gaya miki su waye iyayen naki ba?"
"Bamu taba yin irin wannan hirar da shi ba, ya dai ce mini iyayena suna raye, sai dai shima bai san inda suke ba".
"’Yan wane gari ne?'
"Ya ce dani Mamana daga kasar Bulgaria aka auro ta, Baturiya ce. Kuma danginsu sun ki karbarta a matsayin matar dansu, su kai ta uzzura mata shi ne ta gudu ta barni ina da shekara biyu........" A yanzu kam muryata karkarwa take, cikin rishin kuka.
Mami ta zamo daga cikin kujera ta zauna dab da ni, kana ta janyo ni ta rungume a jikinta tana shafar bayana a hankali, cikin rarrashi ta ce "Shi kuma Baban fa?'
"Baffa ya ce da ni tun da aka raba shi da Mamana ya tafi, babu wanda ya kuma jin duriyar shi".
"Kin yarda shi Baffan naki jinin mahaifinki ne?"
"Eh, na yarda Baffa wan mahaifina ne, saboda kaunar da yake min da kuma tarbiyyar da yake bani baya yi wa 'ya'yansa. Kuma ya taba nuna min hoton Babana, ba su da maraba da shi".
Ta ce "Kyawun naki ne Lanto da yanayin fatar jikinki, ya sa nake tababa, amma yanzu na gane jikin Mamanki kika debo. Bayan Baffa da Hajara babu wanda kika sani cikin zuri'arku?"
Na ce "Sai Baffa Lawal kanin Baba, shi Yaya Hajara ke bi a haihuwa. Asalinmu garin Bujawa da ke cikin jihar Katsina, kuma duk dangin mahaifi na a can suke. Sai dai ba su da yawa, kuma ba masu karfi bane don haka kowa ta kansa yake.
Su suka korar min uwar kuma suka kasa rike ni sai Baffa kadai, shi kuma mata ta fi karfin shi".
Ta ce "Ki kwantar da hankalinki Lanto, Am by your side (ina tare da ke). Ki dauke ni Uwa-Mahaifiya, ni kuma na yi alkawarin rike ki har gidan aure.
Kuma da sannu za mu nemo iyayenki a hankali, saboda ina da contact da kasar Bulgaria, ina zuwa kan kasuwanci na.
Haka maigidana ma'aikacin sadarwa ne, ki kwantar da hankalinki. Yaushe ne kika ce min za ki je dubo Baffan, ko kin fasa?"
"A'a, ban fasa ba, bana son in yi missing lesson ne".
"Babu komi, goben ki je ki dawo jibi, karatun ba zai wuce ki da yawa ba".
Washegari Mami ta sa direban yara ya kai ni Bujawa, da tsaraba rankatakaf na kai wa Baffa da iyalin shi cike da boot din mota.
Ganin na zo da fagon kaya, yau Inna Laminde ta yi min kyakkyawar tarba, duk ta gigice, ni kaina na san yadda na canza ne ya gigita ta. Ta sunto kudi a habar zaninta ta sa murya tana kiran danta Salihu.
Ya shigo ya tsaya a jikin kofa hannuwanshi bisa kofar shigowa, duk tsamin da jikinsa yake yi ya cika dakin. Ya ce “Wace nan nake gani kamar Lanto?"
Na yi murmushi na ce "Ni ce Yaya Sale".
Ya ce "hala cikin inji aka sa ki a birnin aka wanke aka maido ki kamar Uwarki?" Ban amsa ba.
Ta gama kiciniyar kwanto kudi, ta ce "Kai, bana son sakarci". Ta qyafta mishi ido tana nuna mishi galleliyar akwatin da na zo da ita "Ungo maza, sayo mata ruwan leda da lemun kwalba".
Ya karba, shima rawar jiki yake. Zai fice na ce "Akwai direban Mami da muke tare yana waje, ka ba shi lemon ni a koshe nake".
Ya ce "Ai biyu zan sayo, wallahi yau sai kin sha lemon tunda kin zama Hajiya, har hakimcewa kike direba ya tuko ki a galleliyar mota".
[1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: Ya fita yana fatattakar yaran da suka yanyame mota mai sitiyari a hannun dama.
Kan ka ce meye wannan ya dawo da ruwan swan da lemon kwalba, ya ce "Na bawa direban ga naki, Allah ya sa a ci damu a Hajjin bana tun da kin zama Hajjaju".
Laminde ta ce "Kai kam! Allah ya sauwaqe maka da shegen kwadayi, tashi ka bamu wuri mutumin banza!"
Ya mike zai fice yana cewa "Ya sauwaqe mana tare da ke, Inna".
Baffa bai shigo ba sai bayan sallar isha, kafin nan na bude jaka na ware ma Laminde kasonta na turmin atamfa Ghana guda biyu, da kwalbar turare wadda ko yadda ake fesawa ba ta sani ba balle fa tsadar sa.
Bakinta ya ki rufo, ta ce "Tattara muje gun Malam ayi kasafin a can".
A kwance muka samu Baffa akan katifarsa kamar ba shi ba, idanuwanshi sunyi ja ainun masu nuna alamun ciwon kai mai tsanani. Jikina ya yi sanyi, duk farin cikin da nake ciki yau sai ya kau, hankalina ya tashi matuka. Da kyar ya kokarta ya tashi, ya ce "Lanto ce?'
Na ce "Eh Malam".
"Jikina ne yau bana jin dadin sa Lanto, lafiya lau na yi sallar magariba, amma zuwa isha'i ciwon kai mai tsanani ya cimmani".
"Allah zai yaye Baffa, zan je chemist yanzu na amso ma magani". Yace
"Ai na tura Sale tun dazun na san idan har ba ya tsaya shiriritarsa ba, zuwa yanzu yana hanyar dawowa".
"Mami na gaishe ku dukkanin ku".
"Allah sarki baiwar Allah, Allah dai ya saka mata da mafificin alkhairinsa, amin".
Na fidda mashi bandirin shadda guda biyu, da takalmi, ya yi ta godiya.
Sale ya yi sallama daga can bakin kofa ya cillo min maganin yai tafiyar sa yana kara jaddada min lallai in tabbatar Hajjin bana da shi za'ayi. Ko ina na ga kujerar Makkan oho. Yanzu na tabbatar da rade-radin da ake yi masa na cewa, yana shan kwaya.
Na janyo kwanon shan ruwan Baffa dake gefe, na balli maganin na matsa na ba shi ya haxe su duka ya kora da ruwa tare, na fiddo masu dogayen wanduna na jeans guda biyar, wato adadin 'ya'yan Baffa. Domin dai shi Allah bai nufe shi da haihuwar 'ya mace ba, watakila shi ya sa ya dauki son duniya ya dora a kaina, ko kuma saboda dan'uwanshi ne da baya da kamar sa? Allahu a'alam.
Laminde ta koma kicin don sako mana tuwon dare.
A nan ne muka samu damar kebancewa ni da Baffa, hirar da muka yi da Mami rannan ya sanya min kwadayin bin diddigi akan iyayena, wanda tun da na girma na taso ban taba yi ba.
Ya zauna sosai ya jingina da bango, na yi saurin cusa mishi filo a baya yadda zai ji dadin jingina sosai.
Ko da Laminde ta kawo kwanukan tuwon ta aje mana, daga ni har Baffa babu wanda ya kalla. Ga dukkan alamu shima Baffan cikin damuwa yake.
"Kin ji ni shiru kwana biyu ban zo na duba ki ba ko? Bana jin dadi a kwanakin nan shi ne dalili. Amma na ji dadi da kika yi hankalin zuwa, in ka ji wanda ya damu da kai kwana biyu shiru, sai ka neme shi ka ji ko lafiya?"
"Haka ne, Baffa".
"Tashi jawo min akwatin can ta karfe daga qarqashin gado".
Na yi yadda ya ce, amma jikina ya yi la'asar, sannan faduwar gaba ta same ni duk a lokaci guda.
Ya lalubo mukullaye a kasan katifarsa ya bude, ya soma bincike, har Allah ya taimake shi ya zakulo abubuwan da yake nema. Hotuna ne guda biyu na zamanin da, wato masu farin kala, ya miko min.
"Kin ce min kina daukar karatu a can gidan, ke nan za ki iya karanta wasiqa?"
"Idan da Hausa ne, zan iya".
"To duba ki gani".
Rubutu ne mai kyau da tsari, sai dai kash! Cikin harshen turanci ne.
Na ce "Turanci ne, amma zan bai wa Uncle Dini (Malamin lesson) ya karanta mani, ko shi ko Mami".
Ya ce "Da kyau, mahaifiyarki ce ta bar maki, ta bani amanar idan kin kai munzalin aure in ba ki. Ko me ya faru da ke mu muka jawo miki muka rabaki da iyayenki karfi da yaji. Ba kuma yadda ba ta yi damu ba ta tafi da ke amma mun ki, kuma ita ma ai da laifin ta, ta ki musulunta ya ya za'ayi mu karbe ta a matsayin matar auran dan mu?
Muna tsoron kada ta tafi da ke ta sanya ki a turbar kafirci.
Can ya gano ta a kasar da ya je karatu, ya jajibo, mu kuwa bamu ga me za mu ci da mushirika ba, har gobe har jibi. Ga ta nan ita ce mahaifiyarki, sunanta Grace, mutuniyar kasar Bulgaria ce".
Na samu kaina da rungume hoton wadda aka kira ‘Grace’ a kirjina, hawaye na malala.Baffa ya ce "Daina kuka KAUTHARA.......! Sunan da mahaifinki ya yanka rago ya sanya miki ke nan. Ban san inda yake ba, bamu da labari akan shi, ya tafi ya barmu da kewa.
Wasu kan ce kurciya aka yi mishi, mu kuwa mun san dalili, zuciya ya yi. Kalli mahaifinki sosai bamu da maraba, shi ya ke bina a haihuwa. Sai Lawal, shi kuma Hajara ke bin shi, mu biyar mahaifanmu suka haifa, shi ne da na biyu, Adamu shi ne auta, amma ya rasu tun da kuruciyar sa.
Na yi matukar mamakin rashin zuwan Hajara gare ki a tsayin shekarar nan da ta barki, amma ba komai, abin da ka yi wa dan wani tabbas shi za'ayi wa naka. Ni na ma fi gamsuwa da zaman kida wadannan mutanen masu alheri, fiye da ita.
Allah ne ya kawo mu wani zamani da naka zai ki ka, bare ya rungumeka. Don haka ta je, idan wani ya ki ka da wuni, wani da kwana zai so ka. Muma nan da ne ta kan zo din, yanzu kuma ta jima ba ta leqo ba.
Ko da wasa kar ki yi tunanin wata rana za ki koma gare ta ki zauna, sai ranar data furta miki da bakin ta tayi nadamar abinda tayi miki, domin kema ta shegantaki, ni kadai na karba. Gaba ce sosai tsakaninta da mahaifiyarki, ni kadai na karbe ki don ta ce ba ta ga dalilin da za ta karbi diyar mushirka ba.
Ki nemi ilimi, ki nemi miji ki yi aure ya fiye miki komi.
Ki tsaya da digadiganki Lanto, ki rabu da su wata rana su da kansu za su gane kuskurensu, ki kama kanki ko ba dade ko ba jima wata rana iyayenki za su neme ki".
Na yi ma Baffa godiya tare da neman alfarmar in tafi da hotunan in dinga gani, in nuna wa Mami, don ta ce ita ma da maigidanta idan ya dawo daga kwas din da ya tafi za su taimaka min wajen nemo min su".
Baffa ya ce "Allah yai miki albarka Kauthara".
"Ya yi mana tare da kai Baffa".
Ya murmusa ya ce "Ba ki tambaye ni sunan Baban ba?"
Na yi murmushi cikin jin kunya,
"Ina da wani Baba ne bayan kai, Baffa?"
Ya rausayar da kai, ya ce "Babu Kausara, sunan shi Nasir, likitan zuciya ne kwararre". Karshen tattaunawar da muka yi da Baffa ke nan.
Na koma Kano da sati daya aka aiko aka gaya min rasuwar Baffa, na dade bana cikin hayyacina, sai da Mami ta hada da sawa ake yi min rubutun dangana. Amma har gobe idan na tuno da Baffana sai na zub da wasu hawaye masu tsananin zafi.
***
Mami ke gaya min mijinta an tura shi kwas ne na tsawon shekara guda a Jami'ar California. Kuma a wannan watan ne ake sa ran dawowar shi.
Ba tare da shawara dani ba Mami ta shigar da ni makarantar su Mukhlis (Nigerian Turkish) da ke Tarauni. Wannan ya kara kular da Mukhlis, ya soma sanya min kahon zuka, komi na yi sai ya kushe ya gwale ko a gaban waye. Ya kuma dage lallai sai Mamin ta sauya mishi makaranta ba zai dinga shiga mota da ni ba.
Mami ta nemi dalili. Ya ce
"For now kam, she is not dirty......"
"………To why? Mukhlis din Mami?"
Ya ce, "I just hate her, and I donno why?"
"Komai yana da dalili……..".
"Kyawunta is too much, sai ka ce wata Devil? Ga ta dai daga kauye amma duk ta fi mu kyau, kina saya mata kaya irin na su Huda, 'yarki ce? Ai ga shi nan ta fi naki 'ya'yan kyau".
Ta yi murmushi "Na dai gane Mukhlis kishi kake da Kausar. Sai me dan ta fi su kyau, sai aka ce ba za su sami mijin aure ba? Ko kuwa duk kanninmu mu muka halicci kanmu?”
Ya kyabe baki, ya dage, ya maya ya rantse, ko a fidda ni daga Turkish ko shi ya fita, in ba za a kai shi wata makarantar ba to zai zauna a gida ya dinga daukar lesson. Amma ba zai yi makaranta daya dani ba.
Mami irin masu halin turawan nan ne masu masifar son 'ya'ya, dole ta mai dani ‘Ansar College’ don farin-cikin Mukhlis.
Dokokin Mukhlis ba su tsaya nan ba, sai da ya kara da lallai sai an raba mana motar zuwa makaranta, kuma direban gidan guda daya ne, sai ya zamanto kullum sai an fara sauke su sannan a dawo gida a dauke ni.
Wannan ne ya sa kullum nake zuwa makaranta a makare, har malamai suka gane. Suka tuntube ni kan dalilin da ya sa kullum sai na makara, na gaya musu cewa ina da matsala ne da dan uwargijiya ta. Don haka suka kawo shawarar the best solution Mami ta samu mai taxi su tsadance a wata kullum karfe bakwai da rabi ya zo ya dauke ni, in an tashi ya je ya dauko ni.
Mami ta amince, don ita ma fitinar Mukhlis ta ishe ta, ga shi ba ta son abin da zai bata ranshi ko miskala zarratin.
A wani week end muna hira da Mami, na ce "Kudin aiki da ta ce tana tara min za ta bai wa Yaya Hajara in sunyi yawa. Na ce ta yi wa Allah ta barshi, tun da ta tsaya min akan karatu ta gama yi min gata na duniya baki daya.
***
Kwanaki biyun nan na week end Mami is very busy cleaning, clearing and decorating gida lungu-lungu, saqo-saqo. Sannan ta ce in shirya da yamma zan raka ta saloon.
Duk sanda za muyi irin wannan fitar, kanti ne ko wani wuri, ni ke rike wa Mami jaka tare da kula da Muslim, Houda da Nourr don kar suyi wani wajen. Wankan su, shirin su da walwalarsu duk ya rataya a wuya na.
Mami na zuwa (Zaynab-Saloon) ne a Mukhtar Muhammed Link, ba ta canza wurin Saloon. Waje ne da larabawan Lebanon suka bude a cikin Kano. Su Mami har dasu pedicure & manicure ta fito kamar wata yarinya 'yar shekaru ashirin, sai ka rantse da Allah ba ita ta tsugunna ta haifi su Mukhlis ba.
A kan hanyar mu ta dawowa ne ta ke gaya min gobe Baban su Mukhlis zai dawo.
Don haka ko da muka dawo gidan bamu zauna ba, Mami da Larai suna ta tsarin girke-girken da za a tanadarwa Daddy kamin ya iso. Ni kuma sai nake ganin zuwan Daddyn zai takura ni (ki ji karfin hali), tun da ba zan dinga samun lokacin da nake samu da ita ba, dole hankalinta da lokutanta su koma kan mijinta. Na saba da Mami sosai, ina sonta kamar yadda nake son mahaifiyata, Grace, wadda ban sani ba, ban taba gani ba.
Ko da yake Baffa ya gaya min sai da ta dauke ni a bakin nono ta tafi, lokacin ina da shekaru biyu a duniya.
A washegari kuwa da asubahi Daddyn ya iso, duk muna barci. Haka har na shirya yara suka tafi nima mai taxi na ya zo muka tafi bamu sanya su a ido ba.
Sai yanzu ne na gano hikimar Mami na dauka na wannan hidimar, da abubuwan sai sun yi mata yawa. Ga ta kuma da son barcin safe don samun nutsuwa. Don ta gaya min ita kam in ta yi sallar asubahi komawa take, in ba haka ba sai kanta ya yi ta ciwo.
Ko da muka dawo, suna bangaren Daddyn, a matse nake da son ganin wane ne mijin da yai katarin sa'ar samun Mami as a house wife? I would like to see him!
Hakan ba ta samu ba, sai da daddare, inda ta aiko Huda in zo in gaida Babansu.
Na dora mayafi akan doguwar rigar da ke jikina na bi bayan Huda.
Zaune yake bisa dan qankanin carpet din da ke tsakiyar falon, ya mike kafafunsa sambal ya dora kafa daya a kan daya, da remote control a hannunshi yana canza channels. Yayin da Mami ke kishingide a kujerar da ya jingina, tana ta zuba mishi hira kamar ta lashe abinta don so. Kallo daya na yi mishi, ban iya na maimaita ba, saboda tsabar kwarjini da cikar zatin da Allah yai masa.
Da kam ina ganin Mami mai kyau, Mami mai tsabta, da babu na biyun ta a duniya. Ashe Mami mummuna ce, qazama ce ‘yar dukununu akan Baban Mukhlis.
Fuska a sake yake amsa gaisuwa ta, ya ce, "Ya ya karatu da 'ya'yan Mami?"
Na murmusa na ce "Alhamdulillah, bani da abin da zani ce muku, sai godiya".
Shima ya murmusa "Na kawo tsaraba har da ke, sabida labarin ki dana ke sha a bakin su Huda, da safe Mamin yara za ta ba ki". Kaina a sunkuye nace
"Na gode". Na mike na koma daki.
Tun dawowar Daddy sai ya zamanto Mami ba ta da lokacin kowa, har da kanta kuwa, sai nashi. Kacokam kula da su Nurr sai ya komo hannuna.
Wani zubin sai ta hada mu da direba a renakun da ba makaranta, ta ce in kai su Roxy ko Kano Zoo. Hakiqa rayuwarsu abin koyi ce wadda babu hatsaniya a cikinta.
Na koyi abubuwa da dama daga gare su, hatta maganganun da yaran ke yi ina koyon ilimi a ciki.
Satin shi daya ya wuce Abuja, inda ya ke aiki da NTA Abuja (Nigerian Television Authority).
Sai ya zamanto ba mu da abin yi da daddare sai sauraron Daddy, yana feso labarai da tsabtataccen turancin sa kamar Obama.
Daddy News-Caster ne cikakke, kuma fitacce.Duk wani da yake sauraron labarun kasa ya san MU’AZZAM KANTI MU’AZZAM. Duk da ba fahimtar abin da yake cewa nake yi sosai ba, na san MU’AZZAM KANTI yana BURGE NI. Da zarar an nuno shi kuwa 'ya'yanshi za su hau tsalle, har Ice-cream suke lasawa screen din dai-dai bakinsa, wai shima ya sha.
Haka da ya baro ofis waya suke yi ta awanni masu tsaho da iyalan sa, ya yi ta biye ma shirmen yaranshi. Ranar juma'a kuwa komin dare sai ya taho.
Duk inda ake neman mace ta gari, kuma managarciya to Hajiya Mami ta zarce, wajen nunawa miji kulawa, kauna da soyayya kam na jinjina mata.
A duk karshen mako throughout bama jin duriyar Mami, sai in ta fito girka mishi delicious dinta, tana can sassanshi sai Monday idan ya tafi kafin ta sami lokacin kowa da komai. Duk abin da za su bukata ni da Baba Larai ke tanadar musu, in ka ganta ta shiga kicin to girkin Daddy za ta yi, wanda bai taka kara ya karya ba. Bayan wannan komi na gidan mu muke tafiyar da shi.
A qokarin Mami na gyara mu'amala ta da danta Mukhlis, wanda yake kusan tsarana, ta ce in dinga gyara mishi daki kullum, in dinga fidda mishi kayan wanki, in daina damuwa da duk abin da yake yi min.
Ba Laptop dinshi ce baya so in taba ba? To in daina tabawa, ba kuma don kyara yake yi min hakan ba, don kada in bata mishi aiyyuka ne, tun da ba iyawa na yi sosai ba. In sha Allahu za ta tafi Dubai cikin satin nan za ta sayo min nawa.
Duk yadda ta ce haka na mai da hankalina wajen kwatantawa. Dama Uncle Dini ne ya ce mu dinga yin amfani da ita tare duk sanda yake yi mana lesson din Computer.
Gidan iyayen Mami yana nan a unguwar Sultan Road, kuma ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ta sha aike na kuma mukan je tare. Babu wanda bai sanni a dangin Mami ba da kuma matsayin da nake da shi a wurin ta. Hajiyar su Mami mutuniyar kirki, duk abin da ta san Mami na so ita ma tana so.
A karshen satin Mami ta tafi Dubai ta barmu a gidan kan harkokin business din ta. Shahararren Boutique ne da Mami a Beirut Road, wanda ya qunshi duk wani nau'in sittiru 'yan waje (designers) na maza da mata. Daga jakunkuna, takalma, trollies, agoguna, kayan yara da kayan wasansu, fashion jewalleries da sauransu duk babu nau'in da babu a ciki.
Wani zubin Mami har a cikin kantin zama take cikin ofis dinta, idan kuma ba ta nan akwai mataimakiyarta Mrs. Ngozi. Gaba daya karatun Mami ta yi shi ne akan harkar kasuwanci (Business Administration) har zuwa (master) daga jami'ar Bayero.
A wani week end Daddy ya zo, ina dakin su Nour ina shirya ta don za muje tarbar Mami Airport, yau ne take dawowa.
Na jiyo Mukhlis ya fito yana ta fada, shi kam wannan Lanton, must go back to her village, in ba haka ba shi zai fice ya bar musu gidan, har da kukan sa.
Baban shi da ke falo cikin tulin ayyukan takardu ya dago kai a hankali ya dube shi, ya yi mintuna uku yana nazarin sa kafin ya tausa murya ya ce "Zo Mukhlis".
A fusace yake sosai, ya matsa gaban Uban,shikuma ya rungumo shi gefen damar sa, ya ce "Ya ya haka? Ina laifin mai taimaka maka?"
Ya ce a fusace "Ni dai a ba ta komai take so ta fita ta bar mana gidanmu, I just hate the girl………...!"
Ya yi murmushi cikin rashin jin dadin kalaman shi ya ce
"To meye laifinta na yau kuma?"
A gadarance ya ce "Tana min misplacing things, in aje abu a wuri kaza ta dauka ta canza mishi matsugunni in yi ta shan wahalar nema".
"To ko ta daina yi ma gyaran dakin?"
"A'a, ina so a gyara min, amma a nemo wata ba wannan ba, wannan kyanta ya yi yawa, har yana tsorata ni".
Ya tintsire da dariya, ya ce "Ke nan ka fi son a nemo ma mummuna?"
Ya ce "ta wani bangaren na fi son hakan".
"To bari aje a dauko Mamin sai a san abin yi, ta zo ta raba wannan rigima tunda ita ta qulla ba ni ba!".
***
[1/1, 14:07] Nrs Zainab A S: Ban taba hawa motar Daddy ba sai yau, sai dai in ganta kawai a harabar adana motoci, in karanta sunanta in sake karantawa. Wani zubin har in kai hannu in dan shafe ta cikin sha'awa, 'Volvo'. To a yau dai gani a cikin ‘Volvo’ din Kanti Muazzzam, sanyin A.C, qamshin car-fresh hade da sassanyan turaren Daddy ‘Gio-Gio Armani’ (Armani-Code)sun hade sun cakude a cikin motar.
Na samu kaina da satar kallon Daddy babu dalili. Hakan nan dai idanuwana ba sa gajiyawa da kallon sa. Sai da na yi tsam da raina na gane shigar da ya yi ce cikin ‘suit’ ke burge ni, take kuma matukar bani sha'awa.
Na rasa shigar da tafi amsar M.K (yadda Mami ke kiransa ke nan watau Mu'azzam Kanti). Ban san mai ya sa nake yawan tunanin al'amarin M.K ba. “He is classique!" Ina yawan fadar hakan a cikin raina.
Tuni jirgin su Mami ya sauka, muna baya ni da yara ina ta ci gaba da satar kallon sa. Mami tana gaba, don Mukhlis bai biyo mu ba, ya ce da ya shiga mota da ni, gara ya zauna a gida.
Har muka fito Airport din Malam Aminu Kano, ban daina kissime-kissimen banza akan mijin Mami ba.
Muna isa gida Mukhlis ya tada bala'i, shi lallai a yau din nan sai Mami ta mai dani inda ta dauko ni.
Mami ta fidda hannu ta zabga mishi wani irin wawan mari da bai taba ji ba, ta ci gaba da kai masa duka ta ko'ina.
"……..Sai ka gaya min abin da yarinyar nan ta tsare ma a gidan nan.........."
"Ba ta tsare min komi ba, I just hate her...na fada na kara! Ki ci gaba da duka na, ba zan taba son ta ba!!"
Daddy ya janye danshi da karfi, ya ce "Ba zai yiwu ba, ba za ki nakasta min yaro a kan 'yar da ko asalinta ba ki sani ba.
Ni duk wannan kame-kamen da kika gaya min akan iyayenta ban yarda da shi ba, balle in yi wani taimako wurin nemo su. Wot's your own business?"
Ta ce "Na ji, ba za ka taimaka min wurin nemo iyayenta ba, amma ya bar min 'yata ta zauna lafiya".
Ya kyabe baki ya ce "An barki, amma ba zan dauki duka ba, babu gaira babu dalili".
A hakan dai da dadi ba dadi muka ci gaba da rayuwa cikin gidan nan, ni da Mukhlis. Yana gaba dani da aji daya, don haka ya rigani kammala karatun sakandire.
Daddy ya shirya mishi liyafar taya murna (dinner) shi da abokanshi a gidan cin abinci na