sauraron ki". Ta yi murmushi, sannan ba tare da wani haufi ba ta ce, "So nake a aura ma M.K Kausar". Gaba daya muka dago muka dube ta a tare, ji yake kamar ya miqe ya rungume matarsa. Doctor Naseer ya yi sakale yana kallon ta, ya ce, "Kan ki daya kuwa Binta?" "Kaina daya Daddy, alfarma ce nake nema". "Su suka ce miki suna son juna?" Ta miqe a ya yin da ta sakala jakarta ta sunkuya ta dau Fatima wadda ta yi barci a jikin Hajiya, ta yi saman bane save da ita a kafada. Ta ce, "Ga su nan ka tambaye su, suna son juna ko ba sa so suke neman halaka kansu? Ita kullum a zaizaye, shima kullum a zaizaye. Al'amarinsu ba

Chapter 9 of 10