“nagode Salim muje” he felt really bad ta wuce yana biye da ita har zuwa wajen dakin da Baba yake ta zauna a kujeran wajen tabuga tagumi tana kallon dakin gabanta faduwa kawai yake jijiyoyi na bayyana na fuskanta, hawaye suka sauko takara gogewa dasauri ita kadai tace “Safeerah bataji, bataji, bataji, yanzu abinda ta aikata wani fa’ida ke tattare dashi? Saidai tashin hankali look at where Baban ta yake yanzu” Mama tai shiru saikuma tajuyo takalli Salim da kyau ranta abace tace “tasan mahaifinta baida lafiya Salim mesa kome aka mata bazatai hakuri ba, eh?” Kallon Mama yayi asanyaye she is really angry kana ganinta kasan she’s feed up tace “Babanta baida kudi but muna rayuwan farin ciki da muna Kano, abu yafaru dayasa aka kona gidanmu bayan sunma Malam duka shine har yau baida lafiya, ga baya gani da kyau, nine nakira yayarsa Kubra wannan damuke gidanta na sanar da ita ga abinda ke faruwa haka ta aiko da kudi dubu dari da bamu dashi muka biya a asibiti aka dan bawa Baba taimako na gaggawa kafin drebanta ya iso yadaukemu muka dawo Abuja wajenta” Mama tai shiru saikuma tafashe da kuka sosai Salim ya sauke kansa kasa, Mama tace “nasan the reason Safeerah ke all abubuwan datakeyi sabida she had enough, kullum tana ganin ana zagin iyayenta ana cimana mutunci between Kubra da yaranta but nasha gayamata ke haka masu kudi suke barinma yan Abuja, society yakoma wani iri da me kudi ake respecting banda talaka, yau da ace Malam na da idanu yana aiki nasan rashin mutuncin bazai taba kaiwa haka ba sabida yanada nasa yanada na rike iyalansa no ita takiji takasa ganewa shashashan kanason kaga fadan Safeerah azageni ko mahaifinta agabanta bata iya hadiyewa, kasan mi Safeerah tayi rannan kuwa”? Mama ta share fuska da hawaye ke kwance tace “rashin kunya da rashin da’a ta sufafawa Yayar Babanta, wacce ta girmi mahaifinta fa sannan ta kama Salma da dambe, aiko Kubra tasa hannu da Salma suka bata kashi ban hanaba maganin mara kunya ai kenan fitsararriya” har lokacin bai dago kai ya kalli Mama ba, Mama ta fuzar da iska tace “Salim kaga nasan waye Mama Kubra nasan metakeyi amman no matter what ba abune mai kyau karamin yaro ya kalli tsabaragen idanun babba yayi rashin kunya ba bahaka iyayenmu suka taso damu ba, Mama Kubra tamana abubuwa da dama ciki harda lalata rayuwan Safeerah kaga bayan dawowan mu Abuja dayake anata fama da kai Malam asibiti tace tagaji zata aurar da Safeerah ga mai kudi ayi amfani da kudin a kai Baba asibiti tagaji da kashe kudinta wai kudinta gadon yaranta kasan marigayi tsohon gwamnan jigawa take aure” Mama ta hadiye wani abu awuya tace “ninasan harda jin haushi da tsanan Safeerah cewa sukayi wai abinda yafaru ita tajawo mana fitinan so she just wanted to teach the girl a lesson shine tasamo wani yaro mara tarbiya wai Abbati dan kawarta Malam na tsaka da ciwo tace aurar da Safeerah zatayi da ni da Malam babu wanda ya isa yace wani abu, haka ta aurar da yarmu agaban mu yabiya sadaki miliyan biyar” Mama tafashe da kuka sosai kaman maganan was very personal for her kana goge fuskanta da bakin hijabi kana ganinta kasan she has been swallowing this pain aranta, Mama tace “yarinya ta was just a little girl ko zance basu tabayi da yaron ba banda so daya da aka nuna mana yaron atare da mu da ita muka gansa yazo wajen Mama Kubra bata taba kebewa da yaron sunyi wani magana ba, rannan da akakai Safeerah rannan takirani tana kuka yamata duka sosai tana nishi kaman zata rasu!” Dunkule hannu Salim yayi ahankali kansa akasa har lokacin, Mama tace “haka na mike zumbur cikin daren nan hankalina tashe naje flat dinsu natadasu ina kuka wiwi na gayama Mama Kubra ga abinda Safeerah amman kiri kiri tamaidani shashaha tace idan banyi shiru nakoma na kwanta ba sai raina yabaci taso Safeerah nake kota lafiyan kaninta” Mama tai shiru tana kallon tiles na floor na wajen looking lost a tunani tace “kullum rannan duniya for good 6months sai yaron nan yama y’ata duka ba dare ba rana amman dukan yafi faruwa da daddare idan yayi shaye shaye yadawo haka watarana asibiti suka kiramu ita Mama Kubra wai Safeerah na asibiti batasan inda kanta yake ba mukaje muka tarar ya mata shegen duka yasaketa saki uku wai shi bayason haihuwa kuma tayi ciki, watanta daya a asibiti tana jinya babu ko sisinshi Mama Kubra tabiya komi Baba yaso yaje police station tahanasa wai haka yaran masu kudi suke, karmu damu tunda tanada ciki zai dawo menene menene ahaka yarinyar ta haihu Mama Kubra takirasa yace kar akara kiransa ba dansa bane, he is not ready for kids, mu mukai komi, ganin anata surutu shine last 2yrs tasaka yarinyar a school, shima Safeerah tayi kuka dan nursing takeso da kyar na lallabata ta tafi architecture din Safeerah nada taurin kai wani abun sabida mu take shiru ga fada, nadade banyi fushi da itaba amman abinda tayi jiyan nan bazan hakura dawuri ba saitaga fushina this time around…” Mama ta fuzar da iska. Dr neyafito yataho wajen Salim hakan yasa yamike tsaye yace “Dr Isa”? Anatse Dr yace “Alhamdulillah he’s stable for now, BP sa yayi sama sosai any further damuwa can push him to having stroke, Madam ya akayi BP sa yayi raising haka yanada damuwa ne?” Fuska Mama ta goge zatai magana Salim yace “zata iya shiga ta gansa?gyadamai kai Dr yayi yace “of course” Mama Salim ya kalla yace “Mama je wajen Baba bayan nagama magana da Dr zanje nakawo Safeerah” gyadamai kai tayi tace “toh nagode Salim, Allah ya sakamaka da mafificin alkhairi” gyadama Mama kai kawai yayi tawuce ya shiga dakin shikuma yajera da Dr Isa dayace “who are this people Major? Why are you so ordinary dasu? Ina escort naka”? Wani kallo dayama Dr yasa Dr Isa ya kame tareda saramai yace “Sir!” Wani banzan kallo yamai yace “give my patient your best I will be back” yajuya yabar wajen yafita daga hospital din yashiga mota yaja.
EPISODE 2️⃣2️⃣
Bayan fitanshi tadade tsaye anan wajen dinning din kafin daga bisani ta wuce wajen ledan tabude kaman mai tsoro taga kayan yara sabbabbi riga da short masu bala’in kyau da takalmi da pampers sai Chicco cream na yara da powder da soap, saikuma ledan maganin H-medix drugs ne aciki, tsayawa tayi tana kallon komi tana tunanin why is he so thoughtful? Yasan kome suke bukata kaman tabude baki ta rokeshi, wani bakin sealed leda dabata budeba tasa hannu ta dauka tabude ahankali ta ciro abinda ke ciki Saudi abayane mai kyau black ta warware dasauri size nata ne kuma 58, abayan smells kaman turaren sa it doesn’t look like shi wannan yasayo a shago ne kaman daga gidansu ya dauko, maidawa da sauri tayi ta ijiye komi kawai saita wuce kitchen abincin daya zubar shida Waleed tasa broom ta share ta wanke bowl and spoon dayayi amfani dashi and keep everything a waje daya saita dawo falon tabude ledan, kayan Waleed kawai ta dauka da man shafan da sabulun tahada sauran abubuwan tamayar ledan chap itane zatasha magani, she hates magani ita chan magani shine ma abinda ke sata zazzabi, tawuce sama kawai daidai Waleed natashi daukansa tayi tawuce bayi ta tara ruwan zafi tamai wanka tafito ta shiryasa cikin kayan kuma daidai jikinshi yayi kyau tasamai takalmi sai kallonsa take he looks damn expensive a kayan kaman yaron yan gayun nan, kitchen tawuce tamai abinci tabasa yaci sosai itama tazo kaman karta ci abincin but yunwa na neman halakata saita bude taga waina da pepper soup sai rice da stew yaji kaji manya manyan, deban waina tayi taci sosai tanaba Waleed dayaki amsa, ci tayi tai kat sannan tajita tadawo daidai takai komi kitchen tadauki Waleed sukaje daki ta ijiyesa tawuce bayi wanka tayi tafito kayanta takara maidawa tasaka kayan da Waleed ya cire a ledan sannan tadaukesa suka sauko kasa ta zauna falo zuciyanta sai bugawa yake tanaso takirasa ita tanaso ta tafi tun wuri dan tasan ya ake ciki, ball daya sayoma Waleed da kansa yaron yajawo daga leda yahau wasa da ball din ta tsare yaron da ido he’s so happy baisan trouble da Mamansa ke ciki ba.
Sunkai kusan 2hrs zaune nan falo sai taji alamun mota dasauri tamike tace “Waleed zo” tadaukesa tana karban kwallon ta ijiye akasa cike da rigima yace “Ummy Balllll” hade fuska tayi tace “idan baka natsuba zan makeka I’m not playing with you today” kwabe fuska Waleed yayi yana kallonta tasa hannu tadauki zanin goyonsa tarike tana kallon kofa jira kawai take ya shigo ta tafi.
Yana fitowa daga motan yazo wajen kofan saida yafara danna door bell sannan yasa key yabude kofan ganinsu yayi a tsaye, Waleed na ganinsa yashiga kokarin sauka daga jikin Maman aiko Safeerah takallesa da sauri tana hararanshi ko ajikinsa kiciniyar sauka Waleed keyi da karfinsa da yaji. “come” taji maganan sa agabanta dayake tana fama da Waleed kwata kwata batasan sanda yama karaso gabanta ba dasauri tadan koma baya tasakanmai Waleed yadaukesa Waleed na washemai baki yana kallonsa, calm murmushi Salim yayi kadan yana kallon Waleed din yace “kayi kyau Fine Boy?” Kofa Safeerah ta kalla ganin ya kulle kofan yasa tai wajen dinning da sauri gabanta na faduwa ta tsaya daga wajen, ahankali Waleed yanunamai ledan dake center table yace “juice” dan tuntuni yakeso yasha Safeerah tahana, yana dauke dashi yabude ledan idanunsa na dauka kan rigan dayaga ta bude ta maida ledan ta ijiye, ledan maganin da bai kama da an bude ba hannu yasa yaciromai caprisone yabude ya basa yadauko cheese balls ma yabude saiya saukesa akan kujera yace “zaka kalli cartoon” gyadamai kai Waleed yayi da gudu yana kai juice din baki, TV parlor ya kunna yasamai a Disney Junior volume bai wani yawa ba Waleed yawani natsu yanaci Cheese balls yanashan caprisone gabaki daya attention nasa na TV. “Zamu tafi!” Yaji maganan Safeerah hakan yasa yajuyo da kansa ya kalleta dasauri ta sauke kanta kasa, dan takowa yayi one two three step dawani irin sauri tai baya itama ta tsaya daidai kofan kitchen gabanta na faduwa sosai, hakan yasa ya tsaya anan falon gefen kujeran da Waleed ke kai yakai hannayensa tabaya ya harde, calmly yace “ina zaki yanzu?” Dan dago kanta tayi ta kallesa dasauri ta maida kasa, ahankali tace “nima bansani ba!” Waleed yajuya yakalla saiya juyo da kansa yakalleta yace “kina tunanin Waleed?” Dasauri tadago kanta dudda bata kallesa ba Waleed ta kalla he’s so happy yanacin cheese yana kallon cartoon a tv spidey akeyi abunda yadade bai kalla ba cus ba’a musu sub ba, a falon Mama Kubra kuma bai İsa yayi kallo ba saidai in basanan, abu taji ya tsaya mata a wuya ahankali tace “I will protect Waleed da duka rayuwana”? “How? Yawo a street kina begging da shi under the hot sun, ko kasan bridge dakika ce zaku koma or Kano da people are there ready to kill you!” The way kalamansa ke dukan kirjinta ko batasan sanda hawaye yazubo mata wani tsoro na shiga ranta ba, kalamansa just made her thing for the first time kaman abunda tayi was wrong, bayan hannu takai ta share fuskanta da sauri, anatse Salim yace “the moment a girl becomes a mother you can’t be considering kanka first always you neeed to think of yaranka, danka abinda ka haifa, because of yara koda ana zaginka saikai hakuri iyayenki sunyi hakuri sun jure komi not because they’re weak but because of you! Why can’t you do that for Waleed”? Wani huci tayi kukan bakinciki da kunci na fitowa daga idanunta tana sharewa da bayan hannu, sauke kanta kasa tayi zuciyanta na yin baki kirin tana wani irin shakkan sa hakan yasa takasa maganan da kyau hannayenta ta harde da karfi gabanta ma mahaukacin faduwa cikin murya yar kankanuwa tace “ni…..ni…..dai ka banni natafi nariga na rantse baram koma gidan ba!” Tsareta yayi da idanu yayi shiru hakan yasa tadago kanta jin shiru wlh ayanda taga idanunsa batasan sanda tajuya zata bude kofan kitchen dasauri tafada ba strictly yace “don’t try that!”
Kasawa tayi ta tsaya jikinta na rawa, lumshe idanu yayi yadan sassauta muryansa yace “bazanso this poor innocent boy suffer sabida foolish and childish decision naki ba, you can stay here as long as you want, bring parents naki su zauna tareda ku nabar miki this house! I will give you the papers anjima! The house is yours!” Dawani irin sauri Safeerah tajuyo gabanta na faduwa so take ta kalleshi but takasa dan lankwasa kanta tayi ahankali tace “thank you amman ni bazan karbi gidanka ba!” Tsayawa yayi yana kallonta shima babu wani wasa ko tausasa murya yace “idan ego dinki bazai barki ki amshi gidan nan dana baki ba how about nabaki gidan ta dalilin aure!”Dummm! Dummm! Dummm! Gaban Safeerah yawani irin fadi this time around saida ta dago idanunta ta kallesa shima kallonta yake fuskansa babu alamun wasa kowani kwana kwana kai tsaye yace “marry me Safeerah!” Sarawa kanta yayi da bugawa all at the same time batasan sanda ta lumshe idanu ba, is this man okay ko daman ance sojoji nada mental problems ko cus mema yakawo maganan aure? For someone that she just looked yanzu bataga wani sign ko alamu na yana sonta ba ko yakamu da sonta but he is proposing marriage auren mene? Mezatayi da aure? Ita da babu abinda ta tsana kaman aure she promised kanta bazata kara wani aure ba har abada aure daga ina kuma? Juyawa tayi zata bude kitchen tashiga yace “don’t get me wrong! Ba auren ki zanyi ba because ina sonki, or I need wani abu from you or anything nope! On the contrary bakida wani abu dazaisa namaji sha’awan aurenki, I don’t do small foolish girls!” Yayi dan shiru kafin ahankali yace “I told you earlier as a mother you don’t own your life, rayuwanki belongs to children naki, the moment ka haihu you have to give your all for yaranka, hakkine akanki to protect your children, you need to be strong for them, kajure komi for them, this is the same thing your parents did for you, I spoke to iyayenki, I just left d hospital Mahaifinki na asibiti” dawani irin sauri Safeerah tajuyo jikinta na rawa tama kasa magana sai hawaye, calmly yace “he is stable for now, mahaifinki was saying he is ready to support you shima bazai kara komawa gidan ba kuje wherever you lead them to, ina zakikai mahaifinki dakeda serious BP kuje kuna bara? Ina zaki kai small little Waleed? How will you manage ki rikesu? Are you trying to jefa kanki a halaka? Idan karban gidan nan dana baki for free hurts your ego so much then ki karbi gidan a matsayin sadaki and marry me that way ba kyauta bane and it’s yours kinada right akansa kisa Abba da Mama anan, ke da Waleed i will take responsibility naku, you have from yanzu zuwa dare to give me an answer, let’s go to the hospital” kawai yajuya yasa hannu yadauki Waleed yawuce yabude kofa yafice Safeera ta kankare a wajen kanta kaman zai fashe maganganun sa were to heavy for her to chew ta fahimta kuma.
EPISODE 2️⃣3️⃣
Kusan 7mins yana zaune a mota shida Waleed yanama yaron wasa Waleed sai wannan hausan da yar turenci kadan dayakeji yake masa yana amsasa gogar bata fitoba, kofa yaji an bude hakan yasa yadago kansa dayake tinted ne glass na motan tsareta da idanu yayi bakinta is still showing signs na kumbura, idanun nan sunci kuka sunyi suntum but she still looks very pretty, zanin goyon Waleed ne kawai a hannunta, ganin key jikin kofan ta gaba yasa ta murza ta zare, bakinsa ne yayi motsi yana kallonta yace “stubborn girl!” Zagayowa tayi tabude motan Waleed yayi wani ihu akan jikinsa yana murna yace “Ummyy kalle” yajuya sitarin mota ta dauke kai batare data kulasa ba tamaida kofan tarufe, reverse yayi abinsa baice mata ci kanki ba Waleed sai murna yake yana tayasa tuki, saida suka shiga major road yasa hannu daya ya rungumesa gently ajikinsa yace “be good okay” gyadamai kai Waleed yayi yay lamoo ajikinsa, suna shiga asibitin Safeerah tashiga bin ko’ina da kallo idanunta suka ciko da hawaye sosai, parking yayi yabude motan yafito ko’ina a hospital din sojojine yana fitowa few sojas dake wajen suka kame suna saramai, da hannu yamusu alamu su bace yahade fuska Waleed sai kallon sojoji yake da uniform ajikinsu, fitowa Safeerah tayi ahankali ta maida kofan tarufe hakan yasa yawuce rikeda Waleed, lurada bata biye dashi yasa ya tsaya yadan juyo ya kalleta hada ido sukayi kiris take jira tafashe da kuka tana kallonshi idanunta suka kara cika da kwalla, anatse yajuya yacigaba da tafiya hakan yasa da kyar tadaga kafafunta dasukai sanyi tacigaba da binsa harciki wani daki taga yayi knocking ya dakata aka budemai kofan Mama tafito tana ganin Waleed a hannunsa yayi kyau sosai sanye da tufafi masu kyan gaske tace “laaaa Waleed ayoyo taho” tamika hannu cikeda kewan yaron zata daukesa kin zuwa Waleed yayi yamakalkale Salim sosai dadan sauri Safeerah tazo wajen ta rakube tana kallon Mama dataki kallonta cikeda barkwanci tace “kayi babban aboki fa Salim” dan murmushi kadan yayi baice komiba, gaban Safeerah na faduwa sounding so guilty tace “Mama ina wuni” ko kallonta Mama batayiba tajuya tace “shigo Salim Bismillah” tafito ta matsamai gefe shiga yayi ciki Mama tama Safeerah wani mugun kallo haba sai kuka, Mama tanunata da hannu tace “idan banzo na mammakeki awajen nan ba basunana Maryam ba, Safeerah, Safeerah, Safeerah sainaci miki mutunci, kinci sa’a asibiti muke” Mama tajuya zata koma ciki dasauri Safeerah ta matso takama hannunta cikin kuka murya kasa kasa tace “Mama dan Allah kiyakuri wlh bazan karaba” “karya kike cikani, cikani, kuma bazaki shigo dakin nan ba wannan ne hukuncin ki wuce kujeranchan ki zauna kiyi tunanin abubuwan dakikayi da basu kyauta ba, sai kinyi realizing mistakes naki kin fadesu da bakinki sannan zanyi tunani idan zan hakura na yafemiki ko bazan hakura ba, cikani” Mama tajuya fizge hannunta tanuna mata chairs na zaman wajajen, wucewa Safeerah tayi ahankali taje ta zauna, Mama tace “good start evaluating your action mara kunya” tana maganan tabude kofa tashiga tsaf Salim yaji komi amman yayi kaman baisan abinda yafaru ba, yadubi Baba da oxygen ke hancinsa yana bacci yace “ya farka Mama?” Mama na daukan Waleed dayazo wajenta tace “eh ya tashi dazu sun kawo masa abinci bai iyaci ba sai suka basa orange juice ya shanye” gyadamata kai yayi yace “Allah kara sauki bari naje naga Dr Isa” Mama tace “angode Salim Allah yasaka da mafificin alkhairi” yamike tsaye Waleed ya zabura zai sauka daga jikin Mama tarikesa tace “dadina dakai bakasan ya isa ba ko Waleed, ba’a yawo a asibiti likita zaije gani kaji” raurau Waleed yayi da fuska zai fashe da kuka hakan yasa Salim yaji wani iri a ransa saiya kawo hannu yace “barsa Mama” tsare Salim Mama tai da idanu tasaki Waleed dasauri yasauke jikinta kawai yayi hugging Salim, Salim felt something da little hug da yaron na yaro saiya duka ya daukesa yace “ba inda zani don’t be sad” murmushi Waleed yamasa ya kankamesa, kofa yabude yafito Mama tabisu da kallo kaman wacce noticed something.
Yana fitowa yahada ido da Safeerah da idanun nan suka rine da kuka is true fa old habit die hard tun tun tana yarinya daman ta iya kuka yanzu ma still ta iya, aransa yace “stubborn girl” dauke kai yayi yaja kofa yarufe yawuce abinsa batare daya kara kallonta ba tafiya one two three yayi yaji muryanta. “Please kacema Mama tayakuri tabarni inga Baba” juyo da kansa yayi dasauri ta sauke kanta kasa tana wasa da yatsu, murya kasa kasa yace “why should I beg for a stubborn person when I know very well zaki karayin rashin kunyan” girgiza kai tayi tana goge fuska da bayan hannu tace “bazan karaba” tsayawa yayi yakalleta kukan ya isa haka shima yagaji da ganinta tun jiya tana abu daya one thing about Salim is baida kunya and he’s not just super bold he’s extremely bold, dauke kai yayi yawuceta yakoma wajen dakin Safeerah tajuyo dasauri ta kallesa kofan yayi knocking tareda budewa Mama dake zaune gefen Baba tadago kai tana sauke ijiyan zuciya dan tunani take, ahankali yace “Mama amata afuwa! Bazata karaba!” Mama na kallonsa tace “karya takemaka indai Safeerah ce saita kara” ta gefen idanu yaga Safeerah tazo wajen tadan rakube a bangon dake gefen kofan hakan yasa strictly yace “Mama duk randa takarama babba rashin kunya I promise dakaina zan umarci sojoji suzo su dauketa akulleta gidan gyara hali!” Dawani mahaukacin sauri Safeerah ta kalli Salim dake kallon cikin dakin gabanta da kirjinta sun mugun bugawa, wanda yagama cewa ta aure sa ne zaisa a kulleta wato muguntan sojoji daban ne, Mama najin maganan tawani sauko daga gado tace “ubangiji Allah yamaka albarka Salim! Kai kai kai Alhamdulillahi yau ka farantamin rai, ina ja’iran hope tana jinka, ni dama kasa an tadı da ita yanzu an horata ta gyara halinta” dudda yanda idanunta suka kumbura saida ta kwalalosu sosai jin abinda Mama tafada, yace “Mama tace bazata kara ba kibata second chance amata afuwa bari naje” yajuya yawuce batare daya kalli Safeerah ba yana wucewa Mama ta leko ta kalleta tace “Allah yakawomin maganinki bazanji tausayi ba wlh duk randa kika kara zan badake akaiki gidan gyara hali” ahankali tace “bazan karaba kiyakuri” kwafa Mama tayi tajuya takoma ciki Safeerah tabiyota da gudu tai wajen Baba dake bacci ta rungume sa sosai sai kuka Mama ya watsamata harara dudda tabata tausayi Safeerah can be stubborn but abu kadan ke horata, she is sure maganan gidan gyara halin nan ya tsoratata tadauka da gaske suke.
Saida Salim yayi hanyar office na Doctor ya dakata da tafiya ya kalli Waleed saiya tsuntsure da dariya, dariya looks so wired a face nasa dan baisabayi ba the way fuskansa was looking da dariyan yasa Waleed ya kwashe da dariya, ganin yanda Waleed kemai dariya yasa ya gyara fuskansa yayi murmushi kadan yace “matsoraciya!” Abun really crack him up he can’t remember the last time yayi dariya haka, bude office na Dr Isa yayi yashiga.
Almost 10mins yayi an office din suka fito tare zuwa mosque yana rike da Waleed sukaje masallaci sukai salla suka fito yakalli Waleed yace “kanajin yunwa?” Gyadamai kai Waleed yayi hakan yasa yadaukesa yashiga dashi cafeteria na hospital din cake yasaya masa yabasa bayan ya budemasa yafito suka wuce cikin hospital din sallama yayi gaban dakin tareda budewa daga Mama har Safeerah kallonsu sukayi Waleed da kansa yake tafiya hannunsa daya rikeda cake yanaci while dayan hannun nasa Salim na rike dashi gently yace “jeka wajen Mama bari naje office” tsayawa Waleed yayi yakallesa saiya dakatar da cake din dayake ci yayi wani iri da fuska zaiyi kuka Mama ta taso ta daukesa tace “kaifa bakada adalci ko Waleed ka barsa yatafi aiki sainamaka bambooo” Mama tadanmai kallon tsoratar da yaro lamo yayi ajikin Mama sai kawai yafashe da kuka that is so deep wani yirrrrr jikin Salim ya dauka ganin yanda Waleed yafashe da kuka Safeerah ta sauke kanta kasa ahankali, Mama tace “laaaaaa kaga harda hawaye da gaske ne kukan nan yau” adan hankali Salim yace “Mama kawosa” Dasauri Mama tace “mance dashi katafi aiki abinka Salim zaiyi shiru” juyoda kansa Waleed yayi yakalli Salim wani irin kuka yake harda ijiyan zuciya yana hawaye dawani irin sauri Salim yamiko hannunsa Waleed yataho dasauri daukansa yayi feeling very bad yaron na kuka yayi hugging nasa yajuya yace “shiiiii stop crying ya isa ya isa” yabude kofa yafice Mama tabisu da kallo zuciyan Safeerah yayi wani iri this cry confirms to her how much Waleed ke son mutumin nan, sai zuciyanta ya sosu ta tuna Abbati da shine yakamata Waleed nama kuka haka but he hates yaron tun yana ciki, wani tausayin Waleed yarufeta hawaye ya gangaro mata da sauri ta share Mama tace lurada ita but sai tayi kaman bata ganiba,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 15