(Pink Peacock Restaurant).
Ina zaune, haka kawai, na samu kaina da son yin wani abu na taya murna ga Mukhlis, a wannan rana mai muhimmanci a gare shi da duk masoyanshi suka hallara. Ko da kuwa a ce zai gwale ni ne ko ya dizgani a bainar jama'a.
Ni da Huda da Nur, Mami ankon wata dakakkiyar shadda ta yi mana babbar riga, Senegalese. Kowa ka kalla a wurin kyawu ne ke dukan kyawu, boko ne ke dukan boko.
Mukhlis ma'abocin abokai 'ya'yan manyan ‘yan boko irinsa, har da jajayen fata, hadi da malaman makarantar su baki daya Larabawan Turkiya.
Ko Mami ban gaya wa uzuri na ba, na bi tasi zuwa Country Mall, na sayo katuna masu matukar qayatarwa na fatan alheri, hadi da turaren da ya ke so, Hugo Boss na dawo.
Karfe takwas duk mun gama shiryawa. Takalmin kafata channel dogo ne sosai mai madauri siriri a idon sawu, wanda Daddy ya sayo min a matsayin tsaraba lokacin da ya je kwas California.
Allah bai yo ni ma'abociyar son kwalliya ba, don ni ko powder bana shafawa, iyakacina in yi wanka in yi brush. Tun Mami na mita har ta haqura ta qyale ni, in ka ganni ina shafa mai to ‘vaseline’ ne, shima sai a lokacin sanyi kadai.
Shi Mukhlis tuni ya bi tawagar abokansa sun tafi, don haka daga ni sai 'yan kannena a bayan mota. Mami da Daddy sunyi shiga ta alfarma, farin cotton lace ne a jikinsu iri daya sak, sai dinkin maza da na mata da ya bambanta, farin cikin da ke cikin zuciyoyin su a yau ba zai misaltu ba.
Ni na san Mami da Daddy duk sun fi son Mukhlis cikin 'ya'yan su, saboda hazaqarsa. Ko hakan ne dalilin da yasa ya zamo mai kaushin hali? Allah masani. Don haka idan har ni din wata 'yar halak ce, dole in taya su son abin da suke so, yana so ko baya so, ba don shi nake son shi ba, alfarmar iyayensa ne. Masu tarin alfarma a gareni.
Aka ci gaba da gudanar da walimar yadda suka tsara shi da abokan sa. Abokin shi Isma'il shi ne mai gabatarwa, shi ya karanto tarihin Mukhlis Mu'azzam Kanti, cikin tsaftataccen turanci, bayan shugaban makarantar su ta bude taro da addu'a.
In ban da faduwa ba abin da gabana ke yi, na ci gaba da kara makale jakata da na sako kunshin katunan cikin wrapping. Yanzu idan ya dizgani a wannan bainar jama'ar ya ya zan ji a raina? Kada kuma in bata musu farin ciki tun da ko gani na Mukhlis ba ya so ya yi, tsawon shekaru biyar da muka dauka tare.
Wata murya daga can cikin kaina na ji tana fadin
"Ki dubi niyyarki ta alheri, ki sadar da alherinki".
Don haka na mike cike da qwarin gwiwa, a ya yin da aka soma miqa mishi prizes, a matsayin shi na head boy wanda ya yi wa makarantar kyakkyawan jagoranci na shekara guda, ya fiddo da makin da ya fi na kowa, ya kuma fi kowa tsabta, qokari da iya turanci, makarantar ta ba shi prizes har babu iyaka. Ta kuma dauki nauyin karatunshi a wata jami'ar kasar Turkiya. Aka dauki tafi gabadaya.
Nima sai na ji ya burgeni, ya ya za ai Da irin wannan mai wanke zuciyar iyaye da farin ciki ba zai samo mafificiyar kaunar su ba?
Cike da sunan Allah a bakina na karasa, na qakalo wani tsorataccen murmushi na miqa mishi.
Jikinsa a sanyaye ya karba ya miqa ma wanda ke tarawa, kasa-kasa (to my surprise) kamar bai son kowa ya ji. Ya ce
"Na gode Kausar".
Farin cikin da ya ziyarci zuciyata a yau ba zai misaltu ba. Daga Daddy har Mami bude baki su kai cikin mamaki, Daddy ya samu kanshi yana yi mana tafi raf-raf-raf!.
Da aka zo daukar hotuna har kujerar da nake ya zo shi da mai daukar hoton, ya ce "A yi mana hoto". Sannan muka hadu dukkanmu family din gidan aka dauke mu tare har ba adadi.
Da haka walimar ta watse kowa cike da farin ciki.
Tun da yake dan qwalisar gidan ya gama nashi karatun, sai Mami ta sallami mai tasin da yake kaini muka ci gaba da tafiya a motar yara, kamar yadda suke kiran ta, alhalin ni ban ga dalilin da zai sa a kira 'spyker' motar yara ba.
Shekara kwana, muna cikin daliban da Ansar za ta yaye shekara mai zuwa, zuwa wannan lokacin duk wata boyayyar surata ta bayyana. Ni Kausar-Lanto, doguwa ce sambal, babu kiba, babu cikar jiki. Ni kaina na san muhimmin abin da yake kara mini kyau shi ne shatar bakina, wanda yake kamar yankar reza, idanuwana ba manya ba, ba kanana ba, hanci miqaqqe straight har baka, kai ka ce dosana mini a ka yi. Sannan gashin kaina baida yawa cancan, sai santsin tsiya, kuma ban taba sanya mishi relaxer ba.
A kullum na dauko hoton Mamana sai in ga ba maraba, kamar ta yi kaki ne ta tofar, ta fannin kirar jiki kam sai hamdala.
Mun zana WAEC cikin kwanciyar hankali, muna shirin tarbar NECO tafiya ta sake kama Mami Dubai again. Ta tafi litinin da niyyar zuwa friday ta dawo, to kuma sai ta yo min waya ta landline din gida, take ce dani in ci gaba da kula da yara wasu abubuwa sun rike ta sai wata juma'ar.
Na ce "Daddy fa? Ya iso tun karfe biyar na yamma". Ta ce "Babu damuwa, zan kira shi yanzun in mishi bayani".
Ban san mai yasa na fiya jin nauyin Daddy ba, ko don bai sakar min fuska ne, oho?Ban ji dadin yadda Mami za ta barni a gidan daga mu sai shi ba, don shi ko cokali da kofin shayi matarshi ke dauko mishi, ko hanyar kicin baya bi. Na ja numfashi cikin rashin sanin abin yi.
Bayan magariba suna zaune da yaranshi a falo, yana koyar da su home-work, na zo na wuce hannayena rike da kayan wankin yara da aka wanke aka goge, ban yi musu magana ba na wuce, ina ganin sanda Daddy ya dago ya kalleni na sami kaina da samun tangarda a yayin tafiya.
Na yi dakin su Nurr na adana kayan a muhallinsu, sai da na fito ne na russuna ina gaishe shi. Na rasa me ya sa bana son hada ido da Mu'azzam Kanti, kwarjinin shi har ya so ya yi yawa, ilhamar shi da cikar zati suna razana ni. Shi kadai duk ya bi ya cika falon.Duk da tsawo da sirantar da nake taqama M.K ya fi ni, ban taba ganin namijin da sirinta ta yi mai kyau irin M.K ba.
A hankali ya amsa gaisuwa ta, ya kuma kara da cewa
"Ko zan samu rowan zafi in sha coffee Kauthara?"
Na yi hanzarin dago idanuna na dube shi, ban taba jin wanda ya iya furta kalmar 'Kauthara' irin M.K ba. Ko da ya ke shi haka yake, komai na shi ya fi na kowa. Abin nufi,komi nashi extraordinary ne, wato,duk abin da zai yi, ya yi ko ya ke da shi, sai ka ga ya zarta na kowa da ka sani, musamman wadannan kyawawan 'ya'ya da Allah ya ba shi.
"Akwai rowan zafi, sai kuma me?"
Ya yi murmushi, ya ce "Sai a duba a cikin firji idan Mami ta rage gasashshen namanta a dumama mini".
"Mami ba ta rage ba, sai dai a gasa wani".
"Za ki iya?"
"Zan iya Daddy, kai din ne dai nake tunanin za ka iya cin jagwalgwalon nawa ko a'a?"
Ya yi murmushi sosai, ya ce
"A kawo min kowanne irin jagwalgwalo ne".
Kafin ka ce meye wanna na fiddo naman saniya a firinji, Allah ya so ni bai yi qankara ba, don yanzu direba ya kawo Baba Larai ta sanya a firjin, na wanke na gyare na ci gaba da yi kamar yadda na ga Mami na yi.
Duk irin hade-haden da take yi ban kara komai ba, ban kuma rage komi ba. Kafin in sa a ‘oven’ ruwan zafin da na jona har ya tafasa. Na sanya naman a ‘oven’ na wanke hannuwana da sabulun wanke hannu da ke makale a kichin din kusa da sink na tsane da duster.
Na juye ruwan a karamin flask, na aza kofi da cokali, suger da coffen nasa a karamin ‘tray’ na kai mishi.
"Naman da saura Daddy, amma ba zai wuce 20 minutes ba".
Ya dube ni sosai kamar mai nazarin wani abu a karshe yace "Cikin 20 minutes din Kauthar, ba za ki daure ki taya ni hira ba?"
Ya juya ga 'ya'yan shi,
"To Muslim, kalas, a tafi a yi game a daki karatun ya isa".
Nan suka tsallake littattafansu suka yi dakin wasan su, mai cike da duk wani nau'in kayan wasan yara masu sanya nishadi.
Gaba daya duk na bi na takura, na rasa inda zan sa kaina, ji nake kamar ya zauna a tsakiyar kaina saboda nauyin da jikina yai min.
Wani bangaren na zuciyata na gayamin hakan ba daidai bane, musamman da ya tashi su Muslim, ba kyautawa bane ga Mami.
Ya taso daga mazauninsa ya zauna gabana muka yi facing juna, wannan maganadisun da ya dade yana dawsiniya dani akan Muazzam Kanti ya soma yi min yawo a gangar jiki da ruhi. A take na ji duk jikina ya mace, bani da sauran kuzari sai yadda M.K ya juya ni.
"Zauna sosai".
Dabas, na bi kilishi na zauna, kamar wadda ta yiwa sarki karya!
A tun ranar da na fara ganin M.K nake jin wannan al'amarin na yawo cikin zuciyata da ban san ko mene ne ba. Ni dai na san ina jin nauyin shi, ina kuma matukar ganin girman shi. Amma al’amarin yafi karfin bayyanuwa da harshen dan adam.
Amma a yau al'amarin har ya zarce na baya, da zai min babban adalci shi ne kawai ya barni in tafi, amma na ga shi da gaske hirar yake so mu yi.
Dai-dai lokacin da Mami ta kira shi a waya, ban san me suke cewa ba. Ko da yake ita din ce ban san me take cewa ba. Ya dai yi murmushi nasu na ma'abota soyayya, ya ce
"No matsala take your time lady and let me have mine". Me ta ce, oho?
"Yau na samu kaina da son hira da 'yarki, I really want to help...".
Me ta sake cewa, oho? Ya ce "Farin cikinki shi ne nawa".
Zuwa wannan lokacin na samu na dai-daita nutsuwata, ya sakar min wani lallausar murmushi ya ce
"Kausar feel free with me? Am I not your Dad?
Na lura da ke kina cikin damuwa, ina so in san abin da ke damunki. In dai Mukhlis ne sati mai zuwa zai wuce Turkiya".
Da sauri na dago na dube shi. Ya daga min gira cikin ba da qwarin gwiwa. Da sauri na girgiza kai,
"Bani da matsala da Mukhlis yanzu, ya sauko muna gaisawa cikin dadin rai".
"Don ya ga zai tafi ya bar miki gidan ne shi ya sa ya sauko. Ina so in sani, mene ne sirrin?'
"Sirrin me?"
"Sirrin rashin jituwar taku, komi sai da dalili".
Nima na murmusa
"A nawa dan tunanin, kaunar da Mami ke nuna min ne yake ma kishi, kuma banga laifinsa ba. Abin da kake so shi kake ma kishi, yana son Mamarsa, ita kuma tana nuna ta fi so na.
Sai abu na biyu, nake jin kasancewar na fito daga kauye, shi kuma gaye ne, ko ba haka ba?"
Dariya na ba shi sosai, ya ce "To ina labarin iyayenki? Shekarun can baya Mami ke gaya min abubuwa haka-haka, to ban ba ta hankalina ba, don haka ban fahimci al'amarin ba".
Na kwashe duk yadda Baffa ya gaya min na gaya mishi, babu dadi babu ragi. Saurarona yake da dukkan zuciya da attention .
Ya ce
"Yanzu ina hotunan da wasiqar?"
"Suna nan a ajiye a cikin kayana. Abin da ke damuna ke nan, ina matukar son ganin su.
Ban tashi da soyayyar Uwa ba, a galabaice na tashi. Sai yanzu ne da na samu Mami nake jin na samu Uwa".
"Dauko min hotunan da wasiqar zan gani".
Na nufi daki na yi ta bincika kasan kayana, har Allah ya bani sa'ar gano su cikin baqar ledar da na sa na daure, na kawo mishi.
Kafin ya gama nazari na koma kichin na duba naman, na tabbatar ya gasu. Na kashe oven na juye a plate, na sa wuqa duk da zafinsa na yayyanka. Har na kawo gefen shi na ajiye bai gama nazarin wasiqar ba.
Na samu waje gefe guda na zauna, ya kare ya ajiye a gefe ya ce "Ta ce ne idan da rabo watarana za ku ga juna, dangin mahaifinki sun ki karbarta a matsayin mata, sun raba ta da Babanki karfi da yaji, bayan kuma kafin ta aure shi danginta sun sallamata.
Don haka yau da zaman ya zo karshe, ba ta da fuskar da za ta dubi ‘yan uwanta, don haka kar ki yi tsammanin ta koma Bulgaria kice zaki bita. A'a', ta tafi neman mijinta (Babanki) wanda shima ya ce duk ranar da ta bar kasar nan shima ranar zai bari, tana da yakinin cewa, 'yan'uwan Babanki asiri su kai suka raba su, suka kuma raba shi da kasar haihuwarshi bayan izayar da suke gana mata.
Don haka Kausar ki kwantar da hankalinki kin ji? Ko ba jima ko ba dade watarana iyayenki za su neme ki da kansu, tunda suna sane da ke. Duk da haka zanyi amfani da hoton ga gwamnatin Bulgaria, ko za a dace".
Cike da jin dadi na ce "Na gode Daddy, Allah ya saka da alkhairi".
Washegarin asabar na tashi da masassara da matsanancin zazzabi, don haka na kasa fitowa har misalin karfe sha daya. Inda Allah ya taimake ni yau ba makaranta ana hutun karshen mako.
Har suka yi kalacinsu suka gama Daddy bai ji motsina ba, ina jin shi yana tambayar Baba Larai da ke ta aiki ita kadai a kichin.
"Mutuniyar Mukhlis ina ta shiga ne?'
Ta ce "Nima kam, ban ji duriyarta ba, bari in duba dakin in gani".
Ta daga labule tana kallona ta ce "Lafiya ko? Wannan wane irin barci ne har sha dayan rana?"
Da kyar na amsa mata da cewa "Masassara da zazzabi ne ke damu na".
Ta karaso dakin sosai ta ce "Ayya! Sai ki qunshe a cikin bargo ki ki fada a kai ki asibiti?" Ta dafa kaina da wuyana, zafi rau, ta fita tana gayawa Daddy.
A tare suka shigo, ya tsugunna dai-dai kaina ya dora hannunshi a goshina, wani irin shock ya ratsa tun daga qwaqwalwata har yatsar kafata.Na rantse da Allah son M.K nake, duk da ban san mene ne son ba. Ji nake kamar in tashi in rungume shi ko na samu sa'ida.
Na runtse idona da karfi, hucin numfashina na fita da sauri da sauri.
Ya yi saurin janye hannunsa, ya ce
"Mike, kokarta, hospital za mu. Baba Larai!"
Ya qwala mata kira.
Ta iso da sauri ta tsuguna a gefe, ya ce "Kamata ki shigar da ita mota, ki kula da yara asibiti za mu". Ta ce "To". Shi kuma ya juya ya fita.
Baba Larai ta samo min mayafi na yafa, ta shige kafadata ta rungumo quguna, a haka muka fito harabar gidan. Tuni har ya yi ribas mu yake jira, ta bude min murfin kofar gaba na zauna, ga direba a zaune a bencin maigadi, amma bai ce direban ya kaini ba.
A gani na ban kai wannan matsayin ba. Haba? A kujerar Mami? Anya zaman nan da na yi a gaban motar nan na yiwa Mami amana? Sai dai zafin zazzabin da nake ciki ya hana ni yin tunanin na yi dai-dai, ko ban yi dai-dai ba.
[1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: Asibitin Premier da ke Gyadi-Gyadi muka dosa, bai fito daga motar ba ya fiddo wayarshi cikin aljihu ya kira. Wa ya kira oho? Na hango Nurses biyu na fitowa, suka zo suka kama ni zuwa ciki.
Mun yi sa'a babu layi, daga wanda yake ciki sai wata mace guda daya a kujerar jira. Nan na zauna a kan daya daga cikin kujerun, har layi ya zo kanmu. A lokacin shi Daddy ya fita harabar asibitin yana ta kiraye-kirayen wayarsa.
Sai da layi ya zo kanmu ne ya shigo, tare muka shiga ofishin likitan, suka cafke hannu cikin sanayya, suka yi 'yan hirarraki kafin Dr. ya maido hankalinshi gare ni, da tambayar abin da ke damuna.
Na ce "Masassara ce fal bakina, ba zan iya hadiyar komi ba".
"Sai kuma me?'
"Sai zazzabi mai zafi".
Ya taso daga tebir dinsa ya zo gabana, yana 'yan aune-aunen sa. Jikina ya bani M.K ya qura min ido, yana ci gaba da uzzirawa rayuwata da idanun nan nasa.
A duk sanda nake tare da shi, ko na gitta ta gabanshi, na ganshi, ina samun kaina cikin wani irin nishadi.
Na dago ido a hankali na dube shi, shima kallona yake ba sassautawa. Wani al’amari mai girma ya samu muhalli a zukatan mu.
Na yi hanzarin sunkuyar da kaina cikin dimaucewa da abin da na tabbatar yana shirin faruwa dani, koma in ce ya faru da ni, son mijin MAMI!
Ya ilahi, ya Ubangiji ina neman tsarinka da kariyar ka daga Shaitan mal'uni. Ya Ubangiji ina rokon kariya daga butulci da cin amana. Ya Ubangiji ka dau raina kafin abin da zuciyata, qwaqwalwata da gangar jikina ke son assasa min in yarda da shi a bisa tilas ya zan tabbatacce. Na tsani kaina a karo na farko, amma shi Mu'azzamun nayi-nayi in yakice shi na kasa.
Allurai ne da magunguna likitan wanda na fahimci abokin M.K ne ya rubuta mini. Haka kafin in bar asibitin sai da suka tsikara min allura kwaya daya, duk da tsoron allurata yau har aka yi, aka gama ban san an yi ba. Domin hankalina, ya tafi can ga so da kaunar angon Mami.
Doctor ya ce, za a ci gaba da kawo ni allura har zuwa rana i ta yau. Har muka hawo bisa kwalta, ba mu ce da juna uffan ba. Maimakon shirun, sai Daddy ya kunna sautin kira'ar Ahmad Sulayman cikin motar, (Suratul Rahman). Dadin kira'ar ya soma nutsar min da zuciya.
Kacokan ya dauki jinyar ya aza a kansa, shi ne ke zuwa bani magani akan kari, yana kara kusanta ta, yana kara dagargaza min zuciya. Na nemi da ya koma aikinsa,ya ce ba inda za shi sai na kare daukan allura da magunguna na, ya ba da 'excuse' a office. Dole haka na zubawa sarautar Allah ido.
Mami ta yo waya a washegari yake gaya mata jikin 'yar lelenta ya ki dadi. Mami dadi ya kashe ta, ta lura yanzu dai Daddy ya sauko, yana taya ta son abin da take so.
Ta ce "In sha Allah friday ina nan tafe, kayan da na auno ne nake jira a fara yo min gaba da su. Miss you too much……, a bani Lanto".
A handsfree ya sa wayar, bai damu da ina jin su ko bana jin su ba.
"Me kike so in sayo miki Lanto?'
Hawaye suka zubo min sharrr! Na yi hanzarin juyawa wai kada M.K ya gansu, idanunshi fes a kaina, kamar mai nazarin wani abu. Don haka na kasa baiwa Mami amsa. Kamar ya san halin da nake ciki.
Ya amshe wayar ya ce "Ke ma kin san me take so ai, Pakistani da Abayat, ko ba sune tsarabar da kullum take cewa a kawo mata tsarabar su ba?”
Ta ce "Ni dai a bani my daughter ina son jin muryarta, ko masassarar ta hana ta magana?'
Na amsa cikin dauriya da fin karfin zuciya, na ce "Mami yadda Daddy ya ce, haka ne".
"To shi ke nan, agaida Baba Larai, a shafa min kan autata (Nurr)".
***
Sai dakina ya zamto nan ne wajen hirar M.K ni da shi da Baba Larai, idan yara sun tafi makaranta. Mukhlis ya jima da fara karatun ‘Law’ a Turkiya, ko waya ma ba sosai yake yowa ba, duk kuma sanda ya yo, sai ya tambaye ni, na lura Mami na jin dadin hakan qwarai da gaske.
Hankalin Daddy bai kwanta ba sai da ya ga jikina ya soma murmurewa. Akwai wanda ya kai Daddy iya jinya? Ban taba gani ba. Na yi ma kaina fada da kakkausar murya akan in daina bari tunanin M.K na min tasiri. Shima kuma bai taba nuna min wasu alamu na wai shima yana cikin soyayyar ba, sai kulawa (care and concern) kadai.
Ranar juma'a tun safe muke shirin tarbar Mami, wadda za su sauka karfe hudu na yamma. Na gyara su Nurr sosai, kowa ya gansu sai ya yi sha'awa. Ba su da kiba sam haka suke siri-siri uwa Babansu, don kam Mami ba siririya ba ce, kuma ba mai kiba ba.
Karfe uku da rabi muka tafi Airpot din Malam Aminu Kano, ina sanye da atamfa super koriya mai ratsin baki da shudi. Na kawo after dress mara nauyi na dora a kai baqa. Takalmin kafata mai tsayi ne sosai, don ni bana sanya flat shoes sai a cikin gida, kuma haka Mami da ke sayo min su cokal-cokal, ita Mami flat take sanyawa.
A gaban kowa suka rungumi juna, wani maqoqo ya zo ya tokare ni a maqogwaro. Ni Kauthar na shiga uku, na yi asara, in rasa da wadda zan yi kishi a duniya sai da MAMI? Anya MAMINta cancanci hakan?
So nake in yi wa kaina dukan tsiya, ina ruwana don Mami ta rungumi mijin ta. Wata zuciyar ta kara kular dani da cewa"shima ya rungume matarsa, sai ki mutu. A'a, ba zan mutu ba, kwakwalwata ce ba dai-dai ba, ina bukatar ganin Psychiatric Doctor, watakila am in a Serious mental disorder!"
Mami ta iso kaina ta rungume ni, ta ce "Kin rame sosai my dear Kausar".
"Kewarki ce Mami".
Na samu kaina da kantara karya ga mami karo na farko a rayuwa ta. Tun da a zahiri kam zazzabin son mijinta ne ya kayar dani. Shin jama’a a nan duniya akwai butulu irina???
Muna dawowa kowa ya nufi dakinshi don gabatar da sallar la'asar. Da suka fito ne suka hau tebir, ni dama bana cin abincin tare da su.
Ina iya qokarina wajen kaskantar da kaina a gare su, wanda na lura su kuma basa son hakan. To amma yadda suke so in zaman wato, 'YA' da sauka haifa a cikinsu ba zai taba yiwuwa ba.
Ba wai ban yarda da matsayin da suka bani a zuciyoyinsu ba ne, a'a, yaro tsaya matsayinka, kada zancen 'yan duniya ya rude ka.
Na nufi kicin ke nan don in ci nawa abincin a dakin mu, Daddy Kanti ya sa murya ya ce,
"Kausar!"
Mummunar faduwa gabana ya yi, kafin na amsa. Na fito zuciyata cike da addu'ar Allah ya sa ba cewa zai yi in shiga cikinsu da 'ya'yansu in ci abinci ba. Addu'ata ba ta ci ba.
"Come and join us…, daga yau duk sanda nake gari ki tabbatar dake a kan tebir, in ba haka ba nima ba zan ci abincin ba.......".
Daga ni har Mami muka dago ido a sukwane muka dube shi, ko a jikinsa, ya mai da hankali ga cin itacen Apple ba tare da ya bude kowanne dish ba, kai sai ka rantse ba shi ne ya furta abin da ya furta din ba.
Ban karaso ba ban koma ba, haka Mami ba ta ce komi ba, sai ta share kawai ta ce,
"Kin tsaya sororo, ko ba ji abin da Daddy ya ce da ke bane?'
Na daga matacciyar kafata na isa gare su, na ja kujera kusa da Muslim na zauna. Mami ta mike tana serving kowa, babu komi a fuskarta na alamun rashin jin dadi.
Na nemi taimakon Allah na zauna na fara cin abincin duk da raina ba so ya ke ba, tusawa kawai nake yi.
Yadda kika san dusa haka nake hadidiyar abincin da nake cin, duk da irin haduwarsa da dadinsa kuwa, kai ba ka ce ni da Baba Larai muka girka ba. Don duk wasu nau'in girke-girke na zamani mun koya a wajen Mami idan tana yi wa Daddy. Ba ta kuma iyakance mana ga abin da za mu girka ba, tun da har ‘ya’yanta wani zubin a tukunyarmu suke ci.
Bamu kara jin duriyar Daddy ba yau tun da darling ta dawo, duk yadda na yi don in yi barci a wannan daren na kasa. Na kwana cikin rokon Allah ya rabani da wannan mummunan al'amari da yake faruwa da ni, kada Allah ya bawa Mami ikon gane na fada a matsiyaciyar soyayyar mijinta. Yaa Allah! Da wanne ido zan dube ta?
Sai ya zamanto na fara janye jikina daga yadda Daddy ke son ganina a gidan, musamman ta fuskar cin abinci tare